Showing 90001 words to 93000 words out of 196754 words
Chapter 31 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
mukullin mommy na
store. Kafin ya fita kai mata mukullin sai da ya kirawo Ahmad yace
“Ya Ahmad Abba ya ce na bawa Umman su Nawwara mukullin Mommy na store, wai nata ya bata.”
“Uhmmn, ok ka bata kawai.”
“Toh Ya Ahmad mu me za mu dafa kuma? Ko debowa zan yi kafin na kai mata mukullin?”
“Haka ne fa, toh kana ji ko kayi shopping list yanzu zan turo maka kudi account dinka in kun dawo daga
masallaci kuyi sayayyar kai da Khalifa. Ka bata mukullin kawai.”
Suna ajiye waya ya dauki mukullin ya je ya sami Bala ya bashi yace ya kai mata. Yana zuwa ya buga mata
kofa ya rage tsaho ya gaisheta sannan ya mika mata yace
“Dan Alhaji ne yace a baki wannan Hajiya.”
Ta harareshi tare da fizge mukullin
“Wa ye kuma dan Alhaji?”
“Salim ne Hajiya.”
Ta ja tsaki ta juya ta rufe kofar ta barshi a nan, tana shiga ta jefa mukullin a bayan wardrobe dinta tana
fadin
“Sai in ga inda za a debo abinci a dafa ayi min rainin hankali.”
Da yake Juma’ah ce kuma ranar hutu sha biyu aka taso yara daga makaranta, neman duniya ta yiwa Bala
ya dauko mata su bata ganshi ba don haka ta hakura ta koma cikin gidan
“Wannan Balan ma sai na raba shi da gidan nan don na kula su yakewa aiki.”
Haka ta goya Baffa ta dauki Hanan ta tafi dauko su. Tana dawowa da su Nawwara su Khalifa ma suka
dawo, bayan sun yi shirin masallaci suka fito suna rufe kofa suka ji Bala yana bude gate yana ta sannu da
zuwa, yana gama budewa motar Baba karami ta shigo. Dabi’ar tace da an taba gate sai ta leka ta ga
waye don haka yanzu ma tana hangosu ta taga, tana ganin bala tayi tsaki tace
“Munafiki ai yanzu ya dawo, zan yi maganinku ne.”
Abinda bata sani ba shine Bala buya yayi da yaga lokacin dauko yara ya kusa, kamar yanda bata damu
dashi ba shima bai damu da ita ba amma kwana biyun nan yanda take mishi magana da hantara ya sa
shima yace in dai ba a gaban Abban bane toh ba za ta more shi ba.
Baba yana shigowa suka mayar da kofar suka bude suka tsaya suna masa oyoyo, Auta ne ya dauki
jakarshi suka huce ciki gaba daya. Nan da nan shima ya shirya yace
“Toh ku zo mu tafi masallacin gaba daya.”
Har sun mike Salim yace
“Ya Baba mu fa in aka idar da Sallah sai mun tsaya a kasuwa mun yo sayayya.”
“Ah, yanzu ku kuke shopping a gidan ne?”
“Mukullin store Abba yace mu bawa Umman su Nawwara wai nata ya bata, shine Ya Ahmad yace mu
siyo kayan abinci saboda namu girkin.”
“Ah, ba Abba yace ita take girkin ba ai shike nan kun huta sai muci abinda ta dafa, amma bari na kira
Ahmad din.”
Yana dauka yace
“Har ka iso ne?”
“Eh, ina gida ma. Salim ne yace min wai ka ce su yo shopping shine nace su barshi mana muci abinda
aka dafa.”
“A haba, ai ka barta kawai a bata homework. Ka san duk ita take gotawa Abba saiti hora ta za muyi
tukunna su siyo kayan abincin kawai.”
Dariya yayi yace
“Zama da Madu ya lalata ka wallahi, toh shikenan sai mu je gaba daya.”
