Showing 225001 words to 228000 words out of 265571 words

Chapter 76 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28946

bai kamata su mutu ba..?
Mutane nawa suka gama wahalan karatu su mutu basu ci moriyarsa ba..?
Meyasa su bamu ce bai kamata su mutu ba..?
Mataa nawa suka rasa rayuwansu wajen Haihuwa suka mutu suka bar Abunda suka Haifa meyasa bamu ce bai kamata su mutu ba..?
To ku Sani Mutuwa gaskiya ne..Duk wanda kuka ga ya mutu iya Lokacin sa ne..Sannan bakomai bawa yake samu yadda yake so ba..Yana Tafiya ne kan Tsarin da Ubangiji ya Tsara masa..!
Labarin TA FITA ZAKKA reality ne ba Kamar sauran Labaran da kuke Tunani bane.._








*Janafty*
*TFZB2025*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*


Su Mamanmu na tsakar gida suna ta Hidima akazo da labarin Hajiya tace suzo ga Amina ta dawo Mamanmu sai taji kamar bataji da kyau ba badai Amina ba,in ma Aminar ne bata taba Tunanin ganin abunda zataje ta gani ba Saboda mai Fadar bata Fadi cewa Amina da tsohon ciki ta dawo ba.
Ana fadin ga Amina ta dawo kowa da kowa ya zura Hijabi har da goggo Husai da su ya Jawahir domin sun yi kewar yar kanwar tasu tarr da mutanen Gusai,har da matan su ya jafar dake gidan tunda chan gidan su Abida suka bar ma gidan su suna nan ana ta aiki dasu.
Mamanmu ko Hijabi bata tsaya sawa ba,Zanin goyon Zulfa ne Dake kan igiya ta Rataya sai gidan Baba mallam itace kan gaba so take taga da gasken Aminar ne..?
Domin har alokacin gabanta bai Fadi ba bata sare ba ballatana ranta ya kawo mata yau ranar Tonon asiri ce.
Sai dai me suna shiga falon sai kallo ya koma kansu Mamanmu bata lura da ko su Anty Amarya ba ballatana Uban kayan lefem Dake zube a falon Hajiya Burinta kawai taga Amina domin ta gasgasta abunda aka Fadamata yasa tana shigowa ta Daga Murya tana Fadin"Ina Aminar da akace ta Dawo..?
Amina..!
Ta fada da dan karfi domin ita a zatonta karye ne ba wata Amina,Sai dai ga mamakinta wata ta gani kamar Amina ta mike tsaye Dakyar har Yakaka na Taimakamata ta mike Sai ga Cikinta ya bayyana Cikin Ido tana kallon Mamanmu cikin wani yanayin Da ta kasa Fassarashi tace"Ga ni nan Mamanmu..!
Tafada da wani Sauti na Rauni Sai taji bata ji kunyar cikin dake jikinta ba Ko Hannunta bata saka ta kare kamar yadda ta saba ba so take taga yadda Mamanmu zatayi in ta ganta da Ciki.
Aikuwa Mamanmu ido ta Zaro Jikinta ba inda baya rawa ido ta murza ta kara Murza,kamar yadda su Ya Jalela suka saki Baki suna kallon Amina sun ma kasa mgana.
Goggo Husai ce Cikin mamaki tace"Amina..!
Tafada tana takawa gabanta Amina sai taji kunya kanta na kasa tace"Ina yini goggo..!
Sai goggo Husai ta rike baki ta kara Leka Fuskar Amina kafin ta kalli Cikin jikinta ta rike Haba tace"Ikon Allah Zainabu duk yaushe haka ta faru ba Labari ina tunanin ko Sa'idu bai Tabamin zencen Amina ba Domin da Jadwa ta fadamin bata a gida dana masa mgana yace min kinsan inda take bai taba Fadamin Halin da yarinyar nan take ciki ba..!
Hajiya na Tsaye ta murmusa Kafin tace"Ai ko shi Sa"idun bai sani ba..Dagani sai mallan Sai mijinta kadai muka san da wannan cikin Husai..!
