Showing 210001 words to 213000 words out of 265571 words

Chapter 71 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28915

achan ita kuma na dan Lokaci ne.
Sai Washegari yaje gidan mallam su Hajiya suka gansa yace sai jiya suka Dawo ya tabbatar musu da Amina tana lafiya tace agaishesu da Aisha mallam yaji Dadin haka shi da Hajiya Duk da Hajiya tasan daman Amina Zata samu kulawa sosai a inda ta kaita
Hanne da Hamida ma ya basu Sakon Amina na gaisuwa,ammh ya gargardesu kada su fadama kowa yaje wajen Amina sukace bazasu fada ba Hankalinsu ya kwanta Tunda Amina na Cikin koshin lafiya.
Aranar Amina ta kirasa suka yi mgana ta Tambayesa ya suka sauka yace Lafiya lau basu yi wani mgana ba suka yi sallama Har alokacin Amina Haushinsa take ji baisan me yayi mata ba ita ko Tunda yace zai tafi bakin ciki ya isheta in ta tuna inda zai koma shiyasa tayi kwanciyarta kamar tana barci da zai tafi Ahalin idonta Biyu bata son tatashi din ne.
Shima ganin yanayinta sai bai matsa mata ba,shirin tafiya ma suka fara domin yana ta Cukun cukun nema musu Visa, cikin ikon Allah kuma an samu Visar da wuri zasu tashi nan da kwana Hudu tunda ya fadama Amina zai koma da Sakina da Sarood Amina ta Daina walwala a kaduna Ya Aisha duk tasan Dalili itama abun na Amina ma Dariya yake bata wani Lokaci kishi sosai take yi in kuma an ce tana son ya Danmallan tace atafau ita bata son shi.
Ana saura kwana Biyu su koma ta Tadamai hankali awaya tana kuka Dole washegari ya taho Abuja da kansa ya Tuko kansa sai dai suka kara ganinsa kwatsan jidalin Amina yayi kira,Ranar bai kwana ba ko Awa Hudu bai yi ba ya Samu ya lallashi Amina ta Daina kuka bai dai yi shagalinsa chan ciki ba sai dai ya sha Shagalimsa Daga sama kuma bata Hanasa ba sai ma ta taimakamasa,Da wuri ya tafi bayan ya bata kudade a hannunta saboda Tasowar wani abu Amina kuka riris take yi kamar karamar yarinya mamakinta kawai yake ya rumgumeta yana lallashinta yana Fadin"Da Hajiya zata bari da na tafi dake Amina ni kaina ina Bukatarki kusa dani..!
Baki Ta tura tana Hawaye tace"In ka tafi yaushe zaka Dawo..?
Yana rike da Hannayenta yace"Wlh bazan Dade ba ai nasan Halin da na barki ga kuma waya ZAMU dinga mgana da juna kin ji ko..?
Kai ta gyadamai tana share kwallah ya taimaka ya share mata Cikin salonsa Sannan ya kalleta Cikin ido yace"Zan yi kewar ki Aminata..!
Baki ta Turamai kafin tace kasa kasa"Uhm in guzumayen matanka sun barka kayi kewata ba. !
Yajita sai da ya Bude baki yana kallonta da Sauri ta juyamai baya yafa riga ya sani Amina kishinsa take yi dashi da matansa ba nawa wasa ba Na Sakina kadan ne.
Juyo da ita yayi ya kama bakinta ya tsotsa sosai sannan ya saketa yana Fadin"Ba ruwanki da matana..Ai nasan dasu nazo wajenki Tundaga Gumel Amina..?
In kikace haka sai naga kamar ban yi miki adalci bane .?
Ganin ya Damu yasa ta fada jikinsa ta Rumgumesa sai Hawaye tace"Kayi hakuri..!
Yana shafa bayanta yana fadin"Baki tabamin komai ba..Sai kuka ne kadai Tsiya na Dake kuma shima na yanke shawaran ki gayamin kudinsa na siyesa na Huta.!.
Tana Dariya tana Dukan kirjinsa yana Tayata ganin zai bata Lokaci yasa ya saketa yana fadin"MEENA zan tafi..!
Kanta na kasa tace"Allah ya kiyaye hanya..Allah ya tsareka. !
Ya amsa da Ameen cikin sanyinsa har ya juya ta rike mai riga ya waigo yana kallonta kafin ya sami bakin mgana ta Zo gabansa ta yi Dage ta kama Bakinsa da Hannayenta ta yi mai Dogowar sumba sannan ta a sakesa tana sharan hawaye ta shigo Tiolet ta kulle sai da ya tafi ta fito duk ta sha kuka ya Aisha da yakaka na mata tsiyan bata som miji tana kuka zai tafi sai ta kara fashe musu da kuka ji take yi kamar zata mutu shikenan sai tayi wattani zata sake ganinsa..?
In da ma shi kadai ne achan da sauki ammh har da matansa fa shine karin Haushinta..
Shi kanshi Danmalllan in za"a bashi Zabi Tsab zai ijiye sakina ya tafi da Amina sai da bamai zai fara ba Hajiya bazata taba yarda ba,Wlh har acikin Ransa yake jin mgana washegari jirgin yammah suka bi zuwa Jidda kamar an zare mai lakka haka yake ji bai da karsasashi kan tafiyar har su Sakina sun fahimta.
Anty Amarya dai sai hamdala domin Hankalinta bai kwanta ba sai da Sakina ta kirata tace sun sauka a madina sannan taji Ta Sauke numfashi ta gama da wannan bangaran yanzu Haj.Uwani zata nuna ma bata isa ba zasu goga shege ka fasa..!
Domin Taga alamar zata iya nasara akanta Tunda har yanzu Tare da Nazeem Aba ke komai abunda bata sani ba,Haj.Uwani ta fita sanin komai kan Dukiyar mallam,Domin zama take da Nazeem tana dukan ruwan cikinsa tana jin komai balle ma da Aba ya sakarmai bangaran Lissafi da Shigar kudi da Fitarsu Hajiya uwa ta gama Tsara taci nasara ma ta gama Domin ta fara hango kamshi hakan.

