Showing 144001 words to 147000 words out of 196754 words

Chapter 49 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15388

kalau Rabi.”

“Ya yara? Ya karin hakuri kuma.”

“Alhamdulillah.”

Yayi gyaran murya don yanda yaga yanayinta yanzu yana sa ran abun zai zo da sauki don ya fara ma
tunanin yanzu za su tafi.

“Yanzu Rabi daga magana sai ki ‘bace ‘bat, mu nemeki mu rasa?”

“Hmn, toh ai gani ko.”

“Hakane kam, toh Alhamdulillah.”

Suka yi shiru na dan lokaci. Binta kawai yake yi da kallo saboda yanda kwarjininta ya karu, jimawa kadan
yace

“Rabi.”

Ta kalleshi ta amsa

“Uhm.”

“Na san fushi kika yi da ni kuma na san ni na janyo, toh don Allah kiyi hakuri komai ya wuce. Ki koma
gidanki ni da yaranki duk ke muke jira.”

Murmushi tayi irin murmushin da idan tayi yake haifar masa da faduwar gaba saboda ya san zancen da
zata fada ba zai yi masa dadi ba. Tace

“Gidan ne ai na gaya maka ban siya ba, zai dan dauki lokaci amma in aha Allahu da na samu na siya zan
koma.”

Cikin yanayi na damuwa ya bata amsa

“Rabi, Rabi yanzu don Allah me za kiyi da gida ina nan da raina da lafiyata. Ga gidanki can don Allah ki zo
mu tafi.”

“A iya sanina bani da wani gida yanzu sai dai niyya, kuma na gaya maka da na samu zan koma.”

“Gidanki da kika baro yaranki kuma kiyi yaya da shi Rabi?”

“Wannan kam su ai gidan ubansu ne dama nice bare a gidan shi yasa yanzu nake kokarin na mallaki
nawa ko don gaba.”

Ya dafe kai, wadannan kalamai na Rabi kara saka shi a damuwa sukeyi domin gaba daya ta goge masa
haddar kalaman da ya zo dasu don tsarata.

“Na san kin ji haushin kalamai na amma na gaya miki kuskure ne nayi kuma in sha Allahu hakan ba za ta
sake faruwa ba. Ki yi hakuri ki zo mu tafi.”
Dauke kai tayi tana kallon wani gefen, yanda tayi haka ya san ba za ta sake cewa komai ba don haka
shima yayi shiru. Jimawa kadan yace

“Rabi.”

Ta juyo ta dubeshi tace

“Na’am.”

“Na yi miki alkawarin babu wani ‘da da zan kuma cewa ki rike min, ki zo mu tafi in sha Allahu yanda kike
so haka za kiyi a cikin gidan nan. Ke idan ma wani gidan kike so ni sai na saya miki in ya so ki koma ciki.”

Tayi murmushi tace

“Kada ma ka bata kudi ka ni din ma zan saya in sha Allahu.”

Suka sake yin shiru na dan lokaci, ya gyara zame yace

“Rabi.”

“Uhm.”

“Kin san ban sake ki ba ko?”

“Eh.”

“Kuma ba zan taba sakinki ba don wannan auren da kike gani daga nan har aljannah.”

Har cikin ranta wannan kalaman nashi sun mata dadi, amma sai ta kauda kai ba tare da tace komai ba.
Sai da ya gaji da shirun yace

“Toh yanzu idan kika sayi gidan can za ki zauna kenan baza ki dawo gidanki ba sai dai ni da yaran mu
dinga zuwa ko ya kike son yi?”

Ta dubeshi tace

“Idan na sayi gidan na koma sai kuma ayi wannan maganar.”

Mamakinshi ya karu kuma ranshi ya fara baci saboda yanda maganganunta suke kara masa damuwa
gashi ita din sai murmushi kawai takeyi kamar bata san zafin kalamanta ba.

“Yanzu Rabi auren nawa za a jingine kenan har sai kin sayi gida.”

Cikin halin ko in kula tace

“Toh ai kai ka jingine kayanka ko.”

