Showing 249001 words to 252000 words out of 265571 words

Chapter 84 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28904

after har asibitin sun koma Dr.Ghali ya tabbatar musu da komai lafiya sai hankalinsu ya kwanta.
Bangaran Aba kuma komai Lafiya lau Anty Hadiza na kula dashi ta karbo Jawaad wajen Hajiya ya Dawo wajenta Abun yayi ma Aba Dadi tazo Ranar ta yinin ma Amina da Daddare Aba yazo ya Dauketa Dakyar ya shiga Gidan Amina yasa albarka Amina baki har Kunne saboda Murna Aba yazo Ruwa kadai ya sha ya saka albarka suka tafi Yakaka itama ta Bisu da saka albarka.
Bangaran mallam kuwa acikin Satin nan ya samu Lokaci Yaje Tsafe Idi ya Tukasa yayi ma yan"uwan Uwani Gaisuwan rasuwar Batula,Akwai mahaifiyarsu agidan da abokan zamanta Biyu bayan yayi musu gaisuwa nan ake fadamai Uwani na kwance ba Lafiya an je asibiti an yi Duk Gwaje gwaje an kasa gano abunda ke Damunta sai tace kirjinta da zuciyarta ke ciwo an ta neman Lambarsa afadamai ba'a samu ba..!
Sanda ya shiga inda Uwani take sai da ya kusa mata kuka tana kwance ta Zabge ta rame ta lalace Ba wannan kibar yau gata kwance ba kwalliya ba kayan kawa tana ganinsa ta fara kuka tana Fadin ya yafe mata.
Mallam ya jinjina kai yana kallonta kafin yace"Na yafe miki uwani..Saura ke da wanda ya Hallicceki..Sannan zan yi mgana da su Nazeem zasu zo su Dubaki..!
Daganan ya mike bayan ya ijiye mata Takardan daya rubuta mata Sakinta ya Fice ko bai Fadaa mata ba tasan ko na menene yasa ta Dinga kuka Tari ya Sarketa iyayanta yayi ma sallama da kudi 50k ya basu domin suna cikin yanayi don ma yaran maza na taimakawa.
Sai bayan fitarsa mahaifiyar uwani ta shiga Dakin ita ta karanta Sakin da mallam yayi ma Uwani Sai ta saka kuka tana fadin daman tasan za"a rina Domin zaman uwani bana Lafiya bane ba ya"yanta ba Dangin mijinta tasan wani abu ta aikata aranar Duka yan"uwan Uwani suka taru tana kuka tana Nadama ta basu labarin duk abunda ta aikata,Sun ji tsoron Duniya sannan sun yi Tir da ita har ta mahaifiyarta sai da tayi tir da ita tana kuka tana Fadin Batula ta rasu a Hanyar Shirka wannan wani irin tabewa ne sun fito daga babban gida ammh sun watsar da Tarbiyansu Tundaga ranar harta mahaifiyarta ta Daina bi ta kanta tana yashe Cikin Daki sai wanda yaga Allah yaga Annabi ne ma yake lekota yau ina ya"yan nata Datake yin komai Saboda su..?
Sun gujeta saboda mugun Halinta sannan ba mallam din ya Saketa ballatana ta hango cikar Burinta gata kwance ba Lafiya tana girban abunda ta Shuka kaiconta tayi kuka kamar ranta zai fita bamai lallashinta

Aranar da mallam ya Dawo Daga Tsafe ya Kira Anty Amarya Har Shashensa ya bata takardan Sakinta Ko da bata karanta tasan Dalili ta Fadi gabansa tana kukan ya yafe mata ya kalleta yace"Na yafe miki marliya..Yanzu Tsakaninki da Ubangijij ne..!
Daga haka ya shige ya barta nan tana kuka kukan nadama da rashin Madafa.
Bata zauna ba Kayanta ta Hada ta Rufe Shashen ta bama su Lami key din tace su kaima Hajiya ta Fice Daga Gidan tana kuka yau ina Burin nata..? Ta biye ma rudin zuciya ta karre a Tutar babu Tana kuka ta isa tasha ta samu Motar Dutse lokacin data isa Gidansu sai da tayi nadama.
Yan"uwanta basu karbeta ba haka suka gana mata tir da kaico har da uwar data Haifeta sai da ta juya mata baya ba yadda zasu yi su koreta ne ammh Kashi ya fita Daraja abinci sai dai yan aiki su bata tayi kuka tayi nadama Lokacin da bai da amfani ta Kira wayoyin su Sadiya ba wacce take Sauraranta.
Sakina kuma tana Gidan A"i ita ta Dauketa tana kula da ita bayan an sallamosu Daga asibiti Dayake nan kusa take aure Ranar da Anty Amarya Taje sai da ta raina kanta Har Marin ta sai da kanwarta A"i tayi abaya yadda suke jin mganarta Saboda auran Babban mutum kamar mallam..agaban idonta Sakina tana kuka tace itace ta cuceta ta rabata da auranta da kuma Halin Datake Ciki gashi sanadiyar barin cikin data dinga yi mahaifarta ta samu rauni Har ta fara Dagargajewa yanzu haka an cire mata mahaifa ita da Haihuwa har Abada ta Tsaneta bata son ganinta
Anty Amarya na kuka tana rokonsu gafara suka Tarkatota waje bayan A"i ta saka megadi ya sakar mata karnuka su suka kadata har waje nan bakin get din gidan ta durkushe tana wani irin kuka mai Cin rai kukan Nadama da nasani.

