Showing 72001 words to 75000 words out of 196754 words

Chapter 25 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15366

mata fada.”

Bai ce mata komai ba sai dai kawai ta fuskanci cewa ya yarda da abinda ta fada don haka sai tayi shiru da
bakinta. Jimawa kadan ta tashi ta kwashi su Nawwara da Ummi ta kaisu dakinta tayi musu shimfida suka
kwanta. Ya fice tana yi masa sai da safe.

Bayan ya gama yi mata bayanin a nan zai kwana ta dube shi tace

“Don Allah to ka bari Yaya Ummu ta zo tunda ni kadai bazan iya da wannan jinyar ba, ina bukatar taimako.”

Yace

“Da safe Zulaiha za ta dawo na gayawa Baffansu, sai ta tayaki jinyar. Sun Nawwara can za su kwana wajen
Mommy.”

Gaba daya ma ta manta dasu don haka babu abinda tace. Tayi dai zaton zai bari Yaya Ummu ta zo amma
ya hana, don haka ta hakura tunda daman Zulaihan ce mai taya ta. Tayi zaton kwana zai yi yana mata mita
sai kuma ta ji shiru. Duk da kowa a dakinsa ya kwana amma ta sami natsuwa da ta tabbatar yana nan, ko
da wani abun zai faru sai kawai ta taso shi. Da yake ma Baffan ya gaji sosai ga kika da yayi sannan da
alluran da akayi masa sai yayi ta baccinsa har asuba.
EPISODE 17



Kafin karfe bakwai da rabi ta karasa Madu har ya shirya da yake ya ji lokacin da likita yace karfe bakwai
da rabi za su kawo shi a sake wankewa. Abba ya ji dadi sosai da ya fito ya tarar Madun ya shirya, nan da
nan ta fito ya daukar mata Hanan ta dauki Baffa suka kama hanya. Haka aka kuma sa Madun ya rike
Baffa aka sake wanke kunar sannan aka mommotsa yatsun, aka sa bandeji da magani aka daure.
Ma’aikacin lafiyar yace

“Yallabai sai kuma gobe, amma za ku dinga motsa masa yatsunsa idan ba haka ba in hannun ya warke za
su makale a haka. Ai ka ga yanda yanzu nake motsa su yana kuka ko?”

Yace

“Eh.”

“Haka za a dinga yi masa a kalla sau uku a rana, idan ta fara kamewa sai a kara yawan motsawar.”

“Toh bari na kirawo ta sai kayi mata bayani.”

Ya fito wajen ya bata Baffan sanan suka koma ciki inda ma’aikacin ya kara yi mata bayani, suka sallamesu
suka tafi. Kafin karfe tara na safe Zulaiha ta iso don haka ayyuka suka dan yi mata sauki. Mahaifiyarta ma
ta zo tare da ‘yan uwanta domin duba Baffa. Ahmad ma har da kayan dubiya ya shiga har wajen nata ya
duba shi. Ko da yamma tayi ta so ta motsawa Baffa hannun kamar yanda likita ya bayar da umarni amma
ta kasa, saboda da ta kama hannun sai ya sa kuka. Don haka ta kirawo Abban ta sanar dashi ta ce masa
sai dai su koma asibiti a motsa masa ita ba zata iya ba. Sai da ya gama yi mata fada sannan ya ajiye waya
yacewa Madu ya taso daga kasuwa ya ajiye shi a gym ya huce ya kaisu asibiti

“Abba ai ni zan iya motsa masa.”

“Ka tabbata.”

“Allah Abba zan iya.”

Nan da nan ya kira ya sanar da ita ta jira sai sun dawo. Ana dawowa Madu ya rike shi ya mommotsa
hannun yana ta ihu. Daga nan ya zama in aka je asibiti akayi dressing da safe sai Madu ya motsa yatsun
da yamma.




Haka kawai Nawwara ta koyo zagi, idan suna wasa ita da Ummi abu kadan sai ta cewa Ummi banza, ko
shegiya ko kuma tace ubanki zan ci. Ana ta kokarin hanata amma bata hanuwa, ga shi ta hada da
murguda baki. Kwana uku da konewar Baffa Karami suka shigo falon Mommy ita da Ummi, Auta yana
zaune yana video game suka karasa wajenshi suka zauna. Yana game dinsa yana jansu da wasa. Mommy
ta fito ta basu alawa sai auta ya dauke ta Ummi yana tsokanarta kamar zai shanye, ai kuwa nan da nan ta
sa kuka. Kafin ya mika mata alawar sai Nawwara ta dube shi tace

“Ka bata alawarta shege kawai, ubanka.”
Kafin ta rufe bakinta shi kuma ya buge mata bakin yana fadin

“Ba na hanaki wannan zagin ba, in kika kuma sai na yanke bakin.”

