Showing 18001 words to 21000 words out of 265571 words

Chapter 7 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28881

har Kuma alokacin ko Fegin Fili bai dashi na kansa Duk inda yaje za"a basa Gida ya Zauna har sai ya gaji ya tashi Tunda alokacin Duniya na kwance Malamai Darajasu akeyi sannan ana Kimantasu da musu kallon su din magada Annabawa ne ba kuma kamar yanzu da suka yawaita ba Alokacin basu da yawa.
Agarin da Malam Yunusa ya fara Zama agarin Gusai ne anan ya siya Gida mai suna gida Suka zauna Domin su samu natsuwar zuciya Shida Zainabu Tunda Tana da karancin Shekaru malan zanna ya aura masa ita kimamin Shekaru goma Sha Biyar alokacin.
Yayi Shekaru akallah zasu kai goma agarin na Gusai Anan ya bar Zainabu sai dai yana yin Tafiye Tafiye ballatana alokacin Malamai sun Fitar da da"awan da suke zuwa gari gari suna yi Domin Sanar da addinin Allah kuma Malam Yunusa yana Daga Ciki bayan Haka a Inda yake yana karantar da Kimamin Dalibai da baisan adadinsu ba Sannan itama Zainaba Daga Cikin Gida Tana karantar da mata kafin kace me Sunan Malam Yunusa yayi Tambari a garin Gusai da kewanta ballatana kowa da arzikinsa ya gansa Yana da katon Fili kusa dashi nan yake kiyonsa da masu kula dasu samnan yana da gonakinsa na garin bazanga da ake Nomamai Duk Shekara sannan Duk garin daya zauna yana samun kyautatawa da kyautar gonaki da Dukiya tunda bai Taba amsar ko Naira Biyar Domin wani ya amfana da Saninsa ba.
Shikenan Kafar Nasararsa sai ta bude alokacin yan Siyasa sukayi Tunanin irin nasu ne, suka fara zuwa mai da Bukata sai dai yana kokarin Sanar dasu shi baya Shirka baya Duba ammh in kace ya tayaka Rikon Allah Domin Biyan wata Bukata naka zai Tayaka wannan Dattakomsa nasa da Wadatar zucci da ko Duniya zaka basa bazai karba ba,Yaje Saudiya Da kudinsa Har Sau biyu ballatana Lokacin yana Madina Duk Umura da Hajji Dashi akeyinta.
Shikenan kimarsa ta Karu aka Fara Gayyatansa Taron karama juna Sani na Malamai sannan Har ana gayyatansa Gidajen Radio da Gidajen Talabijin Abunda ya karamai Daukaka yana Daraja na sama Dashi Malamai haka yake Daukan su Tamkar Madubinsa komai girmamsa haka zai Duka gabanka yana neman Sani wannan Dabi"a ta Siyamai Soyayya da Daukaka da Nasara Lokaci Daya da ba"a taba Tsammani ba.
Har kuma zuwa Lokacin da Daukakar nasa ta fara ko bari Zainabu bata tabayi ba Duk da yana Fatan Samun magaji bai Taba Korafi ko nina wani abu da Zainabu zata Fahimci ya Damu ba Mutum ne mai Tsantsani da Tsoron Allah da Wadatar zucci.
Ana cikin Hakame kwatsam Allah ya Hadasa da Shaharran Dan Siyasa nan wanda ke rike da Mukamin Kakin Majalisar Ta Jahar zamfara.

*AMINU GUSAI* basu hada komai ba sai da sun Taba Hada yin Makarantar allo anan garin na Bichi kano A talabijin yaga Malam yunusa yana ganinsa ya ganesa Domin alokacin ba wanda baisan Yunusa bazanga ba, Yayi Tattaki har gida yaje ya samesa sukayi Zumunci da Tambayan bayan Rabuwa,Aminu ya sanar dashi bayan Sun yi Sauka yayi karatu shima Har matakin Masters sannan kuma sai ya Fada Siyasa Daman gidansu gidan yan Boko ne da kuma Tsofaffin masu Kudi Dayake awanchan zamani Karatun allo yana da Daraja ba kamar yanzu Domin yawancin manyan mu na yanzu in da zasu baka Tarihinsi zaka Ji cewa sai da suka fara da Karatun allo kafin su dawo su Dora na bokon
Aminu yaji mamakin ganin yadda Malam Yunusa ya koma sannan ya kara yarda ma kamsa yana na nan bai Sauya ba Tunda Har ya iya bari Garin Madina yazo kasarsa yana Wahala.
