Showing 189001 words to 192000 words out of 265571 words

Chapter 64 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28951

ta wahala wajen amai sannan gata da karancin Shekaru Allah ya bata wannan kyautar ita da tana son Cikin ammh har yau ko bari bata taba yi ba Allah bai kawo ba. !
Ita ta Wanke inda tayi aman a Cikin Tiolet ta kamo Aminar suka tafi tana Tambayanta me zataci tace Tea shi ta Hado mata ta samu ta sha ya Tsaya Daganan Aisha ta barta ta koma Dakin Yakaka ta iske su Hajiya sai Hirar garinsu Bama suke da yakaka nan Hajiya ke fadamata ai su ma sun a zauna a bama su yakaka asalinsu yan Maiduguri ne a bama da labari ya yi Labari Hajiya ta san har gidan su yakaka anan bama kafin yan Boko Haram su Tarwatsa su kowa yayi ta kansa..
Daman ai Yakaka ba ruwanta akwai Hira tare suka ci abinci da Hajiya tayi Sallarta anan wajen Uku saura tayi Shirin Tafiya suka rabu da Yakaka Cikin Aminci kafin su tafi Hajiya ta Damka ma Amima wayar nan da Jafar ya taba kawo mata.
Ta bata ta Sanar da ita Tuntuni mijinta ya aiko da ita sai dai a wanchan Lokacin bata bata ita bane Saboda wasu Dalilai ammh yanzu gata nan zata Fadama Danmallam Saboda ya rika kira yana jin Lafiyarta Sannan tama Aisha bayanin Da Amina Zata Zana jarabawa ammh Dalilin haka yasa zata fasa sai wani Lokacin in ta Haihu.
Amina sai da taga Hajiya Zata tafin da gaske sannan ta riketa tana ta kuka Hajiya tana llashinta tace zasu yi mgana ta waya tana ji tana gani Hajiya ta tafi ta barta sai kuka Aisha ce ta Zauna ta na bata baki Saukinta Daya ma akwai ya Aishar duk da ba kamar su hanne ba ammh da Sauki akwai wanda ka sani a kusa Dakai....
Sai da tayi sallar La"sar barci ya Dauketa Yakaka kuma na jin ance Amina ta kwanta tace maza Aisha ta Tasheta ba kyau barcin yammah Sannan gata da Ciki Dole ta tasheta ita yakakan tazo Dakin Aminan ta Zauna da ita tana janta da Hira ai Tun Amina bata Saki ba har ta Saki jikinta Saboda Yakaka akwai ban Dariya da barkwanci haka ta Dage tana bama Amina labarin Lokacin suna bama farkon hareharen yan Boko haram yadda suka ringa Gudun ceton ransu sai ga Amina na Dariya harda kyatatawa Aisha taji Dadi sosai domin yakaka uwace kamar Hajiya yadda take Daukanta kamar yarta Shiyasa ta matsa sai da Usman ya Daukota daga kaduna wajen kaninsa ya dawo da ita wajensu tasan Amina Zataji Dadin ZaMa da ita sannan zata Dauki darasin wasu abubuwan..!

Hajiya sai Dare ta Kira tace sun isa lafiya har sukayi mgana da Amina ta bata Labarin yadda su hanne suka Dinga kuka ta Fada musu Ta kaita wani waje bazata Dawo ba yanzu Amina itama taji kamar tayi kuka Hajiya ta kara Lallashinta da Fadin kada ta saka Damuwa har ya shafi abunda ke Cikinta To in batayi hakuri ba ya Zatayi..?
Ai hakuri ya Zama Dole tunda haka Allah yayi da ita daga wannan sai wannan..!






