Showing 33001 words to 36000 words out of 196754 words

Chapter 12 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15409

ta zuba kaya kamar kala biyar, bata yi niyyar tafiya da
yaran ba don haka bata daukar musu ko tsumma ba ta rataya jakarta ta fice. Tana fita ta da su Nawwara
sun shigo falon, ta dauki Ummi ta kama hannun Nawwara suka fice ta rufe kofa ta jefa mukullin a jaka,
suna fitowa ta ja su suka nufi wajen Rabi.

Daga kichin ta amsa sallamarsa ta fito tana goge hannuwanta da dan tsumman kitchen. Nan da nan
Nawwara ta kwace hannunta ta karasa wajenta tana

“Mommy ika kwana.”

Ta rike hannunta ta amsa

“Lafiya kalau mutuniyata, kin tashi lafiya.”

Ta rikota suka karaso daf da bakin kofa inda Saudah take tsaye tana kokarin sauke Ummi tace

“Umman Nawwara shigo mana, unguwa za ku ne?”

Sai da ta kau da kai sannan ta amsa tana ta gatsine fuska

“Ba unguwa za mu je ba gidanmu zan tafi na kawo masa ‘yayansa gasu nan idan ya dawo ki bashi.”

Ta zaro ido tana tafa hannuwa tana fadin

“Subhanallahi. Kin san kuwa me kike fada Saudah? Lafiyarki kuwa? Kina da gidan da yafi wannan ne a halin
yanzu?”

Ta karasa ta dafa kafadarta tare da rike hannunta tace

“Mu karasa ki zauna babu inda za ki ai aure ba wasa bane bautar Allah ne da zai barki ki tafi ba tare da
wani babban dalili ba.”

Tana tura ta tana turjewa a haka har ta kaita gaban kujera ta zaunar da ita, tana ta cika tana batsewa.
Itama ta koma gefenta ta zauna ta rike hannunta don gani take kamar in ta saketa za ta tafi. Ta kwalawa
Zulaiha kira wadda take daki domin yau sai da yamma take da lecture. Nan da nan Zulaiha ta fito Mommy
ta Umarceta da ta dauki su Nawwara su je daki su yi wasa kafin su gama magana ita da Saudah. Ta so ta
tsaya a nan don yanda taga Mommyn ta rike Saudah ta zata wani abun zata yi mata tana daukar Ummi
take fadin
“Mommy lafiya ko?”

“Lafiya, nace ki ja min yara ku tafi.”

Ta juyo wajen Saudah tace

“Ko ma me yayi miki ai hakuri ake yi ba saboda shi ba saboda Allah, kuma ki dubi yaranki ko kin tafi baza
ki sami natsuwa ba idan basa tare dake, zama gidan ubansu shine babban gatan da zakiyi musu.”

“Mtsewwww!”

Saudah ta ja tsaki sannan ta bata amsa

“Ba ni zaki gayawa wannan zancen ba ki gayawa mijinki, ko da yake ai kin san me ake ciki tunda dake aka
hada baki ana tauye min hakki sannan ana nema ace ba’a son abinda zan haifa tunda kin riga kin cika gida
da ‘yayan da ake so. Ba zan juri tsangwamaba gara na tafi gidanmu ko babu komai na san ana so na a can.”

Idanuwanta suka kara fiffitowa tace

“Wai wannan wane irin zance kike yi ne? Idan ma akwai mai tauye miki hakki toh mijinki ne kuma babu
inda za ki je saboda shi aure ai dama zaman hakuri ne musamman a wajen mace.”

Har yanzu tana rike da hannun Saudah, ta mika daya hannun nata ta dauko wayarta da take kusa a kan
kujerar, ta kira wayar Abban. Yana dauka ko sallamarshi bata amsa ba tace

“Me yake faruwa ne Saudah ta kawo yara wai ita gidansu zata tafi?”

“Mtsewww.”

Ya ja tsaki sannan ya cigaba

“Toh ta tafi Mana, wa ya tare mata hanya?”

Ta ce

“Ni na tare domin kuwa babu inda zata. Haba Abba ina zata tafi ta bar yara har biyu, ko babu komai ai ba
girmanka bane ace matarka ta yi yaji.”

“Toh wa ya koreta, ba ita ta zabi tafiyar ba? Allah ya kiyaye hanya.”

