Showing 228001 words to 231000 words out of 265571 words

Chapter 77 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28875

gagije ta koma Cikin su Mamata ana ta Daga kaya da ita babu Abunda ya shafeta ko Kaffara bazatayi ba Karya ne balaraba tace batasan Amina nada Ciki ba..?
Ita Zata rufe abai bai..?
Daman ai Tun tuni ta daina Hada hanya da ita saboda taga ta riga ta gama Taimaka mata ta samu Duniya shine zataci Amanarta ta juya mata baya..?
Wlh yadda tayi alkwarin indai nata Burin bai cika ba to gayyar sai ta watse.
Tana cikin wannan Tunanin ne kawai Taji Ihun Sakina da Sauri ta juya sai taga Sakina a kasa tana gunjin kuka su Aliya na riketa da Sauri? Anty Amarya ta kariso da Sauri tana rike Sakina bata so tayi wani abun da Hankalin Mutane zai dawo kansu yasa Cikin Tsawa tace"Miye haka Sakina.?
Aliya da Sadiya ku kama min ita muje Bangarena .!
Tafada tana kokarin wucewa Sakina tayi kukan kura ta Fincike daga rikon su Sadiya ta dira gaban Anty Amarya Duk da yadda Cikinta ke murda mata Ammh ina idonta ne ya Rufe bata ganin kowa sai Hango Amina da Ciki da kuma Uban Dukiyan da Umar ya Laftama Amina.
Anty Amarya ta kauce ma Sakina tana Fadin"Miye haka..?muje bangarena Sakina..!
Tafada tana kama Hannunta ganin yadda Hankalin kowa ya koma kansu Sakina ta Fizge hannunta Tana kallon Anty Amarya da Jajayen idanuwanta Cikin karaji tace"Ba inda zamu. Anan zamu yita ta kare..!
Tafada Sai hawaye Anty Amarya tasan bata Cikin Hayyacinta yasa ta Fizge ta zasu bar Falon ammh sai Sakina ta Kwace hannunta ta Turke Anty Amarya tana Fadin"Kunya kike ji kada mutane su ji yadda kika Dade kina Rainamin wayau Anty..?
Tafada tana sakar mata manyan Idanuwanta, Anty Amarya ta Zaro Ido Tana Fadin"Sakina kina cikin Hayyacinki kuwa..?
Sakina ta Kwashe da wata Dariya kafin tace"Eh tabbas bana cikin Hayyacina..Daman ai na Haukace..kalli kazamar yarinyar nan da Ciki Haihuwa ko yau ko gobe..Ni kuma kalleni shekara ta nawa ina Wahala ban samu ba..!
Koda yaushe mganar ki kenan na kwantar da Hankali na ni kadai zan zana Mowa a wajen Umar da Danginsa..Hakan ne Mowa..?
Ki kalli abunda ke faruwa a Falon nan kowa ni yake ma kallon kaskasci wannan ne Mowar..?
Ko dai Bora na zama mara amfani..?
Ina alkawarin naki..?
Ashe duk karyace bazaki iya komai ba Daga ke har malaminki makaryata ne Babu abunda zaku iya tunda har Amina ta Samu Ciki da Umar baku sani ba..!
Ta karishe Fada Cikin gunjin kuka Lokaci Daya tana jijjiga kafadun Anty Amarya tana Cigaba da Fadin"Kin manta kin Fadamin auran Amina haka zai kare a banza..?
Kin manta kin Fadamin yadda aka Daurasa haka za"a kwance sa..?
Ashe duk karya ce..?
Ashe ni kika raina ma wayau Marliya..?
Ta karishe Fada Cikin Tsawa da Budewar Murya da ya Sandarar da kowa acikin Falon har da su Sadiya da Jidda da suka zaro ido sun kasa Fahimtar me ya faru Hajiya na gefe tana kallonsu tayi mirmishi takaici ta Harde Hannayenta saman kirji Tana kallon abunda ke faruwa.
sakina ta sulale kasa tana kuka Tana Fadin"kin cuceni kin sa na yarda da kowa sama Dake...Ashe karya kike Fadamin..Ashe bazaki iya ba..Bazaki iya ba..!
Tafada tana Saka fuskarta Cikin Tafukan Hannayenta tana wani irin kukan Bakinciki da kishi.
Anty Amarya tana kokarin Daidaita kanta kada su tona ma kansu asiri ta Duka Zata riko Sakina tana Fadin"Sakina Saurare n..!

