Showing 87001 words to 90000 words out of 196754 words

Chapter 30 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15379

dai shi na gani, shekara talatin ko yaji bata taba yi ba amma ace wai yau an koreta. Toh amma a
hankali za mu bi in sha Allahu za a same ta. Kin duba wajen kawayen naku kuwa?”
“Wallahi duk na bincika, kin ga Salma Habu ita ma ta shiga tashin hankali, ga shi ko a waya an rasa Bibi.”

Jimawa kadan Mubarak ya kirawo su a waya ya sanar da su sun fito don haka suma suka shiga motar
Yaya Shafa suka kama hanya.




Tunda aka wayi gari ba’a ga Mommy ba har yau Baba karami basuyi waya da Abba ba, yana so ya kirawo
Abban amma bai san me zai ce masa ba. Tunda yake a rayuwarsa bai taba zata Abba zai iya yiwa
Mommy haka ba, ko ba a raga mata don komai ba ai a raga mata dominsu. Ji yake kamar shi Abba
yayiwa wannan cin fuskar, duk da bai san me zai cewa Abban ba amma yana so ya kirawo shi don ya
nuna masa ya san me yake faruwa. Bugu daya Abban ya amsa yace

“Babana ka ji abinda yake faruwa ko?”

“Eh Abba, har yanzu ba a ga Mommyn ba ko?”

“Eh Baba, muna dai ta rokon Allah, zuwa jimawa ma police station za je ma kai rahota ko Allah zai sa a
dace.”

Suka dan yi shiru kamar masu kirga numfashin juna. Abba me ya karya shirun yace

“Ka dinga bawa kannenka hakuri, Yusufa ya fi kowa shiga damuwa, kuma ka dinga addu’a, in sha Allahu
tana lafiya ina ji a jiki na za a same ta.”

Yace

“Toh Abba.”

Suna ajiye waya Baba karami ya ja tsaki yana fadin

“Toh wa ya janyo mana wannan masifar? Da ka ce mu dauketa baka son ganinta da duk ba’a sami
wannan matsalar ba.

Ya ajiye wayar ya ci gaba da shirin tafiya aiki, in sha Allah shima ranar Juma’ah da safe zai tafi yaje ya
gano abinda yake faruwa.




Da yake ta gama jarrabawa yau ‘yan makaranta kawai ta shirya, ba ya cikin yanayin da zai sa Madu ya
kaisu don haka shi ya daure ya kaisu. Da wuri ya fito don yana so ya hada da su Khalifa da Auta suma ya
kai su. Yana dawowa yayi shirinsa na tafiya zuwa kasuwa duk da ma baya son zuwa amma haka dai ya
daure ya shirya ya fito. Bayan ya zuba komai nashi a mota sai ya koma falon Saudah ya zauna yana jiran
zuwan su Munzali don tun dare ya gaya masa za su zo. Yana nan zaune yaji shigowarsu don haka yayi
hanzari ya fito daga falon yayi musu iso zuwa falon Mommy. Madu ne kawai da Salim a ciki sune ba su
da makaranta suna kwance a falon, suka tashi suka yi musu sannu da zuwa suka koma gefe suka zauna.
Gabaki daya suka gaisa amma shi Baba Mubarak da kyar ya mikawa Abba hannu suka gaisa saboda
yanda yake jin haushinsa, shi kuwa Abba kwantar da kai kawai yake yi saboda ya san shine da laifi. Suka
dan yi shiru Abban da kanshi ya karya shirun ya dubi Munzali yace

“Baku same ta ba kenan?”

Kafin yace wani abu Yaya Shafa ta bashi amsa

“Da mun same ta ai ba za ka gan mu ba ita ba Abban Khalifa.”

Mubarak ya bude baki cikin fushi yace

“Toh ya ma za ayi ace da azumin man ka cewa mace wadda ba jiya ka aurota ba wai ta fice maka daga
gida, wannan ai ba daidai bane. Ga shi nan yanzu ai duk mun shiga rudani ko? Ta fice maka daga gida,
gidan ai yayi maka dadi ko?”