Amina bata warware ba saibayan kwana Biyu da suka yi mgana Danmallan yace mata sun sauka Lafiya ya kuma bata Lokaci wajen bata baki adaran ranar ya kirata yamata bayanin yadda zata sha ruwan Zam zam din Dake ledan kayan Tsaraban Daya kawo mata yace duk Dare ta rika shafe jikinta ko"ina dashi ta yi addu"a in zata kwanta Tunda tace ta Daina Tsorata in tana barci.
Sannan yace mata ta dinga shan ruwan Cokali uku Kullum arana sau uku ta sha da Bismillah da Fatan waraka a wajen Allah.
Bata ko yi kasa a gwiwa ba ta fara yin sa kamar yadda yace mata sannan wani Lokacin in zata kwanta shi ke kiranta ya tuna mata watarana ma baya kashe wayarsa sai tayi sunyi addu"an tare ta kwanta sannan yake a kyaleta kuma Sakina ko Sarood ba wacce ya bari ta Fahimci wani abu yana Kafa kafa domin shima yanzu ya gane Dan adam ba abun yarda bane.
Barin ma wanda kake tare dashi yafi Cutar Dakai.
Bangaran Mamanmu kuwa babu abunda ya Shafeta harkan gabanta kawai take yi ta samu Duniya yadda take fata Hamida ne kawai agabanta Sai Jawaad data jasa ajiki saboda kada ta bada Fuskar da za"a zargeta itama Shawearan Madiina ce ta Dauka Aba kuma yanzu ba kowa agabansa sai Balaraba,Da shawarta yake komai ko Jafar ya fara ganin Sauyi domin sai sun gama mgana da Aba sai kuma ya sauya mgana in yace meyasa sai yace Balaraba ce tace in akayi kaza yayi..?
Tun baya mamaki har ya fara ko yaya Lokacin tana da rai Aba bai taba cewa tace kaza ba ballatana mamanmu akan harkan da bai shafeta ba sai dai bai Taba mgana ba sannan Tsakaninta yaran Lafiyau suna waya ko da yaushe sun rike matsayin uwa harta da Jafar din kuwa Amina kuwa in ba hirarta akayi ba mancewa take yi da ita ke ma fada ma yan gusai Hajiya takai Amina maiduguri kowa yaji sai yace saboda mene .?
Mamanmu tace ita bata sani ba to ba wanda ke Mgana sanin Hajiya ai bazata Cutar da Amina ba.
Su Hamida sun gama WEAC suna Shirin Fara Neco har sun fara Sabawa da rashin Amina..
Ranar suna zaune afalon mallam Gabadayansu matan yaran ne kawai basa nan suna ta kallon tashar Labarai suna Hira sama sama.
Anty Amarya ta kalli Haj.Uwa suka ma juna wani irin kallo kafin taa kalli Baba maalllam tana fadin"Mallan nace Hala dai Nazeem shi zai gaji
Sa"idu awajenka kenan..?
Kowa ya tsaya yana kallonta ita kuma da Biyu tayi saboda Uwani tasan matsayinta.
Baba Mallam ya kalleta kafin yace"Bangane tambayar ba marliiya..!?
Hajiya kuwa sarai ta gane Sai dai batace komai ba Huruminta bane.
Anty Amarya tace"To ai gani nayi yanzu tare suke komai..kamar Sa"idun ya fara sakarmai komai..!
Baba Mallam ya kalleta na wani Lokaci kafin yace"Cikin ku wake da Tunanin cewa watarana zan sauke Sa"idu daga kan dukiyata na Dora wani Cikin ya"yanku .?
Dukkansu suka kasa mgana Haj.Uwani banda Hararan Anty Amarya bata komai ita kuma sai mirmishin nasara take yi..
Mallam ya kallesu Daya bayan Daya Cikin kaushinsa yace"To in ma wata Cikin ku na wannan Tunanin ta Ciresa daga zuciyarta..Dukiyar da Sa"idu ya sha wahalan tarata ba tare da Taimakon ko Daya daga Cikin ku ko na ya"yanku ba rana Tsaka kawai sai na Dauketa daga hannunsa saboda na Zama Butulu..?
To ba haka nake ba..Nazeem yana samun aiki zai kara gaba daman saboda ya taimaka ma Sa"idu ne ba wani abu ba ko Mutuwa nayi yau RABIN Dukiyata ba tawa bace kuma sani Daga yau din nan..!
Gabadaya suka kallesa da mamaki banda Hajiya da riga tasan Mallam ya Bama Aba Rabin duk abunda ya mallaka saboda mallam yace shi yayi walahanta tun yana matashinsa har Tsufansa..
Haj.Uwani Cikin wani yanayi tace"Na waye ..?
Mallanm ya mike yana Fadin"Ta SA"IDU ce..Da iyalansa..!
Komai yana nan a Rubuce yadda ya Bauta ma samuna ko Duka na basa ban biya sa ba..In ma zaku bama ya"yanku shawaran neman na kansu ku basu Dukiya dai tawace ba ta Daya Daga Cikin ya"yanku ba..!
Daga haka ya tashi ya shige Hajiya tayi wani mirmishi ta mike ta fita Haj.Nasara ke da Turaka tabi maalllan Ciki akabar Haj.Uwani da Anty Amarya na kallon kallo.
Haj.Uwani na kallon Anty Amarya kamar ta Tashi ta mata Duka itama ta mata Dariyan mugunta.
Mikewa tayi ta isa gaban Haj.Uwani Tana fadin"Kin dai da kunnen ki ko..?
Ko kina bukatar na kara sanar dake. !
Haj.Uwani ta mike ta bangaje Anty Amarya sai da ta kusa Fadi Cikin kaushinta tace"Wlh Tallahi ki sa aranki bani kadai zan rushe ba Marliya..Dukkamu sai dai mu rushe uban kowa ya rasa..!

