Showing 126001 words to 129000 words out of 265571 words

Chapter 43 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28926

kirji yana kallonta Amina ma ita take kallo ita aranta ma Dadi taji Allah yasa taki Bude Dakin ya maidata gida.
Cikin Kaushinsa yace"To yanzu ya kike son ayi sakina..?
Kai Tsaye tace"kai ka sani..!
Daga haka ta koma ta zauna tana Jijjiga kafa Lokaci Daya tana Hararan Amina Dake ta sharan kwallah.
Bai ce komai ba ya kalli Amina yana nuna mata hanyar Dakin Sakina Lokaci daya yace"Zo ki wuce..!

Kamar tayi mgana sai kuma ta fasa ganin yana mata wani kallo Sakina da mamakinsa ya cikata na ganin Dakin daya nuna ma Amina Dakinta ne.
Sai dai batayi mgana ba sai da taga Aminar ta nufi bedroom dinta sannan ta Mike kamar kububuwa sai gata gaban Amina ta tare gabanta Cikin Zare mata ido tace"Kan uba..Badai Dakina ba..Allah ya Tsareni wannan kazamar ta shigarmin Daki..!
Sai Amina ta Tsaya ta kasa gaba ballatana baya Umar yana Tsaye inda yake yana kallon Sakina da Idanuwansa da suke kokarin bayyana yanayin dayake ciki.
Kokarin Daidaita kansa yake yi yasa bai yi mgana ba Sai da yaga Sakina ta Hankada Amina sai da ta kusa kaiwa kasa tayi Saurin Dafa Kujeran Dinning
Sakinar kuma ta jawo kofarta ta Rufe da makulli tana fadin"Yau ni Sakina naga Rainin hankali..Dakin nawa zaka saka Kishiyata..?Allah ya tsareni ma da ta zama kishiyata Har Abada..!
Take fada tana jijjigan Jikinta Danmallan yayi tsai yana kallon wani waje bai yi mgana ba.
Babu makullin daki ko daya a hannunsa na Gidan duka yana hannun sakina Sauran kuma suna gida wajen Hajiya,sannan akwai wajen Jafar,Shi bai taba Hausan makullayen gidan sa su zauna awajensa ba.
Bayason su yi wani abu gaban wannan yarinyar girmansa ya Zube shiyasa ya dinga maimaita sunan Allah har ya samu ransa yadan sauka Cikin Sanyinsa ya juya yana kallon Sakina kafin ya mika mata hannu yana Fadin'"Naji bazata zauna adakina ba..da Dakin ki ba.Bani key din Dakin Sarood sai ta zauna aciki..!
Shekeke take kallonsa sai dai taji shakkansa Lokacin daya kara sakarmata wani Kallo yana fadin"Ko shima bazaki bani ba..?
Jin haka yasa ta nufi kofar Dakin ta saka makulli ta Bude kada ta basa ya Bude Dakinsa tunda duka suna Hade ne waje daya gwara Dakin Sarood din ita kam banda nata Dakin kuma shima ban da nashi.
Tana gama Bude Dakin ta koma gefe tana kallonsa bai kara ko kallon inda take ba ya kalli Amina Dake dannen kukanta yace"Shiga..!
Ba musu ta shige shi kuma ya Dauki ghana dinta guda Biyu yabi bayanta Tana Tsaye Tsakiyar Dakin ko zama ta kasa yi bai ko kalleta ba ya ijiyemata kayanta nan ya fice tana bin Dakin da kallo ya sake shigowa ya ijiye mata Dayan ghana din ya Sake fita wannan karon har yana bame mata Kofar ta bisa da kallon ganin ya Ficen ne yasa ta sulale nan kasan Cafet din Dake Dakin ta hada kanta da Bango ta fashe da kuka,kukan da ko Rasuwar yaya batayisa ba kukan kewa da rasa wani abu a Rayuwa ta yaya zata fara zama in da ba hanne ba Hamida ba mamanmu.!
Tuna haka yasa ta kara sakin wani kukan ta dora kanta jikin gadon ta cigaba da Rera kukanta,Bata ma ji shigowarsa ba sai karan bude kofa taji tana Bude ido ta gansa ya shige wani kofa Dake Dakin ya kullo,sai tayi tsit tana ware idonta da sukayi zuru zuru da kuka duk ta wani yarkace ko motsi bata karayi ba ita azatonta uwar Daka ya shiga shiyasa ta kasa motsi sai chan taga ya fito Fuskarsa na Digan ruwa alamun alwala yayi ko barayinta bai kara kallah ba ya sake Ficewa ya bame mata kofar yana Fita ta Dora hannu akanta ta fashe da kuka tana fadin"Na shiga uku ni Amina..!
Sai kuka harda Birgima a kasa kamar wata yar yarinya ita kadai bamai lallashinta.
Tanayi tana rufe bakinta kada ya jiyota ya shigo,yadda take kukan sai ka Tsausayamata kuka ne Dake fitowa Daga kasan ranta.