Suna gamawa da masallaci suka huce kasuwar tarauni, kudin ma da Ahmad ya tura musu ba suyi amfani
da shi ba Baba ne ya biya kudin komai; kaza, kifi, nama, kayan miya, vegetables da duka wani abu da
suka san Mommy tana siya sai da suka siyo, shinkafa, taliya da macaroni ma carton suka siyo sannan ga
dankali da doya da kwai. Haka aka zubo musu a mota suka dawo gidan. Tana sallar la’asar suka dawo
don haka bata san sun shigo da wasu kaya ba, ta zata dawowa kawai suka yi daga masallaci. Daf da sallar
magriba Madu ya dawo gidan, kusan tare suka dawo shi da Ahmad don yana shiga shima ya shigo. Kofar
kicin a bude take don haka daga nan falon ya hango kayan da aka ajiye ya dubi Salim yace
“Kayan meye a kichin haka.”
Ya bashi labarin abinda ya faru yace
“Me yasa ka bata, da ka Sani ka kirawo na bata in ya so na gyara mata saitin ta da ya goce.”
Ahmad da ya riga ya shigo yana jinsa yace
“Rabu da ita, ita ai in aka hanata mukullin store babu yanda za tayi taci abinci tunda shi kadai ke ci da ita
a duniya, ai sabon homework za a bata.”
Ya kyalkyale da dariya yace
“Mu je zuwa.”
Baba karami da yake kwance a daki ya kwalawa Madu kira ya karasa da sauri yana Fadin
“Ai yanzu zan zo na kwashi gaisuwa.”
“Ina Abban?”
Ya karasa cikin dakin sannan ya bashi amsa
“Ba dashi muka fita ba ai, makaranta naje wajen supervisor na.”
Kafin su gama magana suka jiyo dawowar Abba dukansu suka fito don yi masa sannu da zuwa banda
Auta da Madu, su zamansu suka yi a daki. Yana fitowa daga mota Baba ya gaishe shi, yana ta raba ido ko
zai ga auta bai ganshi ba ya san yana ciki. Kafin mommy ta bar gidan kullum Auta ne yake raka shi cikin
gida da kayan da ya siyo, ko bai siyo komai ba sai ya karbi wayarsa ya kai masa har falo sannan su rabu
amma tunda abun ya faru ya ma daina kula shi kwata kwata. Nan suka rabu ya shige wajen Saudah suka
koma wajensu. Kamar kullum kafin a tafi masallaci Khalifa ya shiga ya karbo musu abinda ta dafa, duk
sun huce masallaci don Baba ma da Abban suka tafi Madu ya tsaya ya bayar da abincin. Ta yi matukar
mamaki da takaici da taga sun bayar da abincin, bayan ta zuba musu sai da ta samo gishiri da yawa ta
zuba yanda ta tabbatar bazai ciwu ba amma gashi ko dubawa basuyi ba suka bayar. So tayi ace basu dafa
komai ba kuma wannan ya ki ciyuwa. Ta jijjiga kai tace
“Na san dai ba zai huce indomie ba ko bread, amma za mu hadu ne.”
Bayan Abban ya zauna a kan dining table tana tsaye tana hada masa shayi ya dauki waya ya kirawo Baba,
kafin ta gama hada shayin yayi sallama Abban ya amsa sannan ya shigo
“Kana wani abun ne Baba?”
“A’a Abba abinci kawai zan ci.”
“Zo ka zauna a nan mu ci abincin.” Ya fada yana nuna masa kujera.
Ya karasa ya zauna, Abban ya dubi Saudah yace
“Ki dauko masa Kofi da plate yaci abinci.”
Ta huce kicin ba don ta so ba ta dauko abun da akace ta dauko ta dawo ta ajiye masa a gabansa, shi
kuwa ko kallonta bai yi ba. Ya janyo kayan shayi ya hada Abba ya tura masa flask ya debi dankali da kwai
ya dau wani kwanon ya debi farfesun kaza ya fara ci suna hira da Abban. Ta tattara yaran ta debi abinda
za ta diba ta huce daki, duk da tana so taji abunda za su tattauna amma takaici ba zai barta ta zauna a
wajen ba. Abba ya dubi Baba yace
“Yanzu kai bakabda wani clue na inda Mommy za ta tafi.”
“Wallahi ban sani ba Abba, Allah ya sa dai ba wani abun ne ya sameta ba bayan ta fita ko kuma aka sace
ta.”
Ya jijjiga kai yace
“Ka bar wannan zancen in Sha Allah ba sace ta aka yi ba, tana nan lafiya. Na fi tunanin fushi dai tayi
kawai ta tafi wani wajen, Allah dai ya sa a sameta kawai. Wallahi na zata gidan Shafa za ta tafi.”