Gogggo Husai ta kara jinjina kai kafin tace"To ina tayi renon Cikin..?
Hajiya tace"Abuja..wajen Aisha na kaita..!
Goggo Husai sai ta samu waje ta Zauna tana Fadin"Ikon Allah..!
Saboda abun ya bata mamaki ne dayasa kalamanta suka kare,Mamanmu kuma kamar suman Tsaye tayi daga inda take ko motsi ta kasa kamar yadda Anty Amarya da Haj.Uwani suke Dansare a tsaye sun rasa ma wani Tunani zasu yi duk yaushe hakan ta faru..!?
Su ya Jawahir kuwa karisawa gaban Amina sukayi suna kiran sunanta sai ta amsa tana gaishesu har da su ya Zulfa ya Zahra suna ta kallon Amina mamaki yasa sun ma kasa mgana ya Zulaihat ne sai da ta Rumgume Amina tana fadin"Allah Sarki Aminene..Aminene ta kusa zama uwa. !
Amina batace komai ba kanta na kasa,nan da nan falon ya kwace me da Hayaniyar mata yan gusai suma suna ta Tofa albarkacin Bakinsu,yan"uwan Amina kallonta kawai suke yi kamar wata Hallita ya Jadwa Mirmishi take yi a kasan ranta Lokaci Daya Hawaye suka kawo idonta afili ta Furta"Yau ina Yaya take..?
naso tana raye taga yadda Amina ta koma..Yau Amina ce da Cikin Haihuwa Sannan uwa uba Amina tayi hankali ba mgana ba fada ba tsiwa ba kunkuni madallah da uwa irin Hajiya madallah da Uba irin Baba mallam..Sannan madallah da Gwarzom Miji irin Yaya Danmallan..!
Ya Jaleela ta share kwallah ta rike Amina tana fadin"Amina naji Dadin ganinki haka naji Dadi..!
Kawai sai ta Fashe da kuka itama Aminar daman kiris take jira sai kuka Yakaka ta riketa ta koma ta zauna tana Fadin"ku daina sakata kuka tana da Lalura sannan kusanta akwai Daman arhan kuka..!
Kamar an ce ta kara ne haka Amina ke kuka su Jaleela ma suna Tayata su suna kukan yadda Allah ya inganta Rayuwar Amina ne da kuma kukan Rashin Uwa garesu ita kuma Amina Wani Daci ne acikin ranta in ta Dago tana ganin Mamanmu a gabanta.
Mamanmu kwata kwata kamar kunnuwanta sun Dode haka taji Hajiya na lura da ita tayi Mirmishi acikin Ranta kafin ta karisa gabanta ta Dafa Kafadarta kamar wacce Shooking ya taba haka ta Zabura sai kuma taga Hajiya Daga ganin yadda tayi Firgai Firgai sai ta baka mamaki Hajiya tace"Balaraba ki karisa mana ki gaisa da yar naki..Sannan ga kayan Lefenta nan nace baza"a bude ba sai k???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?in zo ke da sauran yan"uwanta..!
Mamanmu sai taji kamar Bakinta yayi Nauyi ta kasa mgana Hajiya taja Hannunta har gaban Amina sannan ta Saketa Mamanmu kafafunta ne suka kasa Daukanta ganin wani irin kallo da Amina ke Binta dashi da shigargun Idanuwanta kawai sai ta Zube agaban Amina ta saka kuka sai kallo ya koma kanta Kuka take yi sosai tana rike da Hannun Amina Fadi take yi"Amina yanzu Ciki kike dashi bansani ba..?
Nice fa Mamanki Amina duk duniya ko kowa baisan Halin da kike Ciki ba Ni bai kamata na Sani ba..?
Tafada Cikin Karaji da nuna yadda abun ya Dameta Goggo Husai ce tayi mgana tana Fadin"Ke Balaraba to wa ya sani..!?
Kina ji ai ko Sa"idu bai sani ba..!
Mamanmu sai ta rumgume Amina ta na kuka Fadi take"Amina waya yi miki Ciki..?
