Showing 126001 words to 129000 words out of 196754 words

Chapter 43 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15361

suka barshi. Yana karasowa wajen Malam
Bala ya taba kafadarshi yace

“Malam Bala ikon Allah ya dai.”

Idonshi yana kan tagar wadda shima Salim ya kai nashi duban wajen yace

“Fada ake yi yallabai ai gara kaje ka raba kada ayi batacciya.”

Ya kyalkyale da dariya yace

“Au ai da na dan ji hayaniya na zata daga makota ne, ai babu abinda zan raba Malam Bala su ci kansu su
sha bakin ruwa.”

Nan suka jiyo Baffa ya fashe da kuka wanda fitowa yayi daga bacci ya tarar suna fadan abun ya bashi
tsoro ya fashe da kuka. Salim ya wuce Malam Bala ya kama hanyar gate zai fita Malam Bala ya riko
hannunshi yace

“Ka ji fa kukan ‘yan biyu don Allah kada ka fita ka barni da rigimar nan kaje ko Alhajin ne ka kirawo musu
kada ayi kisan kai.”

Yayi tsaki ya kama hanyar falon a daidai lokacin da kukan Baffa ya kara tsananta Hanan tana taya shi. Har
ya kusa zuwa kofar falon ya zaro wayarshi ya bude camera, yana saka kafa a falon ya daga wayar ya
danna video yana fadin

“Bari mutum ya sami na status.”
Kokawa sukeyi tuburan kuma da yake babu mai kitso a ka duka sun tsige dankwalayen gashin kansu ya
mimmike kamar masu hauka, kowacce kai duka take tana huci. Yayinda su kuma su Baffa da Hanan suna
tsaye daga bakin kofar dakin Ummansu suna kuka. Cikin haki da karaji Saudah tace

“Sai na yi maganin ku ke da munafukar uwar taki.”

Zulai ta kara kamo gashin kan Saudah tace

“Ke kuma daga uwar taki har kakar taki duk gayyar munafukai.”

Ai kuwa iya karfinta ta dage ta tunkuda Zulaiha tayi baya da karfi sai da kusan zuwa wajen dining table
sannan tayi kasa ta sa hannuta ta tokare ta fadi a kan hannun. Zafin da ta ji a hannun nata ne ya sa ta
kwalla kara

“Ahhh.”

Ta kama hannun ta rike bayan tayi zaman ‘yan bori a kasa ita kuma Saudah tana tsaye tana haki tana
huci. Ta juyo ta kalli Salim yayinda itama Zulaihan ta kalleshi da idanuwanta wadanda suke cike da
hawaye saboda yanda hannun da ta fada a kai yake mata zugi. Sun ji lokacin da Salim din ya shigo amma
da yake dukkansu hankalinsu na kan fadan babu wadda ta damu da shi. Sai a lokacin ya rufe kyamarar
wayar yana fadin

“Yauwa, mutum ya sami na dorawa a status. Mutane sai kace ‘yayan jakai.”

Kafin su ce wani abu ya juya ya fice sai jiyo rufe gate suka yi. Saudah ta kalli Zulaiha da take zaune rike da
hannun tace

“Kadan kika gani, wallahi sai kin bar gidan nan tunda ba gidan ubanki bane.”

“Sai ki zauna da yake ke gidan ubanki ne.”

Ta bata amsa tana mata kallon sama da kasa hawayenta suna kara yawa saboda yanda hannun yake
radadi. A nan ta wuce ta kwashi yaranta ta shiga daki ta rufo kofar, ta bar Zulaiha a nan tana kokarin
tashi.

Tana shiga dakin ta lallaba yaran ta ajiye su sannan ta shiga bandaki ta gyara fuskarta da gashin kanta ta
fito ta zauna. Dole ne yau Abban ya san abun yi don wallahi ita baza ta zauna da munfuka ba, gashi har
an kai Zulaiha ta isa ta mareta kuma ta zagi iyayenta. Zamansu ba zai yiwu tare ba don haka in baza ta
fita daga gidan ba toh sai dai ta koma bangaren Mommy su karata can.

Har ya kama hanyar makaranta ba tare da ya gayawa kowa ba sai kuma ya kasa nutsuwa. Yanda yaga
suna fada suna yagar junansu kada su je suyi kisa tunda ita Saudah ma yaranta da suke tsaye suna ta
kuka ma basu sa ta fasa ba. Ya zaro wayarsavya kirawo Abba

“Salim ya dai?”

