Showing 165001 words to 168000 words out of 265571 words

Chapter 56 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28891

ta musu wani banzan kallo kafin tace"kusan dai ni yanzu ba Sa"arku bace ko..?
Igiya uku ne akaina..Taimaka muku ma nake yi ina yawo da yara. !
Hanne da Hamida suka saki baki ganin haka yasa ta Musu gwalo tatashi da gudu ta Fada Dakin su Hanne Tana Dariya suka mara mata baya suna fadin yau sai ta gayamusu su waye yara..?
Ranar dai anan suka wuni Shashen Hajiya suna abunda suka saba sai bayan sun dawo islamiya ne Hajiya ta saka aka maida Amina gida tana kunkuni Tana komai bata samu yima Baba mallam bayani ba sai washegari da suka dawo makaranta ta Fadamai ya Dade yana mamaki ya tambayeta yaushe ta fara tsorata tace tun tana karama ta dade mallam ya Dinga Fadin Sakacin mamanmu da Aba da Amina na Fama da wannan Laluran ammh bsu sani ba Hajiya ce ma ta Lallasheshi ya bar mganar da yace har Aba din sai ya kira da mamanmu ya musu Fada.
Shi ya Rubuta mata addu"o'i ya bata yace ta Rika karantawa Duk Dare in zata kwanta Tare da Sauran addu"an barcin da Annabi ya koyar damu.
Amina yadda Taga Mallam ya Dau abun ne yasa itama bata Dauka da wasa ba sannan Danmallam ma sun sake mgana da wayar Hajiya Data Fadamai yadda sukayi da mallam ya mata Fada kan ta Dage kada wasa ya Dauke mata Hankali ta rika kwanciya bata karanta su ba.
Shiyasa ta Dake bata kwanciya sai ta karanta sai gashi kuma Cikin ikon Allah tunda ta Dage sai ta samu Saukin Firgita din sai abunda ba"a rasa ba Danmallam har da mallam sun yi mgana Mallam nata fada yana Fadin da Haka Umaima ta Fara gashi nan suna so su taba mata kwakwalwa Dannallam yana so ya Fadama Mallam bayan haka ma yana Zargin akwai wani abu Tattare da Amina sai dai kuma bai da Hujjan hakan ammh yana so sai in ya kara Dawowa ya Zauna ya Fahimci matsalanta Domin Ranar da abun nan ya Faru tsakaninsu da Washegarin nan da Safe yaga tana wasu abubuwan da Dole tana da wani abu a Tattare da ita.


*******

Kwantashi ba wuya a wajen Allah su Amina har sun gama Jarabawarsu sun yi Hutu taso ta zauna anan tayi Hutunta Hajiya ta hanata sai ta Roki Baba mallan kan su Hanne su Bita ko Sati Daya su yi da Farko Hajiya ta Hana sai da Mallam ya saka baki Sannan ta amince suka Tattara suka koma chan da Niyar Sati Daya zasu yi Saboda islamiya basu yi Hutu ba.
Mamanmu bata Damu ba da akace Hamida zata je gidan Amina Domin alokacin tana Tsakar Cin Duniyarta ne Domin komai tace Aba ya bata baya Gaddama Kudi yake sakar mata bana wasa ba ta zama Tauraruwa a wajen sa Mamanmu ta samu Cikar Burinta Fiye ma da yadda take fata shiyasa ta manta da kowa da komai ko Anty Amarya ta kirata bata ma kaunar Hakan gani take tana neman Takura mata Shiyasa Amina ma bata gabanta Ta barta da Anty Amarya chan itace Zatayi mganinta ita yanzu Sa"idu ne agabanta yanzu shawaran komai sai yayi da ita sai abunda tace koda yace Jafar yace kaza ya kamata ko Hajiya sai tasan yadda tayi ta Kushe mganarsu ta sauya da nata Shiga kawai take tana fita Daga kayan alfarma kamar wata Yarinya sannan Malaminsu tana sakarmai kudi sosai Domin ta yaba da aikinsa
Anty Amarya kuma tana nan tana Jiran gawom Shanu domin ta yarda da aikin Malam ya sanar da ita Nasara tatace shiyasa bata Damu ba ta koma ta Zauna tana jiran tsammani kamar yadda ta basa duka yardanta Shiyasa ko Sakina ta kirata tana mata Korafi take mata Fadan bata da Hakuri aiki nawa suka basa kuma ya Biya musu Bukata..?
To wannan ma ta Zauna ta Jira komai zai zama Daidai da yardan Allah abunda basu sani ba Daga wannan Lokacin aikin ya kuskure musu sannan zasu cigaba da jiran majirata ne Jiran da zai kai su ga Ranar Nadamar su da Tonon asirin su..!

