Showing 171001 words to 174000 words out of 265571 words

Chapter 58 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28956

Allah ya Fadamana suna karya sihiri ko asiri ko .?
Ai kasan su..?
Cikin Sanyinsa yace"Eh mallam..!
Maalllam yace"karantomin su naji..!
Umar ya gyara Tsayuwa ya fara fadin"SURORIN AL'QUR'ANI GUDA SHIDA DAKE KARYA SIHIR KO ASIRI.

1. SURATUL TAUBA: AYATA 14.
2.SURATUL YUNUS :AYATA 57.
3.SURATUL NAHIL: AYATA 69.
4.SURATUL ISRA"I :AYATA 82.
5.SURATUL SHU'ARA :AYATA 78_82
6.SURATUL FUSILAT: AYATA 44.

mallam ya jinjina kai kafin yace"Dakyau..To kamar yadda ka lissafasu ka samu ruwan zamzam ka karantasu duka ka tofe aciki ka rika Shafe al"auranka duk dare in zaka kwanta da jikinka gabadaya sannan ka rike addu"a da azkar domin koma menene Yana jikin ka ne ba jikin ita Saratun ba..!
Danmallam ya jinjina kai yana Fadin"zanyi haka insha Allahu nagode mallam Allah ya kara girma..!
Mallam ya amsa da Ameen yana fadin"Allah ya warware mana..Allah yasa adace Allah yasa asamu waraka..!
Daga haka sukayi sallama Danmallam Ya Dade tsaye kafin ya koma cikin ajin sa ya cigaba da koyarwa karkashin Ransa kuma yana gasgasta mganar Aliyu koda mallam bai fito yace sihiri bane ammh Yanayin addu"o"in da ya basa na karya duk wani Sihiri ne ko asiri.
Yana fitowa da ga ajin ya koma Office ya Kira Aliyu ya fadamai yadda sukayi da maallam Aliyu ya rike baki kafin yace"Kaji mganata ko..?
To ka gaggauta fara abunda yace maka Fatan nasara Allah y bamu waraka..!
Daga haka suka rabu Daga cikin makaranta gida ya wuce daman yanaa da Ruwan zamzam din Sarood bata nan tana makaranta sannan in ta Dawo Zata biya gida Mami Sara na Fama da Zazzabi.
Alokacin ya samu Lokaci yayi Duk abunda mallam ya Umarcesa ya Tofesu acikin Ruwan zamzam din a kuma wannan Daran ya Fara amfani Dashi da yakinin Ciwonsa Daga Allah ne kuma waraka na wajensa..!
Sannu sannu dai..Bata hana zuwa sai dai a Dade ba"a je ba..!
Daga yanzu aikin nasu ya fara Lalacewa Alalan geronsu ya riga yayi Ruwan da bazasu taba iya Dauresa ba koda kuwa sun mai Cikon Gari acikinsa..!