Bai san me zai ce mata ba don haka ya koma ya zauna sosai ya jingina da bayan kujerar, ya cire hular da
take kansa ya ajiye. Dama shiyasa yake cikin fargaba da ya ganta tana walwala, in dai aka yi mata abun
fushi ya fi so ta bata rai tayi fada son ranta amma in dai ta fara wannan murmushin tana cewa ba’a yi
mata komai ba to haka take ba za ta bari a yi wata tattaunawa mai ma’ana ba. Yanzu gashi nan tunda
yazo yake surutu amma ta kasa fahimtarsa sai abu daya suke faman maimaitawa. Yanayin shirun ya
isheshi kuma ya san ita ba zata yi magana ba don haka yace
“Idan ma so kike na raba muku gida sai na raba in sha Allahu zuwa gobe ma sai a gyara miki wani gidan ki
koma.”

Da murmushi ta amsa shi

“A’a, idan har komawar ta kama nan din ma ya isa tunda matarka ai ba ita ta koreni ba mai gidan ne.
Nan din ma ya isheni.”

“Toh na janye korar don Allah kiyi hakuri ki zo mu koma.”

“Hmm, ai na gaya maka zan koma idan na sayi nawa gidan.”

“Toh kizo muje ni zan siya miki gidan kiyi duk yanda kike so dashi.”

Ta dube shi tana murmushin tace

“Ka barshi ma in sha Allahu nan da wasu kwanaki zan sayi nawan.”

Ya koma ya kwantar da kansa a jikin kujerar. Ya rasa yanda zai yi da Rabi, yana jin ko kwana zai yi a nan
zancen da za ta dinga maimaita masa kenan, gara ya tafi yaje ya samu Munzali yaji maganar gidan nan.
Ya nisa yace

“Toh ni zan koma Kanon.”

Ya zata za ta ce wani abu sai kawai tace

“Toh Allah ya kiyaye hanya.”

Ta fara kokarin mikewa, cikin hanzari yace

“Rabi.”

Ta dan koma ta zauna tace

“Na’am.”

“Don Allah ki daina yawan fita, ko ta kama za ki fita ki dinga sanar dani tunda dai kin san har yanzu a
matata kike ko? Kin ga kenan kina bukatar izini na kafin ku fita ko?”

Ta dube shi da fara’arta tace

“Wane izini kuma bayan wanda ka bani, ai maganar da kayi kace na fice maka daga gida ta nuna duk
inda nake so naje in dai ba gidanka bane ko?”

Ya kalleta da tsananin mamaki ya ma rasa mai zai ce. Sai da ya jijjiga kai sannan ya daure yace

“Toh na janye maganar tawa kin ji, don Allah ki dinga sanar dani in za ki fita kuma don Allah ki duba
maganar komawa gidan kafin na dawo kin ji.”

“Toh.”

Da taji yayi shiru ta mike tana fadin

“Ka gaida mutanen gidan.”
“Ki turo min Barakan mu gaisa.”

Ta amsa ba tare da ta juyo ba ta shige ta rufe kofar.

Yana nan zaune ya rasa me yake masa dadi Baraka ta turo kofar ta shigo da sallama. Sai da ta zauna
sannan ta gaishe shi tare da sake yi masa gaisuwar Baffa. Bayan ya amsa yace

“Hajiya Baraka kenan, kawai sai kika boye min yayar taki.”

Tayi dariya tace

“Anya kuwa, dama ba buya tayi ba muna nana daga gafe.”

“Toh ai shikenan hakan ma yayi.”

Ya dan yi jim sannan yace

“Don Allah ki tayani bata hakuri ta yi fushi wallahi.”

“In sha Allahu za ta huce, ka dai cigaba da hakuri kana bata baki amma na san za ta huce. Abinda ya faru
ne dai ya bata mata rai sosai.”

“Na sani wallahi, na sani. Ni kaina sai daga baya na gane rashin kyautawa ta, amma don Allah ki kara
bata hakuri.”

“In sha Allahu.”

“Ni idan ma so take na raba musu gida na amince, kuma tana maganar sai ta sayi gida ni zan bata
kyautar gida ma tayi hakuri ta dawo don Allah.”

“In sha Allahu zan mata magana, ai kai da ita kun wuce ace kuna wannan sa in sar.”

“Toh ai shine.”

Sukayi sallama ya fito yana fatan Allah dai ya sa kada Baraka taje tayi sabanin aikin da ya sakata, domin
duk wannan rikicin da Rabin take yi masa gani yake duk aikinta ne. Shi a yanda ya san Rabi tunani yake
bata da wayo, ya dai san idan ta dade tana hakuri da abu toh tana da fushi amma bai taba zaton tana da
wayon da zata dinga gara shi haka ba.

