Showing 96001 words to 99000 words out of 196754 words
Chapter 33 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
kuma. Ba zan dinga siyan abinci kullum ba saboda
ke yanda na saba cika store haka zan cigaba da yi kuma ba zan fara kirgawa mace abincin da zata yi
amfani da shi ba saboda ke amma tabbas zan dauki mataki. Ba wai yawa kudi suka yi min ba nake ajiye
abincin haka, rufin asirin Allah ne kuma saboda kar a nema amma na ga ke baki gane ba.”
“Don Allah kayi hakuri, sai ma in tura a dawo da su.”
“Rabonsu ne ya riga ya huce, Allah dai ya sa kada ki sake.”
Ya shige bandaki ya barta a nan zaune. Da kyar ta samo karfin da ta iya tashi ta fice daga dakin. Ko
kwayar shinkafa bata taba dauka ta bayar masa ba sai yau gashi ta gamu da tsautsayi. Mommy ce take
tsayawa a kan kayan kullum ita da yara su sauke komai su jera, ita sai dai kawai ta debo idan za tayi
amfani da shi. Kuma da yake kullum Mommy tana gidan bata so tayi abinda kishiya za ta raina ta bata
taba gwadawa ba ma, yanzu ma gani tayi kayan da yawa ko ta diba ma ba za a gane ba shine haka ta
faru. Wannan abun haushi da yawa yake, gashi a gaban su Salim yacewa Abba ita ta aike shi ga inda zai
kai. Lallai yau ta ji kunya. Haka ta wuni jikinta babu kwari gashi tayi niyyar tayi masa tunin dinkunansu na
sallah ita da yara, tun tana jarrabawa ya bayar gashi har ya zu saura kwana hudu sallah ba a kawo ba.
Washegari saura kwana uku sallah Abban bai dade da fita ba sai ga telan da yake bawa dinkinsu ya kawo.
Ya riga ya saba shiga gidan don yaro ne sa’an Madu kuma sun saba da yaran don haka sai da ya fara
mikawa Saudah nata da na yaranta sanna ya shiga wajen su Khalifa, bayan sun gaisa ya mika musu leda
yana ffadi
“Kayan da Alhaji ya bayar a dinka muku ne, sai dai da yake baku kawo style ba an dinka muku irin wanda
ake yayi. Wanda ba’a dinka ba na Baba ne da Ahmad da Madu ya ce za su same ni kuma basu zo ba,
yanzun ma kauye zan tafi shine na hado musu da shi kar na tafi ban basu ba.”
Suka karba suka yi sallama ya fice. Kayan Mommy ne a saman ledar don haka su suka fara fadowa, nan
da nan Auta ya sa kuka, Salim ya matso ya rungumeshi ya rasa me zai ce masa sai shima ya fara kwalla.
Khalifa ne yayi ta maza yace
“In sha Allah za a ga Mommy kafin sallar ma.”
Yana rufe baki shima sai hawaye, haka suka zauna sai da sukayi me isarsu sannan Salim ya kwashe kayan
duka ya kai dakin Mommy ya ajiye. Haka suka wuni zuciyoyinsu babu dadi, ko da su Ahmad ma suka
dawo ba a dauko kayan ba don sun riga sun ce baza suyi kwalliyar sallah ba in dai ba a ga Mommy ba.
Ita kadai take shirin sallah a gidan don shi Abba ma ko dinkin sallah bai yi ba, ya bayar da na kowa da
wuri yace nashi sai daga baya. Kafin ya siyo Mommy ta tafi, a halin yanzu ma gaba daya ya manta ana
wani kayan sallah. Duk inda ya san zai ji labarin Mommy ya duba bai ganta ba, kullum sallah yake da
daddare baya rokan komai sai Allah ya sa a ga Rabi. Ga shi Baffa ma ya saka shi a gaba, kullum ce masa
yake
‘Baka yiwa iyayen yarinyar nan adalci ba Usman, cikin girma da arziki suka baka yarinyar amma sai da
suka mutu sannan ka kada musu ita uwa duniya.’
Wannan maganganu na Baffa sun tsaya masa a rai, ga shi kullum yaran nan kara bashi tausayi suke yi.
