Showing 153001 words to 156000 words out of 265571 words

Chapter 52 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28942

tace"Dayyaba ni Hankalina yaki kwanciya gani nake yi abubuwa duk suna ta lalacemin Tsarina duk ya lalace..Umar din ya tafi ni Kawai Burina ya Dawo ya Dauki Sakina su koma,in har ya tafi mallam yace ba lalle ya dawo nan kusa ba kinga mallam da Hajiya haka zasu gaji da ganinta ahaka su raba auren daman wanchan balarabiya Hoto ce itama in ta gaji zata kara gaba ne..
Mamanmu tace"Sosai ma ina amfani Zama da miji Hotiho ba wani amfani ina mai Tabbatar miki bazata zauna ba..Ki kwantar da Hankalinki Saura Kiris burinmu ya cika kada ki manta Sakina ba Juya bace tana samun cikin yana Barewa ne..!
Anty amarya tace"Dayyaba shine abun Damuwata ko an samu cikin baya Zama na fara Tunanin akwai wani a kasa..!
Mamanmu tace"Ko..?
Kanar na menene..?
Anty amarya tace"Ciki wajen sau Hudu da an sanu sai ya lalace anya Dayyaba..?
Mamanmu tace"To kin sa malam ya Duba mana kuwa..?
Tace"Eh ya Duba yace bai ga komai ba..Ammh ni haka kurum nake ji akwai wani wanda muke Tufka Daga Gefe yana mara warwara ko shakka bana yi.. kinsan daman ya taba Fadamin acikin matan mallam akwai wacce itama bata zauna ba..bai dai Fadamin sunan kowa ba.
Mamanmu tace"to wa kike Zargi..?
Anty Amarya tace"Cikin matan mallam ne dai..Ko Haj.Nasara ko Hj.Uwani..Akwai wacce acikin su bata so mu cimma namu burin..!

Mamanmu ta zaro ido kafin tace"in ma sune to saboda mene..?
Anty amarya tace"Saboda cikar Burinta itama..Kamar yadda muke son mu cimma namu Burin..!
Mamanmu tace"Tabdijam akwai kura Tsugunno bata kare mana ba..!
Ni fa basu nake zargi ba ina Tunanin ko dai Hajiya ce bata so Sakina ta Haihu..?
Anty amarya tace"Ba Hajiya bace..Bata yar da za"ayi ta hana Sakina Haihu wa kada ki fa manta Umar D'anta ne..zata fi kowa son ganin kwansa a duniya..!
Mamanmu ta jinjina kai kafin tace"Kuma fa hakane..!
Ni ban ma taba kawo wannan Tunanin ba sai da kika Fada na gane zai iya Faruwa..!
Anty amarya tace"Ai ki bar mugu..Bai da kama Dayyaba..Da mugu nada kama da Tuni Sa"idu da ya"yansa basu baki Dukkan yarda ba..Da mugu nada kama da Yaya bata taba Sakin miki Ragamar ya"yanta ba har Abada..!
Mamanmu ta bata rai kafin tace"Bangane ba..?
Ki sa min jaye mugaye zaki ce..!
Anty amarya tayi wata Dariya kafin tace"Ban kai ki mugunta ba Dayyaba. ina mai kara gayamiki ban kai ki ba..Domin ko ni sanda kika zomin da Fuskarki ta Dayyaba domin mu Hada Hannu na Girgiza ballatana Sa"idu da ya"yanku..?
Ina mai Tabbatar miki kiji Dadinki yanzu ammh in alalan geren mu ya tashi yin Ruwa da Tsami wlh naki sai yafi Nawa Tsamewa..!
Mamanmu tace"Da izinin lahi bazan ga haka ba..Ni Dayyaba Nasara na sani ba Faduwa ba Madina..!

Dariya tasake yi kafin tace"Muna fatan haka yanzu ba wannan ba yaushe zamu hadu..?
Ya kamata mu sauya Tsarin mu sannan mu san ta yadda zamu gano wanda ke kokarin batamana aiki..!
Mamanmu tace"Ina so mu hadu bana samun Lokaci ne gida ba kowa sai ni kadai..Hamida bata nan tana gidan Amina..!
Anty Amarya ta Zaro ido kafin tace"Wata Aminar..?
Mamanmu ta tabe baki tana fadin"Wacce kika sani mana..Bakisan suna gidan Amina ita da Hanne ba Tun Ranar alhamis da yammah Hajiya ta turasu..!
Anty Amarya ta mike Daga Zaunen Datake gefen gadonta tana fadin"Kan burauba..Bansani ba..Naji dai jiya Sa"adatun na fadin bata ganinsu a Hadda ban maida mganar mai ma"ana ba shiyasa ban bincika ba..Na Shigesu Dayyaba Sakinarma tun aranar da Umar ya koma tana Dutse..!

