Showing 75001 words to 78000 words out of 196754 words
Chapter 26 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
amma Mommy ta sa ana kai mata daki.”
“Doya da dankali kuma ko kuwa za ki maimaita haukan da kika yi jiya?”
Takaici ya kamata, tace
“Ai sai ka ce min kawai ba za ka bani dankalin ba ba sai ka mayar dani mahaukaciya ba.”
Kafin yace wani abu ta ajiye wayar. Nan da nan ya kira Mommy ya tambayeta, tace
“Baba ne ya bayar a kawo yanzu muka gama waya, dan aiken ne yace a bani shi yasa Bala ya shigo da shi
nan amman Baban ma ya ce kai ya bawa.”
Yace
“Kai yaron nan baya gajiya, nima yanzu zan kirawo shi. Ki sa Balan kwashe ya mayar store din ko kuma
barshi a nan sai na dawo din.”
Tace
“Toh babu damuwa.”
Suka yi sallama.
Sai daf da magariba sannan ya dawo da yake a wajen Saudan zai Sha ruwa can ya fara shiga don ya ajiye
kayansa. Da kyar tayi masa sannu da zuwa ya amsa yana dariya sannan yace
“In dai dankali da doya kike yiwa toh ba ni na saya ba, Baba ne ya saya daga Jos yace a kawo mata.
Amma na San zata raba dake kar ki damu.”
Ko kallonshi bata yi ba saboda bata son tayi rashin kunya don Zulaiha ta na wajen, ya huce yana mata
dariya. Har aka sha ruwa tana ta wani faman zumbura baki shi kuwa yayi burus da ita.
Da gari ya waye bayan ya gama shiryawa sai ya shiga wajen Mommy, kuma da yake saboda azumin sai
wajen goma da rabi yake tafiya kasuwar sai ya zauna a falon ta yana kallon labarai, wayarshi tayi kara ya
dauka. Baffan Zulaiha ne bayan sun gama gaisawa yace
“Sa’a ce dama me babur ya bugeta yanzu babu dadewa.”
A firgice Abban ya bashi amsa
“Subhanallahi! Yaushe kenan? Allah ya sa dai bata ji ciwo da yawa ba.”
“Eh toh, gamu dai a asibiti yanzu likita ya dubata, an dai bamu gado don ta dan ji jiki.”
“Subhanallahi, Allah ya sauwake. Ni ma ya zu zan taho in sha Allah.”
“Yauwa daman shine zan ce ko za a taho da Zulaihan saboda babu mai zama da ita a asibiti a nan din.”
“Hakane, nan din ma da yake Baffan ya sami lafiya in sha Allah tare za mu taho da Zulaihan.”
Suka yi sallama suka ajiye waya. Mommy da take gefensa ta dubeshi tace
“Me ya sami Sa’an.”
Ya gaya mata abinda ya faru tace
“Ai sai na shirya mu je tare ko?”
“A’a, ku bari idan na je na gano kwa je daga baya.”
Ya kwalawa Madu kira yace ya fito za su tafi Bichi. Kafin ya gama shiryawa ya shiga wajen Saudah ya
gaya mata. Tace
“Toh yanzu da Zulaihan za ku tafi.”
Yace
“Eh, ai Baffan ya fara samun sauki na ga ya rage rigima kuma tunda na ga kin sami mai wanke wanke ai
kinga aiki ya ragu.”
“Toh ai ita mai wanke wanken bata raino saboda tsohuwace fa.”
“Au yanzu ke sai ki bata yaran saboda ba kya daukan darasi ko? Yayi miki daidai.”
Zulaiha ta fito tana share hawaye tayiwa Saudah sallama suka kama hanya sai Bichi. Suna isa suka huce
asibitin inda suka same ta a kwace har an yi mata dinki a goshi inda ya fashe, kuma da yake an yi mata
allura bacci take yi. Sai daga baya Baffan zulaihan yayi musu bayanin cewa ta sami tsagewar kashi a kafa
daya kuma ta bugu a kanta shi yasa likitan yace a bari ta kwana a gani. Ya dubi Zulaiha da take ta kuka
yyac
“Ki daina kuka ba wani babban abune ya same ta ba, da yake mai babur din da ya kadeta ba da gudu
yake tafiya ba abin da sauki, idonta ma biyu tana hirarta sai da likita yayi mata allura sannan ta fara
bacci.”