"Kada ki kara Tabani malama..!

Sakina ta Katseta Cikin karaji da sai da Anty Amarya ta fadi kasa jidda da Sadiya suka karisa suka riketa Jidda Ta kalli Sakina Cikin bacin rai Tana Fadin"Sakina Lafiyan ki kuwa..?
Kada Zafin kishi ya saka ki rasa natsuwarki mana..!
Sakina ta Dago Jajayen idanuwanta Ta balla mata Harara kafin tayi mgana Anty Amarya tayi saurin kwace jikinta cikin nasu Jidda tana Fadin"Yau za"ayi walkiya kowa zai bayyana..Na rantse da Allah ni MADINA bazan karbi Faduwa ni kadai ba..Sai dai mu yi Faduwar Guzuma..!
Tafada Lokaci Daya tana neman Balaraba Dake falon sai kawai ta Tsince ta Sum sum zata fice tun da taga Abunda ke faruwa tsakanin Madina da Sakina ta fara kokarin Barin Falon Cikin Rawan jiki Anty Amarya na Hangenta ta Daka Tsalle ta Rikota tana Fadin"Ina zaki kuma..?
Munafuka..Ai sai ki Tsaya kiga yadda wasan zai kare ko DAYYABA..?
Tafada Cikin tsaananin Tashin Hankali Datake Ciki da Jajayen Idanuwanta.
Mamanmu ta fara kokarin kwace kanta Cikin Borin kunya tana Fadin"wata dayyaban kuma..?
Marliya kada Zafin kishin ganin Amina da Ciki yasa ki fara Hauka mana..
Ko kafin ta rufe Baki Anty Amarya ta Tsinketa da mari mai Lafiya sai da kowa afalon ya Zaro ido Cikin mamaki Mamanmu sai da ta Duke Anty Amarya ta Bita ta Chakumo Wuyan riganta cikin karaji take fadin"Zaki ga Hauka yanzu nan Don Kutumar Ubanki Dayyaba..!
Lokaci Daya ta Jawo ta Tsakiyar Falon kamar kayan wanki ya Zulfa ta tare Anty Amarya tana fadin"Meyasa kika mareta kuma kike janta haka..?
Anty Amarya ta balla mata Harara da Jajayen Idanuwanta tana Fadin"Matsa ki bani wuri..Ai ke Mamanmu kika sani Balaraba baki san Wacece DAYYABA..ba yau zaku san aihinin wacece Fuskar wannan azzaluman matar..!
Sai kowa ya saki Baki Amina na Zaune tayi Dariya jin Dadi sai Hawaye afili ta Furta"Komai yazo karshe..!
Hamida ta kalleta Cikin wani yanayi tana Fadin"Me..ya ke faruwa..?
Sai Amina ta kasa ce mata komai Tsausayi suke bata yau zasu yi kwanan bakinciki in suka gano wacece ainihin mamansu.
Anty Amarya ta yarfar da Mamanmu nan Tsakiyar Falon Hajiya Goggo Husai ta mike tana Fadin"Ke marliya meye haka kuke yi kamar wasu yara..?
