Showing 255001 words to 258000 words out of 265571 words

Chapter 86 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28930

rame ta lalace kamar ba ita ba su ya Nazeem suma sunyi kuka Halin da suka iske mahaifiyarsu aciki suma basu ji Hauahin kowa ba domin Gaskiyan mallam ne a wannan gabar sai su ya"yanta suma sun yi kokarin kaita asibiti aka Fada musu ko sun je baza"a ga komai ba Yayanta ne yayi musu kwantance wani mai mganin gargajiya anan kauyen Tsafe nan suka kaita ya Dubata yace babu abunda zai mata Ciwonta kaikayi ne ya koma kanta Sai dai Kawai ya bata wani mganin da Zata rika sha kirjinta ya kwanta mata da Tarin dake Sarketa haka suka Dawo da ita gida suka tasata suna faman kuka tana Hawaye tana Nishi wajen rokonsu gafara suka riketa suna Fadin sun yafe mata Nazeem shi yaje yazo da Likita ya Dubata yayi mata alluran barci Saboda ta samu barci sai abakin kakarsu suka san Mallam ya Saketa to damam ai sun san haka zai faru sai dai sun jinjina ma mallam ba Tozarci Cikin Lamarinsa Mutum ne mai Dattako..!
Ganin yaranta sun Sauko sun nemeta yasa suma yan"uwanta suka Sauko Daman Hannunka bazai taba Rubewa ka yanke ka yarba Dole itace Dolensu,Nazeem da Uzairu kwana Biyu sukayi suka koma bayan sun bar ma Nazifi kudi sosai Dayake Nazeem ya Fara aiki Shamsu kuma Sai ranar da zasu tafi ya iso nan suka barsa,Umaima dai gata nan ne dai sai ahankali Ita kanta aljanun su taba kwakwalwarta yau lafiya gobe Hauka ne Nazifa ce aka bari tana kula da Hajiyan Uwanin wanda har taji Sauki Data ga ya"yanta sannan Danginta sun mata afuwa..!
Chan Dutse ma abun yayi muni Domin sun je sun iske Anty Amarya ta Fita Daga cikin Hayyacinta Domin Tsorata take yi acikin barcinta sai ta rika ganin Yaya tana fito mata Tun abun na karami har ya Girmama bata iya barci Sai abun ya taba kanta gabadaya ta Birkice yan"uwanta sun taimaka mata sun kaita asibiti Shashen mahaukata ana Dubata To Cikin wannan Halin suka isketa ta Rame ta lalace duk ta Firgice kamar ba Marliya yar kwalisa ba alokacin Duka yan"uwanta sun koma Tsausayinta harta Sakina da Anty A"i sun koma suna Tsausaya mata ganin Halin data koma ko da Rana ne ana Zaune sai ta mike tana Firgita da Ihu su ya Jidda suma sun koka matuka haka suka Rumgumeta suna kuka Tsausayin Mahaifiyarsu ya kamasu Nadama suka kamasu na yarda suka ki nemanta na tsawon Lokaci.
Sukaji aransu sun yafe mata har Abada anan suka Hadu da Sakina da ta Dawo nan da zama sai sabon kuka Tana Faman fada musu ta gaji da kiran Danmallam bai Dauka ba ta turamai sako ba adadi bai mata Reply ba in ya Saketa ne ya Fadamata sakina duk ta Rame gwanin ban Tsausayi..
Nan Sa"adatu ke fadamata daga wajen sunan Amina suke yara sun ci sunan Aba da Mallam sannan Sarood ma Cikinta har ya fito Sakina sai kuka Nadama da tsoron Rayuwa na kara shiganta har hotunan yaran ta gani Aliya ta Turo mata ita yanzu ta gama ganin rayuwa wani kishi baya gabanta ta sanu ta san makomarta kawai irin yadda Anty Amarya ta koma ya isa mai Hankali ishara..!
Sa"adatu ce ta fara komawa gombe Daga baya kuma ya Jidda,Ya Sadiya na nan Dutse ita tunda sunzo ne ita da Mijinta Tana Cigaba da kula da Anty Amarya..!
Mallam yaji Dadi da yaran suka kirasa sukace sun je sun Duba iyayan nasu ya Dinga saka musu albarka sanna yaji ba Dadi da labarin halin da suka samu su Marliya abun dai sai Addu"an da Fatan gamawa da Duniya Lafiya..!
