Showing 1 words to 3000 words out of 196754 words
Chapter 1 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
© 2022
Mallakar Sakina Yazid
Ba a yarda ayi amfani da wannan rubutun ta kowacce hanya ba tare da izinin marubuciyar ba.
EPISODE 1
Ta riga ta saba duk tsahon rayuwarta idan ta tashi da asuba bata komawa bacci. Bai taba bari ta dauki mai
aiki ba ko da wasa, don haka ta sabarwa kanta fara hidimar gida da ta yara da zarar ta sallame sallar asuba;
tunda babu inda take zuwa. Har kawo yanzu da yaranta suka girma kuwa. Duk su shidan gaba daya maza
ne kuma sun saba taimaka mata, amma wannan bai chanza ba. Karamin cikinsu mai kimanin shekarun tar
shima ya iya yiwa kansa shirin makaranta da taimakon yayyensa. Nan da nan kowa yasa hannu a gyara
gidan kafin 7:30 babansu ya kwashe su zuwa makaranta. Yan higher institution kuma su uku kowa ya kama
hanyarsa lokacin da ya shirya.
Har kawo shekaran da ta gabata ya kara aure bata fasa hakan ba. Da yake kowacce da bangarenta ba
kullum ma suke haduwa, don haka ko da ba itace da kwana ba babu abinda ta sauya a dabi’unta.
Doguwar riga ta sanya bayan da ta yi wankanta ta zauna a kan kujera me zan mutum uku tana shan shayi
kuma tana ta danne danne a wayar ta wadda ta kunna rediyo a ciki. Auta da yayyensa biyu kuma suna
zaune a dinning table suna cin abincin safe, kowannensu sanye da uniform. Da yake mutum ne mai sanin
ya kamata toh ko ba wajenki ya kwana ba idan gari ya waye zai shigo ya duba ki da yara, ya tabbatar komai
lafiya sannan ki bashi list din abun chefane wanda idan ya fita zai bawa yaronshi na kasuwa ya kawo domin
a sarrafa.Haka ya shigo daga wajen amarya a shirye da mukullin mota a hannunsa ya same su. Bayan amsa
sallama yaran duka suka gaida shi
“Abba ina kwana”
Ya amsa su cikin fara’arsa, domin shi din mutum ne mai yawan wasa da raha.
Nan da nan suka kwashe kwanukansu suka kai kitchen kowa ya dau jakarsa suka fice domin su jirashi a
mota. Nan suka tarar yayansu Baba karami ya gama wanke motar.Suna fita ya mayar da hankalinshi kan
uwargida yana daga tsaye ita kuma tana zaune tana shan shayinta.
“Toh mu zamu wuce, Lalo zai kawo chefane. Babu wani abu ko?”
Ya fada yana daga tsaye.
Ta ce
“Babu komai. A dawo lafiya, Allah ya bada sa’a”
“Amin ya Allah.”
Kamar zai fita sai kuma ya dan tsaya. Ta dago daga kallon wayar dake hannunta ta kalle shi da
murmushinta ta ce
“Ko shayin zan sammaka ne naga ka kasa tafiya. Ko kuma dai kasuwar zan raka ka.?”
Shima yayi dariya ya ce
“Bayan kin shanye sannan kike min tayin kurbar karshe? Na ki din.”
Ya dan nisa ya ce
“Ni jiya da daddare tuwo kuka dafa ne?”
Da dan mamaki a fuskarta ta ce
“Tuwo kuma? A’a wallahi. Taliya ce Baba karami ya dafa mana duka muka ci.”
“Kin dai rantse baza ki daina sa samarin nan girki da wanke wanke ba ko? Ai shi kenan Allah ya sauwake.”
“Toh ai su Allah ya bani Yallabai, wata rana duka baza mu yi ba in sha Allah.”
Ta fada da muryar lallashi kamar yanda ta saba bashi hakuri duk lokacin da yayi mata wannan korafin.
“Toh yanzu yaushe za ki yi tuwon?”
“Kai jama’ah, toh ai ka ga yau ma baka nan don haka ni da yara tun jiya muke tanadin shinkafa da wake.