Anty Amarya ta Cire Dankwalinta Taci Damara tana Zaran ido ta nuna mamanmu Dake kifta ido ta rasa mafita Tace"Wannan zaku tambaya Abunda ya faru..Domin tasan komai..Nima shi nake tambayanta yanzu..Dayyaba ni zaki munafunta..?
Ni zaki yaudara ki Ha"inceni..?
Wlh na yi Rantsuwan
ko kaffara bazan yi ba kinsan inda Amina take da Halin Datake Ciki gani kikayi Burinki ya Cika Kin KASHE YAYA..sannan kin Samu Sa"idu yadda kike Fata shine yasa kika juyamin baya..?
To wlh kin yi Kuskure Ni Madina Fitilar Sharri ce ko ba kalanzir sai na kai Safe yadda ta bare dani da Uban kowa sai ta bare yau..!
Tafada Cikin karaji da Ihu kamar wata Mahaukaciya Daidai Lokacin da su Mallam sukayi sallama suka shigo Falon bayan sa kaf Zaratan ya"yansa ne kama Daga ya Danmallam Nazir ,Nasir,Nazeem,Jafar Uzairu,Shamsu Akilu da zubairu, Da Aba Aliyu abokin ya danmallam atare suka bayyana acikin Falon sai kuma waje ya Dau shuru kallo ya koma wajensu mallam.
Hajiya na ganinsu ta murmusa kafin tace"Yauwa ku kariso..Yau abun dake Boye ne zai fito Fili..anyi walkiya za"a ga kowa sannan an Dade ana ruwa kasa na Shanyewa...!
Kai Tsaye ta maida kallonta kan Anty Amarya da ko ganin su mallam bata Damu ba Burinta kawai gayyar ta watse Cikin wata murya tace"Marliya naj kin Fadi wata mgana da sunan HADIZA..?
me kike so ki fada ne..?
Anty Amarya ta kalli Mamanmu wacce ta ke kallonta Cikin Zaro Ido Jikinta na rawa ta tuma gaban Madina ta rike kafarta tana fadin"Madina don girma Allah ki rufamin asiri..Wlh na Rantse da wanda raina ke hannunsa bansan komai kan cikin Amina ba..!
Anty Amarya ta saka kafa ta Ture Mamanmu ta fadi Gefe Cikin Taruwan Hawaye tace"Wlh baki isa ba Balaraba..Ai ke kwalba ce uwar Sharri..Qur"ani kadai zaki Fadamin na yarda Dake..!
Yadda Kasuwar ta bare dani ban ci Riba ba kema yau sai ta bare dake Dayyaba..!
Tafada Lokaci Daya ta maida kallonta kan su Hajiya tana fadin"Hajiya..Mallam Sa"idu ina ya"yan Yaya su Jadwa..?
Tafada tana Binsu da kallo Cikin son suji me take son Fada suka tsura mata ido Ta juya tana kallon Mamanmu dake kuka tana rokonta kada ta Fada ta juya mata baya ta kalli Idon Aba tace"Kunga wannan matar ba Matar kwarai bace..Shekarun data kwashe tana Zaune daku duk na Cutarwarce..Muguwa ce Azzaluma ni Duk Mugunta na ban taba Kisa ba..Ammh Kunga wannan..?
To Tayi kisan kai ta kashe rai Har Lahira..!