Hajiya ma dataji Hankalinta sai ya tashi ta tambayi Izini Mallam bai hanata ba ya barta ita da Hajiya Nasara da Anty Hadiza suka tafi Gusai suka Duba Mamanmu a asibiti haka ta rike Hajiya tana kuka,Hajiya na Faman share mata hawaye tana Fadin ta Yafe mata har ta Hajiya Nasara Sai da Jikinta yayi sanyi,Sun iske Zulaihat na asibitin ita ke kula da ita,Basu jima ba suka gaisheta da kayan Dubiyansu Daganan suka Dawo Washegari kuma Tsafe sukaje suka Duba Hajiya Uwani..Hajiya Babba sai da tayi mata kuka tana kuka tana rokonta gafara ta yafe mata da ita da ya"yanta Hajiya tace bakomai Nazifa ta nan bata tafi ba,Sannan Umaima na nan jiki Sai ahankali kawai..
Basu jima ba sallah kawai sukayi suka juya Dagan suka je Dutse suka Duba Amarya Halin da suka ganta sai Allah Amarya hauka Tuburan sun isketa sai da aka Rirriketa,Sadiya ke nan tare da ita da Sakina Hajiya sai da ta Tausaya ma Sakina duk ta Bushe ta gaida Hajiya sai Sharan kwallah take Sai ta bama Hajiya Tsausayi har tayi alkawarin yima Danmallan mgana in suka koma..!
Koda suka koma Jikinta Duk a Sanyaye bata samu yima Danmallam mganar ba sun dai yi da Mallan shima ya jinjina ya kada kai yayi musu Fatan Dacewa mganar Sakina kuma yace tana Hannun mijinta abunda ya yanke shine Daidai.
Amina kuma ana chan ana ta Jego Yakaka sai da Allah ya sakamata ita ke kula da Amina da yaranta sun koma asibiti an yi ma yaran Shayi na pampers har sun warke,Yaran sun yi Kiba sun yi Bulbul Saboda Amina Nononta mai kyau ne sannan Danmallan kullum sai yazo ya Dubasu Safe da yammah kwana ne yake yi Wajen Sarood Amina bata dai nuna Damuwarta ne ammh fa abun na cin Ranta,Don ma Yakaka na mata Fada sannan ta Dage da kokarin gyara Amina kamar yadda tayi alkawari hakama Anty Hadiza ba"a barta abaya ba Tana kokarin gyara Diyar tata.
Hajiya na Shirin samun Danmallam da mganar Sakina sai gashi yazo yana mata mganar Sarood zata koma Madina sun koma makaranta shi zai jira in Amina ta gama wankan jego su tafi Tare Hajiya batace komai ba tace Allah ya Tsare daganan ne tamai mganar Sakina sai ya nuna mata Sakon Datake Turamai na ban hakuri
Harda mganar cire mata mahaifa da akayi Hajiya jikinta ya karayin sanyi da Rayuwar nan ta kalli Danmallam cikin wani yanayi tace"Kayi hakuri Danmallam in har baka saketa ba kaje ka Daukota ka maidata gida..Na tabbata ta ga Ishara ga abubuwan da suka faru. !
Danmallam yace"Ban saketa ba Hajiya..Sai dai ina tsoron na Sake Dawo da ita ta batamin zama na..Ta Rikitamin gidana Hajiya. !
Hajiya tace"Bazatayi haka ba..Insha Allahu..!
Kai ya kada kafin yace"Shikenan insha Allahu in na gama chukun Chukun Tafiyar Sarood zan je na Taho da ita .!
Hajiya tace"Allah ya bada iko..Sannan ina so in kun sun samu Lokaci kai da su Nasir da Jafaru kuje ku Duba su Uwani da Marliya suna cikin wani Hali.
Bai yi gaddama ba ya amsa mata Domin sunyi mganar dasu Jafar zasu je su Dubasu ciwo ya kore komai ko don Darajan zaman tare da kuma ya"yan da suka Haifa.
Danmallam ba yi gigin Fadama Amina zai Dawo da Sakina ba asatin aka sama ma Sarood Visa ya kawota sukayi sallama da Amina yana zaune yana kallon Amina da mamakin yadda yaji labarci na Fita abakinta Kanar wacce ta zauna a madina bai Taba Sanin ta iya ba ballatana yayi Zaton tana ji..
