Showing 189001 words to 192000 words out of 196754 words
Chapter 64 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
na nemi na dawo ba kai ka nemi na dawo amma shine zata jefe ni da wannan jafa’in. To yanzu na
hakura na janye kara zan cigaba da yawo ana nunani ana yi da ni ana min kallon mutuniyar banza, ba
shikenan ba? Ina fatan dai Allah yasa kada yarana suje neman aure a hanasu saboda wannan zargin ko
kuma wani ya tsaya takarar siyasa a nunashi da wannan maganar da ta yada. Don Allah ku barni na huta,
wallahi bana son fitna kuma kai ka sani. Duk abinda zaku yi kuyi amma ni dai ku daina saka ni a ciki don
Allah, ku barni nayi rayuwata a nutse.’
Ta kawar da kanta ta kalli gefe, ya sa tafukan hannunsa ya juyo da fuskarta takalleshi yace
‘Na ji Rabi, kin ji duk na ji. Kuma in sha babu wata fitna da zata sake faruwa daga wannan in sha Allah.
Kuma ina sake baki hakuri a kan duk ma abubuwan da suka faru, kin ji.’
Ta sake kawar da kai, ya tashi daga gabanta ya koma gefenta a kan gadon ya zauna ya kwantar da kanta
a kafadarsa yana shafa kanta
‘In sha Allahu komai zai wuce, babu wani zargi da zai yi tasiri a kanki. Na san nine mijinki kuma ni na san
ke ba mutuniyar banza bace, in sha Allahu komai zai wuce.’
Sukayi shiru a haka sai ajiyar zuciyarta ake ji. Jimawa kadan ta mike ta dauki hijabin da ta ajiye a kan
gadon yayi sauri ya dafe
‘Na zata kin hakura kuma ina za ki?’
Ta kawar da kai
‘Babu inda za ni sauke kayan zan yi ina so na dan kwanta a kan gadon ne na huta.’
Ya daga mata hijabin ta dauke ya mike ya kwashe kayan kan gadon ya mayar mata wardrobe din sannan
ya rufe kit din ya sauke shi kasa. Tace
‘Bari na shiga bandaki in na fito zan dan yi bacci ne.’
‘To shikenan nima ina dakina idan zan fita zan gaya miki.’
Ta shige bandakin shi kuma ya fice ya shiga nashi dakin. Bayan ta fito daga bandakin ta cire kayanta ta
saka doguwar riga sannan ta kwanta. Bata dade da kwanciya ba Ahmad ya kwankwasa mata kofa ya
shigo, ya zagaya ta bangaren da take kwance ya tsuguna a gabanta yana duban fuskarta yace
‘Mommy bacci zakiyi?’
‘Eh, ka sallami Barrister.’
‘Eh mun gama dashi yace yana godiya.’
Ta dafa hannunsa da ya ajiye a gefen gadon tace
‘To shikenan komai ya wuce ka ji, Allah ya kyauta.’
Kai kawai ya iya jijjiga mata bare da yace komai ba. Jimawa kadan ya mike yana fadin
‘Bari naje na barki kiyi baccinki Mommy.’
Ya fice ita kuma ta gyara kwanciyarta. Shi kuwa Abba ranar ko kasuwa bai iya zuwa ba yana ta zarya
tsakanin falo da dakinsa saboda gani yake kamar idan ya fita ba zai dawo ya tarar da Rabi ba.
…………
Ita kuwa Saudah suna shiga wajen nata ita da Yaya Ummu ta zauna a falon ta sa kuka, Yaya Ummu ta
dubeta da mamaki tace
‘To ba shikenan ba kuma tunda an fasa zuwa kotun, sai dai kawai a kiyaye gaba.’
Ta share hawayenta tace
‘Hakane.’
Kawai yanda taga Mommyn tana kuka ne itama sai taji babu dadi, ba wai ta damu da Mommyn bane
amma tabbas ta ji kunyar kanta kuma ta ji kunyar Baba Yalwa ace itace ta aikata wannan aika-aikar.