Cikin waye ajikin ki..?
Mganar ta fito ne kamar ma bata san Sadda ta fito ba sai kallo ya koma kanta Cikin mamakin kalamanta Haj.Nasara ce ta kalleta tana Fadin"Ke kam Balaraba da wata mgana kike yi Amina ai kinsan tana da miji..Cikin jikinta kuma ai Jikan mallam da Hajiya ne..!
Mamanmu sai ta Dago gabadaya ta Rude idanuwanta ta fara wurgawa Cikin Falon karaf suka hada ido da Anty Amarya Dake tsaye gefenta Sakina ce da Sadiya sai Aliya sai wasu Dangin su Daga Dutse.
Kallon kallon sukayi ma juna,kallon da basu taba yima juna ba Mamanmu ta kara tsurewa cikin wani yanayi ta kauda kanta kafin ta kalli Haj Nasara tana Fadin"Ba...Ba sun rabu ba. ?
Sai kowa ya Zaro ido yana kallonta Mamanmu sai ta rude ta fara inda inda Tana fadin"A"a na dauka da Hajiya ta Dauketa anan ne..Auren ne ya lalace..!
Sai kuma ta kara saka kuka tana Fadin"Amina kece kika koma Haka..?
Allah Sarkin kyauta da kari..!
Sai kuma ta kara rike Amina wacce in ta riketa kamar wani abun kyama ya Tabata yadda ta Tsani mutuwarta haka ta Tsani ganin Mamanmu shiyasa sai binta da kallon mamaki take yi kamar yadda Hajiya ke gefe tana yi Lokaci Daya tana Sakin mirmishi.
Kafin wani yayi mgana su Hanne sun shigo da Ihu suna fadin ina Aminar take..?
Amina na jin muryan su Hanne ta Bangaje mamanmu ta mike Cikin Fara"a da Tsantsan murna bakinta kamar zai Tsage tace"Gani nan Hanne..Hamida..!
Sai kuma Hawaye Hanne ne kan gaba sai Hamida sai su ya Abida dasu Sa"adatu idon su ya rufe ko Mutanen Falon basu tsaya kallo ba ballatana Cikin jikin Amina suna ganinta Hanne ce ta fara Buga Tsalle ta fada mata Sai Hamida da Zafira wacce dazu tazo Suna murnan ganinta.
Kadan ya rage su kadata Yakaka da Hajiya har suna Hada Baki wajen fadin"Ku kula fa..Tana da Lalura..!
Sai Sannan sukaji wani abu mai Tauri ya Tokaresu suka Dagota suna Binta Da kallo Daga sama har kasa,cikin mamaki da Budewar Baki Hanne ta kalli Hamida itama ta kalleta suka kalli Amina Dake sharan kwallah tana kallonsu cikin Annuri fadi take"Nayi kewarku..Nayi kuka nayi kukan kewarku kamar ba gobe..!
Tafada tana dora kanta saman kafadan Hanne Lokaci Daya tana rike hannuwan Hamida Zafira dake gefe Ta leka Amina tana fadin"Amina..?
Amina ta kalleta tana yar Dariya tace"Na"am zafira..Zafira..!.
Tafada Cikin dariya da Hawaye zafira ta jingina da kafadan Amina tana Fadin"Itace.Wlh Amina ce..!
Tafada tana Dariya,Amina ta rikesu kamar ta samu salama bakinta yaki Rufuwa Hanne ta Taba Cikin Amina tana kallon Hamida kafin tace"Hamida Wlh Ciki ne ajikin Amina..!
Taba kiji..!
Hamida itama ta taba Cikin kafin ta kalli Hanne tana fadin"Ciki ne..Amina Zaki Haihu ne..?
Sai Amina ta kasa mgana ta Buge hannunsu tana fadin"Bansani ba..!
Tana hararansu Lokaci Daya kawai sai suka Bushe da Dariya ga hawaye na Binsu suka hada Baki wajen fadin"Wlh Aminene ce..!
