Showing 102001 words to 105000 words out of 265571 words

Chapter 35 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28944

miki zan tare komai nice fa
Ko Duniya zata juya miki baya ni ina Tare Dake..?ko na taba juya miki baya..?
Amina ta girgiza kai da Sauri tace"Yauwa to tashi kije..Ki bari sai Aba din ku ya shigo gida sai ki tafi Wajen Mallam din..!
Da kai ta amsa mata ta kasa mata Musu,Ammh tana ganin kamar abunda tasata tayin bamai kyau bane Tayaya zata Bijirema Aba da kuma Baba Maallam anya in tayi haka batayi Butulci ba..?
Sai dai kuma ta kasa yima mamanmu Musu har ta baro Dakin ta bar mamanmu na Hararanta cikin Takaichi kafin tace,"Shashasha..!

Amina kuma Dakinsu ta koma ta kwanta kan gadonta tana kukan yadda Rayuwa ta juya mata baya aduk ranar Duniya sai ta tuna da Aminu tayi kuka,da kuma kewarsa tare da Tunanin Halin Dayake ciki..!

Bata da mai gayamata kuma ita bazata nemi taji ba Tun bayan Mutuwar yaya tayi alkwarin daina Zame kowa Jidali so take ta wanke kanta wajen Aba kada ya kara ganin bakinta ammh kuma meyasa mamanmu zata ce sai tayi haka..?
Tana kwancen taji Shigowar Aba,chan kuma sai ga Mamanmu tazo Dakin tana tashinta yi tayi kamar mai barci tatashi tana sosa ido.
Mamanmu tace"Tashi kije Aba din ku ya shigo shi da jawad..!
Dole ta mike tana Tsaye kanta har ta saka Hijabi tare suka fita ta iske hamida na barci ma saman Tabarma har kofar gida ta rakata ta bude mata gida tana Fadin"In kin dawo ki shigo Sai ki Rufe..Ko kuma kiyi kwanciyar ki Bangaran Hajiya kada Aba din ku yaji Dawowarki..!
Hawaye ya cika idonta yasa ta kasa mgana,Haka ta wuce sum sum har Zuwa gidan Baba mallan megadi kansa yayi mamakin ganinta Tara na Dare har ya wuce,sai dai bai yi mgana ba.
Gabadaya kamar an cire mata wani karkashi Jiki a sukuku ta karisa har Falon Baba mallam data ga haske acikin Alamun bai kwanta ba.
Ta Dade tsaye ta kasa shiga tana saka tana warwara,Har sai da taji mganar Baba Mallam daga ciki yana Fadin"Waye anan..?
Jikinta sai ya fara rawa cikin Inda inda ta Daga Labulen falon ta shigo Tana fadin"Nine Baba mallam..!
Mamakin ganinta yayi da Daddaran? nan zaune yake kan kujera mai zaman mutum Biyu sanye da Shigarsa kamar bai ma Sauya kaya ba Harda Rawaninsa da Farin gilashinsa yana Duba wani littafin Larabci..!

Cikin mamaki yace"UWATA..!

Jin sunan daya kirata yasa taji Rauninta ya fara bayyana kaawai sai ta Fashe da kuka kukan data ke rikewa Baba Mallam ya ijiye littafin hannunsa yana fadin"Ashh..Kari so naji waye ya tabanin Uwata..!
Dole ta karisa gabansa ta Zube tana kuka ya Dafa kanta yana fadin"daina kuka Fadamin damuwarki ni kuma nayi miki alkwarin Magance miki ita..!
Sai taji Wani irin kaunar da bata jinta ba kan Baba Mallam ya taso mata? tayaya zata iya kallon wannan Dattajon mai Farin Alheri taki jininsa taki Alherin daya kulla da ita duk da Rashin Fahimtar dake Tattare da Rayuwarta gaskiya bazata iya ba..!
Kawai sai ta sulale kan kafar Baba Mallam tana Cigaba da raira kukanta..
Cikin Damuwa ya saka Hannu yana Shafa kanta zuwa bayanta Allah ne ya Hada wannan Kaunar kwatankwancin kaunar da yake ma Sa"idu..!
Cikin wata murya yace"Kiyi hakuri Mamana..Ki yi hakuri nasan ban kyauta miki ba..Na aura miki Umaru Jinina sai daga baya naji kamar nayi son kai..ban kyauta ba kamar na Zalunceki..!
Da sauri Amina ta Dago Idanuwanta Jajir cikin kuka tace"Har Abada bazaka Taba Zaluna ba..Na karbi wannan gatan da kayi min na yaba..Allah yafini yabawa Baabaa..!

