Showing 159001 words to 162000 words out of 265571 words

Chapter 54 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28925

yana shafa Sumar kansa data fara Tohowa.!

Gajiya ce ajikinsa domin yau tun Safe ya bar gida yana da ajin karfe takwas na Safe zuwa goma sannan bayanan ya shiga na goma zuwa sha biyu daganan kuma suna da meeting da zasu yi na malaman shashin Dayake koyarwa gabadaya
Sakamakon yau Alhamis ya tashi da azumin Lada kamar yadda ya saba so yake ya tashi ya isa babban masallacin Cikin makaranta yayi karatun Qur"ani kafin lokacin Sallah yayi ammh ya kasa tashi kasala Tare da Gajiya sun Taru sun lullubesa.
Kansa ya kwantar kan kujeran Dayake zaune idanuwansa suna lumshe kamar mai jin barci nan kuwa ba barci yake ji ba Tsabar Tunanin abunda ya faru tsakaninsa da Sarood jiya da Daddare ne ya Addabesa
Shi bai taba Daukan matsalan sa da Sarood mai girma ba sai jiya daya kara jaraba Kusanta ta abu yaci tura kamar dai baya da ya riketa ajikinsa tafiya ta fara tafiya sai yaji komai ya koma ya kwanta a duba da abunda ya faru tsakaninsa da? Amina ya Dauka Komai zai yi daidai tsakaninsa da Sarood sai kuma yaga akasin haka,Bai taba Daukan abun da Serious ba sai jiya Saboda abun kamar zai yuyu sai kuma abu yaki yuyu shiyasa wani Lokacin baya son rabarta kar yajamata matsala tunda ita macece Tana da Rauni Fiye dashi sannan shi yana da wata matar ita fa..?
Shi ne kadai mijinta kuma Wanda zai Biya mata Bukararta in ta taso.
Ajiyan ya dauka komai yazo karshe Ganin yadda abun nasu ya fara kamar gaske sai dai ina Yana zuwa gabar sai komai ya kwanta yaji bai iya Tabuka komai abaya ya Dauka Sha"awan ce ke Daukewa shiyasa girman nasa bata Mikewa alokacin ammh Daga Jiya ya fara Zargin da wani abu Saboda shi kanshi yayi mamakin yanayin da ya shiga jiya da Taimakon addu"a ne kawai ya iya Sarrafa kansa.
Sarood kuma kwana kuka tayi bai ga Laifinta ba tayi hakuri wajen wata bakwai ba wani labari Tabbas akwai Cutarwa acikin zamansa da ita Dakyar ya samu ya lallasheta bayan ya mata alkawarin zai Binciki kansa Domin ya sama musu mafita da wannan Tunanin ya barta agida ya fito zuwa makaranta ya kasa samun Mafita,ya rasa da wa zai Tattauna wannan matsalan da Farko kamar ya Kira Mallam kunya da nauyi bazai barsa ba yayi Tunanin Baba Sa"idu kuma sai ya fasa Tuna yanzu ba Da bane..In abaya yana yayansa ne yanzu har da karin Surukanta Tunda ya aura masa yarsa ta Cikinsa da Kunya ya Kirasa yana Fadamai bai iya kwanciya da wata mace Abokiyar zaman yarsa duk da yasan Waye Baba Sa"idu auran Amina bazai taba Chanza Tsakaninsu ba Sai dai shi din ne Bazai iya ba yana jin nauyi,Hajiya kuma ba wannan Sakewar Tsakaninsu,koda ma akwai ita uwa ce bazai taba iya fadamata wannan mganar ba Aliyu ne ya fadomai arai aboki kuma Amini garesa da shi kadai ne ya kamata ya Tattauna wannan matsalan dashi.
Shawaran kiran Aliyu ya Zauna aransa bai Tsaya ba ya tashi Zaune Dakyau ya Fiddo wayarsa cikin Aljihun Wandon Pakistan din Dake jikinsa kafin ya kira lambar Aliyu layin Amina ya kara kira wanda Jafar ya Turo masa ammh kamar kullum ana Kara fadamai wayar tana kashe ne. damuwarsa ba Daya bace har da Damuwar rashin jin Aminaa har Jafar ya sake kira a jiyan yana kara tambayansa ko ya kaima Hajiya wayar..?
Jafar ya kara Tabbatar mai da wlh ya kaima Hajiya wayar ta kuma Ta tabbatar mai? zata bama Amina wayar sai dai baisan meyasa har yanzu bata bata ba ammh zai je ya mata mgana sai Danmallam din ya hanasa yace zai kirata da kansa shi kanshi Jafar yayi mamakin yadda Danmallan din ya Damu da sai an bama Amina waya wannan yarinyar da baisan yaushe zatayi Hankali ba ko Shekaranjiya ya ganta sun dawo islamiya suna tafe ita su Hamida sai Mgana take cikin ihu Suna bakin masallaci kofar gidan Baba mallam har sai da Nasir ya kada baki yace Amina in aure bai gyara ba to bazata taba yin hankali ba shima ya yarda da mganarsa..!