*****

Sati dayan da Malam ya Dibar ma Anty Amarya na cika ya Kirata a waya Daman kiransa take jira tana Lissafe da Ranakun.
Sai dai yana fara bayanin Idanuwanta suka Rufe Daga sanda yace Wace ke Lalata Cikin Sakina tana cikin matan mallam sannan tafi kusa da Hajiya da kowa acikinsu sannan bama Take lalalata Cikin ba ko yau sakina ta kara Samun ciki bazai taba zama a mahaifanta ba akwai abunda aka bata Tacin ma cikinta wanda yake hana Cikin zama acikin maranta. !
Anty Amarya na Tsaye ne acikin Dakin su Sa"adatu in da su Sakina suke bata gama Sauraran mganar mallam ba ta yi wurigi da wayar sakina ta Tsorata tabi ta kallo ganin yadda ta fita a fusace.
Haj.Uwani na gaban madubin bedromm dinta tana Saka dan kunne a kunnenta Kamar Daga sama taji an bango kofar lokaci Daya da shigowa Cikin mamaki ta juyo tana kallon ikon Allah..
Idonta fes a na Anty Amarya wacce ke kallonta Cikin Jajayen idanuwanta da suka rine da bacin rai da wani Bakinciki.
Haj.Uwani Cikin mamaki tace"A"a Amarya Lafiya kika shigomin har Cikin kuryan Daki ba sallama..?
Kawai sai Anty Amarya ta Nufeta ta Shako wuyanta idanuwanta sun firfoto waje cikin Karaji take fadin"Ke baki chanchanci sallaama ba..Baka mai bakar aniya muguwa azzaluma mai fuska Biyu da izinin Lahi Uwani sai kin ga sakamokon ki Tun aduniya muguwa macuciya azzaluma kaawai..!
Haj.Uwani ta Fincike Wuyanta Cikin Wata irin kallo take bin Anty Amarya da shi kafin ta kece da wata irin Dariya tace"Azzalumai bakake masu bakar Aniya zaki ce Marliya sannan ki rika saka min jaye..Bazamu gama da Duniya Lafiya ba DA NI DA KE..tunda duk jirgi Daya ya kwasomu..!

Tafada tana dariya lokaci Daya tana mata kallon Nasan ki, ni tuntuni ke kuma sai yanzu kika sanni..?






*Janafty*


*TFZB2013*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*


Anty Amarya ta dago tana kallonta cikin rawar baki dana jiki tace"Ban..ga ne ba..?
Me kike nufi Uwani..?
Haj.Uwani ta saki wani kayattacen Mirmishi mai hade da cin nasara tana kallon cikin Idanuwan Anty Amarya wacce ta fara tsorata da Lamarin Uwanin tace"Kina sane da abunda nake nufi marliya ko na kira ki da Madina ne..?
Tafada cikin tsaida kallonta kan Anty Amarya wacce ta zaro ido jin Sunan da Uwani ta Kirata dashi Sunan da mutanen da suka santa dashi ba su da yawa suna ne da ta saka ma kanta Tun tuni domin cikar wani Buri nata.
Haj.Uwani ta fara taku acikin Dakinta tana Zagaye Anty Amarya tana Sakin Dariya kasa kasa kafin ta nufi kofar Bedroom dinta ta kulle ta harda Murza key ta juyo tana Fadin"Komai na Bukatar sirri madina duk da bansan da wacce kike zo ba..?
Anty Amarya da tagama Tsorata da mganganun Dake bakin Hj.Uwani baisa ta yi saurin karaya ba yasa cikin Gyara Tsayuwarta tace"Kina sane da duk abunda nazo dashi Uwani..Tunda ke kike aikata shi..Kashe rai fa kike yi fa Uwani..?
Kina lalata duk cikin da Sakina take samu yanzu in wannan mganar ta fita kina Zaton zaki kara Minti Daya acikin gidan nan ne..?
Tafada tana kallon Haj Uwani wacce ba karaya ko nadama ko kaadan a Tare da ita sai ma Zama da tayi gefen gadonta ta Dora kafa Daya kan Daya tabi Anty Amarya da kallo kafin tace"Ranar Biyan Bukata rai ba abakin komai yake ba Marliya a wajen ki na koyi wannan Tsarin sannan Da kike mganar in Labarin nan ya fita bazan kara ko minti Daya agidan nan ba..?
To wayace miki zai fita yanzu..?.
Ai ko zai fita sai na gama cika Burina Likacin na zama giwar mata ko mallam babu yadda ya iya dani marliya ballatana Hajiya da ban Dauketa wata Tsiya ba..Atafin Hannuna take kinsani..!
Bama ita ba gabadayanku a nan dina kuke ba wacce bansan duka motsinta ba..!
Ta karishe Fada tana Nunatafin hannunta cikin gadara Anty Amarya tayi wani mirmishin takaici kafin tace"Aiko kunyi kuskure Uwani..Wlh yadda kika yi sanadiyar Salwartar da Cikin Sakina sai nayi Sanadiyar da asirunki ya Tonu yau a idon Duniya..Yanzu ba sai anjuma ba, zan je na Sanar ma Hajiya komai domin ta gano Muguwar bakar Fusarki..!
Tafada a fusace kafin ta juya zata fita ta tsinkayi muryan Haj.Uwani Cikin Gadara.