Ta dan share hawayenta ta matsa kusa da Umman. Abba ya ja Baffan suka fita Suka zo wajen motar ya
zaro kudi ya bashi naira dubu ishirin yana fadin
“Ga wannan ko za a bukaci wani abu, idan akwai wani abun kuma sai muyi waya. Allah ya bata lafiya,
don Allah kuma in ta farka ko Zulaiha ka gayawa tayi min waya muyi magana.”
Ya karba yana godiya
“Toh Alhaji an gode Allah ya bar zumunci, in Sha Allah za a kirawo ka da ta farka.”
Suka kama hanya shi da Madu suka dawo.
Tunda suka tafi da Zulaiha Saudah take ta fargaba, gobe tana da jarrabawa ta gama sakankancewa
Zulaiha tana nan zata rike mata yara taje ta dawo gashi kuma yanzu Zulaihan ta tafi babu ranar dawowa
tunda mahaifiyarta ce a kwance. Gaba daya tunaninta ya kare, ta san dai babu zancen Anti Hadiza don
ko an barta ma ba zata sake iya bata raino ba balle ma ba za a barta ba. Ta san ba zai barta ta kaisu gida
ba duk da ita ma ba so take ta kaisun ba saboda bata jin za a kula dasu yanda take so. Ta dai so ace ya
bar Yaya Ummu tazo don in a nan ne zata kular mata dasu tunda babu wani abu da za ta yi. Haka dai har
ta gaji da lissafi don haka ta barshi a zuwan in ya dawo zata yi masa maganar, duk da tana tsoron yi masa
maganar ma don bata san mai zai ce ba. Fatan ta daya Allah ya sa kada yace zai hanata zuwa jarrabawar
nan don kuwa za ayi rigima da ita. Ta riga ta game ba son karatun nan nata yakeyi ba, ita kuma babu ya
da za ayi ta zo har level 3 sannan ta bari, ba zai ma yiwu ba.
EPISODE 18
Daga Bichi kasuwa ya huce don haka sai daf da shan ruwa ya dawo, lokacin kuwa tana tsaka da aiki da
yake itace da girki. Bayan an sha ruwa yana kashingide a falonta yana kallon TV yayinda ita kuma take
zaune tana bawa ‘yan biyu abinci, ta dan yi gyaran murya tace
“Abban Nawwara gobe fa ina da jarrabawa.”
Ba tare da ya kalleta ba ya bata amsa
“Allah ya bada sa’a.”
Ta dan yi shiru kamar tana tunanin wani abu, jimawa kadan tace
“Toh a ina zan bar yaran?”
“Da ya kika shirya za kiyi da su?”
“Toh ai ka ga dama Zulaiha nake tunanin bari da su gashi ta tafi gida.”
“Eh, don kuwa Sa’an ma tana kwance likita ya ce a barta ta kwana biyu bata komai saboda ta buge a
kanta gashi kuma kan nata yana ciwo. Dazu ma Baffan Zulaihan yace min sun je an yi hoton kwakwalwa
sai gobe za a kaiwa likitan in ya ga babu matsala watakil ya sallameta goben.”
“Allah sarki, Allah ya bata lafiya.”
Suka dan yi shiru da taga ba zai sake cewa komai ba tace
“Su Ummanmu kuma bayan fitarka na kirawo su ashe ita da Ya Ummu sun tafi Warawa, a kan maganar
gonar Baban su Umman da ake rigima akan rabon gadonta.”
“Ikon Allah, ashe har yanzu basu samu an raba wannan gonar ba?”
“Uhm! Kasan tana da girma kuma masu son ta suna da yawa har wadanda basu da gadonta nema suke
suce ya sayar musu da wani kaso kafin ya rasu.”
“Allah ya sauwake.”
Suka sake yin shiru na wani dan lokaci sannan tace
“Umman dai ta ce min goben kafin magriba za su dawo don haka jibi zan iya kaisu, amma goben nake
tunani. Ina da paper 4pm to 6pm.”
