Showing 168001 words to 171000 words out of 265571 words

Chapter 57 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28890

Gidan malamin nasu chan wani kauye ne kafin a shiga garin Dutse ne da wuri ta isa akwai layi ta jira kadan sannan aka bata izinin shiga tana shiga ko kafin tayi mgana ya Zayyana mata Duk abunda ya faru yace Garzali ya sanar dashi komai saboda haka ta Bada kudin da aljanu zasu sha jini kawai tayi tafiyarta nan da Sati Daya zai kirata abunda ke nan zai sanar da ita komai nan ta Bude bakin jaka ta Zazzage mai kudi da batasan ko nawa bane Kudi ne dai masu yawa har da wadanda Sakina ke samu a asibiti in anzo gaisheta sannan shekaranjiya Jafar ya kawo mata 30k yace in ji Danmallam yace ta rike a Hannunta koda wani abu zai taso ta saka a jaka Saboda komai na kudi mallam ke gudanarwa ko sisinsu basu kashe ba Har da su ta zubema Malamin nasu sannan ta kamo Hanyar Gumel Ranta na kuna ta kosa agano wacce ke neman shiga Tsakaninta da Burinta yadda zuciyarta ke azalzalanta
Har taje ta Dawo ba wanda ya Sani daga ita sai Dayyaba sai Allah kawai yasan inda taje ko da tadawo Sakina ta samu barci kanwarta kuma ta zata Gida ta koma tayi wanka ta Huta Shiyasa bata Damu da Tambayarta ba.
Sai da Sakina ta kwana goma asibiti sannan aka sallameta ta koma gida Saboda yanayinta yasa sai mallan ya yarda da Rokon Anty Amarya kan Dawo da Sakina gabanta har sai ta Warware,Daman Amina tunda akayi haka tana nan gidan Mallam bata koma chan ba mallan yace Tunda hakane dukkansu su zauna anan in Sakina ta kara jin Sauki sai su koma Tare abun yayi ma Amina Dadi daman ta Tsani zama agida chan sannan ta Tsani zama inda ba Hamida ba Hanne ita dai murnanta da Farincikinta ta gansu tare tana musu Jidalinta suna Dauka.
Har ta da Amina duk kinta da Sakina sai da ta Tausayamata ganin ta yadda ta Rame sai katon kai,Dayake ranar da aka sallamo su suna makarata sannan bayan sun dawo islamiya suka tafi sai da suka Dawo ita da Hamida da Hanne Hajiya tace su shiga su gaisheta suka iske ta cikin Dakin sus Sa"adatu zaune ana bata abaya abaki sai ido zuru zuru kamar na mayu in ji Amina da suka fito.
Hamida tace"Gaskiya ta bani Tausayi ji beta kamar ba ita ba duk ta rame..!
Amina tace"Sai yanzu na kara ganin Gajartan ta ga Katom kai ashe ma dan jikinta na Rufa mata asiri..!
Hamida tace"Amina ciwo dai na kan kowa..!
Amina ta Harareta kafin tace"Ai ban ce bai kan kowa ba..In kin ji mgana na Tsausaya mata ne..!
Hanne dai batace komai ba sai alokacin tace"Tasha Wahala inji Hajiya tace sosai.Sannan ta tada Hankalinta barinta na Hudu fa kenan har ya Danmallam naji hajiya namai Fada har ciwo sai da ya kwanta fa..!
chan madina..!
Hamida tace"Wayyo da Tsausayi kam..Allah ya basu rayayye..!
Hanne ta amsa da Ameen banda Amina da Haka kurum taji ranta bai yi Dadi ba, wai har ciwo yayi saboda barin Cikin wanchan gajerar matar basu Fahimci yanayinta ba ta wuce Shashen Hajiya ta bar su nan Daman a Bakin Shashen Haj.Nasara suka Tsaya suna maida Zencen.
Tun daga lokacin sai Kulawar Sakina ta koma karkashin Anty Amarya tunda ashashenta take sannan Hajiya ma har nan take zuwa tana Dubata ta saka su Ladidi su yi ma Sakina Fatan wake da ferfesun kayan ciki Saboda jininta ya Dawo sosai har Hajiya nasara ba barta a baya ba ita da Haj.Uwani Wacce Anty Amarya ke jin takaicin inda ta ganta ta rako Hajiya tana wani iyayi ita hakanan aranta taji bata yarda da ita ba..
