Showing 15001 words to 18000 words out of 265571 words

Chapter 6 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28877

wacce take Kitsa ma ya"yanta Sa'idu bakomai bane a wajena Tayi kuskure..Sa"idu D"a na ne..Shine Babban yarona sai da na Sameshi na Samu UMAR..!
Sannan nan gidan da Gidan Sa"idu Duka abu Dayane ya"yansa Jikokina ne..Har Abada..Kamar yadda ku da ya"yanku kuke da iko da Gidan nan da Dukiyata da ni kaina kuke alfahari dani Haka Sa"idu da yayansa zasu yi Na Rantse da Allah in na kara jin wata mgana mai kama da wannan Dukkanku Daga ku har ya"yanku sai naci Mutumcinku..!
Ku tashi ku bani waje mutanen banza Ke Sa"adatu ban gama Dake ba..Ki Taka kije har gida ki bama Mamana Hakuri in ba Haka ba Wlh sai na maidake Kauye nayi miki aure kinji ma na Rantse tashi ki bani Waje..!
Ya karishe Fada Ransa na kuna da wani kunya da Nadama yaya zai ji in Sa"idu yaji wannan mganar Tun bayan Haduwarsa da Sa"idu bai Taba ganin Daraja da kima kamar yadda Sa"idu ke ganin kimarsa ba ko Umar baya masa Biyayya irin yadda Sa"idu yamai dashi komai nashi ba..Shekaru nawa ya kwashe yana gina Iylansa Domin su zama abu Daya ammh ya Fahimci akwai babban baraka barakan in da ta barke baza tayi masa Dadi ba ya zama Dole yayima Abun Tufkar Hanci Ransa yayi Mummunar bacin da ko matansa sun Dade basu gansa Cikin wannan yanayin ba.

Sa"adatu kuka ta saka ma Anty Amarya Tana Fadin"Anty ki bama Baba Hakuri kada yakaini Kauye..!
Anty Amarya Farar mace alkyabban Mata itace kadai mai kananan Shekaru acikin Matan Baba Malam faman Zagaye take a Tsakiyar Falonta Ranta ya baci meyasa komai sai Sa"idu da Ahalinssa ta tabbata ko Yayan Daya Haifa da Cikinsa Mallam bai musu soyayya kwatankwancin yadda yake kaunar Sa'idu da Iyalansa .!

SA'IDU....SA"IDU..SA"IDU..!


Halitta kwara Daya da Tun Shigowarta Rayuwar Malam ya Hanata Rawan gaban Hantsi komai na Mallam din kafin ya"yansa suzo agaba Sa"idu ne kan gaba meyasa haka..?Tasan itama ta fito Daga gidan Manyan Mutane kakanta Shehin Malami ne kafin Rasuwarsa Malam kamar Dalibi yake garesa Duk garin Dutse ba wanda baisan Malam Armaya"u ba Shine ya Haifi Mahaifiyarta,sannan shi ya Daura mata Aure da Malam lokaci Rayuwarsa Duk da itama Tana ganin Baba Malam din a Talabijin yayi mata Duk da ya kasance ya Manyanta ammh bata Damu ba azatonta zatazo Tayi Mulki sai kuma taga akasin Haka Bamai iya Mulki agidan Baba Malam Suna Biyu ne ke yawo Daga na SA"IDU sai na HAJIYA BABBA..!
Suna da matukar Tasiri a Rayuwar Baba Malam din..