"Bani kadai zaki tona ma asiri ba marliya Har da ke karan kanki..da wacce ta hada hannu Dake kuka KASHE YAYA..sannan kuma baya zatayi Zani marliya harta Danmallan zai gano cewa ba da Ra"ayinsa ya auri Sakina ba ke kika shiga kika fita hakan ta kasance..!

Da wani irin mamaki da al"ajabi da Faduwar gaba Anty Amarya taci Burki ta kasa juyowa ta Fuskanci Hj.Uwani Domin tana faman kokuwa da Faduwar gabanta na yadda Uwani ta san wannan Boyayiyun sirrukan da ga ita sai balaraba sai Malaminsu suka san anyi haka sai gashi a bakin Uwani to garin ya akayi ta san duka sirrukan su haka su basu taba sani ba..?
Tana wannan Tunanin taji Muryan Uwani a saitin kunnenta tana fadin"Kin yi mamakin ya akayi nasan Duka wadanan sirrukan naki ko nace naki keda Balaraba ko..?
Anty Amarya ta kasa gaba ballatana baya ba inda jikinta baya rawa Haj.Uwani ta saki Dariyan nasara kafin ta fara Tafiya zuwa gaban madubin Dake Dakinta tana Fadin"Nayi mamakin da sai a yanzu malaminki ya gano miki ni marliya ai na Dade ina shirina kusan ma nace na Rigaki shirya komai..Ni tuni Mama ta Bincikomin komai naki da ke da wacce ke tayaki dukkan ku wani motsinku ko sirrinku yana Cikin Tafin Hanuna Marliya abunda baku sani ba Kuna aikin ne ni ina warware muku..Kamar yadda Sakina ke barin Cikinta haka in wannan balarabiyar ta samu ciki ita ma haka zatayi ta barinsa hakama Amina ita kanta ban kyaleta ba na shigo da ita cikin Tsarina..Tsarin da zai kai ni nan da Lokaci kadan na cika Burina..!
Sai alokacin Anty Amarya ta Juyo tana kallon bayan Haj.Uwani Cikin Rawan baki tace"Wani irin Buri ne wannan da kika Zabi ni ki hanani Cikar nawa burin.
A bar batun Rufa Rufa Uwani Tunda kinsan komai ba amfani na cigaba da Boye miki manufata ni in kinyi Hakuri ba mallam nake so na mallaka ba..Kawai Sakina nake so ta Zama Mowar mata wajen umar da Danginsa..Sannan ita kadai ce nayi ma alkawarin zata haifa ma Umar magaji ta kuma Haifa ma Hajiya da mallam jika mafi soyuwa bayan ita ban yarda wata tazo Daga baya ta fita ba..Sannan in hakan ta faru nasan nima zam zama Shalele a wajen mallam da Umaru tunda nice silar duk abubuwan da suka faru..!
Ki fadamin meye naki burin da yasa ni kika ki bari nawa burin ya cika..?
Ina so naji irin naki Burin akan mallam da zur"arsa..?
Haj. Uwani ta juyo tana kallon Anty Amarya ido na cikin Ido kafin tace"Ko baki tambayeni ba zan fada miki..Boye boye ai ya kare. tunda malamin ki ya gano miki ni Marliya..Karkade kunnuwanki Ki sha Labari yanzu zan sanar Dake yadda naki Cikar Burin ke neman yayi min Cikas kan nawa Burin da nayi shekaru ina Wahala akansa..!
Komawa tayi ta zauna ta kara Dora kafa Daya kan daya kafin ta fara Fadama Anty Amarya duka shirinta da nata tsarin da Burin datake dashi akan mallam da ahalinsa ta karishe da Fadin"In har na bar Sakina ta Haihu Da Umar kin batamin Tsarina marliya..shiyasa na hana faruwar haka sannan bama ita ba indai ina Raye Umar bazai ga kwansa a Duniya ba..Tunda na gano Mallam yana matukar son yaga jikokinsa ta bangaran sa na mike tsaye na shiga na Fita na hana faruwar hakan..Ya"yana kadai ne zasu haifama mallam jikoki kuma ya sosu ni kadai ce zan zama Tauraruwa ba Hajiya ba..In ta samu mallam a baya awannan gabar Lokacinta ya kusa karewa..!