Ko Hutun da su hanne suka tafi Sakina kamar ta Haukace saboda Bala'i Amina Mahaukaciya take so ta maidata,gwara ma su Hanne suna dan jin mganarta banda Amina sai ta gama masifarta sun ba'ta mata Falo ko Kitchen Amina ta mata gwalo ko Ta mata Tsaki ta shige Daki abunta Sakina taci ji Yatsa kamar me..?
Kamar yadda yace a Cefanan watan nan an kawo su Goldemorn su Amina an samu banza ana ta Wadaka madara kuma da kayan Tea kafin Sati sun kare saboda yadda suke barnan sa basa da aiki sai dan sululu ko Wainar Fulawa gashi Sakina bata son kazanta su kuma in suna aiki a Kitchen din sai sun yi kaca kaca dashi in tayi mgana Hanne da Hanida kadai ke Sauraranta banda Amina da take maidata ma mahaukaciya.
Sakina abun ya isheta kullum sai ta Kira Danmallan ta kaimai karan Amina da kannensa shi har ma ya gaji Saboda bai isa ya kore su ba Amina Matarsa ce sannan su Hanne kannensa ne ko ba aure suna da Damar zama agidansa watarana da abun ya ishesa sai yace ta bama Amina wayar da an bata ya fara mata Fada sai ta saka kuka tace In ta gaishe da Sakina sai taki amsawa ta bita da Zagi sannan bata barin su suna shiga Kitchen sai tace suna mata kazanta Ayadda take mgana ne yasa Dole ma ayadda da ita sannan tace ga su hanne ma yaji ta bakinsu su hanne kuma basu taba kwaye ma Amina baya ba, sai su karantamai yadda Amina tace Daga karshe sai abun ya koma kan Sakina yayi mata Fadan itace babbar banza tana Biyema yara sun rainata sannan kada ta kara Hanasu shiga kitchen ta bar su dafa abunda suke so itama ta Dafa nata baya son Fitina.
Tunda ga ranar ko Takai ma Korafin Amina ta mata kaza bai Sauraranta Anty ma Zaginta take yi tace ta Daina Danunta tunda ita Sakarya ce zata Zauna yara kanana su gagareta
Alhalin basu san yadda yaran nan suka Sakata gaba bane barin ma Amina in ta fito falo ta gansu ta rika waka kenan tana cema mata agwagwa in ta yi mgana ta maidata mahaukaciya sannan ba Tsayawa ma take yi ba,ballatana ta Daketa ta huce.
Su hanne wajen kwanansu goma Daga su Har Aminar basa zuwa makaranta da Hajiya tayi mgana ne Mallam yace ta rabu dasu Idi ya rika zuwa yana Daukosu yana kawo su makarantar Daganan,saboda dukkansu yara ne sannan nan gaba kadan In Aminar ta bar garin ina zasu ganta..?
Sannan kuma suma watarana gidan auransu zasu watarana sai dai labari..da Haka ta kyalesu suka zauna achan sai dai Idi ke zuwa yana Daukosu da an tashi kuma ya maida su.
Cin Duniyarsu da Tsinke suke yi ko ajikinsu Sakina ta koma zaman Daki bata Fitowa saboda su in tana son Tsira da Mutumcinta Ranar kwatsam sai ga Aliya matar Aliyu sun zo kawo Amarya wata Diyar kanwar mamanta ne shine tazo gidan ta iske Sakina cikin Daki Amina ta gagareta bata iya ma Fitowa sanda Sakina ke Fadamata tana kuka Sai taga Laifin Sakinar da ta Zauna yarinya karama ta gagareta.
Taja Sakinar suka fito su Amina na Falo sunyi Daidai ga Filets nan da Kofuna da gorinan lemuka da suka gama dasu nan basu Dauke ba suna Hira Ita a Dole sai ta kwatan ma Sakina yancinta..
Haka ta Dinga surfama Amina Zagi tana kiranta kwaila kazama mara Tarbiya su hanne sukayi Tsuru Tsuru Amina ranta ya baci ta mike ta rama Zaginta da Aliya ke yi ita kuma tace Zata Daki Amina ai ko sun ga Hauka Amina ta Tsaya kikam idanuwanta sun juye ba baki sai Fari tace in Aliya ta isa ta tabata tagani Sakina ke jan Aliya tana ta bari kada ta tabata ta ja mata bala"in wajen su Hajiya.
Ita kan Aliyan ta Tsorata bata Taba Aminar ba suka koma Daki tana Borin kunya Amina kuwa ba wani Abunda ya Sameta Zafin ranta ne ya taso mata Taso ta tabata ne Daga Sakinar har Aliyan sai sun raina kansu Wlh sai kuma Allah yaso su su Hanne na tabata Hakuri ta balla musu harara tace sun cika Tsoro ba wanda ya isa ya Takura musu acikin gidan nan.
Aliya taso kwana ne ammh ganin yanayin Amina yasa taki kwana ta koma gidan Amarya ta kwana ko Washegari Datace zata dawo bata Dawo ba ko da Sakina ta Kirata tace mata gata a Hanya zata koma gida ammh Tana zuga Sakina kan Wlh in Amina ta kara mata rashin kunya ta kamata ta mata Dukan tsiya Sakina jinta kawai take ina ita ina taba wannan yar gold din ai sai Hajiya ta saka Umar ya Saketa.
Allah ne ya taimaketa suka koma makaranta Hajiya tace su Dawo gida idi yazo ya Dauketa sai ta Samu Sauki Bata ma haduwa da Aminar sai ta bar gidan take Fitowa sannan Daga ranar jumma"a sai Lahadi take dawowa tana ganin Lokacin Dawowarta yayi zata shige Daki karfi da yaji Bala'in Amina da jindalinta ya Saka Sakina ta kasa Sakewa agidanta.
Gashi Danmallam ya Daina Sauraranta indai kan Amina ne yace yana wata kasar ta daina tadamai da Hankali baya so in bazata kama girmanta ba bazai iya Hana Amina ta mata Rashin kunya ba abu goma da Ashirim ga rashin miji ga Fadan Anty Amarya Data Kirata sai tace laifinta ne sannan ga Amina ta Sakota gaba..!
Ana cikin Haka Sadiya Diyar Anty Amarya ta Haihu bakwaini yarinyar tazo ba rai anan Dutse su Sakina ana ji sune gaba gaba ita da Hj.Nasara da Hajiya Babba suka tafi suka Duba Sadiya Dake asibiti domin ance ta Zubar da jini sosai achan suka Rabota Tunda Danmallan ya barta ita ta zauna da Sadiyan har aka sallamota Daga asibiti duk da ga yan"uwa ammh Anty Amarya tafi yarda Sakina ta Zauna da Sadiyan.
Bayan sun Dawo gida ne Sakina ta Fara Zazzaabi har da su karin ruwa koda akaje asibiti akayi Test aka gano Tana da Shigar ciki kimanin wata Uku da kwanaki Ashe koda Danmallam ya Tafi ya jefa kwallinsa araga a maran Sakina basu sani ba.
Murnan wajen Anty Amarya da Sakina ba"a mgana kamar an basu aljannah Hajiya da mallam ma Tare da shi kanshi gogan Danmallam Domin yana matukar son yaga kwansa a Duniya,Sannan da kansa ya Sanar da Sarood ta tayasa murna Har dai yanzu shuru ne ba wani cigaba ammh basu sare ba suna cigaba da shan mgani shi dai har yanzu ne bai yarda da Shawaran Aliyu na ya kira mallam ba yana tunanin al"amarin nasu ba Sihiri bane.