Kafin a bashi amsa suka jiyo sallamar Baffa Hassan a kofar falon, kafin su amsa sallamar tashi ya shigo.
Madu ne ya fara mikewa ya karaso da Baffan ya nuna masa kujera domin ya zauna, ya dube shi yace

“Ba zan iya zama sama ba Muhammadu, matsa na zauna a kasa.”

Nan ya zauna a kan kafet inda Madu ya tashi. Abban ne ya mike ya dawo kusa da shi

“Baffa ina kwana.”

“Ban ganshi ba Usmanu, ka ji. Ina ruwanka da kwanana ko kasan inda na kwana ne?”

Yaya Shafa ce ta katse su da ta dawo kasan tana gaida Baffa, da yake ita ta sanshi. Bayan ya amsa
gaisuwar tata sai ta sami gefe daga kasa itama ta zauna, gaba dayansu suma suka gaisheshi sannan suka
zauna a gabanshi. Ya mika hannu ya kama hannun Munzali yace

“Yayanta ne ko?”

Ya daga masa kai alamar eh

“Kuyi mana uzuri mun yi muku wauta, in Sha Allahu za a ganta cikin koshin lafiya. Don Allah kuyi hakuri
mubi a sannu.”

Kafin su bashi amsa ya dubi Abba wanda yake zaune kanshi a kasa yace

“Usmanu, da Raina da lafiyata amma ka kori yarinyar nan ba tare da ka yi shawara da ni ba Usmanu? Me
na gaya maka? Nine ubanta idan ta yi maka laifi ka gaya min ashe baka ji ba Usmanu? A kwana a tsahi
babu ita amma ka kasa gaya min? To yanzu ka ji dadin gida da ta tafi ko? Kai na gayawa idan ka biyewa
son zuciya za ka rushe iyalanka da ka dauki shekaru kana ginawa, gashi da kanka ka sa kafa ka ture
foundation din ginin ya rushe ko Usmanu? Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiuna.”

Hawaye suka biyo fuskar Baffan ya sa gefen Babbar rigarshi ya goge. Abba ya bude baki da kyar yace

“Baffa kayi hakuri in Sha Allahu za a ganta.”

“A ina za a ganta Usmanu? A ina? Tana nan a dakinka iyayenta suka rasu, da kai aka binnesu kuma aka
sayar da gida aka raba gado, toh in ka ce ta tafi gidansu gidan su wa za ta je Usamanu? Kwararo?”
Yaya Munzali ne ya yi gyaran murya yace

“Kayi hakuri Baffa, in Sha Allahu za a ganta.”

Ya sunkuyar da kai yayi shiru na dan lokaci sanna ya dago kai yace

“Toh a ina za a ganta dana?”

“In sha Allahu za a ganta.” Shafa ta sa musu baki.

“Duk can dangi ko wajen iyayen naku kun duba babu labarinta.”

“Duk mun duba Baffa suma duk bata je ba, har kawayenta ma duk an tambaya.”

“Ikon Allah. Toh sai dai mu dage da rokon Allah kenan kuma yanzu sai ku tashi ku tafi police station ku
kai rahota da gidajen radiyo.”

“Haka ne Baffa.”

Munzali ya bashi amsa.

“Allah ya warware wannan al’amarin alfarmar wannan wata da muke ciki.”

Gaba dayansu suka amsa

“Amin.”

Baffa ne ya fara mikewa Madu ma ya mike domin yi masa rakiya, Ya dubi Munzali yace

“In Sha Allahu za a same ta, mu dai cigaba da rokon Allah.”

Ya mika masa hannu suka yi sallama, haka ma ya mikawa Mubarak. Abba ya tashi domin yiwa Baffa
rakiya, ya dubi Munzali yace

“Bari in zo.”

Bayan sun fice Yaya Shafa ta dubesu tace

“Muma ai sai mu tashi mu tafi, ko me kuma za mu Jira?”

Gabaki dayansu suka mike suka biyo bayan su Abban. Tijjani da ya kawo Baffa yana can waje don haka
gate Baffan ya nufa Abba ya bishi a baya yana magana yayinda Madu ya shige gaba don ya Bude masa
kofa.

“Baffa.”

Ya juyo ya dubeshi yace

“Ba zan saurareka ba Usmanu, idan kana so da ni da kai muyi magana ka nemo min yarinyar nan, ka ji na
gaya maka.”