Mamanmu tayi shewa kafin tace"Au to..Aiko tayi wauta suna chan ta bar musu gidan suna Yadda suka ga Dama..!
Anty Amarya bata jira cewar Mamanmu ba ta yanke kiran ta bar Mamanmu da Hararan waya Lokaci Daya ta Ijiyeta nan kan Tabarma ta koma Kitchen tana fadin"Kawai kin zo kin Tsaidani kan mganar banza..Badai nawa Burin ya cika ba..Ban Damu ba..In dai ni na samu abunda nake so Uban kowa kada ya samu..!
Bana kaunar Amina ta Dawomin gidan nan zata lalatamin Tsarina Yadda tatafi tatafi kenan har Abada Shegiyar yarinya mai kama da Uwarta..!
Haka tayi ta manganganu ita kadai.tana ciga da suyan kifinta Duniya tayi mata Dadi.

Anty Amarya kuwa Lambar Sakina ta Kira sai da kusa katsewa ta Daga ko Sallamanta bata amsa ba ta fara Fadin"To shashassha..kina nan kwance ga Amina chan da su Hamida suna yadda suka ga dama da gidanki. !
Sakina na kwance ne sai da ta mike tana Fadin"Bangane ba.?
Nan Anty ta shaida mata abunda mamanmu ta fadamata Sakina tace"Kuturun uba.... to ubansu zasu ci na kulle ko"ina har Kitchen fa..!
Anty Amarya kamar ta Zageta haka taji cikin Tsawa tace"Dayake ke kadai ke da key din gidan ba..?
Karki manta Uwarsa ma na dashi kuma na tabbata sun tafi dashi ki cigaba da zama agidan da nayi Burin ki Rayu ke kadai tun ba"a je ko"ina ba yana neman ya zama ba naki ba..!
Daga haka ta Datse kiran tana Faman Huci Dagachan Dutse kuwa Sakina ta Diro Daga kan gado ta Fada wanka sai yanzu ta Dawo Cikin Hayyacinta.
Allah ya taimaketa akwai wani yayanta zai taho kano shi ya Daukota har Gumel har kofar gidanta ya ijiyeta sannan ya wuce alokacin Shida na yammah har tayi san da ta abuga get din megadi yazo ya Bude mata bata Tsaya amsa sannu da zuwansa ba taja akwatinta ta nufi Cikin Falon.

Amina da Hanne suna Zaune Saman Cafet hamida na Saman kujera suna Hira sannan ga filets nan da suka gama cin wainar Fulawarsu nan da Ferfesun naman rago da sukayi ga Kofuna ga abun maltinan da suka gama sha Falon dai kaf ba Kintsi? Saboda? tunda suka gama suka koma gefe suna Hira sun ma manta yau zasu koma gida Tsabar yadda Rayuwa tayi musu Dadi gaddamace ta Sarke Tsakanin Hanne da Amina kan lokacin Bikin su ya Abida Amina na Fadin yadda Hanne ta manne ma Sa"adatu saboda yar"uwatance ita kuma Hanne tana kokarin nuna ma Amina Daga su har Sa"adatu duk Dayane hamida kuwa bata sako bakinta ba sanin Halin gaddaman Amina ko bata da gaskiya bata saki. kwata kwata basu san Sakina ta Shigo ba ashe ta Dade Tsaye taba Bin Falon gidanta da kallo yadda ya zama.
Ranta in yayi Dubu ya baci akwatin Hannunta ta saki ji kake garam lokaci Daya ta Rike kugu tana fadin"Kutumar Uban chan Falo na ne ya koma kamar gidan abinci?
Lalle yau zaku gane baku da wayau duk sai naci Ubanku daga ku har kazamar data jawo ku..!
Ta karishe fada tana Cire gyalenta ta Ci Darama dashi Tana jifan su Amina da wani matsiyancin kallo wadanda sai alokacin suka san da wanzuwarta afalon Hamida da Hanne ne suka Tsorata Amina kuwa ko ajikinta itama kallon rainin ta maida ma Sakina kafin ta tabe baki ta kauda kai.
Hanne ce da Hamifa suka mike da Sauri Jikinsu na rawa Hanne na faman Fadin"Sannu da zuwa Anty Sakina..!
Ita kuma Hamida ta fara Tattara filets din tana fadin"Kuyi hakuri yanzu zamu share mu gyara ko"ina..!
Sakina ta kariso Falon tana Hararansu Lokaci Daya tana fadin"Dilla kumin shuru..uban wa ya baku izinin zuwarmin gida batare da sanina ba.?
Hannu hamida tabi da kallo kafin tace"Kan uba har kitchen dina ma kuka Bude kuka shiga kuna min kazanta..?
Yau zan ga wanda zai Rabamu daku acikin gidan nan..!