Yana tuna lokacin da innarshi ta rasu sai da yayi kamar zai bar duniya, su kuma yanzu gashi tasu innar
basu ma san inda take ba ko a mace ko a raye.
Ana I gobe sallah bayan ya gama shirin zai fita ta same shi a daki, bayan ya amsa sallamarta ta zauna a
gefen gadon tace
“Zan debi shinkafa da alkama a store na bayar ayi min wainar shinkafa da funkaso saboda abincin sallah,
don kar kaga kamar an fitar da abinci.”
Da mamaki ya bar abinda yake ya dubeta
“Au yanzu kuma saboda lalacewa waina da funkason ma sai an yi miki, jiki kalau gari kalau.”
Ta sunkuyar da kanta tana kallon yatsun hannunta tace
“Ni dama ban taba yi da kaina ba, bayarwa nake ayi min na biya don baka zaman gidan ne baka sani ba.”
Mamakinsa ya karu
“Ikon Allah, amma ai ina ganin Mommy tana sa murhu a bayan kichin dinta tana soyawa ko ma menene
take so.”
Cikin halin ko in kula da kosawa da zancen tace
“Ai ita ka gani, ni baka taba gani na ina yi ba. Abincin fa da yawa gashi kuma da wahala.”
“Allah ya sauwake.”
Ya cigaba da shirinsa, ta dan yi jim sannan tace
“Akwai kudi da ake biya na yin aikin, dama biya nake yi kuma yanzu bani da kudi.”
“Nawa ne?”
“Naira dubu hudu ne, waina za ayi kwano biyu da funkaso kwano daya.”
Ya laluba cikin wallet dinshi babu kudi sai dai naira dari biyu, ya dubeta yace
“Bani ma da kudin, amma bari Madu ya fito sai ya bayar.”
Bai sake cewa komai ba ya ci gaba da shirinsa, da taga dai ya gama maganar ta tashi ta fice tunda dai ko
babu komai ta gaya masa balle ya ga ana fita da abinci ya zata bayarwa za ta yi.
Duk sallah ko da ba itace da girki ba Mommy ta saba sai tayi abincin gargajiyar; masa, tuwo, fankaso da
sauransu; haka matar da take tayata aikin azumi za ta zo su yita suya kafin karfe tara sun gama sai rabo.
Ko ba itace da girki ba kuwa saka ta yake yi a gaba sai tayi abincin nan domin mutane da yawa suna zuwa
gaishe shi, haka za ayi ta cin abincin nan da kunun aya ko zobo. Sannan kuma a kaiwa su Baffa da sauran
dangi. Don haka yanzu Saudah ta san ita zata yi shi ya sa take shiri.
Yana fitowa ya zauna a falo ya kirawo Madu ta waya, bayan ya gaisheshi yace
“Muhammadu kawo dubu biyu a bawa antinka.”
Ya mike tsaye ya zaro wallet daga aljihun wandonshi ya bude ya zaro dubu biyu ya mikawa Abban, ya sa
hannu ya karba ya mika mata da yake tana zaune a kusa da shi. Ya dubi Madu yace
“Ka turawa Alhaji Safiyanu kudin nan?”
“Eh, na tura mishi dazu da asuba.”
“Yauwa sai ka sa a karbo kayan.”
Abban ya mike ya mikawa Madu kayansa suka fice bayan ta yi masa a dawo lafiya. Ta tsani Madu, ya za
ayi ace kudin Abba duk yana hannun Madun. Yanzu kam tana jin Madu ya fi Abba sanin nawa ya mallaka
gashi kuma in ya bada shawara ta zauna. Wannan Madun ma dai tana jin ko mutuwa Abba yayi ba zai
bari a raba gado da ita da yaranta ba. Dole ma ta dauki mataki a kansa.
Da yake ranar jajiberin ranar aiki ce sai a ranar sannan Baba Karami ya samu isowa Kanon, haka ya tarar
da su duk sun yi zuru zuru kowa yayi kuka ya gaji kamar masu zaman makoki. Bayan ya dan huta ne ya sa
su a gaba da tambayar me suka shiryawa bikin sallah, kukan dai aka sake yi sai da suka lafa yace
“Mu zama masu godiyar Allah mana kuma mu kyautatawa Allah zato. In Sha Allahu za a ga Mommy, idan
muka shiga damuwa ranar sallah za mu bawa masu son ganin kukan mu dama suyi mana dariya. Komai
zai huce da izinin Allah.”