*Janafty*

*TFZB2017*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*

_A WEEK LATER._

Bayan Sati Daya da Tafiyar Amina Abuja acikin Satin Dayan data yi a garin Abuja karo na farko tun da take ta fita garin gumel taje wani waje da sunan Zama na wani dan lokaci.
Alokacin da Hajiya ta mata mganar zuwanta Abuja ta shiga Damuwa,Da kuma Tunanin zatayi zaman kadaici ba hanne ba Hamida sannan inda bata Saba ba sai gashi kuma Cikin kwanaki da zuwanta Abuja ta Saki jikinta sosai da garin Musamman ma da Yakaka data kasance mai kirki da Dattako Sannan Aisha ma na iya Bakin kokarinta sosai akan Amina abaya Amina tasan ya Aisha bata da Hayaniya sosai da yawan mgana ammh yanzu haka zata zauna tayi ta jan ta da hira suna tuna irin Rashin ji da su kayi ita dasu hanne Tana bama Yakaka Labari itama Dayake sunan Amina gareta ake ce mata Yakaka tace ai masu suna Amina haka suke yarintarsu an sha kwallo sannan haka suke basu Daukan raini su taru da Amina su yita yabon masu sunansu Nan da nan Amina ta Saki jikinta Dakin Yakaka ma take kwana yanzu Saboda bata son kwana ita kadai yakaka tace ta dawo Dakinta su Zauna tare itama ta samu abokin zama.
Haka kuwa akayi sai da ya Aisha taga Amina ta kwashe kayanta takai Dakin Yakaka suna Zamansu lafiya batayi mgana ba saboda ko bakomai yakaka Zata kula da ita sannan ga Ciki ajikinta tana Bukatar wani a kusa da ita.
Usman mijinta ya Dawo ya ga Amina har sun gaisa saboda yasanta abakin ya Aisha lokacin tana amarya in kewar gida ya isheta sai ta Zauna ta rika basa labarin kannenta Amina da Hamida da Hanne sannan yasan mganar auranta da ya Danmallam din Tunda sukan yi mgana da shi Lokaci bayan Lokaci haka Itama Aminar tasan Usman sun taba ganinsa Sanda yazo wajen ya Aisha kafin auran sannan sun gansa ranar Daurin auran shiyasa dukkansu basu Tarbi juna abaki ba..
Achan gumel kuwa Hanne da Hamida sun gaji da tambayar Hajiya ina takai Amina..! Sun kyaleta saboda bata gayamusu sai dai tace Amina na nan Dawowa insha Allahu sun Damu Matuka,Ammh kuma Dole suka hakura sai dai kana ganinsu kasan sun rage walwala Sannan a makaranta ko an tambayi Amina cewa suke yi tayi tafiya,Hamida har mamanmu tama mgana ko tasan inda Hajiya takai Amina..?
Mamanmu tace bata sani ba tadai san Hajiya tace ma Aba bata wuce Tsakanin gidajen yaran gidan nan ko na gidan mallam ba,ita duk a Tsammaninta bata wuce Tsakanin gidan Jawahir ko Jalela ba tafi ma Tunanin Jalela saboda tayi mgana da yan Gusai kuma bataji Labarin Zuwan Amina ko Hajiya abakinsu ba ita bama wannan ne agabanta ba shiyasa bata Damu da tasan Inda take ba,Saboda kada azargeta da rashin kula da Jawad yasa ta jawosa ajiki ganin yana neman yaki Zama wajenta ya koma wajen Hajiya Hamida kuma ganin ba Amina sai ta Dawo kwana agidansu tana kula da kanta da jawaad tunda Daman Amina ta bar mata Amanarsa to shima ganinta yasa bai Damu ba Duk da shima ya gaji da tambayar ina ya Amina..?
Sai dai Hamida tace mai tayi tafiya ammh ta kusa Dawowa..
Sun kusa fara jarabawar Fita nan da Sati uku hanne da Hamida suna Zaton Amina Zata dawo kafin su fara jarabawa Tunda Hajiya bata sanar dasu komai ba.
Sakina ta koma gidanta mallam yace Tunda taji Sauki ta koma Gidanta ta Jira Mijinta Dole ta tattara tatafi ammh Sai da ta roki mallam ya bata Sa"adatu tatafi da ita sai yace sai dai Tatafi da Sabeeha tunda ta gama primary zata shiga Jss1 kafin a sakata to da Sabeehan ta koma bayan mallaminsu ya Kira Anty Amarya ta koma wajensa ta Zubaimai kudi ya bata wani kullin mgani yace Sakina ta sha da Ruwan Zafi duk abunda Uwani ta bata taci ko ta sha Zatayi amansa ko Tayi kashinsa Domin ya tabbatar ma da Anty Amarya wani abu ne Aka bama Sakina taci acikinta..
Haka kuwa akayi ranar data sha mganin kwana tayi tana Zagayawa har safe ta Kira Anty ta Sanar da ita Tana jin haka Cikin farimciki tace in Sha Allahu nasara tasu ce.
Tsakaninta da Haj Uwa kuma ko mgana basa yi sai agaban idon da bai san tsakaninsu ba kamar mallam da Hajiya da Suke Dauka bata san boyayyin Fuskokinsu ba..Ammh in suka hadu su Biyu su harari juna sannan kuma kowacce ta wuce tana ikirarin sai taga bayan yar"uwanta.