Ta yi sauri tace

“Ai kuwa sai dai mu tafi tare mu bar maka yaran a makota.”

“Wannan wace irin magana ce?”

Kafin ya karasa ta cigaba

“In ta tafi me zan zauna in yi? Rainon yaran? Ba zai yiwu ba gata nan a wajena ka yi sauri ka dawo ko ma
me ke tsakaninku ku warwareshi ta koma dakinta in ba haka ba wallahi kafin taje gida ni na je in ka dawo
da ita ka kira ni na dawo.”

Ta ajiye waya, ta dubi Saudah tace

“Kiyi hakuri mu jira shi yanzu zai dawo.”
Ta sa hannu ta share hawayen dake fuskarta ta bude baki za ta yi magana ta jiyo karar wayarta dake jaka.
Ta fizge hannunta da Mommy take rike da shi ta bude jaka ta zaro wayar, tana kallon screen din wayar ta
ja tsaki. Tana daf da tsinkewa Mommy ta karbe wayar ta amsa kiran

“Hello ka yi sauri fa ka zo in ba haka ba wallahi za ka tarar gidan babu kowa.”

Yace

“Ki bani ita.”

Nan da nan ta mika mata wayar, da taga kamar zata bata mata lokaci sai ta kara mata wayar a kunnenta
sannan ta sa hannunta ta dafe don haka Rabin ta saki ta ‘dan matsa.

Daga daya bangaren yace

“Kar ki tafi ko ina ki koma gidan yanzu zanzo.”

Da ya ji shiru yace

“Kina ji na ko Saudah?”

Tace

“Uhmn.”

Ta ajiye wayar ba tare da ta saurari abinda zai ce ba. Ta sa hannu ta sake goge hawayen takaicin da ta kasa
hanashi fitowa ta mike tsaye ta rataya jakarta. Itama Rabin ta mike tsaye tana fadin

“Kiyi hakuri har ya dawo kinji komai zai huce in sha Allah.”

Ba tare da tace mata komai ta juya, kafin ta kai bakin kofa Mommy ta kwalawa Zulaiha kira tace mata

“Kuje wajen Umman, in ta fito kafin Abban ya dawo ki zo ki gaya min kinji Zulaiha?.”

Tace

“Toh”

Suka huce suka bi bayanta, har ta juya za ta shiga kichin ta dawo ta huce bakin gate wajen Bala me gadi ta
same shi yana yiwa fulawoyi ban ruwa. Bayan ta amsa gaisuwarshi tace

“Malam Bala don Allah idan kaga Umman Nawwara ta zo fita kayi sauri ka kirawo ni.”

Yace

“Toh Hajiya an gama in sha Allah. Allah ya sa dai lafiya.”

“Lafiya kalau.”

Ta amsa sannan ta huce ta koma ciki, tana shiga ta huce kichin don ta karasa aikinta tana fadin

“Haka kawai ki tafi ki barmin kananan yara gayyar tsarkin kashi da fitsari ko ni uban wa na tafi na barwa
nawa ‘yayan? Ki zauna kiyi zaman ‘yayanki aure kam mutu ka raba idan wata tsiya yake bani a cikin aure
gashi nan kema ya baki.”
……..

Kafin wani lokaci ya dawo gidan, ya zata tana wajen Rabi don haka can ya fara zuwa da ya tarar bata nan
yace

“Ina zuwa bari naje wajenta.”

Ya juya ya fice.

Yana shiga wajen ya tarar da Zulaiha a falo ita da yara suna kallo, bayan ya amsa sannu da zuwansu ya
huce dakin. A zaune ya sameta a gefen gadon tana kuka harda shessheka ko sallamarshi bata iya amsawa
ba domin ko dagowa ma bata yi ta kalleshi ba. Ya mayar da kofar ya sa mukullin da dama a jikin kofar yake
ya kulle kofar don yanzu Nawwara ta iya bude kofa. Ya karasa kusa da ita ya zauna, ya bita da kallo na yan
dakiku sannan yace

“Toh kuma da aka hanaki tafiya gidan an dokeki ne da kika zauna kina kuka.”

Shiru tayi masa bata amsa ba don haka ya cigaba

“Yanzu ke ba za ki ji kunya ba ki je musu gida da sunan yaji?”

Ta dago ta share hawayenta ta kawar da kanta sannan tace

“Indai ba a ji kunyar yi min wulakanci ba toh ba zan ji kunyar tafiya gidan ubana ba.”

