Showing 150001 words to 153000 words out of 196754 words

Chapter 51 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15380

ba aka nemo masana suka yiwa gidan kudi hade da shagunan ana gaya masa kuwa yace ya siya ba
tare da wani neman ragi ba. A take aka sayar masa aka gama ciniki aka bashi account number, ranar
Laraba da safe ya turo musu kudin ya zo ya karbi takardun a wajen mai kula da gidan. Yana sanar da Yaya
Munzalin an gama ciniki ya sanar da Mubarak suka saka rana da za a raba musu kudin. Kafin a raba kuma
Mubarak ya sa a samowa Rabi gida a tsakanin sheka unguwar su Yaya Shafa zuwa zoo road. Ta saka shi
ya wakilceta idan an zo rabon sannan kuma idan an sami gidan kafin ta dawo Kanon toh ya nemi Ahmad
a yi duk abinda ya dace.




Turarukan da aka hada tun ana fito dasu suka cika gidan da kamshi, turaren wuta kala biyu a
matsakaitan bokitai halut da sandal sai kuma humra kala biyu fara da baka kowacce kusan lita hudu. Nan
da nan gidan ya cika da kanshi. Zahra ta tashi ta kunna gawayi ta dawo tace

“Inna bari in kona ma fi shaka da kyau.”

Nan da nan kuwa falon ya cika da kamshi, Rabi da Baraka murmushi kawai sukeyi saboda yadda kamshin
yayi musu dadi. Sunata zubawa a kwalaben, ita kuma Zahra bayan ta ajiye gawayin sai kuma ta dauko
robar humar ta dubi Baraka tace

“Inna bari na shafe jikina da wannan, don ni yau ji nake yi ma kamar da turare zan yi wanka don a san
diyar mai turare nake.”

Suka sa dariya, Baraka tace

“Ba kya jin kunyar surukarki.”

Ta rufe fuskarta da tafukan hannunta tana fadin

“Laa Inna wallahi mantawa nakeyi.”

Zata tashi Rabi ta rike ta tace

“Yi zamanki ai na gaya miki ni ba surukarki bace itace surukarki, ni Innarki ce ita kuma Innar Ahmadu
kuma bama jin kunyarsu.”

Mai aikin Baraka da take taya su aikin tace

“Ai kuwa ko ni na shaida.”

Suka kyalkyale da dariya, duk da haka tana sakinta ta ruga da gudu ta haye sama.

Kafin azahar sun gama, aka karbo zannuwan gado suma masu kyau sosai. Manya irin na amare masu
quilt guda shida sai kuma normal masu pillow case biyu suma dozen uku ga kuma burners masu kyau na
kunna turare da masu aiki da wutar NEPA da masu gawayi suma dozen biyu. Da aka baje kayan nan a
falo suna duddubawa Rabi ta kalli kayan ta dubi Baraka tace

“Baraka na gode miki sosai wallahi har ban san irin godiyar da zan miki ba, ba za ki gane yanda kika sani
jin dadi ba.”

Ta bata rai
“Godiyar dai ki barta kafin yanzu mu bata, dadi kam na fi ki jinshi wallahi. Tun farko da akayi bikinki nake
jiye miki takaicin rashin aikin yi da sana’a wallahi, saboda sune mutum. Idan da dan abun hannunki babu
wanda zai miki kallon raini, kiyi sadaka kiyi kyauta lokacin da kika ga dama.”

Nan da nan aka kirawo Zahra ta sa kayan a gaba tana ta daukar hotunansu. Abban Ummi yana shigowa
Baraka ta nuna masa kayan a falo tace

“Abba kayan mu fa sun iso, daga yau Bibi ta zama business woman.”

Yayi dariya

“Kai ma sha Allahu, Allah ya sa albarka.”

Ya sa hannu ya dan daga zannuwan gadon yana fadin

“Ai sai na fara sayawa matata ko? A bamu zanin gadon guda biyu.”

Nan da nan Baraka ta mike ta zabi guda biyu tana fadin

“Bari na turo maka account number Yallabai, godiya nake Allah ya barni da kai ni kadai.”

Yayi dariya ya kalli Rabi yace

“Kin ji addu’ar da take min ko, mata tsala tsala duk sun ki kulani saboda wannan addu’ar.”