Abban ya tambaya bayan ya amsa wayar.

“Abba Umman Saudah fa fada sukeyi ita da Zulaiha, na dai fito na barsu nace bari na gaya maka kada su
jiwa kansu ciwo tunda ba kowa a gidan don Bala ma ina fita ya fita.”

“Subhanallahi, fada harda jin ciwo kuma Salim?”
“Abba kokawa sukeyi fa sosai ba sa ji ba sa gani.”

“Kai yanzu ka tafi makarantar?”

“Eh Abba ina hanya.”

“Toh shikenan, bari naje gidan.”

Nan da nan ya tashi Lalo ya tuka shi suka nufi gidan.

Yana shiga babu kowa a falon amma yanda ya ga falon ya tabbatar masa fadan aka yi. Fulallukan kujera
duk gasu nan a watse a kasa, an zame kafet din ita kuma kujera mai zaman mutum uku da yake a
gabanta aka fara fadan itama an tura ta baya sannan ga center table shima an tura shi gefe an kifar da
shi ga dankwalaye guda biyu a wajen wanda ko ba’a fada masa ba ya san daya na Zulaihan ne daya na
Saudah. Ya jijjiga kai yana mamakin abinda zai hada su fada haka kamar wasu kananan yara, musamman
ita Saudah. Daga dakinta yake jiyo motsin yaran don haka ya karasa ya bude kofar ya shiga. Tana kwance
rigingine a kan gado yayinda yaran ke wasansu a tsakar dakin. Ta tashi zaune tace

“Sannu da zuwa.”

“Yauwa, sannunku. Ya gajiya?”

Ta riga ta fahimci abinda yake nufi don haka ta kara bata rai ta dauke kai. Ya dauki Hanan wadda take ta
daga masa hannu tana masa gwaranci. Ya karasa gefen gadon ya zauna ya ce

“Yanzu don Allah me ya hadaki fada da Zulaiha?”

Ta kara zumbura baki tana ta kokarin tokare kwallar da ta taru a kwarmin idonta. Da yaga baza ta bashi
amsa ba ya cigaba.

“Yanzu ke baki san kimar da Allah yayi miki ba za ki biyewa Zulaiha har ta kai hannunta jikinki? Ko baki
girmeta ba ai aure ya kamata ace ya kara miki ‘kima ga yaranki suna kallo. Me kike koya musu don
Allah?”

“Mtseww.”

Ta ja tsaki ba don ta so ba sai don shima Abban da yake wadannan maganganun ya fara bata haushi. A
fusace kafin yayi magana tace

“Zagi na fa tayi, ta zagi iyaye na saboda tsabar raini.”

“Haka kawai ta zage ki ko kuwa anyi wani abun kafin ayi zagin.”

Sai da ta murgude baki sannan ta bashi amsa

“Kawai saboda ina tambayarta dalilin da yasa ta kwasar min zance ta kai Bichi kuma ina gaya mata bana
so kada ta sake idan tana son zama dani shine ta fara zagar min iyaye.”

Yanzu ya fahimci inda zancen ya samo asali, mamaki ya hanashi magana ya tsaya kawai yana binta da
kallo. Jim kadan yace

“Irin wannan ai ba a magana, sai ka bar mutum da halinshi kai din ka kiyaye kawai.”
Ta harareshi

“Kana son ka dora min laifi kenan?”

“A’ah babu wanda zan dorawa laifi tunda bana nan aka yi, amma dai gaskiya baku kyauta ba kuna mata
ke kuma kina uwa ai kun fi karfin ku tsaya kuna kokawa.”

Ta share hawayen da ta gaji da tarewa ta mike tsaye tana fadin

“Zaman mu da ita ba zai yiwu ba gaskiya, ko dai ta tafi gidansu ko ta koma wajen Mommyn amma ni ba
zan iya ba.”

Ta wuce ta shiga bandaki ta barshi a nan da baki bude.

Mikewa yayi shima ya bar mata yaran a nan ya fice ya ja kofar. Yana zuwa tsakiyar falon ya kwalawa
Zulaiha kira, ta fito rike da hannunta wanda ta fada kai tana kuka sosai fuskarta har ta yi ja. Kafin ta
karaso inda yake yace

“Wato saboda kuyi fitna ko makaranta baki samu kin fita ba kika zauna rashin kunya ko? Me ya hadaki
da Umman Nawwara?”

