Showing 240001 words to 243000 words out of 265571 words

Chapter 81 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28910

nemi Amina da farko Allah bai yi ba..!
Tafada tana kallon Danmallan din Daya Hade ransa kanar bai taba Dariya ba,Aminu kallo daya yayi mai ya Maida kansa kasa azuciyarsa yana jin wani Nauyi Har yau har gobe bai Daina son Amina ba ya sota da dukkan Zuciyarsa ne sai dai ganin Danmallam a matsayin wanda ta aura sai ya Sare domin ai ta samu babban Goro ne.
Sannan duk da bai taba ganinsa ba yasha jin Labarinsa wajen Amina ashe shine mallan ya aura mata..?
Hakane mganar Nanne Rabo ne..Sannan bawa bai isa ya kankare abunda Allah ya Tsara ba,Sannan matar Mutum ya tabbatar mishi da itace Kabarinsa.
Har su Danmallan suka kariso gaban Nenne bai iya Dago kansa ba yana jin Nura na mai mganar ga Mijin Amina wanda ya kasa sa nan bai ko Kara marmarin kallonsa ba.
Ita kuwa kallon Danmallam take Cikin Fara"arta kafin tace"Masha Allah..Sannun kaji Allah yayi albarka..Ashe Amina kuma rabonka ce..?
Aminu ya so Amina son da bai taba yima wata Diya mace ba..kaganshi nan Saboda rashin Amina Dakyar muka samo Aminu da Addu"o"i da Nasihu yakusa shekara yana jinyar Zuciyarsa Dakyar da sidin goshi muka samu ya Farfardo nasha Fadamai yayi Hakuri yayi takwalli Akwai tanadin da Allah yayi masa agaba haka kuwa akayi kwatsam sai ga Mallam ya Dira a yola wajen Alhaji Babba da mganar Ya bama Aminu auran Hannatu yarsa..Shima bai yi gaddama ba, ya amsa domin na Fadamai daman itace maatarsa Amina kawai Sanadi zata zame sa..Gashi kuma komai ya Faru yadda Allah ya Tsara..muna namu ne Allah na nashi..Allah ya baku zaman Lafiya dukkan ku..Ita kuma Amina Allah ya sauketa Lafiya yasa abokiyar arzikinkace..!
Gabadaya suka amsa mata da Ameen har da Aminu da su Nura sai ya Danmallan yaji Nenne ta Burgesa kansa na kasa ya amsa mata lokaci Daya yana fadin"Mungode Mama...Allah ya kara girma..!
Ta amsa da Ameen ita da Rahina Amina dai kanta na kasa tana Satar kallon Aminu sai taji ya bata Tsausayi Ashe har jinya yayi tayi bayan rabuwarsu..?
Ai ita kanta Shaida ne Aminu ya sota sai dai bata Taba Zaton abun har yakai haka ba nan da nan sai Idanuwanta suka kawo kwallah.
Jin yadda Nenne ke Fadama Hajiya wuyar da suka sha kafin Aminu ya manta da komai anan ne taji har ya bar Kano da waka gabadaya ya koma Yola yana cigaba da kasuwancinsa shekara daya da wani abu kenan an samu ya Dawo Cikin Hayyacinsa..!
Hajiya ta jinjina kai ita kanta Lamarin ya Dauremata kai da Farko da Mallam ya Sameta da mganar zai nemi iyayen Aminu kan mganar Hannatu shi fa har yanzu sai yake ganin kamar bai kyauta ma yaron nan ba sannan da gaske yake yi tun a wanchan Lokacin da yace zai bashi Hanne.
Hajiya bata iya yin gaddama da Shawaran mallam ba Sai dai tayi Fatan Inda Alheri Allah ya Tabbatar in babu kuma Allah ya watsar da al"amarin sannan Tunda taga mallam ya Dage sai ta bishi da Fatan Alheri tasan yana da Dalili Tunda bai taba Tallata ya"yansa ba wannan din ma Domin da Dalili ne.
Daman yana da Lambar Alhaji Babba tun wanchan zuwan da sukayi ya karbi Lambarsa basu taba mgana ba sai da Mallam din ya yanke shawaran zuwa chan yola suyi mgana sannan ya Kirasa suka Tattauna a kuma Satin Mallam yaje Yola shi da idi suka gana da Alhaji Babba ya kuma karbi mganar hannun bibbiyu sannan ya labartamai yadda suka sha Fama da Aminu mallam yaji Tsausayinsa sosai alokacin aka kira Aminu yazo jin Bukatar yasa bai yi gaddama ba. Ya Dauki hakan a matsayin nasa kaddaran kenan Mallam ya ga karamcin rikesa sukayi sai washegari suka juyo shi da Idi..
