Showing 42001 words to 45000 words out of 196754 words

Chapter 15 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15360

da
ta ji motsinshi ta leko su gaisa. In Sha Allahu yau sai ta ga Baba karami a yita ta ‘kare don ita a halin yanzu
bata ‘ki a ce kafin karshen shekarar nan a daura musu aure ba ko ba komai ta yi mijin da yafi na kowa a
garinsu. Ahmad ya fado mata ta ji kwalla ta cika mata ido, tana son shi amma ta hakura don Umma baza
ta yarda ta jira shi ba kuma itama ta matsu tayi auren. Cikin dabara ta goge kwallar don kada ta shafe
kwallinta. Tana karasowa bakin gate din ta ji karar mota, ko da ta leko sai bayan motar ta hango sun riga
sun tafi. Ta cije lebe saboda takaici, kwallar da ke makale a idonta ta wanke mata fuska da hawaye masu
dumi.

Wannan wane irin abu ne, ko dai bata da rabon auren ne. Duk wannan shirin da take yi amma gashi ta sa
kwallin da turaren ya ki tsayawa su hadu mutum ya dinga bacewa kamar wani micijin tsafi. Sai a lokacin
sannan ta ji kamshi turaren mai kama da na ‘yan bori ya dameta. Ta kama hijabinta ta goge hawayenta ta
gyara fuskarta yanda Baba Yalwa bazata gane ta yi kuka ba sanna ta koma cikin gidan ta huce daki tana
takaici. Haka ta wuni ranta baki kirin saboda takaici. Ta dai kulle ragowar kwalli da turarenta ta jefa a jaka
da niyyar idan Baba ya kuma zuwa in Sha Allah za ta yi amfani da kayanta.

Sai da ta kwana biyar a gidan Baffa sannan da Abban ya zo da kanshi yace ta shirya su tafi in an kwana
biyu ta dawo. Ai kuwa da tsallenta ta hada kayanta domin daman zaman ya isheta, amma da ta tuna zaman
da za ta je ta ci gaba a gidan sai murnar ta bace. A can kasar zuciyarta kuma tana addu’a Allah ya sa Ahmad
yana nan ko kallonshi tayi saboda kyakkyawar fuskarshi tana saka mata nishadi.
EPISODE 11



Dawowarashi kenan ya shige daki yayinda Mommy ta tashi ta fara gyara dining table don ta san yanzu zai
fito domin ya ci abincin dare. Kafin ta gama gyarawa wayarta dake ajiye a kan kujera ta fara waka, ta ajiye
farantin da ta dauko ta karaso wajen kujerar ta dauki wayar. Tana kallon sunan me kiran tayi murmushi
sannan ta kara wayar a kunnenta. Sallama aka yi mata don haka ta amsa

“Wa alaikum salam, Hajiyata kin….”

Ta dan yi shiru tana sauraro. Nan da nan ta dafe kirjinta tace

“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun Allah sarki Hafsa Musty, Allah ya ji kanshi,
Allah ya sa ya huta.”

Sukayi sallama ta jefa wayar kan kujerar itama ta bi wayar ta zauna jabar. Hajiya Salma ce ta kirawo ta
take gaya mata mijin Hafsat Musty ya rasu yanzu. Dukansu kawayen ne tare sukayi secondary kuma a
unguwa daya suka taso, aure ne ya rabasu kowacce aka kaita inda mijinta yake, dayake zamani ne na waya
har kawo yanzu suna zumuncinsu kuma in dai abun biki ya faru ko jaje duk suna zuwarwa juna. Yaransuma
har sun san junansu sai dai da yake Salma da Hafsa yaransu yawanci mata ne ita kuma nata maza. Nan ya
sameta a zaune bata ma san ya fito ba sai da yace

“Lafiya dai na jiyo salatinki?”

Sai da ta share kwallar da ta makale a idonta sannan ta bashi amsa

“Mijin Hafsa ne ya rasu, Hafsan unguwarmu. Yanzu Hajiya Salma take gaya min.”

“Allahu Akbar, bashi da lafiya ne?”

“In ma dai yayi jinyar toh gaskiya ban ji ba da yake mun kwana biyu bamu hadu ba.”

“Toh Allah yayi masa rahama, Allah ya sa ya huta.”