Bai kira Aliyu ba kamar yadda ya kudira daga farko sai ya maida akalan kiran nasa ga Hajiya, mallam sun yi mgana dashi da Safe agogon Dake kafe a afishin nashi yabi da kallo yaga karfe 12 da wani abu na rana yana Tunanin achan Nageria yanzu Tara ne da wani abu na Safe.
Wayar Hajiya ta shiga gabda zata katse ta Daga kiran cikin Sallamarta ya amsa mata Cikin Ladabinsa kafin ya Fara gaisheta ta amsa tana Fadin"Lafiya lau Danmallan ya madinar da wajen aikin ka..?
Ina Saratu ina Fatan tana lafiya..?
Kansa na kasa kamar yana gabanta yace"Duk muna Lafiya Hajiya..aiki kuma alhamudulillah cikin Nasara da addu"arku..!
Hajiya tace"Masha Allah Allah ya taimaka..Allah ya kare ka Dammallam ya baka Zuru"a Dayyaba..yadda kake mana Biyayyah Allah ya jikan ka ya baka mai jin kanka kaima..!
Addu"a hajiya yasa yaji kamar yayi kwallah kaunar Mahaifiyar tasa na kara shiga ransa.
Cikin muryan sa mai cike da Zati da Haiba yake amsa mata da Ameem Ameen.
Mallam da mutanen gidan ya tambaya tace duk suna Lafiya kafin yace"Hajiya yau she ne tafiyarki maiduguri.?
Hajiya tace"Satin na sama ne zan tafi inaga Ranar Laraba..!
Kai ya jinjina kafin yace"Allah ya kaimu zan turo ma Jafar sako..Ki kaima Goggo ta kara Allah ya bada zaman lafiya..!
Hajiya cikin Farinciki tace"Angode Allah ya kara Wadata Allah ya Dafa maka..!
Ya amsa mata da Ameen kafin su yi shuru na wani Lokaci jin shurunsa yasa sai ta Fahimci yana so yayi mgana ne.
Cikin Dattakonta tace"Danmallam me kake so kace ne..?
Ya sosa kansa kamar tana gabansa kafin yace"Hajiya jafar yace ya kawo miki waya ko..?
Hajiya tayi yar Dariya kafin tace"Eh wlh ya kawomin tun kwanaki na Shafa"a ne ban bama Aminar ba..Dayake bata zama Da sun Dawo makaranta abinci kadai suke ciki sai su tafi islamiya da sun dawo kuma nake sawa akaita gida ni kuma Shaf na manta..Ammh bari in ta Dawo yau zan bata insha Allahu..!
Kansa na kasa kamar yana gabanta yace"To nagode Hajiya Allah ya kara girma..!
Ta amsa da Ameen Daga haka sukayi sallama Hajiya ta zauna gefen gadonta Tana kara nazarin meyasa Danmallam ya Damu da Amina ta rike waya Daga baya alhalin ita ta kawo Shawaran siyan waya Daga baya da suka Tattauna da mallam sai ya nuna mata illar hakan saboda Har yanzu Amina yarinya ce sannan Karatu ne agabanta,in ta rike waya yanzu zai Shagaltar da ita daga karatunta in Saboda su rika mgana da Mijinta ne ga wayarsa ko ta Hajiya duk wacce shi Umarun ya kira zai yi mgana da Amina shiyasa bata maida kanta kan bama Amina wayar ba ko ayanzu ma Datace mai zata bata tadai cemai ne kawai ba domin zata Tsallake Shawarar da mallam ya bada ba.!

Danmallam kuwa suna gama waya da Hajiya sai ga kiran Sakina ya shigo Yana ma kokarin kiran Aliyu ne kamar bazai Dauka ba sai kuma ya Kashe ya Kirata Tuna yau kwana Biyu basu yi mgana ba Shifa har yau Haushinta yake ji kan abunda tayi mai In ya tuna yadda ta kulle ko"ina ta tayi tafiyarta shi abu daya ya Damesa yadda ta tafi ta bar yar Mutane acikin gida in da yunwa ya kamata ko kuma wani abu ya Sameta ai da ya shiga uku wajen Hajiya da mallam kila sai sun kusa mai baki.
Sama sama daman yake da ita in ya kirata shima saboda sauke Hakki da Nauyin Dake kansa ne ba da domin haka ba sai ta kara Raina kanta.