In dai tuwo kake so in aiki ya zo kaina zuwa jibi in sha Allah sai na yi maka tuwon.”
Kamar zai tafi sai kuma ya tsaya daidai lokacin ta kurbe shayin ta ajiye kofin a kan hannun kujera.
“Kanwarki ce dama bata jin dadi ta kasa cin abinci tuwon kawai take so. Ko za ki dan tuka mata ko kadan
ne ta dan karya tun jiya rabon da abinci ya zauna a cikinta.”
Tace
“Allah ya raba lafiya. Zuwa jibi idan da rabonta in na tuka tuwon ta ci.”
“Yanzu ke karamar yarinyar tana fama da laulayin shine bazaki yo mata tuwon ba.”
Ta dan yi dariya
“Ai ta girma tunda ta auri mijin babba. Don Allah in tambaye ka ma, ni da nayi nawa laulayin wa ya dinga
bani tuwon? Ni ce nayi mata cikin ne? Ko cikin zan karbar mata ne gaba daya ta huta?.”
Zuwa yanzu ranshi ya fara baci. Ya ja tsaki ya juya zai fice.
“Ka ga tuwon fa gashi nan ana sayarwa a bakin titi ka siyo mata mana?”
“Ba shi na siyo ba jiya ta ci ta dinga kwara amai wai an sa curry a ciki.”
Ta mike ta ce
“Toh Allah ya sauwake . A dawo lafiya. Bari na je na dan rage bacci.”
“Yanzu ba za kiyi tuwon ba kenan?”
Ya tambaye ta.
“Toh ai baka bani amsar tambaya ta ba. Ni da ina nawa laulayin wa ka sa ta dinga yi min tuwo?”
Ya kara jan dogon tsaki ya juya ya huce domin kai yara makaranta. Ita kuma ta shige daki ta kwanta tana
tunanin yanda ta dinga goyon ciki. Shi ba zai girka mata ba, kuma idan ta roka a makota ya dinga fada
kenan haka ta hakura. Sai dai kawai tayi ta cin gayan buredi. Cikin fari ya fi bata wahala, tuwon take so
amma ko ta girka bazata iya ci ba. Ita ko siyo mata ma bai taba yi ba, sai dai kawai ya ce fitina kawai ce ta
sa bazata ci wanda ta girka ba. Don haka a wahala da yunwa take goyon ciki, domin ko ta fadi abinda take
so cewa zai yi fitina ce. Sai dai kawai in ta faki idonshi ta fada makota kafin ya dawo ta samu wani abun ta
ci.
Ta gyara kwanciyarta ta ce a fili
“An ce in an yi amarya zan huta za ta rage min ayyuka kuma a sani tuka tuwo da safe. Allah ya baku lafiya,
kanku ake ji.”
Nan da nan kuwa bacci ya kwasheta. Ko da ya dawo bayan isha’I ya shiga a kan dining ya same ta tana
waya, nan da nan ta ajiye wayar ta yi mishi sannu da zuwa.
“Babu wani dan ruwan sanyi ne.”
Ta ce ai kuwa akwai zobo. Nan da nan ta mike ta dauko masa zobo mai sanyi da kofi ta ajiye masa. Ya
zauna a kan table din ya dan fara sha.
“Kin dubo kanwar taki kuwa tunda na fita?”
Ya tambaya.
“Au wai amarya? Ai ni tunda ka fita wallahi ko tsakar gida ban leka ba.”
“Yanzu Rabi ashe baza ki taya ni kula da yarinyar nan ba? Ke kin ma manta akwai mutum a gidan ko?”
Mamaki ya cika ta.
“Ai daman bamuyi da kai zan tayaka kula da ita ba ko? Ko ka taba ji ance mace ta kara aure. Allah ya san
mu mata yanda ya halicce mu ba za mu iya ba shi yasa bai ce mu kara aure ba. Ni ban kara aure ba kuma
a tashe ni tsaye? Kai da kanka fa cewa kayi idan ka kara aure zan huta, to a barni na huta mana. Don Allah
mu bar wannan zancen. Kai da kanka ka fada lokacin da ka kawo ta duk matsayin mu daya, toh kuma kular
me zan yi da ita. Ita ba ‘ya ta ba ita ba komai ba?.