Ai kuwa ta fashe da kuka iya karfinta ta tashi ta fice da gudu. Ya dubi Ummi ya ‘daga ta tsaye yace

“Je ki ki cewa Umma zagi Nawwa take yi.”

Nan da nan Mommy ta fito daga kichin tace

“Na ce ka daina bawa yarinyar nan kuka ko? Me kayi mata?”

“Mommy shege fa tace min.”

“Toh kai baza ka iya hakuri da yaro ba?”

Ya sunkuyar da kai ita kuma ta koma kicin don ta karasa aikinta.

A guje Nawwara ta shiga falonsu tana kuka, kafin ta karasa Zulaiha wadda suke zaune tare da Saudah
tace

“Faduwa kika yi ne Nawwa.”

Kafin tayi magana Ummi ta shigo da gudunta itama tace

“Ya Auta ne ya fasa mata baki, ya ma ce zai yanke bakin in ta sake zagi tace shege tace banza.”

Zulaiha ta rungumota tana bata hakuri

“Yi hakuri, ai wannan yayan naki ya iya mugunta wallahi.”

Ta bude bakin kamar tana duba leben tana duban Saudah tana fadin

“Kalli fa, har saida ya fasa mata lebe.”

A fusace ta ajiye remote da yake hannunta tace

“Sai ayi ta dokar maka yaro saboda ba’a san ciwon haihuwar ‘ya mace ba, ko su wa ya doke su ohtac

Ta mike a fusace tana fadin

“Wallahi yau sai na je na ja masa kunne idan ma saka shi ake yi a san ba zan dauka ba. Tunda aka fara
fasa mata baki wata ran za a zubar mata da hakoran.”

Zulaiha tace

“Gaskiya dai ya kamata.”

Ta fice ta nufi wajen Mommy. A zaune ta sameta a falo. Bata yi sallama ba ta shiga amma ita Mommy sai
taji kamar ta yi sallama don haka tace

“Wa alaikum salam, Umman Nawwara.”

A fusace tace

“Ina Auta “
“Yanzu ya fita, wani abu zai yi miki?”

“A kan me ya daki Nawwara har ya fasa mata baki saboda mugunta.”

Mamaki ya cika Mommy ta dai san ya buge mata baki amma bata san anyi fashewar ba, tace

“Subhanallahi, ai kuwa zai zo ya sameni. Nawwara ce yanzu ta baci da zagi amma kuwa bai kyauta ba.”

“Bana son wulakanci tunda ba uwar wani ta zaga ba na meye za a fasa mata baki saboda mugunta.”

Mommy ta ji abun wani banbarakwai tana tsaye a kanta tana mata wadannan maganganun, itama sai ta
mike tsaye. Saudan ta bita da harara daga kasa har sama tana fadin

“Ki dai ja masa kunne don ban ga uwar da ta haifar min yarinya ba da za a dinga dukanta kamar wata
jaka.”

Mamaki ya kara cika Mommy tace

“Ikon Allah, kada fa ki zage ni Saudah.”

“In na zage ki ma na zagi banza, danki ne ya janyo….”

Kafin ta rufe bakinta Mommy ta wanke ta da mari ta nuna ta da yatsa tana fadin

“Ki hanata zagi ko ki hanata shigowa nan, ko da yake ma gadon rashin kunya ta yiwo. Amma mudin za ta
shigo na tayi zagi toh za a tsawatar mata daidai gwargwado.”

Tuni ta dafe kumatu idonta ya cicciko da hawaye tana bin Mommy da kallo cikin takaici da mamaki don
bata taba tsammanin za ta iya kai hannunta jikinta ba. Ta ce

“Kika mare ni?”

“Eh tunda baki da kunya ba, kuma na mari banza.”

Tuni idanuwanta suka rufe domin hawaye duk sun cika idanuwan tace

“Wallahi sai kin ga wadda kika mara, za ki gane kurenki.”

“Ko kuma ke ki gane naki kuren ba, mara kunyar karya kawai.”