Tana Dauka ko Sallama batayi ba ta Fara fadin"Habibi..!
Rai ya bata kafin yace"Bana fada miki..Ki daina daukan wayata baki min Sallama ba..?
Tuna haka yasa tayi Saurin mai Sallama ya amsa mata yana tambayanta lafiyanta tace"Lafiya lau Habibi ya aiki..?
Yace"Alhamdulillah ya naji kamar kina kwance ne..?
Gyara kwanciya tayi kafin tace"Wlh kuwa ban tashi ba..Tunda nayi sallar asuba na koma barci..!
Cikin mamaki yace"To Haka Aminar ke tafiya makaranta bata yi kari ba kenan..?
Sakina ta bata rai kafin ta tabe baki Tace"Wacece haka..?
Yana jinta sai bai tanka ba Sanin Halinsa yasa tace"Kace min wannan kazamar matarka taka..Ohon mata Daman na Fada maka bazan dinga mata Bauta ba, ba zamanta nake yi ba..!
Sai kuma yaji bai ji Dadin sunan Data kira Amina ba Duk da shine silar saka mata sunan sai yaji bai Dace ba Domin karshen kazanta kenan ya Ratsa Amina ahakanta,aiko kazanta ya kare.
Tattare naman goshinsa yayi bai yi mgana ba yana kokarin Daidaita yanayinsa Sakina ta cigaba da Fadin"Da Safe ake zuwa Daukanta makaranta ni bana ma sanin Tafiyarta..Sannan bata Dawowa sai yammah ranar jumma kuwa in tatafi makaranta da saafe sai Lahadi da yammah take dawowa sai mu yi kwanaki bamu hadu ba in ma mun Hadu bata min mgana sai kallon banza Habibi yarinyar nan ta gama Rainani bata da kunya Ranar fa Har Zagin Ubana tayi bayan tafiyarka ba Dadewa..!
Yana jinta bai ce komai ba aransa yasan Amina zata aikata A dan Sanin da yayi mata da labarinta dayaji Sama sama Zata aikata sai dai bai yarda ba Sakinar ce ta fara Zaginta ba yasan ta Sarai Itama Sakinar bata da Hakuri.
Yana jinta tana cigaba da Fadamai Rashin mutumcin Amina shidai bai ce komai ba illah"Kiyi hakuri zan kirata zan mata fada..!
Sakina tace"To tana da waya ne..?
Kai Tsaye yace mata"A"a chan gida zan kira abata na mata fada..!
Sakina taji Dadi yasa ta gyara kwanciya tana kara shigewa Cikin blamket tace"Habibi yaushe zaka zo ka Daukeni..?
Ni in bazaka zo ba sai Su Jafar su Nemin Visa na taho..!
Yana jin mganarta yamata shuru Sai da ta fara magiya tana Fadin"Don Allah Habibi kayi Hakuri na tuba nabi Allah na bika..Wlh Daga yau bazan kara saba Umarninka ba..!
Ta karishe Fada Cikin kukan Shagwaba Saboda ko jiya sun yi mgana da Anty ta tabbatar mata da cewa mallam ya sanar da ita Umar zai zo ya Dauketa Dolensa..!
Shiyasa ta tadamai da mganar ita a Tunaninta komai ya zama yadda suke Fata abunda basu sani ba ba kowani Lokaci Allah ke basu nasara ba akwai lokacin da aikin da suke da yakini a kansa zai basu mamaki..!

