Showing 135001 words to 138000 words out of 265571 words

Chapter 46 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28948

kawai sakina ta samu Ciki ta Haihu in hakan ta Faru kamar na gama cika duka Burina ne..!
Mamanmu tace"Kema lokaci kadan ya Rage..Dukkanmu wahalar mu bazata tashi a banza ba..!
Anty Amarya tace"Tabbas..Domin bazan gaza ba..Sai naga abunda ya Turema Buzu nadi..Zan tafi yadda ake ciki zan kiraki..!
Mamanmu tace"Ki sanar da mallam Sa"idu ya fara zuwa hannu..Ammh ina so ya zama ni nake fadi yana amsani..
Anty amarya tace"Kamar yan amshin Shata kenan..!
Gabadayansu dariya suka saka kafin su tako atare har bakin Titi kowacce Adaidaita Dabam Dabam suka hau Daya ta koma cikin gari Daya kuma ta Mika hanyar tashar garin na Gumel..!



_SHIN KINA DA LABARI AKAN HA?IN SABAYA KOKUMA IN ?ARA MIKI BAYANI AKANSA DOMIN WANNAN HADIN INGANTACCE NE BA IRIN WANDA KUKA SABA AMAFANI DASHI BANE_

Shi wannan din SABAYA COCONUT FLAKES ne, duk wani hadi da ake nema na gyaran jiki akwaishi aciki duka hajiyata, naturally zaki cicciko babu abubuwan illa aciki.

*Ina ?an mata da zawarawa kai harma da matan Aure? To ku matso kusa ga Sabaya wanda akayi hadinsa da coconut flakes kuma kun san kwakwa ba karamin taka rawa yake wajen gyaran jikin 'ya mace ba, SABAYA COCONUT FLAKES zai taimaka wajen ciko da duk wani lungu da sa?o na jikin mace, ta dawo mul-mul da ita tamkar jinin ?an Chadii.*

*yana sa ?irjin mace ya ciko sosai, idan ma ?irjinki a kwance yake sabaya na iya mi?ar dashi ya koma kamar na buduwar ?ar shekaru sha 18. Duk wannam aikin na SABAYA COCONUT FLAKES ne shi kaWai =؃?=؃?=؃?, bayan haka yana ?ara ni'ima a jikin mace gamida ?ara mata Wumin jiki. Ga matar Aure kuma yana ?ara mata juriya wajen gamsar da mai gidanta cikin sau?i. Tareda Worewar nishaWin su gabaWaya.*

*Hajiya maza ki nememu don ki mallaki SABAYANKI, don kema ki zama mace mai aji kuma ?asaitacciya, karki yarda ki zauna yarkace-yarkace kamar kin fito gidan Yari=??, Gyara shine Mace Hajiya, idan bakya gyara jikinki sunanki mata maza, ko kuma in kiraki da suna wadda ta rako mata duniya Kawai=?E?
@&?*

*_Domin niman ?arin bayani ku tintiSeni kai tsaye ta wannan lambar:_* +234 706 548 1260 *_Muna tura kayan mu ko wani gari da zarar kinyi order

=؃?. Kuma duk akan farashi mai Rahusa>?p?

muna maraba da masu siyan daya ko sari..mungode sai kunzo=?O?

07065481260




*Janafty*
*TFZB2004*


*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*

BAYAN KWANA BIYU.