Sannan sun biyosa Daga baya akayi neman aure aka biya Sadaki da Lokaci bayan nan ne Aminu yazo suka gana da Hannatu kowannensu yayi mamakin ganin Dan"uwansa barin ma Hanne da tayi ta kuka tana tunanin me zata ce Amina..?
Shi kuma Aminu Kwatan kwacin Soyayyar da Amina keyi ma su Hannatu da wanda ke tsakaninsu yasa ya amince da auran Hanne Dari Bisa Dari.
Nenne bakinta har kunne take ta Godiya tana Fadin"Munga karamci Munga Kauna da kara..Allah yayi ma wannan zuru"ar albarka..!
Hajiya na amsa da Ameen aranta taji Dadi tasan Hanne bata fada hannun banza ba Nenne da zuru"arta masu karamci ne
Amina na chan tayi nisa cikin Tunani ashe har su ya Danmallam da su Aminun sun yi ma su Hajiya sallama sun Fice Daga Falon tana chan cikin Tunani bata ma sani ba sai da suka Fice ta waiga taga basu afalon sannan ta iya Sauke Nunfashi mai karfi Sulalewa tayi daga wajen Nenne ta koma kusa da Yakaka ta zauna suna Hira sama sama rabin Hankalinta na kan Dangin Hajiya yan maiduguri Dake ta shiga suna fita sannan suna kuma Rangada guda sai da Hajiya ta Tsawar tar musu sannan suka Daina ita Amina bata kawo komai aranta ba ta Dauka dai suna yi ne saboda Bikin su Hannatu.
Su Hanne take jira taji Dalilinsu na Boye mata Aminu ta aura Shuru Shuru basu kariso ba wayarta ta Dauka ta Dokama ya Aisha kira ta Dauka kafin Amina ta fara Mita tace mata suna kofar gida gasu nan shigowa..
Minti Biyar Tsakani sai gasu sun shigo Duka da Amaran har Sa"adatu da zugan su ya Jadwa Allah Sarki su ya Zulaihat suna baya baya duk sun yi wani zuru har su ya Jidda ma sun dan fi su Sakin jiki sai suka bama Amina Tsausayi sai da ta Share kwallah Bedroom din Hajiya aka shiga Dasu Amina bata bisu ba,ganin mutane nata shiga sannan su Nenne ma sun Shiga suga Amaryansu sannan taji Dadin zamanta bata so kuma tatashi.
Sai da ya Abida tazo ta mata mgana Sannan ta iya jijjibiwa ta mike tana mata Dariyan Amina ta zama uwar mata Baki ta tura batayi mgana ba..
Daga Dakin Hajiya Dakin su Hanne aka Maido su daganan sai Falon mallam Abun ya Sauya wannan karon Duba da abunda ya faru jiya.
Amina na shiga ta iske Hanne da Hamida sun hada kai suna kuka Sa"adatu kuma na gefe ita da ya Sadiya suma duk sunyi Laushi..
Cogewa tayi kofar Dakin da katon Cikinta tana Fadin"Meye kuma haka..!
Kun wani Hade kai kuna kukan munafunci..?
Sai alokacin suka Dago Hanne na kuka ta mike ta rumgume Amina,Amina sai ta riketa bata so tayi kuka tana Fadin"Ni sake ni ai fushi nake dake..!
Hanne ta Dago Cikin kuka tana Fadin"Me nayi..?
Amina tace"Yanzu Ashe Aminu ne kika aura shine jiya cikin ke da Hamida ba wanda ya Fadamin..?
Ai kun kyauta..!
Tafada tana kara shan kunu Hanne ta kara sakin kuka kafin ta juyama Amina Baya tana Fadin"Na kasa Fada miki ne Saboda bansan da wani ido zan kalle ki ba Amina..!
Amina ta juyo da ita tana Fadin"Ki jimin gulma irin na Hanne Hamida..Da wani ido kika Saba kallona don kaniyarki..?
Ta fada tana Maida abun wasa Hamida na sharan kwallah Tataso tana Fadin"Tunda yazo ta ganshi Hanne ke Cikin Damuwa..!
Amina ta kallesu shekeke kafin tace"To Saboda mene..?
Hamida ta kalli Hanne kafin tace"Saboda Tana jin kunyarki..Zata auri Saurayinki..!
Amina tayi wata Dariya kafin tace"Ammah wlh Hanne kin bani mamaki yau ko ban yi aure ba ni mai bar miki abunda nake so ne..?