Daganan Zumunci ya fara Har Ya kawo Iyalinsa Hadiza da Dansa Daya mai Suna SA"IDU mai kimamin Shekaru goma sha biyar alokacin tun gaanin Farko da Yunusa da Zainabu sukayi ma Sa"idu ya shiga ransu Matuka suna son yara suna kewarsu sai dai Allah bai basu ba,Sannan ga Hadiza mai kunya da karamci Sa"idu shima yana son zuwa gidan Malam Yunusa kodomin yaga Dabbobi kaunarsu acikin Ransa yake Ranar har cema Malam Yunusa yayi Baba ina son ka bani Rago in na kara girma na kula Dashi alokacin gaban Dukkan ne ya Fadi mganar Malam Yunusa ya Dafa kansa Cikin Kauna yace"Insha Allahu Watarana kai zaka kula dssu Sa"idu..Fatana ka Dake da Karatu..!
Wannan mgana ta saka Sa"idu Farinciki kuma abunga ga yaro ya rike mganar acikin kansa.
Tundaga Ranar yake murna yana Fadin in ya girma zai zama mai kula da Raguna kowa yana ganin Shirme ne da yarinta.
Duk da alokacin Zainabu zata girmema Hadiza ita Allah ya bata Haihuwan da Wuri tana da kananun Shekarunta Ammh sun zama kawaye tunda Zainabu batasan kowa agarin ba sai suka zama kamar yan"'uwa koda yaushe suna ziyatar juna Sannan Sa"idu duk karshen Sati wajensu yake yi kaunar yaron ta fara ne tun Tuni Sannan Shi kauna Allah ke hadashi ma Mutum ba.
Akwai Ranar da Malam Yunusa suna mgana da Aminu ya kallesa yana Fadin"Aminu ina kaunar Sa"idu ina jinsa kamar dan cikina..Ina ji kamar ya zauna Dani har Abada..!
Alokacin Aminu Dariya yayi ya Dafa Kafadar Malam Yunusa yana Fadin"Haba yunusa ai ni da kai mun Zama Daya..Wlh har araina na yarda da wannan kaunar Dake Tsakaninka da Sa'idu Dama Hadiza nada juna Biyu sai ta Haifa mana wani kai kuma ku rike Sa"idu kai da Zainabu har abada na tabbata ko bayan Raina Sa"idu zai fi Alheri Dakai Fiye Dani..!
Wata mganace da Malam Yunusa ya Dauketa kamar Fadice sai dai ba Haka bane Har azuciyan Aminu haka take Malam Yunusa bai Tabbatar ba sai da Aminu ya Tara Duka yan"uwansa ya Fadamusu ba wanda yayi gaddama Sanin Waye Malam Yunusa Shiyasa kowa yayi Na"am da Batun Hadiza ma bata kawo Damuwa ba macece mai kunya da kawaici Duk da kasancewarta Bazanfara gaba da baya.
Malam Yunusa yayi kukan Murna Aranar da Aminu da Hadiza suka Dauko Sa"idu da duka kayansa suka kawo musu shi Har abada shi da ZAINABU sun kasa Daina kuka suna ganin kamar mafarki ne sai dai Zahiri ne,Sa"idu bai damu ba ya Saki Jikinsa Sosai Saboda Dabbobi daman yafi son gidan Baba Malam kamar yadda Sa'idu shine Mutum na Farko Daya Fara Radamai wannan suna kuma yake binsa yana alfahari dashi.