Suka sa dariya ya wuce ya barsu a nan. Bayan ya fita Rabi ta dubi Baraka tace

“Ki barshi don Allah ba sai kin tura masa ba ki dauka kawai.”

Ta kalleta da mamaki tana zaro ido tace

“Ikon Allah, a haka za ki rabar mana da kayan. To wallahi kowa sai ya biya, kin san Allah Bibi in kina haka
toh za a karya ki kwanan nan. Don Allah kar kiyi mana wasa ki kyautar da kayan, duk wanda ya dauka ya
biya a tara kudi a juya.”

Ta kalleta taga yanda ta sha kunu tana bata fuska ta dafa cinyarta tace

“To shikenan in sha Allahu kowa biya zai yi.”

Kafin su tashi daga nan kudin da Abban Ummi ya turo sun shiga account din Rabi, naira dubu shida kudin
zanin gadon biyu. Ta daga wayar ta nunawa Baraka, ta karba tana murmushi tace

“Toh Alhamdulillah, haka ake so. Kin ga kafin su kare idan aka hada abinda ya samu sai a sake order.
Madu zan samu ma yayi nana hanya mu dinga shigo dasu daga China don yarona international business
man ne.”

“Kamar kuwa kin sani, china, India, Dubai duk ya san yanda ake order ba tare da ya je ba.”

Suka gama lissafi suka kwashe kayan. Duk yanda Baraka ta ke ki sai da Rabi ta zare mata ido ta ajiye
mata turaren wuta kala biyu da humra kuma tace ba za ta biya ba, ta kara da

“Sai ma na tafi inda ba kya nan zan yi miki na musamman ba don hancinki ba sai don Abban Ummi.”
Tun dare su Ummi yaran Baraka suka zabi bedsheet a status din Baraka da ta dora kowa da turare daya,
Rabi tana fadan bazasu biya Baraka tace

“Sai sun biya, kowacce da kudinta duk ma’aikata ne.”

Kafin gari ya waye suma sun turo kudin abinda suka dauka. Itama Yaya Shafa da ta gani a status din
Rabin ta zabi zannuwan gado guda biyu da turaren kowanne daya da burner guda biyu a kan idan sun zo
Kano sai ta tura kudin. Nan da nan Rabi ta ware mata nata guri guda, gari na wayewa kafin su fita sai ga
alert din Yaya Shafa. Da suka je makarantar su Baraka ma haka Baraka ta kunna turare a office dinta ta
bar kofa a bude, duk wanda suka zo wucewa sai sun tsaya sun gaisa da HOD. A haka aka sayarda kusan
Rabin turaren da zannuwan gado guda uku, wasu a take suka turo kudinsu wasu kuma sai daga baya za
su turo. Sai bayan azahar Baraka ta tashi daga aiki suka tattaro suka dawo gida. Bayan Magriba suna
zaune a dakin Baraka suna cin abinci message ya shigo wayar Rabi, ta duba ta cewa Baraka

“Abokiyar aikin ki ce gashi ta turo kudin turare.”

“Yauwa, ai gara haka.”

Sai da ta karanta sakon nan sau wajen uku tana sake duba total balance din da yake cikin account dinta,
da yake daman akwai dubu ashirin a ciki tunda Ahmad ya bude account din ya saka mata. Baraka da ke
kallonta tace

“Wai alert din kike karantawa kina ta murmushi haka.”

Ta dago kanta daga wayar tace

“Wallahi Baraka, haka kudi suke da dadi. Kinga fa daga jiya zuwa yau kusan dubu dari duk nawa.”

“Hmm, sai ma an kara kwana biyu hajiyata, ai wallahi kudi ko babu abinda za kayi dasu sanin kana da su
kawai ya isa ya saka ka farin ciki ba kadan ba. Kuma kunga munyi sa’a ko kwana uku ba ayi da yin albashi
ba shi yasa kika ga ana ta biya take. Haka kasuwa take wani lokacin da ka kasa ka siyar, wani lokacin
bashi wani lokacin ma kuma ki ga kamar an ki saye. Shi yasa naji dadi da kika hada ga turare ga zanin
gadon, idan ba a sayen wannan a sayi wannan.”