Sannan Har mallam ma ya kan shigo ya Dubata Lokaci bayan Lokaci uwa uba kuma duka kannen Danmallam wadanda ke gidan auransu sun ji Labari sun kuma kira sun ma Sakina Sannu harta da Nazir da matarsa matan su Jafar kuma sun je asibiti sannan da suka Dawo ma sun zo sun Kara Dubata Ikram dake kusa tazo ita da Sadiya da Zulaihat sun zo sun kwana Daya sun Dubata sun koma Tunda Mamanmu ta Kirasu ta Fada musu har da goggo Husai Dake Jordan taji Labari ta kira tayi ma Sakina Ya jiki da jajen Abunda ya Faru haka su ya Jawahir suma sun kira harta Aba da basa wani Shiri da Anty Amarya Yaje assbiti bai san iyaka ba da suka Dawo gida ma sau biyu yana shiga Dubata ba saboda alherin kowa ba sai Saboda Danmallam
In sakina ta fara kokenta Anty Amarya ta Dinga ce mata kenan"Ai kuka bai kamaceki ba Sakina..Godema Allah zaki yi..Ki kalli abunda ya faru Dake mijinki bai juya miki baya ba yana Tsaye kanki da lafiyarsa da Aljihunsa shi da Danginsa da yan"uwansa hajiya da mallam Sakina kullum suna tafe Shashen nan wajen Duba Lafiyarki wannan kadai ba matakin nasararmu bace.?
Tabbas mun samu nasara domin ko bakomai Danmallam da Danginsa suna kimanta ki Sakina suna Darajaki Daraja mai yawa ban gane haka ba sai da wannan abun ya sake Faruwa..!
Sakina cikin kuka take fadin"Na rasa Cikina a karo na hudu Anty..Na kara rasashi yaushe zan samu wani Cikin har ya zauna na Haihu..?
Anty Amarya tace"Kada ki damu zaki Samu wani cikin..kuma da yardan Allah sai kin Haifar ma Umar Magaji in baki Haihu ba to sai dai ya Dauwama shima bai Haihu ba..Na Rantse da wanda Raina ke hannunsa in Zargina ya Tabbata sai na yi Fito na Fito da duk wanda ke Rusamin aikina ko waye shi kuwa..!.
Tafada cikin kaushinta akoda yaushe kalamanta yanzu tuni sun Daina ma Sakina aiki a kanta ta fara Sarewa da al"amarin kwata kwata.


Amina suna cigaba da zuwa makarantar su,Sannan tafi zama bangaren Hajiya har Hamida ma tare suke sai suyi sati basu kwana agidan Aba ba suna Shashen Hajiya saboda Hanne sannan ita kanta Mamanmu bata wani Damu ba Amina ba yanzu Duniya ta samu,Daga ita sai Aba ko Jawaad wani Lokacin Wajen su Amina yake kwana ashashen Hajiya Duniya ta samu yanzu Aba bai mata gaddama ko Hajiya da mallam tasha gabansu sai su gama mgana dasu yazo mamanmu na tambayansa zai kwashe ya Fadamata shawara kuma akomai da ita yake sai abunda tace shi yake yi ta kankane komai tana baza buraubanta yadda ta gama Dama shiyasa har Hamidan ba Damuwa da take yi da ita ba yanzu tasan dai lokacin auran su nayi za"a aurar dasu Amina kuma Daman sunan auranta gantali
Ita kanta Aminar tasan Mamanmu ta Rage kula da ita kamar baya sai ta Danganta hakan da yanzu ba Yaya ba su ya Zeenatu Hidima tayi ma mamammu yawa tayi mata uzuri sosai,Su Hajiya kuma basu wani Lura ba saboda basu fiya saka ido ba ko da yaya nada rai Amina da Hamida yan Shashenta ne kowa ya sani shiyasa ko yanzu da suka Tare anan bama wanda ya Damu.
Sannan in Allah zai ikonsa kan wani abu da karesa da kansa sai ya kaudar da Tunanin mutane akan hassashen wani abu to kamar hakane ya Faru da Amina cikin Lokaci kadan gabobinta suka fara girma kirjinta ya fara Cika har yazo ma yafi na Hanne yana neman fin na Hamida sannan Daga kasanta Hips dinta ya Bude ta fara Fashewa kibanta Daga sama ya Fara sai kuma ta Bude ta kasa sannan Fuskarta ta Ciko sosai yawancin kayanta ma sun mata kadan riguna sai da Hajiya ta saka aka kai aka Buda mata itama taga kiban da Amina tayi sai bata kawo komai ba azaton Cin abincin da Amina ke yi saboda cin abincinta ya ninka na baya har Cikin Dare ci take sannan ga shan Tea madara bata sati take karewa Amina hakanan take hambalamta har sata take yi tatafi da ita makaranta.