Tun daga Dutse har suka shigo garin Kano bai cewa Lalo komai ba, tunanin ma ya kasa don haka ya tura
kujera baya ya dan kwanta. Sai da suka shigo garin Kano sannan ya lalubi wayarsa ya kirawo Munzali don
yaji inda zai same shi, nan ya sanar dashi yana gidan gonarsa don haka ya yiwa Lalo kwatancen wajen
suka dauki hanya. A cikin falonsa dake gidan gonar ya sameshi, bayan sun gaisa ya mayar masa da yanda
sukayi da Rabin sannan yace

“Toh nace mata zan mallaka mata gida tayi yanda take so tace bata so zata sayi nata, ni na rasa wanne
gida ne wanna.”

Munzali ya gyara zama yace

“Eh to gaskiya nima bamuyi maganar wani gida da ita ba amma bari na tambayi Mubarak ka san shine
abokin shawararta.”
Ya kirawo Mubarak din a waya inda yake sanar da shi in sun raba gadon gidansu shi ya bawa Rabi nashi
za a hada da nata ya saya mata gida. Yace

“Toh amma ka san da aurenta ko, don haka babu yanda za ayi ta sayi gida ta koma ga gidan mijinta kuma
yana so ta koma.”

“Eh, na san da haka kuma ni din ma na fi so ta koma gidan mijinta. Idan an sayi gidan ‘yan haya za a saka
saboda ta dinga samun dan kudin kashewa, haka mukayi da ita. Ai ko mutuwa mijinta yayi ba za tayi
wannan zaman ba da ranmu da lafiyarmu balle mijinta yana nan.”

“Toh ko da na ji.”

Sukayi sallama ya ajiye waya sannan ya dubi Abban yace

“Kana ji gidanmu ne dama mukayi magana za mu sayar mu raba, toh ashe shine Mubarak ya bata
kasonshi yace a hada da nata kason sai ya saya mata gida ya saka mata ‘yan haya. Ai babu inda za ta
zauna sai gidanka in sha Allahu in dai ba wata matsalar ce kuma ta taso ba.”

“Toh da kyau, Allah ya sa albarka. Nawa aka yiwa gidan kudi ai ko ni sai na siya don ayi a gama kawai.”

Duk da ya san basu kai ga sakawa gidan kudi ba amma ya san idan har ya bari Abban ya shigo maganar
gidan toh zai iya janyowa Rabi da Mubarak su zargi wani abun don haka yace

“Ai an samu mai saya ma sai dai idan cinikin bai fada ba zan yi maka magana in sha Allah.”

Haka sukayi sallama Yaya Munzali yana kara bashi tabbacin babu inda Rabi zata zauna sai gidansa.

Sai da ya zauna a mota ya fara jiyo kiran sallah, yana duba waya yaga karfe daya da rabi. Nan ya bawa
Lalo umarni su tsaya a restaurant inda yake sayen abincin masu diabetes ya siyo masa alala da miyar
hanta sannan suka wuce kasuwa. Ya so kwarai ya koma gida ya huta amma da ya tuna ya baro Saudah a
gidan ya san idan ta ga dama toh ba zata bari ya huta ba don haka ya gwammace ya je kasuwar.