Ta bama Sarood Atamfa da Su Turare da Sabulai Saboda ta mata kokari Sannan ta Dauki su Aba da suka yi Wayau ta Rumgumesu har Yakaka sai Yabon Sarood take yi,Haka ta Rumgume Amina suka rabu kan sai sun zo tunda Danmallan yace tare zasu Taho da Amina ita Aminar bata ma san mganar ba.
Daganan gidan mallan ya kaita tayi musu sallama Hajiya ta bata Turaren Wuta tace ta kaima Mami Sara.
Washegari ya kaita kano Jirgin yammah Tabi zuwa Jidda dare yayi mai ya kwana a Hotel da Safe ya Dawo.
Lokacin Amina saura kwana Uku tagama wanka Danmallan nata musu Shirin komawa Madina Hajiya tayi mai bakam sai da Amina tayi arba"in yayi mganar Tafiya Hajiya tace sai ta Zaga yan"uwanta ransa ya baci sai dai bai nuna ba gashi yana son kebewa da matarsa an hanasa da gangan Yakaka ke Tsare waje in ya shigo bata so basu gama gyara ba ya bata musu saboda ta Lura ita kanta Aminar Ja'ira ce..!
Kwana Biyu da arba"in dinta suka fara yawo ta fara zuwa Hadeja wajen goggo Jumai ta kai musu Yaran ta gani ta saka albarka suka kwana Daya ita da Yakaka Idi yakai su bayan sun Dawo Washegari suka tafi gusau wajen kwanansu Hudu,Har asibiti taje ta Duba Mamanmu Halin Data ganta sai da taji ta manta da komai ta yafe mata Ya Jamela ta rakata Mamanmu na Hawaye Amina ta Dora mata su Aba Ajikinta haka take son tayi mgana ba hali Hannunta mai Lafiya ta saka ta Dafa kansu tana hawaye ya Zeenatu suka samu a wajenta tana kula da ita raba raba suke da junansu.
Amina ta yawata Dangin Aba kusfa kusfa Har kwana sai da tayi agidansu Zafira,suka sha Hira Yakaka kuma ta Shige Cikin Dangi kamar yar gida Ta zama yar gidan baba mallam yanzu.
Ranar da suka Dawo gidan mallam suka kwana washegari suka tafi Dutse Gabadayansu har ya Danmallam da Su Ya jafar da Hajiya ta koma suka Duba Anty Amarya data koma bata mgana sai kuka duk ta Firgice wani Lokacin in abun ya tashi sai an Daureta Amina da su ya Jafar sun kara jin Tsoron Duniya Sadiya ta nan tare da ita Sannan sunga Sakina Amina tayi mamaki Sakina har da karban su Aba duk ta rame sai Amina taji ta bata Tsausayi basu Dade ba Daga Dutse Tsafe suka wuce chan din ma sai ahankali Hajiya uwani dai ba wani Cigaba tayi ta rokonsu Danmallan da Amina Gafara Allah yasa ita da Bakinma sai dai Ciwo duk yaci Jikinta Nazifa ta koma sai Yan"uwan Hajiya uwani ke kula da ita itama har Su Aba aka Doramata kan jikinta tana kallonsu tana Kuka.
Da zasu Dawo suka Dauko Umaima suka Dawo da ita,Umarnin mallam ne
Washegari kuma su ya Danmallam suka je gusai suka Duba mamanmu Suma kansu jikinsu yayi sanyi Tana kuka ba baki tana mika musu Hannu Tana neman gafara sukace sun yafe mata Duniya da Lahira sun bama Zeenatu kudade kafin su kamo Hanyar gida suna Hirar yadda Allah ke nuna ishara da izina tun a Duniya.

Amina taso taje gidajen yan"uwanta Mata Mallam ya hana yace ta shirya tabi mijinta alokacin Sai Hajiya ta hana tace sai dai yaje ya Dawo ,sai ya tafi da ita Lokacinn yaran sun kara wayau bazai Daukesu tana Danyen Jego ya Hau jirgi da ita.
Sannan kuma zatayi Jarabawaarta ta Fita alkawari tayi kuma sai ta cika.
Mallam sai yama kasa mgana Daga baya yaso ya nuna ma Hajiya bata isa ba sai dai data mai bayani sai ya gane gwara Amina tatafi da Tarkadunta sannan yaran su kara Wayau shi ya Lallashi Danmallam da bai da tacewa Hajiya ai tagama dashi.
