Showing 99001 words to 102000 words out of 265571 words

Chapter 34 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28899

ma malaminsu korafi aka Samo mata kansa shine har ta Fara Tunanin Burinta ya fara cika Sa"idu da komai nasa yana Hannunta..
Tunda yanzu In ya dawo aiki yaci abinci yayi wanka ya kan zauna su yi hira koda bazai amsata yadda take so ba ammh cikin kaso goma tana da Nasaran kaso Takwas aciki Abunda ya Rage mata shine ta fara sanin komai nasa kamar yadda yaya ta sani sai dai har zuwa yanzu yaki bata Damar haka!

Yau ma kamar kullum safiya ranar asabar ce ta hutun karshen mako,Ba kowa agidan duk sun tafi Hadda,Sai ita kadai da Aba bai fita yau da wuri ba,Kamar yadda ta tsiro dashi yanzu Gari na wayewa kafin Aba ya fita sai ta Chaba kwalliya Kamar wata yarinya bayan makircin karkashin kasa har da na Kissa Madina tace ta Dinga Hadawa duk a Kokarinta na sai taja Hankalin Sa"idu akanta gabadaya..!
Abunda bata sani ba ita zuciya ba"ayi mata Dole kan abunda tagani kuma tasan dashi ammh ta nuna bata so..Sannan duk da tana son mai kyautata mata bata cika bashi matsayin daya Zarta wanda ta zabe ta da kanta ba koda bai taba mata wani abu na Alheri ba..!
Zaune suke afalonsa yana karyawa ita kuma tana gabansa kamar mai kirga yawan Numfashinsa Hira take yi mai yana jinta yawancin Labaranta ba wasu masu amfani bane,Shiyasa yake mata Shuru kawai batare daya tanka ta ba,Har kuma gobe bazai daina kukan Rashin Hadiza bai jin zAi iya mantawa da ita.
Jin tayi shuru yasa ya Dago Daga cin Soyayyan Dankalin data soyamai ya ganta tayi Tagumi tana kallonsa Cikin dan mamakinta yace"Lafiya..?Me kike Tunani..?
Alokacin bakincikin Tambayarsa taji Saboda tafi kama data rainin wayau ta Zauna tanayimai Hira yayi mata banza sannan ya Dago yana ce mata Lafiya..?Saurin Daidaita kanta tayi ammj bacin rai yasa Kiris ya Rage Dayan Fuskar tata ta bayyana.
Cikin sosa ido da hanci ta fara fadin"Yaya na tuna..Bana iya kwana na Wuni ban yi kukan rashinta ba..Ballatana in na gifta Dakinta sai naji gabadaya Duniyar ta Juyamin baya..!
Tana Fade tana matso hawaye kamar gaske ya Dade yana kallonta kafin ya maida kansa ya cigaba da cin Dankalinsa yana jinta tana Fadin"Wlh nima sai naji Duniyar duk ta isheni Abbansu..Dama nima na mutu kamar yadda yau ba yaya adaron Duniya..!
Sai da ya Kurbi Tea din Dake hannusa sannan ya Dago yana kallonta Cikin Sanyinsa na koda yaushe yace"Zo nan Balaraba..!

Baki ta bude tana kallonsa Ganin haka yasa ya gyada mata kai alaman tazo ba musu ta mike ta isa kus????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? a dashi ta zauna Juyowa yayi suna kallon juna Hannayenta ya kama Duka ya Rike yana Tuna Nasihan Baba Mallam aranar da Hadiza tayi arba"in da Rasuwa ya Horar dashi Kada rashin Hadiza yasa ya cutar da Balaraba ya sani Ko sau Daya ya Danne mata Hakki Allah zai tambayesa..!