Nan ya sa su a gaba saida suka je suka yiwo cefanen sallah, vegetables kawai suka siyo don suna da
sauran kayan sai kwakwa da dabino saboda suyi kunun aya.
Ranar sallah tun wuri aka kawowa Saudah abincinta, dama tun dare ta riga ta yi miya, don haka nan da
nan ta hada zobo suka shirya ita da yara suka sha kwalliyarsa. Abba ya saba tafiya da Nawwara idi don
bana ma ta zata zai hada da Ummi. Tun dare ya gaya mata ba zai je da Nawwara ba, bai gaya mata dalili
ba kuma itama bata nema don ta ga kamar kwana biyu haushin kowa yake ji.
Tun asuba Ahmad da Salim suke kichin, sai daga baya khalifa da auta suka shiga. Fried rice suka dafa da
peppered chicken sannan suka yi salad da kunun aya. Shi kuma Salim ya dafawa Abba alkubus da miyar
taushe kadan dai dai cikinsa.
Sai da ya fito daga wanka sannan ya tuna bashi da kayan sallah don haka sai ya dauko wasu kayan masu
babbabr riga ya saka. Ya tsaya a gaban mudubi yana dora hula ya yi murmushi da ya tuna da Rabi tana
nan in ya gama yiwa kowa kayan sallah haka zata saka shi a gaba har sai taji yace ga nashi kayan. Da
itace a gidan da ya tabbatar sai ta saka shi yayiwa kansa kayan sallah. Nan da nan idonsa ya ciko da
kwalla, ya sa yatsa ya goge sannan ya daga hannu sama kamar me addu’a yace
“Allah kaine Allah.”
Sai da yayi da gaske sannan ya tattara nutsuwarshi ya fito, ya sa yara a gaba suka shiga mota biyu suka
tafi masallacin idi. Bayan sun dawo aka zauna cin abinci, haka Abba ya sakata a gaba sai da ta cika musu
kula da waina da funkaso. Bayan ta zubo masa nashi abincin yana kan dining yana ci, funkaso da miya ga
kuma zobo. Salim yayi sallama ya shigo da kwanuka a kan tray da karamin jug. Bayan ya gaida Abban ya
ajiye tray din a kan tebur din yace
“Ya Baba ne yace na dafa maka alkubus.”
Nan da nan ya fara murmushi ya bude kwanukan yana dubawa
“A’ah, sannunku fa, amma Yaya fa ya kyauta min.”
Ya ture kwanon funkason ya zuba alkubusa ya fara ci yana tambaya
“Zobo ne a kofin?”
Salim yace
“A’a kunun aya be.”
Fara’arshi ta karu ya nunawa Salim din kofi a kan durowa yace
“Daukomin kofin can na sha, baka sa suga ba dai ko?”
“Ba suga Abba.”
Ya zuba masa kunun ayan ya juya ya fice.
Tana jinsu ta jira saida ya fita sannan ta fito daga kichin yara suna biye da ita. Ta sha kwalliyarta ta zo ta
zauna a kujerar da take kallonsa, sai da ta karewa abincin kallo sannan cikin halin ko in kula tace
“Yanzu baza kaci funkason ba kenan?”
Ya dago ya kalleta ya bata amsa
“Naga dama ba ke kika dafa ba? Da na ci da kar na ci ai duk daya, tunda matar wani ce ta dafa.”
Ya mayar da hankalinshi ya cigaba da cin abincinsa. Su Nawwara suka zagayo kusa da shi ya janyo faranti
ya zuba musu ya ajiye musu a kasa suka zauna suka fara ci. Takaici ya kamata, ta tashi a fusace ta shige
daki ta mako kofar.