Damuwar da ya gani a fuskar Abban ta sa yayi matukar tausaya masa yace
“In Sha Allah za a sameta Abba.”
“Allah ya sa, haka nake fata.”
Suka yi shiru na dan lokaci sannan Abban yace
“Ka ga Auta kuwa, yana ta kuka fa.”
“Ai ya daina Abba.”
“Hmmn!”
“Ya aikin naka?”
“Lafiya kalau.”
“Toh ma Sha Allah, Allah ya kara tsarewa. Ka ga yau ashirin da daya ga wata Allah ya sa dai a sami
Mommy kafin Sallah.”
“Amin.”
Nan suka gama cin abincinsu sai da Abban ya tashi ya koma kasa sannan Baba yace
“Abba bari naje can din.”
“Toh Baba, nima in an jima zan shigo.”
Ya fice ya bar Abban a nan. Ko daya Abba baya so faruwar wannan lamarin ya shiga tsakaninsa da
yaranshi, wace irin rayuwa ce ‘yayan da suka girma ba su damu da kai ba kananan kuma kafin su girma
ma ai mutum ya mutu. Fata kawai yake a sami Mommy don ita kadai ce za ta dawowa da yaran nan
walwalarsu.
Sai da suna dawowa daga sallar tarawih ne Baba ya ja Auta suka yiwo gaba, a nan yake bashi baki yana
ce masa ya dinga yiwa Abban sannu da zuwa. Bayan sun koma gidan dukansu suna falo a zaune Baba ya
dubi Madu yace
“Wai me yasa ka daina zuwa kasuwa da Abba.”
Ya dauke kai yace
“Babu komai ina da abun yi ne a makaranta.”
“Toh daga yau kada ka sake barinshi ya tafi kasuwa shi kadai in ba haka ba ranka zai ‘baci.”
Ya dubi sauran yyac
“Mommy bamu san inda take ba, dai dai muke da marasa uwa. Abban shi kadai yayi mana saura babu
yanda za muyi dashi. Idan ya fadi ya mutu ai sai mu zama marayu gaba daya ko, ita matarshi bata da
asara.”
Duk suka yi shiru na dan lokaci suna share kwalla, bayan sun nutsu yace
“In dai Mommy ce in Sha Allahu za a ganta.”
Suka sake yin shiru bayan wani lokaci ya dubi Ahmad yace
“Ni na ga ma kamar Abban bashi da lafiya.”
“Wallahi nima haka nake ganinshi, ina ga damuwa ce kawai.”
“Toh Allah ya sauwake.”
Washe gari da safe kafin Abba ya fito Madu ya sa Bala ya wanke mota, ya koma ya sa kujera a tsakar
gidan yana jiran Abba. Abban yana fitowa ya tashi ya taro shi bayan ya gaishe shi ya karbi jakar Abban da
wayarsa ya nufi motar, Abba yace
“Yau ba za ka makaranta bane Madu.”
“Eh, na gama da supervisor din.”
Abban ya mika masa mukullin CR-V din da ya dauko don da da ita zai fita yace
“Toh mayar da wannan ka ajiye.”
Ya karba ya huce, Abban ya bi bayanshi suka shige wajen Mommy din. Can dakin Abba na wajen Mommy
ya kai mukullin ya ajiye.
Ayyuka da yawa da Madu ya saba kula da su a kasuwar haka ya je ya tarar da su babu wanda ya yi, don
shima Abban ko ya je kasuwar ma ba wani abu yake iyawa ba, zama kawai yake yi. Suna shiga yau Abban
ya sami waje ya zauna shi kuma Madu ya shiga aiki. Kafin wani lokaci azahar ta yi don haka aka fara tashi
ana alwala, Lalo be ya zubawa Abba ruwan alwala yace
“Alhaji an zubi ruwan.”
“Toh Lalo bari in tashi, kaina ne yake dan ciwo kadan.”
Ya yunkara ya mike kenan yaji yana yin baya kamar zai fadi har sai da ya rike bango, yaran da suke
shagon suka taso suka matso
“Ba komai, na ma mike in sha Allah.”