Tunda aka gaya mata rasuwar jikinta yayi sanyi don haka kusan shi kadai yake hirarsa don bata iya bashi
amsa yanda ya kamata. Sai da ta ji ya ‘dan yi shiru sannan ta dube shi tace

“Gobe in Sha Allah ina son naje mata gaisuwa da safe, wajen 9am tunda ba ni zanyi abincin dare ba ka ga
bayan la’asar sai na dawo.”

Yace

“Toh Allah ya kaimu, in ya so in na isa kasuwar kiyi min waya sai na sa Lalo ya zo ya kai ki.”

Tace

“Toh na gode.”

Lalo yaron Abba ne, duk wani aike in dai a mota za a je shi ake aika in ba shi ba sai Madu. Don haka ko a
gidan idan za su unguwa in ba Abban ne zai kaisu ko yara ba toh sai dai Lalo.”
Sai da ta gama shiryawa tsaf sannan ta kira Abban.

“Abba na shirya.”

Ta fada bayan ya amsa wayar. Ya ce

“Tab, kinga kuwa har na manta wallahi yanzu na aiki Lalo kuma zai kai bayan azuhar kafin ya dawo.”

Ta san halinshi in bai so ta fita ba haka yake yi ya fake da rashin driver, domin shi baya son matarshi tana
fita a motar haya, tun lokacin ma da yake fama da mota daya balle yanzu da yake da motoci uku da masu
tuka motocin cikin gida. Nan da nan tace

“Ai sai kawai na hau tasi na tafi in ya so bayan la’asar sai ka turo shi ya daukeni.”

“Saurin me kike? Ki jira bayan azuhar din mana. Toh Allah ya so ki ga Madu nan ya shigo, bari na turo shi
ya kai ki.”

Tace

“Yauwa, na gode.”

“In kin tashi dawowa kiyi min waya sai a zo a dauke ki.

Tace

“Toh.”

Suka ajiye waya.

Sai da taji karar bude gate Madu ya shigo sannan ta tuna tana son ta kai yan biyu asibiti a yi musu allurarsu
ta riga kafin su wadda ta kyanda ce. Tun wancan watan ya kamata ta kai su amma ta manta sai yanzu da
taga yara sun fara kyanda ga zafin gari sannan ta tuna. Nan da nan ta dauki waya ta kira Abban bayan ta
gama yi masa bayani ya fara fada

“Toh da can mai yasa baki kai su ba kuma kika bari sai da na fito za ki gaya min. In an kwana biyu kuma sai
ki kwaso musu kyandar a makaranta ko?”

Da yaji shiru ya ci gaba

“Mommy zai kai unguwa in ya kaita sai ya dawo ya kaiki.”

Tace

“Don Allah dai ya fara kai ni, ina da test 12pm, yaushe har naje asibitin Nassarawa na dawo na tafi
makaranta kafin sha biyu kuma gashi yau alhamis idan ban je yau ba sai dai mu jira next week fa.”

“Mtsewww! Toh ai duk shiriritarki ce ta janyo ko? Ki je ya kai ki bari nayi masa magana.”

Har Mommy ta shiga mota ta zauna wayarshi ta fara waka da ya duba yaga Abba sai ya ce mata Abba ne
ya tsaya bai ja motar ba ya amsa wayar. Bata san me Abban yace ba sai ya sa wayar a speaker sannan yace

“Eh Abba bari ta fito sai na fara ajjiye Mommy tunda ita kafin 12 zata dawo sai kawai na jirata a asibitin.”
Abban yace

“Baka ji me nace bane, in ka tsaya ajiye Mommy za ka makarar da ita tana da test 12pm, Mommyn ta jira
ka in ka dawo sai ka kaita ba gaisuwa za ta ba?”

“Abba Mommyn fa har ta shiga mota.”

“Mtseew! Wai me ke damunka ne? Bani mommy.”

Abban ya fada a hasale.

Sai da ta kashe loudspeaker sannan ta kara wayar a kunnenta

“Kina ji ko, ki koma gida ya kai Sauda asibiti in ya dawo da ita sai ya kai ki. Kafin 12pm za ta dawo za ayi
wa Baffa da Hanan allurar riga kafi ne.”

A sanyaye tace

“Toh su je mana in ya so ni sai na hau tasi.”