Maganar Mommyn ce kawai take mata yawo a ka ‘duk abinda kika yi min kema Allah yayi miki.’ Ta yiwa
kanta alkawarin zata nemi yafiyarata domin idan ita akayiwa irin wannan bata ma san yanda zata yi ba,
sai yanzu nema idan ta hango ita aka yiwa hakan sannan ta gane girman cutarwar da tayi. Shine abinda
ya sa ta kasa daina kukan. A haka Yaya Ummu tayi mata sallama ta tafi saboda bata so Abban ya fito ya
sameta a gidansa. Tana fita ta kirawo Yaya Maryama ta sanar da ita abinda ya faru
‘To ki bi su a hankali ita da Abban, in sha Allahu komai zai wuce. Ita din ma idan kika bita a hankali zata
yafe miki in sha Allahu, ke dai ki zauna lafiya da kowa a gidan kin ji na gaya miki.’
Sukayi sallama suka ajiye waya.
EPISODE 40
Haka suka kwana biyu kowa zuru-zuru, da Abba da yaran gaba daya sai faman lallaba Mommy sukeyi.
Kafin ta fito sun gama abincin safe da ma na rana saboda Abba yana tafiya da shi kasuwa. Shi kuwa
Madu da ba don yanzu akwai nashi harkokin a kasuwar ba da tabbas ba zai je ba, amma haka dole yake
shiryawa su tafi. Gabaki dayansu lallabarsu Abban yakeyi don ya san ransu ya baci, baya so su dauka ya
goyi da bayan Saudah ne. Yana ji yana gani da ya shigo falon kowa zai yi masa sannu da zuwa amma fa
daga haka duk sai su watse su koma dakinsu, ita kuwa Mommy dama ta daina zaman falon kwana biyu
in ya bita dakin kuma sai dai ta barshi yana ta kame-kame. Ranar talatar da abun ya faru haka Rabi ta
barshi ya kwana shi kadai yana juyi da yake kwananta ne; don tun wuri ta kwanta a dakinta tayi bacci shi
kuma ya ji tsoron tashinta. Ranar Laraba haka tayi masa ta tafi dakinta da wuri ta kashe fitilar tayi
kwanciyarta, tana jinsa ya shigo dakin wajen karfe goma tayi kamar bacci take don haka ya juya ya fita.
Sai da ya gama abinda yakeyi ya je yayi sallama da Saudah ya dawo ya rufe kofar, ya wuce daki ya gama
duk abinda yakeyi ya fito ya rufo dakin ya wuce dakinta. Zuwa lokacin ta riga tayi bacci don haka bata ji
shigowarsa ba, kawai sai ji tayi mutum a kusa da ita. Firgigit ta tashi zaune ta mika hannu ta kunna fitilar
gefen gadon, ta muttsike ido ta kalleshi tace
‘Abba, ya na ganka a nan?’
Yana daga kwance yace
‘To kinyi min yaji ba dole na biyoki ba tunda kin san ga inda ya kamata ki kwana amma sai ki taho nan ki
kama bacci.’
Ta kalleshi ta kau da kai
‘Don Allah ka tashi, yara fa suna nan.’
Cikin halin ko in kula yace
‘To ai dama dasu kuka hada baki gaba daya kuke min yaji don haka tunda nan kike so mu kwana ai
shikenan sai ki kashe mana fitila.’
Ta kama haba tana mamaki
‘Don Allah ka tashi zan taho dakin naka ai, bari na fito daga bandaki zan sameka a dakin.’
Ta fada tana mikewa daga kan gadon. Ya gyara kwanciyarsa yace
‘To ina jiranki ki fito sai mu tafi.’
Ta juyo ta kalleshi yanda ya bata rai a dole shi da gaske yake, ta shige bandaki tana yi mamakinsa. Shi dai
ko daya baya so a ki kulashi amma shi idan ya so nashi wulakancin sai ya ki kulata, gashi ya bata mata rai
amma ko irin a dan bar mutum ya huta din nan ma shi baya iyawa. Dole haka ta hakura ya tasata a gaba
har dakinshi sannan suka kwanta.
Ko da gari ya waye da wuri ta shiga kicin don bata son Salim ya rigata, tana sane da yanda gaba daya
shekaran jiya zuwa yau suke kin kula Abban don haka tana so ta nuna musu ta huce suma su huce. Ko ba
komai su ubansu ne babu yanda za suyi da shi, sai su sami matsala a rayuwa idan basu kyautata masa ba.