Amina mamaki kamata yayi ganin yadda Hamida da Hanne suke bata Hakuri jikinsu na rawa sai Faman Zaginsu take yi ranta ya baci ta Dauka tayi sanyi ashe batayi ba batasan Sadda ta Mike ba sai jin muryanta sukayi tana fadin"Dillah ku daina bata Hakuri..Kun zo din ai ba gidan Uban kowa bane nan..Gidan mijina ne kamar yadda yake gidan mijinta sannan kada ta manta nan din gidan yayanku ne ko sama da kasa Zata Hade shi din jininku ne wata fa..?Yar karo ce..Saboda haka ku saki jikin ku ku Wala ba wacce ta isa ta Daga muku Hannu ina gidan nan wlh..!
Ta karishe Fada itama tana Hararan Sakinar da manyan idanuwanta.
Hamida da Hanne suna ta kyafta ma Amina ido bata bi ta kansu ba Sakina ta nuna kanta tana fadin"Wai dani kike..?
Amina ta karkace baki tace"Ban kira suna ba..Ammh in kin Tsargu ba ruwana..!
Sakina taji ranta ya kara baci Tayi kukan kura tayi kan Amina tana Fadin"Yau sai naci Ubanki acikin gidan nan.!
Su Hamida suka shiga Tsakani suna bata Hakuri Hanne sai ta Fara kuka tana fadin"kiyi hakuri yanzu zamu gyara ko"ina Hanida ko ba"a zo Daukan mu ba yanzu zamu tafi..!
Amina datayi ke Tsaye Cikin mamakin ko Sakina Dukanta zatayi tayi Shewa kafin tace"Wlh badai ubana ba..kin gama Zagin Ubana na kyaleki..!
Sakina tace"Sai nawa Uban ko..?
Amina ta Tura dankwali Gaban goshi kafin tace"To nidai ban ce ba..Ko banza nasan Darajan tsohon wasu..!
Sakina ta Harzuka haka take Zagin Amina har tana fadin"Badai ke yar iska bace ko...?
Bari? zan kira? habibin Wlh bazan iya Zama Da kazama irin ki acikin gidana ba. !
Amina tace"Gidanki ko gidanmu..?
Malama ki kara Min jaye..!
Mu uku keda wannan gidan Dake da ni Amina da yar balarabiya baki da kuma yadda zaki yi..!
Ran sakina ya baci tana mamakin yadda yarinya karama ta zauna tana Fada mata mgana Hamida da Hanne na Faman bata Hakuri suna fadin zasu tafi.
Amina ta kallesu tace"kudai wlh bazanye ne..To uwarki ce ita..kun zauna kuna ta wani bata Hakuri tana Kara Zagin ku..bazaku gyaran ba tayi abunda zatayi..!
Hanne tace"A"a Amina mu muka bata bari mu gyara mu zo mu tafi..!
Amina tace"In kun tafi Allah tsinan naga mai fita agidan nan..!
Ta fada tana wani juya ido kafin taja Tsaki Sakina taji kamar tayi Bindiga ta koma ta Dauko akwatina Kamar Kububuwa ta wuce ta Bude Dakinta ta Shiga tana Tunanin yadda zata yi Biji Biji da Amina Umar ya ja mata raini wajen wannan yarinyar.
Tana shigewa ta banko kofa Amina tayi Tsaki ta koma ta zauna hakanan taji Ranta na kuma kamar tayi Bindiga haka take kada kafa tana Girgiza jikinta Hamida da Hanne suka Bita da kallo basu tankata ba Azaton su Jidalin Amina ya ragu ashe karuwa yayi basu sani ba hamida ta tatattara komai Takai kitchen ta Hada wanke wanke Hanne kuma ta Fara gyaran Falon Amina na Zaune tana kada kafa Ranta na mata wani Zafi kamar ana Hura mata wuta ita kanta Hanne bata taba ganin Amina tayi irin wannan ba,Shiyasa bata tankata ba itama batace mata komai ba..!












