Showing 222001 words to 225000 words out of 265571 words

Chapter 75 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28928

sa na dawo nan..!
Aliya tace"Sannu sai Hakuri..Zuwa gaba zaki ji Dama dama in Laulayin ya ragu..!
Sakina tace"Allah yasa ya hanya..!
Ina Aliyun da hammad..?
Aliya tace"Suna wajen tare da Umar..!
Sakina tace"Yazo kenan..?
Aliya tace"To nadai gansa a waje fa..!
Sakina tace"Rabona da ganinsa tun shekaranjiya da muka zo nan..!
Bai sake nema na ba. !
Ta fada cikin wani yanayi Aliya tace"To kinsan kila saboda mutane..!
Sakina tace"Waya fa..!
Ai sai ya Kirani yaji ya nake duk wannan wahalan da nake sha duk shine Sila fa..!
Aliya tace"Kuma fa hakane..kimai Uzuri dai ammh ai naga kishiyarki dana shiga Shashen Hajiya sai wani washe min Baki take yi nayi kamar ban ganta ba. !
Sakina tayi tsaki tana fadin"Bar munafuka ita wai ta ganki ta ganeki mana..!
Aliya tace"Ta gane Ubanta..!!?
Aiko taga wulakanci domin ko kallo bata isheni ba..!
Sakina tace"ai tunda muka zo bata kara ganina ba..Na yakiceta ajikina..!
Aliya tace"Ai hakan ya kamata ina Wani Cigaba ka hada kai da kishiya..Duk fa Kirkinta sunanta Kishiya..!
Sakina tace"Ai saboda na sami abunda nake so ne..kuma na samu shiyasa na yakiceta Daga jikina..!
Aliya tace"Wlh hakan ma yafi..!
Daganan suka cigaba da Hirarsu suna ta zagin Sarood Aliya ce ta kalli Sakina tana fadin"Wai ina ita Labarin Kazamar yarinyar nan .?
Sakina tace"Wace wai..?
Aliya tace"Amaryanki mana..Waa ma take da suna..?
Amina take ko wa..?
Sakina ta ja wani Dogon Tsaki kafin ta mike tana Fadin"Ina na sani..!
Nifa na manta ma da ita kwatakwata sai da kikayi mganarta..!
Aliya tace"Wato ma kin manta da ita..!
Ni fa ina mamakin ina Hajiya ta kaita..?har Aliyu na Tuntuba yacemim bai sani ba bama suyi mganar da Umar ba. !.
Sakina tace"Ai hashashemu ya tabbata. inaga ba auran nan..!
Aliya ta zaro ido tana fadin"Ta ya akayi kika sani..?
Sakina ta Bude kofar Tiolet tana Fadin"To in da auran da baki ganta ba. ?ai ba haka ake aure ba Aliya.
Bari nayi alwala ban yi sallah ba .!
Aliya ta bita da kallo tana fadin"Nima ki fito nayi muna hanya ta same mu..!
Ammh a kasan ranta tana Tunanin Ta yaya Umar zai saki Amina..?
Hajiya da mallam kuma sun sani basu ce komai ba..? Gaskiya tunanin hakan bai zauna mata ba sai dai in wani abun ne Dabam ammh banda mganar Rabuwa.
Sakina na fitowa itama ta shiga tayi alwala sukayi sallah bayan sun idar Aliya taci abinci suka kimtsa Sakina tace su leka wajen Walima ana ta Tafiya,Koda suka fito duk an watse har Anty Amarya ta tafi da wasu yan"uwansu Daga Dutse Hajiya ce kadai ya rage bata tafi ba sai wasu yan maiduguri,Sakina gaba sukayi ita da Aliya sai a hanya ne suka hadu da su Zulfa da Yara sun dauko musu waina da za"a raba awajen Walimar suka Dumguma zuwa haraban makarantan koda sukaje har an fara Amaren ma sun iso sun yi shigar bakaken jallabiya da Farin Hijabi Sa"adatu ne dai Fuskarta acike ammh Hanne da Hamida sai kwarmin ido,sun yi wani Zuru zuru dasu su ya Aisha ne kan gaba ke ta Hidiman Baki.