Suka koma suka rumgume juna gabadayansu suna Hawaye suna Dariya kowa afalon sai da yaji kamar yayi musu kuka ya Abida ce da ya Zeenatu suka matso kusa ya Abida ta Dafa su Hanne tana Fadin"Dillah ku matsa ai Aminar bataku ce ku kadai ba..Har damu..!
Suka saki Amina suna Dariya Amina ta Daga baki Cikin Murna tace"Ya Abida..!
Tafada Cikin murna kawai sai tace"Na"am Aminene..!
Sai suka rumgume juna suna mai Farinciki haka ma da ya Zeenatu ta Shafa kumatun Amina tana fadin"Allah mai iko Amina ba Fada ba tsiwa..Agaida ya Danmallam..!
Amina ta sunne kai tana Dariya Goggo Husai tace"Ai rabon dake tsakanin su ne yasa auran yazo Cikin gaggawa..Allah ya Rubuta wannan Rabon ajikin Amina yake..!
Mamata mahaifiyar Zafira tace"Kwarai Rabo ai bai bar komai ba..!
Yakaka ta amsa da cewa"Ai yana ma kisa..In aka hanasa bayyana sai ya kashe rai..!
Hajiya na gefe tana ankare da motsin kowa tana dan Mirmishi sai alokacin tayi gyaran murya tana fadin"Ku Dakata da wannan murnan ga lefen Amina nan da kayan Haihuwarta..Sannan akwai gidanta da Mijinta ya siyamata an zuba komai aciki Yana Babura Road zuwa gobe in an watse taron Amare sun mika za"a raka Amina Gidanta nan zata Haihu tayi Jegonta kafin tayi Arba"in Mijinta ya Dauketa su koma inda yake aiki..!
Hajiya Nasara ta zabga Kabbara ita dasu ya Abida,Ya Aisha na Dariya jin Yakaka na fadin"Kwarai Hajiya. kafata kafar Takwarata sai garin ma"aiki..!
Hajiya nasara ce ta fara Bude kayan su ya Jalela na Tayata su hanne na kamkame da Amina suna zaune suma suna kallon abunda ke faruwa Lokaci Bayan Lokaci suma bin Amina da kallon mamaki ita kuma sai ta Hararesu tace"magulmatan Amare kawai..!
In tace haka dadi suke ji Aminar su bata tafi ba ta dawo wannan ranar ta Farinciki ne.
Akwatuna Bakwai na lefe Biyu na kayam Haihuwa gabadayansu aka Bude su a Tsakar Falon Hajiya su Anty Amarya na inda suke sun kasa motsi ballatana Mamanmu da tunda ta Jabe ta kasa tashi Haj.Uwani na daga Bakin kofa rike da Fashasshiyar wayarta ta kasa gaba ballatana baya.
Hajiya ta kallesu tana Fadin"Amarya..Uwani ku kariso mana..Sakina ku kariso mana..!
Tafada tana kallonsu Daya bayan Daya Har Sa"adatu data koma barayin Uwarta tana kallon ikon Allah kamar kazar da bata da maiko haka suka tako Har wajen kayan suna Tsaye ana ta Daga kayan arziki su Mamata ne gaba gaba da wata abokiyar wasan Aba ana Dagawa su ya Abida na kirga kayan.
Sai da aka Kirga manya atamfofi Talatin da Biyar lesuna Takwas Materil Biyar,Shadda Hudu,Abaya shida,Ya Abida ta Daddage ta Rankwada guda ya Zeenatu na Tayata aka fara Daukan sauran Innes da kayan kwalliiya kayan arziki sai wanda ya gani aka gama aka zo na kayan Haihuwa akwati guda na Amina ne Tsalalan Atamfofi da lesuna kala goma duk an Dinka sai dayan na Kayan yara ne masu kyau da Tsada sai wanda ya gani.
Mamata ta kalli kayan kafin tace"Wadan ga duk kayan na Fitar suna ne Hajiya..?
Ya Aisha ce tace"Duk na sunana Mamata..Na Amina Daya..sauran kuma na Bbys dinta..!