Cikin Idanuwanta ya kallah kafin ya fara fadin"ki daina Fadin haka Balaraba..Mutuwa ta Allah ce..Hadiza batayi gaggawa ba sannan muma da muke Duniyar jiranta muke..Ko yau ko Gobe zamu mutu..Saboda haka ki Sani Hadiza tatafi ba domin tana son Tafiya ba..Addu"rmu take Bukata ba kuka ba..Don Allah in kin Tunata,ki Dinga mata addu"a don Allah..!
Kai ta gyada tana kara Jan hanci Lokaci Daya tana fadin"Wlh Abbansu na kasa ne..Kullum in na tunata sai nayi kuka..Barin ma in na Juya naga gidanan yanzu Dagani sai kai yau babu Yaya..Sai naji kamar nayi ta kuka har Abada..!
Sharr sai hawaye suka Zubo mata Taausayinta ya kamasa yasan ita mai Hidima ce agaresa shi da ya"yansa har Abada wannan kyautatawar nata yana cikin ransa kuma yana gode mata.
Hannu ya Sanya ya share mata Hawaye cikin Tattausan murya ya cigaba da fadin"Haka Allah ya Tsaara..Daman chan ita din bamai Tsawon rai bane..In kina wannan kukan zaki tadamin da hankali naga kamar na gaza ne balaraba..Sannan in kuka ya Haifar miki da Damuwa ina zan saka raina ni da ya"yana da kike zama mana tamkar wata inuwar gingiya mu Rabe ki mu ji Dadi..!
Wlh tallahi nayi rashin Hadiza sai dai nasani da yau baki cikin Rayuwarmu da Raunin mu ya fi bayyana..Allah ya Dauketa ne saboda yasan ina Dake..Na tabbata ko ni yau Allah ya Dau raina ke zaki zama madadina da madadin Hadiza..Girmanki a idona mai girma ne Balaraba..Yau zan gode miki bisa Hidimarki gareni da ya"yan Hadiza da? baki bari sun yi maraici ba..!
Tunda ya fara mgana take kallonsa Zuciyarta ta cika da Farincikin da shekaru aruru basu sa tayi shi ba sai yau..Daman haka take so ta zama Komai na Sa"idu da ya"yansa wanda basu da wata Dama sai ita ta Kasance itace jinsu da ganinsu kuma tayi nasara bayan Shekaru ashirin da wani abu akallah yau ta fara Hango kamshin nasara cikin Wahalar data Dade tanayi..!
Ammh sai bata nuna ba sai ta Sadda kanta tana fadin"Basai kamin godiya ba..Aikina ne nayi maka Biyayya da Hidima mganar yara kuma ka bari bana so..Tun yaya nada rai yaran suke ya"yana Har ga Allah ina masu kaunar da banayi ma ya"yan cikina..!
Cikin Farinciki yace"Nayi kuskure..bazan kara Fadin haka ba Allah ya jikan Hadiza ke kuma Allah yayi miki albarka..!
Ta amsa cikin Farinciki acikin ranta da Ameen Ameen..!
Tare suka karisa karyawan cikin Farimciki ranakun da Balaraba bazata manta dasu ba acikin Rayuwarta..!
Ita ta kwashe kayan da suka bata zuwa Kitchen sannan ta Dawo Dakin nasa.
Sai ganinsa tayi Tsaye yana saka agogon Hannunsa na fata cikin Mamaki tace"Fita zakayi..?
Bai kalleta ba yace"Ina so na fita saboda akwai wadanda zasu zo Diban kwai yau..Sannan masu aikin gonar mallam ta bazanga sun kirani Suna bukatar taki nasu yaja baya gaskiya shine nake so na fita na leka Mallam muyi mgana sai na Kira Jafaru naji ya zamu yi..!
Farinciki ya cikata abaya fa sai dai Ya fadama yaya irin wannan batun ammh yau babu yaya Dole dai kanwar nakin itace komai cikin Alhini tace"Na Dauka yau zaka tayani zama..Tunda yaran duk suna makaranta..!
Ta karishe Fada cikin Shagwaba kamar wata yarinya Mirmishi kawai yayi yana Fadin"Bazan dade ba zan dawo..Daukomin Hula in saka..!