Yace

“Toh an daina yi miki wulakancin, shike nan?”

Ta kara kawar da kanta ba tare da ta ce komai ba. Ya mike tsaye yace

“Shike nan koh, in an jima Sule zai kawo cefane idan kuma akwai wani abu da kike so a hado dashi ki turo
min ta waya.”

Shirun dai ta sake yi masa. Yace

“Baki ce komai ba?”

Ta zumburo baki sannan tace

“Na ji.”

“Yauwa toh bari nayi sauri na koma kasuwar don yau muna da aiki.”

Ya juya ya fice ya barta a nan zaune tana share ragowar kwallarta kuma tana takaici don ba haka ta so ba,
ta saka rai zai yi ta bata hakuri yana lallabata amma shi sai wani aikin girki ma yake bata kamar in tayi
girkin ita ya taimakawa ta ja tsaki a fili ta mike ta huce bandaki don ta wanko fuska.

Yana fita ya huce wajen Rabi ya sameta a zaune a falo, kafin ta amsa sallamarshi yace

“Yanzu ke don abin kunya saboda karamar yarinya ta yi yaji kema sai ki ce za ki tafi?”

Yanda yake magana ya bata dariya don haka ta kyalkyale da dariya yayinda shi kuma ya karaso ya zauna a
kusa da ita. Harararta yakeyi saboda yanda ta bashi takaici yace
“Bafa na son wannan dariyar da kika tsiri yi min idan ina magana sai kace wanda yake miki wasa, in ba a
wajenki ba ina na taba jin mace tayi yaji saboda kishiyarta zata yi yaji abinda ma wasu haka suke so amma
saboda ke ce Rabi har kina fada idan ta tafi kema tafiyar zaki yi.”

Sai da ta ‘bata rai sannan tace

“To in ban tafi ba zaman ‘yayanta zan zauna inyi, na gama rainon nawa ‘yayan tace zata tafi ta bar min
wasu. Tabbas da ta tafi za ka dawo ka tarar nima na tafi in ta dawo sai na dawo, amma tunda Allah ya sa
bata tafi ba toh in sha Allahu aure mutu ka raba Allah ya karo zuri’a ta gari.”

Da kyar ya hadiye malolon da ya tokare masa makogoro don maganganun Rabin sun bata masa rai. Fuuu
ya tsahi ya fice daga falon ya barta a nan zaune tana dariya. Har yaje kasuwa yana tunanin yanda Rabi ta
canza gaba daya daga lokacin da ya auro Saudah, da ya zata ya santa ya haddace dabi’unta amma kullum
sauya masa take yi, ya kasa gane kishi ne ko kuma tsabar kiyayya ce da take yiwa kishiya. A haka komai ya
huce, Saudah ta cigaba da rainon cikinta. A daidai lokacin Nawwara tana da shekaru uku yayinda Ummi
take da shekara ‘daya da rabi.

…….

Tun da suka fara aiki a Abuja su hudu suka kama daki daya duk da ba wajen aikinsu daya ba, dukansu yan
Kano ne kuma basu da aure. Aminu Ahmad ne kadai yake da mota a cikinsu don haka duk lokacin da zasu
zo Kano sai su taho dukansu a motarsa. Yau ma kamar kullum sun kamo hanya suna tafe suna hirarsu
kuma kowa yana chatting a waya. Status ya budo yana kallon na mutane, hannunshi ya kai kan status din
Farida Bukar, wata ‘yar ajinsu a jami’a. Set ne na zobe da warwareya masu ruwan gwal masu kyau sosai
ta dora tana siyarwa, sun bashi sha’awa kuma ya san Mommy tana son zobe don haka ya ji yana son ya
siya mata. Ya tamabaya ta gaya masa kudin kowanne set naira dubu tara, ya nuna mata wanda yake so da
sharadin zai zo ya gansu a fili sai ya bata kudin ta karba, ta turo masa kwatancen a kan da ya shiga Kano
zai tsaya ya karba. Suna shiga Kanon kuwa ya sauka a unguwarsu Farida ya duba zoben ya tabbatar da
kyansu sannan ya biya. Har ya karba zai tafi ya tsayar da ita ya tambaya

“Abun nan wai gold ne?”

Tayi dariya tace

“Gold din zan sayar maka dubu tara? An dai kwaikwayi gold din ne kawai aka yi wanna.”