Mamata ta jinjina kai kafin tace"Allahu akbar Diyar Balaraba tayi goshi..!
Goggo Husai ta gyada kai kafin tace"Kaya sun yi kyau masha Allah..Naji Dadi Allah ya sauketa Lafiya..!
Ya Abida ta kara sakin guda Hanne ta mike tana Tayata ita da zafira hamida ce ke Dariya Cikin Daga murya ya Abida ta kara sakin guda Hajiya ta Harareta tana Fadin"Nan gidan bai dace da gud'a ba..kabbara ya kamata kiyi..!
Ya Abida ta kara karkacewa ta saki gu'da ya Aisha ta d'aka mata duka abaya tana Fadin"Mara kunya Hajiya na mgana..!
Ya Jawahir itama ta Daga hanci ta saki nata gudan Ita da ya Zulfa sai Ya Zeenatu itama tayi nata ya Abida ta kara Dorawa suka ruda Falon Hajiya Mamata ma ta Dauka goggo Husai sai Dariya take ita da yakaka Hajiya sai Faman Hararansu take yi ba"a kara Saka Dariya ba sai da Hamida ta karkace tayi nata aka kwashe mata da Dariya Har Amina sai da ta Dara Hanne na Dariya tace"Gaskiya ne Amina TA FITA ZAKKA..wannan zakkan gaskiya ne gashi mun gani..ako"ina itace Zakka komai nata na mussaman ne..!
Ya Abida ta amshe da Fadin"Kwarai Wlh..Aminene badai ta mutum ba sai ta Allah..!
Suka kara karkacewa wannan karon har da su ya Zulaihat suna Sakin guda Hajiya kai kawai ta kada tana Mirmishi,Amina na zaune ita da Hamida suna kallonsu suna Dariya.
Da gayya Hanne da ya Abida suke wannan gudar saboda Sakina domin har Bikin nan da suka hadu bata musu mgana ba tun Lokacin auran Amina da Danmallam bata kara musu mgana ba ko sun hadu sai ta kauda kai..shiyasa suke kallonta suna kara Ruda Falon da gud'a Sakina Gabadaya ta Jike da Zufa,Jikinta ba inda baya rawa kanta ya gama Daukan abubuwan datake ji har wani Dum..Dum yake yi kamar ba nata ba Hakama Anty Amarya gadai tanan ne kawai abubuwan sun tsaya mata Cak ta kasa wani Tunani kamar yadda Mamanmu ke jabe suna jin Abun Al"ajabi tare da Tsamanin Abunda basu yi Tsammani ba..!
Duk wannan Budurin da akeyi Sarood na Falon nan sai kallon kowa take yi tana Bin Baki ita ba wani sanin Amina tayi ba shiyasa bata gane komai ba ammh kuma Kayan data gani ta Zata na su Hanne ne da za"ayi ma aure gobe Ita ba Hausa take ji ba,Shiyasa sai bin Bakin Mutane kawai take achan gefe kamar ma bata afalon.
Haj.Uwani ce ta juya kawai ta Fice Daga Falom Idanuwanta sun kad'a sun yi Jajir Dishi Dishi ma take gani Saboda tashin Hankali.
Tana fita saboda yadda ta Rude yasa bata ko nemi Kebewa ba tana fitowa ta Laluba wayarta Allah yasa gefenta Da saura ana gani haka ta saka lambar Batula saboda yanayin Datake Ciki bama zata tsaya neman Lamba ba.
Batula ta kira gabda zata katse ta Dauka Cikin karaji da wani yanayi Haj.Uwa tace"Mun shiga uku mun Lalace Batula..Hajiya ta gama lalatamin Duka shirina..Hajiya ta Ruguzamin Burina da na Dade ina Tanadinsa..!
Dagachan bangaran Cikin Tashin Hankali tace"Innalillahi Uwani me ya faru..?