Abu kamar wasa karamar mgana ta zama ba Sa"idu ya dawo hanun Malam Yunusa da matarsa zainabu abun Tsusayi Cikin Da Hadiza ta Samu ta Haifeshi ba rai ammh duk da Haka basu Damu Sa"idu ya cigaba da zuwa makarantar Boko sannan kuma Malam da Zainabu suna Karantar dashi karantun addini acikin Gida sannan suna iya bakin kokarinsu wajen Tarbiyansa da Rike Amanar da aka basu
Wajen sau uku Hadiza na Haihuwa ba rai sai ana Hudu ta Tsaya macece mai Suna Hafsah sunan Mahaifiyar Aminu ce suna cemata Husai sai kowa ya samu nashi Sa"idu na zuwa ganinsu Lokaci bayan Lokaci kamar yadda suma basa gajiya da Ziyartan Juna.
Tun alokacin ana ta yima Malam yunusa Tayin ya"ya Domin ya kara aure ko zai Samu Haihuwa sai yace A"a Domin Zainabu nada kima awajensa,Sannan koda an mai mganar Haihuwa sai yace Sa"idu ya isheni Rayuwar Duniya da Lahira Saboda irin kauna da Shakuwar Dake Tsakaninsu suna bashi Dukkan wani Gatan Duniya sai dai suna kokari wajen Kula da Tarbiyansa.
Cikin Ikon Allah kamar yadda Malan Yunusa yace Haihuwa ta Allah ce Hakan ce ta kasance Domin Sa"idu ko Shekara uku bai yi da Dawowa Hannunsu ba Zainabu ta samu Ciki kuma Haihuwarta na Farko Ta Haifi Namiji Malam Yunisa ya saka masa Suna UMAR IBN YUNUS..!
Koda zainabu ta Haihu mganarsa Dayane Sa"idu ne babban yaro na Domin kafin na Samu Umar Sa"idu na Haifa,Duk da Mutane sunsan ba Dansa bane ammh suna Girmama Kaunar dake Tsakaninsu kuma koda suka samu nasu babu abunda ya Sauya Daga soyayyar da sukemai.
Yayinda Aminu Daga Husai Hadiza bata kara ko barin wata ba kuma basu Damu ba Tunda Da ga Allah ne sun Tabbatar Sa"idu yayi Dace da iyaye nagari kuma ko bayan ransu Watarana sai yayi alfahari da hakan
Tundaga lokacin Haihuwa ta Budema Hajiya Babba Daga Umar tazo tayi Nazir wanda Tsakaninsu ba Nisa alokacin kuma Malam Yunusa ya kara aure Shima Bashi matar akayi sun je Da"awa garin Tsafe na Jahar Zamfara gidan Malamin da suka sauka Malam Hamza ya Dauki Yarsa Kwara Daya cikin jerin ya"yansa Uwani ya bama Yunusa shi kuma bazai iya Bijiremasa ba ya karba Hannu Bibbiyu achan aka Daura aure sai dai ya Dawo da mata kawai Sannan bai samu matsala da Zainabu ba ta karbi Uwani Hannu Bibbiyi suka cigaba da zaman Amana ko ita sai Daga baya tasan ba Malam ya Haifi Sa"idu ba shima sai da ya Fadamata ta yarda ammh tana Girmama wannan kaunar Daga Malam din har Zainabun da ya"yanta basu da Mganata sai ta Sa"idu ko"ina kaje agidan nan Sa"idu ne wannan kaunar Daga Allah ne.