Ya fice ya barshi a nan tsaye. Su Munzali suka karasa inda yake Munzalin ya mika masa hannu yace

“Mu zamu huce, Shafa za ta bayar da cigiya a gidan radiyon jiha da kuma freedom radio.”
“Toh Babu laifi, nima yanzu zan fita na je police station din har wajen ‘yan civil defence ma dama tun jiya
mukayi magana da area commander dinsu na division 7.”

“Toh Allah ya sa a dace.”

Mubarak ya matso ya mikowa Abba hannu yana fadin

“Idan ba’a ganta ba gaskiya za mu samu matsala da kai Alhaji Usmanu, don bazan yarda ba sai inda karfi
na ya kare.”

Ya zare hannunsa ya huce ya barsu a nan. Shi Abban ma ya rasa mai zai ce, suka huce shi za su fice yace

“Baraka.”

Ta juyo ta tsaya tana sauraronsa, yace

“Yanzu babu wani clue na inda kike tunanin Rabi za ta je? Ni fa wallahi na ma zata wajenki ta tafi.”

“Toh, Suma su Yaya jiya kirana da suka yi sun zata tana can ni kuwa rabo na da Rabi tun dawowarmu fa
daga Umrah, ga shi su Salma Habu ma duk babu wanda ya ganta.”

“Ikon Allah, wannan abu sai dai muce Allah ya warware.”

“Amin. Bari na huce kar na barsu suna Jira na.”

Yace

“Don Allah ki bawa su Yaya hakuri, wallahi tsautsayi ne. Ke kin san Ina son ‘yar uwarki ya za ayi da
gangan na bari wani abu ya sameta, wallahi na zata gidan Shafa za ta tafi.”

“Hmmn!”

Ta huce ta barshi a nan tsaye. Da kyar ya ja kafa ya koma falon, addua kawai yake yi Allah ya sa a ganta.
Baya son yayi tunanin ko sace ta aka yi saboda yanda wannan tunanin yake firgita shi. Haka ya shiga
falon ya zauna yana ta Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun, a nan falon ya kashingide ya ma rasa me zai yi,
yana nan zaune ya kirawo area commander na ‘yan civil defence wanda dama mutuminshi ne ya sanar
da shi cigiyar Rabi. Haka ya daure da kyar ya dauki mukullin motarshi ya fito, har ya zauna ya bawa
motar wuta sai kuma ya ji ba zai iya ba. Don haka ya fito daga motar ya shiga falon Mommy, babu kowa
a ciki don haka ya kwalawa Madu kira. Yana fitowa Abban ya jefa masa mukullin motar yace

“Muje gidan Baffa.”

Babu yanda ya iya domin tun da su Baba Munzali suka zo ya kula kamar Abban baya jin dadi don haka ba
tare da ya ce komai ba ya chafe mukullin ya sa takalminshi suka huce. Haka suka yi tafiyar babu wanda
yace komai domin shi Abban ma kanshi ya kwantar a kujerar motar yake kallon waje. Suna shiga suka
sameshi a tsakar gida da Baba Yalwa suna mai da zancen, ta mike tayi musu sannu da zuwa ta basu
wajen suka zauna. Baffa ya kawar da kanshi gefe ya ki kallon Abba

“Ka yi hakuri Baffa, in Sha Allahu za a ganta.”

“Ba zan yi hakuri ba Usmanu har sai ka nemo yarinyar nan.”

Ya sunkuyar da kai yayi shiru, sai da Baffa ya gaji da shirun sannan yace
“Usmanu, matarka ta rufin asiri kayiwa haka saboda ta ce ba za ta rike maka yara ba, toh ai ba aikinta
bane. Yaran da ta Haifa maka ta rike su bisa amana gasu nan duk wanda suka raba sai son barka kuma ka
auro wata ka ce sai ta rike mata nata yaran, har kuma ka koreta saboda ta ki. Wannan wane irin lissafi ne
Usmanu? Ai ko don yaranta ayi musu kara a zauna da uwarsu.”

“Baffa in Sha Allah za a ganta. Wallahi Baffa tsautsayi ne, ni ma na zata gidan yayarta za ta tafi.”

“Uhmmn.”

