Showing 186001 words to 189000 words out of 265571 words

Chapter 63 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28882

Jarabawarki bazaki yi ta yanzu ba sai in kin haihu nayi miki alkawarin karatu zaki yi shi har sai kin gaji..Danmallam ma bazai taba Tauye miki Hakki ba..!
Amina sai ta fara Tunanin ko Hajiya tasan wani abu ne kan mamanmu da Anty Amarya..?
Sai dai bata ga wani alama ba,Ita yanzu zata iya yin komai Saboda Cikin jikinta sannan Zatayi komai Saboda Tonama mamanmu asiri da Anty Amarya kuma Cikin jikinta ne makami shiyasa bayanin Hajiya bai Dameta ba Hawaye suka kawo Idanuwanta in ta tuna Shekarun data kwashe bata san Dadi da muhimmancin Uwa ba,Gashi yanzu tana Cikin wani Siradi,Siradin da uwa ce kadai Zata tallafamata sai dai ina Mamanmu ta yanke wannan abun Saboda son zuciyrta da kuma Mugunta da zalunci.
Ganin Tana Hawaye Yasa Hajiya tayi Tunanin Rabuwa da su hanne da karatunta yasa ta saka Hannu ta Rumgumo Amina kan kafadarta Tana Lallashinta Lokaci Daya tana Fadin"Kiyi hakuri Amina..ki daina kuka na dan Lokaci ne watarana sai Labari..!
Amina na Shesshekan kuka tace"Hajiya ba ina kukan hukuncin ki bane..
Ina kukan rashin yaya ne..ayau bata a Duniya ina jin matukar kewarta..!
Hajiya Tsausayinta ya kamata ta Dagota tana share mata Hawaye lokci Daya Tana fadin"In kin Tunata ki mata addu"a kin ji ko..?.Sannan in kin ji kewarta ki tuna Dani Domin tamkar Uwa nake gareki ina nan Saboda ke Amina ni ba Uwar Umar nake ba Har Abada ni ina matsayin mahaifiya gareki ne nayi kuma alkawarin Kareki da yardan Allah ke da abunda ke Cikin ki..!
Tana Fada tana share mata Hawaye wasu na Bulbulowa Hajiya fadi take"ki daina kuka nasan zaki ji Dadin Zama da Aisha na dan Lokaci ne Zaki Dawo in Lokacin hakan yayi.!
Amina ta gyada kai tana Fadin"Hajiya ke da mallam nasan har Abada bazaku kai ni inda Zan cutu ba..Sannan duk abunda kuka Zartan kan Rayuwata ina maraba dashi..Na yarda da Hukunci ku kuma Insha Allahu Zaki Sameni mai Bin Umarninki..!
Hajiya taji Dadin haka ta Dinga shafa kan Amina ta saka mata albarka kafin ta mike tana fadin"Kayan ki duk suna gida ko..?
Amina tace"Eh akwai wasu anan hajiya..!
Hajiya tace"To ai ba kaya da yawa Zaki Diba ba nan gaba ma kadan zasu yi miki. Sai ta Dinka miki wasu achan kawai..!
Har Hajiya ta Fice Daga Dakin Amina bata kara mgana ba,wani irin Dakiya ne da Taurin zuciya ke shiganta da kwarin gwiwan da bata san tana Dashi ba Duk da tasan zatayi kewar su hanne da makaranta ammh Gaskiyan Hajiya ne datace na dan Lokaci ne watarana sai labari.
Daya da wani abu na rana su Hanne suka Dawo sun ji dadin ganin Amina taji Sauki basu damu da yanayinta ba sun Dauka saboda bata da Lafiya ne ita kuwa kallon su kawai take yi Tana Tunanin sai dai suga Hajiya ta Dawo ita kadai zasu yi kewarta kamar yadda itama Zatayi kewarsu Hamida kuma Tsausayinta take ji domin in ta kalletasa sai taji kuka ya taso mata ya Zataji in taji Abunda mahaifiyarta take aikatawa..? Bazasu iya Daukan wannan abun ba su take Tsausayi domin ba d'an da zai so uwarsa ta kasance bata gari ba abun akwai taba Zuciya ammh Dolen wata watarana Allah ya Tona musu asiri kamar yadda ya Fara Tona musu awajenta.