Kawai sai yaji sukuni sukunin da bai Taba samu ba Tunda ya hada wannan auran cikin Tausasawa yake fadin"Allah yayi miki albarka..Nagode sosai .Allah ya jikan Hadiza da gafara..!
Da amin take amsawa ta na godema Allah da baisa ta tafka wannan abun kunyar ba watsama Wanda Alherinsa ya Lullube rayuwarta data iyayanta gabadaya..!




*Janafty*

*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*


*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janaftyd'?*


*Sadaukawa ga Halima yusuf gwarzo Besty Alherin Allah ya kai miki a dukkan inda kike Ameen*



*
Ranar Hajiya Uwani keda Shashen Mallam shiyasa ta chaba ado tana tashin kamshi ta ko"ina,Ta shigo da Fara"arta sai dai kuma ya mamaye hakan da bakincikin ganin Amina gaban Mallam suna hira saboda Takaici ji tayi kamar ta koma da baya sai dai sun riga sun ganta bata da yarda zatayi sai ta Saki Fuskarta ta Kakaro Dariya da Mirmishi ta Dora Saman Fuskarta..!
Baba Mallam ya dago kansa Daga kan Amina ya sauke kan Hajiya uwa data Tsaro kwalliyanta cikin Doguwar rigar shaddanta Nan da nan ya saki Fuska yana kallonta acikin matansa kaf ko Anty Amarya bzata gwadama Uwani Kwalliya da kamshi ba Duk da Ta kwana Biyu a duniya bata yarda ta zauna ba gyara ba ita din yar Kwalliya ce kowa ya sani.!
Cikin Fara"arsa da Sautinsa yace"Lale da zuwa Hajiya uwa..Uwanin Alheri uwanin Yunusa daman yanzu nake Fadi araina ko an tsaya yanga ne yanmatancin ne ya tashi!
Kanta sai ya kara girma ta kariso Cikin takun mata har ta kariso gefensa ta zauna sai Amina ta matsa gefe Tana gaisheta ta amsa Tana Fadin"Ka fahimci abunda ya Tsaidani ko Mallam..?
Yana kallon Fuskarta yace"Na fahimta..Uwani uwayen kwalliya da ado..!
Dariya tayi Tana kallon Amina da kanta ke kasa tana wasa da Gefen Hijabinta cikin Fara"a tace"Allah yasa ban katse Hirar surukanta ba. !
Sai da ya kalli Amina kafin yace"Ko da Sakina bana Surukanta Uwani..Ballatana Amina..Itadin Uwatace..Hira muke ta Tsakanin Uwa da abunda ta haifa kin kum san bamai iya raba wannan soyayyar..!
Tana Mirmishi tace"Ba shakka kam.Ko na koma sai kun gama ne Mallam..?
Kai ya girgiza kafin yace"A"a ai bazata kare ba..sai dai mu barsa zuwa gaba..Mamana tashi kije shashen Hajiya ki kwana zuwa safe Dare yayi su Akilu sun kwanta ballatana na Taso shi ya rakaki..!
Amina batayi gaddama ba ta mike tana musu sallama ta fice zuwa shashen Hajiya babba tana jin sukuni aranta da bata Furta abunda Mamanmu da tsarata mata da batasan ina zata kai kunya ba..!
Sai da Amina ta fice sannan Hajiya uwa ta gyara zama tana fadin"Mallan kayi mgana da shamsu kuwa..?
Kai Tsaye yace"bai kirani ba meya faru..?
Cikin kwantar dakai tace"Kudin hannunsa ne duk suka kare wajen Registration,yace min yana son aturamai wasu kudin..!
Dayake shamsu ya samu gurbin karatu a Federal Universty Dutse ne har ya tafi..!
Baba mallam kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Nayi mgana da Aliyu abokin Umaru yace min har Daki ya samu nan Kusa da makarantar bai ce Komai ba..Ammh zan kira shi Shamsu naji kinsan ba kasafai zaka rika sakarma yara kudi domin sun Tsallake gaban zuwa karatu ka rika saka ido kada watarana sakewarka ta saka su jawo maka wani abun mgana zan yi mgana dashi kuma zan saka shi Aliyun ya Bincikamin inda bukatar wani Abu zam ma Sa"idu mgana zai Turamai Insha Allahu..!