Sa"adatu ce ta kara kallonta yadda tayi Zurfi wajen Tunani Kafarta ta taba Tana Fadin"Anty baki ce komai..?
Dayake Tun zuwanta gidan Anty Amarya ake cema yasa bayan ta Haihu Sunan yabita har bakin ya"yanta.
Anty Amarya ta Sauke ajiyar rai kafin ta koma kan Kujera ta zauna Kusa da Sadiya Dake kallonsu kala batace ba Daman ai bata da Hayaniya.
Sabeeha na gefe itama ta Damu da ganin Sa"adatu na kuka.
Kanta ta Dafe kafin ta Dago Tana Fadin"Mafita dayace..Kiyi abunda yace..!
Sa"adatu tace"Naje na bama Amina Hakuri Anty..?
Kai ta gyada mata kafin tace"Eh haka nce..Kinsan Waye babanku..Tunda ya Rantse bazai Sauya mgana ba..kuma bazai Fara kaffara Saboda ke ba Sa"adatu..!
Sa"adatu zata sake mgana ta Daga mata Hannu lokaci Daya tana Fadin"Kiyi abunda yace..Koma meya Faru ke kikaja..?Amina..Amina wannan Shegiyar yarinya kinsan yadda Babanku ke Somta baya ganin Laifinta me yasa kika Biye mata..?kin ja An Tozartani gaban Kishiyoyi Kin jamin Kallo da Zubewar kimata a idanuwan Malam Kimar da nayi Shekaru ina Ginata Sa"adatu Kin jawomin Kafar Zargi da kallon Reni Daga ya"yan Cikin gidan nan Sa"adatu ki kyaleni da abunda kika jawo na raasa yau ki barni nayi Tunanin yadda Kimata zata dawo a Idanuwan Malam..Naki mai Sauki ne ki je ki bama Amina Hakuri Shikenan Mganar Zata kare..!
Daga haka tana Huci Fuu ta shige Bedroom dinta ta bango Kofa Sadiya ma ta mike batace komai ba ta wuce Dakinsu aka bar Sa"adatu da Sabeeha.
Gaskiya Anty ta Fada Mallam bazai Sauya mgana ba in tana son Tsira Daga Fushin Malan tayi yarda yace.
Kwana Tayi kuka da Bakimciki Zata kaskantar da kanta gaban Amina sai dai bata da Mafita Baba mganarsa Dayace kuma ba Sauyi.
Dole yasa da Safe tana Shiryawa na Tafiya makaranta,Tace Sabeeha ta rakata gidansu Amina Lokacin da taje gidan kowa yayi mamaki Saboda ya"yan Anty Amarya basa zuwa gidan Sai da wani Dalili mai karfi
Sanda Take bama Amina hakuri ita tasani Aranta wani abu ya faru Sai da sukaje Makaranta Hanne take Fada musu yadda akayi Amina tayi Dariya ta Hura Hanci kafin tace"Amina Aminene..Wlh badai ta Mutum ba sai Allah..!
Tundaga Lokacin Sa"adatu ta Fita Sabgan Amina bayan Baba Malam ya Kirasu ya musuvFada sosai atare sannan yasa suka yafi juna baisan na Ciki na Ciki ba ita kuwa Anty Amarya Sai da tasan yadda tayi mallam ya yarda ba wajenta Sa"adatu taji mganar ba Har Kara Dukanta tayi Saboda malam din ya yarda da ita kuma Hakanta ya Cimma Ruwa Saboda Har gidansu Aminan taje ta kara bata Hakuri ta yi mgana da Mamanmu wannan abun yayi ma Malam Dadi har ya yarda da Gasken Amarya bata da Masaniya kan abunda Sa"adatun ta aikata yarinta ke Damunta daganan aka bar mganar ammh Dai Sa"adatu da Amina sai dai kallo Daga nesa basa mgana ballatana wani abu ya kara Shiga Tsakaninsu.
