Showing 39001 words to 42000 words out of 196754 words

Chapter 14 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15364

a Kanon. Gashi tunda aka fara bikin ‘yanuwan babansu suke
mata habaici ance za ta sami miji a makaranta har yanzu sun ji shiru, bata iya basu amsa sai dai wanda aka
yi a ganan Sa’a tace

“Garajen me kuke yi, yana tafe in Sha Allah kafin a gama karatun.”

Lafiya kalau aka gama biki, mahaifinsu da kanshi ya zabi masu kai amarya mutum shida harda Sa’a kuma
da kawar amarya daya, ango ya kawo mota sienna aka kwashe su sai Sokoto. Sa’a kam ta yi mamakin ganin
yanda gida ya cika tunda ta san mahaifinsu gado da kujeru kawai yayi set daya, dangin uwarta kuma cewa
sukayi su da kansu za su kai nasu kayan a gani a dakin amarya, shima angon yayi daidai gwargwado don
shi yasa labule a duka gidan; daki uku da falo da kicin, kuma ya sa gado a master bedroom. Yan uwan
uwarta kuwa sun shake kichin da kaya ga TV da fridge harda carpets masu kyau, dangin uban ma kuma
sun nuna mata gata don suma da nasu kayan don haka gida ya fito fes. Kallo kawai take yi tana girgiza kai,
zargin ma da take yi shine ko lokacin bikin Ummi dangin ubansu basu yi hidima kamar wannan ba amma
yanzu saboda sun fi son Maryama da uwarat gashi nan sun fito da kudi sun kashe. Kwana daya suka yi
suka baro amarya suka dawo, har kuwa suka zo gida Sa’a tana ta wassafa irin wulakancin da zata yi wa
dangin ubansu in aka tashi bikin Zulaiha da Baba.

Ranar Lahadi suka dawo, Umma tace wa Zulaiha komawarta ba zai yiwu ranar litinin ba ta bari sai ranar
Talata don akwai shirye shiryen da take yi mata. Ranar Talata kuwa da safe bayan yaran gidan sun tafi
makaranta sai Mahmud kawai da yake wasanshi a tsakar gida ta kirawo Zulaiha suka shige kuryar daki. Sai
da ta bankada adaka ta dauko wata bakar leda sannan ta kama hannun Zulaiha suka zauna a kan carpet
din da yake tsakar dakin, sai da ta dora hannunta daya a kan gwiwar Zulaihan sannan tace

“Kina ji ko? Ga taimako na karbo kuma wannan malamin aikinsa kamar yankan wuka ne.”

Ta ajiye bakar ledar a tsakiyarsu ta kwance ta zaro wani Kwalli ta mika mata tace

“Kinga wannan kwallin ki kula dashi, sai kin tabbatar ya zo sannan za ki saka ki fito kiyi kokari ki kalli kwayar
idonsa ko na sakan ‘daya ne an gama domin da sunan shi aka hada kwallin nan.”

Ta kuma sa hannu ta zaro wata yar’ kwalba irin ta fiya fiya tace

“Wannan kuma turare ne, Shima da sunan Baban aka hada shi. Rana daya za kiyi amfani da su ki fito masa
gaba daya, ki saka kwallin ki shafa turaren ki fito masa. Turaren kadan za ki shafa don yace yana da karfi.
In dai kika yi haka ya bani tabbacin ko sati ba za a yi ba zai fara maganar aurenki don soyayyarki taso masa
za ta dinga yi kamar amai.”

Ta karba tana jujjuya su ba tare da tace komai ba. Sa’an ta nuna ta da yatsa tace

“Kin ji dai na gaya miki, don wannan auren idan bai tabbata ba garin nan sai ya gagare mu zama kina dai
jin tun ba a je ko ina ba dangin ubanku sun fara yar mana da magana.”

Tace

“In sha Allah zan yi Umma.”

Sai da aka yi azahar sannan Zulaiha ta shirya ta koma Kano.