Ai kin wuce haka a wurina na Daukeki kamar uwa Daya uba Daya ko Mijina ne ya nuna yana sonki ni mai basa goyon bayan ya aureki ne ballatana Wani Saurayi chan da muka yi soyayyah ina cikin yarinta..Wlh Hanne ki saki jikin ki ki daina Damuwa Dani Dubeni ni ban nemi komai na rasa ba ya Danmallan ne Duniyata yanzu komai baya gabana .!
Suka Saki baki suna kallonta Amina ta Shafa Cikinta tana Fadin"Baku ga alama ba ma..!
Ta karishe fada tana kashe musu ido Sai gashi sun kwashe da Dariya har da Tafawa ya Sadiya da Sa"adatu sai suka Tsargu tunda basa jin me suke fadi sai suka ga kamar sunayi dasu ne.
Hanne tace"Amina dai bazaki taba Sauyawa ba. !
Amina tace"Dillah nayi hankali fa..Nan da wani Lokaci ni Uwa ce..Kun ga kuwa Dole na rage wasu abubuwan..!
Suka Hada Baki wajen fadin"Ba shakka Mami Amina..!
Dariya suka saka gabadayansu Kafin Amina ta rumgomsu dukkansu tana Fadin"ku daina kuka..Insha Allahu Alheri zaku tarar a gidajenku..Hanne ina miki albishir da kin Dace Aminu mai Kirki ne zai kula Dake..Sannan kin samu Suruka mai kirki irin Nenne..Kema Hamida duk da bansani ba..Nasan kema kin Dace saboda Baba mallam bai taba ma ya"yansa Zabin da bai kamata ba..!
Gabadaya sun yarda da mganarta sai gashi Amina ita ke faman lallashinsu Sa"adatu da ya Sadiya basu mata mgana ba itama tayi kamar bata gansu ba Gabadaya Haushi suke bata sannan Daman basa wani shiru da Sa"adatun sai kallonta suke yi ita ko har da gayya take turo Cikinta Tana Tafiya irin ma masu Ciki aranta tace Dan Bakinciki sai dai ya mutu..
Su ya Abida ne duk suka shigo Dakin da su ya Jadwa da sauransu Su ya Zulfa sai da ya Aisha ta jawo su suka shigo nan suka hada kai da Hamida suna ta kuka an basu hakuru sun ki Dainawa Amina na gefe ita bata ma kuka ganitake yi a kyalesu su koka Domin Abun kukan ne yazo.
Suna cikin Hakane ya Aisha ta Fallasa Labarin Auran Aba da Hadiza Amina mamaki ya kamata baki Bude wato shiyasa Dazu ake ta nuna ta tasan Anty Hadiza kuwa Diyar Goggo Yagana ne lokacin auran su ya Aisha ita tayi musu ma gyaran jiki sannan Da ita akazo wannan Bikin Dazu ta ganta tana Sanye da Hijabi sai Faman Dukar dakai take yi Ashe shine Dalili

Kawai sai taji Hawaye ya kawo mata Alherin Mallam bazai fadu ba sai dai sumai Fatan ya gama da Duniya Lafiya.
Nan fa su Ya Jadwa suka Rangada guda ya Jawahir cikin Hawaye tace"Yaya tatafi..Ga Wata YAYAr ta dawo..!
Kai Allah ya saka ma Baba Mallam da Alheri gwara Balaraba ta san ba mai yi sai Allah sannan da ranta zata ga Aba da wata mace sai dai Bakinciki ya kasheta muguwar mata..!.
Sai kuka ya Jamila ne ma ke nuna mata su ya Zulfa da sukayi wiki wiki ga bakinciki ga kunya ammh bakinta ita da ya Jadwa bai yi shuru ba sai Dakin ya koma na koke koke Su Hamida nayi su ya Jadwa nayi sai da Hajiya Nasara ta shigo ta tsawa tar sannan kowa yayi Shuru.
Daganan Shashen mallam aka kai su Hanne yayi musu nasiha shi da Aba da Sauran yayyi irin su Ya Danmallam Amina dai ta gaji da Zirga Zirga tana Bangaran Hajiya sai alokacin Taga Sarood duk yadda taso ta karbi Fara"an Datake mata kasawa tayi Domin wani Kishi ne ya taso mata afakaice Hararanta tayi ta Dauke kanta ita kuwa Sarood daman Yar Fara,"a ce koda yaushe Fuskarta a Sake ne.
Ita abunda ma ya bata mamaki yadda Aliya matar Aliyu ke ta faman mata Sannu in ta ganta alhalin a baya ko mganar arziki bata taba Hadasu ba Amina bata amsa mata ita bata son munafunci wato taga ta bare ma Kawarta Sakina shine zata zo ta mata Bariki aiko gidan ta taras itama sai ta basar da ita kamar ma bata ganta ba.