Kamar sun san Amina zata koma wani wajen Ranar wuni sukayi tare ko Hamida bata ko leka gida ba suna Tare har Dare,Da mallam ya shigo har Shashen Hajiya ya Dubata ya Dafa kanta yana fadin"Allah yayi miki albarka..Allah ya Saukeki lafiya ya kareki mamana..!
Ta amsa kanta na kasa kafin ya Sake fadin"Kina tsorata Cikin barcin ki har yanzu ko kin bari..?
Amina tace"Yayi sauki baba..!
Malam ya jin jina kai yana Fadin"Zai bari gabadaya ki Dage sosai ki Daina kwanciya ba alwala sannan ki Rike addu"o"in nan da yawaita karatun Qur"ani..!
Amina ta amsa da toh ya Dade yana mata Nasiha kafin ya fita,Dakin Hajiya ya shiga sukayi mgana ya Fadamata ya Kira Usman mijin Aisha yace ba wata matsala sannan bayama gida yana Lagos,Daganan sukayi mgana sama sama kafin ya fice Daman shi da Aba suka shigo shima ya shiga ya gaida Amina bai Dade ba shima ya fita Amina bata Damu ba Sai ma wani Tsausayinsa Daya kamata Mace tatasa shi gaba da makircinta.
Mallam nan ya bar Aba Hajiya tamai mganar Zata kai Amina gidan D'aya Daga Cikin yaran nan tadan koyi wasu abubuwa tunda ga yanayin yarintarta bata koyi wasu abubuwa ba sannan nan da Lokaci kadan Danmallan zai zo ya tafi da ita madina..
Aba bai Tambayi ina Za"a kai Amina ba Sai kawai yabi Hajiya da godiya yana komawa gida ya Fadama mamanmu yadda sukayi da Hajiya anan nema take jin Amina bata da lafiya Mamanmu dataji haka shewa ta Saki aranta tace auran da Zai kare a gantali ne za"a je koyon zama da Miji..!?
Shiyasa kwata kwata bata Damu ba,ita Atunaninta Wahalar da kai kawai Hajiya take yi ammh Amina da Umar ai sai hange Daga nesa ammh a fili sai ta nuna Tasauyawanta da cewa da Safe zata shiga ta gaida Ameenan kafin su tafi ko aranta bata Damu da Sanin ina Hajiya zata kai Aminar ba wannan baya gabanta yanzu.
Adaran Hajiya Ta kira Aisha tace gobe tana nan tafe Aisha taji mganar kamar Daga sama murna ta Cikata Dayake Usman din bai riga ya Kirata ya Fadamata ba Hajiya ta rigasa sai taga kamar ta zama mai sa"a domin Hajiya basa zuwa gidan mutum hakanan sai da babban Dalili ammh ita yau gata Hajiya Zata zo gidanta Murnan ta ya kasa Boyuwa suna gama mgana da Hajiya ta tafi Dakin kakar mijinta Dake zaune tare Dasu da suke Kira Yakaka ta sanar da ita Hajiyarsu na tafe gobe.
Har gari ya waye su hanne basu san komai ba da Safen dai Hajiya tace ma Hanne zasu fita da Amina su shirya su tafi hadda sukace to basu yi wani tunani ba, sai sukayi Zaton Ko asibiti zasu koma basu damu ba.
Ammh Sanda suke shirin tafiya Amina na kwance na kallon Hamida na shiryawa ta fito wanka aran Amina tana tunanin Hajiya zata zame ma Hamida uwa kamar yadda ta Zame mata uwa,Idonta ya kawo ruwa in ta Tuna zatayi nesa dasu saurin share Hawayenta tayi ta kira sunan Hamida bata Damu data waigo ba ta amsa mata.