Alkubus din ya bugu, gashi miyar ta yi masa dadi, ya daga kofi ya kora kunun aya. Tunda ya fara diabetes
haka Mommy take masa kunun aya ta sa kwakwa sosai da dabino sai madarar gari don haka rashin
sugan baya rage masa dadi. Yana hadiye wanda ya kurba hawaye suka ciko masa a
Ido ya sa yatsa ya goge. Ya za ayi ace har yanzu ba’a san inda Rabi take ba? Wannan lamarin na batan
Rabi yana bashi tsoro? Hawaye ya sake taruwa a idonsa, ya kalli abincin sai ya ji baya son ci. Da yanzu
haka za ta saka shi a gaba yana ci tana masa hira. Ya share hawayen fuskarsa ya daure ya dan kara cin
abinci saboda yana jin yunwa amma yana tuno Rabi karsashin cin abincin ya tafi. Ranar haka ya wuni
zuciyarshi babu dadi, ana ta zuwa masa barka da sallah yana faman yake.
Tunda tayi aure duka karamar sallah ranar sallah take zuwa gidansu bayan azahar, ya yi zaton wannan
sallar za ta hakura sai uku ga Sallah tunda Mommy bata nan kuma gashi zai yi ta yin baki ana kawo musu
abinci. Yana falon Mommy wajen Baba; sauran yaran duka sun fita; don haka sai ta buga masa waya, ya
fito yazo ya sameta a falonta. Yayi mamakin ganinta a shirye da yara harda jakarta a hannu, tace
“Gidan Umma za mu je, mun shirya.”
“Uhm, ai na zata za ki bari sai wajen jibi tunda kinga zan yi ta yin baki in ba kya nan wa zai kawo musu
abinci.”
“Yau fa kowa ‘yan gidanmu suke haduwa, ga yara nan ba sai su kawo abinci ba. Idan muka bari sai jibi
baza mu sami kowa a gidan ba sai Umman ita kadai, ka ga kuma haduwa daman daga shekara sai
shekara.”
“Haka ne, toh sai kun dawo.”
Ya bata amsa ba don ya so ba, ya juya zai fice, tayi sauri tace
“Toh bari mu fito sai ka kai mu.”
“Ba mota ai, sun fita da motocin CR-V da kike gani babu mai a ciki, bari dai na baku kudin mota in kun
gama sai ku dawo kawai.”
Ya zaro sabbin kudi a aljihunshi ya mika mata naira dubu yace
“Ku gaishe su.”
Ya fice ba tare da ya saurari amsarta ba. Ita kuwa takaici ne ya hanata magana, ta san sun fice yaran
gidan amma dama ai shi yake kaita ba su ba don zancen man mota ma gani takeyi gaya mata dai kawai
yayi. Sai da ta fito ita da yaran ta ga motar Baba a tsakar gidan Malam Bala ya wanke ta yana gogewa, da
kyar ta amsa gaisuwarshi saboda takaici, ta ja yaranta suka fice.
A gajiye ta karasa saboda gidan na su ya dan shiga loko, kuma da yake ana hidimar Sallah rasa wanda zai
shigar da ita tayi. Suna shiga Umman ta tashi ta fara neman mayafi saboda idan ya kawo su sallah ya
saba shiga ya gaisheta, ta dubeta tace
“Ki bar neman mayafi ba shi ya kawo mu ba a motar haya muka zo.”
Ta koma ta zauna tana fadin
“Ina yake, ko yaran ma babu wanda zai kawo ki ga yara rabe-rabe.”
“Wulakancinshi ne kawai ya tashi Umma.”
Da yake yayyenta da matan yayyenta sun zo sai aka shiga hidima ana ta hirarraki ana cin abinci, gashi
miyar Umma ta sha kaji bana. Sai can bayan la’asar an fara raguwa sannan Umma da Ya Ummu suka
saka ta a daki. Umma ce ta fara cewa
“Yaya gidan? Ya fara samuwa?”
Ta tabe baki sannan ta bata amsa
“Wane samuwa Umma, sai kara yi min wulakanci kawai yakeyi yanda kika san matarshi ta tafi da
hankalinshi da nutsuwarshi wallahi.”
Ya Ummu tace
“Yanzu haka kuma yawon banzanta ta tafi ba ‘bata tayi ba.”
“Babu mamaki.” Inji Saudah.