Bayan an fito dasu Daga shashen mallan har yan gusai maza da basu koma ba sun yi nasu nasihan yan bazanga dai sun koma har ta da kawun Hajiya sun Dauki Hanyar Bauchi tunda sun yi mai wahalar an Daura auran Sa"idu da Hadiza kamar yadda mallam ya nema..!
An riga an gama saka kayan gara da Sauran kayan da baza"a rasa ba a motcin da za"a tafi da Amaren su kawai ake jira Hajiya ta ga Hamida da Sa"adatu bai kamata su tafi basu yi sallama da iyayensu mata ba
Yasa ta Damka Sa"adatun Hannun Sadiya tace ta kaita wajen marliya suyi sallama itama Hamida ta Damkata Hannun Zulfa tace suyi Sauri kada Mallam ya sani. Kowa mamakin Kirkin Hajiya da zuciyarta ake yi ganin ko a Fuskata bata nuna Wata alama ba.
Haka kuwa akayi Sadiya takai Sa"adatu shashen Anty Amarya da ko kaunar barayin yanzu basa yi tana Ciki kwance daga kuka sai kuka cikin kwana Daya ta fara sauya kamanni Tana ganinsu ta mike jikinta na rawa Zata rumgume su suka matsa baya.
Ya Sadiya ta kalleta Cikin wani yanayi kafin tace'Ba wata mgana ya kawomu ba. sa"adatu zata tafi gidan mijinta..gatan nan in kinga dama ki bata Shawaran daya dace in kuma kin ga Dama ki Dorata kan hanyar da kike kai ayau..!
Da haka ta Saki Hannun Sa"adatu ta Juya tana Sharan kwallah ta Fice Daga Shashen gabadaya Anty Amarya taji gwiwanta yayi sanyi ta Duke gaban Sa"adatu tana Fadin"Sa"adatu don Allah kada ki gujemin kamar yadda Sauran yan"uwanki suka gujeni..!
Sa"adatu ta girgiza kai sai Hawaye Cikin kuka tace"Abunda kika aikata abun kunya ne da abun Tir..Ina Fatan kada Rayuwarki ta Shafi namu Rayuwar..Ko Sau daya baki Tuna kina Damu ba..?
Sai yanzu ne da Kika Fara Girban abunda kika Shuka zaki ce kada na gujeki..?
Nagodema Allah da zan yi nisa da Rayuwarki gabadaya sannan kuma Insha Allahu zan zauna da mijina da Danginsa Lafiya zan masa Biyayya har karshen Nunfashina..!
Daga haka ta juya tana kuka Anty Amarya ta Tashi Tana kiran sunanta bata juyo ba tana shirin Barin Falon tace"Wani Hali Sakina take ciki..?
Cikin Dakushewar Murya Sa"adatu ta Tsaya Cak kamar bazatayi mgana ba Sannan tace"Saboda abunda kika aikata ta kara rasa Cikin jikinta..Sannan su Anty A"i sun Dauketa ita da sauran yayinta sun maidata asibitin Dutse Dazu da Safe..!
Da haka ta fice ta bar Anty Amarya da Gunjin kuka Duniya ta juya mata baya alokacin da batayi zato ba ballatana Tsammani ba..!
Abangaran mamanmu kuwa Ita take ganin Abunda ta aikata Domin ko yan"uwanta sun ce badai zuru"arsu ba Ta nemi wani Ahalin sukan sun yafe ta,Tayi kuka kamar ranta zai fita Tana gani suna Hada kaya sun ce ana wucewa da Amare zasu kama Hanya Tazama kamar wata mujiya acikin mutane ya"yanta kaf sun juya mata baya bama ta su Jafar wadanan tasan Da wuya su iya yafe mata.
Ita kadai agidan dukkansu suna gidan Hajiya tana cikin Dakinta tana gunjin kuka,Sai ga su Hamida har aranta taji Dadi ta mike da Sauri zata rumgumesu Hamida ta tureta sai da ta Fadi Cikin Bakinciki ta nuna ta da yatsa tana Fadin"kul kar ma ki fara..Na Fada miki ban sanki ba baki sanni ba..!
Zulfa ta kasa mgana sai kuka Daga karshe ma sai ta fice Daga Dakin Mamanmu na kwance in da ta Fadi tana wani irin kuka take fadin"Hamida ni fa mahaifiyarku ce..?
Ko Duniya zasu juyamin baya na Dauka kuna tare dani..?