Amina tace"Hamida don Allah ki kula da Jawaad..!
Hamida sai da ta saka Rigar wata atamfar dake jikinta sannan ta Juyo jin abunda Aminar tace da yanayinta yasa Cikin mamaki tace"Wasiya kika fara bari ne Aminene .!?
Amina tayi Mirmishi tace"Eh mana kinsan Rayuwa haka ta gada..muna tafe ne bamu san muna tafiya da mutuwarmu ba .!
Hamida ta fara Dariya tana Fadin"Lalle Amina ta fara Tunanin mutuwa..Hanne tazo kiji..Hanne. !
Ta shiga kwalama Hanne kira sai gata ta Dawo da Faratin kayan karinsu tana Fadin"Kiran me kike min hamida kamar kin bani ajiya..?
Hamida na Dariya tace"Amina ce ta fara barin wasiyya..!
Hanne ta ijiye abun hannunta saman Cafet tana kallon Amina Lokaci Daya tace"Topa ta fara Tunanin mutuwa ne..?
Ko azara"ilu ta gani..?
Ta fada tana yar Dariya Amina ta balla musu harara tana fadin"Bansani ba. kufa yan iska ne baku san abun arziki ba.!
Hamida tace"Mu ko ke ne bamu san abun arziki ba..?
Ke Amina uban wa ya kaiki maida abun arziki na fada ma. !
Hanne ta Zauna tana Fadin"Ki zauna mu karya hamida kada mu makara..Amina inaga asibiti zasu koma da Hajiya. !
Hamida tace"Shiyasa ta fara barin wasiyya kenan. !
Duk tana jinsu batace musu komai ba illah tasowa da tayi tace su karya Tare harda Jawaad daya shigo yanzu gabadayansu suka karya suna yi suna Hira Amina tana tunanin shine na karshe Zaman su tare Indomie ne sai soyayyan kwai da Tea Amina kwan taci ya taso mata da zuciya sai da tayi Amai ta koma ta kwanta tana maida Numfashi su Hanne na mata sannu da Zasu tafi haka taji kamar ta Bisu har suka fice tana musu bye bye suka fita Suna Dariyanta wai Amina ciwo yasa ta fara Tunanin mutuwa
Basu san cewa Amina Zatayi nisa da su na wani dan Lokaci ba..suna fita ta Fashe da kuka sai da tagaji tatashi ta rarrafa tayi wanka sai a yanzu da aka Tabbatar tana da Ciki take jin wani Sauye Sauye ajikinta na masu juna Biyu.
Ta shirya Cikin Riga da zani na kayan da Hajiya ta Dinka musu ita da Hanne da Hamida abunda yasa ma rigar tayi mata daman tun farko dinki yayi mata yawa saboda Sizes din Hamida aka mata kuma tun Lokacin ba"a rage kayan ba Ta yi shirinta da wuri ne Sabida Hajiya tace da wuri zasu tafi Tunda ita ayau din zata Dawo.
Yan kayanta Dake nan kawai ta Hada kala uku sai Azakar da addu"o"in da mallam ya Rubuta mata' sai mangunanta,wasu kayan nata suna gidan Aba wasu kuma suna gidan ya Danmallam bata kwaso duka ba,Zama ta yi kawai tayi Tagumi tana Tunanin yadda Sabuwar rayuwa zata Bude mata ita da abunda ke Cikinta tana tunani tana Hawaye sai ga Hajiya ta shigo tayi saurin goge hawayenta saboda kada ta gani ashe ta gani sai bata nuna mata ba
Kallonta tayi tana Fadin"Mamah kin gama shiryawan .?
Amina kanta na kasa tace"Eh Hajiya ina kwana..?
Hajiya ta amsa tana fadin"To kin kar ya kuwa..?