*******

EDD din Amina har ya tsallake da wajen Sati uku Bata haihu ba Sannan Cikinta ya fita wata na Tara har ya shiga goma sai kuma hankula suka fara tashi ita kanta Aminar ta kosa ta Haihu Cikin ya mata girma ya koma yana Rinjayanta.
Danmallam duk ya Damu ya koma yana matukar jin Tsausayinta Hajiya ta bada Shawaran su koma asibiti haka kuwa akayi da ita suka koma wajen Dr.ghali da Amina shi kanshi yanayin Daya ganta yasa yace zai sanya mata ruwan naguda ya gani.
Allah Sarki Duk mai imani sai ya Tsausayama Amina an saka mata Ruwan Naguda ta fara asa asa kamar abun zai yuyu sai kuma shiru sau Biyu ana saka mata sai nagudan ta Fara ta Tsaya anan asibitin ta kwana Tare da Hajiya da Yakaka Danmallam kuma duk hankalinsa a tashe yake washegari asibitin ta cika da su Anty Hadiza da su Aba har da ya Jafar da matansu..
Mallam ma yazo ganin yadda Amina ke kukan azaba tana fadin acire mata Ckkin jikinta zata mutu yasa yace bari ya koma gida ya yi mata addu"a a ruwan Zamzam ya kawo mata tasha tagani shi ya hana asake mata alluran nagudan ganin yadda take wahala kamar zata mutu kuka reras haka Danmallam ke yi saboda ganin Halin da Amina ke ciki hatta Sarood da tazo asibitin sai da ta tsausayama Amina da kuma kanta Tunda itama ai cikin gareta
Tafiyar mallam ba Dadewa sai gashi ya aiko Hajiya Nasara da ruwan zam zam din da yayi ma Amina addu"a shi kuma yana gida yana cigaba da taya Amina addu"an Allah ya sauketa Lafiya Hankula duk sun tashi.
Kamar an kara ma Amina azaba tana sha ruwan zam zam din nan abubuwa suka taso mata haikan tana kamkame jikin Hajiya hannayenta cikin na Danmallam tana kuka tana Fadin su yafe mata mutuwa zatayi Aba duk Dauriyansa bayan rasuwar yaya da abunda Balaraba tayi mishi wannan ne karo na uku Daya ji ya raunana Waje ya fita chan haraban asibitin yana kuka tare da Fatan Allah ya Sauke Amina lafiya..
Anty Hadiza ma har da kwallarta Kowa fa jiki yayi sanyi ganin Haka yasa Danmallam yace ma Dr.Ghali a yi ma Amina aiki a ciro mata abunda ke Cikinta.
Nan da nan kuwa aka fara shirin yima Amina C.S,Bayan Danmallam ya saka Hannu kudin aikin ma su jafar sukayi ta Zirgan Zirgan Biya Hajiya ta amince da hakan saboda Amina ta Wahala har mallam data kirasa ta Fadamai ya amince yace indai za"a samu mafita ayi din yafi Alheri.
Koda aka shiga da ita Dakin Tiyata Amina ta fita Daga Hayyacinta Danmallan ko addu"a ya kasa yi ya Fara Hango kansa Rayuwarsa ta lalace in ya rasa Amina sai da Yakaka ta yi bashi baki sannan ya iya fita hataban asibitin ko Sallar da yaso yayi ya kasa Cikin Mota ya koma ya Dafe kansa kawai yana kiran sunan Allah hatta Hajiya ta kasa mgana Saboda itama ta Shiga Dimuwa..!
Allah mai hikima ana shiga da Amina Dakin Tiyata Nagudan gaske tataso mata Sai dai su Hajiya suka ga Nurses suna kai da kawo da gudu suka zo suka karbi akwatin kayan Haihuwa suka shiga dashi Dr.ghali yayi matukar mamakin Lokacin Daya Duba Cm din Amina yaga Saura 2cm sannan kan yaro na kokarin fitowa Kananun shekarunta yake kallo yana Tunanin Haihuwa da kanta zai ja mata Tsinkau? Tsinkau ko yoyon Fitsari sai gashi Cikin Hikimarsa Amina ta fara kokarin Haihuwa da kanta Nishi kawai take yi da kakari da Taimakon Dr Ghali da Nurses dinsa Amina ta Sintalo manyan ya"yanta guda Biyu abun mamaki Kusan atare Jariran guda biyu suka Sulmiyo Daya na Fitowa Dayan ya Biyosa sai kuma Amina ta koma ta yi yaraf kamar bata da rai Dr.Ghali ya taimaka mata Uwar ta fito Nurses suka fara aikin gyara wajen Wasu kuma suna faman goge yaran bayan sun yanke musu Cibi Amina kuma Dr.Ghali ya samu natsuwa ganin tana Da rai allurai ya Hada yayi mata sannan ya fara kokarin gyara mata jikinta bai cika Tsayawa Irin haka ba da zarar mace ta Haihu ya gama mata abunda ya dace yake barin ma Nurse sauran ammh Amina ta Dabamce Matar Bazanga ce..!
Yaran duka maza ne sannan sun fito a wahale yasa basu yi kuka ba sai da Nurses din suka Daga su sama suka Daki bayansu sannan atare suka Callara kuka Gabadayansu sai suka washe Baki Dr.ghali na mirmishin jin Dadi yace"Alhamdulillah..!