------

Abincin da ya fi so shi ta dafa wato wainar shinkafa da miyar taushe ta sha tantakwashi, sanna ga zobo
wanda aka hada da lemon Zaki da kayamshi na musamman ta ajiye masa a tebur. Ta san duk ranar alhamis
rana ce da suke lissafi a kasuwa su lissafa cinikin da suka yi a satin da kuma kayan da yayi musu saura a
shagunan shi, don haka a gajiye yake dawowa da yunwa. Sai da ya yi wanka sannan ya fito falon, daga ita
sai auta suna hirarsu, bai sauraresu ba ya huce dining. Ta tashi ta zuba masa abincin, kafin ta gama zubawa
ya cika kofi da zobo ya shanye, ta tura masa kwanon wainar tace

“Toh ai ka koshi ma, ka cika cikinka da zobo.”

Ya ce

“Saboda kin shirya yi min rowa ba.”

Tayi dariya tace

“Ni na isa na yiwa maigida rowa.”
Saida yaci ya koshi sannan ya dawo wajen TV ya zauna ya dauki remote ya kai BBC, kafin wani lokaci kuwa
Auta ya tashi yayi musu sai da safe ya shige daki.

Hira sukeyi sosai yana bata labarai kala kala tana bashi amsoshi irin wadanda yake so. Kawo yanzu ta riga
ta saba in dai ba fada take so suyi ba to hirarshi kawai ake yi, ya bata labari duk irin wanda yake so ta
saurara, ta karanceshi sosai don haka ta san amsar da yake so ta san amsar kuma da idan ta bayar fada za
suyi. Dama ita tuni ta hakura da bayyana masa ra’ayoyinta in suna hira domin shi ra’ayi in dai ba nashi ba
toh ba me kyau bane. In wani abu aka yi a TV toh in ya fadi ra’ayinshi sai tace hakane don in dai ra’ayinta
ya banbanta da nashi ko sauraronta ma bazai yi ba balle ya fahimci inda ta sa gaba. Ya dan tsaya da bata
labari ya mayar da hankalinshi ga TV yana sauraro, sai da ta fahimci ya gama sauraron point din da yake
son ji tayi gyaran murya tace

“Abba.”

Sai da ya kalleta sannan ya amsa

“Na’am.”

Ta sunkuyar da idanuwanta tace

“Ina son komawa islamiyya.”

Ya tashi zaune daga kashingidar da yayi ya dubeta sannan yace

“Toh islamiyya kuma ai yanzu yan ajinku sun yi graduating sai dai idan ajin ‘yayanki za ki shiga.”

Ta yi dariya tace

“Basu gama ba tunda Maman Farida har yanzu tana zuwa, kawai dai na san dole na koma baya tunda an
huce ni sosai. Kuma tunda karatun addini ne ai ba gamashi ake yi ba, in Sha Allah duk ajin da aka sani ma
daidai ne.”

Yace

“Hakane, Allah ya bada sa’a.”

Tace

“Amin ya Allah. Toh za ka siyo min form din gobe?”

Yace

“Au ke da kike dalibarsu ma sai an sake siyo miki form?”

“Eh mana. Nafi shekara goma fa rabona da makarantar kuma sun san kai ne ka hana ni, ai gara ka siyo min
form din su san da izininka na dawo.”

Yace

“Haka ne.”

Washe gari kuwa yana tashi ya je islamiyyar da kanshi ya siyo mata form din ya biya kudin makaranta da
na litattafai sannan ya kawo mata form din don ta cike in za ta tafi ta tafi da shi. Daga wannan ranar ta
koma isalmiyya wadda suke zuwa ranakun alhamis da jumaah da yamma. Ajin baya aka saka ta amma bai
dameta ba saboda tana son karatun ba sauri take ta gama ba, fahimta take so. Ta ji dadin komawa
islamiyyar nan saboda ko babu komai ta samu ta dinga fita daga gidan tana shan iska kuma a tattauna da
yan uwa mata ayi raha a san me duniya take ciki.




Tunda ta dawo daga hutu take jira ta ji ranar da za ace Baba karami zai dawo bata ji ba har gashi an kai
sati biyar. Ahmad din dai da take so ta tursasawa zuciyarta barinsa shi take gani kullum, saboda duk da
yana bautar kasa yana yawan zuwa gidan domin inda aka kaishi babu aiki sosai kamar yanda yake fada;
kuma kullum ta ganshi kara son shi take yi. Tana da lambar wayar kowa na gidan har Ahmad din, tana son
ta yi masa magana ko hira ne su yi ta Whatsapp amma tun sau daya bata kara ba, shi ma da tayi sai da tayi
nadama. Ranar haka kawai zuciya ta rude ta da ta ganshi online ta tura masa sako

‘Salam.’