Nan da nan ta hada wake ta bawa Mal Bala ya mika markade. Kafin ya kawo ta dama kunu, yana
kawowa ta hau soya kosai. Karfe bakwai da rabi Ahmad ya fita da ‘yan makaranta, daga baya kuma suka
zauna a falon ita da Abban suka karya. Haka ya saka ta a gaba ya na ta janta da zance tana bashi gajerun
amsoshi don bata da isasshiyar walwala. Shi kuma baya son ya barta cikin damuwa, ya fi so ya tabbata ta
saki ranta tukuna. Musamman irin wannan abun da takeyi masa, ita bata ki kulashi ba domin duk
hakkokinsa ta sauke amma yanda take sakewa ya fada mata duk wata hirarsa itama tayi tata cikin
walwala duk babu; idan kuma yace fushi take tayi hakuri sai tace ita ba fushi take ba babu abinda aka yi
mata. Haka dai ya gaji ya hakura ya dau abincinsa da kayansa suka wuce kasuwa shida Madu da Salim;
wanda suma tun ranar talatar basu da walwala don yana kula da yanda suke share shi gaba daya.
Haka Baba Karami ya zo weekend ya tarar da su gidan kowa zuciyarsa babu dadi, sun riga sun gaya masa
abinda ya faru a waya don haka shima sai da ya sami Mommy a daki ita kadai ya sake bata hakuri. Tace
‘Ai na hakura Baba, dama na gaya muku ba wai don in rama tozarcin da tayi min bane zan je kotun don
dai kawai a tsawatar mata ne amma hakan ma ai an tsawatar.’
Suka dan yi shiru, jim kadan tace
‘Ka yiwa ‘yan uwanka fada, sun fi ni fushi da Abba. Ina kula da su gaba dayansu har Ahmad din sun daina
kulashi, da ya shigo suka gaisheshi sai su bar wajen. Shi kuma baya jin dadin hakan. Ko babu komai ai ku
ubanku ne dole ku yi masa biyayya, ban sami lokaci bane shi yasa ban yi musu magana ba amma tunda
ka zo kayi musu in basu ji ba kuma za mu sa kafar wando daya da su.’
Ya jijjiga kai yace
‘To Mommy.’
Daga baya ya tashi ya fice. Shi din ma da ta barshi zai dan taba fushin amma maganar da tayi sai ya ga
zancenta gaskiyane, gara dai tunda ita ta hakura su bari haka komai ya wuce. Shi dai in haka akeyi idan
an kara aure gara ya zauna da mace daya, don bai taba ganin Mommy ta shiga damuwa ba kamar yanda
yake gani tunda Abba ya kara auren. Don haka a daki ya samesu gaba daya ya kare musu, ya sa dole sai
an fara kula Abban.
…………
A hankali al’amuransu suka dawo dai-dai, shima Abban ya daina fushi da Saudah. Sosai ta nuna masa
nadamarta kuma a aikace ma ya fara ganin hakan don ta dan canza. Gaba daya yanzu tsoron ma shiga
harkar Mommy takeyi ko kiran sunanta ma bata son yi, ita kuwa bata ma gabanta.
Sai da satin ya wuce gaba daya sannan Saudah ta koma makaranta, haka zata kwashi yaran ta kai
gidansu in ta dawo ta biya ta daukosu su dawo. Ta riga ta san yanzu duk wata dama da take da ita na a
taimaka mata da yaran nan a gidan ta tosheta don haka bata ma nema ba, za dai a kai mata su
makaranta.
……..
Ranar Talata ce, sha biyu suka fito daga jarrabawa don haka ta wuce gidansu don dauko yara. Da sallama
ta shiga gidan amma tun kafin ta karasa cikin gidan ta jiyo Kaka tana fadin
‘Yauwa! Ga Sauden nan ai. Ke Ummu fito ga Sauden itace kika ce ba a tambaya ba.’
Da hanzari ta karasa, kakace a zaune a tsakar gidan a kan tabarma ta mike kafafunta yayinda Yaya
Ummu ta fito daga daki ta zauna kusa da kaka. Ta karasa itama ta zauna ta ajiye jakarta ta dubi Yaya
Ummu tace
‘Menene ba’a tambayeni ba?’
Kaka tace
‘kudina, kudina Ummu ta kwashe amma tace wai bataga kudi ba.’
‘A’a Kaka wai sai ki dinga cewa na kwashe, na gaya miki ni ban ga komai a cikin kayan ba fa.’