Mamanmu dataji itama tayi murna sannan tasan yanzu tunda Cikin Sakina ya samu sai Madina ta barta taci Gumin Wahalarta ta Daina Damunta.
Su ba Fatan cikin ya zauna suke yi ba kansu yayi girma suna ta Feleke Anty Amarya taso Sakina ta Dawo gabanta ta raini cikin mallam ya hana Saboda za"a bar Amina ita kadai Gidanta ta koma ammh sai Ta tafi da Sa"adatu tana kula da ita ana zuwa Daukansu Ita da Amina da ko mgana basa ma juna Amina taji zencen cikin Sakina ko ajikinta tunda ko"ina Zencen cikin ya Zaga.
Haj uwani na gefe tana kallonsu aranta Dariya take musu domin tasan wannan karon ma ba zai zauna ba Haka kuwa akayi yana da wata Hudu watarana da Daddare Sakina ta tashi Cikin Jini Hankalin Sa"adatu ya tashi ta Kira Anty Amarya koda ta zo ita da Idi Direba suka tafi asibiti sai wankin Ciki akayi ma Sakina cikin jikinta ya Sake fita karo na Hudu.
Abunda Haj.Uwani bata sani ba in na Sakina ya sake zubewa daman chan Allah bai yi Rayayye bane ammh wanda Allah zai rayasa yana nan har ya fara zama gudan jini batare da kowa ya Farga ba Hatta kuwa da wacce Cikin ke jikinta.