Yace

“Yayi kyau sosai.”

Ya karba ya huce gida. Sai bayan magriba sannan ya isa gidan ya same ta a falo ita da Ahmad, Salim, Khalifa
da Auta suna hira. Suka amsa sallamarshi auta ya tashi ya karbi jakar kayanshi ya kai daki yayinda Khalifa
ya kawo masa ruwa. Bayan ya zauna sun gaisa da Mommy ya mika mata yar karamar ledar da aka saka
awarwaron nan a ciki yace

“Mommy wannan naki ne?”

Ta karba tana washe baki tana fito dasu daga leda, ta bude kwalin ma ta zaro su duka. Ta zira warwarayen
guda biyu sannan ta zira zoben ta daga hannun tana kara dubawa tana fadin

“Iyye, kai gaskiya na gode Allah yayi maka albarka ya kara arziki.”
Yace

“Amin Mommy.”

Yana ta murmushi ganin yanda itama take ta kara dubawa tana jin dadi. Auta da yake zaune a kusa da
kafarta ya kamo hannun nata yana fadin

“Iyye! Su Mommy an sa daham.”

Duk suka kyalkyale da dariya ta doki kan auta tace

“An saka din sarkin tsokana, baki abun magana da yake na zama kakarka.”

Yace

“Aah murna fa nakeyi Mommy.”

Ya juya ya dubi Baba yace

“Ya Baba ina tawa tsarabar?”

Ya mika masa ragowar ruwan robar da yake sha yace

“Gashi.”

Ya sa hannu biyu ya karba ya fara bude ruwan ya sha sannan yace

“Bari in sha hannun da ya baka ruwan faro ai wataran zai baka ice cream harda kazar Yahuza.”

Suka tuntsire da dariya.

Duk wannan hirar da sukeyi a kunnen Zulaiha tana manne a jikin kofar dakinta tana jiyosu kuma tana leko
su ta kofar mukulli, wanda daman kullum indai sun zauna suna hirarsu to tana labe tana kwashewa.

Washegari ya kama ranar Asabar don haka ana gama cin abincin safe Zulaiha ta fito zata tafi wajen Saudah,
ta sami Baba a falo bayan ta gaishe shi ya dauko alawa a leda ya bata yace ta kaiwa su Nawwara, ta karba
ta fice.

Tana shiga bayan sun gaisa ta mika mata ledar ta gaya mata Baba ne yazo jiya ya kawo wa yara. Saudah
ta tabe baki tace

“An gode, na ji shigowarshi ai.”

Tace

“Allah sarki.”

Sauda ta sake cewa

“Ku kuma me aka kawo muku tsarabar Abujan?”

Ta tabe baki tace

“Mu a su wa? Ya dai siyowa Mommynshi warwaro da zobe na gwal.”
Ta zaro ido

“Gwal fa kika ce?”

“Kwarai kuwa da idona na ganshi dankarere kuwa.”

Ta yatsina baki sannan tace

“Yanzu shi Baba albashinsa har ya kai ya sayi zobe harda warwaro na gwal, lallai.”

Zulaiha ta danyi dariya sannan tace

“Idan albashinsa bai kai ba ai Abbansu ya tara.”

Ta tabe baki tace

“Hakane kam.”

Suka dan yi shiru daga baya kuma ta tashi ta tura katon cikinta ta huce daki ta bar Zulaiha a nan ita da su
Nawwara. Tana ta mamakin yanda za ayi ace albashin Baba ya sayi zobe da warwareya guda biyu na gwal,
ta san tsadar da gwal yake yi don haka ta san tabbas da kudin Abban aka hada aka yi wannan sayayyar ita
kuma tana zaune bata da ko dan kunnen gwal.

Ranar da girki ya zagayo kanta kuwa sai da ta bugi cikinsa a kan haka. Duk yanda ta kai ga so taji ya ce
mata an sayi gwal ya ‘ki, ya kafe a kan babu yanda za ayi ba Baba ko wani ne ma ya bawa Rabi kyautar
gwal bata gaya masa ba don haka babu wannan zance. Da dai ta ga ba zai amsa ba sai tace

“Toh ni yaushe za ka siya mi dankunnen gold din da kayi min alkawari tun haihuwar Nauwara?”

Yace

“Na gaya miki in sha Allah idan na sami hali zan siyo muku don kin san dole sai dai na sayi guda biyu ko?”