Yace

“A’ah, ki jira shi kawai.

Ta mika masa wayarshi ta fice daga motar kafin yace wani abu. Shima ya kawo iya wuya don takaici, dama
gashi ya tsani a ce ya kai Saudah unguwa. Kafin Mommy ta karasa bakin kofa sun fito ita da yarinyar dake
mata aiki da ‘yan biyu a hannunsu. Yana kallonta ta mudubin mota ta kalli bayan Mommy tayi irin dariyar
nan mara sauti ta toshe bakinta domin ta kalli mai aikinta itama tayi dariyar sannan suka karaso suka shiga
shiga bayan motar.

Tana shiga ta jefar da jakarta a falo kwalla ta fado kan fuskarta, sai da shafa fuskarta sannan ta yarda kuka
take. Ta rasa kukan takaici ne ko Hafsa take yiwa kuka ta san itama tana sa rai da ita tunda ita Salma tana
Abuja. Kullum bukatarta bata da muhimmanci kenan sai dai a biya ta Saudah in da sauran lokaci sanna za
a yi mata tata. Vaccine fa yace za a kaisu wanda ta san ba abu ne na sauri ba ko wanne lokaci ma za a iya
kaisu, kuma me zai hana su fita duka a ajiye ta amma an ce ita tana da makaranta wato itace bata da abun
yi don haka sai a bata mata lokaci yanda aka so. Irin wadannan abubuwan su ke sa tana kara raina Abban
tana kuma gane yanda ta dauke shi ba haka ya dauketa ba.

Ta kasa daurewa, ba zata iya barin Hafsa ita kadai ba a rana irin ta yau don haka ta sake dabara. Ta daga
waya ta kirawo Abban

“Salma ta iso zata biyo min yanzu mu huce, da yamma ma zata dawo dani.”

Yace

“Ah, har ta zo daga Abujan?”

“Eh, yanzu jirginsu ya sauka kuma kaninta ya kai mata mota airport za ta zo mu huce.”

Yanda ya ji muryarta ya san ba za ta karbi amsar da bata so ba don haka yace

“Toh shike nan sai kin dawo. Allah ya ji kanshi, kiyi mata gaisuwa kafin na zo.”
Kafin ta fita sai da ta yiwa Madu message

‘Na tafi gidan gaisuwar in ka gama ka koma wajen Abban.’

Har ya kaisu asibitin bai ce musu komai ba tunda daman shi ko gaisheta ba kullum yake yi ba sai ya ga
dama. Ya samu inuwa yayi parking suka fita daga motar, ta zagayo ta inda yake tace

“In mun fito a nan zamy sameka?”

Ba tare da ya kalleta ba yace

“Eh.”

Har sun fara tafiya ta juyo ta bude bayan motar ta jefa jakarta tana cewa Jamila (Mai tayata aiki)

“Na san ba zamu bukaci wani abu ba tunda yanzu za a tsira musu mu fito.”

Ta rufe kofar motar suka huce cikin asibitin. Suna matsawa ya sake karanta sakon Mommy sai ya kirawo
ta, tana dagawa yace

“Mommy fushi kikayi ko?”

Tace

“A’ah, ka gan ni ma har na zo. In an jima za mu huce gida da Anti Salma ba ma sai ka zo dauka na ba, na
gayawa Abban in ka dawo da su kawai ka koma kasuwar.”

Yace

“Toh Mommy, a dawo lafiya.”

Yana ajiye waya ya kashe wayar tasa gaba daya yayi fito

“fyiiiitt”

Ya yi baya da motar ya juya ya fice daga asibitin, bai zame ko ina ba sai dakin abokinshi Adil wanda suke
BUK tare da yake shi ba dan Kano bane shi yasa ya kama daki a unguwar ‘Danbare. Yana isa ya fito ya rufe
motar, har zai huce ya hango jakarta a bayan motar wadda ya riga ma ya manta da ita. Ya kyalkyale da
dariya har sai da ya sunkuya ya dago ya kara kallon jakar yayi fito yace

“Bonus.”

Yana shiga dakin Adil yana tsaye yana shirin fita yace

“Mutumina ya za ayi ne? Kana nan naje na dawo ko za ka bani lift cikin gari.”