Amina bata Sauya ba Tana nan da Jidalinta a gida da makaranta,acikin Satin ma sai da aka bata Suspention na Sati Daya saboda ta fadama wata yar ajinsu Anty Sara Basic Teacher dinsu Tana warin maza ita kuma ta Fada har mgana takai kunnen Anty itakuma Anty Sara ta kai mgana Gaban Sir Gumel ya Rabbata mata Kora Daman ta Taba yima wani English Teacher dinsu Dariya dan Bautar kasa wai wuyansa kamar Lema Mgana Har sai da Ya Jafar yazo makaratar Duk da Dukan da Amina taci agida da makaranta baisa tayi Nadaman abunda ta aikata ba to wannan karon Allah ya Ceceta Mamanmu bata bari mgana takai kunnen Aba ba ta kai ma Baba Malam Waya kadai yayi mganar ta wuce ammh da Sharadin in ta kara cin Zarafin wani malami kora ce Baba Malam yace ya yarda Yayi ta ma Amina Fada da Nasiha wanda yasa Jidalinta yadan Ragu ammh Dalibai Kam bata Daina ba Kafin atashi an sha Fada in an tashi ma Amina yi take Wani Lokacin ya Shamsu ke taka mata Burki.
Da gaske ne mganar Auransu Ya Zulaihat ya taso kamar yadda Hanne ta Tsegunta ma Amina,Ya Zulaihat wani Dan Sanda zata aura Dcp ne anan garin Jigawa kuma yana Daga Cikin Daliban Malan Duk Ranar jumma"a Wajensa yake zuwa Daukan karatu Daga Jigawa shi dan asalin kano ne aiki ne ya kawosa nan kuma Baba Malan yana da Hannu wajen zamowarsa a wannan matsayin.
Ya Aisha kuma a kaduna zatayi aure Itama wani Soja zata aura sojan kasa ne mai Mukamin Captain,shi Mahaifinsa ne abokin Malam sai Ikram da anan garin Gumel zatayi auran kuma agidan Sarauta Domin Jikan Sarkin Gumel zata aura Sai Sadiya da zata Auri Yaron Yayan Anty Amarya yana America yana Karatunsa har yafara aiki achan kan abunda ya Shafi Dilar magunguna.
Duka ya"yan Baba Malam auran gida ake yi musu yawanci ya"yan abokan Malam ne da kuma Dalibansa bashi yake Hadin ba Baya Tallar ya"yansa Sai dai akwai masu son Hada Zuru"a Dashi Sosai Da an zo Tambaya zai yi Bincike in yayaba da Hali da kuma abunda Annabi yace aduba shi zai ga wacce ta Dace da Mutum Wata Shida kafin mganar tataso sai ya bada Izinin ganawarsu da juna Sai dai Kiji ance ki Shirya yau kina da Bako Gabadaya yan"matan gidan haka yake Faruwa Dasu Mazan ne kai zaka nemi abunka da kanka ya aura maka sannan baya bambamci Da gidansa da Gidan Baba Sa'idu komai na auransu shi yake Gudanar dashi babu wani bambamci Shi kanshi Aba sai da yaji Baba Malaman yana Fadamai wane kaza yazo nema ma Dansa aure acikin Gida na yanke Hukunci cikin ya"yanka zai zoya gana da Daya daga Cikinsu nashi Shima Bin Umarni ne Domin Malam ya wuce komai awajensa.
Mganar auran tatashi Sannan kowa yasan Hajiya Babba itace ke Rufe Amaran da komai itace Malam ke sawa agaba Kayan Daki kuwa da komai da komai Daga Dubai ake Oda sai dai akawo kayan abinci kuwa Store ne guda basu da mtsalansu Domin ashekara ba wanda yasan adadin abunda Baba Malam ke Noma??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????wa.