Ta dubi Ummu tace
‘Wai tun ranar da aka kaita asibiti ta kafe kayan da na kai mata akwai kudi a ciki wai ni na kwashe, na
gaya mata babu kudi a kayan taki yarda.’
Ta tabe baki
‘To kuma ni me na sani a kai da za a tambayeni.’
Kaka tace
‘Don Allah ki fadi gaskiya baki ga kudin nan a hannunta ba, ko kadan baki ga wata alama ba.’
Ta daga hannuwa
‘Ni Kaka ban ga komai ba fa.’
Yaya Ummu tace
‘Babu fa wasu kudi, kinga Baba ma fa nan yazo ta gaya masa ya tambayeta nawane kudin ta ki fada,
kuma ya ce kudin wa ya bata nan ma taki fada. Saida fa ya bata dubu goma amma ko dubu daya bata
bani ba tana cewa na kwashe mata kudi.’
Ta daga sandarta zata bugawa Ummun wadda ta ja da baya tana fadin
‘Dama baki da wasu kudi Kaka.’
Saudah tace
‘To ai Kaka sai ki hakura tunda ma Baba ya biya.’
‘Ni ai kudina sun fi dubu goma.’
Ummu tace
‘To nawa ne?’
Ta sake kai mata duka tana fadin
‘Ke kika kwashe kudin nan algunguma.’
Ta shige daki da gudu, Saudah ma ta mike ta shiga tana fadin
‘Ki rabu da ita Kaka Allah zai kama miki ita.’
Tana shiga dakin suka gintse dariya ita da Ummun, tace
‘Ina Umma?’
‘Ta fita.’
Suka kyalkyale da dariya harda tafawa. Tunda Sauda taga kudin bayan Ummu ta dawo daga asibitin ta
bata dubu goma sha uku a ciki ta zuba hamsin a jakarta tace idan ta tambaya kawai suce basu ga wani
kudi ba, don in dai Umma taji cewa zatayi su bawa Kaka kudinta. Haka kuwa aka yi, tunda Kaka ta dawo
daga asibitin take cigiyar kudin nan amma kiri-kiri sai Ummu tace babu wasu kudi, rigimar tsufa ne Kaka
takeyi. Kuma da yake Kakan taki ta fadin yawan kudin da kuma yanda akayi ta samesu sai Umman da dan
uwanta suka fi yarda da cewa tsufan ne. Don hakama ya bata dubu goma yace tayi hakuri.
………………..
A cikin ‘yan kwanakin suka gama jarrabawar su ta karshe, Zulaiha da Salim duk sun gama ba tare da
wata matsala ba Amma ita Saudah sai tayi spill over da courses uku.
Kwarai Zulaiha ta so ta koma gidan domin har Ummanta ta sa ta kirawo Abban ko zata dawo yace mata
a’a. Tunda dai Baba Yalwa taki tashi daga Kano to tayi zamanta a can kawai, ita kuma Zulaiha daga ita
har Sa’an basa son zamanta a can. Fadan da sukayi da Saudah ya sa ba zai iya cewa ta koma wajenta ba
duk da yanzu tana bukatar taimako musamman da yake bata da mai aiki amma ya san kowaccensu da
son zuciyarta ba zasu zauna lafiya ba. Ita kuwa Mommy a yanzu ba zai iya ce mata wata Zulaiha zata
dawo ba musamman ma da yake yara sun riga sun koma dakin don haka dai gidansa babu dakin Zulaiha.
A hankali aka gaji aka daina wannan zantukan da ake yadawa a kan Mommy, don yawancin ma wadanda
suka daina harka da ita duk sun dawo sai dai itace ta ki sakewa da su ta kan cewa Maman Farida
kawance in babu amana bata sonshi.
A cikin gidan ma kuma babu wata fitna, abu daya ne da yake damun Abban ya rasa yanda zai yi da shi.
