Showing 204001 words to 207000 words out of 265571 words

Chapter 69 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28886

da Dogon wando plazo Sai Dogom Hijabin Dake jikinta duk hannun Data sanya mbai iya kare Cikinta Daya bayyana ba sannan tayi Kiba har ta Fuskarta ta Cicciko Idanuwanta duk girmansu sun shige Ciki.
Yakaka na ganinta ta koma ta zauna tana Fadin"ki zauna kina wani Tafiyar wahainiya ni dai na riga na yi fashin Dan Madina abuna..!

Amina ko kanta bata Dago ba har ta kariso falon Aliyu Sai kallonta yake yi ya Bude baki yafi a kirga yana Rufewa saboda mamaki Danmallam kuma Hannayensa Sarke saman kirjinsa yana kare ma Amina kallon Tundaga sama har kasa yana mamakin girmanta yarinyar daya barta marabanta da kwaila kadan ne itace ta koma wata Big mama..?
Ko"ina ya cika haka?
Cikinta kawai yake kallo duk nacinsa taki yarda su hada ido shi ko Aliyu ba mamakin ganin Amina bane ya Razana shi ba illah Cikin Dake jikinta ne ya fi bashi mamaki ya kalli Umar yafi sau goma ya kasa mgana shi kuma sai ya basar dashi bai shirya mgana dashi ba yanzu.
Amina kuwa kanta na kasa ta nemi kasan Cafet ta zauna Dakyar yakaka na fadin"kada ki takura kanki kowa yasan Lalurace hau kujera ki zauna mana..!
Ko kallon yakaka batayi ba tayi zamanta Saman cafet kanta na kasa Ya Aisha sai kallon Amina take yi tana Hararanta ganin yadda ta hade rai Yakaka ta saki baki tana kallonta kafin tace"Yau naga Tsiya Indo..?
Amina fa sai Addu"a jira take su gaisheta kenan..?
Amina sai alokacin ta Dago kanta karaf suka Hada ido da ya Danmallam Daya gama kafeta da ido tun shigowarta ya kasa dauke ganinsa akanta yana ta mamakin girmanta sannan yana Tunanin yadda yaganta da Cikin nan bai taba Hasaso hakan nan kusa ba akanta ba sai gashi Allah ya nuna nashi Ikon.
Saurin Dauke kanta tayi Saboda wani Dum dataji da yanayin kallon nasa sai da taji dan Cikinta ya koma gefe daya Ta Cikin Hijabin ta dora hannunta kan cikinta tana jin wani kaunar abunda ke Cikinta na kara shiganta Tun ranar da sukaje Scan aka hasko mata abunda ke Cikinta wani soyayyarsa ta ratsa kirjinta taji duk duniya bata da wanda take so kamarsa abun ya bata sha"awa dan mutum acikinta yana Rayuwa..
Bata kara kallonsu ba cikin shakewar murya tace"sannun ku da zuwa..!
Aliyu ne ya amsa yana kallonta Cikin Shanye mamakin sa yace"Yauwa Amina ko..?
Amina ta dago ta kallesa kafin ta maida kanta kasa ta gyada mai kai Cikin mirmishi yace"Allah Sarki ashe kina nan..?
Ya nauyin jiki kuma..?
Sai ta kasa mgana Yakakace ke fadin"Ai ta Dade anan watan ta biyu ko Aisha..?
Ya Aisha tace"Eh ta dan jima..!
Aliyu ya jinjina kai yana kallon Amina yace"Allah ya rabasu lafiya..!
Yakaka da Aisha suka amsa mai da Ameen ya Danmallan dai bai ce komai ba,Sai kallon Amina yake yi kasa kasa.
Aisha tana Lura dashi sai ta isa wajen Amina tana fadin"Amina taso na ganki mana..!
Tafada tana taimaka mata ta mike Tsaye yakaka ta kalleta tana Fadin"Ahto gwara ki jata ki Fadamata gaskiya ko zataji..Koda yake ta makara na riga na kwace mijin Dani zai koma garin Manzo..!
Aliyu na Dariya yace"Kwarai baba. !
Hararanta Amina tayi tana Tura baki Yakaka tace"Ni miye nawa..?
Ga wanda zaki tura ma bakin nan..!.
Tafada tana nuna Danmallam da suka Hada ido da Amina ta Tura mai bakin sannan tabi bayan Aisha Mirmishi ya subucemai tuna Kirarinta Aminene ce fa..badai ta mutum ba sai ta Allah .!
Yakaka ta bita da kallo tana rike baki tace"Mun shige su ta ko turamai bakin Ali kana dai gani ko..?