Aan basu kyauttuka Hamida an bata na Tajweed da Kira"a am bama Hanne na Larabci da sanin Nahahu sai Sa"adatu ita kuma na zuwa makaranta ba Fashi Hanne sai da tayi kuka sun farota da Amina ammh yau ba ta awajen da zasu yi bankwana da makarantar su haka ma Hamida sai da sukayi kuka,su ya Abida duk sum san kukan da suke yi na rashin Amina ne suma ai sun damu sai dai ba wanda yama Hajiya mgana, ba Tarbiyansu bane yin katsaladan a Hukuncin babba sai dai su hanne sun Fada musu Hajiya tace zata zo insha Allahu.
Su ya Zeenatu aka bari da lallashin su Sai da suka saki ransu,Sannan suka koma Bangaran sallaman Baki su da sauran yan ajinsu na Hadda sannan kawar Hajiya tazo tayi ma Amare nasiha sosai sai shidda na yammah aka tashi Sakina anan suka Hadu da Sarood tana ganinta ta manne mata sai Hararanta suke ita da Aliya ita ko Allah Sarki bata sani ba tana tare dasu da zuciya daya ne,Har Hajiya tazo wajen Walimar chan gabda za"a tashi mamanmu kuma ai suna gaba gaba ita da Anty Amarya sun saka kayan alfarma Anty Amarya Shadda ta saka itama mamanmu shadda ce taji aiki ammh kalan kowa Dabam kafafunsu sun ji Lalle kamar wasu yara har yan gusai nama mamanmu Tsiya ta koma yarinya tace a wajen Sa"idu ai ita yarinya ce Danya sharaf
Sai Dariya take yi cikin Nishadi suma suna tayata da tsiyan da suka saba mata musamman ma abokan wasan Aba Na gusai.
Ana tashi daga wajen walimar aka Dumgumo zuwa gida Amaran dai Gidan su ya jafar suka koma su da ya Zeenatu da Abida sauran kuma sun koma gidan baba mallam wasu kuma gidan Aba Dayake ana ta kiran sallar mangariba suna komawa sai kowa ya fara shirin salla a waje kuma su ya Danmallan sunyi alwala suka Shiga masallaci duk da mallam ya Dawo shi ya bada salla da mangariba suna da Karatu yasa duk suna cikim masallacin suna Sauraran karatun Baba Mallam Har Nazir da shima Gabda mangariba ya sauka Daga Lagos.
Adaidai Lokacin misalin karfe bakwai da yan mintina na Dare Motar Usman Mijin Aisha prado mai lambar Abuja ajikinta ta yi Diran cin Taya a kofar gidan Baba mallam Dake Dauke da Haske Tar domin an kunna Gen da wuri saboda Sha"anin da ake ciki ko"ina Haske ya bayyana sai dai kofar Gidam ba kowa duk suma masallaci Tsit mata kuma duk suna Cikin gida.
Ya Aisha ta fara fitowa bayan Direba ya Bude mta kofar Mota ita agidan gaba ta Zauna yayinda Amina da Yakaka ke gidan baya.
Tana fitowa tace"Salihu bude booth ka Fito da kayan Dake Ciki Duka..!
Ba musu ya amsa mata ya nufi Booth din ya Bude ya fara Fiddo da akwatunan Amina Sabbi yana jerawa a kasa ita kuma Aisha ta Bude bangaran da Yakaka take tana Fadin"Yakaka Bismillah mun iso..!
Yakaka ta Fara fitowa tana Salati Lokaci Daya tana Fadin"Mun isa barka..Tafiya ai yankin azaba ce..!
Lokaci Daya tana kare ma gidan mallan kallo da yanayin anguwam ta Furta"Masha Allah..yau gani agidan mallam..!