Ta share hawaye tana shesshekar tace

“Kansile mana lecture aka yi, kuma ina daki ta kirawo ni ta fara zagi na.”

Ya ja tsaki ya kauda kai saboda shi baya son yaga ana kuka musamman karamin yaro ko kuma mace.
Yace

“Toh kuma kukan me kike yi, ba kun yi yanda kuke so ba?”

Ta dafe hannun da yake ciwo tace

“Hannuna ne yake ciwo.”

Ya matsa don ya duba hannun yaga har ya Dan fara kumbura, ya kai hannu ya dan kama wajen ta ja da
baya ta dan yi kara jikinta har rawa yake tana fadin

“Ciwo yake sosai ban sani ba ko karyewa yayi.”

Ya ja tsaki ya matsa ya janyo kujerar dining table ya zauna ya zaro waya yana fadin

“Haka ake karayar, sai dai ko targade. Koma ciki bari mu ga ko za a samu mai gyaran targade sai a kaiki
ya duba.”

Har ya daga waya zai kirawo Madu sai ya tuna shi da Lalo suka zo don haka sai ya fito bakin gate ya
tambayi Lalo ko ya san wajen mai gyaran targade. Ai kuwa yace ya sani ana iya kai mutum kuma idan ma
so ake yazo zai zo, don haka Abba yace Lalo yaje ya taho da shi. Kafin wani lokaci Lalo ya je ya dawo da
mutumin. Suka zauna a nan falon Saudah ya shiga ya sanar da Saudan cewa akwai mutane a falon za a
dubawa Zulaiha hannunta. Sai a lokacin ma sannan ta ji cewa Zulaihan ta sami matsala, ta tabe baki a
ranta tace Allah ya kara in bata mayara da hankali ba ma har kafa zan karya mata munafukar banza.
Zulaiha ta fito ta zauna a gaban mai dubata, yana kama hannun ta fara hawaye ya dago ya dubi Abba
yace
“Alhaji ai ba targade bane gocewar kashi ce, ina ga da karfi sosai ta fada a kan hannun amma in sha Allah
yanzu za a gyara. Kafin karshen satin nan za ka ga yayi sauki da yardar Allah.”

Sai da nai gyaran kashin ya sa suka matsa bango ya sa Zulaiha a loko, Abba da Lalo suba tsaye ya cewa
Lalo ya tsaya saboda ko da zata nemi gudu ya tare ta. Yana rike hannun kuwa ta fasa ihu, ya faki idonta
ya fizgi hannun sannan ya juya shi kamar mai daure kusa har sai da kashin yayi wata kara ‘kas’. Karkarwa
kawai take yi tana hawaye saboda azabar zafi.

“Sannu kinji, an gama in sha Allahu ya koma daidai.”

Ya dauko jakarshi da yazo da ita ya zaro magani a ‘yar roba ya shafe hannun sannan ya kama hannun ya
daure da bandeji sannan yayi mata tofi. Ya dubi Abba

“Alhaji an gama, sai jibi zan dawo a kwance hannun shike nan.”

Abba yayi masa godiya ya sallame shi yace da Lalo su jira shi a waje zai fito sai su ajiye Malam su koma
kasuwa. Sai da ya sami Saudah a daki ya kara bata baki yana jaddada mata kada ta sake su sake yin wani
fada, yayi mata bayanin ciwon da Zulaihan ta ji. Ya fito zai fice Zulaihan ta fito daga dakin tace

“Abba in an jima za je Bichi.”

“Me za ki je yi ana tsakiyar karatu, kuma gashi Malam yace jibi zai dawo ya kwance miki hannun ki bari
kawai sai hannun ya warke kya je.”

Haka ya fice ya barta ta koma daki tana kuka. Kashe ta ake son ayi, ga shi an gota mata hannu sannan
kuma an ce kada taje gida. Tana shiga daki ta dauki waya ta kirawo Ummanta, kafin ta amsa sallamarta
ta fashe da kuka

“Ke lafiya haka, mutuwa aka yi ne.”

“Umman su Nawwara ce ta yi min duka kuma ta gota min kashi.”

Ta ji wani banbarakwai tace

“Ba ganewa fa nake yi ba, me yake faruwa ne?”