Hamida tayi wani Dariya kafin tace"Wlh nayi Nadaman dana fito Daga Cikin ki..Nayi nadamar kiran ki da sunan uwata da nayi..Yadda kika Cutar damu kika bar mana Bakin Fenti kema Bazaki taba Gamawa da Duniya Lafiya ba..!
Sannan ga wani karin albishir Aba Yayu din nan tare da auran mu mallam ya Kara Daura masa aure..Da Diyar kanwar Hajiya kin ga kenan tundaga nan kin fara ganin karshenki..!
Mamanmu ta Zaro Ido gabanta ya Fadi cikin rawar baki tace"Au...Reee..?
Hamida ta gyada mata kai Ta cigaba da Fadin"Kuma na tabbatar da cewa ke ba matar Aba bace yanzu..Gwara tun wuri ki neni inda zaki..Ni dai zan tafi gidan mijina ina Fatan kada Laifin ki ya Shafi rayuwarmu kije Duniya ce..Da Sannu zaki girbi abunda kika Shuka..!
Ta juya tana sharan kwallah zata Fice Mamanmu ta riko kafafunta tana Kuka tana Fadin"Hamida kada ki tafi ki barni ina zan je..?
Kuma ai Sa"idu bai ce ya sakeni ba ko..?
Hamida na kuka da kuma Dariyan Bakinciki tace"lalle Balaraba kin raina ma kanki wayau ba kuma ki da kunya. ! Duk abunda kika aikata kina Tunanin kina da wani Sauran kima ne..?
Kima kara gaba tun kafin kifara wulakanta..!
Daganan ta Fizge kafarta ta fice tana kuka,a haraban gidan ta hadu da Zulfa suka rumgume suna kuka jin su shuru yasa Ya zulaihat ta Biyo bayansu ganin suna kuka itama sai ta Fara kai mamanmu ta lalata rayuwar ya"yanta.
Hakanan suka fito suna kuka Daman duk an fito ana kofar gidan baba mallan ganin Tafiyar Amaran duk yadda Amina taso kada ta fito sai da ya Abida taje ta Taho da ita domin Hanne da Hamida sun ki shiga mota sai kuka suke yi Ganin Amina yasa suka kara rudewa Amina taso ta Daure ammh ta kasa itama sai kuka Aminu kansa kawai ya kauda har da su Nenne a yan Lallashi,
Hajiya bata wajen tana cikin gidan su goggo Yagana da su Hajiya Nasara sai yan gusai dake wurin ya Danmallam ma na falon mallam ya Shamsu yaje ya Kirasa yazo ganin yadda suke kuka shima sai da ya tabasa ba kunya ya Riko Amina ajikinsa ya Rumgumeta yana lallashinta ita kuma jinsa ajikinta yasa ta kamkamesa tana kuka Da haka aka samu suka shiga Mota Sa"adatu tuni har sun mika Hajiya da kanta ta sakata a Mota Allah Sarki Hajiya mai rama Sharri da Alheri
Su ya Abida suna ta gulmar ya Danmallan ganin ya nufi Cikin gida rumgume da Amina suna Fadin abaya ya Dammallan ko mgana da matarsa bai iya yi gaban mutane sai gashi yau har da su rumgumewa gaban mutane..!
Dakin su Nazeem ya shiga da ita yana ta lallashinta Sai da ya dan mata jan ido ne ta Daina kuka ta koma ta Lafe a Kirjinsa tana kuka sai da ya tabbatar da ta daina kuka sannan ya fito da ita da kansa ya rakata har kofar shashen Hajiya sannan ya Dawo..sallama sukayi da Aliyu zasu wuce shida Aliya,Hajiya ta rkota har haraban gidan ta mata godiya bayan ta bata kayan Biki haka su Aliyu suka Dauki Hanya ba tare da sun kara tada mganar abunda ya Faru Jiya ba
Sun dai yi mganar Amina yau za"a rakata Sabon gidanta Aliyu na mai Tsiyar yau ango yake shi kuma yana jin Dadi ita kuwa Aliya duk jikinta yayi sanyi ta kara tsorata da Duniya.
Ana tafiya da amare yan gusai sukayi Harama Zafira dai tun kafin tafiyar su Hanne ita da mamata sukabi yan Daurin aure suka koma.
Ba yadda Hajiya batayi su bari su raka Amina Gidanta ba sukace bakomai in ta Haihu zasu dawo suna gab??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????adaya ransu babu Dadi kaf dinsu suka juya aranar gidan Aba bako Tsinke sai Mamanmu ita kadai da Halinta kaf su ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login