*****

Achan Madina kuwa Danmallam dai da Sarood balarabiya suna ta gwangwajen amarcin su sosai fa ya Saki jiki yana Morewa Saboda ai ya Dade Rabonsa da mace tun Kan Amina wannan kuma ai ya Daukesa a matsayin Rabo ne shiyasa daya samu wannan Damar yake ta amfana da ita Domin Daman Daurewa kawai yake yi Yana fama da azumin Litini da alhamis saboda kariya da Tsare kansan.
Ita kanta Sarood din sai alokacin tasan ta yi aure sai kuma ayanzu tasan tana kishin Mijinta ada kamar bata Damu da kishin Sakina ba ammh yanzu da tasan waye Umar sai taji har Sakina ma tana matsanancin kishi da ita ballatana Amina datafi Tsayamata arai ganin itace yarinya sannan kuma Amarya.
Sosai take ta shagwabanta shi kuma yana lallabata Dalilin haka ne ma yasa har yau bai kira Amina ba Saboda ai sun yi mgana da Hajiya washegarin Ranar data koma Gumel a wayar Nazir Saboda ya cika alkwari yaje ya kwana Daya Ranar Litini da Safe ya hau Jirgi ya koma hankalinsa ya kwanta daya ga Hajiya lafiyanta kalau Cikin koshin Lafiya.
Da farko kafin Bullowan Cikin jikin Amina har ya fara Cuku cukun nema mata Takardan Zama madina sannan har sun yi shawara da Aliyu kan zai shigar da Takardan kan zai karbi Gidan malamai na makaranta Saboda gidansa yayi musu kadan sai ya saka Amina ana Cikin makaranta,Sai kuma ga wannan al"amarin da hajiya tace ya Dakatar da komai Shiyasa ya dan Samu Sauki ya fara shirin Tahowa saboda Sakina sannan uwa uba Amina yana son yazo ya ganta Tunda ya tafi bai fi sau hudu sukayi mgana ta waya ba sannan Sakina duk sanda sukayi mgana ta Dinga mai kuka keman tana fadin yazo ya tafi da ita Tsausayinta yake ji ganin halin Datake Ciki yasa yayi mata alkawarin zai zo nan da wata Biyu zai zo sai su koma Tare Umra yake so yayi shiyasa ya Dakata da Tafiyar Sannan Sarood ma tayi Damara sai taje kuma in yace bazai je da ita yayi rashin adalci ko Iyayanta sai sun ga rashin adalcinsa...!
Tunda suka yi mgana da Hajiya tace kada ya sanar ma kowa ko Aliyu bai Fadama komai ba yadai Fadamai laluran nan tasa Allah ya basa waraka da Taimakon shawarwarin mallam Daganan kuma sun ma Dade basu yi mgana ba daya kirasa sai ya Fara mai Tsiyan ya barsa ne yaci amarcinsa da yar Balarabiyarsa Danmallam Tsaki kawai yake yi da Dariya domin ba karya yana fa shan amarci.
Sai da Amina tayi kwana Goma A Abuja sannan ya nemi wayarta da lambar da Jafar ya Dade da Turomai sai kuma ya kara jin wayar a kashe bai ji Dadi ba in yace Amina bata aransa yayi karya abubuwa ne suka sha mai kai sannan da Tazaran Dake Tsakaninsa da ita da rashin shakuwa da kuma Basu wani saba da juna ba.
Aisha ya kira kawai saboda ko ya Kira Hajiya bata kusa da Amina.
Daman duka kannensa suna kiransa awaya suna gaisheshi lokaci bayan Lokaci Haka suke basu yar da tarbiyan gidan mallam ba ko da yayyinsu basa kusa dashi suna Kiransu a waya suna Zumunci dasu Lokacin Ba'rin Sakina sun ta Kiransa suna mai Jaje.
Lokacin da yake tambayan Aisha mganar yaji wayar Amina akashe ya Aisha tace bata sani ba ammh Zata tambayi Aminar taji tunda ita tama manta da mganar wayar sannan batama Taba ganin Aminar da wayar ba.
Yace to ta fadama Amina yana son mgana da ita ta kuna wayarta Ya Aisha ta amsa da insha Allahu zata Fada mata ya tambayeta ya jikin Aminar..?
Ta sanar dashi lafiyanta kalau sai godiya Zazzabin Dare dai take fama dashi sai amai sannan bata iya cin kowani abinci sai Tea sai Kuma wainar Fulawa,Komai Taci baya Zama sai ta Amayar dashi sai yaji Tausayinta gata yarinya ga shi ya Dora mata nauyi sun yi mgana da ya Aisha sosai ya sanar da ita suje asibiti tace eh Usman ne yace ta bari ya Dawo yaje Kaduna wani aiki Da haka suka rabu..
Suna gama wayar Aisha ta nufi Dakin Yakaka tana shiga ta iske Amina Zaune saman Cafet tayi Daidai tana cin wainar Fulamai mai manja da Saude mai aikinta tayi mata Tun Safe bata ci komai ba Tea din ma yau taki sha ita sai Wainar Fulawa Shine Yakaka tace Saude tayi mata Wainar Fulawan har Sauden tana Dakin ne suna ta Hira Yakaka na basu labarin Cikin kakan su Usman har ta Haihu kanwa ne abincinta sai da bakinta ya Lashe saboda Cin kanwa tana Fadama Amina ta godema Allah tayi ma Ciki mai kyau tunda batayi mugun laulayi ba sannan ta iya shan Tea da Cin wainar Fulawar tayi kyan ma Laulayi.
Amina sai cin abunta take yi tana Dangwala yaji tana Sanye Cikin Bakar Doguwar riga cikin kayan ya Aisha ne da ta bata take sakawa tunda kayanta sun Daina Shigarta Cikin fa Kiba kawai da Budewa yake saka Amina ta bari ne Usman ya dawo su je asibiti da kasuwa ta siyo ma Aminar Dogayen Riguna tunda duk ta bata na wajen nata sannan sun ma Aminar karanci.