Don Allah ka bari, kowa tashi ta fissheshi.”
Kafin ya ce wani abu ta mike ta ce sai da safe, nan da nan ta fada dakinnta ta rufo kofar.Mamaki ya cika
shi ko haushi ne?
Shekaru 24 da yake zaune da matar nan bai taba saka ta taki yi ba amma ga shi yau shi ta tashi ta bari.
Lallai kishi kumallon mata. To ya zai yi da amarya ne? Ga shi ya tsani mai aiki, don haka ma duk nacinta
bai taba daukar mata mai aiki ba kuma haka take hadawa da cikin da goyon da hidimar gidan. Yana tuna
lokacin da har kuka takeyi a kan ya daukar mata mai aiki ya ce shi ba a gidanshi ba, don a lokacin gani yake
yi son jiki ne da ita.
Toh wai cikin ne na yanzu ya fi na da wahala ko kuwa matan ne suka canza? Yanzu shi ake so ya tuka
tuwon? Wallahi babu mace da ta isa ya yi mata girki.! Toh idan kuma ya dauki mai aiki ai ya kuma siyo wa
kanshi raini a wajen Rabi, don ko yanzu ma ta gaya masa cewa ita a wancan lokacin jaka ya aura shi ya sa
duk yanda za a samar mata hutu baya so, yanzu da ya auro yar mutane gashi ya kasa zaune ya kasa tsaye
a taya shi kula da ita. Shi bai taba ganin fitna irin wannan ba. Ko lokacin da yace mata zai kara aure ma
bata tada fitna ba, Allah ya sanya alkhairi kawai ta ce don ba shi ba kowa sai da yayi mamaki. Ko da yace
mata wane shire take yi ma ce masa tayi
‘Ni da ba ni zan kara aure ba shirin me zan yi?’
Haka dai ya gama tunaninshi ya tashi ya tafi gun amarya domin kuwa kwananta ne kuma tuwo ta aiko shi
ya samo mata.
EPISODE 2
Ko da gari ya waye ba ita ce da girki ba don haka ta san ba ita ce za tayi abincin safe ba. Amma da rana zai
dawo dakinta, don haka kamar yanda ta saba tana tashi ta dafa masa abincin rana wanda take saka masa
a kwando ya tafi da shi kasuwa. Shinkafa da miya ta dafa masa, ta hada masa salad mai kyau kamar yanda
yake so. Zuwa karfe takwas na safe ta gama, da yake ranar asabar ce yara baza su makaranta sai wajen
tara na safe yake fita. Ta hada komai ta ajjiye a dining table tana jiran shigowarsa.
Chan wajen 9:15 ta ji shi a wajen mota yana shirin fita, ta yi matukar mamaki don ko ba zai dau abincin ba
yana shigowa su gaisa. Ta kirawo auta wanda yake tsakar gida yana wasansa a tsakar gidan ta bashi
kwando daya tace
“Kaiwa Abbanku wannan mota sai ka dawo ka kai dayan.”
Tana nan tsaye ya dawo da kwandon ya ce Abban ya ce a barshi, tace
“Toh ajjiye a nan kan table din.”
Ya ajiye ya koma wajen da gudu, ita kuma tayi sauri ta fada daki domin ta san duk wanda ya shigo ya dubi
fuskarta ya san ranta a bace yake. Tana shiga ta fada bandaki saboda ta san ko kowa bai biyota da tambaya
ba sai Baba karami ya biyota, domin a gabansa Khalifa ya kai abinci aka dawo da shi. Tana shiga kwallar da
take kokari hadiyewa ta kwace. Wannan shine karo na biyu a tsahon shekaru 24 da aurensu da ya taba kin
cin abincinta harma ya dauki gaba da ita, kuma duk a dalilin wannan yarinyar da ya aura. Ta wanke fuskarta
ta yiwo alwala domin yin sallar walaha. Ta fito ta saka hijabinta, ta shinfida dadduma amma madadin ta
tsaya ta tayar da sallah sai kawai ta fada kan gadonta kamar wadda aka tunkuda.