Sakina tana tsaye tana jijjiga jikinta ya fito nan saman cafet din falon ya Daidai gabas ya tada sallah Shafa"i da wuturi yayi sannan ya zauna yana Tasbihi da hannayensa ko barayin Sakina bai sake kalla ba har ya gama yayi addu"a ya shafa Rigarsa ya Cire ya rataye ta nan saman kujera daga shi sai dogon wando ya samu Filon filon kujerun ya jera saman kujera 3siter ya kwanta Kansa na kallon Rufin Falon hannayensa kuma ya Saka ya Dunkule su waje daya ya Dora su saman Filo kansa na kai.
Wayarsa daya ciro cikin aljihun rigarsa ya ijiyeta nan saman center Table din Dake falon,Sakina sai Binsa take da kallo ta kasa mgana sai alokacin kuma jikinta yayi sanyi mganganun Anty suna dawo mata da tace kadatayi wani abun da ran Umar zai baci tabi komai a sannu ammh ita Kishi ya Rufe mata ido da kuma mgaganun Aliya dazu da sukayi mgana ita ta kara tunzurata.
Takowa ta farayi cikin Falon Cikin Sanyin jiki a gabansa ta Tsaya tana kallonsa kafin ta sauke numfashi tace"Bari na bude maka Dakin ka..!
Baice mata komai ba ta koma ta Bude Dakin sannan ta Dawo gabansa tana Fadin"tashi ka shiga ciki Habibi..!
Mikewa yayi ta Dauka zai shiga Cikin ne sai taga ya isa ma kunni wutar Falon ya kashe duhu ya gauraye wajen gabadaya ido ta zaro tana Fadin"Habibi...!
Ko kallonta bai yi ba ya koma ya kwanta Har da Juya mata baya Sakina taji ta Muzanta Sai ta Duka gaban inda yake kwance tana saka hannu ta riko hannunsa tana fadin"Habibi..Dom...!

"In kika kara tabani Sakina wlh tallahi zan sharara miki mari..Zaki ga Oder side of me da baki taba gani ba..!

Ya katseta Cikin Tsawa Daidai Lokacin daya juyo yana kallonta Cikin hasken Dake shigowa ta windows din Falon Baya Sakina taja tana zaro ido kafin tace"Ni zaka mara Habibi..?
Ni kace zaka mara saboda ka kawo wannan kazamar yarinyar nace bazata shiga Dakin ka ba..?
Wani matsiyacin kallo yake binta dashi bayaso yayi wani abu Saboda Amina na gidan yasa ya koma ya kwanta ai sai Sakina ta saka kuka ta Durkushe a wajen tana Fadin"Shikenan..Nagode yanzu har ka fara wulakantani saboda wannan yarinyar Habibi..?
Saboda na hana ta shiga Dakin ka kakemin ihu haka..?
Yar Cikin ka ce fa karamar yarinya da bata isheka komai ba..!