Ya samu Amina yana mata magiyan taje tace ma Hajiya ita zata Bisa su tafi Amina tace bazata iya ba sai yayi Fushi batare da sanin kowa ba ya Nema ma kansa Visa shi da Sakina Sai ana Saura kwana Biyu Tafiyarsu yaje ya Daukota Sakina sai da tayi kuka har ta cire rai da auranta da Umar ganin san da suka zo ko fuska bai Sakin mata baHakama yan"uwanta nata jin Dadi,Gidan mallam ya fara kaita Hajiya da mallam suka Taru suka mata Nasiha mallam kanshi yaji Dadi yadda Umar ya zama mai Afuwa
Sai alokacin yake shaida musu jibi zasu koma Madina shi da ita Hajiya tasan don Turama Amina Haushi yayi sai bata nuna mai ba kuma bai Fadama Amina zai koma ba Dauke mata kafa yayi ana gobe Tafiyar yazo yaga yaransa ita tana barci sai da Safe Yakaka ke Fadamata,Bata san ya tafi ba Sai da sukayi waya da ya Aisha take Fadamata Ya Danmallam ya tafi da Sakina itama Hajiya ke Fadamata Ranar Amina wuni tayi kuka Yakaka na lallashinra abun fa da Ciwo aiko bai Fadamata komai ba ya Fadamata Zai Dawo da Sakina ammh Duk Sai dai Taji Daga sama itama sai ta Zuciya ta Cigaba da kula da kanta da ya"yanta.
An biya mata Jarabawar ta a Unity dinsu da an fara zata fara zuwa sannan Huce Takaicin abunda Danmallam yayi musu Hajiya ta saka Baki mallam ya barta sukaje Abuja suka kwana Biyu ita da Yakaka dagachan har da ya Aisha suka Dumguma sai Zaria wajen Hamida suka kwana Daya gidanta suka kwana Gidan ya Zulfa suna ta murna da ina suka saka da yan"uwansu sun je har kaduna gidan Abida sun je kano gidan ya Jidda Lagos ne da parthercourt yayi nisa basu je ba Amina ta taka yola Wajen Hanne sai gata agidan Aminu Taga Nenne Dangi kuwa sai zuwa ganin Aminan Aminu ake yi yara kam sun sha Dauka shi kanshi Aminun ya kasa sukunu ya siyo wannan ya siyo wanchan,Amina sai yi ma Hanne Tsiya take ganin ta da Ciki.
Kwanansu Biyu suka Dawo Gida suka Sauke Gajiya..
Danmallam bai nemeta ba itama kishi da Haushin Abunda yayi mata ta yi biris dashi,Shi ma Yayi zuciya ransa ya baci da abunda tayi mai sannan kuma bayan ya tafi bata nemesa ba abakin Mallam yaji Tafiye Tafiyen da Amina tayi ko izininsa ba"a nema bai Taba Jin Haushi in Hajiya ta yanke Hukunci kan matansa ba sai kan Amina ya Lura tafi son Ma Amina da kowa komai take so shi take yi..
Amina Taurin kanta bai barta ba,Tana nan dashi shiyasa ta nuna ma Danmallam kalanta Har Yakaka taji Haushinsa Sai dai tayi ta lallashin Amima kada ta Damu sai ya Nemesu.
Ana cikin haka suka fara WAEC ta Dinka sabbin kayan makaranta ta fara zuwa Ranar datake da paper yakaka take barin ma yaran Agidan mallam in ta Dawo sai ta biyo sai yammah su koma gida Domin yakaka bazata iya Ronon yaran ita kadai ba gasu sun fara girma da kiba suna samun kulawa sosai..
Tana kokarin ya kice Takaicin Danmallan aranta taurin kanta yasa bata ko nemesa ba shima yaki nementa Amina tasan yaushe zai nemeta yanan chan wajen Guzumanyen matansa ita kuma tana nan tana mai renon ya"ya..!
Zai gane shayi ruwa ne da Aminene yake zencen..!