Ranar Juma’ah ce wadda babu aiki da makaranta saboda kasancewarta ranar good Friday. Tun dare ta
sanar da Abba cewa ita da yara za su je gidan Ummanta su wuni in ya so ya dauko su da daddare. Bata
son zuwa gidan Umma saboda ta san in dai ta je sai an yi mata maganar kudin malamin da yayi mata aiki,
kuma gashi naira dubu goma kawai ta samu da kyar. Amma ya zata yi, ta gaji sosai komai ma ya isheta.
Tunda Zulaiha ta tafi hidimomin gidan suka sake yi mata yawa, za a zo ayi mata wanke wanke da shara
amma nai aikin nata tana gamawa zata tafi sai kuma gobe. Duk hidimar yara da sauran ayyuka suna
kanta, gashi idan dare yayi ma yanzu ba sosai take samun isasshen bacci ba. Da Nawwara da Ummi a
wajen Zulaiha suke kwana don haka babu ruwanta da saka su fitsari ko basu ruwa idan sun farka duk
Zulaiha ce take yi, yanzu kuwa duk sun dawo dakinta. Don haka sai ta farka ta saka su a fitsari duk randa
ta manta haka za suyi mata shi a kwance, gara ma Nawwara wani lokacin tana farkawa ta tashe ta.
Sannan ga Hanan da Baffa kuma ga zuwa makaranta, don haka duk ta gaji da ta zauna sai gyangyadi
kawai take yi. Gidan Umman ne kawai za ta je ta saki yaran ta samu tayi bacci kuma ta samu inda za ta
tattauna damuwarta. Da wuri ta gama hidimarta ta hada masa abincin safe yana gamawa ya fita da su
ita da yaran ya ajiye su a gidan Umman.
Su ma su Ahmad sun sanar dashi za su Jigawa wajen Mommy don haka kafin ya dawo daga kai su Saudah
gidan Umma sun gama shiryawa. Gaba dayansu suka tafi har Madun, shima Abban da can din yaso zuwa
tunda har sun yi waya ya sanar da ita. Da suka sanar dashi za su je sai shi ya canza gurin zuwa ya bari
ranar Asabar ya je. Suna fita ya koma falo ya kirawo Alhaji Kabiru Babangida a waya ya sanar da shi zai zo
yanzu ya sameshi a cikin gari.

Alhaji Kabiru Babangida abokin Abban ne na amana sai dai shi a Abuja yake zaune yake nashi
kasuwancin, da yake ranar hutuce toh ya zo Kanon tunda iyayensa suna nan sannan kuma matarsa guda
daya tana nan. Duk lokacin da Abba yake son mallakar wata kadara wadda baya so a san da ita Alhaji
Kabiru yake sawa ya siya shima kuma Abban yana yi masa hakan. Basu dade da fita ba shima ya fice.

Bayan sun gaisa da Alhaji Kabiru sun dan taba hirar kasuwa, cikin hirarrakin nasu kamar wanda ya tuno
wani baun yace

“Ya madam kuwa, tunda kace min an ganta da ana zaman makokin Baffa ban sake maganar ba. In ce ko
dai tana lafiya.”

Ya dan canza fuska kalar tausayi

“Toh, Alhamdulillah. Sai dai har yanzu bata dawo ba don yanzun ma shi yasa nake nemanka.”

“Ban gane bata dawo ba toh tana ina.”

“Tana gidan kanwarta suna min yawo da hankali tukuna.”

“Ikon Allah, ai ni na zata tuni ka sami bakin zare ta dawo dakinta.”

“Wallahi sam ta ki, yawo da hankali kawai take min tunda ka ga yanzu haka wai gida zata saya tunda na
koreta daga nawa sai ta saya sannan sai ayi maganar ko za ta koma nawa gidan.”

Ya jijjiga kai

“A’a! Mata masu gari.”

“Wallahi kuwa.”

Ya sake jijjiga kai ya dafa cinyar Abban yace

“Wato mutumina dole ta ja ka a kasa don kayi wasa da damarka. Allah ya danka maka ita a hannunka ka
kulleta a cikin gidanka sai yanda kayi da ita tunda a lokacin ko gate kace kar ta fita bazata fitan ba. Kai
kuma sai ka zo ka koreta, ka ga wannan fitar da tayi zai buda mata ido ya nuna mata wasu damammamki
da da bata dasu saboda aurenka. Duk wasu abubuwa da take ganin wasu matan suna yi yanzu ka bata
dama ta fahimci yanda itama za ta canza rayuwarta. A da ta zata baza ta iya rayuwa ba in ba a gidanka
ba, ka ga yanzu ka bata dama ta gane za ta iya rayuwa cikin walwala ba tare da kai ba. Ka san fa yanzu ko
ta dawo toh ba fa za ka sake samunta yanda da ka sameta da ba.”

Ya jijjiga kai yayi tsaki mai cike da nadama

“Wallahi duk sai yanzu nake fahimtar hakan.”

“Ai sai hakuri kawai, haka za kayi ta binta a hankali har ka samu ta dawo don gaskiya zan gaya maka ta
kai a lallabata, ba za ka sake samun mace irinta ba a wannan zamanin.”
“Hmn, ba gashi nan ina gani ba.”

“Toh yanzu ya za ayi biko za muje ko siyan baki, ko kuma zance zan raka ka na shiga na canza kaya.”