"Karamar yarinyar da kike mgana akanta yanzu Daya kike da ita a wajena Sakina..Dani da mutanen da sukasan abunda suke yi..!

Ya katseta a fusace,Sakina ta ji kukanta ya Tsaya Cikin mamaki tace"Daya fa take dani kace Umar..?
Saboda ma ya tabbatar mata yasa ya Mike Zaune yana fadin"Eh..Kamar yadda kike matata haka take matata..Kamar yadda igiya uku ta hau kanki..Nawa itama suna kanta Sakina..Saboda haka dake da ita Daya kuke awajena..!
Galala tayi tana Binsa da kallo Kafin tatashi Fuuu ta je ta kunna wuta Haske ya bayyana kafin ta Dawo gabansa tana kallonsa cikin karaji tace"Maimata abunda ka fada..Dazu baka kallon idona yanzu kuma idona na cikin naka nake so ka maimata Umar..!
Karamin Tsaki yaja ya koma ya kwanta yana Fadin"Sai ki sani na maimaita din..!
Sakina idonta ya rufe ta mike tana Fadin"Har gaban abada bazan zama Daya da wannan kazamar yarinyar ba..Wacece ita..?Yaushe take..?
Wlh ita bata isa in yi zaman kishi da ita ba in nayi da Sarood ita bata kai wannan matsiyan ba..Amina ba Sa"an auranka bace Umar ba sa"an zaman kishina bace..!

Kamar ya Rufe ta da Duka haka yake ji kai Tsaye ya mike zaune yana kallonta yace"Wacece ita kike tambaya Sakina..?
Kinsan wacece ita ai..in ma kin manta bari na tuna miki..Ita diyar BABA SA"IDU ce kuma Diyar YAYA ce..Sannan Unarnin HAJIYA DA MALLAN NE..Ta riga ta Hada mutane masu Daraja atare dani..Ko ba aure Tsakanina da ita ni me rike Amina ne acikin gidan nan Sakina ballatana da aure Tsakanina da ita in kina Tunanin Zata bar gidan nan to kidaina kamar yadda zaki zauna itama haka zata zauna..Kuma da kike mganar Ita ba sa'an aurena bace..Daman sai sa"an auranka zaka aura..?
Wlh in da ana bin chanchanta har Abada Dake sakina baki CHANCHANTA dani ba..!

Yafada yana nuna ta da yatsa cikin fushi ido ta zaro mgana take son yi ya hanata Cikin Kaushinsa yace"Ba shawara nake nbaki ba..ba kuma Umarni ba.ki natsu ki zauna lafiya da yarinyar nan domin zamanta Daram acikin gidanan in kika ki natsuwa ke kika sani ni dai tafiya zan yi..in kin kama girmanki ta girmamaki in baki kama ba ta fiki iskanci sai ku goga wata dai bata isa ta kori wata ba..!

Sakina taji jikinta yayi sanyi me kalaman Umar suke nufi..!?
Gabanta ya fadi kada kishinta ya Bullo mata wani sabon aiki Dakyar ta Hadiye miyau tana Sharan kwallah tace"To don Allah in ka tashi tafiya ka tafi dani Habibi..wlh bazan iya zama da yarinyar nan anan gidan ba..!

Umar ya kalleta daga sama har kasa kafin ya koma ya kwanta yana Fadin"Sakina na yi rantsuwan bazaki koma ba yanzu
Ki tashi ki bani waje bana son yawan mgana kaina ya riga ya fara ciwo..Kada zamanki agabana yasa na rasa Cont????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  rol dina..!
Batayi musu ba ta mike Cikin kaushinsa yace"Ki kashe min hasken da kika kunna min..!