Ta juya ta fice daga falon a fusace tana shiga falonta ta fizgi wayarta da take kan kujera ta shige dakinta,
Zulaiha tana faman tambayarta me ya faru bata ko saurareta ba ta rufo kofa. Nan da nan ta tashi ta
manna kunnenta a jikin kofar dakin don ta fuskanci waya zata yi kuma tana so taji me za ta ce. Tana
shiga dakin ta kirawo Abba, yana dauka ta sa kuka

“Subhanallahi, me ya sami Baffan?”

Ya tambaya domin ya zata wani abune ya samu Baffa ko kuma hannun aka fama masa. Cikin kuka tace

“Mommy ce ta mare ni.”

“Mari Kuma?”

Ya tambaya da mamaki matar da ya san ko yara bata fiya dukansu ba yau itace za ta mari wata.
“Eh, har sau biyu ma.”

“Toh ke me ya hadaki da ita har ta mare ki?”

Ta zuke majina irin na me kuka tace

“Auta ne ya fasawa Nawwara baki har Saida aka wanke mata da ruwan dumi shine don nayi magana ta
dinga kwada min mari.”

Mamaki ya cika shi, sai ya ji abun kamar a mafarki domin idan shi za a tamabaya Rabi bata ma da fada
balle har ace ta mari Saudah.

“Toh yanzu ina Mommyn take?”

“Ta tafi ta dauko bulala wai zane ni zata yi.”

“A’ah, sai kace wasu kananan yara.”

“Ni dai na gaya maka wallahi idan ta shigo nan baka zo ba nima ba yarda zan yi ba komai zai iya faruwa.”

Yayi tsaki yace

“Bari na kirawo ta.”

Tana ajiye wayar Zulaiha ta bar bakin kofar tana dariya tana fadin

‘Amma Mommyn nan muguwa ce wallahi.’

Ta koma ta zauna kamar bata taba tashi ba. Ita kuwa Saudah komawa tayi gefen gadonta ta zauna ta
fara murje idanuwanta tana durje fuskarta domin tayi shirin yiwa Mommy sharri, tunda ta mare ta yau
sai ta koya mata hankali. In batayi wasa ba sai ta saka mijin nata ya mare ta.

Bayan Saudah ta fita sai ta janyo kofarta ta sa mukulli ta rufe ta shige dakinta ta kwanta don tayi bacci.
Bata Dade da kwanciya ba kiran Abba ya shigo, ta kalli wayar ta mayar ta ajiye tace

“Bazan dauka ba don bani da lokacinku.”

Haka wayar tayi ta tsinkewa yana sake kira har sau uku bata amsawa, sai ma ta saka wayar a silence ta
juya ta cigaba da baccinta. Da yaji ya kirawo ba’a dauka ba sai yayi tunanin kada fa zancen Saudah ya
tabbata, ko dai zanetan ta tafi yi shi ya sa bata ji wayar ba. Nan da nan ya mike ya dauki mukullin mota
ya kamo hanyar gidan. Yana hanya ya sake kiran Saudah yace

“Yanzu ke din kina ina?”

Har yanzu cikin muryar kuka take bashi amsa tace

“Ina dakina.”

“Toh ki zauna a nan kada ki fita sai na zo, Ina Zulaiha?

“Suna falo ita da yaran.”

“Toh shike nan ku rufe kofa ku zauna yanzu zan zo.”
Ya ajiye waya ya kara gudun motar, don kada ayi batacciya kafin ya isa. Yana tsayawa a bakin gate ya bar
motar ya shigo, Mal Bala yana bacci don haka babu kowa a tsakar gida. Yayi mamakin matuka da bai ji
wata hayaniya a gidan ba. Ya nufi wajen Mommy ya kama hannun kofar yajita a kulle, mamaki ya lullube
shi. Yana da mukullin amma sai ya juya ya huce wajen Saudah. Yana shiga ya sami Zulaiha da yara a falo
yace

“Ina Umman take?”

‘Tana ciki.”

Ya huce ya sameta mamakinshi yana kara yawa don ya zata a hargitse zai zo ya tarar da gidan. Yana Buda
kofar dakin ya ganta a zaune tans ta share hawaye. A kusa da ita ya zauna yana mata kallon mamaki yace

“A’ah, a ina ta ganki ta mareki. Na ji kofarta a rufe.”