Ba musu ta shiga ciki Ranta Fes ta Zabomai hula kadan shaddan Jikinsa kalan Sararin samaniya ita da kanta ta sakamai ta feshesa da Turare ta Daukomai Bakin Takalminsa Budadde ta Gogemai ta bashi ya saka ta Dauko Wayarsa da key din Motarsa ta mikamai ya karba yaana yaba Kokarinta akansa cikin yabamanta yace"Allah yayi miki albarka..!
Kanta na kasa ta amsa da Ameen
Fita yayi tabi bayansa sai da suka zo Tsakar gidan sannan ya Tsaya Dakin yaya ya kalla na wani Lokaci kamar ita zai gani tana zaune kofar Dakinta Cikin baranda kamar yadda ta saba Sai dai ina mai Rabawa da Riga ta raba..!
Mamanmu kuma Tuni Farincikinta ya Gudu ganin inda yake kallo cikin Kissa ta kalli wajen kafin ta Sauke Numfashi Tana fadin"Kaima sai kaji kamar zka ganta ko..!Nima haka nake ji Koda yaushe..Su kansu yaran sun kasa sakewa Wuni suke cikin Dakin musamman ma Amina gani take kamar yayan zata Dawo watarana..!
Kai ya jinjina yana kokarin Daidaita kansa yace"Nayi tunanin ko na Dauko Goggo Jumai ce tazo ta zauna Dakin yayan..tunda chan gidan nasu fa ba kowa ko ya kika gani..?
Mamanmu taji kamar ta saka kuka Yaya ta rasu ammh bazata Huta ba..!
Cikin Danne abunda ke ranta ta kallesa kafin tace"Ka raina kulawar da nake basu ne..?
Cikon Daburcewa yace"Me ya kawo wannan maganar kuma..?
Sai ta fara kuka tana fadin"Eh mana ka raina ne..In ba haka ba meyasa zakaje ka Dauko goggo Jumai Salon mutane suju suce bana rike su Amina Tsakani ga Allah in ko ka jamin wannan Shedar bazan taba yafe maka ba Sa"idu..!
Sai ya Rude ya Rikota yana Fadin"A"a fa ba Haka nake nufi ba..Kada kimin mumman Fassara..!
Cikin Jan hanci tace"sai dai in ka janye mganar Dawo da goggo Jumai sannan zan yarda ba haka kake nufi ba..!
Da sauri yace"Na janye..Daman Dake kadai nayi mgana ko Mallam ban yi mgana dashi ba..Itama goggon da wuya ta yarda tunda wajen jikanta Take zaune dake Hadeja..!
Sai alokacin ta saki ranta da Fuskarta tana Fadin"Bana son abunda zai min Shamaki da yarana..Ina matukar kaunarsu kamar ni na Haifesu mussaman Diyata Amina..!
Mirmishi yayi bai ce komai ba ya Fara Tafiya tabi bayansa ganin har sun fita Koridi yasa ya Juyo yana fadin"Na zama dan gata kenan..Rakiya za"ayin har waje kenan..?
Sunkuyar dakai tayi tana Dariya sai kawai ya kalleta yana fatan kada ya Dannen hakkinta domin karfi hali kawai yake yi.
Har bakin get ta rakasa Motarsa tana Gidan Baba mallan sukayi sallama har zai fita ya juyo yana fadin"Kin Duba Cefanan kayan abincin da Jafaru ya kawo jiya kuwa..?
Tace"Na duba komai yayi..!
Yace"Ba abunda za"a karo..!
Kai tsaye tace"Sai dai goldenmorn saboda yaran nan..Sai Cornfkles naga Kwali Daya ne .!
Kai ya gyada kafin yace"Shikenan zan fadama Jafar zai kawo anjuma..!
Daga haka sukayi sallama ta Bishi da Allah ya Kiyaye hanya.
Yana wucewa ta koma cikin gidan Tana takun Daidai kamar wata Sarauniya sai da tazo Tsakar gidan ta Juya ta kara juyawa kafin ta kyalkyace da Dariya tana Fadin"Burina ya cika..Abunda na Dade ina neman ya Kusa Tabbata..Sa"idu ya zama nawa Dashi da komai nasa..Ni Dayyaba duniya Sabuwa..!