Ta juyo tana kallonsa kafin tace"Bazaka ko..!
Kallon da ya bita dashi ne yasa tayi Saurin yin gaba Hasken ta kashemai ta Fada Dakinta gabanta na Fadi Gabadaya mganar Umar na ita ma bata Chachanta dashi ba ya Tsorata ta In ta Kira Anty ta Fadamata tasan sai taci Zagi Allah yasa ba abunda suka Binne bane yake son ya bayyana ba..
Da sun shiga uku kuwa..!
Mafarin komai in ya lalace ai sun gama yawo..!







*28 September 2022*
*Janafty*

*TFZB2002*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*

Karfe hudu na asuba ya farka kamar yadda ya saba,Kwata kwata bai ji dadin barcin ba akan kujera sannan zuciyarsa tana cunkushe ne ya dade bai samu barci ba kuma kasala ya rufeshi ya kasa tashi yayi ko nafila ne.
Sai da asuban ya shiga dakin nasa yayi wanka ya dauro alwala Jallabiya mai ruwan madara ya saka da Hula ya Dau cashabahansa ya fice zuwa masallaci ko ta kan Sakina bai bi ba ballatana wata Amina.
Sai shidda saura ya shigo gidan,yana shigowa tsakiyar falon suka ci karo da Sakina ta fito daga dakinta yarkace yarkace da ita idanuwanta sun kumbura sannan kanta ba dankwali kanta ba kitso gashinta ya baje kansa tana sanye da rigar barci mai taushi iyakarta gwiwanta ayanayin yadda yaganta sai da ya kara kallonta ganin yanayinta.
Kamar zai mata mgana sai kuma ya fasa ya dauke kansa zai shiga Dakinsa Da hanzari ta daga kafa zata bisa jin takunta yasa ya Dakata bai juyo ba taji muryansa yana fadin"Ina zaki..?

Cak ta tsaya jikinta yayi sanyi kanta ta maida kasa kafin tace"Da..Dama zan gaisheka ne Habibi..!
Shuru yayi mata bai yi mgana ba taga yana shirin shigewa ya barta yasa tayi saurin cewa"Ina kwana Habibi..!
Kamar bazai tankata ba sai kuma ya amsata kamar baya so da Lafiya Lokaci daya ya shige dakin nasa ya banko mata kofa saman fuskarta baya taja Hannunta Dafe da kirji tana fadin
"Na shiga uku ni Sakina..!