*Godiyata ta musamman ga iyayena guda biyu da sune silar tsayuwa kan kafafuna da nayi ayau din nan Alhaji Umar Muhammad mailoki da Malama Hadiza Muhammad Ba"are,Baba, mama ina matukar godiya da jajircewan ku akaina Ina godiya da Goyon bayanku ina godiya ga Allah da kuka kasance iyaye nagari a wajenmu Allah ya saka muku da Alheri ya muku Tukwaici da gidan Aljannah Firdausi Ameen Ina matukar son ku Babanmu da Hajiya mama tamu Allah ya kara muku nisan kwana da kwanciyar Hankali Ababen Alhafarinmu..*





*Janafty*

*TFZB2031*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*


Shifa Namiji duk inda yake sai ya nuna kansa barin ma in yana da mace fiye da Daya,Sannan su fa abunda muke kallonsa abun kunya a wajensu Daidai ne kuma mai kyau ne sannan in zaki shekara kina kyautatamusu Rana Daya in kika karkace sai ya manta baya ya Dora miki laifin duk Duniya akanki sannan ba kasafai suke Fahintarmu yadda Ubangiji Ya bamu ikon mu fahimcesu ba.
To kamar haka ya faru Tsakanin Danmallan da Amina ko yaya ne so yake ya nuna mata ba ita kadai garesa ba in bata bishi ba ai ya tafi da Sakina Sannan yayi hakane domin ya kure Hakurinta yana ganin kamar in ya tafin zata nemesa ta basaa hakuri sai kuma yaga akasin haka ya fahimci Tana da Taurin kai da kafiya domin shima Daurayewa yake da bai nemeta ba shi adole sai ta nemesa ta basa Hakuri sannan su sai su daidaita ammh Ina Sai ya Fahimci Amina tayi nisan da batajin kira.
Wajen watansa Biyu da Tafiya ko Flashing bai taba mata ba, itama haka Sai dai ya Kira Hajiya ko mallam yaji Lafiyansu wani Lokacin ma suna gidan in Amina ta tafi Jarabawarta koda wasa bai bari kowa ya Fahimci akwai baraka Tsakaninsa da Amina ba ballatana ita data share batunsa Sai dai Yakaka Datake zaune da ita ta Fahimci Tsakanin ma"aurata basa mgana Dole wani abu na faruwa.
Amina sun gama WEAC dinsu Cikin Nasara suna jiran Ta gaba lokaci Daya tana kula da ya"yanta sai kuma alokacin Danmallam ya gaji da Jiran Amina ta Kirasa su sansanta shi ya Sauke Girman ya Kirata taki Dauka Har sai da ya jera mata wajen sati yana Kiranta Tana gani bata taba Dauka ba sai abun ya kara bashi mamaki gashi dai anan hankalinsa yana kwance ne saboda Sakina tayi Laushi Sosai kamar ba ita ba,ga Sarood Daman bata da Hayaniya Cikinta ya shiga watansa na bakwai kusan duka ayyukan Sakina ta Dauketa mata ita ke yi tace Sarood din ta Huta duk yadda yake jin Haushin Sakina Sai da ya Tsausayamata da aka cire mata Mahaifa,duk son ta Haihu Allah ya nuna mata nasa ikon Da Farko bai Sakar mata ba sai daga bayaa shima din ba Sosai ba kadahan kadahan dai kada ya shiga Hakkinta sannan ya Duba Nasihan mallam da Hajiya ammh Daidai da rana Daya bai taba mantawa da Amina ba yana Madina ne ammh gabadaya ransa da Tunaninsa na Nageria wajen Amina da ya"yansa yaso ya jure sai ya kasa ammh Sai gashi yana kiranta bata Daga wayarsa.
Daya Dameta sai ta Fara Dagawa ammh yayi sallaman Duniyan nan tayi mai bakan sai da yayi ta jin kananun kukan su Aba na yara tun yana ganin Lamarin nata wasa har ya Fahimci abun nata yayi nisa,Ita kuwa yadda Danmallan ya kunsa mata Bakinciki ya raina mata wayau ne ta Dauki alkwarin sai ya gane bai da wayau sai yasan ya wulakantata Shiyasa ko da yazo yana kiranta Daga baya bata Taba bashi Dama ba Tayi alkwarin sai ta rama Fiye da yadda yayi mata sannan ta koyamai Darasin da har Abada bazai kara gigin mai da ita mara amfani a wajensa ba !
Yakaka Tasan basa mgana da Mijinta ammh bata taba mata mgana ba Sai Ranar Aba na wajenta mallan ne ke wajen Amina tana basa Nono,ta kawo mata shi kenan ta iske waya gefen Amina ta saka ta speaker Muryan Danmallan Tar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login