Showing 6001 words to 9000 words out of 265571 words

Chapter 3 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28912

Har damu da muka Hade dasu muma Dokarsa muke bi Domin har yau har Gobe in ba"a Fada maka ba Mutanen gari Dauka Suke mu jikokin Mallam ne BABA SA"IDU ne babban yaron Malam..!
Kai tsaye shashen Hajiya Babba ta wuce Domin nan ne Dakin su Hanne Auta take ga Hajiya,Bata Tsaya sallama ba ta Tura kofar shashen da Karfi Tana Kiran sunan Hannan.
"Hanne...Hanne..Hanne..!
Take Fada lokaci Daya tana Wulka manya Idanuwanta Cikin kayattacen Falon na Hajiya Dayaji komai na More Rayuwa.
Sai dai mamaikon taga Hanne sai taci karo da Hararan Ya Aisha Dake Zaune kan Darduma tana karatun pass Q domin suna gabda fara WAEC da NECO, Bata katse Karatun nata ba ammh Amina tasan Hararan ko ta macece Yasa ta Daga Hannunta tana Fadin"Yi Hakutri Ya Aisha..sallamu Alaikum..!
Tafada kai Tsaye tana kara Wurga ido wajen neman Hanne.
Abida Dake zaune kan kujera Tana Karatun Qur'ani
Wacce Tunda taji Bangazan kofa Da kira tasan sai Amina itace kadai bata da natsuwa Kaf acikin ya"yan gidansu da gidan Baba Sa"idun.
Itama Hararan ta jefa mata kafin tace"A tsakiyar falon ake sallama Amina..?
Sai alokacin Amina ta ganta aranta ta Furta"Uwar sa'ido..!
Afili kuma sai ta Dan Rasauya ido kafin tace"Sallama fa sunanta sallama Ya Abida..!
Abida daman ai tasan bazata koma ba Kafiya ce da ita kamar kafura.
Bude mata ido tayi tana Fadin"Au bazaki koma bakin kofa ki sake wata ba kenan..?
Amina ta Bude baki tace"Ah gaskiya..!
Cikin kunkuni tace"Haka kurum..Tab...
Abida tace"Me kikace..?
Kallonta tayi da manya Idanuwanta kafin tace"Nifa ban ce komai ba..!
Abida Kai ta Rausaya a cikin Idanuwan Amina akwai wani kaifin da indan ta kalleka sai kaji gwiwanka yayi sanyi..!
Da hannu ta nuna mata tana Fadin"Hanne tana Dakinmu tana Guga..!
Ai bata gama Rufe baki ba Amina ta Kwashi gudu tana kara kiran sunan Hanne Wacce sai Lokacin taji kiran da Sauri ta kashe Iron din Daman Hijabin haddarsu na gobe take gogewa ko mafarki take yi tasan Sautin Kiran Amina Dabam yake kuma akowa da Hannatu yake Kiranta Aminene ce kadai ke kiranta da Hanne.
Akofar Dakin sukaci karo Dakin Dake kusa da Bedroom din Hajiya sai wani Wanda suke Saukar baki Dangin Hajiya in sun zo nesa dana Hajiya.
Kusan karo sukayi da juna Wanda yasa Hanne tayi baya tana Fadin"AMINA gani nan fa..!
Tsayawa sukayi suna kallon Juna kafin Amina Taja hannunta su koma Cikin Dakin Tana Fadin"Hajiya fa..!?
Hanne tace"Tana Dakinta..!
Amina tabi Dakin da kallo ta Sauke ganinta kan Hijabin da Hanne ke gogewa tace"Dadina Dake kina da Zafin Nama Hanne..ni fa ban ji ma Hijabin nawa awanke yake ballatana akai ga gugansa..!
Hanne Dukawa tayi ta kunna Soket ta Cigaba da Guganta ita kuma Amina kan Karamin gadon Hanne ta Zauna Babban na Ya Abida da ya Aisha ne
Hanne bata damu ba tace"ai ke babba ce..Amina kike ni kuma Hannatu..!
Amina Tayi dariya tana Fadin"dillar Sarkin Tsoro..Ki Saki jiki ki amsa sunanki Hannatu Yusus Abdurraham Bazanga kowa shakkarki zai yi..!
Hanne na Guganta bata Dago ba tace"Uhmm..Meya fito dake Daga gida da Daran nan..?nasan da Dalili..!
Amina ta Tabe baki tana Kwabe Hijabin Jikinta Lokaci Daya tana Fadin'"Ke da kika sani..Yau fa Har Yaya sai da ta Dakeni Hanne su Ya Zeenatu suka min gami wajen su ya Jafar harda fadamin in ya Dawo sai na Sani..!