*Janafty*

*TFZB2009*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*

Hamida da Hanne cikin rawan jiki suka gyara komai Hanne ta share falo ta goge shi tas hamida kuma ta kintsa Kitchen din ta wanke kwanukan da suka bata ta goge kitchen lokacin har an fara sallar mangariba a masallatai yasa suka wuce dakin da Amina take suka isketa Ta fara salla,suma alwalan suka Dauro suka zo suka jera da Amina suka tada salla har suka idar Amina bata musu mgana ba suma ganinta cikin wannan yanayin yasa suka mata shuru.
Tana ganinsu suna hada kaya sai ranta ya kara baci Haka kurum take jin wani zafin zuciya wanda ko a baya ba irinsa take ji ba tasan dai tana Saurin Hasala ammh Bata da Saurin Harzuka kamar na yanzu sai ta Danganta haka da Tafiyar su Hanne Abunda bata sani ba wannan zafin zuciyar da aka kara mata ne maimakon tayi shi ga wanda akayi Domin sa sai ya kuskuremai Bashi a kusa da ita sai abun zai tsaya ga wanda ke kusa da ita da kuma wanda ke bata mata rai a kusa.
Sallar da tayi ne ma yasa taji dan Dama Dama ammh ranta yagama baci da abunda Sakina tayi mata yau ji take yi daman ta Tabata da sunan daambe da ta gane bata da wayau a yadda take jin kanta da karfi sai sun kwashi yan kallo domin karfin jikinta ya Dawo sannan ta warke kasanta ma batajin wani ciwo ruwan zafi da mgangunar nan sun tainaka mata wajen dawowa da ita Daidai shiyasa ko su Hanne basu Fahimci komai ba tota ina ma zasu gane..?
Amina ta fi su Budewar ido kan irin abubuwan nan saboda ita tana karance karancen Littafan hausa su kuma fa dukum ne su basu riga sun san wasu abubuwan kamar yadda ta sani ba.
Suna cikin Hada kayan ne suka ji knooking daga kofar falon Amina ta Dago tana kallonsu hanne ma ta kalleta kafin ta mike tana fadin"Ina ga Idi ne..!
Ba jimawa sai ga shi ta dawo tana Fadin"Shine Hamida..Hajiya tace maza maza ya Daukomu gobe akwai makaranta..!
Hamida batace komai ba ta Zura Hijabinta haka Hanne suka Dauki Ledan kayansu Hamida ta kalli Amina Dake Zaune tana kallonsu tace"Amina mu zamu tafi..
Amina tayi kamar bata ji su ba kuka taji yana neman tasomata Hanne ce Cikin karfin hali tace"Kiyi hakuri ai gobe zamu biyo mu Dauke ki..Ki shirya da wuri..!
Hamida da Hanne suma karfin hali suke kada su yi kuka ganin yadda Amina Tayi ganin ta musu banza yasa Hanne taja Hannun Hamida suka Fice Daga Dakin Amina na ganin haka ta mike Zaraf ta biyosu falon tana Fadin"Yanzu wai tafiya zaku yi..?
Ku bari gobe mana basai mu tafi makarantar tare ba..!
Hanne tace"To ai uniform din mu na gida kuma kinga Hajiya ce ta aiko a Daukemu..!
Amina bata kara mgana ba kawai ta Juya ta koma Dakinta ta Zauna gefen gado sai kuka wiwi kamar wacce aka Daketa Tana jin karan Bude get tasan su Hanne sun tafi kawai sai ta kwanta Saman Cafet ta cigaba da kukanta kuka mai Cin rai rabin kukan na kewa ne da Zaman kadaici rabin kukam kuma na kuncin zuciyar da ta rasa Dalilinsa wani Kululune ya Tsaya mata? arai yaki wucewa tana Tunanin in tayi kuka zata samu sauki.