Kasa tsayuwa tayi kamar mahaukaciya haka ta kwashi gudu zuwa Dakinta saman gadonta ta koma ta Zauna gabanta na fadi meta aikata kenan .?Jiya ko barci batayi ba in ta tuna Kalaman Umar zuwa gareta.
Taso ta kira Anty tun jiyan sai ta kasa Tasab Halin Anty in taji abunda ta aikaata sai ta Zageta saboda haushi Saboda sai da ta tausheta akan kada tayi wani abu sai ta tambayeta yanzu in ta Kirata ta fadamata abunda ya faru ta tabbata sai Anty ta mata fada sosai.
Sai dai bata da wata mafita Anty zata kira ta fadamata abunda ke faruwa ko zata samamata mafita.
Wajen shidda da rabi ta dokama Anty Amarya kira tun da taga kiran tasan ba Lafiya cikin Tashin hankali ta Daga kiran tana fadin"Sakina kada ki fadamin kin kara aikata sakarcin naki ..?
Sakina tafara Fiki Fiki da ido tana fadin"Anty...!
"Don ubanki ki fadamin abunda ya faru..!
Sakina cikin sanyi ta fara fadamata Duk abunda ya faru jiya har zuwa yau Anty Amarya ta mike Har hijabin jikinta datayi sallar asuba na neman Hardeta ta fadi ta Dafe jikin gadonta Cikin Firgici tace"Kikace Umar da kansa yace baki Chanchanta dashi ba..!?
Sakina tace"Wlh haka yace Anty..!
Anty Amarya bakinciki suka kusa kasheta alokacin cikin Tsawa tace"Sakina na rantse da wanda Raina ke hannunsa in kishin ki na banza yayi sanadiyar Tono Abunda muka Binne da Dadewa babu ruwana..zan zame kaina ne na barki ke kadai..Kin kuma Tabbatar ma kanki wannan kokawar tafi Karfinki..!
Jin haka yasa Sakina ta kara Rudewa kawau sai ta saki kuka tana Fadin"Anty don Allah kiyi hakuri..Ba laifina bane..Kishi ne ya rufemin ido kinsan ina son Umar bazan juri ganinsa da wasu matan ba..Sannan Aliya tacemin kada na barta ta zauna Dakin Mijina..!
Anty Amarya ta lailayo Ashar ta saki kafin tace"Aliya Burauban ki Sakina..Ina ruwanta da wannan mganar ban fada miki kada kiyi wani yunkuri sai nace ba..?
Da kika kwantar da hankalinki Lokacin Sakaryan balarabiyar nan ba gashi yanzu muke da riba ba..Itama in kin kwantar da hankali kamar haka zata zama nayi alkawarin ko zan rasa komai Amina bazata yi zaman kishi Dake ba Sakina ammh shegen Taurin kan ki yana neman jawo mana matsala..!
Sakina na sharan kwallah tana Fadin"Nidai Anty ki fadamin ya zan yi..?Wlh ko son ganina bai yi ina mgana Dakyar yake amsa mun..!
Anty Amarya tace"sai kin bata komai kizo kina Damunna da kukan banza..Yanzu ina ita Aminar..?
Sakina ta tabe baki kafin tace"Tana chan Dakin Sarood..Tun jiya bansan isalinta ba..!
Anty Amarya tace"Shi kuma fa..?
Sakina tace"Ya dawo daga masallaci ya shiga Dakinsa ya kulle..!
Anty Amarya tace"To ki tashi ki shiga kitchen ki hada breakfast ki yi wanka da kwalliya kije ki tasosa ki basa Hakuri..Mganar Amina kuma kada ki shiga mganarta ki koma gefe ki zama yar kallo kawai a na nan ana aiki akanta kin ji ko..?
Sakina ta gyada kai kafin tace"Anty Dakyar ya Saurareni fa..!
Tsaki Anty Amarya taja kafin tace"To Tunda bazai Saurareki ba..ki Zauna..!
Daga haka ta katse kiran tana Huci ita Kadai adaki Sakina fa Bata san ciwon kanta tasan kudin data kashe kafin Umar ya kalleta da sunan so..?
Tasan wahalan data sha kafin Umar ya kalleta da kalmar aure..?
Batasani ba shiyasa take son bata komai ba bazata yi wannan saken ba in abubuwa suka fara Lalace mata bata samu Cikar Burinta ba anyi ba ayi ba kenan ko zata rasa komai sai Sakina ta zama Tauraruwa awajen Umar da danginsa gabadaya Wata mace bata isa ba kuma tayi kadan.