Hanne na Duken ta Dago kanta tana kallon Amina Kafin tace"Kan Tafiyarki yawon da kika saba in an tashi makaranta ko..?nima fa ana tashi nazo ajinku bakya nan..!
Gajiya akayi da jiranki Ya shamsu yace mu taho gida..!
Amina ta Zabga mata Harara tana Fadin"Ni daman bance ku jirani ba..Nasan Hanya..!
Hanne tace'Koma miye dai baki kyauta ba..Amina don Allah ki daina Wasu abubuwan kai tsaye ko ni in kika fadama zakije wani wajen.ko Hamida haka zata faru..?
Amina ta Juya idanuwanta kafin tace"Hanne..Hanne..Ki kyaleni don Allah kada ki batamin rai bazaki iya da Jidali na ba..!
Hanne bata Kara mgana ba itama Aminan haka Sai da ta juya taja Littafin Data gani kan gadon Hanne Ta Fara Budewa kafin ta Dago Tana Fadin"Hanne akwai Kwazo..Kin yi aikin Malamin Lissafin nan..!
Hanne na Nimken karshe a Hijabinta tace"Ba Dole ba kada ma na manta kinsan mugu ne wlh ya Rantse Bulala goma ga duk wanda bai yi ba..!
Amina ta tabe baki kafin tace"Kan bala"i..Wai haka yace..?
Hanne ta kashe Soket din ta Mike Dauke da Hijabin tana Fadin"Ajinmu ba..Bansani ba ko ku bai Fada muku ba..Ammh nasan komai tare yake mana ba bambamci..!
Amina tace"Oho ni fa sanda ya shigo ina chan ina Karatun littafin da Ziyada ta daukomim adakin Antyta Garin Kallon Ruwa kin ji Dadinsa Hanne..!
Hanne ta tsaya kyam tana kallon Amina kafin tace"Amina Daman baki Daina wannan karance karancen nan ba..?kinsan fa in aka sani bazaki ji Dadi ba..!
Amina tayi tsaki tana Fadin"To sai me..?ke zaki fada..?ke ni kyaleni Sai fa nayi kema zan koya miki Allah da dadi..!
Hanne tace"Allah ya Tsareni..!
Amina ta tsuntsire da Dariya tana ganin Hanne ta Bude babban Wadrope din Dake Dakin gefen inda kayanta yake ta sakashi Kana ta Rufo Tana kallon Amina kafin tace"ki Tafi da littafin gida ki kwafe kada muje Ranar Monday Uncle Gaddafi ya Dakeki kinsan Halinsa..!
Amina tace"Dillah Rabu dashi..Duka na Kisa ne..?da yana Kisa da babu Burbushin Amina aduniya kuma ya Dade bai yi Dukan ba Alqur"an bazan yi ba..!
Hanne ta kada kafin tace"Ammh in kika kiyye taba Lafiyarki fa Amina..?
Amina tayi kamar bataji ta ba ganin Haka yasa Hanne ta karisa gabanta Tana Fadin"In ya jafar ya dawo fa..?
Amina na Dariya tace"Ke bazai dawo ba kema kinsani..Yaushe mai wannan Dakalin bakin zata barsa..!
Hanne na Rufe baki tana Fadin"Ke Amina Anty Shamsiyan ne mai Dakalin baki..?
Amina na Dariya Harda Buga Kafa tace"Eh mana baki taba Lura ba..Sai ma in tana mgana..Sweetheart..!
Amina ta fada tana kwaikwayonta Dayasa sai da Hanne ta Duka saboda Dariya Kafin ta Dago ji kake Tas sun Kashe da juna Cikin Nishadi Tare suke Zube kan gadon Amina nama Hanne Rada akunne dayasa ta kara Saka Dariya tana Tureta Lokaci Daya Tana Fadin"Ba ruwana..Ba ruwana Amina..Bazan iya Da jidalinki ba kinsani..!
Amina bata Damu ba Chanza Fuska tayi tana Fadin"Kin Tuna sadda Muna aji uku a islamiya kullum Karatunta Dayane..Anjadada.Kalli Leben nata jadaddaad..!
Dariya sai da tasaka Hanne Hawaye Saboda yadda Amina ke yi da baki kamar Tsohuwa zatace isuhu..!
Cikinta ta Dafe tana Fadin"Ki barni haka Amina kada ki kullarmin da ciki da Dariya..!
Dariyan suke gabadayansu Basu san da shigowar Hajiya ba sai dai sukaji mganarta Daga sama.