Sukayi shiru na dan lokaci Baffa ya dubi Madu ya yake gefen damanshi yace

“Muhammadu kuyi hakuri ka ji, da kai da ‘yan uwanka. In Sha Allahu babu abinda zai sami mahaifiyarku
za a ganta, nan ma na gayawa liman a ci gaba da rokon Allah. Idan Baba karami ya zo kace ya zo ina
nemansa, ku hadu ku ginawa uwarku daki don in ta dawo ta sami wajen zama.”

Abban da kanshi yake a sunkuye ya dago a firgice yace

“Baffa! Baffa ga dakinta kuma.”

“Yo wane daki kuma tunda an fara yi mata gori.”

“Kuskure ne ai Baffa in Sha Allah ba za a sake ba.”

“Toh Allah ya sa.”

Suka dan yi jim sannan suka sallami Baffa, Abba yace masa za su je police station son su bada rahoto
suka fice. Bayan sun fita ne kuma Baba Yalwa ta dubi Baffa tace

“Kana ta yi masa fada a gaban Yaro Mallam”

“Ina sane, shima yaron ai namiji ne don ya san ba haka ake busar iska ace da mace ta fice daga gida ba.
In bai ga an yiwa ubanshi fada ba sai ya dauka karamin laifi ne.”

“Hakane kam.

Haka suka je police station suka bayar da rahota harda hotunan mommy da duk wasu bayanai da ake
bukata, bayan sun fito daga police station sun zauna a mota Madu ya dube shi yace

“Kasuwa za mu?”

Ya duba agogon wayarshi ya ga karfe uku saura

“Ba zan iya zaman kasuwa ba Muhammadu muje gida na huta, ai munyi waya da manaja tun safe.”

Ya karkata kan mota suka huce gida. A bakin gate ya tsayar da motar yana fadin

“Zan je post office na karbo wasu kayana.”

Da yake tunda ya saba da manajan gym din da Abba yake zuwa sai ya nemi Abban ya bashi jari ya fara
shigo da sport wear da takalma na motsa jiki yana siyar musu, gashi yanzu har su Baba duk suna samar
masa customer. Don haka takalma ne da yayi order daga China suka zo ta post office yake son ya karbo,
kuma ya san in dai yana gidan tunda Abban ya ga ya mike ana jimawa zai ce ya je ya dauko su Nawwara
a makaranta shi kuma ba zai je ba. Ya biyo bayan Abban suka shigo ya kirawo Salim suka rufe gidan suka
fice da yake khalifa ma yana da mukulli.

Mai wanke wanken ta da wuri take tafiya, in ta zo wajen goma na safe ta gyara mata gidan sai kuma ta
tafi sai gobe don akwai wani gidan da takewa aikin yamma. Don haka ita kadai ya samu da ‘yan biyu a
falo tana shafawa Baffa magani a hannusa, bayan ta yi masa sannu da zuwa ya zauna a falon ya dube ta
yace

“Police station muka je muka basu rahota ko Allah zai sa a dace.”

“Allah ya sa a dace.”

Ya dan zauna yana yiwa Hanan wasa sannan ya tashi ya dube ta yana fadin

“Bari na je na kwanta ko zan samu kaina ya daina ciwon nan da yake yi.”

Ta bi bayan shi da kallo sai da ya rufe kofar sanna tace

“Sahibarka ta bata ai dole kayi ciwon kai.”

Tun wuri ta fara shirin dora abun buda baki tunda da yawa za ta yi, kosai da kunu ta shirya za ta yi sanna
kuma da dashishi da Miya. Baffa yana bayanta a goye saboda in ta barshi haka zai yi ta fama hannunsa
yana rigima, yayinda ita kuma Hanan take kaiwa da kawowa a kicin din. Sai da ta ji Kiran la’asar sannan
ta duba agogo ta ga karfe hudu saura, lokacin dauko Yan makaranta ya yi. A hankali ta tura kofar dakin
Abban ta shiga, tun kafin ma ta karasa ta jiyo minsharinsa don haka ta san bacci yake yi. Ta zauna a
gefen gadon sannan ta dafa shi a hankali ta na kiran sunanshi. Ya juyo yace

“Ya aka yi ne?”

“Lokacin dauko su Nawwara daga makaranta ya yi ko za ka dauko su?”