Duka duka nan da Wata Biyu Baba Malam yace za"ayi Bikin Tunda su Ya Zulaihat sun gama WAEC har sun Fara Neco dinsu sannan za"ayimusu Walimar Sauka ana gobe Daurin auransu ne,Shiyasa Duka bangarorin ke ta shiri Amina ba Haka taso ba taso harda ya Zeenatu Daki ya zama Daga ita sai Hamida ammh itama ai wata Shekara ne zasu bugar dasu kamar yadda kowa ya sani.
Bikin yana Saura Wata Daya Dan Malam Dake Madina yayo ma Malam Waya yace cikin Satin nan suna Tafe Shida iyalansa Hutun karshen Shekara da kuma Bikin Sannan yace Jirgin yawo zai Fara yo gaba da kayansu su sai daga baya zasu iso.
Sai Shagalin ya ninka na Baya Ga yadda aketa Murna ma zakasan ko waye wannan ana Matukar ji dashi agidan Anty Amarya sai Shiri take Saboda Zuwan SAKINA nageria Mganar Shirin Biki kuma yana Hannun Hajiya Babba ne da Hajiya Uwa Ita da Hajiya Nasara yan Shawara ne da kallo kawai..,!








*Janafty*

*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janaftyd'?*

*Sadaukarwa ga Halima yusuf gwarzo(Besty)Alherin Allah yakai miki aduk inda kike*