Sai kuma ta fara Dariyan kamar tayi hauka Karan wayarta Dataji shi ya Sa ta Ruga zuwa Dakinta sunan wanda ke kira yasa gabanta ya fadi ta Dauka da Sauri tana Fadin"Gabana ya fadi madina..Kada ki cemin min kuskure ma wannan karon..?

Tsaki Anty Amarya taja Dagachan bangaran kafin tace"Kice zaki kuskuremin Dayyaba..!
Da mamaki tace"Ni kuma..?
Kai Tsaye tace"Eh mana..Tayaya zaki shanyani ina jiranki ban ji wata mgana Daga bakin ki ba..?
Ko Saboda na taimaaka miki kin samu cikar Burinki ni kuma sai ki ki bani Damar da zan cika nawa..?Auto kin samu Sa"idu atafin hannunki Dayyaba zaki juyamin baya..To baki isa ba..In kikace zaki haka na Rantse har ga Allah zan sakaki a Tara ba uku bama..

Cikin Tashin Hankali da Sigan Lallashi Mamanmu ta fara fadin"Haba Madina taya zaki min wannan Fahimtar..?Sa"idun ai bai gama zuwa Hannuna ba ke kinsani kuma komai zan yi yanzu sai da Lura kada ki mamta Fuskarmu ta Balaraba da Marliya akasani ba"asan Fuskar Madina da Dayyaba..Ina sane da aikin mu kan Amina Dayyaba..ina sane so nake nabi komai Daki Daki yadda in komai ya Lalace baza"a taba zarginmu ba..!

Sai alokacin ta sauke Numfashi tana Fadin"Kinsan abunda yasa Sakina bata Damu ba..Saboda nace mata zan Lalata wannan auran zai zama mara amfani Dayyaba..Kuma ke zaki mun wannan kokarin bana shiri da yarinyar..Ke kin jata ajikinki tana ganin girmanki Fiye data uwarta..Bana son na gaza..Sakina ce kadai Tauraruwa agidan Umar Dayyaba..kina saka Amina ta samu Baba Mallan tace mai bata son wannan auran zai rabashi,Sannan shi kanshi Sa"idun ki hillacesa ya Furta ma Mallam kinsa akan auran Daganan Mallam zai kullacesa Burina Zai cika ma ganin baraka Tsakanin Mallam da Sa"idu sannan Wannan yarinyar ta fita Daga Tsarina..!
Mamanmu tace"Kada ki damu yau zan fara aikin mu..nayi miki alkwarin yau zan Turata gobe zaki ji Labari mai Dadi..!
Cikin Farinciki tace"Dakyau..Nasan zaki iya..In hakan ta faru ki Sani Sa"idu zai kara zama naki ke kadai har gaban Abada..!
Atare suka saki Dariyan Nishadi da Tunanin Duniya ta Bude musu sabuwa abunda basu sani ba Alkwarin Allah bazai taba tashi ba sannan Dan Hakin Daka raina watarana shi zai tsole maka ido..!

*****

Sai shidda da wani abu na yammah suka dawo daga makaaranta Karfe hudu suka tashi Hadda suka shiga Islamiya,Amina da Hamida sai da suka Biya suka gaida Hajiya babba da ke Fama da kafa.
Sun fito Daga Dakin Hajiya Babba suka iske har ya Abida ta baje afalo da passQ tana Faman dubawa Daga Dawowarta dayake sun yi nisa a jarabawarsu sun kusa gama Neco zasu fara Weac,su kuma su Amina sun gama Exam hutu suke yi sai in sun koma zasu shiga SS2..!
Amina ta kalleta tana fadin"Ubanki Boko..Boko..Bokoko..!
Abida ta Dago tana kallonta cikin Harara tace"Allah yasa dai ba ni kika Zaga ba Amina..?
Da sauri Amina tace"A"afa..Ni Ubanki Boko nace..!
Kai ta gyada kafin tayi kyaci tana Fadin"Da kin Daku na Rantse..!
Amina ta Murguda mata baki tana Fadi kasa kasa"Sai dai ki Daki wannan mai Dogon wuyan..!
Ta jita sai dai bataji karshen ba Hanne da Hamida ne sukaji suna kunshe Dariya Saboda tuna wanda zai auri ya Abidan da Mallam ya basu izini su zo su gana,Har na ya Zeenatu yazo shi dai bai da Muni sai bakin masifa kamar na Zunubi na ya Abida kuma Fari ne girman Lagos tunda hannun yayan babansa ya tashi Dake lagos Jikinsa na Hutu ne sai dai kamar mace har muryansa kamar ta mata yaa wani Lamgwabe kai sai Dogon Wuya rana Daya sukazo su Amina saboda Bala"i sai da suka Labe suka gansu haka suka dinga Dariya,sai kuma suna Tsokanar su kasa kasa suna Dariya..!
Yau ma ya Abida cewa tayi"Amina maimaita abunda naji kince..?