Hajiya uwani gabadaya takaici ya Rufeta,kamar ta saki kuka haka take ji sai dai bata nuna ba sai ma kai data Rausayar tace"Shikenan hakan yana da kyau Mallam ka bincika din..!
Daga haka ta tsuke bakinta tana wani Nazari har yaushe ne ya"yanta zasu zama na Farko wajen Mallam bayan ya"yan Hajiya Babba da Sa"idu Burinta na shekaru bazai cika da wuri ba kenan.
Shi ya katse mata tunani da Fadin"Ya jikin Umaima ina Fatan ta daina Ihun nan cikin Dare..?
Ya famo mata inda ke mata kaikayi Cikin Karin Damuwa tace"To yayi sauki za"a ce Mallam..Anya ba mganar malamin nan gaskiya bane..?
Cikin Kallon sama sama yace"Dayace mene..?
Sannan wajen wani malami kika kai min yata ban sani ba..?

Sai alokacin tasan tayi barambarama ai baisan sunje har Niger kan matsalan Umaima ita da Batula ba..!
Cikin Inda inda ta fara mgana da sauri ya katseta cikin Kaushinsa yace"Ina kika kaita kuma me malamin da kika bashi yarda Fiye da Ubangijinki yace..?in kikamin karya wlh zan ci Mutumcinki in nayi bincike na gano gaskiyan mgana..!

Sai Jikinta ya fara rawa tasan Halin Mallam in bata Fadamai ba bazaman Lafiya ita kuwa dake cikin Kishiyoyi har uku mezai sa ta dinga Fada da Miji..!
Da hanzari tace"Wlh ba da son raina naje ba labarinsa naji ance yana bada mganin Aljanu..k..

"Ki amsamin Tambayata..!

Katseta yayi cikin bacin rai bakinta na rawa tace"Niger ne..Mukaje kuma..kuma yace ne wai Ture ne akayimin bai sameni ba ya Fadama Umaima..!
Wani wawan Tsaki yaja kafin yace"Wa ya rakaki wajen..?
Kai Tsaye tace"Kanwata Batula ce..!
Yana kallonta cikin bacin rai yace"Ba tun yau ba na lura da Batula ta yarda da Bin malaman nan makaryata makiyan Allah kema shine ta jaki kikai min ya gaban wani mushuriki da sunan neman mgani akwai abunda zai baku wanda Allah bazai baku bane..?Meyasa wani Lokacin baku da Tunani ne Uwani..!

Da sauri ta tareshi ganin yadda Ransa ya baci tace"Wlh ni da batula muka je..Ban je da Umaima ba..!
Cikin bacin rai yace"Ko baki je da ita ba kin kai laluranta gabansa kin Tallatamai shi kuma ya cikaku da karyansa..Banda Hada fada da karya waye zai miki sihirin da har zai koma kanta..?To ban yarda da wannan ba Ni ya'ta Lalurarta daga Indalahi ne kuma garesa nake nema mata waraka in ta warke wannan ikonsa ne in bata warke bama wannan ikonsa ne..Kada na Sake ji koda wasa wata mgana irin wannan in haka ta sake faruwa komai ma zai yi faruwa zan dauki mataki mummana akanki kin ji na Fadamiki..!