Har su Hamida sai da suka ce Amina tayi kiba yanzu ko Hamida albarka.
Ita kanta Aminar tana jin Canji Ajikinta ammh bata Damu ba Sai itama take Tunanin cin abincin datake yi shiyasa da kuma kila girman da batayi bane abaya sai yanzu take yi.
Ranar ma suna shiri zasu makaranta da Safe Dakyar Amina ta iya saka Rigarta ta matseta duk da an kara Budeta.
Ta saka tana Nishi kafin tace"ni dai girman nawa bai zo min da Dadi ba..Ku kalle har Tumbi fa na fara..!
Suka bi Cikin nata da kallo kafin su saka Dariya Hamida tace"Kirjinki wlh sun fi nawa..Tumbi kuma wlh gashi nan Hanne..!
Tafada tana Taba cikin Amina Daya Fara tasawaa taji Tauri ta cire Hannunta Tanacfadin"Sai Taurin bala"i..!
Hanne tace"Ke kuwa wannan Abincin Datake narka ai ba Lafiya bane..Dole ta Ijiye Timbi taurinsa kuma Uban Madaran Dake sha ne wlh in baki Daina ba kikayi Kiba Ya Danmallam bazai je dake madina ba domin in kika Hau seleken awon Nauyi aka ga kin yi kiba bamai zuwa Dake..!
Amina ta balla mata Harara tana Fadin"Dama wake son zuwa..?
Dariya suke mata ita kuma tana masifan ita ba inda zata je Daganan suka shashantar da mganar.
Aranar da sukaje gaida mallam kan su tafi makaranta da suka fita yana Tare da Hajiya ne sai da yayi mata mganar Kibar da Amina tayi hajiya tace kila gabobin girman nata basu bayyana ba sai yanzu Shima sai ya yarda da Haka.
Duk wanda ya ganta bai kawo ma kansa wani Tunani sai Tunanin gobobin girma ne suka bayyanan mata Mamanmu kuma bata bi ta kan Amina ballatana ta iya ankarewa da wani abu na Faruwa Anty Amarya kuma sai tayi sati ma bata ga Amina ba in ma ba ta ganta ba, bata ma Tsayawa kare mata kallo balle ta zargi wani abi zai faru.
Ana cikin haka aka fara Biyan kudin jarabawar fita ta su Akilu Hajiya tace a biyama Amina sai maallam yace da Aminar da sa"adatu da Hannatu da Hamida duk a Biya musu su zana a SS2 dinsu da hajiya ta nemi jin Dalili sai ya sanar da ita cewa in Umaru yazo ya tafi da Amina madina su hanne kewa zai musu yawa sannan sun ma isa auran suma da su zauna suna Damuwa da rashin Amina suma zai aurar dasu nan da wattani kadan zasu cigaba da zuwa hadda da islamiya kafin Mazajen nasu su bayyana Hajiya bata yi gaddama ba Tunda daman Jafar da Nasir sun fadamata cewa Karatun SS3 din duk maimaici ne da Reviosion shiyasa sai tayi na"am da mganarsa acikin Satin akaje aka biya musu su shida har da Akilu da Zubairu.
Amina da taji murna kamar me baza"a rabata dasu hanne ba Sa"adatu ne bata so ba,tayi ta kuka Anty Amarya ko ta kanta bata bi ba, abunda ke gabanta yafi karfi wannan iskancin na Sa"adatu.
Allah shi ke batar da Tunaninmu wani Lokaci ga abu a kusa damu sai mu Dade bamu Fahimcesa ba..!