Aba Cikin rawan baki dana murya yace"Wa...ta Kashe..?
Kafin ta samu bakin mgana Daga bayansu sukaji wata murya Cikin Kuna tace

"YAYA TA KASHE ABA..!

Sai kallo ya koma inda akaji mganar sai ga Amina ta bayyana a Tsakiyar Falin gaban Anty Amarya da Mamanmu da ke tsuggune cikin Fitar hawaye Duka Biyu.
Gabadaya sai kowa yaji wani sanyin jiki Aba sai da ya Dafa ya Danmallam Dake gefensa saboda jirin Daya kwashesa Anty Amarya kuma Amina take kallo da Mamakin a ina tasan wannan mganar..?
Mamanmu kuma kasa kawai tayi Dakai yauma Tubular sara"i babu Tsima babu Dubara.
Ya jalela da su ya Jadwa suman Tsaye sukayi ya jafar ne ya iya takowa ya iso gaban Amina ganinta da Ciki ba shi ne agabansa ba mganar data Fada ne abun Damuwa..
Cikin Fitan Hayyaci ya kama jijjiga Kafadun Amina yana Fadin"Wata Yayar ne ta kashe..?
UMMANMU..?
Ya fada Cikin Tsawa Idanuwansa Jajir kawai sai Amina ta Fashe da kuka ta Fada Jikin ya jafar tana nuna Mamanmu Cikin wata murya tana Fadin"Itace ta kashe mana Uwa ya Jafar..Itace ta rabamu da Aba..Itace ta rabani da Uwata Shekaru goma da wani abu bansan Dadinta ba..
Itace ta maka asiri domin ka lalace sai abun ya Dawo kaina.
Itace ta hada kai da Anty Amarya ana Zaluntar ya Danmallam itace kuma suka ka Hada kai domin su ga bayan aurena da ya danmallan da alwashin har Abada bazan taba Haihuwa ba..
Ya jafar wlh wannan matar muguwace kuma azzaluma ce ta Dade tana Zaluntarmu bamu sani ba..itace ta kashe mana YaYA DA kunnena naji ta tana Fada..!
Ta karishe fada Numfashinta na Sarkewa,Ya Jafar ya riketa Cikin wani yanayi yanayin da baya fatan ya Bude ido yaga abunda ke faruwa da gaske ne.
Durkushewa Amina tayi kasa Jafar ya Bita ya Tallafeta,ya Danmallam ya kariso ya riketa yana Cire mata Hijabi Saboda ta samu iska tana ganinsa ta Damke hannunta Cikin rawan murya tana Fadin"itace..Ita ta kashe mana YAYA..!
Malam dake tsaye yace"innalillahi wa"inna ilaihirraju"un..!
Sai kowa afalon ya Dauka Saboda kowa ya rasa abun Fadi.
Mamanmu na wani irin gunjin kuka tace"Kaico na..Bansan akwai wannan ranar ba..Da ban aikata abunda na aikata ba..Don Allah ku yafemin..!
Gabadaya kallonta kawai ake yi Cikin Wani yanayi Aba kuma zaman dirshan yayi a kasan Cafet ya kasa mgana su ya Jadwa kuma suna dai Tsaye da karfin Imani.
Hajiya ce ta kalli mamanmu tana Fadin"Balaraba me Hadiza ta miki kika Kasheta kika raba ta da wannan Duniyar..?
Tafada cikin wani yanayin muryanta kamar zatayi kuka Ranar da
Danmallan yazo mata da wannan mganar bata gasgasta ba har yau tana cikin Tantaman balaraba zata iya Kasje Yaya sai yanzu da komai yake neman bayyana.
Mamanmu tana kuka kanta na kasa ta kasa Dago kanta saboda kunya balle ta kalli Ya"yanta da yayan yaya ga Aba ga kunya mutanen Dake falon Anty Amarya kuma na Tsaye ta shirya komai ayau Sakina ma duk suna gefe banda kuka babu abunda take yi.
Amina kuma Danmallam jikinsa ya Tarairayota ya azata yana ta faman mata fifita da Hijabinta Sakina na kallonsu tana jin kamar ta mutu saboda bakinciki.
Kan Mamanmu na kasa ta fara mgana.

"SOYAYYAR SA"IDU CE SILA..."









*Janafty*

*TFZB2026*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*


Gabadaya Ilahirin Falon sai da kallo ya koma kan mamanmu cikin mamakin kalamanta,ita kuma kanta ta kara saddawa kasa hawayenta na diga saman cafet din Daya malale falon Hajiya ta cigaba da fadin'"Tabbas kamar yadda na fada da farko Hakane soyayyar Sa"idu ce ta kaini ga komar Nadama dana ke ciki..!