Gaba daya sun daina kula Sauda da yaranta, da suna shiga wajen Mommy amma yanzu kiri-kiri sun
daina; Auta ya hansu da yake daman wajensa suke zuwa. Kuma da tana aiken Auta da Khalifa ko kuma
idan bata fita ba suje su dauko mata yara daga makaranta idan suna nan, wani lokacin ma ko wani abu
zata yi da kanta za tace su je wajen Auta; har bayan Abban ya kori Mommy an yi haka amma yanzu
kwata-kwata sun fita harkarta ita da yaran. Abun yana yiwa Abba ciwo a zuciya don yana so ‘yayansa su
shaku amma yanda yake ganin alakarsu yanzu yana ganin Saudah ta barar masa da wannan damar. Haka
ya hakura duk da yana ganin idan yayiwa Mommy magana zata tsawatarwa yaran amma yanzu baya son
ya tada wannan zancen, don haka yana nan yana fakon lokaci.
Daf da bikin su Baba sakamakonsu ya fito kuma gaba daya sun haye. Yana zaune a falon Saudah ya
kirawo abokinsa wanda yake so yayi musu hanya a barsu suyi bautar kasa a Kano, bayan ya gama wayar
ya dubeta yace
‘Kina nan zaune ga ‘yayanki za su tattara su tafi bautar kasa ke kina kokawa da courses.’
Tana zaune a kan kujera yayinda shi yake zaune a kan kafet don haka ba fuskarta yake kallo ba, Ta
murgude baki tabi bayanshi da harara a ranta tace ‘in da lissafi za ayi ai harda kai a cikin wadanda suka
haifarmin da tangarda’ ta bude baki da kyar ta bashi amsa
‘Uhm, in sha Allahu nima semester daya ne kamar yau ne.’
Ya jijjiga kai yana ‘yar dariya
‘Haka ne.’
…………….
Sai da Saudah tayi da gaske sannan tayi kokawa da zuciyarta ta iya kawar da kai lokacin da taji Abba ya
bawa Ahmad gida a unguwar court road. Gidane aai daki uku da falo, dan matsaikaici mai kyau. Bata
gama jinyar wannan ba kuma taji ana zancen mota.
Da yake Ahmad din ya tanadi ‘yan kudadensa da zai kama gida don haka da Abban ya bashi gidan sai
yace zai sayi mota da nashi kudin. Bayan ya sanar da Mommy tace masa ya gayawa Abba don yace Baba
bai yi shawara da shi ba lokacin da ya fara sayen mota. Don haka da Abban ya shigo yi musu sai da safe
sai Ahmad din ya sanar dashi, yana dariya ya dube shi yace
‘Ai motar ma sai na dan kawo wani abu in ya so sai ka sayi ta zamani ka ga ko nima ka dinga kai matata
unguwa.’
Yana kallon Mommy. Suka yi dariya gaba daya Abban yace
‘Da safe kaje wajen Albarka (kamfanin da Abba yake sayen mota a wajensu) idan ka zaba sai muyi waya
ko 50-50 sai muyi ai.’
Ya yi murmushi yace
‘Abba nagode, Allah ya kara arziki.’
Mommy ma ta tayashi godiya. Sai da safe yana zaune a falon Saudah da yake Asabar ce yara basu je
makaranta ba sai ya tura Nawwara ta kirawo Madu, ba jimawa Madun ya shigo ya sami Abban a dining
table yana cin abinci yayinda sauda take zaune da yara suna kallon cartoon, don haka ya nuna masa
kujera yace ya zauna. Tunda ya shigo ya zauna ta mayar da kunnenta wajen, Abban yace
‘Ku tafi kasuwa kai da Salim za muje jana’iza ni da Baban Farida, idan muka dawo zai sauke ni a kasuwar.
Idan Ahmad ya zabi motar zai turo maka invoice din sai ka tura kudin daga account din zenith bank.’
‘To Abba.’
Ya sallameshi ya fice. Ta taso ta karaso inda yake ta zauna a kujerar da Madun ya tashi, ta dubi Abban
tace
‘Ahmad din ma mota za a saya masa bayan gidan?’
Ya kalleta tsaf yace
‘Eh, akwai matsala ne.’
Ta sunkuyar da kai tace
‘Allah ya sanya albarka wace irin matsala ana abun arziki.’
Jimawa kadan ta tashi ta barshi a waje.
Tana so ta ce wani abu amma haka ta hadiye a ranta, musamman da yake Yaya Maryama tana gaya
mata idan dai za ki nunawa miji kina son abun hannunsa to ba zai baki ba kuma ba zai yarda da son da
kike masa ba. Haka ta danne zuciyarta ta hakura
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good