"Dariyan me kukeyi haka ne..?
Da Sauri suka jiyo suna kallonta Hajiya Babba tana sanye da Doguwar rigar Shadda ajikinta Mace ce Doguwa ga kiba,Akallah ta bama Shekaru hamsin baya sai dai Hutu sun Lullube shekarunta Da ka ganta Kaga su Hanne da Ya Aisha Saboda suna Kama da ita sosai.

Amina ce ta mike zaune tana Fadin"Hajiya ina yini..?
Hajiya na Daga kofar Dakin tace"Lafiya lau Mamah..Sai yau nake ganinki..?
Amina na Dariya batace komai ba Bata iya maidama Hajiya mgana Saboda Kirkinta,Mamah take ce mata Saboda sunan Mahaifiyar Baba Malam Amina kec dashi basa Kiran Sunanta ita tace Mamah shi yace Mamana..!
Hanne ce tayi zaraf tace"Yau ma Laifi Tayi Hajiya..!
Hajiya ta kada kai tana Fadin"Ohh maamah duk baki ji nasihata ba ko..?Don Allah ki natau ki dinga jin mgana Bana son wannan Korafin Kowa yace ke Babanki Sa"idu kullum Mganarki yake yi hakama iyayenki mata Don Allah Mamah ki rika jin mgana ki zama kamar kowacce y"a acikin Gidanan..!
Zaku Dauka yadda Amina tayi shuru Tana jin Fadan ne nan kuwa bata ma Fahimta Domin indai wannan Nasihan ne ta Haddacesu Daga bakin Hajiya da Baba Malam
Ammh Cikin Dan kada ido tace"Shikenan Hajiya..!
Kallon Hanne tayi kafin tace"Ku tashi kuyi sallar isha"i gashi chan ana Kira..Ku fito muje falon Malam mu ci Abinci..!
Da Sauri Amina tace"Hajiya zamu ci namu anan..!
Saboda in akwai abunda ta Tsana wannan al"adar ta gidan mallam Akwai Wadanda bata son Haduwa Dasu acikin gidan nan.
Hajiya ta juyawa tana Ficewa Lokaci Daya tana Fadin"Ba ruwana ku da Babanku..!
Sai da Hajiya ta fice ne Hanne tace"Meyasa indai kikazo gidanan bakya son zuwa Falon Baba cin Abinci..?
Amina tace"Ba wani dalili..Kawai bana son ganin matar nan ne..!
Hanne tace"Wai Anty Amarya..?
Amina ta tabe baki kafin tace"Itafa Bata da Mutumci Ni tun Ranar da Fada ya hadani da Sa'adatu ta Shigar mata Har tana Fadin meyasa ta Hada kashi da irin Tsiya kamata..?na tsaneta Daga ita har ya"yanta kinsan ko a makaranta bana mgana Dasu..kuma ina jiran Watarana yarinya ta shigar min Harka na Sauke mata Hayakin kaina..!
Hanne ta mike tana Fadin"Amina baki da mantuwa..!
Amina tace"Bana manta wanda yayimin Alheri..Da wanda yayimin Sharri..Kina wani abu kamar kuma jin Dadin zama da ita kuke..Saboda Baba malan ne take Rage wasu abubuwan ammh da badomin haka ba Allah kadai yasan iskancin da zatayi..!
Hanne tace"Ni ina ruwana da ita..Iyaka in mun hadu na gaisheta ko Shashenta bana zuwa sai ta kama..Sa"adatu ma ta Dade batamin mgana kinsani Saboda ke..!
Amina tace"Share banza..Itace akasa mu muyin gaba badai ta Mutum ba sai Allah..!