Tana kallo bai bude message din ba kawai sai ji tayi an kwala mata Kira daga falo

“Zulai”

Ta dauki muryarsa amma sai da wani malolo ya tsaye mata a makogoro saboda ta tsani a ce mata Zulai,
kuma yana ji tana fada da Auta a kan ya daina ce mata Zulai amma shine zai yi mata wanna kiran kamar
wata me aiki. Kafin ta fito ya sake kwala mata kira

“Zulai”

A tsaye ta same shi kusa da kofar dakinsu yana kallon waya, ba tare da ya kalleta ba yace

“Me ye kike min Salam ta Whatsapp?”

Karara mamaki ya bayyana a fuskarta, amma da yake ba kallonta yake yi ba bai ma sani ba, sai da ta galla
masa harara ta hadiye malolon da yake makogoronta sanna tace

“Ba komai.”

Ba tare da ya ce mata komai ba ya ja tsaki ya koma dakin ya rufe kofa. Ta dauki yan mintoci tana tsaye a
nan tana takaici kafin ta juya ta koma dakin tana mamakin shi din wane irin bakauye ne da ba zai amsa
mata ta Whatsapp din ba sai ya taso ta yana wani kiranta Zulai. Daga ranar bata sake yi masa message ba,
sai dai kawai ta budo profile picture dinshi wanda ta riga ta yi saving a wayarta tayi ta kallo.

….

Ranar Juma’ah tun da azahar aka kirawo Abba a kan Baffa Hassan ba lafiya, nan da nan kuwa Abban ya je
aka kaishi asibiti. Likita ya duba shi tsaf ya sallamesu da magunguna suka koma gida. Suna da mai aiki guda
daya itama dattijuwa ce amma bata kwana, da yake a unguwar take idan aka yi sallar isha’I sai ta tafi nata
gidan ta kwana. Ga shi Baba Yalwa yanzu bata gani sosai, an yi mata glass amma bata son sakawa, yaransu
kuma su Baba Aliko da kannenshi ba Kano suke zama ba, Amina ce kawai a Kanon ita kuma yaranta kanana
ne sai Aisha wadda ita dan uwa ta aura suna Bichi, yaransu duk maza ne kamar na Abban; don haka sai
dai Amina ta zo kullum ta koma ga nisa Abban da kanshi yace kada ta kuskura ya ji an ce kullum sai ta zo.
Sai bayan la’asar ya gama da Baffa ya koma kasuwar amma ya kasa nutsuwa, ya kamata a ce akwai wani
a wajen su Baffa, musamman ‘dan uwa ba mai aiki ba ko babu komai sa sami nasu a kusa wanda zai debe
musu kewa. Yaranshi duk maza ne kuma mace ya dace ta je musu ko na sati ne ko kuma duk karshen
mako. Yana ta tunani amma ya rasa wanda zai ce ya je, don ko a Bichin ma duk yaran sun bace masa. Yana
zaune sai Rabi ta kirashi don Madu ya gaya mata Baffa ba lafiya. Bayan ta yi masa ya kasuwa tace

“Ya jikin Baffa? Madu yace min kun tafi asibiti.”

Yace

“Eh, mun ma dawo magunguna aka bashi na kai shi gida.”

“Ya Baba Yalwa da ido?”

Yace

“Hmm! Suna nan, tunani ma nake ya kamata ace ko a yaranmu a tura musu wata su debe musu kewa ko
na kwana biyu ne amma duk ‘yan matan namu sun bace min a ka duk wadda na tuna na san tana
makaranta.”

Ta dan yi gyaran murya tace

“Hakane. Baba Yalwa ma ba lafiya ne?”

“A’ah ita Alhamdulillah. Kin san dai tsufa, daga su har mai aikin tasu duk gayyar tsoffi, musamman yanzu
da Baba Yalwa take jinyar Baffa kinga idan da mai jini a jika ko hira a yi a yi dariya kuma a dan taya su wasu
hidimomin.”