Nasan zaki ce ina Nazir da Nasir da na bari suka haihu.?
Ai suma din ba gazawata bane Marliya Tsarin aikina ne..Daga ya"yan Nazir din har Nasir din wa kika gani mallam ya Damu dasu?
Ai nasa mama ta Dakushe wannan Tasirin har Abada kuma bazasu yi shi a idanuwansa ba Nazeem ne kadai da Uzairu zasu haifa masa jikoki su zama Sanyin Idanuwan mallam bayan su kuma nayi alkawarin har Abada ba wanda zai haihafama mallam Jika Tun balle ma Danmallam da mallam ya fi so cikin ya'yansa shiyasa kika ga inayin Duk abunda nake so..!
Niso nake nan gaba ya"yana su zama sune Hop din mallam gabadaya Sune komai nasa bashi da yarda zai yi sannan kuma alokacin ni zama giwar a cikin matansa ko yana so ko baya so..Ya'ya ne kan gaba a dukiyarsa sannan wajen haifa masa jikoki ma sune kan gaba Dole kauna da soyayya ta koma kaina da Ahalina gabadaya..Mganar Sa"idu bai gabana domin ke da Balaraba kun Rage min wannan aikin..Lokaci kadan nake jira na Aiwatar da Tsarina akansa kamar yadda na Tsara..!
Ta karishe Fada tana kallon Anty Amarya wacce tayi mutuwar tsaye ta kasa ko motsi da jin wannan labarin lalle Haj.Uwani ta fi su zama Shedaniya,Su ashe bakomai ma sukeyi ba,Shekaruna nawa ta kwashe tana Wahala ammh Lokaci kadan Uwani tana neman Tsawartata to bazata bari ba,Bazata yi Saurin karaya ba,sai ta nuna mata in ita a Tsaye take ita a tafe ta kwana..!
Ta kalli Uwani cikin Bakinciki kafin tace"meyasa Burinki ya yi kamanceceniya da nawa .?
Meyasa sai dole kin Tsawartsani Uwani meyasa haka..?
Haj.Uwani tayi kasa da Murya kafin tace"Ki yi kasa da muryanki mana marliya..Ai na riga na Fada miki Dalilina..Bake kadai na taba ba..Na Fada miki yadda na Raba Hajiya da ya"yanta a kusa da ita,Na maida Nasir mara amfani a wajen maallam na hanata ganin jikanta ta Tsatson babbar Danta ita meyasa batace ina so na Tsawartata ba sai ke da Duka Dagani har ke muna kan Turba Daya ne marliya..?
Anty Amarya na Huci tace"To baki isa ba..wlh uwani karyan ki ta sha karya..!
Haj.Uwani tayi Dariya kafin tace"Nama isa ai marliya..Kaawai ki yi Hakuri ki mara min baya Burina ya Cika in hakan ta faru nayi miki alkwarin Raba komai gida uku na Dauki Biyu na baki kashi Daya. !
Anty Amarya ta harareta kamar Idanuwanta zasu fado tace"Me kike nufi..?
Haj.Uwani tayi Dariya kafin tace"Ki hakura da Sai Sakina ta Haihu marliya..!
Anty Amarya ta Zumduma ashar kafin tace"Ina..Baki isa ba Uwani..Bazaki Hada baki dani ba..Kowa ya Tsaya da kafafunsa..Sannan kuma sai dai ki kare a muguntarki kina ji kina gani Sakina zata haifarma mallam da Hajiya jika sai dai bakin ciki ya kasheki. !
Tafada tana kumfar Baki Haj.Uwani ta tabe baki kafin ta Daga kaafadanta tace"Shikenan marliya..Kije ki cigaba da Wahala..Ammh ina mai kara gayamiki..in sau Dubu sakina zata samu Ciki sai ya Zube haka Sarood hakama Amina ke ko aure ya kara itana irin Tsarin dana Dora su itama akan shi Zan dora ta Marliya na Fada miki kan Cikar Burina zan iya aikata komai..!
Anty Amarya taji wani abu ya Tsaya mata a wuya kawai sai tayi kukan kura ta kara shako Haj.Uwani cikin Hargagi take fadin"Me kika baa sakina tasha..?