Ashe Sakina duk zaman data ke yi batayi sallah ba,Sai da suka gama waya da Anty tatshi ta Dauro alwala tayi sallah sama sama ta Daura Zani saman rigarta ta fita zuwa Kitchen,Sakina ta iya girke girke Anty Amarya bata barin ya"yanta haka tasan duk cikar ya mace in bata iya Girki ba Saura ce shiyasa ba wacce bata koyama girki ba hatta da Sa"adatu da Sabeeha..!
Cikin Hanzari take aikinta Cikin Lokaci ta kamallah Doya ta Dafa sai tayi miyar kayan miya ta yayyanka mai kwai,Sai ta Dafa Ruwan tea ta soya Buredi da kwai saman Dinning ta jera komai kafin ta gyara Kitchen din sannan ta koma Daki ta shiga wanka.
Bayan ta fito ta shirya Cikin Doguwar rigarta ta atamfa ta gyara gashinta tayi Daurinta na Maryam babangida..!
Gabanta fadi yake bata san wani Tarba Umar zai sake mata ba ta zata Ya kulle kofar ne sai da ta Tura taganta a Bude Cikin Takunta na Takama ta shiga Dakin da sallama sanin Halinsa yanzu sai ya maidata waje.
Yana zaune a kasa saman Darduma yana karatun Qur"ani a hankali cikin Sautinsa mai Dadin Sauraro Dakin tabi da kallo komai neat,Gado ne kawai sai wardrope sai ma"ajiyar takalma sai cafet babba da ya malale Dakin gefen gadon ta zauna tana Jiransa ya idar da karatun ammh wajen Minti Goma sha biyar bai rufe karatunba sai ta fahimci in tayi shuru to sai rana ta Dago zai tashi daga wajen nan.
Gyaran Murya tayi kafin tace"Ina kwana..Wajen ka fa nazo Habibi..!
Ta karishe Fada Cikin shagwaba.
Yana jinta yayi kamar bai ji ba sai da ya kai inda yaga damar Tsayawa sannan ya rufe Qur"ani ya Daga hannu Sama yana addu"a tare suka shafa ya mike ya ijiye Qur"anin saman Side drower din gadon,Yana kokarin Ninke Darduman ne tayi saurin mikewa ta karba bai hanata ba ya sakarmata Ta ninketa ta maidata wajen zamanta tana gani ya hau saman gado ya kwanta harda juya mata baya.
Bata damu ba ta Durkusa saman kafafunta tana fadin"Don Allah kayi hakuri Habibi..Da abunda ya faru sharrin Shedan ne da kuma Kishi..
Ammh nayi alkawarin bazan kara ba..!
Kaji..!
Kamar bazai tanka ba sai chan taji yace"Zaki kara Sakina..!
Da sauri tace"Allah bazan kara ba..!
Ajiyar rai ya sauke kafin ya juyo yana kallonta Lokaci daya yace"Ya wuce..!
Mirmishi ta saki kafin tace"Nagode..Ga breakfast chan na gama Hada maka ka taso muje ka karya..!
Lumshe ido yayi kafin yace"Am ok..Bana jin yunwa..!
Marairaicewa tayi tana fadin"Haba Habibi..Ko baka hakura bane..?
Da Sauri yace"Bani da riko kema kin sani..!
Jin haka yasa tace"To in hakane ka taso muje..abunda kafi so na Dafa maka Doya..!
Muskutawa yayi ya mike zaume yana Fadin"Naji..Zan yi wanka ne ganin nan fitowa..!
Taji dadi sosai ta mike tana Fadin"Bari na taimaka maka Habibi..!
Duk yadda yaso ya yakiceta bata yarda ba Tun yana kin sakin mata har ya sakarmata ita ta taimakaima ya Cire kayansa ta hadamai ruwan wanka ya shiga yayi wanka daya fito ta taimakamai ya shirya Cikin Riga da wando na pakistan sannan ta Tarosa Hannunta Cikin nasa zuwa Falon har saman Dinning jikinta na rawa ta yi Sarving dinsa kallonsa tayi tana zubamai Ruwan tea din dayaji Ganyen shayi masu kamshi tace"Kana so da yawa ne Habibi..?
Kai ya girgizamata kafin yace"Rabin kofi..!
Haka kuwa ta sakamai ta Turamai gabansa baya son madara siga ya kara kadan ya fara sha Bai san yana jin yunwa ba sai da ya gansa gaban abinci Rabonsa da abinci tun jiya da rana..
Ita Tea ta hada maa kanta tana Hadawa da Buredi da kwai shi kuma yana cin Doya daman mutuniyarsa ce.
Ranta yayi mata Fes ganin ya sauko har suna dan mgana jefi jefi Shine ma yace mata"yana da kyau in ana cin abinci a Dakata da mgana har sai an kamallah..!
Daman sai yayi mgana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login