*Janafty*


*TFZB2012*


*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*


Wannan karon ba Anty Amarya kadai da Sakina suka shiga Tashin hankali ba harda mallam da Hajiya Tare da Uban gayyar Danmallam da kuma ilahirin Masoyansu sun tausaya musu bisa rasa wannan cikin ma a karo na hudu kamar sauran.
Mallam shi ya saka ayi ma Sakina gwaje gwajen mahaifa domin a Fahimci inda matsalan take Dayake wani asibitin kudi dake cikin gari Anty Amarya ta kawo Sakina duk kudin da aka kashe mallam ya Dauki Nauyi sannan suna tsaye kan Sakina shi da Jafar da Nasir da ita kanta Hajiya da Aba din sakamakon Sakina ta Zubar da jini yasa sai da aka mata karin jini gabadaya yan"uwanta ne Anty Amarya ta kira tana kuka ta Fada musu wadanda ke kusa suka zo aka samu aka gwada jininsu sai Allah ya taimaka jinin kaninta wanda ke bimata yayi daidai shi aka diba aka sanya mata.
Sakina sai da ta kwana ta wuni sannan ta farfado ko ba"a fada mata ba tasan ta rasa cikin ta ma a wannan karon domin haka take yin indai zata yi bari tayi ta zubar da jini sannan ta Fice Daga Hayyacinta na wani Lokaci.
Sakina tayi kuka kamar ranta zai fita wannan karon Anty bata da bakin lallashinta domin ta Sare ta kuma kara yarda da Hasashenta na Tabbas akwai wanda ke lalata cikin Sakina akwai wanda ke neman shiga Tsakaninta da Cikar Burinta ko waye kuwa in ta ganosa sai ya gane bai da waye ita Madina bata fito ba sai da ta shirya.
Anyi ma Sakina gwaje gwajen da Mallam yace an kuma tabbatar musu da komai lafiya harta mahaifanta Lafiyalau ita Hajiya har tana Fadin ko kila Sakinar tana da Raunin mahaifa ne ammh sai likita ya tabbatar musu da Komai lafiya Sanadin barin dai bai gano wani abu ba sai a bar shi da Allah ke ikonsa Domin shi ke kashewa ya kuma ya rayashi alokacin dayake so Sannan Haihuwa ta sa ce ga wanda yaga Dama yake bamawa Haka Mallam ya dinga fadama Sakina alokacin Dayake mata Nasiha a daran Data cika kwana Hudu asibitin Daya kara zuwa Dubata shi da Hajiya da Daddare.
Hajiya ma ta kara da nata Nasihun Saboda duk mai imani in yaga yadda Sakina ta dawo sai ya Tsausayamata kuka kadai take yi,mganganunsu kwata kwata basu shiga kunnenta ba Hango kanta take a matsayin Bora duk Ranar da Haifarma Umar magaji ya kuskure kanta sannan ta Fara Sarewa da Tunanin Anty bazata iya ba Sannan wannan Burin nata bazai Taba cika ba Nasara kuma su daina Hasasota nan kusa tana da Nisa kafin su isketa bama domin haka ba itama Tana so ta Haihu sosai take son Taga ta Haihu sannan tafi so kowa Sanin yadda Umar ke son Haihuwa ya Fada mata ba Sau Daya ba sau Biyu ba,kawai yana da kawaici ne sannan addininsa yasa ya yarda da Allah ke yi alokacin da yaso shiyasa bai cika nuna Damuwarsa sosai ba..
Shiyasa har su mallam suka fita Sakina ma bata cikin Hayyacinta Anty ke kwana da ita tana kula da ita suna Fita Sakina ta Fashe da wani kuka mai karfi Daga karkashin ranta Anty Amarya ta taso zata riketa ta Daga mata Hannu tana fadin"Don Allah Anty kada ki hanani kuka ki bar ni nayi domin shine kadai zai sa naji Sanyin abunda ke damuna acikin Raina..!
Tafada tana Dakatar da ita da Hannu Dole Anty ta koma baya ta Jinjina kai gabadaya bata cikin natsuwarta Saukinta Daya yadda mallam da Hajiya da yan"uwan Danmallam ke Tsaye kan sakina da shi kanshi Danmallam din,arana ya kira fiye da sau Biyar yana tambayan Lafiyan Sakina Sannan ya Turo abokinsa Aliyu dashi ake ta Zirga zirga in bai zo yau ba zai zo gobe har da matarsa Aliya yazo Abinci kuwa baya zuwa hannu Rabbana da kwalayen maltina da kayan maarmari saboda karin jini ga ita Sakinar
Ta kira Dayyaba sun yi mgana gobe take so in kanwarta A"i tazo daga Dutse zata bar mata Sakina ta kula da ita zata koma wajen mallam tamai bayani so take ta gano wanda ke lalata mata aikin data wahala tayi shekaru tana Fata akansa in ko Zarginta ya Tabbata kan Uwani sai ta raina kanta sai ta Fahimci wacece madina ba marliya ba.
Tana gani Sakina na gunjin kuka bata da karfin gwiwan hanata saboda ta gaza Duka alkawarin data mata ta kasa cikamata,maimakon ta Fahimci Talalar da Allah yayi musu ta kare ne suke ganin sabawa akan lamarinsu ammh ina idonsa ya rufe gani suke a koda yaushe nasara tasu ce.