Shiga Dakin tayi da Sallama Suka amsa mata,Saude tama mgana tace taje Kitchen ta Dora Girkin Rana Ta amsa da Toh ta fice sai da ta fita sannan ya Aisha ta kalli yakaka tana Fadin"Yakaka sannu da Hira..!
Tana Dariya tace"Yauwa Sannu Aisha..Hala har kin kwanta Hirarmu ta, tada ke..?
Aisha tace"A"a Wl???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?h ina ta gyare gyare ne ma Yakaka ban ji ma Hirarku ba..!
Yakaka tace"Au ho..Ai ina nan ina ma Takwarata Tsiya ina fadin ta godema Allah tayi Ciki mai kyau ba laulayi sannan ta na cin abincin Zamaninmu ni lokacin da nayi Cikin Gaddafi har na Haihu kanwa ce abincina..!
Ya Aisha ta jinjina kai tana fadin"Kanwa..?
Taba..Yakaka kin sha wahala..!
Ta yi Dariya kafin tace"Ai Darajan Uwa ta Daban ce Aisha..Allah dai ya bama kowa nashi kema ina miki addu"an Allah ya baki naki Aisha ita Aminatu ai tana mai kyau ma Kinga banda aman da take yi to sai Zazzabin Daren dana ce miki tana Faama dashi..!
Ya Aisha tace"Eh zamu je asibiti taga Likita ma yakaka in Usman ya Dawo..!
Ta jinjina kai kafin tace"Hakan yana Dakyau..Allah ya Dawo dashi lafiya..!
Suka amsa da Ameen harda Amina Data gama ci ta Kora da ruwa ta koma Tana Sauke Numfashi.
Ya Aisha ta kalleta tana Fadin"Amina ina wayar da Hajiya ta baki da Zata tafi..?
Amina ta Dafe Cikinta daya Fara Fitowa ta yamutsa Fuska kafin tace"To ina na sani..?
Tunda ta bani chan Dakin na wurgar da ita..!
Ya Aisha ta hararrta tana Fadin"To daman don ki ijiye Aka baki wayar..?
Kefa kina da sarkaci bayan ma jidalinki wani Lokaci..!
Amina ta kalleta kafin ta Tura baki ya Aisha tace"Tashi muje ki Daukomin ita na saka miki chaji tunda Daman Hajiya tace Sabuwa ce..Mijin ki ya Kirani yace yana son mgana Dake in fada miki ki kunna wayar hannunki..!
Amina ta kalleta Shekeke kafin tace"Mijina kuma..?
Ya Aisha tace"Eh ko ba mijin naki bane..?
Amina ta Hura Hanci kafin tace"Ina Laifin kice yaya danmallan..?
Ya Aisha tace"Ni yayana ne ke kuma Mijin ki ne..karyan iskanci kike yi bakin ki ya Bude yanzu ko..?
Amina ta Yi fari da ido kafin ta bata rai Lokaci Daya tana Fadin"To ni yaushe rabon daya nemeni?
Ko tawayar Hajiya yaushe da Rabon Daya Kira yace abani..!