Haj Uwani tana Sharan gumin Goshinta tace"Komai ma ya faru Batula..Komai ya Lalace..Amina ce ta Dawo da Cikin Umaru ajikinta Batula..Sannan da kayan lefe dana Haihuwa kamar za'a Bude shago sannan ga Makullin gidan daya Siya mata Batula ni fa bama shi ya Dameni ba Batula Amina Tsohon Ciki gareta Haihuwa ko yau ko gobe..!
Batula Cikin tashin Hankali tace"Ciki kuma Uwani..?.
Wai Wata Amina..?
Haj.Uwani na faman kokuwa da yanayinta tace"Batula Amina dai da aka Aurama Umar ita ke da Ciki fa..!
Batula tace"garin yaya..!
Ta yaya hakan zai faru alhalin kince kin tabbata ta sha mganin Mama..?
Haj.Uwani ta Runtse ido sai Hawaye Cikin Rawan murya tace"Bansani ba Batula bansani ba..Hajiya ta shammaceni..Shammatan datamin illah har Abada..!
Batula tace"To yanzu menene mafita..!?
Haj.Uwa ta Share Hawayenta Tana Fadin"Bazan karaya ba..Karaya ba na wa bane Batula..Dole ne nayi Nasara Batula ko ta halin kaka ne..Saboda haka ki Tashi sammako gobe ki koma wajen Mama ki fadamata Halin da ake Ciki..Ina so kada Cikin nan ya fito Duniya..Ina so a kashe koma menene acikinta ta haifesa ba rai kada yazo Duniya da ransa..Naji Samun Cikin kuskure ne sannan Hajiya in tasan wata ai bata san wata ba..Zan nuna mata Ni Uwani Kwalbar Sharri ce ko na Fashe ina da Sauran mamora..!
Batula tace"Gobe goben nan zan yi sammako..Wannan Labarin ya Firgitani ammh Hajiyar nar Allah ya Tsine mata albarka..!
Haj.Uwani Cikin Huci tace"Nayi alkwarin sai na Tarwatsa Farincikin su..Sai na Lalata musu wannan jin Dadin na su..!
Daga haka ta Datse kiran tana Sakin Huci kamar zakayan,Ta juyo a Fusace Kawai sai taci karo da Hajiya Tsaye da waya a Hannunta tana kallon Hajiya uwani Cikin wani yanayi.
Haj Uwani gabanta ya fadi ta Zaro Ido Jiki na rawa tana kallon Hajiya wacce ta Daga mata wayar hannunta ta nuna mata Sai ga sunan MALLAM baro baro alaman kira yana tafiya minti Goma sha Biyar alamun tun fara mganarta da Batula..
Jikinta na rawa Gabanta na Faduwa Zufa na keto mata ta ko"ina kawai sai ta Duka kan gwiwoyinta Domin tagama sanin Hajiya tasan wannan Boyayiyar Fuskar nata.
Cikin Rawan murya ta hada Hannayenta tana Fadin"Dom Allah Hajiya ki Rufamin asiri sharrin Shedan ne..!
Hajiya tayi mirmishin Takaici kafin ta kada kai tace"Ni ban isa na rufa miki? asiri ba Uwani..Asirinki Daman chan a bankade yake..Duk wanda yace Tukuyar wani bazata tafasa ba to nashi ko Dumi bazatayi ba..Ki Fito ki Fallasa kanki Uwani Domin asirinki ya gama Tonuwa kinga wannan wayar..!.To mallam ne akan layi tun Fara mganarki da kanwarki yaji komai ki jira sakamakon ki Uwani..!
Daga haka ta katse wayarta agaban Haj.Uwani Dake zufa ko"ina na jikinta na rawa ta juya ta koma Shashenta Haj.Uwani na Rarrafe tabi bayanta tana kiran sunanta Hajiya Cikin wani yanayi ko waige bata karayi ba.
Tana shigowa Falon nata ta iske su Abida nata shewa sun tasa Amina gaba da? shakiyanci sannan sauran matan kuma suna ta kara Daga kaya.
Anty Amarya ta kallah Dake Tsaye ta kasa gaba ballatana baya Mamammu kawai take kallo Tana auna yadda Balaraba ta raina mata wayau Saboda rashin ta ido ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login