Hanne na Dariya tace"Kinsan fa Diyar yayarta Ya Dan mallam ke aure ko..?
Amina ta yamutsa Fuska tace"Haka naji shiko Duk yanmatan Duniya sai ita .?
Hanne tace"Kowa haka yake fadi..in kinga ya"yan masu Sarauta da masu kudi da malamai yadda suka rika kawo ya"yansu wajen Baba ammh Duk yaki sai kawai Rana Tsaka yace Anty Sakina yake so..Kinsan tare tatashi wajenta dasu ya Jidda !
Amina tace"Eh mana na Tuna lokacin duk da bamu da wayau tafi kowa iskanci kamar gidan Ubanta..Nifa inaga Tun da akayi auran ban kara ganinta ba Duk zuwan da sukeyi har su tafi bama Haduwa har shi Ya D'anmalam din bazan iya Tuna kamaninsa ba gaskiya..!
Hanne tace"Kinsan bai cika yawan zuwa ba..?in yazo ma shi kadai kwana Biyu yake ya koma in kuma Zai zo da ita sai karshen shekara kuma suna Gidansu Dake nan Kano Road sai dai in sunzo gaida su Hajiya kuma Har gidanku yana shiga gaida Yaya Hajiya tace Dan Dakinta ne sosai..!
Amina ta mike itama tana Fadin"Ke ni ban taba ganinsa ba..Kina da Hotonsa .?
Hanne tayi Dariya tana Fadin"Sha Kurumimki naji Hajiya na Fadin nan da wata Daya suna na nan zuwa Saboda Mganar auran su ya Aisha..!
Amina ta kwalalo ido kafin tace"Kice muna da shan Biki..!
Hanne tace"Wlh kuma har dasu ya Sadiya ma za"a Hada fa...kilama Har dasu Ya Zeenatu..!
Amina tayi wata Dariya kafin tace"Allah yasa hardasu..su tafi su barmana Gidan dagani sai Hamida muci uban juna..!
Dariya suka saka Gabadaya Harta Tafawa suna cigaba da Hiransu Salla sukayi Tunda suna da alwala Sai da suka idar kana suka fita Falo ba kowa suna Falon Baba Malam Kichen din Hajiya Hanne ta shigo ta Dibo musu Doya da miyar Stew nan falo suka Fito suna ci suna Hira da Dariya Daga ganinsu kasan kaunar da suke ma juna Daga Allah ne.
Sai wajen 9:30am na Dare su Ya Aisha da Ya Abida suka shigo Ya Aisha Daki ta wuce ita bata cika mgana ba Ya Abida ce ta kallesu tana Fadin"Meyasa baku je Dinner ba..!
Amina ce tace"Mun yi namu mu kadai..!
Kai ta kada kafin tace"Sannu Shafaffu da mai..To Baba na kiranku..!
Amina Rada take ma Hanne tana Fadin"Mijin Ya Abida zai sha Gulma..!
Hanne na Matse Dariyanta Ya Abida ta Zaro ido tana Fadin"Amina me kike cemata akunne gulmata ko..?
Da Sauri Amina tace"Labarin wata yarinya mai Bala"in saka ido nake bata..yar ajinmu a islamiya..ko Hanne..?
Hanne ta Daga kai da Sauri Abida Wucewa tayi tana Fadin"Sai na Daki bakin yarinya yanzu nan..!
Amina ta Rakata da Daga Lefe tana Shigewa suka kyakyalce da Dariya
Saida suka gama Hanne ta kwashe komai takai Kitchen Amina tace"Dauko Hijabina na tafi gida Hanne..!