Ya fada yana daga musu hannu, suka tsaya sai da suka ga ya tsaya sannan suka barshi ya fice. Madu yana
idar da Sallah suka gaya masa suka ce yau shine karo na biyu da yake gwada faduwa a satin nan fa. Kafin
karfe biyar yace a rufe shagon yacewa Abba gara suje ya ga likita. Ya yarda su je asibitin dai amma suna
tafiya yana mita
“Lafiya ta kalau fa, rashin isasshen bacci ne kawai yake damuna, kuma ina sa rai in sha Allahu yau zan yi
baccin.”
“Ai gara dai muje Abba, daga can sai mu huce gida.”
Suna shiga asibitin likitan yana shirin fita amma da yake Abban babban customer ne sai ya koma suka
bishi a baya zuwa office. Bayan tambayoyi da likitan yayiwa Abba sai ya gwada blood pressure dinsa da
kuma blood sugar, sai da ya gama rubuta sakamakon sannan ya dawo ya zauna a kujerarsa yace
“Alhaji jininka ya dan hau fa, shi yasa kake ciwon kai ga shi blood sugar din naka ma ya dan daga.”
“Duk ni kadai doctor?”
“Kwarai kuwa Alhaji, don yanzu ma gado zan baka zuwa gobe mu gani don idan ka fadi za a iya samun
matsala babba.”
“Ba za a samu ba in Sha Allah likita, toh bari muje gida in an Sha ruwa sai mu dawo.”
“Ai yanzu za ka sha ruwa Alhaji.”
“Ai kuwa doctor ba zan sha ruwa yanzu ba, saura fa bai fi awa daya a sha ruwa ba kuma na gaya maka
yanzu ma babu abinda nake ji.”
Madu ma ya sa baki shi da likita suka yi ta lallaba Abba amma ya ce ba zai karya ba, don haka likitan ya
hakura ya basu gado dai Abban kuma ya yarda ya kwanta da sharadin gobe zai tafi gida. Sai da Madu ya
tabbatar Abban ya kwanta sannan ya fito daga dakin ya kira Baba ya gaya masa. Nan da nan suka shiga
dakin shi na wajen Mommy suka dauko masa kayan bacci, Baba yasa Khalifa da Auta a gaba suka hau CR-
V din Abban suka fita, ya barwa Salim tashi motar in sun gama yiwa Abban abinci su taho. Da yake sun
riga sun dora farfesun kaza sai kawai Salim ya debo ragowar alkamar da Mommy take yiwa Abba
dashishi da yake bata kaiwa store; musamman take bayar da alkama a gyara mata ita na store din kuwa
na kamfani ne wanda Abban yake siyowa, take ya dora dashishi ya hada kayan miya ya yi sauce. Ana daf
da shan ruwa ya gama ya zuba ruwan zafin a flask ya dauko ya kawo musu mota. Ahmad ya fito suka
rufe kofar suka shiga mota suka fice.
Tana kichin ta jiyo tashin CR-V sai da ta leko don ta tabbatar. Yanzu ma da ta ji ana bude wata motar sai
da sake lekowa. Ta yi mamaki kwarai da ta ga suna shiga mota da abinci, ta tambayi kanta ko dai Abban
ne bashi da lafiya. Ya za a yi kuma bashi da lafiya ya kasa kiranta, sai dai idan daya daga cikinsu ne bashi
da lafiya. Sai kuma ta tuna zai iya yiwuwa Mommy aka gani , ta tabe baki tace
“Su karata.”
Ta koma ta cigaba da shirya abincinta a kan tebur.
A hanya Baba ya tsaya suka sayi burodi da kayan shayi, bayan sun shiga wajen Abban suka dan yi mishi
sannu Baba ya zauna a gefen gadon kusa da Abban. Ya faki ido ya kashe wayar Abban saboda ya san da
an yi kirana magariba za a fara damun shi da waya, da yake shima a gajiye yake bai ma san an yi ba. Ana
kiran magariba su Salim suka shigo, nan da nan ya zuba masa abinci Auta ya hada masa shayi mai kayan
kamshi ya matse masa lemon zaki guda daya a ciki don haka Mommy take masa tunda ya daina shan
sugar. Saka su yayi suka rufe abincin sai da yayi Sallah sannan ya zauna ya fara ci, su kuma suka fice
Ahmad ya ce su je su nemi restaurant su ci abinci. Baba ne kawai ya zauna yace su yo masa take away,
shima ya hada shayi ya zauna yana sha Abba yana cin bainci.