Amina ta gaji da kuka ta daina domin ta tabbatar ma kanta ita inda kaddaranta ta kawota kenan bata da wani tsumi ballatana Dubara kukan tayi shi har ta gaji ta hakura cikin kwana Biyun nan duk ta rame tayi Firgai Firgai ba walwala bata da sakewa sai zama waje daya da zaman kunci tundaga ranar bata kara saka Ya danmallam a idonta ba itama taji dadin haka sannan In yana gidan ta lura Sakina zata kawo mata abinci sau uku arana in kuma ranar baya gida to sai dai ta sha yunwarta sai dare bamai lekota ita kuma bazata iya fitowa ba har alokacin akwai sauran tashin hankali da kuma kokuwa da abunda ya sameta sannan uwa uba kuma rashin Sabo da inda take zaunen.
Amina bata wanka rabonta da wanka Tun ranar da Umar ya Tursasata tayi bata kara ganin ruwa ba sallah ce da ta zame mata dole take yinta sai abinci in Sakina taga dama ta bata wannan kam tana ci domin ta tabbatar ma kanta in ma bata ci ba sai dai ta Mutu daga sakinar har mijin nata ba wanda ya damu da ita acikin gidan sai filet din sun taru take fita dashi kitchen bata bari su hadu da Sakina domin har yanzu bata shiryama wannan rigimar datake janta dashi ba.
Ruwa kuwa bata matsama kanta ba na Tiolet take tara ta sha abunta Daki ba Shara ba komai Amina ita dai ta Wuni aciki ta kwana aciki ne kadai aikinta in kewar su hanne ya isheta taji kamar ta gudu gida sannan tana kewar makaranta abaya ranta baci yake yi in Monday ta zagayo ko Asabar sai gashi yanzu ido rufe take kewar makaranta tana ji dama ace tana da wannan damar da kewa bata isheta ba taji tana son zuwa makarantar ba Dama baba mallam bata kara ganinsa ba ballatana Hajiya kai wani Daga chan gidan ba wanda tagani balle taji ita ya makomar karatunta tunda yazo nan ya sar da ita bai damu data rayu ko karta rayu ba Allah sarki rayuwa tasan su hanne suna cigaba da zuwa makarantarsu tasan kuma yan ajinsu suna ta tambayanta kila sun fada musu an mata aure har an kawota gidan wannan mara Imanin.
Abunda bata sani ba shi Danmallan mantawa ma yake da ita agidan Shiryen Shiryen Tafiyarsa kadai yake yi Sakina sai da ta ga tafiyarsa tasa ta taso sannan Hankalin ta ya tashi Ana saura kwana Biyu Jirgin su ya tashi Ranar ya dawo da Daddare taji suna mgana da Aliyu ta waya yana Fadamai zai Dauki kimanin wata bakwai Cikin na takwas kafin ya Dawo.
Hankalin Sakina ya tashi duk da sun yi mgana da Anty ta Fadamata ta kwantar da hankalinta mallam ya tabbatar mata da cewa ko Umar ya tafi Bazai iya sukuni ba sai ya Dawo ya Tafi da ita saboda in ya barta anan ai anyi ba"ayi ba kenan Ga zamanta da wannan kazamar yarinya ga kuma rshin miji a kusa ta ina zata samu Cikin in baya nan bayan duka kokarinsu kenan yau ta ganta ta samu juna ya Tsaya mata ba ya bare kamar yadda yayi mata har sau uku ba.
Kafin ya gama waya ta Durkushe gabansa tana ruwan hawaye kallo Daya yayi mata yasa kwanan zencen sai ya shareta,Shifa gabadaya sha"anin mata ya fara fita kansa yau sai da ya yi ma Sarood fada soaai bisa yadda ta Kirasa tana kuka tana mai korafin ya tafi ya manta da ita tunda yana da mata har Biyu anan to ta gaji in bai dawo ba zata Biyosa bai hanata ba yace tazo ammh ta sani nan zata zauna itama bai kuma fadamata ga shi dawowa ba ya riga ya gama Shakan takaicin su gabadayansu ba Sakinar ba,Ba sarood din ba dukkansu ba kwanwar lasa bane,A baya sai yake ganin Sarood mai Hakuri ashe itama kyallece haka kawai ya fadamata ya Datse kiran yayi Rantsuwan in har tazo wlh sai dai ta Dauwama a Nageria ita da Madina sai da ziyara ai shima ba kasarsa bane cin arziki yake yi shi yanzu Damuwarsa daya yadda Hajiya ta Dage sai ya nema ma Amina muhallin Zama a Madina Tsakani ga Allah zai Takura baisan ta ina ma zai Fara ba kuma yadda Hajiya ta kafe din nan ko mallam bazai iya Tankwasata ba shima baya so ya fara Saba Umarninta tunda bata taba katsalanta kan sha"aninsa da matansa ba wannan ma Saboda yar gold ce.
Sakina ganin yaki bi ta kanta yasa ta fara jan Hanci tana fadin"Yanzu Habibi haka zaka tafi ka barni sai bayan wata bakwai ka dawo..?
Kana ganin ko ta bangaran addini kayi Daidai kenan..?
Suna Cikin Bedroom dinsa ne yana zaune gefen gadonsa tana sanan Cafet yayi mata kallon sama da kasa kafin ya Dauke kai Sakina ta riga ta tabbatar ma kanta bazai taba Sauya Ra"ayinsa ba.
Shiyasa ta mike tana fadin"Shikenan kasan dai ni macece kuma in da Hakki a kanka..In sha"awata tatashi Watarana har na cutu kai da Allah Umar..!
Ta karishe fada tana jan majinan kuka,har ta fice yana kallonta kafin yaja karamin tsaki bata san shi bane sai yanzu zata san shi ko ajikinsa komawa yayi ya kwanta yana jinsa kamar akan kaya ya kosa ya Bude ido ya gansa a madina matsalan Sarood karamace tsakaninsu ne ya lura in bata ganin Sakina tafi Hankali da natsuwa da kuma Hakuri ammh in dai tana Ganin Sakina akusa da ita tafi korafi da kananun mganganu.