Na taso tun ina karamata ban taba ganin wani Namiji daya taba Burgeni kamar Shi ba,Tun tasowata shi kadai ne Namiji kwara Daya daya ke Burgeni Sannan na kamu da sonsa da kananun shekaruna batare dana sani ba,Sa"idu ya shiga raina yayi kane kanen da bazan iya rayuwa ba sai da shi Tun Lokacin suna Gusai kafin barowarsu chan su dawo nan Gumel da Zama saboda Sa"idu yasa ban taba Daga kai na kalli Samarin Dake kara kaina akaina ba ina ganin kamar zai so ni watarana sannan kuma Hankalina da duka Tunani ya karkata akansa shi kadai.
Sai dai me..?sai da girma ya fara kamani Sa"annina suna aure sannan na Fahimci bana gaban Sa"idu bai taba min wani duba ba sai na yan"uwanta duk da kaunar da nike ta Nuna mai a Fakaici in yazo garin yazo Gidanmu Tunda ni ina matsayin Diyar abokin wasan Marigayi Baba Aminu ne,yazo kaida Babani Lokacin Tana Raye bana iya sukuni na Dinga Bare baren jiki kenan a kansa bani da wani Sauran sukuni ammh bai Taba Daga ido ya kalleni ba ballatana yasan Halin da na Dade aciki alokacin har Babani sai da ta Fahimci ina son Sa"idu so kuma bana wasa ba.
Hankalina bai tashi ba sai da naji Zencen auransa ranar sai da nayi karamin Hauka Babani Allah ya jikanta ta Dinga Tausata ta bani Hakuri akan nayi hakuri na Cire Sa"idu a raina na bama wani Cikin Manema na Dama tunda dai Sa"idu bai Juyo gareni ba na Hakura dashi alokacin kamar in make Babani haka naji Sai dai ban nuna mata ba ammh a wannan gabar gaba nake kullawa ga Duk wanda yace na Rabu da Sa'idu ko waye shi kuwa..!
Auran Sa"idu da Hadiza kadan ne ya Rage bai kaini kushe wata ba Saboda Bakinciki da Zafin kishi har sai da na Fara Tunanin na kamu da ciwon zuciya ammh duk da haka ban makara ba sannan ban cire rai ba.
Ana cikin wannan Halin Babani ta amsa kiran Allah ta rasu dani a bakinta da Fatan na yi aurre kada na jirasa ammh ban jita ba Tunda ni kadai ce tare da ita bayan bakwai dinta sai kawu Salisu ya maidani babban gidanmu ina zaune a wajensa..!
Saboda Sa"idu da Soyayyarsa sai da Kaf sa"o"i na suka tafi gidan mazajensu har kannen baya na ma an fara aurar dasu a wanchan Lokacin ana auran wuri ammh ni nafi Shekara ashirin ko Tsayayyen mgana bata akaina Saboda bayan Sa"idu har Abada bana jin zan iya bama wani Namiji Dama.
Kwatsam Naji Labarin Haihuwar yaya da yadda Sa"idu ya dinga rawan jiki akanta da abunda ta Haifa sai Gyambo na ya Dawo sabo naji bazan iya Hakura ba,Da taimakon wata kawata Samira da mukayi Primary tare na Zayyane mata Damuwata tace ta kwana gidan Sauki ita ta Daukeni ta Fara kaini gidan wani malami ko Boka zan ce wanda ke mata aiki akan mijinta acikin garin Tsafe na ZAyyanemai Halin da nike Ciki ya Tambayeni me nake so nace Sa"idu nake so..Ya aureni ko ta Halin kaka ne yana so ko baya so ni ban Damu ba kawai Burina na ganni agidansa a matsayin matarsa..!
Yace an gama ammh zan zube kudi masu yawa na karin aiki ban Damu ba Daman ta Fadamin na Tanadi kudi alokacin wajen Biyan Bukatata komai zan iyayi Zoben Zinaren da na gada wajen Babani na Saida na yi amfani da kudin wajen jawo cikar Burina.