Haka Rayuwa ta cigaba da gangarawa da Dadi ba Dadi Malam na Cigaba da nenan sani da Da"awa sannan Lokaci Daya yana karantar matasa Abunda ya sani na Addini Alokacin Aminu gusai akayi Chanjin gwannati bai samu Kakin majalisa ba sai aka Nada wani Daga Shekarar kuma Jinya ta kamasa na Ciwon kafa Daga Sama Sama sai abu ya Zarce baya iya tashi Sai dai a kwantar atayar Jinya tayi Jinya anyi mganin Asibiti anyi na gargajiyam Duka ba"a Dace ba Sai da Duka Abunda Alhaji Aminu ya Tara ya kare Malam ma bai zauna ba Shima Duk in da yaji wani mgani zai amsomai Sai dai ita Kaddaran Allah Daman Dayace komai Tsalle Tsallen bawa bai isa ya Gujemata ba, Aminu gusai ya Rasu Lokacin da Jinyarsa ta karar da komai ya Rasu ya bar Matarsa Hajiya Hadiza da Yarsa Husai da Sa'idu ko kafin Rasuwarsa ya kara Jadaddama Malam Sa'idu nasa ne har Abada wannan karamcin na Aminu Malam har ya koma ga Allah bazai manta ba.
Yaso ya Dauko Husai da Hajiya Hadiza ya Rikesu sai yan"uwan Aminu suke roko alfarman ya bar musu Rikonsu sai ya kyale musu Tunda karamcimsu garesa mai girma ne Gidan yayan Aminu Hajiya Hadizan ta koma da zama ita da Husai ba kyashi ba Hasaada riko na Tsakani ga Allah Sa"idu Lokacin yana makarantar kwana ta Hassan gwarzo Dake kano Aminu ya rasu sai da ya Dawo yaje yayima iyayensa gaisuwa Kowa bashi yake tsausayi ba Domim cewa ake Aminu yayi ma Sa"idu gata Domin Uba irin Malam abun Alfaharin kowani Cikakken D'a ne.
Tun Rasuwar Aminu Garin Gusai ya Fita kan Malam Yunusa batare da Shawara da kowa ba ya Fara Binciken yadda zai tashi Daga garin Dayake Tunamai da adalin Amini kamar Aminu,Ba Dadewa ya samu Cikakken bayani kan garin Gumel da yadda Suke da amfanin gona da Sauran Cigaba ba Dadewa ya mallaki Fili a wannan anguwan ta Zango ya Fara Gina iya adadin ida zasu zauna.
Sannan ya samar da Katon Fili Domim Kiwo yayi alkawarin Sa"idu sai ya zama wani abu sannan yana da Burin Cikamai wannan Burin nasa.
Dawowar Malam Yunusa garin Gumel baima Hajiya Hadiza Dadi ba Saboda ta Saba da Hajiya Babba sosai sannan Husai ta Saba da su Umar ammh bata da yarda zatayi tun anan din ma ba Wahala take ciki Yan"uwan Aminu ba suna Rike dasu tsakani ga Allah Duk da itama Duka na gida ne
Shekarun da suka Shude masu yawa ne sannan sun zo da Nasarori da Dadama da kuma akasinsu Sa"idu ya gama Secondary ya Fada Jami"ar garin Dutse yana karantar agric abunda ya Shafi noma da kiwo Ko alokacin Gidan gonar Baba Mallam Dake kusa dasu Sa"idu ke da Ahakin kula dasu Haka Allah ya yisa Zama Cikin Dabbobi sune ke sakashi Nishadi sannam Agarin ba wanda yasan Sa"idu ba yaron Malam bane Sannan kowa Dauka yake Shine Babba sannan su Umar Duka kannensa ne,Malam bai yi kasa a gwiwa ba anan din ma ya Cigaba da Karantar wa Ya Hakura da neman ilimi ya Zauma yana karantar da Duka Dalibin Dayazo wajensa neman ilimi Sannan bai da ina zuwa Da"awa ba duk inda za"a je dashi ake zuwa.
Zuwa Lokacin Malam ya Kara auran yar nan garin Jigawa ce Hajiya Nasara ita yar Masu kudi ce sannan zuwa Lokacin Gidan Malam ya fara Cika da Ya"ya kamar yadda yake fata sannan bai manta da Hajiya Hadiza da Husai ba da Lokaci bayan Lokaci suna zuwa suma suna zuwa sannan babu abunda suka nema suka rasa na bangaran Rayuwa.