Sakina kuwa ko da ta shiga Dakinta ko gani batayi Ranta ya gama baci tana Tunanin karamar yarinya kazama kamar Amina ce zata tsaya tana Zaginta Lalle sai ta gane bata da wayau Zata Kira Habibi ta Fadamai Rashin kunyar Amina sai ya Dauki mataki akanta domin ita bazata iya Zama da ita haka ba Allah nagani.
Wayarta ta Dauka ta kira Lambarsa ta Saudiya ta shiga sau biyu bai Dauka ba ta Duba Lokaci bakwai Saura na Dare su achan zai zama tara da wani abu kenan bai isa ya kwanta ba Duk da Tun da ya tafi sai jiya ta kirasa suka gaisa bai tsawaita mganar ba yace mata yana Aji ne in ya koma gida zai kirata kuma bai kara kiranta ba.
Ganin bai Dauka ba Sarood ta kira ita kan ta Dauka suka gaisa take tambayanta Habibi ta sanar da ita baya nan ya tafi Cikin gari masallaci Har yanzu bai shigo ba.
Sakina ta gyara zama tana cema Sarood? ta rokar mata Umar don Allah ya zo ya Dauketa yaki komawa da ita Madina Sarood tace mata kawai zata mai mgana da haka suka rabu Sakinar ta Lura kamar Sarood din bata son Wata Doguwar magana da ita tana sota kawomata Labarin Amina sai tayi Saurin Dakile mganar da cewa Tana girki ne kada ya kone..
Abunda bata sani ba ita kanta Sarood din tunda ya Dawo sama sama suke domin daman kafin su tafi sun yi Rigimar tahowa tun Tarkon da Sakina ta Hadama mata ita kuma ta Fada har sai da Mahaifinta ya shiga mganar To kishi da kuma takaicin abunda ke Faruwa Tsakaninamsu ya Rufemata ido gani take yi yana chan yana jin Dadinsa da Sakina da Amaryansa ita kuma ya barta anan ita bata ga Tsuntsun ba ga Tarko shiyasa taso ta Biyosa batare da sanin ko iyayanta nata ba Sai dai kalmar daya fadamata na sai tazo ne ya bata tsoro yasa ta fasa zuwa Tasan Halinsa kaifi Daya ne.
To kwana Hudu Tsakani ya Dawo Tunda ya Dawo ta sakamai Rigimar ita bazata yarda ba, da gangan yake yi Ba wai bazai iya kadaicewa da ita bane meyasa shi da Sakina Lafiya kuma gashi har yayi amarya itama tasan ai lafiya kalau meyasa sai itane bazai iya Raba ba .
Alokacin akwai gajiya tare da shi,Shiyasa bai biyemata ba sannan kuma ta wani Fannin tana da gaskiya ta wani Fanni kuma bata dashi Saboda ai ba Laifinsa bane sai da yace su sanar da manya mganar in da cutarwa tace taji ta gani sai kuma Daga baya ta Bullo da wata mgana Ba domin ma Su din ba su cika yarda da Sihiri ba, da haka yasan zatace Duk da shima lamarin ya bashi mamaki ammh bai Taba Zargin wani ba ga Allah kadai ya Dogara shiyasa yake Neman waraka daga garesa..!

******

Amina batayi wani barcin kirki ba Saboda kuncin zuciya sannan ta dinga Tsorata acikin barcinta da Daddare barcinta sai ya zama sama sama ne tasan a gida bata iya barci sai acikin mutane ammh Tsoronta bakai na yanzu ba ko ya ta kwanta ta fara barci sai taji kamar ana Tabata sai ta Tashi a Firgice daganan sai kuka in tayi addu"a ne ta koma sai barcin nata yadan yi Tsayi.
Yau da wuri tatashi ga rashin barci sannan tasa ka Komawa makaranta aranta yau din tayi wankanta sannan tayi sallar asuba Saboda zumudi Amina ko Karyawa bata tsaya tayi ba ta Saka Uniform dinta dake goge Daman Hamida tun agida ta goge mata ta fito da Jakar makarantar data Islamiya ta tura ta islamiyar da Hijabin cikin jakarta saboda chan zata zauna sai sun dawo daga islamiyar yammah Ta saka Safa da Takalminta ko Falo bata fita ba kuma bata ji motsin Sakina ba.
Tun bakwai na Safe ta gama shiryawa tana zaman jiran su Hanne cikin kudin da Danmallam ya bata ta Dauki Dubu Daya yau zasu ci su sha ita dasu Hanne su Sa"adatu kuma Sai dai suga anayi yan bakinciki.
Har takwas saura sai ta fara Tunanin ko dai sun tafi ne sun barta ayadda tayi Shirin zuwa makaranta yau sai ta kama gabanta don bazata fasa ba Kamar daga sama taji Hon din mota dayake motar tasu akwai kara bata gama Tantancewa ba taji Muryan Hanne na Kiranta tayi Zaraf ta Fito Daga Dakinta bayan ta kulle kofar Hanne na ganinta ta washe baki Tana Fadin"Amina Aminene ikon Allah..!
Amina tayi Fari da ido kafin tace"Kwarai ba dai ta mutum ba sai ta Allah wlh..kainuwa Dashen Allah .!
Hanne tayi Dariya kafin ta kalli jakar Amina Datake neman rinjayanta tace"Meye kika sako ajakar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login