Abinda bata son yi dai shi zuciyarta ta ja ta, wato tuno lokacin da ya fara kauracewa abincinta.
Watanni hudu da suka wuce:
Bai gaya mata yana neman aure ba, amma jikinta ya bata, tunda a zaman da sukayi kawo yanzu duk wani
motsi nasa tana da fassarar shi. Sai dai da yake ita mace ce mai gudun bacin rai sai bata tambaye shi ba
kuma bata gayawa kowa ba.
Wata rana suna zaune a falo ita da Khalifa da Salim suna kallon TV Baba karami (babban yaronta wanda
yake level 2 a jami’a ) ya shigo ya same ta. Bayan ya mata sannu da gida ya nemi guri ya zauna. Mintuna
kadan ta dube shi tace
“Meye ne kasa ni a gaba kana ta wasu muzurai sai kace wani mara gaskiya?”
Ya sunkuyar da kai ya shafo kansa
“Ba komai Mommy.”
Suka sake yin shiru na dan lokaci, ya dube ta yace
“Mommy wai da gaske Abba aure zai kara?.”
Duk da ta zargi hakan sai da gabanta ya fadi ta dan yi kokawa kafin ta rike nutsuwarta dake neman
kwacewa saboda wannan tambaya ta Baba karami.
“kai wa ya gaya maka?”
Ta fada bayan ta tattara nutsuwarta tana me kokari kaucewa hada ido da shi.
“Kin san aboki na Badaru ko? Toh yarinyar da Abban zai aura a unguwar su abokinshi take. Harma fa an
kai kudin aure kamar ma saura wata biyu bikin, shi Badarun ma fa da idonshi ya ga Abban ya je zance.”
Ta sake gyara zama domin duk da ta zargi hakan amma bata yi zaton har an kusa haka ba; amma bai gaya
mata ba. Ta kalli Baba karami da kannenshi dake wajen suna sauraron abinda za ta ce
“Toh tunda dai Abban bai fada ba ai sai muyi hakuri ma ji abinda zai ace. Karin aure ai bai haramata a
wajenshi ba ko? Ba wani abu bane kada ma na sake jin wannan zancen.”
Yanayin fuskarta bai bada damar a cigaba da zancen ba, don haka babu wanda ya sake cewa komai. Suka
mayar da hankalinsu ga TV inda zuwa yanzu an fara shirin Super Story a tashar NTA, jim kadan ta tashi ta
bar yaran a falon. Suka ci ga da hirarsu a kan yanda Abbansu zai yi ya kara aure.
Tana shiga dakin ta zauna turus a kan gado, kanta duk ya kulle. A zaman da takeyi da Abban Khalifa bata
taba tunanin zai mata haka ba. Bata cire rai zai kara aure ba, amma menene dalilinshi na boye mata? A ce
yanzu mijinka zai kara aure amma sai dai kaji a bakin yara? Kara auren bai dameta ba kamar yanda boye
mata ya dameta ba, amma tunda haka ya zaba tayi wa kanta alkawarin bazata taba yi masa maganar ba
har sai shi ya zo mata da zancen; ko babu komai ai yana da damarsa da zai kara aure. Kuma kawo yanzu
babu wani abu da zata ce yayi mata na tauye hakki, don haka bari ta bishi taga gudun ruwanshi.
Ba shi yayi mata maganar auren ba kuwa sai da ya kasance saura wata daya a daura masa aure. Ko da ya
gaya mata kuma batayi Masa wani tashi hankali ba; domin ta riga ta san duk namiji mijin mace hudu ne.
Hasali ma mata biyu ne suka yiwa mahaifinta takaba, don haka bata da bakin magana.
“Toh Allah ya sa albarka, abun har ya taho haka?”
“Eh. Ai da yake kinsan ni ba yaro bane ba wasa za a tsaya yi ba, ita kuma yarinya ce ta riga ta gama
jarabawarta ta WAEC, toh babu abida za a jira.”
Ya fada yana ta faman yage baki.
“Gaskiya ne. Allah ya nuna mana.”