Sai da ya gama jinta sannan yayi gyaran Murya yana fadin"Sakina na Fada miki abaya zan kuma kara Fadamiki a yanzu..in har ni mijinki ne mai baki Umarni ki bi to bazaki Dawo madina yanzu ba..Sai nan gaba in kin gaji da zaman gumel din..!
Sakina jikinta ya fara rawa? gabanta na Fadi ta ce"Habi..!
Bata karisa ba ya katseta da Fadin"A wanchan Lokacin sai da nace kada ki zo..Kika jin mganata kikace sai kin zo..Biki nawa ake yi baki san zaki je ba Zan ce miki ki shirya mu taho..?
Abaya bake kika bani Shawaran Dauko ki na kawo ki garin nan ba Ni nayi Ra"ayin haka,kamar ni nace ki Hakura da zuwa Bikin su Abida Tunda ba an gama sha"anin bane akwai wasu masu zuwa kika jin mganata kika kuma Zuga Sarood itama ta Tada min rigima Duk Saboda nace ki Zauna bani da kudi sosai sai wani lokacin..!
Sakina ta kwaso Rantsuwa bai bata Dama ba ya cigaba da Fadin"Ita mahaifinta ya Dakatar da ita bata Biyoni ba..Ke kuma kika Biyo ni kikazo to kuma Miye na jin Zafi Domin nace sai nan da wani Lokaci zaki koma..?
Ai kina son zaman nan din ne shiyasa nayi miki abunda kike so..Wlh itama Data sake ta Biyoni Dukkan nan zan barku nayi Tahowata lokacin da na Sanu Dama da Hali sai nazo na Taho Daku a kallah dai nayi muku abunda kuke so kada kuce nayi miki rashin Daidai..
Kinsan Wlh rantsuwa ce ko..?
Sakina sai in na Samu Lokacin nazo sai mu koma Tare in kuma kika ce zaki Biyoni bansani ba to ba da Izinina ba..!
Daga haka ko cewarta bai jira ba ya Katse kiran yana Faman kokuwa da Bacin ransa Sakina kuwa kamar tayi Hauka haka ta mike tana Laluban wayar Anty sai dai bata Sameta ba Kasa Zama tayi ta mike tana Safa da marwa acikin Dakin tasan Waye Umar kaifi Daya ne in yayi mgana baya Sauyata ammh sai da ts saki jiki da Anty da ta tabbatar mata da cewa zai zo su koma Tare,sai dai wannan Jadadda mganar tasa yasa ta kara Sarewa a baya ma acikin ranta har ta Tsara in bai zo ba zata yi Visa da kudinta ta bisa sai dai ya ganta ai tasan Hanya ba inda bazata kai kanta ba A madina ba.!
Sai gashi furucinsa ya sa wannan Tunanin ya bace mata tasan kuma tunda yace bada yawunsa ba in ta Sake ta taka wani abun ne kuma zai Faru na Dabam wanda bata Fata wayar Anty Amarya tayi ta Kira kamar zatayi hauka bata Sameta ba

Shi kuwa yana katse kiranta ya Kira Aliyu saboda yanayin Yan"uwansa duk suna Nageria ne yasa yake saka Kudi mai yawa saboda yafi Sauki shi ya Kirasu da su Dagachan su kirasa.
Kiran farko Aliyu Dake wajen aiki shima acikin Office dinsa ya Daga kiran yana Fadin"Ango..Kaga angon Amina Larabawan Madinatul munawwara..!
Umar yayi Dariya kafin yace"Taka Sallamar kuma kenan..?
To Allah ya shirya Sallamu Alaikum..!
Aliyu na Dariya yace"Wa"alaikas salam Shehi mun tashi lafiya..?
Daganan suka gaisa kamar yadda suka saba kafin Umar yace"naji hayaniya kana wajen aiki ne hala..?
Aliyu yace"Eh wlh tun Safe ma.!
Umar yace"Daman mgana nake so mu yi..!
Tana da muhimmanci sosai..!
Aliyu yace"To ina jinka ai ina Office dina ne.!
Umar ya gyara zama kafin yace"Matsalace dani na rasa wa zan Tunkara shiyasa na zabi na Fadamaka..!
Nan ya fadamai Halin da suke ciki shi da Sarood.
Aliyu ya Saki baki ya Rufe sau ba Adadi bai sani ba kafin yace"Bangane ba ita Sakinar kuma Lafiya kalau kake in ka Rabeta..?
Umar yace mai eh Aliyu yace"To Amina fa ka jarabata ka gani..?
Sai ya kasa mai mgana sai da yaji Shuru sannan Aliyu yace"Common Mutumina Saboda mu gano matsalan ne yasa kaji ina Tambayanka..!
Sai da ya Runtse kafin yace"Itama Lafiya kalau..!
Aliyu yayi ajiyar rai kafin yace"Umar kune malamai ya"yan malamai adan Sanina da ilimina na hasaso wani abu..!
Umar yace"Me ka Hasaso..?
Aliyu yace"Al"amarin ka kamar Sihiri kamar kuma shafan Aljanun mutanen Boye..!
Umar yayi shuru yana wani Tunani kafin yace"Sihiri kuma..?
A"a sai dai in Shafar aljanun in na rabeni bazan musa ba..ammh ni kam wazaimin Sihiri ni bani da abokin Fada kai Sheda ne Aliyu..!
Aliyu yace"Hakane sai dai shi Rayuwa bata ga haka..Kana zaman zamanka baka Damu da kowa ba wani na chan yana Bakinciki da duk wani Cigabanka..!
Umar yayi ajiyar rai kafin yace"Sai dai shafar Aljanun Aliyu..Bazan musa ba Ammh ina Tunanin ko ta bangaran Sarood ne..?
Ina da yakinin yadda na tsare kaina da addu"a azakar Safe da Rana da Karatun Qur"ani da Ibada aljanu bazasu Shafeni ba insha Allahu..!
Aliyu yace"Duk zai iya yuyuwa hakan din ma.!
Danmallam ya Dafe kansa kafin yace"to menene mafita.?
Aliyu yace"Ni dai a? a shawarata ka Shawarci mallam na Tabbata shi zai san wani abun da bamu hango ba..!
Umar yace"Ina jin kunya fa..!
Aliyu yace"Lalura ce Shehi..Sannan Maallam ba kunya Tsakaninku..!
Umar ya jinjina kai kafin yace"Hakane Shikenan zan yi Tunanin hakan nagani in munyi mgana zan kiraka kaji yadda mukayi Dashi..!
Daganan sukayi sallama bayan Aliyu yace yana jiransa.
Duk yadda Danmallan yaso ya Kira mallam sai yaji ya kasa yafi dai yadda da mganar Aliyu na shafar Aljanun yafi kuma yarda data bangaran Sarood ne ya yanke shawaran in ya koma gida zasu yi magana yasan wasu mganguna anan madina na irin haka da kuma addu"o"in Tsarin Shafar mutanen Boye zai saka ta Jaraba ta gani in abun bai yi ba bai da wata Mafita sai na kiran mallam din.
Aliyu kuma mamaki ya cika sa na wannan lamarin ya fi karkata ga Sihiri ne saboda wani abokin aikinsa da suke Tare anan hakan kusan ya Faru dashi da ya kara aure shi ma Ba wani motsi? tun yana shuru har mgana ta kaima Manya Mahaifiyarsa ce yar gidan malamai nan aka gano Shihiri ne sannan kuma ana Zargin Uwargidansa tayi mishi da aka Mike Tsaye da addu"a da mgungunar karya Sihiri Tuni aka wuce wajen shima yaso Shehi ya yarda da mganar sa ammh sai yaga bai amince ba sai ya bar sa a Inda Tunaninsa ya karkata sai dai yana Fatan In ya kira Mallam din adace.!