Daga haka ta fita Daga Falon kamar Zata tashi sama,Anty Amarya ta Bita da Dariya itama tabi bayanta ammh ko Ita Dariyan karfin Hali take Sa"idu dai shi gaba ta kaisa sannan Dayyaba ta samu Duniya
Har takai shashenta Bakinciki ne ya Cika ka ita ta ma Dayyaba Hanya ta samu abunda take so ammh ita duk wannan Wahalan tana neman tatashi a Tutar babu..Tabdijam..Daman ai balaraba ta Rage neman ta ko wajen mallam sai dai ta Zagaya tatafi ita Kadai wato ta gama samun komai tana neman ta watsa mata kasa ido to bata isa ba kamar yadda Uwani tace ba Zata taba yarda ta rushe ita kadai ba sai dai kowa ya rushe..
Daga ita har Balaraba har Uwani indai ita bata samu Cikar nata Burin ba to sai ta tsawarwatsa nasu Cikar burin uban kowa ya rasa.





*Janafty*

*TFZB2022*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*

Yau da gobe bata bar komai ba Daga yini mun shiga kwana Daga kwana sai a fara kirga kwanaki Daga kwanaki sai a fara kirga satittika Daga Satittika sai a fara kirga wattani to kamar haka ne tunda gashi har su Hanne sun kamallah duka jarabawarsu ta kamallah babban Sakandiri suna gida sai jiran sakamako sai dai basu Daina zuwa islamiya da Hadda ba Daga Umarnin Baba mallam.
Har zuwa wannan Lokacin Daga ban garan Hajiya ba"a wani bayanin inda takai Amina ba,Sai dai irin Anty Amarya da mamanmu da sauran masu Tunani irin su suna Daukan Amina tana maiduguri sannan ganin Dadewa da akayi ba labarin takamammen inda Aminar take sai suke Tunanin auranta da Danmallan ne ya Lalace Hajiya ke son gyarashi.
Ita dai ta koma gefe tayi bakam bata taba nuna tasan wani abu ba, yanzu in an isheta da Tambaya sai tace bata sani ba,Har Abida data isheta haka ta Fadamata har kuma ya Aisha ta kira sun yi mgana ammh bata taba ce mata Amina na wajenta ba ta riga ta rike alkawarin Hajiya da gargadin datake mata akoda yaushe kan Boye Cikin Amina da zamanta a wajenta.
Anty Amarya ita da Uwani ake takun saka yayinda mamanmu ta koma gefe ta Zama yar kallo domin bata da wata matsala,In Anty Amarya ta Kirata sai ta mata Dadin baki da mganganun nasara ta rufe bakinta sai sun gama mgna ta rika mata Dariya Haj.uwani kuwa Amarya bata gabanta domin tana kallonta karamar alhaki ne badai Nazeem din na tare da Sa"idun ba har an sakarmai komai ba..?
Maji mgani an tura uwar Amarya Biko ita har ta hango kanta a matsayin data Dade tana Hango kanta Tunda Dadewa.