Take fada daidai Lokacin da Amina ta Fito Daga Motar kofofin Hancinta na Budewa da Shakkar Iskar gumel din Data Dade bata shaka ba,Gabadaya Sai taji ta kamar ba ita ba,Sai taji kamar bakuwa ce ita tana kallon kofar gidan Mallam da nasu gidan wasu abubuwan da suka shude a baya suna Dawowa mata Daki Daki kamar yanzu komai ke faruwa Sai da taji Hawaye sun kawo mata.
Tana Sanye da Doguwar riga Baka na Saudiya cikin Tsaraban Danmallan ne sai jan hijabin Dake jikinta Tunda adon Rigar ja ne,hijabin gwiwarta kadai ya Rufe Cikinta gashi nan ya bayyana Kafarta sanye Cikin Takalmi mai Saukakken Tudu kafafun sun kara kumbura saboda Zaman mota Fuskarta ta kara Cika tayi kwaba kwaba kamar Danyen Nama.
Duk wanda yasan Amina abaya in ya ganta yanzu da wahala ya ganeta komai nata ya sauya.
Tsaye kawai tayi tana bin gidajen nan guda Biyu data yi Rayuwarta aciki da kallo acikin Ranta tana jin wani Farimcikin da bata taba ji ba Dazu suna Hanya sun yi mgana da Danmallam yace mata dukkansu matan suna wajen Walima har suka iso Bata kara mgana ba taso ta samu Walimar su Hanne ammh Allah bai yi ba.
Tana jin ya Aisha na cema Yakaka bari ta kira waya a daukan musu kaya tunda ba yara a wajen kawai sai ga Ya Shamsu ya fito Daga gida zai shiga masallaci yaga ya Aisha ya tsaya suna gaisawa tana Fadin"Shamsu yaushe ka zo..?
Yace"Dazu da yammh ya Aisha sannun ku da zuwa..!
Ta amsa shi kuma ya juya yana gaida Yakaka ta amsa Cikin Fara"a.
Ya Aisha ke Fadamai kaya ne daman za"a dauka don Allah ko zai taimaka ya kira mata su Akilu su Daukan mata,Yace to bari yayi musu mgana suna Cikin masallaci da Hanzari ya tafi ya kirasu sai alokacin ya Aisha ta Daga kai tana kallon Amina Data jingina jikin mota batace komai ba..
Cikin kulawa tace"Amina kari so mana..Ko jikin ya rike ne zaman mota ko..?
Amina sai alokacin ta tako zuwa wajensu kafin tayi mgana Yakaka ta chabe da Fadin"Dafa gajiya..Ko mu da bamu da komai mun gaji ballatana ita mai Lalura..Jiki fa ya rike sai dai mun shiga ta samu ta watsa ruwa a shafe Jikin da man zafi taji Dama Dama..!
Amina ta tura Baki tana Fadin"Man zafi kuma yakaka..?
Yakaka ta Harareta Tana fadin"Shine zai sakar miki jiki har kiji Dadi wannan kumburin da kikayi duk ya Saki..!
Amina bata samu bakin mgana ba Sai ga Shamsu ya fito bayansa Akilu ne da Zubairu har suka kariso suka gaisa da Ya Aisha da Yakaka basu lura da Amina ba sai da Ya Aisha ta nuna musu Kayan da zasu shigar musu dashi Ciki,Saitin akwatina guda Bakwai sai kuma wani saitin mai Hudu suma Dabam sai kayan su da kuma wasu kaya a kwalaye acikin wani babban Buhu.
Ya Shamsu ne ya fara ganin Amina sai ya Tsaya kawai yana kallonta kamar Amina kamar ba ita ba ita kuma ganin Haka yasa tayi mirmishi tana Fadin"Ina yini ya shamsu..!

Da Sauri ya kara ware ido yana kallonta har su Akilu suma sai alokacin suka ganta da sukaji muryanta ganin ya kasa mgana ne yana kallonta Daga sama har kasa ga Muryan Amina sannan wannan kuma gata babbace ga kuma ciki ajikinta Sai da ya Aisha taga haka sannan tace"Shamsu Amina ce fa ke gaisheka..!