Yace

“No, yau ina nan har karfe ‘dari biyun dare mutumina, wata wuta na kunno sai ta kusa cinye garin sannan
za a ganni. Je ka dawo ka sha labari.”

Suka tafa Adil ya kyalkyale da dariya yace

“Shege mutumina, kana wuta ina sa maka fetur.”
Madu ya kai mishi duka ya goce ya fice daga ‘dakin.




Basu fi minti arba’in ba suka fito bayan an yiwa Baffa da Hanan allurar suna ta tsanyara ihu. Saudah tana
rike da Baffa Jamila kuma tana rike da Hanan. Tun daga nesa ta hango wajen babu motar da aka kawosu,
ta dubi Jamila tace

“Kinga ‘dan rainin hankalin nan ko Ina ya tafi oho, yanzu haka ya canza gurin parking yana kallonmu don
rainin wayo.”

Suka sami inuwa suka tsaya. Minti kadan babu alamar Madu don haka tace da Jamila ta zagaya ko za ta
ganshi. Ta dauki lokaci tana zagayawa, Hanan da ta goya har ta daina kuka ta yi barci bata ganshi ba don
haka ta dawo inda ta bar su Saudah. Mamaki ya lullubeta, tunda ba yau ya saba kaita unguwa ba kuma in
babanshi yace ya jirata jiran nata yake yi. A fili tace

“Toh ina ya tafi. Bani jakata nayi masa waya.”

Kafin Jamilan tace wani abu ta bawa kanta amsa

“Subhanallah, ai jakar tana cikin motar. Kai! Amma kuwa idan wani wajen ya tafi sai na gayawa ubansa
wallahi sai ranshi ya baci.”

Suka koma rumfar da marasa lafiya ke zama suka zauna. Sai faman tsaki kawai take yi ta rungume Hanan
gashi daya zanin goyon nasu yana cikin jakarta balle ta goya ta. Sun kai wajen minti talatin suna zaune
babu alamar shi. Ta matsa ta tambayi wadda take kusa dasu

“Baiwar Allah karfe nawa ne don Allah?”

Tace

“Sha ‘daya saura minti biyu.”

Ta juya ta sake yin tsaki, wani malolo ya tokare mata makogoro da ta tuna hatta ruwan su Hanan yana
cikin jakar da ta bari a motar don ma dai suna shan nono. Gaba ‘daya ranta ya gama ‘baci, bata taba sanin
Madun zai iya karya dokar ubansa ba sai yau. Sai da ta tambayi mutum biyu, a na ukun sannan ta sami
aron waya da yake ta haddace lambar Abban nan da nan ta kirawo shi. Yana dauka bayan ya gane muryarta
yace

“Wayar wa kike kirana da ita ina taki wayar?”

Tace

“Tana mota, mun shiga a yiwa yara allura muka fito ba muga Madun ba, munfi awa daya a nan ba shi ba
alamarsa.”

“Toh ai yanzu haka waje ya canza don kuwa baya nan kuma Mommy ma ta yi fitar ta ta kin ga kuwa yana
nan inda kuke.”

Zuciyarta har tafasa takeyi ta daure ta hadiye malolon da ya tokare mata makogoro tace
“Ban haddace lamabarsa ba ai.”

Yace

“Oh, ashe fa ba kya tare da wayarki. Bari na kira shi ki tsaya a inda ya ajiye ki zan ce masa ya koma ya
sameki a nan.”

Suka ajiye waya mai waya ta karbi wayarta ta huce. Tana gyara zamanta Hanan ta tashi da kukanta ta sa
mata nono ta sha, sai waige-waige takeyi ta ga ta inda zai bullo amman shiru. Minti goma sha biyar suka
kara hucewa shiru, ta fara gajiya don haka ta sake rokar wata mata ta bata aron waya ta sake kiran Abban.
Yana amsawa yace

“Baku ganshi ba?”

Tace

“Eh mana.”

Yace

“Toh ina ya tafi, ina ta kiran wayarsa layukan duk a kashe.”

Tace

“Toh yanzu ya zamu yi, don bani da ko sisi balle mu hau tasi gashi daidai da ruwan shan su Hanan yana
cikin jakar tawa.”