Ki Fadamin abunda kika Binne da kudin da kika kashe akan hana Sakina Haihuwa Uwani..?
Kwace wuyanta tayi tana Hararan Anty Amarya Lokaci daya tana Fadin"Wlh in kika kara saka hannunki kika rikeni sai na Sharara miki mari marliya..!
Ki kama kanki kafin Zuciya tajaki ki aikata abunda zaki zo kina Nadama..!
Anty Amarya na Haki ta nuna Haj.Uwanu tana fadin"Wlh kin yi kadan..Nayi alkawarin sai nayi sillar Tona miki asiri..!
Haj Uwani tace"To ai ban Hanaki ba..tunda baki min godiyar Taimakon ki da nayi ba akan Amina da Sarood ba, wato sakina kadai kike so ta Haihu ban da su ko..?
To tunda baki ga Hallacin da nayi miki ba Shikenan jeki fadama wanda zaki Fadamawa ammh ki sani in asirin ya tashi Tonuwa naki sai yafi muni Marliya ni iya ka dai mallam ya Sakeni ko..?
To in ya sakeni ai bai kare ba ina da Zaratan maza har uku ko da sun ji abunda ya faru basu isa su sauya ni a matsayin uwa ba marliya,Sannan kuma dole zasu neme ni kefa wa kike dashi..? Duka ya"yan ki mata ne baki da wani gata anan duniya iyayanki zasu yi Tir Dake ya"yan ki mata zaki bar musu abun kunya in ma bai taba auransu ba,Sannan Uwa uba kuma agaban idon ki Umar zai Saki Sakina kinga Daganan kin kare a Tutar babu..Wahalar ki tatashi a banza kenan kuma ke ahakan ma naki Tonuwar asirin mai kyau ne,akan na Balaraba ita wlh ko kaffara bazan yi ba kare sai ya fita Daraja in sirrin Boye ya fito Fili sai ta wulakanta ta Tozarta a wajen Sa"idu da Danginsa da kuma ya"yan Yaya da kukayi Sanadiyar barinta Duniya Saboda cikar naku burin..!
In kin yarda da duka Faruwar wannan shikenan u can go..Ki je ki Fadama Hajiya sai mu shirya bankadewar siirikan namu dani da ke da balaraba alokaci Daya ko banza na San Dagani har ke bamu samu cikar Burukan namu ba..!
Tafada tana wata yar Dariya Anty Amarya duk yadda taso kada ta nuna Rauninta sai da ta nuna Hawaye ya wanke mata Fuska ta nuna Haj.Uwani da yatsanta Cikin Kaushim murya mai Cike da karkawa tace"Ki Rubuta ki ijiye Uwani Indai ban samu abunda nake so ba..Na rantse ko Zan yi yawo Tsirara sai naga kema baki samu abunda kike so ba..In juran ki sammako ni madina a tafe na kwana mu Zuba mu gani..!
haj.Uwani ta bata amsa da cewa"Shege ka fasa marliya..!
Daga haka Anty Amarya ta murza key din ta Bude kofar ta Fice tana kuka Duk yadda taso ta shanye kukanta ta kasa bakinciki da Takaicin sun taimaka wajen Fitar Da ita daga natsuwarta uwa uba kuma da yadda Gabadaya sirrukansu yake tafin Hannun Haj.Uwani
Hajiya ta fito kenan Daga Shashenta zata shashen Haj.Uwani suyi mganar wani Turaran wuta da suka je Bikin nan maiduguri tace tana so yagana ta kirata kan mganar ne yasa tace bari ta shiga ta fadamata..
Ta sawo kanta Falon kenan Anty Amarya na fita da gudu tana kuka Hajiya sai ta Rude hankalinta ya tashi ta rika fadin"Subhanallah Amarya Lafiyanki kuwa..?
Ina ko jinta batayi ba batama ganta ba Domin kuncin datake ciki ya Rufe mata jinta da ganinta har ta fice Hajiya na Kallonta sai jikinta ya kama rawa tana Fatan Allah yasa ba wani abun ne ya Faru da Sakina ba kamar ta bi bayanta sai kuma ta fasa ta karisa Cikin Falon Haj.Uwani tana Fatan taji abunda ya faru Daga bakinta.