Sakina na fita Dakinta ta koma tana Shesahekan kuka ta daga waya ta Kira Anty wacce ke shashen baba mallam alokacin sun gama cin abinci kenan dukkansu yaransun fita sai su dake falon gabadayansu har da Hajiya Babba suna hira kan yadda Zaman lafiya da rashin Tsaro ya yawaita hirar Tsakanin Mallam ne da Hajiya Babba sai Haj.Uwani Haj.Nasara na gefe tana saka baki jefi jefi,Anty Amarya ne keda Mallam aranar shiyasa tana gefe tana kallonsu bata saka baki daman tana da yawan ware kanta acikinsu
Wayarta na Hannunta sanda kiran Sakina ya shigo sai taki Dauka sai da taga Kiran yaki ya kare ne sannan ta tashi ta fita ba wanda ma ya lura da ita sai Hj.uwani da take ta sakin munafukin Murmishi Domin duk wani Motsin Marliya ai a tafin Hannunta take duk ta gama kokarin nata sai ya tashi a banza..
Sai da ta isa shashenta sannan ta Daga kiran Sakina Dayaki karewa Cikin Fada tace"Miye haka sakina..?
Kina kirana da wannan daran in Kika bada Kofa aka ganemu fa..?
Kuma mijinki na gida in ya fara Zargina fa..?
Ke meyasa baki da Hakuri ne..?
Sakina cikin kuka tace"To Anty yau fa naji yana fada in ya saka kafa ya tafi sai bayan wata takwas fa zai dawo..!
Anty Amarya tayi Tsaki kafin tace"To shi ne me..?
Sakina tayi kasa da Murya kafin tace"Anty kin manta ne..?in yana chan a ina zai ganni har auratayyah ya shiga Tsakaninmu na samu Cikin da muke Fata..?
Sai alokacin Anty Amarya ta Dawo Cikin Hayyacinta cikin Tashin Hankali ta Dafe kanta kafin tace"Kin gane duk nasan da wannan..Na fada miki mallam yace ko ya tafin zai dawo ya tafi dake Sakina ki daina Damuwa..!
Sakina tace"Nidai Anty mu tafi Taren hankalina zai fi kwanciya..!.Anty tace"To sai dai in Tuntuba ta bangaran Mallam,Ammh ta bangaran Umar kina ganin abunda yace min bazai saurareni ba in na matsa ma sai ya fara Zarginmu..!
Ki bari yau ni ke da Turakan mallan in wadanchan matan nasa sun watse zan mai mgana naji..!
Sakina tace"Yauwa Anty nagode don Allah kimai mgana don Allah..!
Anty Amarya tace"Naji zan mai mgana nace..Ki kuma ki daina Damuwa ki kuma rika hakuri kada wannan zalaman naki ya bata mana aiki..!
Da toh sakina ta amsa daganan sukayi sallama Anty Amarya tayi Tsaki afili ta Furta"Sakina tana da matsala wlh..!
Daganan Toilet ta fada domin ta sake Sabon wanka so take ta ruda mallam da nata salon yadda bazai mata gardama ba.