Su Hajiya kuwa kamar amafarki sukaji kukan jarirai daga Dakin Tiyata sai suka fara Tunanin aikin ko yayi Sauri yanzu fa aka shiga da ita Hajiya tayi Hamdala acikin ranta suna nan dai Zaune suna jiran tssmmani.
Rabin Sa"a kafin Nurses guda Biyo su fito da Jarirai guda Biyu Cikin kayan Sanyi Farare masu kyau Hajiya ta kasa gasgaata abunda ta gani Amina ta Haifi yara Biyu duka maza..?
Allah mai iko Annabi mai Dubun Daraja.
Hajiya Nasara ta karbi ya"yan tana Hamdala daga ita sai su Nasir da Aba da Anty Hadiza da matan su ya Nasir Baki yaki Rufuwa Hajiya kuma Hannu ta Daga sama tace"Alhamdulilah..Godiyata tabbata ga Allah Shugaban Duniya..!
Sai hawaye tana sharewa sai ga Dr Ghali ya Fito Hajiya na ganinsa ta karisa tana Fadin"Sannu likita mungode fa..Ina Aminar ina fata Lafiya take..?
Dr Ghali yace"Lafiyanta kalau mama..Na mata alluran hutu ne sannan ga karin albishir ma Amina da kanta ta Haihu bamu riga ma mun yi aikin ba..!
Hajiya bakinta Har kunne take fadin"Alhamdulillah..Allah mun gode maka..Ashe yan Biyu ne acikin Amina bamu taba sani ba..?
Nidai nace cikin nan yayima Yarinyar nan girma ashe ashe..!
Dr Ghali yace"Hakan na faruwa Mama..ammh ni sanda suka zo na mata Scan na gani.Sai dai ban Fada musu bane ina Tunanin sun sani..!
Hajiya tace"To mudai bamu sani ba.kila dai Aishan ta sani Dayake chan wajenta ta zauna har cikin girma...!
Mungode Likita..!
Ya amsa mata kafin ya karisa su gaisa da Aba da ya Jafar sai.Nasir sannan ya koma Office dinsa ba Dadewa aka Gunguro Amina kamar gawa sai numfashi zuwa Dakin da zata Huta.
Hajiya Bakinta har kunne ta kira mallam tace mai tayi mazaje Shima Hamdalan yake yi Danmallam kusam shine na karshen sani Sai da Jafar ya Kirasa a waya ya Dawo Cikin asibitin.
Ya kasa yarda Amina ta Haifamai yan Biyu Duka maza bai karbi Yaran ba sai da ya yi sudujul shukur Yayi ma Allah Godiya sannan ya Dago ya karbesu hannun Aba yaran kamar yayi kaki Sai dai sun Dauko Fuskar Amina kadan da idanuwanta sannan Kuma Indentical ne bamai iya bambamcesu
Kadan ya gansu ya mikama Sarood su da Bakinta yaki Rufuwa Ya shiga Dakin da aka kai Amina ya ganta Hankalinsa ya kwanta ganin tana Numfashi haka ya Rumgumeta yana kwarara mata addu"a tasha albarka kamar me ya Tsausaya mata domin Hajiya ta fadamai da kanta ta Haihu bai Taba zaton Amina zata iya Haifan Daya da kanta bama biyu ba.sai gashi Allah yayi ikonsa..!