Hanne tace"Kiran baban fa..?
Tace"In mun fito sai na shige gida..!
Hanne tace"Nazata nan zaki kwana..!
Kafada Amina ta Daga kafin tace"Anki din..Ina fa Kirge nice na kwana Na karshe..Malama kece fa da kwana..!
Hanne tace"Dillah zan kwana nima gobe..!
Amina tace"Yauwa sai na baki ma Labarin wannan litaffin..!
Da Sauri Hanne ta Danne bakinta tana Nuna mata Dakin dasu Ya Abida suke Amina Tayi Dariya Kafin tace"Sai me..?Allah yasa ma suji..!
Hanne dai wucewa tayi ta barta Tasan wacece Amina bata da tsoro komai zai Faru sai da ya faru ita zata saka a uku.
Hijabinta ta Dauko mata itama ta Dauko nata tana Fadin"Muje na Rakaki..!
Fita sukayi Daga Dakin suna Tafe suna Hira Amina na Zagin malamar hausansu har tana kwaikwayon mganarta Dukkansu Jss3 suke sai dai Amina Ita da Sa"adatu suna A ne yayinda Hamida da Hanne ke ajin B.
Suna tafe har Shashen Baba Maallan Amina tasan inda suka zo yasa ta Bude baki Daga Kofar Falon ta kwarara Sallama.
Hajiya Dake Cikin Falon gefen Baba Mallam Dake zaune kan kujera yana Duba wani Littafi tace"Ga Mamar taka nan ta iso..Kaji Doguwar sallama kamar ta Kirki..!
Tafada Cikin Zolaya yana Duken yace"Ta kirkin ce mana Zainabu...Mamana Harda yarinta ajikinta da ta kara girma ta mallaki Hankalinta sai dai Labari..!
Kai kawai ta Kada tana Hangen abunda ba Haka ba kan Aminar ita ta amsa Sallamar ta Amina Hanne na Shirin Shiga ta riketa tana Fadin"mu shigo baba cikin harshen larabci
Shi kanshi sai da ya Murmusa ya Dago Fuskarsa Daya cika da Farin gemu Cikin Dattakonsa yace"Na"am...!
Baisan meyasa ba Ko Muryan yarinya yaji sai yaji wani Dadi yana mata kauna wanda ko cikin ya"yansa sai an Tona Amina haka Allah yayi ta mai Farinjini ne Malam yana sonta Saboda Allah da kwazonta Duk da take bata maida hankali Kokari gareta yana ganin makamceceniyar kwakwalwarta Data D'an malam awajensa da itace kadai yake Dogon Mgana da Larabci bata kakare ba Tana Jin Labarci Fiye da yadda kowa ke Tunani kuma Bayan Baba Malam ko Baba Sa"idu baisan wannan baiwar nata ba..
Sannan ko makaranta sun sani tana da Jawo Jidali ammh itace Over roll acikin ajinsu har mamaki ake yi masu Hassada da ita na Fadin Cuta akeyi Amina jidalinta baya barinta gane Karatu shiyasa Sa"adatu ke Kishi da ita matuka basa Shiri ko a islamiya da hadda Itace Zakka kamar yadda ta Fita Zakka acikin gida Daga waje ba,sannan Amina Zakka ce sai kowa Tunani yake sa"a take ci Saboda ba"a Taba ganin tabama karatu Muhimmanci ba nan kuwa basu sani ba Tana da baiwa sau Daya zata ga Abu Ta kuma karantshi ta gane shi kuma ya Zauna Bisa kanta Har Abada.