Ta gyada mata kai tana Fadin"Eh hajiya..Tare da su hanne muka karya. !
Juyawa tayi ta Fice tana Fadin"To bari Idi ya dawo kai su makaranta sai mu wuce..!
Fitan ta ba Dadewa ta Leko tace ma Amina ta fito Dogon Hijabinta ta Saka Jakar data Hada kayan nata Hajiya ta karba ta farayin gaba itama ta shirya Tsab da ita,Hajiya na gaba tana Binta abaya har falon Mallam suka gaisa ya kara mata Nasiha sai ga Idi ya Dawo Hajiya ta mike tace zasu tafi mallam yace"Ko in kira Sa"idu ne su yi sallama..?
Hajiya tayi shuru kafin tace"kyalesa kawai ai na Fadamai jiya..
Mallam bai kara mgana ba shi ya rakosu har bakin mota sai ga Hajiya Nasara ta fito domin ita ke da Turakan mallam jiya ganin Hajiya da Amina yasa tace ko anguwa zasu je Hajiya tace eh ba Dadewa zasu yi ba mallam dai na gefe bai ce komai ba domin yayi alkwarin bazai ma Hajiya kaladan kan abunda ta Tsara ba ya yarda da ita fiye da duka matansa bazata taba aikata ba Daidai ba.
Agaban idon Hajiya Nasara da Mallam Suka fita Daga gidan idi ke jan su a Motar mallam din prado baka suka Dauki Hanyar Abuja Amina na ta sharan kwallah Hajiya na kallonta batace komai ba Domin bazata hanata ta koka ba.
Su hajiya basu yi nisa ba,Aba ya fito zai Tafi gidan gona mallam ke Fadamai su hajiya sun tafi yayi mata Fatan Dawowa lafiya bai Dade ba gaiswawa kawai sukayi da Mallam ya shiga Motarsa ya tafi bayan tafiyarsa sai ga mamanmu ta shigo gaida Amina da Haj.Nasara ta fara Cin karo ita ke shaida mata Hajiya sun fita da Amina mamanmu bata Damu ba aranta tace agayas ayasha ta gaida ayyah..!
Shashen Anty Amarya ta shiga ta Duba Sakina sannan suka kule Daki suna Kulle kullensu da suka saba mamanmu ke fadama Anty Amarya Abunda Aba ya fadamata Hajiya ta Sanar dashi kan Amina da Tafiyar tasu yau.
Anty Amarya ta tabe baki Tana Fadin"Ko shiyasa Daga jiya zuwa yau take wani Shan kamshi..ko Sakina ta Daina lekota su gaisa. !
Mamanmu tace"Yau she kuwa..?
Tana chan tana shirin kaita inda Zata kwace miji..!.
Anty Amarya tace"Aikin banza ne wannan..Ai Danmallan din yana Tafe nan da wata Biyu in ya Dauki Sakina suka koma ai sai naga karyan koyon kula da miji..!
Wai ina ma Zata kaita..?
Mamanmu tace"Oho ni dai yace min Gidan Da'ya Daga Cikin yaran mu..!
Anty Amarya tace"Ni ba ma wannan ne agabana ba Dayyaba..Mallam nake jira ya Kirani so nake ayi ma Sakina mganin abunda uwani tayi mata Datake bari in aka gama da wannan bangaran mganinta bamai matsala bane..!
Mamanmu tace"Ai Allah dai ya Tsine ma Uwani..!
Anty Amarya tace"Amin matsiyaci ce..Ta gaban anuna ma jarida. !
Nan suka Cigaba da Tattauna yadda zasu Taru suyi mganin Uwani hankali kwance in sun gama da matsalan Sakina suna ganin Amina bata gabansu.Suna ganin ita karamar alhaki ce bata isa ba yanzu.
Abunda basu sani ba wanda bai isan ba Allah yafi nuna isarsa akansa sannan alokacin da Uwani ta Dauke musu hankali Dan Zaki zai girma sannan Tsammanin abunda basu tsammani ba zai faru..!.