Tace

“Umm hakane. Toh ai ko Zulaiha sai ta je tunda gidan Baffan kaga a kofar fanfo ne ko a ‘kas sai ta karasa
makaranta, in ya so in ta kwana biyu a can sai ta dawo kafin nan sun ‘dan huta.”

Da zumudin shi yace

“Ai kuwa haka ne, ki bata kudin mota kawai ta tafi. Zan ma yi mata waya ta hada kayanta in tayi musu sati
sai ta dawo.”

Tace

“Nima ina son zuwa in dubo su, sai mu tafi tare in ya so sai na dawo na barta.”

Yace

“Toh.”

Suka yi sallama.

Ji tayi kamar zata yi bindiga da aka ce za ta gidan Baffa ta kwana, da ba don Abba ne ya gaya mata ba
gaskiya da baza ta ba. Tunda ta zo garin nan ko Abban ya ce ta je ta gaishe su daga makaranta ma ba zuwa
take yi ba sai dai idan daga gidan ne yace su je da su Madu su gaishe su. Haka ta hada kayanta tana yi tana
zumbura baki suka kama hanya ita da Mommy. Nan da nan kuwa suka isa gidan.
Mai aikinsu tana nan ita tayi musu maraba ta kawo musu ruwa, Baba Yalwa na ta murna Zulaiha za ta
kwana biyu. Nan da nan aka nuna mata daki ta kai kayanta, ta dawo falon gidan ta zauna ta ‘dau remote
domin TV a kunne take. Mommy tana zaune suna ‘yan hirarraki da Baba Yalwa wayarta tayi kara ta dauka,
Auta ne yake magana bayan ya gama gaya mata abinda zai fada mata tace

“Toh sannunshi da zuwa, nima yanzu zan dawo.”

Suka yi sallama ta ajiye wayar. Ta dubi Baba Yalwa tace

“Baba ne ya zo shine Auta yake gaya min.”

Tace

“Ayiriri mai gida na ya zo maraba maraba, don Allah ki ce masa ina gaisuwa zan zo mu kwance jaka.”

Zulaiha dake cikin falo tana jiyo su ji tayi kamar tayi bindiga saboda takaici, sati shida tana jiran
dawowarashi amma bai tashi zuwa ba sai da aka kawo ta nan. Tana nan tana tunanin dabara taji Mommy
na sallama za ta tafi, ai kuwa tayi wuf ta fito daga dakin tayi tsilli tsilli tace

“Mommy bari kawai na zo mu tafi in ya so gobe na dawo na yi mantuwa.”

Mommy ta kalleta tace

“Me kika manta Zulaiha?”

Ta sunkuyar da kai ta amsa da murya kasa-kasa

“Pad.”

“Au don wannan ba sai a siyo miki a nan ba “

Mai aikin Baba Yalwa tace

“Ai ko nima sai na siyo miki wanna.”

Mommy tace

“Shike nan ma kinga yanzu za a siyo miki ita.”

Ta zaro naira dari biyar ta bawa mai aikin tace

“In kin siyo kya sayi omo da chanjin.”

Ta yi musu sallama ta tafi ta bar Zulaiha tana ta faman cika tana batsewa ga shi Baba Yalwa ta isheta da
surutu. Haka ta kwana tana juyi tana zancen zuci, ta dai yiwa kanta alkawarin tabbas sai ta je gidan kafin
ya tafi tunda ta san in ya zo sai lahadi da rana yake tafiya.

Ranar Lahadi da safe dabara ta fado mata, kunu ta damawa su Baffa tayi dumamen tuwo don shi Baffa
kullum sai ya ci dumame. Nan da nan kuma ta gyara falon ta ajiye musu abincin tace wa Baba Yalwa tana
da test ranar litinin kuma ta manto littafinta a gidan Abba za ta je ta dauko don tayi karatu. Baffa yace

“In dai Abban naku ne zuwa jimawa kadan za ki ganshi ko kiga wani daga gidan, kiyi waya mana sai su taho
miki dashi.”
Tace

“Baffa ai baza su gane inda littafin yake ba don ko ni ma sai na duba na dade ban yi amfani dashi na gashi
dakin a birkice yake.”

Ya kawo kudin mota ya bata ta kama hanya tana ta sauri.