Dariya yayi yana Fadin"Kyalesu yakaka chan tsakaninsu ne mu ba ruwanmu..!.
Yafada yana kallon Umar Dayaki yarda su hada ido.
Inda su Amina suka shiga ya kurama Ido Yakaka da Aliyu suka cigaba da Hirarsu tana ta mai Hirar zuwanta Saudiya ne na farko yana shan Dariya shiko Danmallam gabadaya hankalinsa na kan Amina shi yasan Laifinsa tun kafin ta fada.
Suna shiga Dakin ya Aisha ta ja ta tsaya tana Hararan Amina..
Amina ta nemi gefen gado ta Zauna tana Fadin."To wai ni me nayi ne..?
Ya Aisha tace"Bansani ba..Kada kiban Haushi na make ki wlh..!
Amina ta tura baki batace komai ba ya Aisha ta zauna gefenta tana Fadin"Haka ake gaida mutane .?
Shi fa ya Dannallam ko gaishesa baki yi ba ballatana ya Aliyu..!
Amina tace"To ba nace musu sannu da zuwa ba.!
Ta fada tana Hura Hanci Aisha tace"Ai sannu da zuwa ba gaisuwa bace malama. !
Amina ta tura baki tana fadin"Ni ba ruwana dashi sai fa yau yazo alhalin yafi kwana hudu da zuwa kuma kuma ma sau daya ya kirani tunda yazo wato yana chan wajen guzumayen matansa ni kuma yamin ciki ya barni da Wahala..!
Sai hawaye Ya Aisha ta saki baki tana kallon Amina Dariya na cinta tana auna Dimarar da za"ayi in zama waje Daya ya tabbata Tsakanin Amina da su Sakina akwai kallo.
Ya Aisha data Fahimci kishi Amina ke yi bata sani ba yasa Cikin sigar lallashi tace"To ai gashi yazo yanzu ko..?
In ma zaki nuna bacin ranki bata haka Zaki nuna ba kamata yayi yanzu ki tashi kiyi wanka ki sauya kaya ki gyara Jikin ki kina tashin kamshi,Sai in dan ya shigo kuka gaisa sai ya ce ya kike..? Ko ya bby na..?
Sai kice ai baka so kasan ya nake ba Tunda kazo su Anty na sun sa ka manta dani..!
Irin haka dai cikin shagwaba..!
Amina ta kalleta Sheke sheke kafin tace"Tab uban wa zai ce musu Anty..?
Allah ya Tsareni ni ko abaya ban ce mata Anty ba ballatana yanzu da muka Hada miji kowa yayi ta kansa .!
Ya Aisha na danne Dariyanta tace"To naji Kiyi hakuri ki tashi kiyi wanka ni yanzu Kitchen zani na sama musu abunda zasu ci ni da Saude kin karya ko..?
Tana kunkuni tace"nasha kunin da Saude ta Damama yakaka..!
Ya Aisha ta mike tana Fadin"To yi wanka in mun gama sai Saude tayi miki wainar Fulawanki..!
Da haka ta fice bayan ta kara Lallaba Aminar ganin kishin Ya Danmallam take yi bata sani ba..
Falon ta koma yakaka dai da Aliyu sai hira suke sha,Danmallam kuma na Zaune yayi shuru,Tace bari ta shiga Kitchen suka amsa mata sai da ta leka Usman ta iskesa yana waya sai ta fice ta shiga Kitchen domin taya Saude wasu ayyuka,sun saba tun agida basu taso da son jiki ba.
Amina tana Fushi tana kunkuni tatashi tayi wanka tazo ta Shafa Lotion din da Ya Aisha ta siya mata ta Dauko Cikin Dogayen rigunan da Aisha ta siya mata mai kalan baki da Zanen ja ajiki.
Ta saka Rigar kenan ta juya saman gado ta Dauko bakin Dankwalin Rigar sai ta dan taka Rigar ta kasa ta dan Zame tayi baya zata fadi har ta Sadakar ta sha kasa taji ta ta Fada Hannun mutum tana Bude ido suka Hada ido da ya Danmallam har Gemunsa na taba Fuskarta.
Kallon kallon sukama juna kowa da abunda yake sakawa gajiya yayi da Zaman falo yakaka da Aliyu na Hiransu ya tashi ya shigo Dakin da Amina ta shiga tun dazu Aliyu ya Bisa da kallon mamaki Yakaka dai batama Lura dashi ba Ta tsinke da Hira abunta.