*******

*Bayan shekaru Talatin..*

Cigaba da Nasaran Rayuwa da Rashi da Samu ba wanda Baba Malam bai gani ba ya Samu Nasara ya Daukaka bama Nageria ba Duniya gabadaya ta Shaida Iliminsa da Sadaukarwansa kan kasarsa zuwa Lokacin hatta Kasar Saudiya tasan da zamamsa yasan Manyan Mutane masu Saurata da masu Dukiya yasan manya malamai kala kala ta Dalili Jajircewansa da kuma Dattakonsa zuwa Lokacin baisan adadin Daliban Daya rike ya karantar ba kuma ya Taimaka musu suka zama wani abu baisani ba Sai Dai Burinsa ya Cika ya amfanar da iliminsa ga al"umar kasarsa kamar yadda yake Fata.
Yayi rashin Amini kamar Alhaji Aminu sannan kuma sunyi Rashin Hajiya Hadiza Cancer ce ta kasheta sannan sun aurar da Husai Tana Jordan da zama ita da Mijinta da iyalanta wanda ya kasance amsader ne mai Wakiltan Nageria Akasar sannan kuma Burinsa ya Cika Sa'idu ya zama wani Jigo..Jigon Dayake alfahari dashi har yau har gobe Sa"idu yayi karatu har matakin Master akan abunda ya Shafi sanin Noma da kiwo sannan baisan adadin Kwasakwasan Daya Hallata kan Abunda ya shafi abunda yake so ba Sannan Bayan haka shi ya bama Baba Malam Shawaran Siyan wani Katon Fili a Farkon gari Dake Hadeja Road Inda suka Samar da Katuwar Gidan Gona babu abunda babu,na kiwo awajen katon Fili ne mai kama da alkarya Guda Abaya iya Dabbobi ne yanzu kuwa da aka Cigaba Har da Kaji da Talo Talo komai fa babu abunda babu Sannan kuma an Fadada abun har da Offices acikin wajen sannan akwai ma"aikata masu kula da wajen da masu Dawainiyar Kwashe kwaiyayan in Kaji sun saka sannan Baban Gidan Gona ne da kaf garin Gumel ba Kamarsa da kewaye.
*GIDAN GONAR BAZANGA..!
babu wanda baisan da zamansa ba Sannan Sa"idu shi ke da alhakin Kula da komai na Dukiyar Baba Malam,Sannan bangaran Gonakinsa Sa"idu ke da Ahalin kula da komai Daga Daukan masu Noma biyan su Cire amfani gona Fitar da zakka Komai na Hannunsa ne Baba Malam abu Dayane ke gabansa yakan Koyar da Dalibai Kadan Daga abunda ya Sani ammh Gabadaya alhakin Kula da Dukiyarsa da Komai yana Wuyan Sa"idu ne,Tare suka wahala sannan Kusan kula da komai dukiyar ta habaka Jajircewan Sa"idu ne.
sannan har zuwa wannan Lokacin Sunan Sa"idu ne gaba abakin Malam kafin ya"yansa
Baba Mallam yayi ma Sa"idu Auren Farko da Hadiza Haifaffiyar garin nan Gumel ce sai dai marainiya ce bata uwa bata da Uba ba wani Cikakken Dangi Labarinta yaji ya Tsausayamata Tana daga Cikin marayun da suke samun Tallafi Daga Kungiyarsu na Ahalus sunna Sa"idu tunda yake bai Taba Saba mganar Mallam ba Gabadaya Rayuwarsa ta kare ne a Yimasa Biyayya Da Hannu Bibbiyu ya Karbi Hadiza,Bayan Baba Malam ya gina mai Filin Dake kusa Dashi Daman Tunda ya siyeshi da Sunan Sa"idun ya siya Halak malak.

Shekararsu Biyar da aure Har sun samu karuwar ya"ya Biyu Jafar ne Babba ne sai Jadwa sai kuma tazo tayi Jaleela daganan ne ya kara aure da Balaraba yar"uwansa ce Daga Gusai Daga Dangin Babansa suka auramai ita tazo suka Hade kai da mamanmu suma zaman Lafiya da juna.