Achan Falon mallam kuwa bayan Fitan Anty Amarya itama Hj.nasara tayi musu sallama ta koma Shashenta ya Rage daga hajiya sai mallam Sai Haj.uwani Dake zaune gefen Hajiya Bisa kujera mai zaman mutum biyu Cikin kissarta data shiga Jikinsu gabadaya domin Hajiya ta yarda da ita Dari Bisa dari hakama mallam.
Sai da ta kalli Hajiya kafin tace"Oh Hajiya wai bawanda zai koma ya Dubomana Amina..?Tunda Suka tafi fa ba wanda yabi bayansu..!
Hajiya batayi yunkurin mgana ba Mallanlm ne ya Murmusa kafin yace"Kamar wasu yara kanana Uwani..?
In ita Amina yarinya ce ai Shi Umaru yana da Hankali na tabbata kuma zai kula da ita..Sannan ai ba ita kadai bace Sakina na tare da ita sannan ko Dazu nan mukayi sallar isha"i dashi kinga kuwa suna nan lafiya..!
Kafin tace wani abu Hajiya ta amshe mganar da cewa"Daman ina da niyyar su hanne su je mata..Na bari ne tayi ko Sati ne ta saba da chan kada su je yanzu ta fara koke koken suma ba Tunani ne dasu ba haka zasu hadu su kara Tada mata hankali..!
Haj.uwani tayi mirmishi kafin tace"Hakane kuma hajiya..ni daman nace ne ko zamu lekata Amina wlh da ita nake kwana araina Tsausayi ta bani Ranar da zasu tafi..!
Mallam yace"Da haka kowa ya saba..kema ai haka kika yi ta kuka ranar da zan taho dake daga Tsafe .!
Har Hajiya gatanan tayi wannan koke kokem ko ba haka ba Hajiya. ?
Hararan wasa hajiya ta sakar mai batayi mgana sukayi Dariya Dukkansu mallam ya cigaba da fadin"Zai koma ma jibin nan..in ya tafi su je su ganta su wunin mata sai taji Dadi..!
Hajiya tace"Eh har kwana ma sai suyi mata..Uwani ai mun girma da zuwa gidan yranmu yanzu sai dai in wani abu ya taso wanda ba"a Fata..!
Haj.uwani ta rausayar dakai kafin tace"Ammh in ya koma nan zai barmana ita ko..?
Hajiya tace"Eh nan zai barta ita da Sakina zasu zauna agidan su..!
Haj.uwani tayi mirmishin jin Dadi kafin tace"to Allah ya zaunar dasu lafiya..!
Gabadaya suka amsa da Ameen basu wani jima ba sukayi mai sallama suka fita,Hj.uwani bata koma Shashenta ba ,shashen Hajiya suka yada Zango suna hira sai hillatan Hajiya take yi tana jin wasu sirrikan saboda ko Mallam bai Fada maata abu ba zata jisa abakin Hajiya harta matakin da Hajiya ta Daukan kan tafiyar Amina madina sai da ta fada mata Hj.uwani tace"Wlh gwara haka hajiya..Yazo ya tafi da matarsa..Ni fa marliya ban yarda da ita ba..so suke su mallake Umar din shi kadai to ta Allah bata su ba..!
Hajiya tace"Ameen da yardan Allah Amina da Danmallam mutu ka raba. !
Aran Haj.uwani sai da tace ba Ameen ba afili kuma ta amsa da Ameen kafin tayi ma Hajiya sallama ta koma Shashenta Cikin Farincikin da sai da ya Bayyana akan Fuskarta
Umaima ta leka ta isketa tayi barci gyara mata Bargo tayi ta fice ta koma Dakinta,Tana shiga tayi wani Shewa lokaci Daya tana Fadin"Cikin ruwan sanyi..Burina zai cika..!
Wayarta ta Dauka Dake saman Mirror ta Kira Batula kanwata tana Dauka ta Sakin mata Shewa tana fadin"Batula albishirinki..!
Dagachan bangaran Batula tace"Goro Uwani Sikari baki farin banza..!
Dariyar Nishadi ta saki kafin tace"Tsarin da muka dora yarinyar nan su Hajiya sun taimaka mana ya tafi Daidai batula..!
Batula tace"kai don Allah..?,Bani na sha..!
Nan uwani ta warware mata komai ta Karishe da fadin"Kinga jibi zai koma kuma sai ya Dau Lokaci kafin ya Dawo..Zuwa kafin ya dawon na riga na Dorata kan Tsarin koda ma zai kulatan watarana kamar Sakinar ce haka ko ta samu zai bi Rariya..!
Batula tace"Dakyau..Hakan yayi kyau sai dai kada ki yi sakaci har adauki wani Lokaci bata hau Tsarin ba kinsan yadda zaki yi ko ta Halin kakane ...Cikin kwanakin nan Namiji fa baka shedarsa..!
Haj.Uwani tace"Naso haka sai dai tunda suka tafi batazo ba..Sannan naso na sakama Hajiya Tunanin muje mu Dubata taki bada Dama..ammh nasan zata zo jibi fa zai tafi Batula wlh ina da Tabbacin Mai mata kamar Sakina da balarabiya bazai kula Amina ba kinganta ne..?
Kwaila ce fa ga kazanta ga rashin Natsuwa ina da tabbacin bazai taba kulata ba..!
Batula tace"Shikenan tunda kina da yakinin haka..Sai dai ina tsoron kada su shammacemu..!
Haj.Uwani tace"Na yarda da aikin Mama..Ba wanda ya isa ya shammaceni Batula sai dai ni na shammacesu kamar yadda na saba..!
Dariya suka saka gabadayanau kafin su cigaba da mganarsu sun manta cewa Allah ne ke zana kaddaran bawa ba Mutum ba,abunda basu sani ba shine Komai da zai faru nan gaba Allah ya riga ya Tsara faruwar hakan Lokacin kawai ake jira.
Tabbas Uwani zata Tsammanci abunda batayi tsammani ba.
Bama ita kadai ba iri irenta ma zasu tsammanci abunda basu taba Tsammani ba..!