*
*SHEIK YUNUS ABDURRAHAMAN BAZANGA* Haifaffan garin Bazanga ne Dake Yankaji B karamin gari ne cikin karamar Hukumar D'anja ta Jahar katsina,Mahaifinsa Maigarin Bazanga Abdurrahaman da mahaifiyarsa Aminatu auran zumunci ne a Tsakaninsu Domin suna matsayin abokan wasan juna ne. sakamakon Bazanga karamin gari ne yasa Gabadaya Rabin garin Dangin Abdurrahaman ne da Aminatu wanda suka fito daga Tsatson mai Maigarin na Bazanga Tun Tale tale Duniya tana kwance.
Kowa yasan garin bazanga gari ne mai yalwar amfani gona da kuma Kyautata Kiwo,Dukiya da arzikin Baba Malam ba Haye yayi ba Gadonta yayi Tun asali Mahaifinsa ya Rasu yana da Shekara goma aduniya ya barsa Da Mahaifiyarsa da Tarin Dukiya na gadon gonaki da kuma Dabbobi.
Abu Daya Yususa ya rike dayasa ya Fara Fafutukar nemam Ilimi shine Kafin Mahaifinsa ya rasu ya Fadamai Yunusa kada ka zauna ka fita ka nemi Ilimi Domin Watarana kazo ka iya rike Dukiyar da nabar maka sannan komai sai da ilimi Yunusa da wannan kalmar yasa ya matsa sai da aka kaisa Makarantar allo acikin garin Bichi Dake kano yana da shekara goma sha Daya alokacin Aminatu taki yarda sai dai kuma Hujjar da aka bata na Neman Ilimi yasa ta amince Sannan kuma abaya babu Macuta masu hawa kan Dukiyar maraya,Yunusa bai Samu matsalam Komai ba Saboda wan Mahaifiyarsa shi ya Dinga Noma Gonakin Daya gada da kuma Kula da Dabbobinsa.
Yunusa wannan Nasihan ta Mahaifinsa ita ke rike dashi yasa Duk inda yaje ya zama mai kwazo sannan Yana da baiwar Dauke abu akansa Lokaci Daya shiyasa kafin ya Rufe Shekara Uku ya Sauke aqur"ani Cur asaman kansa Daganan ya Dawo gida ya Fara Cucukin yadda zai Fara Karatun boko Domin ya Fahimci ko na addinin gareka in baka da na Boko baya Tafiya Daidai.
Lokacin yana da Shekara sha uku A Danja ya fara primary dinsa Tunda alokacin Yara da girmansu suke shiga Karatunta,Saboda Ilimin bai yawaita kamar yanzu ba yana Gabda gama Primary Aminatu ta rasu sakamakon Saran Maciji abunda yasa Yunusa ya bar Bazanga kenan kwata kwata ya nausa neman Ilimi Duk da kananun Shekarunsa sai dai ya bar Kula da Dukiyansa Hannun wan Mahaifiyarsa Bala.
A makarantar kwana yayi Duka Secondary School dinsa sannan bai Zauna ba yana neman Sani a Duk inda ya Samu kafin ya gama yayi suna Ba wanda baisan sa ba wajen Kokari da Kuma Sanin ya kamata ta Fanni Addini da kuma Bokon Ba inda akayi masa Zarra yana zuwa gida Lokaci Bayan Likaci in Bukatar kudi ya taso mai yakan je wajen Kawu Bala ya basa Kudi Domin yayi amfani Dashi Wajen Karatunsa.
In suka samu Hutu baya zama Waje Daya yakan shiga Har kano wajen Malaminsu bai yadashi ba yana Daukan Karatun Sauran Littafi a wajensa Shiyasa Lokaci Daya Ilimin Yunusa ya shahara batare da an Farga ba.
Bayan ya gama Secondary Diploma yayi kafin ya bar karatun ya koma Zurfafa a neman ilimin addini Duk inda ya san akwai wani Malami mai karantar da Al"umma Yunusa baya zama Waje Daya yana zuwa ya zauna aduk inda yasan zai karu zai kuma Samu ilimi bai koma makaranta ba Sai da yasan abubuwa da yawa ya Sauke wasu Littafan addini da Hadisai bisa kansa sannan ya koma makaranta yayi Degree dinsa akan Islamis Studies anan Abu Zaria.
Kafin ya gama yayi suna ya Rike Shugaban Dalibai na Bangaran addini musulunci MSS, Sannan Kafin Gamawarsa har Limanci yayi zaman yi a masallacin Cikn makaranta sannan bashi da girman kai ko ka girmesa indai kafisa Sani zai Duka ya nemi Sani a wajenka Sannan shine Overoll student a site dinsu sannan bayan ya gama ya Zama Shine First class alokacin
Babu wanda alokacin baisan Yunus Abdurrahaman Bazanga ba Ana ganinsa wani Dan kauye alokacin sai dai mai Tarin hazaka da Ilimi wanda da Fara raina masa wayau akeyi sai Daga baya aka Fahimci iliminsa da Baiwarsa.
Ya samu Shedar kwalin Degree sannan kuma ya kara Sanin addininsa Sosai,Tun yana da Kananun Shekaru ake mai Lakabi da Malam sannan alokacin ba kasafai akesamun yan Baiwa kamarsa ba yasa Takardarsa ta bama Department dinsa mamaki da Taimakon Shashen addinin Musulunci na Jami"ar Ahmadu Bello Yunusa ya samu Scholorship na Tafiya Jami"ar Madina yayi master dinsa kan Islamis Studies Daukakarsa ta Farko da bai Taba Tsamani ba Domin alokacin har ya koma Gida yana Taya Kawu Bala Kula da wasu abubuwan kafin ya kuma yasan inda Zai Lula sai ga Takarda ta Fito Dauke da Sunansa sannan Ita Jami"ar ita tayi komai Har kudin Jirgin Tafiyarsu.