Dukkansu kusan Hada Baki sukayi wajen Fadin"Amina..?
Cikin Sigan Tambaya Yakaka tayi Dariya tana Fadin"Sun ga ta zama uwar mata ga Ciki ga shi ta yi kiba..!
Amina Mirmishi kawai tayi kanta na kasa kunya taji da Yakaka ta ambaci Ciki su kuma kawai ita suke bi da kallo mamaki ya kashesu.
Shamsu har yana cin Tuntube Daya Dauki kaya zai shiga gida yana waige su Akilu ma mamaki duk ya kamasu wai Amina ce ta koma haka..?
Kuma har da Ciki ikon Allah..!
Harda Salisu Direba a masu Daukan kaya da wasu matasa da suka gani zasu shiga masallaci Ya Aisha ta rokesu suka Daukan musu ita sai ta Dauki karamar akwatinta da na Amina yakaka kuma ta Dauki wata babbar Leda Amina bata Dauki komai ba Saboda yanayinta suka bi bayan su Shamsu zuwa Cikin gida har megadi yana masallaci wajen karatun mallam.
Su ya Nazifa da su ya Fatima duk suna Tsakar gida wajem kitchen ana ta Hidima hada Miyan gobe sannan wasu kuma suna ta gyaran kajin da aka kawo daga wajen Gyarasu,Hajiya na Shashenta Hajiya Nasara ne ke Madafin tana nuna ma su lami yadda komai zai tafidaidai sauran matan kuma duk suna Dakunansu kana dai jin Tashin Muryoyinsu suna ta Hira da Shewa.
Sai ga su shamsu na Shigowa da kaya ya Fatima ce ke fadin"Shamsu wannan sabbin akwatin fa Daga ina..?
Ya Shamsu yace"Ya Aisha ce da Amina suka iso yanzu..!
Kusan dukkansu sai da suka maimata sunan Amina cikin mamaki karaf sai a kunnen ya Sadiya tayi Zaraf ta fito Daidai Lokacin da itama Hajiya Uwa ta Fito Daga Shashenta ya Aisha ta Rafka sallama ta shigo bayanta Yakaka sai Amina Dake bayansu tana Tafiya sannu sannu kamar wata bakuwa.
Tana baya ba wanda ya Lura da ita su ya Aisha ake ma maraba Jidda ke ta Fadin"Maraba da mutanen Abuja..Ai muna ta jajenki mukace Aisha shuru kowa ya iso ban da ke..!
Ya Aisha ke amsa musu cikin Fara"a Tana Fadin"Wlh kuwa muna hanya Tsaiko muka dan samu..!
Salihu Direba ke tambayanta ina za"a kai kayan da sauran matasa ta nuna musu bangaran Hajiya.
Aisha ke nuna musu yakaka a matsayin Kakar Mijinta suna gaisawa Sai Ya Aisha ta juya ta ga Amina abaya tana tsaye kamar bakuwa Cikin Fara"a tace"Miye haka Amina kina ta Nokewa kamar wata bakuwa..!
Sai kallo ya koma inda aka ji an kira sunan Amina Lokaci Daya da Anty Aisha ta jawo Hannun Amina gaban mutanen Dake zaune awajen
Gabadaya ido suka saki da Hanci suna kallon Amina ita kuma kunya cikin jikinta yasa ta Sadda kanta kasa tana wasa da Gefen Hijabinta.
Hajiya Nasara ta Daga Baki Cikin mamaki tana fadin"Amina ce haka..?
Allah mai iko..!
Karaf a kunnen mutane Dadama har da Hajiya Dake shirin fitowa Tunda taga su shamsu sun shigo da kayan tasan Aisha da Amina sun iso.
Anty Amarya kuma kamar a mafarki taji Hajiya Nasara na ambaton Amina shi ya fito da ita waje..