*****

Achan Abuja kuwa a bangaran Amina cikinta na cikin na wata Takwas kenan ta kara kiba sannan komai na Jikinta ya fashe hancinta bakinta komai ya kara girma sannan sai da cikin yakusa wattanin Haihuwansa sannan yayi wani irin girma Allah yasa tana da Tsaho ai da ya shanyeta,Tana cigaba da zuwa awo da ganin Likita In usman baya nan ita da ya Aisha take zuwa ko Zuwansu na karshen nan an tabbatar musu da Abunda ke Cikin Amina yana cikin koshin Lafiya.
Amina in ta kalli kanta a madubi sai ta fashe da kuka wai duk ta sauya kamar ba ita ba watarana Yakaka tayi ta mata Nasiha ranar da yan Fada ke kusata ta mata fada ko kuma tayi mata bakam kamar bata jita ba.
Kishin Amina akan mijinta ba irin na Sauran mata bane nata na Dabam ne akwai Tsabar jidali da neman rigima atare da ita koda yaushe suna waya da Danmallam domin yaji lafiyanta inda ta gane koma wani abu ne mamanmu ta mata ya fara rabuwa da ita ko tace ya rabu da ita gabadaya saboda ta gama amfani da duka mganin da ya Danmallan ya kawo mata Ta daina jin zafin zuciya da kunci sannan ta rage Taurin kai da Kafiya ammh fa bata rage rashin Tsoronta ba Sannan bakinta bai mutu ba Jidali kuma ta gama Fahimtar Halintarta ne sannan kuma Hali ai zanenn Dutse ne..
Ita yanzu ban da su Hanne da Haamida da Hajiya da mallam to sai Aba duk ba mgana take yi dashi ba yana ranta tana kuma bada sakon gaisuwa duk sanda sukayi mgana da Hajiya tace tana gayamai,Mamammu kuma ko Sau daya bata taba cema Hajiya a gaiisheta ba abun na bama Hajiya mamaki sai dai bata ma Aminar mgana ba Sauran yan"uwanta kuma duk da bata waya da kowa acikinsu suna ranta tana tunawa dasu Lokaci bayan Lokaci watarana in bakincikin ya isheta sai ta Zauna ta rika Tunano Rayuwarta Tun daga farko har zuwa yadda yau ta kasance da ita sai ta hau kuka sai tayi ya isheta take yin shuru ta koma tana Sauke Numfashi
Watarana in ta tuna da Aminu sai tace ko yana ina yanzu..?
Bata da masaniya sai dai tana mai Fatan Duk inda yake yana cikin koshin Lafiya duk yanzu bata san Dalili ba,bata jinsa aranta ko Domin tayi aure har da ciki ne..?
Ammh ai da Farko ai tana jinsa aranta ammh yanzu sam sai da ta tuna dashi tausayinsa ya kamata.
Danmallam kuma yana madina ne ammh Babu abuda Bai gani na Jidalin Amina bata barinsa yayi sukuni baya Kiranta in yana gida sai dai in ya fita Wajen aiki ita kuma Amina sai ta Fahimci hakan sai ta hada mai Tsiyarta bata kiransa sai ta Daidaici goman Dare a nan Nageria ko sha Daya sai ta kirasa shi kuma baya iya Share Kiran Amina data zama wata bangaransa a yanzu ammh baya yarda ya dauki waya gaban Sakina ko Sarood saboda komai na Bukatar sirri sannan akwai Tambayan da Sarood tatabamai bayan sun dawo wai ina Amina..?