Danmallam Aliyu ne mutum na Farko Daya fara Kira ya fadamai karuwar Daya samu Aliyu ya tayasa murna Bakinsa har kunne yana Fara"Barkallahu Fika Ya shehi..Amina kwaila yanzu ta zama giwar mata..!
Umar yace"Kai fa banza ne meye kuma na Tuna baya..?
Aliyu nayi ta mai Dariya shima bakinsa har kunne yace"Hakane fa..To Allah ya raya Allah yayi musu albarka Sai mun zo barka..!
Da haka suka yanke kiran Kowa cikin Farinciki Aliya shi ya koma gida ya Fadama Aliya sai ta kara jin Imani ya Shigeta ta kuma kara yarda Duk abunda yaso Faruwarsa sai ya Faru..!
Sakina take tsausayi domin suna waya tasan Halin Data ke ciki har Cire mata Mahaifan da akayi yau wagari ya waya..?
Duk wanda ya bari Duniya ta Rudesa ya gama yawo haka zai zo ya kare a Duniyan ba riba Lahiran ma haka.
Kafin yammah Labarin Haihuwan Amina ta Zagaye Dangi kaf yan"uwanta ba wanda bai ji wannan Haihuwar ba ya Aisha ce duk ta Kira ta Fada musu Hanne da Hamida sai Tsallen murna suna Tunanin Waya ga Amina da ya'ya har Biyu..?
Ya Aisha har ya Sadiya ta kira ta Shaida mawa ita kuma ta kira Sa"adatu Fatan Allah ya raya sukayi Saboda Duniya ta koya musu hankali Sannan dukkansu sukace bazasu gayama Sakina ba kada Hankalinta ya tashi susan Halin Datake ciki..!
Har Jordan Labarin Haihuwan Amina yakai da Gusai suna ji da gayyar aka Dinga Fada a tsakar gida har Mamanmu daje wani karamim Daki tana jinya taji,Domin tana jin mgana sai dai bata iya mayarwa ne sannan kuma bata gani yanzu idon ya koma sai Lalube.
Taji Haihuwan Amina sai kukan zucci Lalle ta yarda Zakaran da Allah ya Nufa da chara..!
Sakina ma ta ji Domin Aliya ta kirata ta Fada mata Kuka take yi reras dataji Labari shikenan Burinta bazai taba Cika ba har Abada bazata ga k'wanta aduniya ba..Tayi kuka ranar kamar ranta zai fita ita kanta Anty A"i ta kasa lallashinta Domin tana tausayama Sakina? gashi har yanzu basu kara ji Daga Bakin Danmallam ba ballatana makomar auran nasu sannan Sakina tace bazata kirasa ba Domin bata san da wani ido xata kallesa ba Anty A"in ne ma ta kirashi da wayar sakinar bai Dauka ba..!
Haka Allah ke tsara lamarinsa Sau Tari wasu Burukan namu mattatu ne har mu koma ga Allah bazasu taba Cika ba..!
Amina haka ta farka ta ga Kyautar da Allah yayi mata tayi kuka ta share Hawayenta ta Rumgume ya"yanta wani son su na kara kamata Ya Danmallam Yahadasu duka ya Rumgume lokaci Daya yana Fadin"Allah ya albarki Rayuwarki Noor Dake da zuru"arki gabadaya..!
Amina na sharan Hawaye a kafadan Mijinta Uban ya"yanta UMAR YUNUS ABDULRAHAMAN BAZANGA murya shake ta Furta"Ameen Ameen Hubby..!