Cikin muryar kuka ta bata labarin duk abinda ya faru ta rufe da

“Kuma nace wa Abban zan zo gida ya ce ba zan zo ba.”

“I, ai gara kiyi zamanki nan. Idan kika zo me zan cewa ubanki kin san idan ya ji wannan labarin ma ba zai
taba baki gaskiya ba kuma cewa zai yi ni na saka ki. Ki yi hakuri kiyi zamanki gobe in Allah ya kaimu ni sai
na zo.”

Da haka ta samu ta lallabata a kan ba sai ta zo gidan ba, don ita a yanzu ma ta manta da damuwar
mahaifinsu. Tun bayan karamar Sallah da sati daya Muntari ya tura aka kai kudin aurenta; wanda da yace
Abban ya karba amma yace sai an kai Bichi wajen dangin ubanta; yanda taga mahaifin nata ya sauko
yana sauraronta tayi zaton komai ya wuce. Ta share hawayenta ta yi ‘kwafa, tabbas wannan fadan bai
kare ba don kuwa sai ta rama. Idan har bata samu dama ta ji mata ciwo ba to sai ta san gulmar da tayi
aka koreta daga gidan tunda ba gidan ubanta bane da har take mata gori.
Ranar dai haka Zulaiha ta wuni a daki don ko abinci bata fito ta ci ba sai bayan sha daya na dare da ta
tabbatar kowa ya kwanta sannan ta fito ta shiga kicin ta sami abinda ta ci. Shi kuwa Abba bayan ya dawo
saka Saudah a gaba yayi ya sake yi mata fada yana nuna mata girman kuskuren da tayi, don haka kwana
tayi tana mitar yanda Abba ya mayar da ita kullum aka yi wani abu toh itace nai laifi. Abu daya ne yake
bata nutsuwa idan ta tuna ta janyo wa Zulaihan gocewar kashi, gani take wannan ya isa dalilin da zai sa
Zulaiha ta ji tsoron sake yi mata gulma.

Yanda suka kwana zukatansu da damuwa haka itama sa’a ta kwana, wannan labari da Zulaiha ta bata ya
daga mata hankali. Fada harda gota kashi? Ita Saudan nan wai wace irin ‘yar daba ce ne? Da da ya aurota
tunani take za su sami yanda suke so amma yanzu gani ma take yi gara Rabi da wannan karamar mara
hankalin. Bata son abinda zai sa a koro mata Zulaiha domin muddin ta dawo toh mahaifinta ba zai bari ta
karasa karatun ba zai bawa Muntari dama a karasa magana a daura aure. Tunda shima Muntari tunda ya
kawo kudi yake cewa Zulaihan ya shirya, itace take dakatar da shi tana nuna masa ta fi son ta gama
karatunta, bata jin za ta iya hada aure, haihuwa da karatu don yanda taga Saudah tana wahala ita ta san
ba zata iya ba. Don haka dole gobe taje ta bawa Yayan hakuri in ya so daga baya za ta san yanda za ayi
don sai ta gyarawa wannan Saudan zama.

Haka ta kwana tana tufka da warwara ita kadai.



………..



Tun karfe shida na safe ta kama hanya don ta fi so taje ta sami Abban a gida, don haka kafin karfe takwas
tana bakin gate din gidan. Dawowarasa kenan daga kai yara makaranta yana kokarin fitowa daga mota
ta turo gate ta shigo. Har wajen shi ta karasa yana kokarin kulle motar

“A’ah, Sa’a ke ce da sassafen nan?”

“I Yaya, fita za kayi ne?”

“A’a dawowa dai nayi daga kai yara makaranta, shigo muje ciki.”

Ya wuce tana biye da shi suka shiga falon Saudah suka zauna. Babu kowa a falon da yake yau lecture din
karfe tara ce da ita don haka tana daki tana shiryawa. A nan ya zauna a falon suka gaisa da Sa’a, kafin ya
tambayeta dalilin zuwanta tace

“Yaya zuwa nayi daman na baka hakuri kai da Umman su Nawwara na ji abinda suka yi ita da ‘yar rikon
tata.”

Ya gyara zama ya jingina da kujerar don bai yi zaton Sa’a za ta bayar da hakuri ba, yayi zaton zuwa tayi a
ci gaba da rigima.

“Ai da ma kin yi zamanki, aikin yarinta suka yi da rashin hankali amma in sha Allah komai ya wuce.”