Ya karishe faada cikin bayyana bacin ransa da sauri ta Sulale kan Gwiwoyinta tana fadin"Kayi hakuri mallam..Insha Allahu haka bazata kara faruwa ba..!
Bai kalleta ba yace"Bana son Rabuwar kai kan mata na da yara na..Nayi shekaru ina hada kan iyalaina Waje Daya..Nan duniya bayan ku da Iyalan Sa"idu bani da wani Ahali da zan kallah nace nawa ne sai ku..To ki sani in kina Biyema mganar malaman karyan nan zaki haifarmin da Gaba cikin Gidana kuma in hakan ta faru Uwani zaki sha mamakin hukuncin da zan yanke akanki Wlh..!

Gabanta ya fadi taya ya komai zai kwace mata Burinta bai cika ba yasa ta kwantar dakai tana ta basa Hakuri sai da taga ya Hakura sannan ta Sauke Numfashi ta koma ta zauna tana kokuwa da bacin ran dake taso mata..!
Ba domin ta kasa galaba akansa ba da Tuni Mama ta samo mata kan mallam ya zama sai yarda tayi dashi sai dai ina ta gaji da kashe kudi akansa ta Hakura Allah yana tare dashi kuma ya kare bawansa wani abu bai isa ya Cutar dashi ba sai dai ko in ya so..!
Ganin yadan sauko har suna Hira yasa ta Sako mganar dake cin ranta"Mallam ya mganar Amina da Danmallam ne..!?
Naji bakace komai ba haryanzu..?
Kai tsaye yace mata"Har gobe sunanan a matsayin miji da mata..wani abu kike son sani kuma..?!
Ya kalleta cikin son Tabbatar da abunda yake Tunanin take son ji game da lamarin.
Da sauri ta sauya mganarta da cewa"Maallam mganar tarewa fa..?ai tunda angama mai wahalar itama sai yayi mata Visa da Shedar zama achan kamar yadda yayi ma Sakina ya Tafi da matarsa ni aganina zai fi mallam..!
Ya dade bai yi mgana ba har ta Fidda rai kafin taji ya sauke numfashi Lokaci Daya yana fadin"Bazan yi haka ba..zan bama Mamana daman da bana ma kowacensu..Bazata tare a matsayin matar Umaru ba sai ta gama makaranta ma"ana in sunyi Candy in Hadata da yan"uwanta in aurar dasu..!
Hajiya uwani da Farimciki ya cika sai ta kanne cikin wani yanayi tace"Nan da shekara nawa kenan Mallam..?
Kai Tsaye yace"Hajiya tace alissafi Shekara Daya da wani abu in bai kai Biyu bama..!
Ranta Fari tas kafin Lokacin nata Burin ya cika wato ma ta kwantar da Hankalinta Amina bata cikin Tsarinta yanzu tunda mijin ma baisan da ita ba kuma tarewar ma ba yanzu ba hakan ya Bala"in yi mata Dadi har sai da Fuskarta ta Nuna cikin dan yanayinta tace"Gaskiya kuma fa hakane..Ko Sa"idu kada yaga anyi mata Rashin Adalci..!
Wani banzan kallo yayi mata Kafin yace"ko Sa"idu ina da iko da Kansa ballatana abunda ya Haifa..Ko cutar dashi zanyi bazai taba mgana ba..Ballatana ba wannan Tsakani na dashi.Kauna ce da Biyayya Tsakanin Uba da abunda ya Haifa..Kada ma na Sake jin wannan mganar Sa"idu namin Biyayyar da ko ya"yan dana Haifa basa min yana wahala dani da Dukiyata batare da na yankamai albashi ba gayamin cikin Tarin mazan da na Haifa akwai wanda ya zauna Dani yake wahala dani kamar Sa"idu..?
Kai ta girgiza ta kasa mgana Miyan bakinta ya kafe cikin Dattakonsa yace"To ki saka aranki Sa"idu Shakikana ne..Kafin na same su shi na Sama kuma ina masa kwatakwacin kaunar da Uba zai yima abunda ya Haifa..Ki saka wannan aranki..!