Abban ya harareshi yayinda shi kuma ya kyalkyale da dariya

“ Ba fa na son wulakanci.”

“Allah ya huci zuciyarka, toh yanzu ya za ayi na canzo kaya mu tafi?”

Ya sake harararsa yace

“Ka ka fiye wargi wallahi. Gidan nasu da suke son siyarwa nake so na turo maka kudin ka siya min.”

Ya kalleshi da alamar tambaya a fuskarshi don haka ya cigaba

“Yayanta yace min wai an sami mai saye amma na bincika na ji ba haka bane nine kawai ba sa so su
sayarwa. Ko ma an samu mai saye ka je ka nuna za ka saya ka yi musu kari in ta kama. Ka ga da an gama
ciniki aka basu kudin sai su saya mata gidan da tace ba za ta koma ba sai ta mallaki nata. In ba haka ba
haka za suyi ta jan kafa ita kuma tana kara jabmin rai, gashi duk inda taso haka take tafiyarta bata Abuja
bata Kaduna.”

“Na fahimceka, wannan ai ba zai zama matsala. Ka bani adress kawai sai na tura yara don in ni naje ma ai
Rabi ta san ni.”

“Hakane.”

Nan suka gama kulla yanda za ayi Alhaji Kabiru ya saye gidansu Rabi ya basu kudin don suyi sauri su saya
mata nata gidan ko ta koma gidanshi ya huta. Ya zauna a nan har sukayi azahar sannan ya wuce kasuwa.




Ban karamin dadi Mommy ta ji ba da su Ahmad suka zo musu Dutse, kuma da yake ranar babu aiki nan
suka same su gaba daya har Barakan. Sun gama hada itacen turare kenan Mommy ta jika Zahra ta dauke
ta hau sama da shi su kuma suka shigo. Nan aka zauna a falon kasan ana ta hira bayan an kawo musu
ruwa da lemo. Basu dade da zuwa ba aka kirawo Baraka a waya daga makaranta akwai takardun da ake
so ta bayar; da yake yanzu itace HOD a department dinsu. Ta shirya ta dau mukullanta za ta fice tacewa
Mommy

“Yanzu zan dawo, kar ki barsu su tafi sai na dawo.”

Kafin Mommyn ta amsa Khalifa yace

“In zo muje Anti? Ban taba shiga FUD ba.”

“Yauwa dan albarka taso muje.”

Auta ma ya mike suka bita suka fice. Akwai game din chess a kan durowar da take kusa da dining table
wanda sun saba yi da Anti Baraka duk lokacin da suka zo tun kafin ma ayiwa su Ummi aure, Madu ya
mike ya dauko game din suka zauna suna yi a dining table shi da Salim. Mommy ta dubi Ahmad wanda
yake zaune a kusa da ita yana game a wayarsa tace
“Ahmadu.”

Ya bar game din ya dago ya dubeta yace

“Na’am Mommy.”

“Ya aiki?”

“Alhamdulillah Mommy, ana nan ana ta fafatawa.”

“Toh Allah ya bada sa’a. Ashe haka Khairiyya tayiwa Baba?”

“Wallahi Mommy, saboda tsabar yaudara ba.”

“Ai shike nan yanzu ka ga yace Fathiyya yake so sai mu yi abun mu a cikin gida.”

“Haka ya gaya min, dama ai tuntuni yake sonta kune baku sani ba yana ta wasu boye boye wai shi ta yi
yarinta da yawa. Ai yanzu da aka kwada shi da kasa idonsa ya bude ya ga gaskia.”

“Hmn, Allah dai ya bashi ikon rike min ita amana.”

“Amin.”

Suka yi shiru ya dau wayarsa ya ci gaba da game. Yana cikin game din ba tare da ya dago ya kalleta ba.

“Ni ma da Anti Baraka za ta bani auren bafulatanar yarinyar nan ai da nima auren zanyi.”

Ya fada kamar wanda baya so a ji.

Ta dubeshi kamar ba daga bakinshi maganar ta fito ba, tace

“Me kace Ahmadu.”

Ya dago ya dubeta, sai kuma yayi murmushi ya koma kallon wayar yana fadin

“Cewa nayi da Anti Baraka za ta bani Zahra da nima nayi auren.”

Cikin fara a da murmushi tace

“Ai kuwa da kun saka ni farin ciki kai da Baban. Ammafa ka tabbatar kana

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login