Amina ta lumshe ido jin kallon nasa har Cikin kanta Saurin tashi tayi ya taimaka mata ta tsaya sosai yana Fadin"Ki kula fa Aminene..!
Da mugun mamaki ta kallesa tana Tunanin ina yasan ana ce mata Aminene..?
Gira ya Daga mata yana Sakin mata Mirmishinsa na koda yaushe Daga sama har kasa yake kallonta yana kara more kallonta Har da jingina jikin Madubin Dakin yana dunkule hannayensa saman kirjinsa yana binta da kallo da dukkan zuciyarsa.
Ita kuma ganin yadda yake kallonta yasa ta Tura mai Baki ta juyamai baya tana kokarin Daukan Dankwalinta ta Rufe Kitson kalaban da ya Aisha ta mata.
Kawai sai jinsa tayi a bayanta gemunsa na taba wuyanta saboda ya fita Tsawo ita tana iya kirjinsa ne Dankwalin ya karba ya rankwafa yana mata rada"Ya kika juya..?
Kada kimin rowan ganin Yadda Cikina ya sa kika tashi daga kwaila kika koma Big mama .!
Batasan Sadda ta sakarmai Dankwalin ba ga kunya sannan ga fushi sai ta ki juyowa tana Tura baki hannunsa duka Biyu ya sa ya juyo da ita yana kallonta Runtse ido tayi taki Budewa.
Dariya ta basa sai ya ja karan Hancinta yana fadin"Duk fushin ne yasa ko kallona ma an kasa yi..?
Kara Turo bakin tayi sai ji tayi ya Sakar mata Kiss a saman bakin da Sauri ta Bude manyan idanuwanta ta ware akansa cikin mamaki gira ya Daga mata yana kallonta itama shi take kallo ya kara fari sannan yayi kiba Yana sanye da Shadda fara dinkin Tazarce da hula sai tashin Sayayyan kamshin Turaransa yake yi mai Dadin Shaka wanda Amina taji yana mata Dadi har Hancinta take Budewa tana kara shaka..
Gemunsa take kallo ganin ya kara Tsawo sai dai yana sheki yaji gyara sosai ya shagala da kallonta yaji ta jamai gemu da Sauri ya kalleta yana Waro ido tura baki tayi lokaci Daya ta kara Juya baya.,Mirmishi yayi kafin ya taka zuwa Gabanta yana kaallonta kokarin kara juyawa take yi ya rikota Cikin mararaicewar da baisan ya iya ba yace"Haba MEENA..a daure a fadamin Laifina mana..?
Meenar da yace ne yasa ta Kallesa Cikin wani yayi a baya Aminu kadai ke kiranta da wannan sunan a kuma Lokacin sai taji yafi kowa iya Kiranta da haka sai dai yau sai taji Duk Duniya sunan a bakin mai Daraja wato Danmallam yafi dadi
Lumshe ido tayi sannan ta Bude tana kallonsa hannunta Daya ya rike Dayan kuma ya Dafa Cikinta yana Fadin"Ko saboda Abunda ke Cikin ki Amina .!
Baki ta kara Turawa kafin tace"Ba kai bane..Sai yau kazo ganina..!
Sai ido ya kawo ruwa da Sauri yace"Am sory kiyi hakuri kinsan gajiyan hanya..Sannan kinsan Dole sai na natsa na samu natsuwa ko .?
Amina ta Hura hanci tana Fadin"kuma ai baka kara kirana ba Tun ranar da kace zaka kirani. !
Sai hawaye sharr suka zubo baisan Lokacin Daya jawota jikinsa ba ya Rungumeta har Cikinta na Dukansa bai Damu ba kam ya rumgumeta yana jin wata natsuwa da salama abun mamaki itama hannayenta tasa ta Zagayo bayansa ta rikesa kanta ta baje saman kirjinsa domin sai taji kamar ta samu kafadan data Dade tana nema domin tayi kuka ta kauda kuncin zuciyarta yau ba yaya aduniya ita kadai ce zata kwanta ajikinta tayi kuka son ranta to sai Mijinta Datake ganin bata da kamarsa sannan yasan abunda ke faruwa yasa ta barke mai da kukan da yayi wata Biyu yana cinta acikin ranta,Lallashinta yake yi da sigar Shafa bayanta zuwa kanta yana dan jijjigata,ammh kamar ana bude mata famfo haka ta saki kukan nata riri riri sai ya rude hankalinsa ya tashi daman tun Fil"azal shi bamai son kuka bane ballatana Hayaniya,Sannan kukan ma irin na Amina duk sai yaji ya Durbuce haka ya sake kamkameta yana fadin"Shikenan is ok..Daina kukan na amsa Laifina..!