Ya gyara zama yana tunani, da aka dan yi jim ya dube ta yace
“Sai ki barsu wajen Mommy tunda jarrabawar ba dadewa bane, zan yi mata magana in an jima in na
shiga wajen nata.”
Tace
“Toh Allah ya kaimu.”
Hakan ya samar mata natsuwa dama ba ta so ta kaisu gidan Ummanta domin can akwai kasa a tsakar
gidan. Gashi Ummansu ba ta hana yara wasan kasan takan ce a barsu suyi na lokaci ne. Kullum suka je
gidan haka ake barinsu suyi wasan kasa su more. Can a kasan zuciyarta ta san Mommy bata da mugunta
don haka bata jin wani abu zai sami yaranta in ta barsu a wajenta, in dai ma ta barsu goben to jibi ma
nan za ta barsu ai dai daga nan an gama.
Bayan ya dawo daga sallar tarawih ya kamata ya shiga wajen Mommy, amma da yake ya bar wayarshi a
falon Saudah kuma yana son yin waya sai bai shiga ba, yana dawowa kawai sai ya huce wajen Saudah.
Inda ya bar wayarshi nan ya sameta, ya dauka ya duba har ma an kirawo shi. Nan ya zauna a kan kujerar
dining table ya fara waya; kayansa ne suka zo bayan ya biya duk wani clearance na custom sai aka ce wai
ba a ga rasit ba sai ya sake biya shine yake ta shige da fice don ya tura musu wani rasit din kada su lalata
masa kaya. Haka ya zauna ya dinga kiran mutane har wajen awa daya, bayan ya gama Saudah ta zuba
masa shayi ya sha sannan ya tafi wajen Mommyn. Da ya shiga wajen nata babu kowa a falo sai Ahmad
yana zaune a dining table yana aiki a computer. Abban yace
“A’ah, lissafin kudin ne har yanzu amsar bata fito ba chief account officer?”
Yayi dariya yace
“Wani dan aiki ne Abba ban karasa ba.”
“Toh Allah ya bada sa’a, Yanyanka ka biyewa kukayi ta yawo gashi ya hau jirgi ya barka da kwanten aiki.”
Abban ya fada. Da yake Baba karami ya zo tun ranar Juma’ah kuma tunda ya zo suke ta yawo suna yiwa
dangi gaisuwar azumi har Bichi sai da suka je, yau da safe ne suka je wajen Baffa Hassan daga can
Ahmad ya ajiye shi a airport ya huce.
“Ina Mommynka? Abban ya tambaye shi
“Tana daki.”
Ya huce ya nufi dakin nata. Tun daga bakin kofa ya ga alamar fitilarta a kashe take don haka ya tura kofar
a hankali. A kan gado ya hangota , sai da ya karasa tsakiyar dakin ya tabbatar lallai tayi bacci don da bata
yi bacci ba yana taba kofa za ta farka. Don haka sai ya juya ya fito ya mayar da kofar a hankali ya rufe. Ita
kuwa tana jinsa tayi shiru saboda tun da ya dawo masallaci take jiransa. Ya riga ya saba idan ba ke ce da
kwana ba yana dawowa daga sallar tarawih wajenki zai fara shiga, baya fin minti ashirin sai ya fice ya
koma inda zai kwana. Da yake yana son fruit salad yau har dibar masa tayi kafin ta sa suga ta sa shi a
fridge yayi sanyi tana jiran in ya shigo ta bashi amma shine sai yanzu wajen sha daya sannan zai shigo,
don haka tana jinshi ta yi luf har ya gama tsayuwarashi ya fice. Ya tarar da Ahmad a inda ya barshi yace
“Kannenka duk sun kwanta ko?”
“Eh Abba.”
“Toh Allah ya bamu alkhairi, zo ka rufe muku kofar.”
Abban ya fice Ahmad ya rufe kofa ya koma ya ci gaba da aikinsa.
Washe gari da safe da wuri ya shirya zai fita saboda akwai wanda ya kamata ya gani a kan maganar rasit
din da ya kai har Lagos aka ce ya bata. Sai da ya gama shiryawa tsaf wajen karfe tara sannan ya fito ya
shiga wajenta. A wannan lokacin har ta gama wanke wanke da gyaran gida da taimakon yaran har sun
tafi makaranta. Ta fito daga wanka tana zaune a gaban mudubi ya same ta, bayan ta amsa sallamarshi
yace
“Jiya ai na shigo kina ta minshari har bakin gate ana jiyowa.”