Kamar wasa sai ga karamar mgana ta Zama babba kawu Salisu ya Kira Sa'idu akan yazo yayi auran zumunci Dani alokacin ko gaddama bai yi ba ya Karbi mganar Daganan na Fahimci zama ba nawa bane samira ta Budemin ido da shiga malamai Domin Cimma Burina ban shiga Gidan Sa"idu ba sai da na saka aka kafani sannan aka Saka soyayyata da kaunata a zuciyar kowa banda ta Sa"idu domin bai kaunace ni Fiye da yadda nayi nazo ba,yafi kaunar yaya da Jafar d'anta data Haifa.
Wannan shine Bakinciki na Biyu dana taba Fuskata agidan Sa"idu bayan aurena dashi,Da Farko ina ganin Komai ya kare tunda na auresa ammh Daga baya sai na Fahimci zama bai ganni ba Duk da kuwa Daga Su mallan har ya"yansu suna so na da Girmamani Uwa uba kuma Yaya itama ta Sakarmin komai kamar yadda na nuna Dayan fuskata ta Salihai.
Na Dade ina Fama da kuncin zuciya da Bakimciki kauna da wannan Tsausayin da bana ganinsa akan kowa sai akan yaya ni kuma sai dai Zaman Tsausayi da yan"uwanta ka ban taba ganin wannan kaunar da nake son gani atare dashi ba Sannan sai na Fahimci Duk wani Buri na Sa"idu yana kan Jafar ne bashi da sukuni in yana gida yana Tare dashi ko da Ranar ni ke da girki sannan duk kokarinsa na yaboye wannan kaunar bata Boyu awajena ba Dalilin Dayasa Idona ya Rufe da Kishi kenan da Bakincikin yaya da ya shiga raina na har Abada.
Hankalina ya kwanta dana Samu Cikina na Farko ina Tunanin Namiji zan Haifa nima Sa"idu yayi rawan jiki akaina da abunda na Haifa sai dai kuma ina hakan bata Faru ba haihuwar ZULFA sai ya koremin wannan Burin nawa sannan kuma sai na Fahimci kamar Sa"idu bai yi murna da wannan Haihuwar ba Duk da yadda ya dinga min Hidima yaya da Hajiya na Tsaye kaina ban taba Gani ba Saboda gani nake yi Itace ta Hanani Samun abunda nake so tun Farko Sannan tasha gabana a zuciyar Sa"idu.
Na yi ta neman Samira domim mu koma wajen mallan sai na samu Labarin mijinta ya tafi da ita Lagos inda yake Neman kudinsa sai hakan ya katsemin hanzarina ban koma wajen maallam da wuri ba har Tafiya ta Cigaba da tafiya alokacin Yaya ta Haifi Jadwa da Jaleela ni kuma ina Goyon zahra kaf alokacin ni nake rainan duka ya"yan da yaya ta Haifa Saboda na kara jawo Hankalin kowa da Tunanin kirkina akansu kuma naci Nasara na zama ban damu da komai ba a Bayanne a boye kuma ba wanda ya kaini Bakinciki.
Hankalina bai kara tashi ba sai da naga na kara Haihuwar Zulaihat ban samu Namiji ba sannan ga Jafar ya girma sai nake ganin yaya ita ke da gida ni kuma ta barni bani da Tsuntsu ballatana ta tarko sai nayi Shirin komawa wajen mallam sai dai nayi Rashin Sa"a an ce ya tashi Daga nan kuma ba wanda yasan inda ya koma Hankalina ya tashi Saboda alokacin na kasa Hakuri so nake ko ta Halin yaya ne na sami mafita na gaji da Kunsan Bakim cikin Sa"idu da yaya.
Hakanan na Dawo gida tunda bansan wani Malamim ba sai dai kafin na Samu mafita zuciyata ta riga ta gama kekyashewa Tsanar yaya da ya"yanta ya gama Cikamin zuciya wannan Bakincikin Tun aurena da Sa"idu yake Cikin Raina bai Taba gushewa ba Sai Ranar da YAYA ta bar gidan Duniya..!
Mamannu ta karishe Fada tana gunjin kuka Mallam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login