Dukkansu kusan atare suka ga Amina Ganin daya razanasu ranazar da basu Taba Zato ko Tsammani ba
Hajiya uwa wayar hannunta sai da ta Subuce ta fadi saboda razana Anty Amarya kuma gani tayi kamar ba Daidai take gani ba sai da ta kara Murza idonta sannan ta kalli Amina ta kara kallon Sadiya Dake gefenta Cikin Rudi tace"Sadiya...wai..wai wa nake gani achan kamar Amina..?
Sadiya Cikin mamaki tace"Amina ce Anty..Wlh Amina ce da Tsoho ciki!
Sai anty Amarya taji kafafunta sun kasa Daukanta tana neman faduwa ba Domin Sadiya ba da wani Labarin ake yi ba wannan ba.
Hajiya kuwa Mirmishi a saman Fuskarta ta kariso tana musu maraba da zuwa Fadi take"Yau ga Yakaka ta Rako Takwaranta..!
Yakaka Cikin Fara"a tace"Wlh Hajiya ai nina nan sai takwara ta haihu mun yi wankan jegon mu na yan maiduguri daganan ai har chan garin ma'aiki Hajiya..!
Tafada Cikin Fara"a Hajiya tace"Kafarki kafar Amina Yakaka da yardan Allah har garin madina..!
YaKaka tace"Insha Allahu..!
Hajiya ta kalli Aisha tana fadin"Ku shiga Ciki Aisha..MAMAH..barka Dawowa..!
Tafada tana riko Amina wacce ta Fada Jikin Hajiya sai kuka Hajiya na Dariyan Farimciki tace"Miye na kuka mamah..!
Baga kin Dawo ba Ai Daga yau Zaman Abuja ya kare miki Daganan Sai Gidan Mijinki da yardan Allah achan zaki haihu.!
Tafada cikin Fara"a tana kallon Hajiya uwani Data ke Tsaye bata ko motsi da Anty Amarya da Sadiya ke tallafe da ita Hajiya nasara ce ta kariso tana Fadin"Hajiya Wai kina nufin Cikin jikin Amina na Danmallan ne..?
Hajiya tace"Kwarai ma da gaske..Ai Cikin Amina Allah ya Killacesa..Dalilinsa Daya sa na kaita wajen Aisha ta zauna kinsan kana Zaune ne da mutane bakasam magautanka ba sai anemi a salwartar da Cikin..Kinga wadanchan akwatunan kayan Lefen Amina ne da kayan Haihuwarta sannam Da dankareren gidanta da Danmallam ya siya mata Chan zata tare ta Haihu achan kafin ta gama wanka ya Dauki matarsa su wuce Madina..!
Yakaka tace"Da yardan Allah kuwa..takwarata sai madina tayi kira..!
Hajiya Nasara ta rangada guda tayi juyi kafin tace"Allahu akbar..Lalle Allah ne mai Hikima ashe Rabo ne tsakaninsa da Amina auran nan yazo kowa bai Zata ba..?
Amina..Amina ta zama uwar mata Allah ya raba Lafiya..!
Su ya Fatima ma sai Guda suke suna Shewa wanda ya fito da su Sakina Dake daki dasu Aliya dasu Jidda Daidai Lokacin da Hajiya ta riko Amina tana tafiya da kyar Saboda Cikinta.
Karaf kuma suka Hada ido Hudu da Sakina kallo kallon sukama juna da Amina Sakina da sai da Cikinta ya juya mata Jikinta na rawa ta kalli Anty Amarya dake Cikin wani yanayi da ganin Amina da kuma kalaman Hajiya,bata iya ma kallonta ba Tana Faman kokuwa da yanayinta Sakina ta kara Bin Amina da kallo har suka shige shashen Hajiya Sakina ta Kalli Su Sadiya tana fadin"Wa nake gani kamar Amima..Amina da ciki..?