“Kai na ciwo yake wallahi, ba zan iya ba gashi Madu ya fita da motar.”

“CR-V fa tana nan.”

“Mukullan motar duka suna hannun Madu. Akwai kudi a durowa ki bawa Bala kudin mota ya dauko su
ko kije ki dauko su.”

“Bala fa nan ya leko yace min in ka dawo in ce maka ya tafi gida sai bayan la’asar zai dawo, ni din kuma
haka zan tafi da ‘yan biyu dauko su?”

Ya tashi zaune yana dafe kai idanuwanshi dun sun kankance saboda bacci da ciwon kai

“Don Allah idan bana nan ya za ki yi?”

Ta bishi da kallo me cike da tambayoyi daban daban, ya kara dafe kanshi ya za me ya kwnata ya juya
mata baya. Yanda yayi haka ta san ba zai saurareta ba don haka ta taso ta fito. Haka ta saka hijabi da
goyon Baffa ta ja hannun Hanan suka fice daga gidan, tana fitowa ta hango su Auta a tsallaken titi shi da
Khalifa ta dauke kai. Tsabar wulakanci a dauko mata yaran ma ya gagara, ga shi ance sai ta dafawa kowa
abinci. Wallahi da ba don tana son ta dan lallaba Abban ba da yau sai ta yi masa tijara. Anya kuwa
wannan ma zai lallabu, an ce ta samu ta lallaba shi ta janye hankalinshi amma tun yanzu ta fara kosawa
don ta ga kamar wani ko in kula yake yi da ita. Haka ta huce ta daukosu ta dawo sannan ta koma kicin ta
cigaba da aiki. Tana yi tana mitar in aka kwana biyu dole ma ya barta ta dauki me aiki wadda za ta dinga
kwana son ba za ta iya wannan wahalar ba, don ma yanzu ta gama jarrabawa kuma babu lecture.
EPISODE 21



Ko da aka sha ruwa ma haka suka sake yi mata, dukansu suka fito suka Bai Abban masallaci sannan ta
jiyo Madu yana bawa Bala abincin da ta dafa musu. Ta Sha takaici kwarai, dole ta koyarwa yaran nan
hankali musamman wannan tsageran Madun da take jin ya kusa ya fara kai mata duka domin shi sai ya
kalli kwayar idonta sannan yake mata rashin kunya kuma gashi ta ga kamar Abban ma tsoronshi yake ji,
don in dai laifi na Madu ne baya ma son a fada balle ya tsawatar. Bayan sun fita da safe ma tana kallo
Salim ya fita da abincin sahur dinsu ya bayar. Tana so ta daina yin abincin da su amma bata san me za ta
cewa Abba ba, don haka haka ta daure ta sake yin abincin da su Kuma suka sake bayarwa. Ga shi Kiri kiri
an rasa mai dauko mata yara daga makaranta, da yake ma daga wannan satin za su yi hutu.

Tun daga ranar Laraba da Madu ya kai Abba gidan Baffa ya daina binshi kasuwa, idan Abban zai fita sai
Madun yace makaranta zai je wajen supervisor dinshi na project shi kuma Abba sai ya bar masa motar ya
dauki dayar ya tafi kasuwa. Yau ma Juma’ah haka aka yi, Madun tun wuri ya fice daga baya kuma Abban
ya tafi kasuwa. Yana kasuwar ta kirashi a waya, bayan ya amsa sallamarta tace

“Ban ga mukullin store ba na wajena ga shi ina so na debo dankali.”

“Garin yaya baki ganshi ba, ba yana jikin mukullin dakin ki ba?”

“Ai na cireshi tun da na fara barin Zulaiha, ina cire na store na bata saboda abinci sai na tafi da na
dakina.”

“Mtseww, toh yanzu ya kike so nayi miki? Ni bani ma da mukullin store din.”

“Uhmmn to ko su Salim za ka yiwa magana su bani na wajen Mommy, in ba haka ba zan yi daren abinci
fa.”

“Hakane, ki tambaye su mana ko basa gidan ne?”

“Eh ina jin duk sun fice don na je kofar a kulle take.”

Sukayi sallama ya kirawo Salim wanda shi kadai ne a gidan ya umarceshi ya bata

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login