Tace
“Toh maigidana ya iya cefane, na ci na koshi ba sai nayi ta bacci ba.”
Yayi dariya yace
“Lallai ne, Allah sarki maigidanki duk kudinshi a nan suke karewa a cefane.”
Itama dariyar tayi tace
“A’a kudi dai ba nan ake kawowa ba banki ake kaiwa, ni cefane kawai na karba.”
“Wallahi custom ne suke son su yi min tsiya duk da na kula kamar akwai Hadin baki shi yasa har wajen
sha daya Ina ta waya sai da na gama sannan na shigo kun yi bacci kebda yara. Yanzu ma can office dinsu
na Kano zan je don kamar matsalar daga nan ne.”
“Toh Allah ya warware, in Sha Allah ba za a sami matsala ba.”
Har ya juya zai fita ya dawo yace
“Za ta kawo miki yara ki rike mata su za ta je makaranta jarrabawa.”
Ta kalleshi tace
“Wa kenan?”
“Saudah mana, tana da jarrabawa in an jima.”
“Allah ya bada sa’a, sai dai nima zan je islamiyya 12pm zuwa 1pm gashi idan na dawo nice da aiki bazan
sami damar rike mata su ba.”
Ya kalleta da mamaki ya saki hannun kofar da da ya rike zai bude yace
“Toh ai ita sai wajen biyu za ta fita.”
“Ta tafi da su kawai, ba zan sami dama ba.”
Mamaki ya kara kama shi
“Rabi, nace ki rike mata su taje jarabawa ko?”
“Don Allah ka bar wannan zancen.”
Ta dauke kai
Ya bita da kallo na dan lokaci sannan a fusace yace
“Umarni nake baki Rabi kina gaya min ba za kiyi ba? Toh idan ta kawo miki su ki zubar dasu ko ki kore
su.”
Ba tare da ta kalleshi ba tace
“Ba wai n….”
Kafin ta karasa fadar abinda za ta fada ya fice ya rufe mata kofar da karfi sai jiyo karar rufe gate tayi ya
riga ya fita. Ta ja tsaki a fili tace
“Wallahi ba zan rike mata su ba sai dai ka zauna ka rike mata su, shekaran jiya ta gama zagi na sannan
yanzu a zo ace za ayi min dole. Kwa san yanda za kuyi da yaranku tunda ba ni na haifa muku su ba.”
Ta kasa gane abinda ya sa yake so lallai sai ya takura mata. Ita fa dama ba mace ce mai son raino ba,
yaranta ma da Allah ya bata Allahn ne kadai ya san yanda tayi rainonsu don wata rana in ta kalle su ita
da kanta ma ta kan tambayi kanta ya akayi ta sami karfin halin jure rainon yaran nan. Shekarun auta
goma sha uku don haka ta manta yanda ake goyo, yanzu raino ko na ‘da ‘daya baza ta karba ba balle na
biyu ko da kuwa na minti daya ne. Da ma ana ganin mutuncin ta ne. Kuma yanzu wannan da yake da
kuna a hannu ma ita ya za ta yi da shi? Shekaran jiya aka gama cewa Auta ya fasawa Nawwara baki idan
ta karbi wannan duk abinda ya sami kunar nan haka za a ce itace. Ta yatsina baki ta fada a fili
“Wallahi bazan karba ba, kwa san ya da za kuyi da su.”
Shi kuwa Abba yana fita daga wajenta ya shige mota ya fice, bai koma wajen Saudah ba domin ya riga ya
gama magana da ita. Ya barta a kan idan ta shirya ta kaiwa Mommy su ta tafi. Har yaje office din custom
yana tunani kala kala, ya rasa wannan kiyayya ta Rabi da Saudah. Ga shi a zahiri sai ya ga kamar Rabi ba
kiyayya take nunawa ba, amma yanda take nuna musu halin ko in kula yayi yawa. Ya san an dan sami
matsaloli amma ai komai ya huce tun tuni. Ita ko tausayin yarinyar nan bata ji ma, balle ta taimaka mata
da yaran. Kafin ya gama abinda yake yi ya isa kasuwa ya manta da wannan maganar ma gaba daya.