Ina bata ma jisa ba kuka take har da Shessheka sai ya fara tunanin kukanta ba na iya fushinsa bane akwai wani abu cikin wata irin murya yace"Uhm fadamin me ya faru..?
Cikin kukan Amina tace"Ka da ka hanani kuka ka barni nayi..Nayi watanni ina fama da nauyi acikin kirjina bansan kafadan da zai tallafamin in yi kukana sai yau..Don Allah yaya Danmallam kar ka hanani kukana.. abu mafi ciwo da Mamanmu tamin arayuwata na iya Tsawon rayuwata bata barni nasan Dadin Uwa ba..Yaya..YAYA bata taba sanin jin dadina ba sai akasin haka har ta koma ga Allah ya kake so nayi..?
Taya zan manta wannan zaluncin Datamin.?anan zuciyata ke min zafi kamar zan mutu..!
Tafada tana gunjin kuka Lokaci Daya tana Dora Hannunsa saman kirjinta Wani Tsausayinta da sonta da baisan ma akwai aransa ba ya taso ya fara share mata hawaye da Hannayensa yana Fadin"Ki yi kuka ammh kadan bamai yawa ba kin ga dai bake kadai bane ko..?
Bazan yafe ma kaina ba in wani abu ya Sameki keda abunda ke Cikin ki ba Amina .!
Amina ta kamkame Hannayensa tana Cigaba da kuka kamata yayi rumgumeta yana fadin"Ki yi kukan dai kadan na Samun saukin zuciya Kafadata da kirjina da Hannayensa zasu miki garkuwa har Abada..Kiyi hakuri ki ma yaya addu"an Allah ya jikanta kuma ni nasan har ta koma ga Allah addu"a take miki bazata taba aibataki ba. !
Jin haka yasa ta kara barkemai da kuka Tana fadin"Shikenan sai a barta ta kashemana uwa kuma tana zaune lafiya..?
Hannunsa a bayanta yana shafawa yake fadin"A"a ai Allah ne zai fara mata hukunci da ita da duk wanda suka hada hannu wajen kashe rai Amina..Duk da munsan Allah ne mai kashewa kuma ya raya ammh su sun zama Sanadi in har sun aikata wannan girman laifin Allah bazai bar su cigaba da zalunci ba sai ya Tona musu asiri kowa ya gansu sannan zasu yi rayuwar kaskaci domin hakkin Rai bazai barsu ba..!
Amina tace cikin kuka"Insha Allahu sai sun Dai'daita aduniya sai sun wulakanta..
Ganin tana neman fita Hayyacinta yasa ya Dago kanta sai ji kawai tayi ya Toshe bakinta da nashi Lokaci daya ya fara sumbatarta kamar Allah ya aikosa cak ta nemi kukanta ta rasa Ta waro ido tana kallonsa shima ita yake kallo yana jin yadda zuciyarta ke faman Bugawa tare da nashi Amina bazata iya ture wannan lamarin ba,Bata san sadda ta lunshe ido ba ta tallafi Hannayensa domin taimakamai shi kanshi yayi hakan da niyar ta natsu sai gashi ya Zarce bai sani ba Daga baki ya koma ya rikice yana Taba duk inda Hannunsa yakai mamakin jin yadda hannunsa ya Cika da kirjinta yake yi Cikin Fitan hayyaci yace"Amina sun kara girma k'wai na mai kyau ne..Aminana ta tashi daga mai Nonon lemon tsami ta koma na kankana .!
Yana fada yana damukansu Amina ma jinsa ai ba baka sai kunne Tana karban wannan sakon sosai fiye da Tunaninta duk da na farkon haduwarsu bata fahimci komai ba saboda farko ne alokacin Sannan abun da ya faru ya faru ne dukkansu batare da sun tsammanci Faruwarsa ba.
Shiyasa wannan karon bata san ta Saki jikinta ba,Kuka kuwa Tsab ya tsaya ta nemesa ta rasa tana jinsa yana mgana sama sama bata ma fahimcesa ba sai kara shigewa jikinsa take yi kamar wata mage neman rasa natsuwarsa yake yi domin wata irin bukatuwan kasancewa da Amina ne ya taso mai kamar an mai Tuni ya Tuna da gidan Aisha fa kuma kanwa take garesa yana kokarin Daidaita kansa yaji ana knooking da Sauri ya Raba Amina da jikinsa kasa Tsayuwa tayi sai ta koma ta zauna bisa gado ta juya baya shi ya yafa mata gyalen rigarta sannan ya bada izinin shigowa Ya Aisha ce ta shigo da Faranti shake da kayan kari Dan mallam ya tarbeta ya amsa yana mata sannu ta amsa Amina ta kallah wacce ko juyowa batayi ba sai yanzu kunya ya kamata na aikin data aikata.