“Lallai kam, gaskiya na ji dadi.”

“Ki yi ta neman albarka wajen Allah a hankali za ki fara kirga miliyoyi.”

Suka yi dariya gaba daya tace

“Allah Amin.”

“Gobe kuma sai ki shirya da wuri mu fita na saukeki saloon, can ma ki tafi da kayan zan yiwa Ogan tasu
magana ko zata karbar mana turaren ta sa a shago.”




Sai bayan isha’I jirginsu ya sauka daga Lagos, nan da nan ya kirawo Madu ya daukosu sai gida. Kafin ya
dawo ta gama binci ta dafa masa dashishi da miyar hanta ga kunun aya duk ta jera a table. Lokacin da ya
shigo yara duk sun yi bacci don haka ita kadai ce a falon, ta mike tayi masa sannu da zuwa ta karbi jakar
hannunsa ta raka shi daki. Ya zauna a gefen gado ita kuma tana tsaye daga bayan kofa, ta dube shi tace

“Ga abinci a kan dining table fa, na san dai baka yi dinner ba.”

“Kema kin san tunda gida na nufo ba zan ci abinci a waje ba, amma sai na yi wanka tukun.”

Ta amsa da “toh.”

Ta juya ta fice, jimawa kadan ta dawo da kunun aya kofi daya da ruwan roba a tray, ta ajiye masa a kan
durowar gafen gadon tana fadin

“Ga ruwa ka sha kafin ka fito.”

Ya dauki kunun aya ya fara sha yayinda ta juya ta fice tana fadin

“Sai ka fito.”

Sai da ya share kusan awa daya sannan ya fito falon, tana gefensa tana yi masa hira yana cin abincin.
Bayan ya gama cin abincin ya taso ya dawo gaban TV ya kashingida a kan kafet ya kunna BBC. Ta zauna
daga gefensa yana tambayarta gida da yara, ya saba duk lokacin da tayi tafiya ko ta kwana daya ce sai ya
zo musu da tsaraba, ko da kuwa chocolate ce da wani biskit wanda ba a saba siyowa haka kawai ba
amma wannan tafiyar babu abinda ya siyo. Ya tashi daga kashingide da yayi ya dubeta yace

“Sai kun yi hakuri da ni wannan karon ban siyo muku komai ba daga ke har yara, tafiyar ce gaba daya
bamu zauna ba gashi kuma bana so mu sake kwana.”

“Ba komai wallahi, daga dan kwana dayan ma.”

“Eh mana, ai gobe kafin Ummina ta tashi dole na siyo mata alawa da biskit in ba haka ba a ci tara ta.”

Ta yi dariya tace

“Lallai kana neman albarka.”

Suka dan yi shiru. Ta san lokacin da yake yin order din kayan gadon don ta ganshi da catalog ta
tambayeshi ko ya koma sayar da kayan gado ya gaya mata ya dan sami wasu kudi ne zai gwada
karambani. Tun a lokacin ta zabi wasu kujeru a ranta ta ‘dana tarko, duk da shine yayi mata kayan daki
da ya aureta amma so take ya canza mata kujerun tunda ga wadanda suka fisu. Kuma ga shi kayan sun
zo a kan gaba ta tsara idan ya bata sababbi tsofaffin sai ta sayar ta biya dubu darin da kaka ta dameta da
su ta zuba canjin a jaka.

Tayi gyaran muryar da dawo da hankalinshi daga kan TV da yake kallo tace

“Kayan furniture din ne suka zo ta Lagos koh.”

Cikin murmushinsa yace

“Eh, sune. Kuma kin ga Alhamdulillah da yake ina wajen aka sauke na biya clearance da komai har an
dorasu a mota gobe da asuba za su taho.”

“Kai ma sha Allah, Allah ya kawo su lafiya.”
“Amin ya Allah, kuma kin ga tun kafin ma su zo Madu har ya sayar da wasu an biya kudinsu ana saukewa
za a kai musu.”