*****

Abuja..!

Misalin karfe Shadaya na rana suka isa gidan Aisha Dake maitama Abuja Kwatsam sai dai ta ga Hajiya abun Farincikin ma harda da Amina Aisha ta kasa Boye Murnanta ta Daka Tsalle ta Rumgume Hajiya sannan ta rumgume Amina Hajiya ta kalleta tana Fadin"Ki mata a hankali bata jin Dadi..!
Sai alokacin Aisha ta Lura da yadda Amina tayi kiba Sannan Fuskarta ta Kumbura,haka ta jasu falonta Cikin murna tana da yar aiki wata yar matashiya ita ta cika gabansu da Kayan Taba ka Lashe,Amina sai Bin Gidan ya Aisha take da kallo mai kyau dashi.
Aisha ta rasa ina Zata saka su Hajiya Saboda Murna Hajiya ta kalleta tana Fadin"Aisha to ki Zauna mana..!.
Ta Zauna gefen Amina tana Fadin"Hajiya murna ce..Ga ki ga Amina.
Hajiya ta yi mirmishi kafin tace"Yanzu dai ba wannan ba. ki sama ma Idi waje yaci abinci ya Huta kafin mu tafi..!
Da azama ta mike tana amsa ma Hajiya yar aikinta mai suna Saude ta ma mgana taa shiga da Idi Dakin Baki na waje tazo takaimai ruwa da abinci.
Tana Dawowa tace ma Hajiya"Hajiya Zaku gaisa da yakaka kakar Usman. !
Hajiya tace"Zan shiga mu gaisa Aisha kada ki damu..!
Aisha ta koma ta Zauna kusa da Amina tana Fadin"Aminene ikon Allah Amaryan ya Danmallam ya naga kin yi Shuru ne bakya mgana..!
Nice fa ya Aisha..?
Ko bakin ya mutu ne basu Hamida..?
Amina tayi Mirmishi ta gaisheta ta amsa tana Fadin"Amina kinyi Kiba Lokacin Bikin su Abida kina lange Langenki fa..!
Hajiya tace"Na sanar Dake bata da Lafiya ne Dalilin zuwana ma kenan..!
Aisha tace"Eh usman ya Fadamin sunyi mgana da mallam..Dama Amina ce Zata Zauna damu Hajiya..?
Hajiya sai da ta gama shan ruwa sannan Ta gyada mata kai Aisha ta Zaro ido kafin tace"Hajiya ba ta tare gidan ya Danmallam ba..?
Ko ansamu wata matsala ne .?
Hajiya ta mike tana Fadin"Mu je Ciki mu yi mgana..Amina kici wani abu kafin mu gama. !
Ta daga ma Hajiya kai Aisha na gaba Hajiya na bayanta har bedroom dinta Gefen gado suka Zauna Aisha Duk ta Tsorata fatanta kada ace auran ne ya Lalace.
Hajiya ta kalleta tana Fadin"Kada ki damu ba wata matsala bane..Auran su na nan sannan da sanin shi Danmallam din da Mallam kanshi na kawota wajenki. !
Sai alokacin Aisha ta ji sanyi Tace"Hajiya har gabana ya fadi na Zata ko wani abu ne ya samu auran nasu..!
Hajiya tace"Ko Daya..Sai dai matakin dana Dauka duk saboda Kara Karfafa auran su ne Aisha..Ina mai Sanar Dake Amina na Dauke da Cikin yayanku har tsawon wata Hudu da kwanaki. !
Aisha ta zaro ido kafin tace"Ciki Hajiya..Aminar..?
Kai ta gyada mata tana fadin"Kwarai kuwa baki ga alama ba ko..?
Aisha ta washe baki tana Fadin"Bangani ba Hajiya sai kibar Data kara..Alhamdulillah na taya ya Danmallam Murna daman ga Sakina na ta samun bari Allah yasa na Amina ya Zauna ta sauka lafiya..!