********


Danmaallam achan madina Ko Sarood sai da ta Tausayamai yadda ya kwallafa rai akan cikin Sakina sannan yazo kuma ya tafi Ranar da Mallam ya kirasa ya fadamai da Zazzabi ya kwana,kwanansa biyu agida baya Fita Tana kula dashi,Ita kanta ta Damu sosai sai ta sakamai kuka ganin ya Daina Cin abinci sosai ballatana yawan mgana,da taimakon Mallam da Hajiya da Aliyu ya Dawo daidai da kuma Sarood itama tayi kokarin matuka wajen kula da shi Sosai take basa Tausayi tana da sanyin Hali kamarsa da kuma Hakuri shi kanshi yanzu ya Fara Tunanin mafitan da Aliyu yaso ya Nema tun farko yaki yarda da mganarsa ammh a yanzu yafi Sarood Damuwa Tsausayi take basa ita macece mai Rauni sannan kuma yaji yana Fatan in bai samu Haihuwa ta bangaran Sakina ba,me zai hana ya roki Allah ya basa ta bangaron Sarood Amina dai bai ma saka ta a Lissafinsa ba bai Taba kawo mata Daukan cikinsa nan kusa ba..!..abunda bai sani ba Daman Sau tari Allah yafi bamu abun da muke nema a inda bamu taba Zato ko Tsammani ba..!
Washegari yana cikin makaranta ya kira Aliyu da niyar ya Tuntubesa da mganar sai gashi shima ya fara mai mganar bayan sun gaisa Aliyu ke tambayansa matsalansa da Sarood ya ake ciki..? Yace mai har yanzu ba Sauki domin ko ya jaraba jiya iyau ne.

Aliyu ya kada baki yace"Shehi ni dai kaki jin Shawarata ne..Naso ka kira mallam ka sanar dashi matsalanka kila ya samo maka waraka Tunda yafimu sanin abubuwan da suka Shafi addini da irin wannan banace ka yarda wani yayi maka ba kasa aranka bamai yi sai Allah kuma wajensa kake neman waraka..!

Umar yayi shuru kamar bazai yi mgana ba Jin haka yasa Aliyu yace"Tunda Sakina ga matsalan da ake Samu Shehi me zai hana ka Jaraba Sarood din itama mu gani..!
Nasan fa kana son ya"ya bama kai da abun nan yake Faruwa Dakai ba ni kaina abokinka i feel ur pain Umar ina Fatan kai ma ka ka ijiye masu yi maka addu"a watarana..!
Danmallam ya gyada,kai kamar Aliyu na ganinsa kafin yace"Shikenan Aliyu zan jaraba shawarka..bari na Kira mallam muyi mgana..!
Aliyu yaji Dadi suka rabu bayan ya Bisa da addu"an Allah yasa adace a samu waraka kamar yadda suke fata..
Nan take ya kira mallam sai dai baya gida yace mai yana Jigawa sun zo Taro ne nasu na Da"awa ammh bazai Dade ba zai koma gida in ya koma zai kirasa.
Dayake abun na ransa kuma ya Kudiri niyar fadama mallam komai yasa bayan awanni kadan ya Sake kiran mallam din Lokacin har ya koma gida Misalin goma na Dare anan madina Nageria kuma suna fitowa sallar mangariba.
Mallam Shashensa ya koma abunda ba Dabi"arsa ba sai sun gama Sallar Isha"a yake shiga gida ammh ganinsa da waya yasa aka san uziri ne ya taso ma mallam din.Tabbas Uzuri ne domin yadda yaga Umaru ya Damu yasa yasan ba lafiya ba wani abu na Faruwa.
Bayan ya Dauka sun gaisa da Tambayan gida da iyalai kamar kullum mallam yace"Umaru meke Faruwa ne.?
Wannan kiran naka bana Lafiya bane ko..?
Danmallam ya kaskastan da kansa Waje ma ya fito saboda ba ya so Sarood taji mganarsu cikin Ladabi yace"Eh ba Lafiyan ba mallam matsala ne dani tuntuni nayi iya bakin kokarina ta bangarena ammh abu ya ci Tura shiyasa na yanke Shawaran kiran ka na Sanar Dakai..!
Mallam ya koma ya zauna gefen gadonsa domin kurya ya shige kada ma wani abu ya katsesa a yadda yaji Umarun yasan da wani abu.
Cikin Dattakonsa yace"Ina jinka..Allah yasa Zan iya maka mganin matsalan ka Umaru..!
Cikin Kunya kamar yana ganinsa ya farama mallam bayanin Tundaga Farkon matsalan har karshe da Mganin Shafan Aljanun da siya mata Tayi amfani dashi ammh matsalan kuma bata kare ba har alokacin..!
Mallam yayi shuru yana jinsa har ya gama kansa ya Daure na wani Lokaci,daya sa ya kasa mgana Har sai da Umar ya Kira sunansa sannan ya amsa Cikin Alhininsa yace"Ta bangaranka da ita Sakinar lafiya kalau ko..?