Anty Amarya sai da ta chanchara kwalliya,ta fesa turaruka sannan ta koma Shashen mallam cikin gayunta,Mallam bashi a falo yana cikin Bedroom dinsa chan ta Bisa ta iske ya fito wanka kenan ya sauya kaya zuwa saukakkiyar Jallabiya mai ruwan madara furfuran kansa duk yana Waje ne tana shigowa da sallama ya amsa mata yana Binta da kallo Lokaci daya da Mirmishi
Gefen gado ta nemi waje ta zauna tana kallonsa kafin tace"Mallam kayi wanka baka jira ni nazo na tayaka ba..!
Mirmishi yayi mata kafin yace"Na Hutassheki ne marliya..!
Mikewa tayi ta isa garesa ta amshi Man dayake shafawa a Hannunsa ta Lakuto tana tayasa shafawa Lokaci Daya tana fadin"Aikina ne fa..Kada kamin Rowan lada mana mallan..!
Yana kallonta yace"Mun girma marliya wannan aikin duk na Dauke muku yanzu..!
Marairaice masa tayi tana fadin"A"a nidai ban yarda mungirma ba....!
Yana yar dariya yace"Baki yarda mun girma ba..?,To in ke kina da yarintarki ai yunusa kan ya Tsufa..!
Tura bakinta tayi kafin tace"Ni dai wlh Mijina bai Tsufa ba..Yaro ne Danye Sharaf..!
Dukkansu yadda ta fadi mganar yasa sukayi Dariya atare ita ta karishe Shafa mai man suka koma saman gado suka zauna mallam ya mike kafarsa tana shafamai man zafi Saboda sun faramai Tauna kuma aki"da ne duk Dare sai ya shafa yake kwanciya
Tana shafamai suna Hiransu samasama sai da ta gama hillatansa sannan ta kallesa kafin tace"Ni ko mallam yaushe Danmallam zai koma ne..?
Kai tsaye yace mata"Jibi in Allah ya yarda yacemin jiya..!
Kai ta Rausayar kafin tace"Ya sanar dakai nan zai bar Sakina..?
Mallam yayi shuru kafin yace"A"a bai sanar dani ba..!
Anty Amarya ta gyara zama tana fadin"To ni dai baisan me ya faru Tsakaninsu ba..kasan yaran nan su yi ta shirme basa neman shawara ashe sanda zasu taho Bikin su Abida yace ta Zauna achan ta matsa sai tazo Shine fa yace bazai koma da ita ba yanzu..!
Mallam ya yi shuru yana kallonta kafin yace"Haka akayi .?
Anty amarya tace"Eh mallam ita kuma Sakinar ta damu tana ta kirana tan kukan wai na rokesa ya koma da ita bazata iya zama ita kadai ba nidai Fada nayi mata nace Laifinta ne da nace bazan saka Baki bane tace nayi maka mgana don Allah ka Rokesa ya tafi da ita..!
Har ta gama mgama yana Nazarinta Kafin ya sauke ajiyar rai yace"Naji batunki marliya kinsan Allah ni bansan ma duka anyi haka ba..Umaru da na ne ammh bana hirar iyalansa Dashi..Tsakani na dashi Hirar duniya sai kuma ta aiki in ta kama sai kuma ta Rayuwa haka ammh ni bana shiga Sha"anin ya"yana da matansu kinsani marliya..Umaru mijin Sakina ne sannan bansn meya faru Tsakaninsu ba domin ina Mahaifinsa ya gama tsara abunsa sai na kirasa nace masa ya Sauya..kina ganin hakan ba rashin girma bane..? sannan kuma shiga Hurumin da ba nawa bane tunda dai bai Tuntubeni da mganar ba..!
Ya karishe fada yana kallonta itama shi take kallo jikinta yayi sanyi domin taga ba Nasara,girgiza kai tayi cikin sanyin jiki kafin mallam ya cigaba da fadin"To kin gani bai kamata nayi mai mgana ba..Sannan ai ba ita kadai zata Zauna ba ga mamana nan itama nan zai barta sai ya sake dawo wa ki bata Hakuri ta zauna inda mijinta ya ijiyeta..!
Anty Amarya sai ta kasa mgana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login