Ya amsa da Amin.
“kuma a ina za ta tare?”
“Eh Daman ina son na gaya miki wannan dakin na baki ki kwashe kayanki sai ta tare a nan, kinga nan falon
ai ya ishe ku da kitchen.”
Ta daga idonta ta bi falon da kallo; dakuna hudu ne duka a cikin falon suke. Dakinta yana kusa da nashi,
amma akwai wani karamin store nashi a tsakani. Daga gefe kuma dakin yara ne, dakin bakin kuma yana
kallon dakin yaran ta daya gefen, tace
“Haba Abban Khalifa! Ai mun cika gidan, da ma wani ka kama mata ko ma ka gina. Kai ko boys quarters
din nan ma da ka baje ka yi mata gini, ai sai ma kun fi jin dadin amarchin ku.”
“A’a. Nan din dai za ku zauna saboda na fi son ku hade kanku yara kuma su saba da junansu sosai. Kuma
kin ga ita yarinya ce sai ana kula.”
Ya bata amsa yana wani zare ido.
Ta yatsina baki ta ce:
“Lallai Kam. Ai tunda ta auri babba girma ya sameta. Amma dai gaskiya nan babu waje ka dai sake
shawara.”
A haka dai suka tashi daga hirar ba tare da sun fahimci juna ba.
Bai tashi sanin Hajiya Rabi da gaske take baza ta bari a saka amarya ba sai da ya turo masu fenti.
Ko da suka zo tare da Aliko yaronsa ta ce su koma ba dakin da za a yiwa fenti.
Nan da nan Aliko ya buga wa Abba waya.
Yayi ta Kiran wayarta ta ki dagawa. Kafin wani lokaci sai gashi ya dawo gidan.
Ko sallama bai yi ba ya fada falon.
Bata ciki don haka ya bi ta daki.
Kafin ta gama yi masa sannu da zuwa ya fara bambami:
“Ina wayarki ne sai faman Kira nake ba kya amsawa? Kuma wane irin abu ne yara sun zo tun dazu kin hana
su aiki? Dakin da na ce miki za a saka kanwarki za su yi wa penti da Yan gyare gyare.”
Tana nan daga zaune ta bashi amsa:
“Toh ai na ce maka gidan fa babu waje. Idan an saka ta a nan ina za mu saka bakin. Na ce maka ka ka kama
mata wani gidan ai. Don Allah Ka zauna mu yi maganar nan a zaune.”
“Rabi! Rabi gidanki ne ko nawa ne da za ki tsara min yanda zan yi? Rabi bafa na son fitina. Kar ki fara
rigimar da baza ki iya gamawa ba fa?”
Har wani huci yake, don haka ta ja bakinta ta rufe.
Ya juya ya fice a fusace.
Yana shigowa falon ya ja kofar dakin bakin zai bude ya ji ta a kulle.
Ya nufo dakin nata a fusace ya banko kofar. Tana nan a zaune inda ya barta. Ya nuna ta da yatsa.
“Rabi kin san za ki iya barin gidan nan a kan dakin nan ko? Don wallahi baki isa ba. Ba zan karya kofar ba
amma wallahi idan na dawo baki bude kofar ba sai ranki yayi mummunan Baci.”
Ya banko mata kofar ya juya ya fice.
Bata taba ganin fushinsa irin wannan ba, don haka abun ya firgita ta. Nan da nan hawaye suka wanke mata
fuska. Godiya takewa Allah da ya sa yaran basa nan duk sun tafi makaranta.
Duk tunaninta ya kare. Abinda ta sani kawai shi ne ba karamin nasara za a yi a kanta ba a hadata zama da
kishiya suna sharing falo da kicin.
Gaskiya ba za ta iya ba. Don haka sai inda karfinta ya kare. Shi ya gano matarsa yake sonta don haka ya
ware musu guri shi da ita suyi ta soyayyarsu bata da damuwa, amma ta san in dai aka hada musu guri toh
tabbas za ayi mata kisan mummuke. Idan hawan jini bai kasheta ba toh lallai ciwon zuciya zai kasheta,
balle Baba karami ya ce mata yarinyar
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good