Yayi tsaki

“Mtsewww, yanzu sai kun taso ni kenan kuma ga shi ina da baki a nan kuma Lalo baya nan. Mtseww, bari
in zo in sha Allah nan da minti talatin zan zo ko Madun, zan cigaba da trying dinshi.”

Suna nan zaune suke ta gaji ga shi Baffa yayi kashi a diaper yana ta rigima saboda shi da zarar diaper dinshi
ta jike ba zama sai an cire masa. Sukayi ta karba-karba ita da Jamila suna jijjigensa. Ta san ma ta riga tayi
missing test sai dai kawai ta fara tunanin yanda zata yi ta je ta tsara malamin yayi mata makeup. Bata ma
da tabbas din zai saurareta don ba ya ragawa dalibai ko daya. Ta tsayar da wata ta sake arar waya, tana
dubawa ta ga 1pm, ranta ya kara ‘baci wato Abban ma shirga su yayi? Ta sake kiranshi da wayar matar
yana jin muryarta yace

“Subhanallah, ai na manta da ku na gaya miki aiki yayi mana yawa. Yanzu zan taho ku jira ni.”

Ba zata iya cewa komai ba don haka ta katse wayar ta mikawa mai ita, suka sake zama. Sai da Abban ya
kwashi wajen minti ashirin sannan ya iso. Tunda suka shiga motar bata ce masa komai ba shima kuma da
yaga tana ta cika tana batsewa ya kau da kansa tuki kawai yake yi. Kafin sun isa gida ya kirawo Salim yana
tambayarsa Madu yace shima tun safe basu sake haduwa ba. Ya kira Mommy itama tace ba ta san inda
yake ba.

Duk da ta kirawo lambarshi a kashe amma tana ji a jikinta lafiya kalau yake duk inda ya shiga. Ta san dai
tsiyar Madu da taurin kansa in yana fitnar shi ba ya shakkar kowa.

Yana saukesu ya juya ya tafi kasuwa suka shiga gidan, haka ta cewa Jamila ta dafa musu indomie sanna ta
je gidansu ta dauko mata Nawwara da Ummi, ita kuma ta shiga daki shirya yaran.
Har dare ba a sami layin Madu ba don haka da magriba Abban ya dawo gida. Wajen Saudah ya fara shiga
tunda itace da girki, tunda ya shiga kuwa take ta masifa an yi mata wulakanci ga shi yasa ta yi missing test
harda kukanta.

“Na ce ki bari ya dawo muji, yaron da ba a san ma lafiya yake ko ba lafiya ba tunda bai saba kashe waya
ba ko cikin dare.”

“Wallahi babu abinda ya same shi, ya dai yi yanda uwarshi ta sa shi. Ya yarda ni a asibiti ni da yara na ya
dawo ya kaita unguwa kuma ya kashe waya. Motar nan bata fi karfinka ba kuma tun tuni nake gaya maka
ka siya min ko don na huta hawa motar haya da yara amma ka ki, ka gwammace kullum ka dinga tura ni
inda za a yi min wulakanci.”

Yace

“Mtseww! Ke wa ya gaya miki haka aka yi? In dai mota ce kuma na gaya miki bazan baki mota ba, bana
ra’ayin in bawa mace mota amma duk inda za ki je zan sa a kaiki.”

“Toh in ba haka bane yaya ne? Kawai sun rainani shi da ‘yanuwanshi kuma ai dama suka samu. Duk abinda
kace su yi min ma ai sai uwarsu ta ga dama.”

Haka ta sa shi a gaba tana mita har sai da ya gaji ga fice ya bar mata wajen. Yana fitowa ya tsaya a bakin
gate tambayi Mal. Bala yace

“Yau kuwa Madu ya dawo gidan nan?”

Bala ce

“Uban dakina bai dawo ba ranka ya dade, ai tunda ya fita da uwar biyu har yanzun nan bai dawo ba lafiya
dai ko ranka ya dade?”

Yace

“A’ah ba komai.”

A falon mommy ya zauna ya kirawo su Salim, itama Mommy ta zauna ana tunanin ta inda za a fara
nemansa kawai suka ji Bala megadi yana bude masa gate yana fadin

“Sannu da zuwa uban dakina.”

Su Salim ne suka fito kafin ya gama parking suka taroshi, yanda suke tafiya a sanyaye suna kallonshi ya sa
yace

“Meye haka ne kuke kallona

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login