Kafin su bata amsa Hajiya Nasara ta sake rangada guda tana Fadin"Kai wannan abun yamim Dadi..Amina Zata Haifa ma mallam jika..Amina ai Yar gaban goshim mallam ce kamar yadda Danmallam yake dan gaban goshinsa wannan jika zai zama Dan gata gaba da baya..!
Ta tafada tana Dariya kafin ta kalli su ya Fatima tana fadin" ku kuma zaman me kuke yi..?.
Ku tashi muje mu ga kayan arziki in ji Hajiya..!.
su ya Fatima na jin haka suka mike suka bayan Haj.Nasara zuwa Shashen Hajiya babba Hajiya Nasara kamar da gayyar take yi duk da bata san komai ba tasan Anty Amarya da Sakina bazasu so haka ba.
Hajiya Uwani Data kame a tsaye ga wayarta Data fashe a kasa suka Hada ido da Anty Amarya suna kallon juna.
Kowannensu yana Fama da Faduwar gaba suna faman kokuwa da abunda yake shirin faruwa dasu.
Awannan Lokacin kowa ta kansa kawai yake yi,Kamar Daga Sama sai ga Hajiya ta leko tana Fadin"Uwani..Amarya ku shigo kuga kaya mana kuna Tsaye jidda Sadiya ku shigo mana..!
Hajiya ta Fada tana Mirmishi sum sum kamar marasa kuzari haka sukabi bayan Hajiya Sakina sai da Aliya ta rike mata hannu tana Faman girgizamata kai.
Suna shigowa tsakiyar Falon Hajiya an baje kayan gasu nan Amina na Zaune a kasan acafet kusa da yakaka kanta na kasa da Dangin Hajiya sai hira suke yi taga yan gida Hajiya tace"A kiramin Balaraba baza"a bude kayan nan ba sai uwar Amina na kusa da kuma goggonta Husai da Sauran yan"uwanta mata...Ke kuma Aisha kira Abida kice su yi maza su iso ga Amina ta dawo..!
Ya Aisha ta amsa ma Hajiya da toh Cikin Yan Biki kuwa har wata ta Zari Hijabi ta bazama gidan Aba kiran mamanmu da goggo Husai da Sauran yan uwan Ami a mata ita kuma Ya Aisha ta dokama Abida kira tana Fada mata sakon Hajiya ta cikin wayar tana jin Sanda tace ga Amina tazo su Hamida suka Buga ihun Murna tayi Dariya ta kashe wayarta.!







_Wani abu ya bani Dariya wai yan bati association sune ke korafin wai bai kamata yaya ta mutu bata ga Tonuwar asirin mamammu ba..? da sauran mganganun da ya zama wannan Ra"ayin su ne abu daya nake so ku sani Koda wannan labarin yake kirkirarre ne,kada ku dauke sa ba gaskiya bane..Gaskiya ne wannan Labarin gaskiya ne akwai sihiri gaskiya ne akwai mutuwa a zahiri sannan gaskiya ne acikin mutane akwai mugaye mara imani Sannan gaskiya ne akwai masu shirka sannan gaskiya ne kishi ya rufe maa mata ido suna aikata komai saboda kishi Sannan gaskiya ne kan Dukiya ba abunda ba"a aikatawa a cikin wannan Rayuwar da muke ciki..Sannan mu musulmai ne mun zo Duniya domin bautar Ubangiji ne Tsarin Rayuwarmu Daga Farko har karshensa Tsararre ne sannan Rubutattace ne Daga littafanmu dake wajen Ubangiji ina so ku sani mutuwa ta Allah ce shi ke kashewa shi kuma ke rayawa..Sannan in Lokacin ka yayi baka isa ka kara ko minti Daya ba zaka bar Duniya Abunda nake so na Fada shi ne meyasa yan"uwanmu da kawayenmu ko abokan arzikim mu suke mutuwa suna cikin gabar jin Dadin Rayuwarsu..?
Meyasa su bamu ce bai kamata su mutu ba..?
Sannan meyasa matasa ke mutuwa suna kam cim kuruciyarsu..?
Meyasa su bamu ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login