********

Bayan sati Daya..!

hajiya bata samu Tafiya Biki ba sai Ranar alhamis idi ya kai su ita da Hajiya uwa datace zata rakata ba wanda yayi mamakin hakan daman in dai sha'ani na Hajiya ne Hj.uwa tana gaba gaba sanin tasu tafi zuwa Daya da Hajiya babba ba kamar su Nasara da Anty Amarya ba kafin su tafin Jafar ya kawo mata 30k in ji Danmallam ta kar ba tana ta godiya ta nuna ma mallam ya saka albarka shima ya bada kudi da kayan abinci suka tafi dashi Kwana Daya idi yayi ya juyo sai sun gama Biki zai Dawo ya Daukesu
Su Amina sun so Hajiya tatafi dasu tace su yi Hakuri su zauna Saboda makaranta sannan kwana Daya Tsakani Ranar jumma"a Mamanmu ta tafi Gusai Biki Amina da Hamida da Hanne sun so su bita Tunda Hajiya bata tafi dasu ba ammh itama tace su Zauna Saboda makaranta Daman Amina ta ma mallamm gana ya basu Hakuri yace su bari wani Lokacin saboda karatunsu,Dole suka Hakura ammh Tundaga Ranar ganin Hajiya bata nan Amina ta share Kafa Tayi zamanta Daganan suke zuwa makaranta da Aba yayi mgana Mallam yace ya kyaleta watarana ba sai an mata mgana ba zata san muhimmancin gidan auranta har yanzu Amina yarinya ce.
Amina kuma Harkan gabanta take yi kamar ba matar aure ba in ba gidan ta koma ba mantawa take yi da wani aure ballatana Danmallan ko Sakina Abu Dayane bata manta dashi ba Har yau shine Abunda ya Faru Tsakaninsu Ko barci ta kwanta sai ta Tuna abun kunya take ji da nauyi in ta Tuna abunda ya Faru Ranar yau itace kan gado ita da Danmallam har wani babban lamari ya faru Tsakaninsu sannan bazata manta da yadda yagama gane mata jiki bakincikinta Daya yan nonuwamta Daya gama gani Tasan ya gama rainata Haushi take ji nata sunki girma ga Hamida Da Hanne har Hajiya ta siya musu Braziya ita kuma sai vest saboda ba su da wani girma sosai in ta tuna Haka sai ta Tura baki tana kunkuni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login