Ta kara fashewa da kuka sannan tace

“Wallahi sai dai in yanzu ta rufe don nan ta gama zagi na ta mareni har sau biyu tana cewa zata dauko
bulala ta zaneni.”

“A’ah, amma fa da mamaki.”

Ya mike tsaye yace mata

“Taso mu je na gani.”

Ya tasa ta a gaba suka huce wajen Mommy, suna zuwa bakin kofar ya sa mukullinshi ya bude suka shiga.
Babu kowa a falon don haka Saudah ta zauna a falon shi kuma ya huce dakin. Bacci take yi hankalinta a
kwance don sai da yaje tsakiyar dakin sannan ma ta yi juyi ta bude ido. Ta tashi zaune ta dube shi tana
mamaki ta dauki waya ta duba lokaci tace

“Sannu da zuwa, yau har ka dawo da wuri haka ko azumin ne?”

Yanda fuskarta ta nuna kamar ma ta dade tana baccin don har wata hamma take yi, ya kara cika da
mamaki yace

“Zo mu je falo kya ji bayanin.”

Ta biyo bayanshi suka fito, kafin sun gama zama ta dubi Saudah tace

“Umman Nawwara, ya jikin Baffan Allah ya sa dai lafiya na ga kamar kuka kike yi.”

Ta galla mata harara ta ja tsaki sannan ta juya mata keya. Mommy ta dubi Abba tana mamaki tace

“Ikon Allah, wai me yake faruwa ne.”

Yace

“Nima shi nazo na tambaye ku.”

Ta kalleshi ta kalli Saudah wadda take ta cika tana batsewa tare da share hawaye tana mamaki, da yaji
babu wadda tayi magana a cikinsu ya dubi Mommy yace

“Ta ce kin mareta har kin tafi dauko bulala ki zaneta ko kin zanetan ne ma ni ban sani ba.”
Mommy ta zazzaro ido ta dubi Saudah tace

“Ni na mareki har na zaneki?”

Ta juya ta dubi Abba sannan ta cigaba

“Ni yau ko haduwa bamu yi ba ai, kana fita na gyara kicin nayi wanke wanke na tafi na kwanta fa don ko
Baffa banje na gano ba nace sai da azahar.”

Ta juya ta dubi Saudah wadda kawo yanzu tayi mutuwar zaune saboda takaici da mamaki don bata taba
zaton Mommy ta iya drama haka ba

“Toh kuma a ina na ganki na zaneki ko marinki ne nayi?”

Ta zumbura baki tace

“Wallahi a nan a tsaye kawai daga na zo ina ce miki ki yiwa Auta fada ya daina dukan Nawwara don ya
fasa mata baki.”

Mamakin mommy ya karu ta dubi Abba wanda yake zaune yana kallonsu da mamaki tace

“Auta ai tun dazu ya fice, kafin dai na kwanta yana nan da su a Nawwaran har na basu alawa. Dana ce
masa kwanciya zan yi kuma ya tashi yace na rufe kofa zai kaisu wajen Ummansu shi waje zai fita. Na rufe
kofar ya fice da su a lokacin ma kuma babu alamar an fasa bakin wani don ko babu komai ai za a yi
kuka.”

Ya juya ya dubi Saudah yana jiran bayaninta. Ta sunkuyar da kai tayi kwafa tace

“Wallahi karya ne.”

Abba ya fara fusata saboda yanda ta bata masa lokaci ta taso shi daga kasuwa ya yi sauri ya tare ta

“Itace take karyar ko kuwa ke kike mata karyar?”

Tace

“Wallahi ka tambayi yaran ma, ai ga Nawwaran can a falo.”

Mommy tace

“Ikon Allah.”

Abba ya ja tsaki a fusace ya dubi Saudah yace

“Sai ki tashi muje.”

Ta mike ta huce tana cewa

“Wallahi haka aka yi sharri me kawai.”

Tana harar Mommy.

Shi kuwa Abba Bai sake ce mata komai ba ya tasa ta a gaba suka fice. Suna fita tabi bayansu da kallo tace
“Yaushe kika zo duniyar da zaki ki fini iya kisisina, ai dama na gaya miki na daki banza.” Sannan ta rufe
kofarta ta koma ta kwanta.

Suna shiga falon Nawwara ta taso tana Abba. Ya tsuguna ya dawo dai dai tsahonta yana duban bakinta,
bai ga alamar komai a bakinta ba sai dankon alawa da ya dan ‘bata gefen bakin yace

“Me kika ci haka bakinki ya baci.”