Amina tace"La cewa fa nayi ina Uncle Jalil..?
Wata uwar harara ta banka mata kafin tayi Tsaki ta cigaba da abunda take yi yasa su ka kwashe da Dariya ta Dago tana kallonsu Suna ganin haka suka Danne bakinsu suna zare ido ganin haka yasa. Ta mike tana fadin"Yaran nan kun ranani Wlh yau sai naji Ubanku..!
Ganin ta Nufosu yasa suka Rumtuma Hanne ta shiga Dakinsu su kuma su Hamida suka fice aguje ganin haka yasa ta Dawo tana fadin"Hanne sai dai in bazaki fito ba..Marasa,kunya ko naga wanda Baba mallam zai kawo muku..Gwara Amina ta ga nata ku? ba"a sani ba ko wasu kala ne don mai garinku..!

Hajiya babba tana Daki tana jinsu Dariya takeyi ita kanta ranar da Jalil din yazo ya gaisheta sai da tayi Dariyan yadda yake karya wuya Gwarama Auwal din Zeenatu sai dai shi kato ne ga baki..!

Aguje suka shiga gidan Mamanmu na Alwala bakin Famfo ta gansu sun fado har ta tsorata ta zabura tana fadin"Lafiya..?
Hamida ce tace"Amina ce ta Tsokano ya Abida shine ta biyomu..!
Tsaki taja kafin tace"Shine zaku shigo da gudu wlh har kun tsoratani..!
Daga haka ta cigaba da alwalanta Hamida ce ta zube kan Tabarman da suke shimfidawa duk dare su zauna zaman hira kafin kowa ya nemi makwanci.
Amina kuwa Dakin yaya ta shige taga ya zeenatu na zaune tana karatu itama ganin yadda Amina ta shigo yasa ta Dago tana fadin"bana son hayaniya ki koma Dakin mamanmu..!
Amina ta kalleta da Hijabinta na Hadda bata cire ba cikin Danne Dariyanta tace"To..!
Ta kama Hanyar fita tana fadin"Baki baki..baki fentin Allah bana Mutum ba..!
Zeenatu ta bita da kallo Lokaci Daya ta bata rai gaskiya Amina ta fada Auwal akwai baki gashi kato Allah na Tuba ina zata kaishi..!
Hamida fashin Sallah take yi Amina ce kadai ke sallah ita tayi alwala tayi sallar mangariba,itama bata Dade da yin wankan tsarkin ba.
Suka fito waje suna Hira abinci suka Dibo ita da Hamida suna ci Shinkafa da wake da Miyar Jajjage suna ci suna Santi Mamanmu na cikin Daki tunda ta shiga sallah bata fito ba ita da ya Zeenatu..!
Da aka kira isha"i ma awaje Amina tayi Sallarta bayan ta idar suka cigaba da Hira da Hamida Amina mantawa take tana da aure in ba wani ya Tuna mata Ba Hamida da Hanne ce tunda sukasamu Amina ta Dawo yadda take? basa Dauko mganar da zai Dagula mata Lissafi.
Mamanmu ce ta Leko tana Fadin"Ina Jawaad..?naga ban gansa bane..!
Hamida tace"Muna dawowa makaranta yaga Aba ya manne masa suna Falon Baba mallan yanzu..!
Kai ta gyada kafin tace"Amina zo ina son ganinki..!
Ba musu Amina ta mike ta Bita Ciki Hamida bata damu ba sanin Sirri Tsakanin mamanmu da Amina sun saba komawa tayi ta kwanta saman Tabarman.
Mamanmu ce kan gaba har cikin Bedroom dinta ta zauna gefen gado tana fadin"Taho ki zauna nan mgana nake som muyi..!