Itama Mommy yana fita ta zira doguwar riga ta kwanta bacci. Sai wajen sha biyu saura sannan ta tashi,
da yake saboda azumin yanzu 12pm zuwa 1pm suke islamiyya don haka nan da nan ta shirya ta zura
hijabinta ta fice islamiyya. Sai wajen karfe daya da kwata ta dawo, har zuwa lokacin kuma Auta da
Khalifa basu dawo daga makaranta ba. Suna da mukullin kofar falon don haka tana shiga sai ta mayar da
mukulli ta rufe kofar saboda wanke fuska kawai zata yi ta dan kwanta ta huta kafin karfe biyu mai taya ta
aikin azumi ta zo, don sun riga sunyi sallar azahar a makaranta. Bayan ta wanke fuska ta kwanta kenan a
dakin sai ta ji bugu. Ta tashi ta fito tana mita a ranta; idan auta ne sai ta rankwashe shi don tace ya dinga
hakuri yana jiran Khalifa tunda mukullin a hannun Khalifa yake, shi kuma in dai ya ga Khalifa ya tsaya hira
sai yayi sauri ya riga shi zuwa gida. Tana bude kofar ta ga Saudah, sai a lokacin ta tuna da maganar da
suka yi da Abba.
‘Au Bai yarda da abinda nace ba kenan, za su gane kurensu.’
Ta Bude kofar kadan ta tare hanyar shiga tace
“Umman Nawwara ce? Ya yaran?”
“Lafiya kalau, cewa yayi na kawo miki su idan zan tafi jarrabawa.”
Ta fada ba yabo babu fallasa.
Mommy ta kalleta tace
“Sai dai ko baki ji da kyau ba gaskiya ba ni yace ki bawa su ba, don yanzu ma ni zan shiga kicin.”
“Ai kuwa nan yace na barsu, bari dai nayi masa waya muji.”
Ta shiga kokarin zaro waya daga jaka ita kuma Mommy ta mayar da kofar ta rufe. Ta ja yaran suka koma
kan barandar falonta tana mamaki, ba wai na kin karbar yaran kawai ba harda ma na kin bari su shiga
falon. Ta ajiye kayan hannunta sannan ta kirawo shi a waya. Yana dauka bayan ya amsa sallamarshi tace
“Kace na bar su Baffa a wajen Mommy ita kuma ta ce ba a wajenta kace na barsu ba.”
Yace
“A’ah, haka tace Miki?”
“Eh.”
“Tana ina?”
“Tana wajenta ai ta rufe kofa.”
Ya ja tsaki sannan yace
“Bari na kirawo ta.”
Kafin ya ajiye wayar tace
“Don Allah kayi sauri ka ga yanzu wajen daya da rabi, karfe biyu za mu shiga na kusa makara.”
Suka ajiye wayar. Ta kagu ta tafi saboda biyu ta kusa, tsayawa tayi ta gama abinda take yi kafin ta fito
tana tunanin a kasa da minti talatin za ta kai BUK. Da ta San ma Mommy za ta bata matsala da tun wuri
za ta fito. Allah dai ya sa kada su bata mata lokaci.
Suna ajiye waya ya kirawo Mommy, bata ma san yanayi ba saboda wayartata tana daki tana chaji ita
kuma tana dakinshi tana gyarawa don shine kadai bata gyara ba kafin ta fita. Tana can tana aikinta
Saudah ta sake buga mata kofa, kamar yanda tayi dazu haka ta yi mata a bakin kofa. A gaggauce Saudan
ta miko mata waya tace ya ce ki karba za kuyi magana ya kirawo ki baki dauki ta ki wayar ba.”
Cikin halin ko in kula Mommy tace
“Oh, tana chaji wayar bari na kirawo shi.”
Ta juya ta koma ta rufe kofar ba tare da ta saurari me Saudan za ta ce ba. Ta kara wayar a kunnenta tace
“Kana jin abinda tace ko? Ta koma ciki. Don Allah kayi sauri kar na makara biyu fa saura.”
Ba tare da ya ce komai ba ya jiye wayar ya sake kiran Mommy. Ko bi ta kan wayar
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good