Duk da yasanni ammh so yake ya Tabbatar in da lafiya ai in ba lafiya ba ta Dinga samun ciki hartana barinsa ba.
Danmallam ya amsa da Eh cikin kunya aransa yana addu"an Allah yasa kada mallan ya sako Amina Har ga Allah bai shirya fadamai ya haikema wannan yarinyar ba duk da ba Haramci yayi ba matarsace ta sunna.
Sai Addu"arsa ta karbu mallam bai Tsawaita tambayarsa ba illah kai da ya Jinjina kafin yace"Umaru kana jina ko..?
Ka bani nan da zuwa gobe zan yi Bincike na acikin littafan malaman musulunci sosai sunyi bayanai game da ira iran wadanan matsalolin naka..Insha Allahu zuwa gobe zan kiraka da kaina nayi maka bayanin komai..!
Danmallam yace"Shikenan mallam..Allah ya kara girma Allah ya kara nisan kwana..!
Mallam ya amsa da Ameen Ameen ya Cike da fadin"Kada ka damu da Yardan Allah zamu samu mafita..Domin Qur"ani waraka ne gamu bayin sa kaji ko..?
Ya amsa cikin yakinin kamar ma ya Samu mafitan daganan sukayi sallama Mallam ya koma yayi jugum yana nazarin matsalan Umar..
Tabbas yana da zurfin ciki sannan yaga Hakurin ita Saratun,bazai ce ga matsalan ba kai Tsaye tunda Basir ko Sanyi na Haifar da haka ammh nasu sai dai Raunin gaban namiji ba ta ki yin amfani ba gabadaya sannan shi da Sakina lafiya lau ita Saratun ne matsalan.
Lalle akwai wata mgana a kasa shi ba Malamin Duba bane ko na Shirka shi malamin sunna ne da Qur"ani in an kawo matsala ba kansa Tsaye yake yi ba yana Duba Littafan addini na malamai da kuma Qur"ani Domin neman mafita sannan akwai Irin irin matsalolin nan na Sihiri da malamai Dabam dabam sukayi littafai da Dadama Domin warware ma Mutane kai dasamun Mafita shima haka zai yi bazai yi zargin wani abu kai Tsaye ba sai ya bincika.
Ana Idar da sallar isha"i ya Sake dawowa cikin gida yau ko Aba basu Tsawaita Hira ba sukayi sallama ya wuce Shashensa Ranar hajiya ke da Turaka ko da tazo ta iske malama nata Nazarin wasu littafai sama sama ma suka gaisa abinci ma sai da ta matsamai yaci kadan
Abun bai bata mamaki ba taga ko barci bai kwanta ba tasan sa da son nazari wani Lokacin ammh bai hanasa kwanciya ammh sai gashi ya kasa barci data tambayasa yace yana wani Nazari mai muhimmaci ne,tayi kwanciyarta in ya gama zai zo ya sameta Dole ta shiga ta kwanta ta kyalesa.
Shi kuma sai wajen biyu na Dare ya gama Bincikensa sannan bai kwanta ba ya Dauro alwala yayi nafilfilu da addu"o'i sannan ya kwanta wajen uku da Rabi Biyar na cika ya Farka ya Tada Hajiya ya fice zuwa masallaci.
Sai Chan Safe ya Dawo Shashensa ya Tsaya masallaci sun yi meeting da Dattajan anguwannin kusa dasu.
Wanka kawai yayi ya karya Lokacin Hajiya ta koma bangaranta ya Kira Umar bai Dauka ba sai da ta katse sannan ya Kirasa yana aji ne yana karatu yana ganin kiran maallam ya nemi lamini ya fita waje ya kirasa.
Bayan gaisa kamar yadda suka saba Mallam ya fara mgana cikin Dattakonsa kamar haka.

"Umaru ka yarda da Allah shine mai yi kuma mai hanawa..Sannan ka yarda da duk abunda ya samu bawa Daga garesa ne sannan kowata Lalura daga garesa ne sannan Waraka ma yana wajensa ko..?
Danmallam ya amsa da eh Mallam ya Cigaba da nuna mai Duk abunda zai Faru da bawa koma ya faru kada ya Zargin kowa ya Dauka Daga Allah ne kuma garesa zai nemi waraka bai Fito ya mai bayanin Sihiri bane ammh Cikin Dattakonsa yace"Ka san Acikin Qur"ani akwai ayoyin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login