Sannan Daga gefe Dayama Malam ya kara aure da Marliya Itace yarinya Cikin matansa ita yar Garin Dutse ce sannan itama kakanta Malami ne sun gaji arziki da malamanta itama yazo ya Hadata Cikin matansa ta shiga Zazzaga ya"ya Kamar yadda gidan Baba Malam ya Cika da Wadatar ya"ya Haka Gidan Baba Sa"idu Wanda suna ne da su Umar suka sakamai kuma ya bisa,Shi Allah ya basa Haihuwar akai akai ba kamar Mahaifinsa ba da su Biyu kadai ya Haifa ba,
Sannan sunan Sa"idu ba arayuwar Malam ba kaf a Duka ahali da Zuru"arsa wannan Kauna Tsakanin BABA MALAM da BABA SA"IDU daga allah ne Kaunace da Duk hassada da Kyashinka sai kabarsu sun Hade sun zama abu Daya da har har gobe Baba Mallam Sa"idu ne agabansa Duk kuwa? ya"yansa sun Girma ammh bakin sai sai ya ambaci Sa"idu kafin su kamar yadda shima Baba Sa"idun duka Rayuwarsa baida wani abin Dubawa Wanda ya zamemai Madubi Wanda shi yake kallo amtsayin komai Daya Taka na Rayuwa sannan yana Mai kauna Kaunar dako Mahaifinsa Daya kawosa Duniya baya masa kwantankwancin kaunar Dayake ma Baba Mallam..Ita Kaunar junansu Daga Indallahine.








*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janaftyd'?*


*
Ayanzu kimanin Matan Auren Baba Malam Hudu Cif ya riga ya Rufe kofar Sannan da albarkan Ya"ya Guda Ashirin Daga duka jerin Dakunan matan nasa.
Hajiya Babba keda shida Daga bangaranta Bayan Umar da Nazir sai da aka Auro Hajiya Uwa kafin ta sake Haihuwan Nasir,Daga sai Aisha sai Abida sai karamarsu ta baya baya ce Ta karshe kuma Auta Hannatu.
Sai Hajiya Uwa Dake da guda Biyar itama Babban shine Nazeem,Su.Nasir sun Girmemasa saboda sai da suka Dawo Gumel ta dan Dadewa ta Haifeshi,Sai Uzairu,Nazifa da Umaimatu sai Shamsu Ta aurar da Nazifa wacce ke garin Abuja ita da ya"yanta Umaimatu ma Saboda bata da Lafiya ne ammh a ka"idan Gidan Mallam bakya wuce sha takwas yake aurar Dake mazan yaransa ne ke Karatu mai Zurfi.
Sai Anty Nasara itama ya"yanta Biyar Fatima ce babba sai Akila sai Ikram,Akilu da Zubairu sune yaran Matasa Sai Anty Amarya ita kuma Tana da yara Hudu Jidda ce Babba saimai bi mata Sadiya sai Sa"adatu karamarsu kuma Sabeehatu.
Hajiya Babba ta gama aurar da Duka Mazan ya"yanta Umar Shine Babba yana Madina,Shi Tun farko bai yi Rayuwarsa anan ba Yana gama Secondary Shcool Dinsa Baba Malam ya Turasa Madina Wajen Abokinsa da Sukayi Karatu Tare A madina Kattab,Wanda yanzu yake kasuwancinsa achan Madina Balarabe ne Asalin Haifaffan Garin Ma"aiki wato Madina achan yayi Degree dinsa na Farko kan Islamis Studies sannan yayi maaster dinsa kan Qur"an and Islamic Studies Domin Shi Umar irin Mahaifinsa ne Tarin Baiwa da kuma Daukan karatu ko wani iri ne shima achan haka ya Fita Zakka cikin Sa"aninsa,Shima kamar Mahaifinsa ne sun rike sa achan yana Musu koyarwa Sannan Tuni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login