Tana shiga gate din gidan ta fara godewa Allah da taga babu motar Abban, ta san tabbas baya nan shi da
Madu don in dai Madu baya tare da shi toh yana makaranta. Don idan akwai wanda take jin zai iya bata
mata aiki toh Madu ne don haka ta shiga tana murna. Ta sami Auta da Khalifa a falo suna hirarsu, ta hucesu
zuwa kitchen ta gaida Mommy. Ita kanta Mommyn saida tace

“Toh ai da kin yi waya da kin hutar da kanki an kawo miki.”

“Ai da yake sai na nemo littafin Mommy shi yasa kada na sa mutumina aiki.”

Nan ta huce ta shiga dakin ta laluba inda ta ajiye kayan aikin nata, ta ji kwallin yana nan turaren ma haka.
Ta fito dasu ta kallesu ta jijjiga kai sannan ta ajiye su a gefen mudubu saboda sai ta ji motsinshi za ta shafa
ta fita, suna yin ido hudu itama ta yi mijin aure. Ta haura minti talatin a dakin bata ji wani motsi ba da yake
nuna mata Baba yana gidan don shi mutum ne da baya buya. Ta fito falon auta yana nan a kan dining table
yana game a wayar Mommy tace

“Autares Ya Baba ya fita ne, kasan bana nan ya dawo ban gaishe shi ba.”

Bai dago ya kalleta ba saboda baya son ya kifta ido daga game din da yake yi yace

“Kafin ki shigo suka tafi gidan Baffa shi da Ya Salim daga can zai kaishi airport ya huce.”

Mutuwar tsaye tayi a nan saboda tsabar takaici, da yake hankalinsa yana kan game din da yake yi bai ma
kula da halin da ta shiga ba. Da kyar ta ja kafarta ta koma dakin. Ta tsaya a gaban mudubu tana kallon
fuskarta tana tunani, ta rasa me yake faruwa gata daf da Baba karamin amma sai ya dinga yi mata nisa.
Wannan sabanin ya yi matukar bata mata rai. Tayi murmushi yayinda wata dabarar ta fado mata tunda
dai gidan Baffan suka tafi. Kwallin da turaren ta dauka ta jefa a jaka ta yiwa Mommy sallama tana fadin

“Mommy bari nayi sauri na koma don nayiwa Baffa abincin rana.”

Mommy tace

“Toh ki gaishe su. Akwai dai kudin mota a hannunki ko?”

Tace

“Eh.”

Sukayi sallama ta kama hanya tana ta sauri kamar zata tashi sama. Ji take yi kamar me taxi din da ta hau
baya sauri amma dai ta daure. Ta san in suka je wajen Baffa basa tafiya da wuri don haka ta na da tabbas
din za ta samesu a can idan tayi sauri. Tana sauka daga taxi din ta hau Babur don ya karasa da ita cikin
kofar fanfo zuwa gidan. Kafin Babur din ya gama tsayawa ta hango motar Daddy wadda a ita suka taho
don haka tayiwa kanta murmushin samun nasara. Nan da nan ta sauka ta sallami mai babur ta shiga gidan.
Kana shiga gate din gidan sai ka shiga ta irin siririn soron nan sannan za ka kai tsakar gida, a nan soron ta
tsaya ta zaro kwallin daga jaka ta sa a idonta sosai sai da ta tabbatar ya ji sosai. Ta dauko kwalabar turaren
wanda dama kamar turaren bai fi digo biyu aka zuba a ciki ba ta samu ta digo shi a hannunta ta shafa a
gaban hijabinta ta Dan gyara jikinta don ta san suna nan a tsakar gida da su Baffa. Da sallama tare da
murmushi ta shiga tsakar gidan ta tarar da me aikin Baba Yalwa tana wanke wanke Baba Yalwa kuma tana
kashingide a kan tabarma daga gefe. Bayan sun amsa sallamarta ta dubi Baba tace

“Baba na ga motar su Ya Baba a waje suna ciki ne?”

Tace

“Mun yi sallama da su ai, sun bi Baffa masallaci wajen liman daga can za su huce ashe a nan suka bar
motar.”

Nan da nan takaici ya lullubeta, wannan wane irin abune mutum ya ki tsayawa a ganshi sai faman sabani
suke yi. Ta huce daki tana ajiye jaka dabara ta fado mata, zuwa zata yi ta jirasu a bakin gate daga ciki

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login