Hajiya ta amsa da Ameen kafin ta Kira Sunan Aisha ta amsa mata Cikin bada Hankalinta ganin yanayin Hajiyar.
Hajiya tace"Aisha na yarda Dake kaf Cikin ya"yana shiyasa na Zabi Amina ta Zauna agidanki ki kula da ita ta Reni Cikinta na wani Lokaci Sannan na zabe ki saboda baki da Surutu achan gida dagani sa mallam sai Danmallam muka san da Amina nada Ciki sai ke yanzu sabida haka ina so ya Zama sirri Tsakanina Dake..Ban so wani yaji labarin Cikin jikinta ballatana labarin tana wajenki Shima ba wanda ya sani Harta ko da Sa"idu da su hanne basu san komai ba.ki kama Bakin ki koda tambayarki akayi kice baki sani ba Dani kadai zamu Dinga mgana in wani abu ya taso kina jina..?

Aisha ta gyada kai Cikin mamaki Hajiya ta Cigaba da Fadin"Nasan Zaki yi mamakin meyasa nayi hakan..!?
To ina da Dalilina ammh ba yanzu zaku sani ba sai nan gaba..Fatana ki kula da ita don Allah da abunda ke Cikinta sannan ki koyamata Girke girke da Sauran Kissa na mata Amina haka tataso Sakaka ba wani abunda ta iya Kinsan Tana da abokan zama dole sai ta kara wayewa kan wasu abubuwan..!
Aisha tace"Insha Allahu Hajiya Zan yi Duk yadda kikace Sannan zan rike Amina kamar yadda Zan rike Hanne .!
Hajiya taji Dadi ta Dinga saka mata albarka sannan tace tatashi ta Rakata Dakin kakar mijin nata su gaisa.
Tare da Amina Hajiya tace suka shiga Dakin da Yakaka take Zaune Yar Dattijuwa kamar zata girme ma hajiya hutu ne da jin dadi suka boye girmanta ta amshe su da Fara"a tana Fadin bata son zuwansu ba,da ta fita sun gaisa Tana nan tunda ta idar da sallar walha bata matsa ba..Hajiya tace bakomai suka gaisa sai kallon Amina take yi Hajiya ta mata Bayanin kanwa take wajen Aisha tana da Ciki zata dan Zauna na wani Lokaci Tare dasu ta karishe da Fadin"Hajiya don Allah a kula..Daga Aishar har Aminan yara ne suna karkashin kulawarki Hajiya ga Amana nan..!
Yakaka na kallon Amina tace"Insha Allahu Hajiya..Na karba zan kuma kula da ita..Allah Sarki gata yarinya karama Allah ya bata..To Allah ya Rabasu lafiya..!
Su Hajiya suka amsa da Ameen Amina ta gaisheta ta amsa Cikin Sakewa tana da Sakin Fuska ga Fara"a nan da nan Hira ta barke tsakaninsu da Hajiya Har Aisha taja Amina suka fita ta nuna mata Dakin dake kusa da na yakaka nan takai mata kayanta Tace nan zata Zauna Daki ne babba mai katifa a kasa sai Cafet da Tiolet aciki Dakin ya Hadu sosai.
Nan Aisha ta bar Amina ta shiga wanka ta fito Cikin Farinciki zata Zauna da Amina sannan gefe Daya tana Tunanin yadda zata inganta Rayuwar Aminene jidali ZUWA Aminene mai aji da Haiba.
Taya Saude tayi suka yima su Hajiya girki ta Dibarma Idi da megadi ta Dibar ma Amina ta mika mata na Hajiya kuma da yakaka Saude ta mika musu Dakinsu.
Aisha tare da Amina sukaci abinci tana yi tana janta da Hira Farar shinkafa ce da wake mai miya Amina kadan taci sai Amai Aisha ta Tsausayama Amina ganin yadda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login