Suna Mota zasu koma gida Hajiya Dake gefen mallam ta kallesa tana Fadin"Mallam ka kira Danmallam ka yi mai Nasiha da Hakuri ko..?
Domin jiya da mukayi mgana yace min yana gida kwance bayajin Dadi..kuma ko shakka babu abunda ya faru ne ya tabasa kamar yadda ya taba Sakina wannan karon..!
Mallam ya muskuta kafin yace"Na kirasa da Safe munyi mgana..Sosai nayi masa nasihan na kuma tunasar dashi cikar imani shine yadda da kaddara mai kyau ko akasinta na horesa da yayi Hakuri ya jira kadan kila Tanadin da Allah yayi masa yana gaba ne Rashin hakurinsa sai ya bata komai..!
Hajiya tace"Hakane kan mallam..Allah yasa mu dace Allah ya basa zuru"a Mai albarka..!.
Mallam ya amsa mata cikin Damuwa a karkashin ransa yana jin Tsausayin Umaru ache kana neman rufe shekaru arba"in ko Haihuwan fari bakayi ba sa"o"insa ya tabbata Har da masu ya'ya goma wadanda sukayi aure da wuri ma kenan ga dai Amininsa Aliyu nan baya baya yayi aure ya"yansa Biyu tabbas yasan akwai Damuwa ammh bazai barsa ya nuna gazawarsa ba zai cigaba da Tunasar dashi Hakuri da Rayuwa a duk s???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?anda tazo masa da kuma yanayin datazo maka sai ka saka Hannu Biyu ka karbeta.

Kamar yadda Anty Amarya ta kwana da kuduri gari na waye saboda ma tana Sauri bata jira A"in tazo ba sun dai yi waya tana Hanya ta kusa shigowa ta bar Sakina tace mata zata je ta Dawo alokacin har Jafar da Nasir sun kawo breakfast Matan su suma suna kokari sunzo sun duba Sakina Daganan kowannen ya wuce wajen aikinsa.
Batare da ko Sanin Mallam ba ta Dauki Hanyar Dutse tunda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login