Tafada tana bata rai saboda Tsakani ga Allah tana jin takaicin hakan wato bai Damu da ita ba..?
Ya Aisha ta rike baki Tana Fadin"Au Daman kina jiran sai ya nemeki ne..?
tab kina da aiki kada ki manta wata matar garesa achan sannan anan ma yana da Sakina mu masu mu kadai muna Kula da Mazajenmu ballatana ke mai Kishiyoyi har biyu.?
To ki rage wannan Sakarcin naki ko ba Haka ba Yakaka..?
Yakaka ta gyara Zama Tana Fadin"Au to gayamata dai ai ni nan Tunda naji yarinyar nan da Zama da kishiyoyi har Biyu nace Zama bai ganni ba..Tana Haihuwa Gyaran yan maiduguri zan
Mata wanda ba su biyu ko su Uku ne itace ta Hudu sai ta fita Zakka..Ai mu masu sunan mu ba Borori bane..Muna da Tasiri sannan wlh badai mutum ba Sai ta Allah..
Amina na Dariya Ita da ya Aisha wacce tace"To ai Kirarin ta kenan Yakaka Aminene badai ta Mutum ba sai ta Allah..!
Yakaka tace"Ai Gaskiya ne..Ke kwantar da Hankalin ki yar nan har nan Zai zo yana mana yar murna sai mun Wahalar dashi ammh dai kafin nan tashi maza ki Dauko wayar ajonata in ta Cika sai ki kirasa ai mune akasansa ba komai in min nemesa muma watarana Zai nememu ko don Darajan wannan abun da ke Tare Dake in ya manta Dake don Kaniyarsa ai bazai manta da wannan aikin Daya kunsamiki ba..!

Amina sai ta kasa mgana kunya ya kamata ya Aisha kuma ta Fice sum sum tana Dariya Dole Amina ta mike tabi bayanta suka shiga Dakin atare ta Dauko wayar nan Gefen katifa inda ta Watsar da ita Aisha ta karba ta Bude ta a kwali ta jona mata achaji Tana ta mata Fada fadi take"Wlh ijiye wannan Jidalin naki Zaki yi agefe wajen bautar aure ba wannan ake Bukata ba..ki iya Kissa da Kisisinan rike miji..Ni ban ma jin balarabiyar nan Sakinar ce mai ido a Tsakar ka..Kema ki Samu ki Zama mace awajensa..!
Amina dai batace komai ba aranta Tace ai so ma suke ya Sakeni baki sani ba.
Afili kuma batayi mgana ba Saboda abun ya fado mata arai duk da Tana kokarin Cire abun aranta ammh kuma har Abada bazai taba Fita ba..
Har ya Aisha ta gama fadanta ta fita batace komai gefen katifa ta koma ta Zauna tayi tagumi in ta Tuna kalaman mamanmu na kashe mata uwa sai taji ta tsaneta kamar tayi tsuntsuwa ta ganta agabanta ta Chaka mata wuka har sai? ta Daina Numfashi.
Sannan ga kewar yaya aranta ga kuma Rashin samun wanda Zata Fadamawa baalle ta samu sauki ta kwanta akan jikinsa tayi kukan abunda ke ranta.
Haka ta Dinga kuka ita kadai ta Share Hawayenta ta sulale nan saman katifar ta kwanta ta na maida Numfashi har barci ya kwasheta bata Sani ba sai Wajen Biyu na rana ta Farka shima Ya Aisha ce ta tada ita tayi sallah Sai da tayi wanka tayi salla Ta maida Doguwar rigar jikinta ta koma Dakin yakaka ta Haye gadon ta kwanta tana jin yakaka Dake zaune a saman Cafet tana goga goranta tana Korafin ta rage yawan barci mai Ciki da zirga Zirga aka santa tana jinta ta kara Dunkule kanta Cikin Filo aranta tana fadin Yakaka ba kisan irin barcin dana ke ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login