A haka ta hakura da zancen tana jiran lokacin da za ta ga wannan gwal din da idonta a hannun Rabi, tabbas
itama sai an saya mata.
EPISODE 9



Tun cikinta yana da wata bakwai tayi scanning likita ya gaya mata ‘yan biyu ne a cikinta mace da namiji.
Tana sane taki gaya masa saboda bata san me zai ce ba, tunda ya nuna mata baya son haihuwa ta daina
yi masa zancen wannan cikin da yake jikinta sai dai fa idan babu yanda zata yi. Kawai ya tambayeta lokacin
da zata haihu kuma ta gaya masa. Ya saba hada akwati na kayan jariri da maijego duk lokacin da za a yi
masa haihuwa don haka yanzun ma su ya hada, sai da ya cika akwatin da kayan baby sannan ya ‘dora mata
leshi me kyau da tsada guda daya da atamfa Cote D’Ivoire turmi daya harda mayafi da takalmin wadanda
suka dace da leshin. Bayan ta gama duba kayan tayi godiya sai kuma ta kawo maganar tana son shadda
kuma ba siyo mata take so yayi ba don kanwar babarta tana siyarwa don haka kudi zai bata ta siya, babu
yanda ya iya haka ya kawo naira dubu goma kamar yanda ta nema ya bata.

Ita kuwa Rabi tunda amarya take haihuwa bai taba yi mata kaya don ta sabunta ranar suna ba. Lokacin da
aka haifi Nawwara ne ma ta tambaya da wasa tace masa ina nata kayan fitar sunan. Ya dubeta yace

“Me haihuwa da ban ke da saka kayan fitar suna, wato kinci zamaninki za ki ci na wata.”

Dariya kawai tayi ta bar zancen don itama zolaya takeyi, tunda shi din mutum ne mai yawan yi wa iyalansa
sutura ko bai yi haka kawai ba in dai Sallah ta zo to kowa zai samu akalla kala uku, don haka in dai sutura
ce toh tana da su sosai.

Tunda satin da zata haihu ya kama da kyar take jan kafa saboda tsabar nauyin da cikin yayi mata don haka
ta sa shi a gaba da magiya ya kai Ummi da Nawwara wajen Ummanta tunda an riga an yaye Ummi; in ta
haihu ranar suna sai a taho da su. Duk da baya son kai yaran gidansu dole ta sa ya amince domin shi ma
ya ga yanda cikin yake mata wahalar dauka sannan kuma ya tabbatar Rabi ba zata rike mata yaran nan ba
ko na kwana daya.

Tare da Zulaiha ya kaisu asibiti ranar da zata haihu, sai da suka isa sannan ta kirawo Ummanta ta gaya
mata tana asibiti, nan da nan kuwa aka turo mata Umma Balaraba kanwar mahaifiyarta saboda Kaka da
Ya Ummu su Abban ya hanasu zuwar masa gida. Zulaiha na nan tsaye tare da Umma Balaraba aka fito aka
ce musu ta haifi ‘yan biyu mace da namiji, kafin me fadar haihuwar ta juya Umma ta rangada guda ta zaro
naira dubu daya ta bawa me fada musu haihuwa tana fadin

“Baiwar Allah dole na baki tukuici irin wannan albishir haka.”

Nan da nan Zulaiha ta kira Abban ta gaya masa abinda aka samu. Kafin wani lokaci ta fara kiran dangi tana
gaya musu an haifi ‘yan biyu, namijin aka fara haihuwa don haka kowa sai son barka an haifa musu Baffa
Hassan. Yana tashi daga kasuwa ya huce ya ga yaran da aka haifa masa, likita yace masa tana bukatar hutu
don aka sai gobe za a sallameta. Ya bar su nan ya tafi gida. Sai da ya shiga gidan sannan yake gayawa
Mommy haihuwar da ta tambaye shi Saudah.

Yace

“Au Zulaiha bata gaya miki bayan ta gama gayawa dangi, har su Atiku fa dake Kaduna ta gaya musu suna
ta murna wai am sami Baffa Hassan.”

Itama nan da nan ta nuna murnarta tana fadin
“Eh gaskiya an sami Baffa Hassan toh macen Inna Hajara ce ko Baba Yalwa? Ma Sha Allah. Allah ya raya
mana su.”

Yace

“Toh ai

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login