Ko sun Rabu ne..?
Ya dade yana mamakin tambayarta Daya turketa sai ta fadamai wanda ya Fadamata saboda ba Tunaninta bane yadda yaga tayi ne yasa yasan Tsara mata akayi kuma ba kowa bace face Sakina abakinta ne Sarood zata ji wannan mganar bai ce ma Sarood komai ba ya bar mganar shiyasa yake kafa kafa bai taba bada Kofar da zasu Fahimci wani abu ba.
Ko a wayarsa Da NOOR yayi mata Saving din Lambarta hankalinsu kuma bai taba kaiwa wajen ba Saboda ma Tsaro yasa duk inda Zashi wayarsa na Hannunsa ko tana Jikinsa
Daya ga Kiranta yake kashewa sai ya ce bari yazo ko ya shiga Dakinsa ko ya fita waje in kuma yana Ciikin gari ya tafi masallaci sai ya sallami Amina da Rigimarta wanda shi da kukan nan nata in da zata mai kudi tsab sai ya siyesu da ya huta basu taba waya sun gama Amina bata tadamai hankali ba haka kurum sai ta kirasa ta sakamai kuka shi kuma Hankalinsa ya tshi bayason yaga Mace na kuka macen ma Amina fa duk yadda baisan Hayaniya yanzu sun kulla abota da ita Saboda Amina..
Ko dan wuni yayi bai kirata ba Daya Kira zata sakamai kuka tace ya manta da ita tana cikin wani Hali shi yana chan yana jin Dadinsa haka zai zauna yayi ta lallashinta har sai ta Sauko watarana ma in ta ji iskancinta bata Daga kiransa sai dai in ya gaji ya Kira Wayar Aisha suyi mgana sai an Lallabeta sannan take Daukan wayansa ta bakin yakaka tace duk ta rikita bawan Allah ita ya Aisha har mamaki take yadda Amina take juyaa Danmallam kamar waina a Tanda da Iskancinta iri iri.
Wani Lokacin fa sai da tashi cikin Dare ta Dokamai kira bata Tunanin wani Hali yake ciki yana tare da matansa ne ko basa tare..?
Ita kawai in ta kasa barci sai itama tace bazai yi ba,ai D'ansa ne ya hanata barcin shiyasa yawancin yanzu a Falo yake karihe barcinsa saboda da Zarar yaga Kiranta sai ya lallaba ya fita Falo in ya gama Lallashin nata bai komawa ciki sai yayi kwanciyarsa anan wani Lokacin ma barci ke Daukansa bai sani ba Tun Sakina bata saka Ido ba har ta Fara Tuhumansa ammh bata taba kamasa yana waya da Amina ba.
Ai shi ya kara ma saka mata suna Aminene jidali Aminene rigima duka taci sunanta domin ba wanda baya gani.
In ta fara kuka tana Fadin wai Cikinta ya Dunkule waje Daya ta kasa barci sai mamaki ya kamasa daman ai Dole Zata Fuskanci haka tunda Wani Hallita ne ke Rayuwa acikinta wani Lokacin sai ta faramai kukan duk tayi muni ta xama katuwa kamar ba ita ba Shi dai ai nashi ban Hakuri ne da lallashi Ranar datake jin yan arziki kuma ayi ta mai Shagwaban an yi kewarsa to sai ayi soyayya ranar kuma da yan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login