Ji yayi kamar ya dade rabon da ya ci abinci a nutse kamar haka, sak yanda Rabi take masa. Ga shi kuma
ya ci sosai ya koshi, rabon da ya koshi haka ma ya manta. Sai da ya ci ya koshi ya shanye shayinsa sannan
ya koma kan gadon ya kashingida ya dubi Baba yace
“Salim ne ya dafa abincin nan ko?”
Yayi murmushi
“Shine Abba.”
“Salim da mace ne da an kwashi girki.”
Suka yi dariya gaba daya, Abban ya zame ta kwanta. Jimawa kadan su Ahmad suka shigo suka zauna
suna hirarrakinsu, sai da suka ga Abban ya fara gyangyadi sanan suka tashi sukayi sallama suka bar
Ahmad a nan don ya kwana da Abba suka huce.
Tun tana saka ran Abba zai zo Shan ruwa har ta gaji ta chire rai. Wato saboda an ga sahibarsa shine ya
manta dani ma gaba daya, tana yi tana faman duba waya. Bayan ta idar da sallar magariba ta gaji da jira
don haka ta dauki waya ta kirawo layinsa gaba daya taji su a kashe. Mamakinta ya karu, ta fara tunanin
akwai abunda yake faruwa amma aka yi mata banza. Lambar Madu kawai take da ita kuma ba za ta
kirashi na saboda kar ya zage ta, gaba daya tunaninta ya kare. Tun tana mitar abincin da ya bari ta dafa
bayan ya san ba zai ci ba har ta fara fargabar ko wani abu ne yake faruwa. Ta fito bakin kofa ta kirawo
Bala mai gadi ta tambayeshi inda su Auta suka tafi, yace mata shima bai sani ba don basu gaya masa ba.
Haka dai tun abun yana bata haushi har ya fara bata tsoro. Sai can wajen goma na dare sannan ta ji
shigowarsu motar Abban ce ta fara shigowa wadda suka fita shi da Madu sai CR-V tana binta, ta yi zaton
Abban ne a motar don haka ta koma ta zauna a kan kujera taga ta inda zai shigo. Har ta gaji da jira nan
ma bai shigo ba, sai wajen goma da rabi sannan ta ji Baba yana magana da Bala megadi, yana komawa ta
fito ta kirawo Bala ta tambaye shi me Baba yace masa
“Cewa yayi na rufe gate.”
“Ba tare da Abban suka dawo bane?”
“Ban sani ba hajiya da yake kafin na mayar da gate din sun shige ciki.”
Jikinta babu kwari ta koma falo, abun ya fara bata tsoro kuma. Ta sake kiran wayar Abban a kashe don
haka ta daure ta kirawo lambar Madu. Wayar tana kusa da Baba Karami yayinda shi kuma Madun yana
bandaki don haka Baba ne ya amsa bayan ya amsa sallamarta yace
“Madun yana bandaki akwai wani abu ne?”
“Ina Abban yake, har yanzu fa bai dawo ba.”
“Oh, ashe bai gaya miki ba an kwantar dashi a asibiti suna can shi da Ahmad.”
Cikin matsanancin mamaki tace
“Au bashi da lafiya?”
“Eh.”
“Hmn, sai da safe.”
Ta katse wayar kafin yace wani abu. Madu yana fitowa daga bandakin Baba ya dube shi yace
“Ashe baka gayawa matarshi yana asibiti ba da yake kai kwallo ne ko?”
“Gani nayi ba ubanta bane kuma ba danta bane, yanzu da tayi wari ba gashi ta ji ba?”
“Allah ya shiryeka kai dai.”
Ko da gari ya waye kafin ma ta tashi daga bacci sun gama shirinsu kawai sai ji tayi suna fita da mota. Tayi
kwafa ta ma rasa me za tace, don haka sai ta dauki waya ta kirawo Ummanta, tana dauka ta fara mita
“Umma Kinga wulakancin kuwa da yaran nan suke min? Tsabar raini Abban Nawwara bashi da lafiya tun
azahara suka huce dashi asibiti daga kasuwa amma aka rasa wanda zai gaya min kuma ya kashe wayarsa
har sai goman dare bayan sun dawo sun sa an rufe gate sannan suke gaya min, shima kuma sai da na
tambaya. Sannan yanzu ma da nake miki magana sun fice daga gidan Babu wanda yace min
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good