“Ni ban san me yake damu Zulaiha ba, ita kuma Umman Nawwara da ta gaya min tana mata wani ba
daidai ba ai da tuni na dau mataki a kai.”
Ta budo kofar daki ta fito ta shirya tsaf Hanan da Baffa suna biye da ita, ta dan yi turus da ta ga Sa’a kafin
ta karasa. Ko bata ce komai ba ta san abinda ya kawo ta, don haka a shirye ta karaso. Tana ta wani
gatsine fuska ta amsa gaisuwar Sa’an, ta shige dakin Abban don ta dauko kudin makaranta da ya saba
ajiye mata duk safiya a kan durowar dakin. Ta fito ba tare da ta ce da su komai ba ta nufi kofa za ta fice
Abban yace

“Ki zo Sa’a tana son ganinki.”

Bata amsa ba ta dawo ta zauna a kusa da Abban. Sa’an ta hadiye malolon takaicin da ya tokare mata
makogoro tace

“Zuwa nayi daman Umman Nawwara na baku hakuri, Zulaiha ta gaya min abinda ya faru na rashin
hankali. Toh don Allah dai kiyi hakuri, yaro dama shi sai hakuri kuma itan ma na yi mata fada in sha
Allahu baza ta sake ba.”

Ta wani zumbura baki ta kawar da kai tace

“Allah ya sauwake.”

Ta dubi Abban tace

“Bari na je na tafi in ba haka ba kafin na kai yara gidan Umma sai na makara.”

“Toh sai kin dawo.”

Ta mike ta fice ba tare da ta sake duban Sa’a ba. Tabbas ya ji haushi yanda ta banzatar da ‘yar uwar tashi
amma ba ya so ya ja maganar yanzu don itama Sa’an ta iya jan fitna, in Sha Allah in ya dawo dole ya yi
mata magana. Suka dan taba hira da Sa’an tace za ta tafi, ya shiga daki ya fito da kudi naira dubu biyar ya
bata yace ta yi kudin mota. Ya nuna mata dakin Zulaiha yana fadin

“Ki shiga Zulaihan tana ciki, kya kara ja mata kunne don itama Saudan sai da na yi mata fada don kada su
sake.”

Ta tura kofa ta shige dakin shima ya shige nashi dakin.

Haka ta saka Zulaihan a gaba tana jaddada mata mahimmancin zamanta a gidan.

“Ki lallaba ki karasa karatun ki a nan din don kin ga yanzu mahaifinku ko cefanen ma sai na yi ciko sannan
yake isa. Suturar da kike sakawa a nan duk ba samu za kiyi ba. Ki lallaba zuwa ki gama a yi maganar
bukinki a nan don mu samu Yayan yayi miki kayan aure irin na birni, tunda in kika koma can kinga sai dai
ya bamu gudumowa. Idan kuwa kina nan sai mu danka masa wuka da nama mu koma cikin yan gayya.”

Wanna tsarin yayi mata itama ko don ta fita kunyar kawaye, gashi kuma gidan me mata za ta je bata so
ayi mata kayan da ba su da kyau. Don haka ta hadiye duk wani fushi nata ta sake damarar zaman gidan.
Kafin Abban ya fito sukayi sallama da Sa’a ta rakata bakin titi ta hau motar ta tafi.

……….

Bacci yake yi sosai lokacin da wayarsa tayi kara, ya muttsike ido ya lalubo wayar. Kafin ya kalli waye mai
kiran sai da ya fara kallon lokaci, karfe hudu da minti goma kenan saura kasa da awa daya a kirawo sallar
asuba. Ya dubi mai kiran Tijjani ne dan wajen Aliko, kafin ya amsa ta tsinke. Ya fara kokarin kira kafin ta
shiga aka sake kiranshi don haka yayi sauri ya amsa ya kara a kunne

“Tijjani lafiya kake dai ko?”

“Wallahi Baffa ne bashi da lafiya gamu nan ma har mun kawo shi asibiti.”

Tuni ya nemi gyangyadin da yake idonshi ya rasa, ya tashi zauna yace

“Subhanallah, shine baka kirawo ni ba. Kuna wane asibitin ne?”

“Muna AKTH ni da shi da Baba Yalwa, an bamu gado an yi masa allurai yanzu bacci yakeyi.”

“Toh shike nan nima yanzu zan taho in sha Allah.”

“Ai za ka iya

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login