Sai da ta canza fuska saboda yanda ta tsani a ambaci sunan Madun nan, shi kuma in dai hirar
kasuwancinsa ake yi toh zance daya biyu sai ya ambaci Madu. Ta kawar da kai tayi shiru tana tunanin ta
inda za ta bullo masa

“Uhm, ni dai ina rikon kujeru don Allah a bani na canza na falon nan tunda ka ga sun kwana biymas

Ya tashi ya zauna sosai ya dubeta ya dubi kujerun yace

“Haba, wadannan kujerun me sukayi abinda ko shekara goma ba suyi ba.”

“Haba duk sun kukkuje fa.”

Yayi ‘yar dariya

“Ai haka za kiyi ta malejinsu su kara kwana biyu, babu ma wata kukkujewa.”

Zata yi magana ya katseta

“Kin san nifa banawa business haka, kin ga irin wannan son zuciyar da zan biye masa toh da yanzu ban
mai haka ba. Kayan wutar ma kullum na shigo da sababbi sai na ji kamar na canza AC, wani fridge ko
komfuta, haka dai hakurar da kaina nake. Saboda in ka biyewa wannan business din ba zai ci gaba ba,
duk na yi da, gani nayi babu riba na daina.”

“Yanzu don Allah don kujerun set daya ai wannan ba zai taba business ba.”

Ya tsahi ya koma kan kujera ya baza hunnuwanshi a saman kujerar yana fadin

“Haba wadannan lafiyayyun kujerun za a wani canza, ai babu abinda suka yi. Kayana na siyarwa ne kinga
da kina da kudi dai sai nayi miki ragi na siyar miki da set daya dubu dari biyu, don gaba dayansu ma babu
kujerun kasa da haka.”

Ta karkata kai kamar abin tausayi, yayi dariya yace

“Toh ki bari in da rai da lafiya wataran za a canza miki amma dai ba yanzu ba.”

“Uhm Allah ya nufa.”

Suka dan taba hira kadan ta tashi ta shige daki. Yanda ta ganshi cikin walwala bata zata zai hanata
kujerun ba, kuma garin bincikenta a takardun da yake shiga dakinta dasu ta gane kujeru set sha biyu
yayiwo order da gadaje set ashirin da hudu don haka ma tayi zaton a dozen ba zai ji komai ba don ya
bata daya. Ta daga wayarta ta dubi lokaci, lallai ta kusa rabuwa da wayar nan don in dai ba wata hanya
ce Allah ya buda mata ba bata san ya da za ayi ta sami wadannan kudi ba. Ta jujjuya wayar, babu abinda
tayi saboda yanda take tattalinta amma haka za ta hakura ta bayar a sayar in ya so tace masa sacewa aka
yi, tunda in dai ba kujerun nan ta samu ya bata ta sayar da tsofaffin ba bata da wani kayan kudi.

Sai da kayan suka kwana suka wuni a hanya sannan suka iso Kano, da yake da daddare kayan suka iso
yana dakinta aka yi masa waya aka gaya masa. Gari na wayewa suka fita shi da Madu da Salim, ana
sauke kayan Abban yana dubawa da na catalog din da yake hannunsa don ya tabbatar iri daya ne ana yi
ana fitar da wadanda Madu ya riga ya sayar; set din kujeru biyu da gado hudu. Aka fito da wasu kujeru
shudaye, har an shigo dasu store din Abba ya kirawo Madu yace a fito da su, yace

“Abba ba su aka sayar ba, bakaken sune ga su can a waje.”

“Eh a fitar da wadannan din ma zan fadi yanda za ayi da su.”

Nan da nan aka fito da su aka ware. Bayan an gama jerasu an rufe store aka kwashe wadanda Madu ya
sayar ya bada kwatancen inda za a kai, ya zama saura wadannan shudayen kujerun da yace a ware
kawai. Ya dubi Madu yace

“A kwashi wadannan ka kai gida ka canzawa Mommynka na falo.”

Da murmushinsa yace

“Toh Abba ya za ayi da tsofaffin?”

Ya dan yi jim yana tunani, yace

“In akwai wanda za ka bawa za ka iya bayarwa ko kuma ka saka su a kasuwa.”

“Toh Abba.”

Nan da nan aka loda kujeru a mota Madu ya ja motar Abba ya wuce gaba suka bishi a baya har gidan.

………….