Ba musu Amina ta zauna tana fadin"Lafiya kuwa mamanmu..?
Mirmishi tayi lokaci Daya tana Dafa kafadan Amina kafin tace"Bakomai mgana zamu yi ki natsu ki Saurareni..
Amina ta natsun tana jinta Mamanmu sai ta gayyato damuwa afuskarta kafin tace"Amina kinsan ina kaunarki ko..?Kaunar da ko Hamida bata same shi ba..?
Amina tace"Bama ni ba Mamanmu kowa ya Shaida Amina ce kadai Diyarki..!
Cikin Fara"a tace"Yauwa Diyata shiyasa na damu da rayuwarki sosai..Abunda ya faru na rasuwar yaya shiyasa ban Daga mganar ba..Ammh abun na raina Amina ko barcin Kirki banayi..!
Amina ta kalleta da mamaki kafin tace"Menene yake hanaki barci mamanmu..?
Cikin Sauke murya tace"Kan auranki Da Danmallam ne Amina..Sam baku Dace ba..Kina karama dake ta ina zaki iya auran wanda ya kusa haifanki uwa uba kuma kishi da mata Biyu..Ni ban ma jin balarabiyar Sakinar dai Daman chan ita da uwarta ba kaunar mu suke yi ba inaga kuma aure ya Hada..!
Shuru Amina tayi jikinta yayi sanyi bata son tuna yau ita matar aure ce..Har yau bata karbi wannan kaddaran ba ta kuma kasa zama ta fuskanci da gaske ne abunda ya faru..!
Yasa ta kasa mgana har sai da mamanmu ta cigaba da bata mgana da kuma nuna mata illah auran kuma ta yarda da ita matuka ta kuma san gaskiya ta fada barin ma inda tace"Amina a kuruciyarki naso ki sami Saurayi kamarki ki aura..Ba Umar ba..Ba sonki yake yi ba wahala kadai zaki sha ahannunsa da matarsa..Me zai hana ki fito fili ki Fadama Baba Mallam bakya son auran nan..?na tabbata zai saka Danmallam ya sakeki ki auri wanda kike so yama sunan Surukin nawa..?
Amina ta Kalleta da Idanuwanta da suka fara ruwa cikin karyen Murya tace"Aminu..!
Mamanmu tace"Yauwa Aminu..Ashema Amina ce da Aminu.
kada ki damu da zarar ya sakeki? zan san yadda nayi kika auri wanda kike so nayi miki alkwari kin san dai ban taba miki alkwari na gaza cikashi ba ko..?
Amina ta gyada kai tana Zubar kwallah kafin tace"Ina tsoro Mamanmu..In Aba yaji wlh zai Kasheeni..Kuma ni bazan iya kallon Baba mallam da Hajiya babba nace bana son jininsi ba kamar in nayi hakan ban kyauta ba..!
Kamar ta kwadaa mata mari haka taji ammh sai ta cije tana Sassauta murya tace"Kada ki damu da wannan Zan san yadda zan yi..Aba dinku ni zan bashi mgana shima ai ya Fahimci an kwareki wlh..Nasan Hajiya da Mallam zasu fahimceki nasani..!
Kidai kije kiyi mai mgana na Tabbata zaki ga abunda nake fadama miki..!
Amina na sharan kwallah tace"To me zan ma Mallam din..?
Mamanmu ta gyara zama tana Fadin"Yauwa ko kefa..?Kuka Zaki sakamai kina fadin baki son auran don Allah yasa Danmallan ya Sake ki shikenan..!
Amina ta jiku da Hawaye kafin tace"Kina ganin ba matsala mamanmu..?
Da sauri tace"Babu matsala nace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login