Shiyasa Har gobe bazai manta da Malamnsa na Abu Zaria ba Domin sune matakin Zamowarsa koma meya Zama arayuwa.
Acham Madina wata irin Rayuwa Yayi Domin waje ne garin Manzon Allah sannan Zaka ga abububuwa kala kala da bakayi Tsamami ba bai da matsalan Wajen kwana da abinci Sannan Har kudi suna samu bai zauna ba,yana Fita yayi aiki ana Biyansa Sannan Nemam ilimi yunusa bai gaji ba Larabawan Malaman nan nasu Haka yake binsu Daya bayan Daya yana kara Fahintar abunda bai Sani ba Yunusa shine Yazo Daga Jahar Katsina Sannan akwai Sauran bakaken Fata irinsa Da kuma Labarawa mazauna chan din sai dai Duk da Haka Yunusa ya Dokesu Duk da ya Sauya Karatun nasa wannan Karon yama Karantar Hadith and Islamis Studies ne a islamic University of Madina.
Ko Larabawan wucesu yake yi basa iya Ja da Yunusa shiyasa tun kafin ya gama kowa yasan Ustaz Yunusa Abdurrahaman bazanga Daga Nigeria Ita Nasara Daman ta Allah ce sannan kuma da Dagewa anan din ma Shine ya Fito da Firstclass kaf a Site dinsu ba ga yan Madinan ba Har ga Bakaken Fata yan Nigeria Jami"ar ta karramasa Sannan ta roki data rikesa yayi mata Koyarwa Duk da alokacin Shine mafi karancin Shekaru acikin Malaman wannan itama wata nasara ce yana da Shekaru Ashirin da takwas a Duniya ya samu wannan Daukakar Daga Ubangiji Duk da yana son ya koma gida kasarsa ta amfana da iliminsa Da kuma Shima yana ganin ilimin bai isheshi ba yana Bukatar kara Sanin Wasu abubuwan.
Ya zauna Amadina Tsawon Shekaru Biyar ya samu Cigaban Rayuwa sosai ya Samu Daukaka da kuma arziki Ta Dalilin iliminsa sai dai bai manta da gida ba yana Turo ma kawu Bala Kudi Daga chan shi kuma batare Daya Fadamai sai ya rika siyan Dabbobi yana karamai Cikin Garkensa.
Alokacin Yunusa yaji gida yake son Dawowa ba yadda Jami"ar madina batayi dashi ba yaki Tsayawa Dole ta Rabu Dashi ya Tattaro ya Dawo Mahaifansa da kowa yake mamakin Yunusa ne ya koma haka..?bakinsa ya Hade da Labarci Da Turanci Hausa ma Kadan kadan ne yake ji yayi matukar mamaki yadda yaga Dabobinsa sun kara yawa sai da Kawu Bala yayi mai bayani Sannan ga amfani Gonar nan da ake Fitarwa Duk Shekara bayan ana Fitar da Zakka Daman Tun a shekarun baya ya hana Kawu bala Noma Sai dai biya suke ana Noma Gonakin Duk Shekara shiyasa yana da kananun Shekaru yana da Dukiyar da baisan iyakarta ba.
Da Farko anan bazanga ya fara zama Yana koyama matasa masu tasowa Cikin Abunda ya Sani Rasuwar Kawu Bala yasa Yaji garin ya fita kansa,Dabbobinsa ya saida wasu wasu kuma yayi kyauta dasu sannan amfanin gonarsa ya Raba ma yan garin Gonakin ne kawai bai saida ba ya barsu Domin Watarana ya Kalla ya Tuna da Mahaifansa.
Daga garin bazanga Yunusa Maidurguri ya zauna yayi Shekaru uku achan yana neman ilimi kuma Shima yana karantarwa sannan yana Noma yana kiwo Domin shine gadonsa Tun kaka da kakkanni Duk inda yaji wani Babban Malami mai Karantar da addini Yunusa sai ya taka baida Girman kai sam shiyasa yake Samun Nasaran Rayuwa Daki Daki.
Hajiya Babba mai suna Zainabu yar Garin Bama ne alokacin yan Boko Haram basu Rikita garin ba Sannan a wajen Mahaifinta ya zauna Mallan Zanna yayi shekaru ukun nan yana neman ilimi Da zai tashi Tafiya ya Dauki Zainabu ya bashi auranta Saboda ya yarda dashi.
Hajiya Babba ba yar kowa bane Mahaifinta Malan zanna malamin Zaure ne bai da komai sai Rufin asiri Duk garin da Yunusa ya zauna zai yi Noma da kiwo in kuma ya tashi Tafiya zai sai Raba biyu ya Dauki Rabi sannan ya bar ma Inda ya Zauna Rabi haka ta Faru da Malan Zanna Da karamcin da yayimai Duk da ya Fadamai Asalinsa da kuma Burinsa na neman ilimi Har ya koma ga Allah.
Malam yunusa ya zauna agaruruwan Nageria baisan iyaka ba Duk inda yaji Labarim Malami sai yaje ya nemi Ilimi Shima ya Bayar Daga Cikin abunda ya sani Sannan Dukiyarsa ya zama kamar Rabata yake duk inda ya Zauna ya sami Riba sai ya bar Abunda yazo Dashi ya tafi da Ribansa Shiyasa Acikin matansa ba kamar Hajiya Babba ita tasan shi tun yana matsayin Malam Yunusa ta kuma yi kokari da Jeka kadawon da suke yi shi da ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login