Tace

“Alawa.”

“Wa ya baki alawa.”

“Mommy ce, Ya auta ya bare min.”

Ya dago ya dubi Saudah suka hada ido, kafin Nawwara ta kara cewa wani abu ya tashi ya nuna Saudah
wadda take zaune a kan kujera tana ta yace

“Bana son irin wannan shirmen, kada ki kuskura ki saki in ba haka ba ranki ne zai yi mugun bacyac

Kafin tace wani abu ya juya ya fice. Kasa hada ido tayi da Zulaiha saboda takaicin yanda yayi mata
wannan fadan a gabanta. Nan da nan idonta ya ciko da kwalla tayi sauri ta tashi ta shige dakinta ta turo
kofa, ta bar Zulaiha a nan tana mamaki don ita da taga ya dawo ta zata Mommy za ayi wa fadan. Haka ya
koma kasuwa yana ta tunani a ranshi don ya kasa gane me ya faru, me ye manufar haka, me yake damun
Saudah ne, ko dai shaye shaye ta fara. Haka har ya Isa kasuwar. Da yake a Mommy ce take da girki sai da
ya Sha ruwa ya gama duk abinda yake yi sannan ya dube ta yace

“Wai don Allah me ya faru dazu ne?”

Cikin halin ko in kula ta bashi amsa

“Na me fa?”

“Da kanwarki ta kirawo ni daga kasuwa.”

Tayi ‘yar dariya tace

“Toh ai ni ban san me ya faru ba, bacci kuka tashe ni kawai kuka yi drama kuka fice baka yi min bayani
ba.”

“Hmm! Haka kawai ina kasuwa ta kirawo ni wai kin mammareta kuma kin tafi samo bulala ki zane ta, da
na kirawo ki naji shiru kawai sai na zata gaske ne.

Ta kyalkyale da dariya

“Toh yanzu ko ni na haifeta ta kai wadannan shekarun ai ta huce duka sai dai nasiha da lallashi, ni ko
haduwa ma bamuyi ba sai da kuka shigo. Wayata na saka a silence na kwanta shi yasa ban ga kiranka
ba.”

“Allah ya sauwake, kema na ce ki daina sa wayarki a silence don kawai za kiyi bacci amma kin ki.”
Har suka kare hirarrakinsu suka kwanta yana mamakin abinda ya faru. Ita kuwa Saudah haka ta kwana
ranta babu dadi don wannan takaici da Mommy ta kulla mata, ita bata ma taba sanin matar tana da
wayo haka ba sai yanzu.

Washegari Abban bai dade da fita ba aka yi sallama a gate, da yake Malam Bala yana bandaki kafin ya
fito amsawa har Zulaiha ta fito don haka sai ta dan tsaya daga kofar falo tana jiran ta ga waye. Bayan
Bala ya bude gate din sai bai gane mai bugun ba don haka sai ya fita daga waje. Bayan sun gaisa ya bashi
sakon dankalin bature buhu guda da doya wajen guda ashirin yace Baba karami ne ya siya daga Jos yace
a kawo. Ya karba suka yi sallama dan aiken ya ja motarshi ya kama hanya sannan Bala ya bude gate din
ya dauki buhun danklin ya saba a bayanshi ya shigo da shi ya huce wajen Mommy. Yana hucewa Zulaiha
ta koma tace wa Saudah

“Dankali aka kawo buhu guda da kuma doya gata can ta fi talatin ana shigarwa wajen Mommy.”

Nan da nan ta mike ta fito ta sami Malam Bala ya dauko daurin doya ta tareshi tace

“Bala ba store yace ka ka kai kayan ba kake kaiwa can.”

Ya russuna kamar yanda ya saba yace

“Ranki ya dade cewa yayi a kaiwa Hajiyan ai.”

Ta jijjiga kai ta juya ta koma falo. Duk lokacin da aka kawo abinci akwai store a kusa da gareji nan aka
saba ajiyewa sai dai kowacce idan za ta yi girki ta diba don haka da taga an huce da dankali da doya sai ta
zata wani sabon wulakanci ne Abban zai yi mata saboda abinda ya faru jiya. Tana shiga ta dauki wayarta
ta shiga daki ta kirawo shi, bayan ya amsa wayar tace

“Abban Nawwara na ga an kawo doya da dankali

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login