Suna nan zaune kaka ta shigo gidan bayan ta gaggaisa da mutane ta shige ta same su a dakin. Suka
gaggaisa sannan ta dubi Umma tace
“Ga sakon Saude nan.” Ta dubi Saudah tace
“Idan kin yi aiki da su ki sami kan gidanki idan kuma kin ki kina ji kina gani zaman gidan ya gagareki, don
wannan kishiyar taki baza ta barki ba. Irin wadannan matan malamai ne da su na musamman da suke
musu aiki, shi yasa za ki ga mijin duk wata hidimarshi daga ita sai yaranta wannan ko mutuwa tayi haka
zai cigaba da bautar yaranta.”
“Haka zancenki yake Kaka, tunda yanzun ma da ta bata banda hidimarsu babu abinda yake yi. Daidai da
abinci ko na dafa in suka so wulakanci sai su dafo masa wani ya ajiye nawa ya ci wanda namiji ya dafa.”
“In ce ko kin ji.”
Umma ta sa hannu ta kwance kullim ledar da kaka ta zo da shi kaka ta shiga bayani
“Wannan a abinci za ki san yanda kika yi ki zuba masa dolen shi ya ci, ke dai ki tabbatar baki ci ba.
Wannan shi kuma na kwanciya ne sakawa za kiyi, in dai yana jikinki ya kwanta dake ba zai sake sha’awar
wata mace ba sai ke, kuma ko kara kika ajiye kika ce kar ya tsallake bai isa ya tsallake ba.”
Tayi murmushi tace
“Ai kaka in a Allahu zan yi daki-daki yanda kika bani.”
“Yauwa, kinga wannan na abincin da yake ba’a so kowa ya ci sai shi kadan aka bayar don haka sai kin
tabbatar ya zauna zai ci abincin sannan sai ki barbada a miya ki juya ki rufe, wannan na kwanciyar kuma
gashi nan zai isa ma kiyi amfani da shi har sau biyu. Kuma an fi so ki daura jan zani ranar da zakiyi
amfanin da shi.”
Ta karba ta saka a jaka, ta dubi kaka tace
“Kaka akwai wani danshi da nake so ni ko ‘batar dashi ne ayi shima ya bi uwar kawai, duk kudin gidan a
hannunsa suke ya kanainaye komai sai dai a tambaye shi don wannan ina jin ma ko mutuwa Abba yayi
ba zai bari a raba gado da mu ba.”
“Allah ‘yar nan.”
“Allah kaka, komai na hannunsa don kamar ma Abban tsoronshi yake ji.”
“Ah lallai, toh bari ki ga akwai kawata ‘Yar Sabo ita ta raka ni wajen malamin nan kuma aikinsa zafi zafi
ne dashi, ita zan kirawo a waya kafin magariba ta koma wajen malamin da yake a kusa suke. In dai taje
gobe I yanzu ya bi uwar shima ya shiga duniya.”
“Yauwa Kaka, in an gama akwai wani kuma wanda yake masa girki. Ko da yake shi idan na yi wadannan
magungunan uban zan sa ya ci min uwarsa ba ma sai an kai shi ko ina ba.”
Ya Umma tayi shewa suka tafa da Saudan tace
“Lallai kin ji wuta, da ana gaya miki kina taurin kai. Ka kashe makashinka kafin ya kasheka in ji hausawa,
ni da nayi sanyi ba gashi ba ina ji ina gani an raba ni da mijin da ‘yan ‘yayana.”
Kaka tayi gayaran murya tace
“Sai maganar kudin aiki, baya karba sai aiki yayi. Dubu dari za ki bashi, don haka idan kika yi amfani da
wadannan kayan abunda za ki fara nema a wajensa kenan ki kawo a kaiwa Malam.”
“Babu damuwa Kaka tunda ma sai kayan sun yi aiki.”
A nan kaka ta kirawo Yar sabo a waya ta bata sako, suka cigaba da hirarrakinsu har magariba sannan ta
tashi ta fito ta hau tasi ta koma gidan. Tana shiga gidan ta ga har sun riga sun dawo don duk ga motocin
nan a tsakar gida, suka huce ita da yaran. In dai gidan nan ne in Sha Allah gobe kowa zai dau saiti, shima
Malam Bala waje za tayi da shi don ta ma riga ta sa a samo mata megadi a danginsu wanda za ta sa Abba
ya dauka in ta sa shi ya kori Bala.
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good