Tana ta Shirin fita zuwa makaranta taji an bude gate sai ta dan tsaya a falon don ta ga waye zai shigo.
Motar kujerun ce ta fara shigowa shi Madu a waje ya ajiye motar. Babu kowa a gidan don haka ya kirawo
Malam Bala suka fara saukewa. Har murmushi takeyi daga inda take tsaye a bakin taga tana tunanin
kujerun da ta tambaya ne da ya gama ja mata rai ya bayar a kawo mata. Jira take a zo ace ta bude kofa
za a shigo da kaya har suka gama sauke kujerun, sai taga Madu ya bude kofa ya kirawo Malam Bala da
masu kawo kayan aka fara fito da kujerun falon, aka gama aka fara kwashe sababbin ana shigarwa
sannan ta gane abinda yake faruwa.

Wannan wane irin abun haushi ne, matar da bata nan ma ita ake canzawa kujeru? Yanda taji shiru
kwana biyu ma ta zata ta fasa dawowa, ta gama yi masa magiya a kan kujerun amma ya dauka ya bawa
matarsa. Lallai yau za ayi masifa. Ta kalli kujerar karshe da ake shiga da ita, kujerun ma irinsu ne
wadanda take so amman ita bakakensu take so shine ya bawa matarsa. Ta saki labulen a fusace ta koma
ta zauna a kan kujerar dining table ta kafa tagumi, wallahi zai zo ya sameta. Wannan ai wulakanci ne zai
yi mata, ta tambayi kujerun kuma ya sa a bawa gudajjiyar matarsa. Kukan Baffa ne ya katse mata
tunanin da takeyi, ta juyo ta dube su a kan kafet suna fada a kan ‘yar tsanar Hanan da ta fizge. Sai da ta
dubi jakarta a kan kujera sannan ta tuna makaranta za ta tafi. Ta ja tsaki ta mike tana duban agogon
bango taga har ta kusan makara. Kafin ta hado kan yaran ta fito an gama kwashe kujerun su Madu sun ja
motocin sun tafi.
EPISODE 33



Kafin ranar Juma’ah duk wani shirin da su Rabi za su yi sun gama, da yake ranar Baraka bazata aiki ba tun
shida na safe suka kamo hanya. Suka sami Yaya Shafa a gida tana shirin fita aiki don haka a tsaitsaye
suka gaisa suka sanar mata su ma za su kasuwar kurmi don haka jimawa kadan za su fita amma ita
Baraka da yamma za ta koma Dutse a nan zata bar Rabi. Sosai Yaya Shafa ta ji dadi domin ita din ma tana
so taga Rabin ta koma dakinta musamman da taga yanda Abban ya shiga damuwa yake ta faman bada
hakuri. Ko babu komai idan dai Allah ya bawa mace dama tayi auren toh zaman ya fi alkhairi idan dai ba
wata fitna ce aka zo da ita ba. Nan ta fice ta barsu da mai aikinta, zuwa jimawa suma suka fice sai
kasuwar kurmi. Dan cinikin da akayi ne na kayan bedsheet Baraka tace lallai sai suje su siyo kayan turare
don ta sake hadawa kafin ta koma tunda an samu ya fara karbuwa, sai bayan azahar suka fito daga
kasuwar suka tsaya a Sahad na cikin gari Rabi ta siyo man shafawarta da sabulai da turarenta. Tun kafin
ma su rabu ta fara kewar Baraka, haka dai bayan la’asar lokacin Yaya Shafa ta dawo sukayi sallama ta
kama hanya. Da kanta ta kirawo Yaya Munzali ta sanar da shi ta dawo gidan Yaya shafa, da zarar an
gama cinikin gidanta za ta koma gidan Usman din. Sosai shima ya ji dadi ya kara yi mata nasiha yana bata
hakuri. Itama Yaya Shafa a daren ta karbi hotunan kayan sayarwar ta saka a status kuma ta tabbatar
mata ranar litinin da su zata tafi asibiti ta sake tallatawa.




Ranar da aka kawo kujerun nan ranar Juma’ah ce tun da yamma Baba karami ya zo, da yake tunda aka
ga Mommy duk sati sai ya dawo yana sa rai ko zata dawo gida

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login