*Janafty*


*TFZB2030*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*

Sai da Amina ta kwana Hudu a asibiti sannan aka sallameta ta dawo gida,saboda tasha wahala sosai har ka ruwa sai da tayi akayi mata Dinki Yakaka ke kwana da ita a asibitin Hajiya sai tayi mata kara Sai dai tazo da Safe ita da Anty Hadiza Da rana kuma Hajiya nasara ke zuwa sai yamma suke tafiya tare da yan Dubiya matan su ya Jafaru har Dangin Yaya sun zo barka goggo Jumai ta koma Hadeja sai ya"yanta ne suka zo sukayi ma Amina barka da sauka.
Suna komawa gida aranar Yakaka ta saka aka nemo mata Murhun karfe da Itace domin tace jego mai kyau zatayi ma Amina bata son gantali wai wanka jego a gas ko a Kittle Hajiya kuma ta bata goyon baya aka hado mata da Tukunya gwarwa babba ta saka ruwan zafi ta saka aka nemo mata ganyayyakin wanka dasu ta Dafa ma Amina ta gasheta tas Amina ta zata zata yi kuka sai kuma batayi ba sai ma Dadin Ruwan dataji saboda jikinta sai Tauna suke kasusuwanta duk sun Sage Lalle ta kara jinjina ma uwa ba abun wasa bane Ta kara ganin Daraja da kimar yaya koda bata araye,Sannan tayi kuka,kukan yadda Rayuwarta tazo a wani yanayin da mahaifiyarta bata taba jin dadinta ba har ta koma ga Allah.
Hajiya ita ta wanke yaran nan tas Hajiya Nasara ta shiryasu Yakaka na ta musu tsiyan sun ga Sabbin mazaje sun Rude ana ta Dariya ita kuma Anty Hadiza tayi girki Sarood da su Anty Fadila nata Faman gyara gyaran gida kowa ka gani Bakinsa har kunne Sarood har Cikinta ya fara fitowa Amina duk yadda taso ta share Sarood da jin haushinta ta sakar mata ganin Tunda ta Haihu a asibiti take wuni yau ma suka dawo gida da ita sai kama ayyuka take tana da Saukin kai da Dadin mu"amala ba ruwanta.
Aliyu da matarsa sun zo duba Amina tun tana asibiti Amina ta ki sakar ma Aliya fuska duk ko yadda take ta wani Shige mata aran Amina tace ai kuma kin makara gwara ki koma inda kikafi auki ta dai karbeta sama sama ammh bata yarda ta saki jikinta da ita ba.
Yan"uwanta kaf ba wanda bai kirata a waya ya gaisheta ba tare da barka da arziki Har Ya Jadwa dake Jordan ita da Goggo Husai sun kirata sannan Hotunan yaran tuni duk yakai ko"ina ya Nasir da ya Jafar suka Dauka a wayoyinsu suna turama mutane mamaki dai ya kare tunda ga Amina da ya"ya har Biyu a lokaci Daya.
Su Hanne kuwa kullum sai sunyi mgana da Amina ji suke kamar su yi tsuntsuwa su gansu suna ta fatan Allah yasa mallam ya barsu su zo suna.
Tunda akayi Haihuwa Danmallam gidansa yake kwana shi da Sarood duk da nan take yini sai dare suke komawa chan gidan tayi ta mai Hiran yaran tana santinsu aransa yana Fatan itama Allah ya Sauketa Lafiya.
Washegarin ranar da suka Dawo Daga asibiti Dadaddare sai ga Mallam yazo shi da Danmallam da Aba aka kawo musu yaran suka kara ganinsu Mallan ya kalli Danmallam yana Fadin"Ka musu Huduba ne..?
Kai ya girgiza kafin yace"A"a mallam..Daman kai nake jira..kayi musu Huduba da sunan YUNUS DA SA"IDU..!
Mallam da Aba bakinsu yaki rufuwa saboda murna Hajiya na wajen Mallam ya kalleta yana Fadin"Hajiya kina ji dai Mazajen naku ma sunan mu sukace..To basu dai fimu ba. !
Dariya aka sanya cike da Farinciki nan take mallam yayi musu huduba da sunan da Babansu yace aka samusu sannan ya diga musu ruwan zamzam da Dabino abaki kafin ya Hadasu duka ya Dafa kawunansu yana musu addu"an kariya..
Hajiya tace"Ina Rokon Allah yasa ku biyo masu sunanyenku..Domin kun Dace da Nagartattun sunaye..!
Aka amsa mata da Ameen basu wani jima ba suka tafi Amina ita kanta Bakinta yaki Rufuwa da wannan karan da Danmallam yayi mata eh mana ai ita yayi ma kara A duk duniya mallam da Aba sune ita Daman abun na ranta sai gashi ya Rigata wani kaunar mijinta da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login