_Naji Dadin yadda kuka karbi Labarin nan kamar yadda kuka saba karban Duka Labaraina Naji dadi nagode matuka Allah ya bar zumunci nayi alkawarin bazan baku kunya ba_






*Janafty*

*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janaftyd'?*

*Sadaukarwa ga Halima yusuf gwarzo(Besty) Alherin Allah ya kai miki adukkan inda kike*

_Intelligent writer's asso_


*

Kai tsaye suka shiga Kayattacen Falon Dauke da wata sabuwar Sallama,Suna Shiga Kamshin Turaran da Duk wanda yasan Baba malam yasan wannan kamshinsa ne wani Turare ne mai kamshi mai Sanya natsuwa Turaren mai Tsada ne dan Kasar Saudi mai suna Arab Saboda yawan amfani da Turaran yasa Duk inda Malan ke yawan zama kamshin ya kama wajen,Kamar yadda Kamshin ya kama Falon Dayake ma mallakinsa.
Kayattacen Falo ne wanda yaji kayan More Rayuwa na alatu Falon babba ne mai Dauke da Royal Chair da Tattausan Cafet na kamfanin Italiayan.
Sannan Daga gefe chan wata Kofa ce data fita Haraban gidan akwai wani Falo shi na ganawa da bakin Baba Mallam ne,Sannan Daga cikin Falon akwai Kofifin Bedroom Guda Biyu sai Daga shashen Yammah akwai wani Cabet na glass mai girma da Fadi kafe ajikin Bango wanda yake Shake da Littafan addini Kala kala nau"i nau"i Dabam Dabam Sannan Daga gefensa wani katon Tebur ne mai Dauke shima Da Tarin Littafai ba masaka Tsinke,sai Kujera Guda Daya wajen zaman mallam ne in zai yi Nazarin wani Littafi kamar yadda ya saba koda yaushe.
Sai katon Talabijin mai kama da Kamar Mutum yana waje ne saboda Girmansa,Sunna Tv ne ke tashi Acikinta Dauke da Muryan Sheik Haruna Kabir Gombe yana kwararo Wa"azi Cikin Barkwancinsa.
Cikin Lokaci kadan Amina ta gama Nazarin Falon Kafin idanuwanta su sauka kan Mafi Daraja a wajenta,Wanda shi kadai ne bata iya kallonsa Kai Tsaye shi kadai take shakka Da bata iya Hada ido dashi shi kadai ne yasan Wasu abubuwa Game da ita Saboda yana janta ajiki Wanda ko Aba dinsu bai kaisa saninta ba.
Cikin Farimciki gabadaya Fararan Hakoranta suna Waje ne ita ce kan Gaba Hanne na binta abaya zuwa Inda Baba malam ke zaune Saman Daya Daga Cikin Kujerun Falon Hajiya Babba na gefensa Zaune..
Kamar yadda take Farimciki da ganinsa haka shima ya Dago kyakyawan Farar Fuskarsa mai Dauke da Farin gashi Daya Lullube gemunsa Dattijo ne mai Kima mai Daraja mai Dattako masanin Addinin Musulunci Dana Zamani SHEIK YUNUS ABDURRAHAMAN BAZANGA kenan Shehin Malami na bangaran Addinin Musulunci da na Sunna Gabadaya ba iya garin Gumel ba Kasa gabaki Daya susan da zamansa yana da kyakyawan alaqa wajen Sauran Malamai sannan kowa na girmamasa Malami ne mai Tsoron Allah da Sanin ya kamata ba Malamin Siyasa ba kuma ba mai ci da addini ba ba ga Jama"ar gari ba Hatta ga iyalan Dake Zagaye dasu sun san karamci da Dattakon Sheik Yunus bazanga.
A kama baya kama da duka ya"yansa Domin shi Fari ne sannan yana da Cikar Fuska da zati Duka ya"yansa sun fi kama da matansa Daya Dayane Cikin Jerin ya"yansa ke kama dashi Shuiyasa har acikin Ransa UMAR NA dabam ne..
Akallah a shekaru bazai gaza 78 aduniya ko ya D'ara ma sai dai yanayin Hutu da jin dadi sun boye shekarunsa yana Sanye da Jallabiya Mai ruwan Madara ya Cire Rawanin kansa,Farin gashin kansa da Rabi da kwata ya koma Fari sai kyali kyalin baki,Wanda Saboda Cire Rawaninsa kansa ya bayyana Fuskarsa Sanye da wani Sirrin Farin Gilashi mai karamai karfin gani Jaridar Rariya ce ta Ranar a Hannunta yana karantawa sanda su Amina sukayi Sallama.
Tun kafin ta karisa Tace Cikin Muryanta"Baba...!
Yana kokarin gyara zaman Gilashinsa yacce"Mamana..Sai yau nake ganinki..?
Yafada yana kallonta Cike da wata Kauna da Allah kadai yasan adadinta
Daidai kafafunsa ta zauna tana Fadin"Baba nazo shekaran jiya kana da baki Hajiya bata fada maka ba..?
Tafada tana kallon Hajiya datayi Saurin Cewa"Na fadamai fa Maamah..Mallam na Fadamaka zuwanta ko..?
Yana Dariya ya dafa kanta yana Fadin"Tafadamin Tsokanarki nake Yanzu Sa"idu ya tashi nake Bidarki sai Hajiya tacemin kina ma Cikin gidan nan nace shikenan Tunda Wajen hannatu kikazo ba wajena ba .!.
Yafada Cikin Mirmishinsa na koda yaushe,Amina ta rike baki Tana yar Dariya Hanne Dake gefenta ta Duka Tana gaida Baba mallam ya amsa yana kallonta kafin yace"Ke kika Rikemin Mamana ko Hannatu..?
Hanne kanta na kasa tace"Baba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login