Ita kuma Haj.Uwani Anty Amarya na fita ta yi shewa ta kara Sakin shewa kafin tace"Mu zuba mu ga??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ni marliya..Karki fara ja da Uwani Domin ni walkiya ce ban Fito ba sai da na shirya..!
Haka take ta fada tana Dariya tasan Daman zatayi mamakin yadda tasan komai nasu Mama hatsabibiyar Bokanyance Dake Niger ita take Sanar da ita duka aikin marliya ita da Balaraba ita kanta da Farko ta Razana da jin sunan mamanmu domin bata taba Zaton matar mugun halinta yakai haka ba, sai dai batayi mamaki ba Sanin yadda Idon kowa yake Rufewa kan neman Duniya..sannan Ta kara jinjina ma wannan kalmar na rai ba abakin komai yake ba wajen Biyan Bukata Tunda Balaraba ta saka aka kashe yaya Matar data Zauna da ita Tsakani ga Allah ta bar mata gidanta da ya"yanta kawai saboda Cikar Burinta na mallakan sa"idu..!

Tana wannan Tunanin kamar Daga Sama taji muryan Hajiya tana Sallama sai ta Rude ta mike da Sauri ta fito Tana kokarin Daidaita yanayinta Hajiya dake tsaye Tsakiyar Falon Uwani ko Zama ta kasa ta kalli Uwanin Yadda ta fito tana abu kamar wani abu dai ya faru yasa da Sauri tace"Wai ni Uwani me ya faru ne acikin gidan nan bansani ba..?
Naga Amarya ta fita Daga shashen ki da Gudu tana kuka ina ta mgana bata jini ba kema mayi sallama kin Fito kamar kina ma a firgice ne Hankalina ya tashi muke Faruwa..?
Haj Uwani na jin haka kawai sai ta Zube saman Cafet din Falonta ta Fashe da kuka yi take yi ba Saurarawa ta kara Tadama Hajiya da Hankali Cikin Rudewa tace"Ko Cikin yaran mu ne wata ta rasu kuke Boyemin..?
Hajiya Uwani na jan majina da Hanci tace"Ai gwara ma Mutuwa da wannan Zargin da Amarya ke jifana dashi Hajiya..!
Hajiya tace"Wani Zargi kuma Uwani..?
Haj.Uwani na kara saka kuka tace"Hajiya wai ni Amarya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login