Dariya kawai tayi Danmallam yace"Ina Aliyu..?
Aisha tace"Yana falo shi da Yakaka yana cin abinci naka ne wannan..!
Danmallam ya kalli Amina kafin ya kalleta yana fadin"ita fa..?
Ya Aisha tace "Ai bata cin abinci iri iren wannan ga wainar fulawanta chan Saude na soya mata. !
Sai alokacin ya tuna da Sakon Hajiya kai Tsaye yace"Kice ma Aliyu ya Dauko Sakon Hajiya da wata leda a Mota. !
Aisha ta amsa mai da toh ta fita tana Fita ya Zauna akasa ya tankwashe kafa yana kallon Amina kasa kasa Dariya ta basa ganin yadda ta kara juya baya baki ya rike kafin yace"bayan kin gama Damuka ni kuma miye na juya baya .!?
Ai tana jin haka sai ta kara juya baya kunya kamar ta nitse dariya yayi da sai da taji Sautinta aransa kuma fadi yake yaro man kaza.
Farantin yaja gabansa tea ya hada ya sha sai Dankali da kwai da yaci duk Amina na zaune ta juya baya Lokaci bayan Lokaci tana satan kallonsa sai zai juyo sai ta kauda kai shi kuma yana Lura da ita Dariya da sha"awa take basa. haka kamar bazata aikata irin abubuwan data aikata ba.
Sai da ya natsa sannan yayi Hamdala ya Ture farantin gabansa wayarsa ce tayi kara kidan Larabawa a gaban aljihunsa ya Dauko yaga Sakina ke kiransa satan kallon Amina yayi kafin ya Daga kira suka gaisa da Tambayan Hanya sai ta bama Sarood suka sauya Yare zuwa Labarci Amina tunda ya fara mgana ranta kawai sai ya baci yana Sauya yare ta mike fit zata fita Daga Dakin tana kunkuni tace"In dai akayi gulma ta dai ban yafe ba..!
Yajita sarai yasa ya rike hannunta tazo zata gifta ta gabansa tana Dagowa yana mikewa sai ji tayi ya kara rike hannunta gam yana kuma cigaba da wayarsa.
Sai ga ya Aisha ta shigo ta kawo leda babba Daya sai karama guda Daya ganin yanayinsu yasa ta fice da Sauri tana ma Amina sigina duka yana ganinsu.
Har ya gama wayar bai saketa ba sai da ya maida wayar aljihu yana kallonta bata san sanda ta ballamai harara ba Dariya yayi yana Fadin"kikace in anyi gulmarki baki yafe ba. ?
Ido ta Zaro Cikin mamaki tana Fadin"Ni..?
Kanta ya shafa yana fadin"Eh ai na jiki..Bama su san wajen ki zan zo ba..!
Amina ta tabe baki batayi mgana ba Cikinta ya shafa sannan ya Duka agabanta yana kallonta ita da Cikin kunya ya bata ta yi saurin kauda kanta Kansa ya kara jikin cikin yana Fadin"Assalamu Alaikum...Ana Abbuka!
Ya fada yana manna ma Cikin Kiss Sai ya bata Shawa"awa tana chan ta shagala da kallonsa sai da taji itama ya mata peak a kumatunta sannan ta farga ta Hura hanci ta tura baki Bai biye mata ba domin kada tasa ya aikata abun kunya.
Ledojin da Aisha ta shigo dasu ya Dauko ya kawo gabanta ya bata na Hajiya bayan ya fadamata daga Hajiya sai nashi yace Tsaraban madina da kayan bbys daya siyo suka Zauna akasa suna ganin kayan sun mata kyau matuka Amina sai Daga wani Overrol na Jarirai take yi tana Fadin"Ya Danmallam yanzu jaririn da zan haifa wannan zai shigesa..?
Yana Dariya yace"Sosai yara suna jariri basu da girma ba kina ganin su ba..?
Ta gyada kai tana Daga kayan nata ya Nuna mata yana fadin"Basu miki kyau bane .?
Ta amsa tana fadin"Wlh sun hadu nagode sosai kamar kasan bana sa atamfa yanzu sai dogayen riguna tun ina gida suka min kadan. !
Kallonta yayi kafin yace"Nagani kin tashi Daga kwaila kin koma Big mama. !
Kunya taji ta sunkuyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login