Daga haka bai jira cewarta ba ya mike? Dauke da Littafinsa ya Nufi Cikin Bedroom dinsa yana Fadin"Ni na shiga ciki sai kin shigo..!
Da kallon Takaici ta bisa kamar tatashi ta Makesa haka take ji Sa"idu rai Daya ya hana Burinta cika agabanta Mallam ke fadin yafi yemai ya"yan daya haifa Dariya tayi acikin Ranta Saboda itace silar rashin zaman Umar da Nazir agaban Ubansu ballatana su taimakamai bata so su sha gaban ya"yanta Yanzu kuwa Burinta yana gabda cika Nazeem ya kusa gama makaranta sannan Tsumi da Tanadi ya karanta wato Economics sannan yayi Degrre dinsa na Biyu kan abunda ya shafi Kasuwanci yana Dawowa zata san yadda zatayi Sa"idu ya matsa ya bama mai waje wajensa ya kasance shine kan duka Dukiyar Mallam din Kafin Uzairu shima ya gama yazo su hada hannu hango kanta Take shekara Biyar masu zuwa ita Amtsayin Hajiya babba..Ya"yanta ne masu gidan ita ce mai Bada Umarni da mgana da yawun mallam wannan Tunanin yasa ta farinciki ta tashi Cikin Takunta ta nufi Bedroom din mallan tana cigaba da Tsara wasu abubuwan acikin ranta..!

Amina kuwa sai washegari Hajiya ta ganta saboda sanda ta shigo gabadayansu sun yi barci Ya Abida ce kadai idonta Biyu tana karatu hanne ma ta Dade da yin barci.
Da safe ko gida bata koma ba kayan Hanne ta saka da hijabinta na Hadda Tunda guda Biyu hannen gareta.
Suka tafi Hadda Hamida bata je ba bata da Lafiya ciwon mara Ya zeenatu ke fadama da Amina taga bata ga Hamidan ba..!
Sai da yammah da suka Dawo Amina ta Dawo gida ita Da hanne suka Duba Hamida taji sauki ma,Hanne bata jima ba tayi musu sallama ta wuce gida Mamanmu daman jiran Amina take yi taji ya ake ciki tun Safe Aanty Amarya ta Kirata taji Labari mai Dadi ba wani bayani shiyasa Hanne na Tafiya taja Amina kuryan Dakinta Tana Fadin"Ya kuka yi da Mallam din..?

Amina ta Sadda kanta kasa kafin tace"Mammanmu na kasa..Bazan iya kallon Baba mallam nace bana son jininsa ba..Bai kamata na rama Tarin Alherinsa da sharri ba..Sannan in Aba yaji Wlh sai ya kusa kasheni agidanan..!

Ta karishe kamar tayi kuka ba Domin mamanmu ta kai zuciyarta nesa ba da sai ta kaima Amina Duka yadda Wani Takaicinta ya kamata ammh duk da Haka sai da ta Tureta tana Fadin"To Shikenan tunda kin kasa..sai kije..Sakina ta gasaki don Ubanki..bakuma zaki taba Daraja ba Tunda baya Sonki..Kuma matar Cushe bata Daraja .!

Yadda ta Zageta ta kuma Tureta yasa tasan ranta ya baci da Sauri ta riko Hannayenta tana fadin"Ba haka bane mamanmu..Wlh na kasa ne bazan yi kallon Baba mallam nace mai bana son auran nan ba..!
Mamanmu da kanta har ya fara ciwo Saboda takaici tace"Shikenan na fita Acikin mganar nan..Ba ruwana daman yancinki zan kwatan miki..!
Amina taji kanar tayi kuka kafin tace"To ke kije mana ki fadamai mamanmu..!
Hararanta tayi kafin tace"Saboda ni ce nake son rabuwa da shi ko..?ba inda zani ke kika sani ni sakamar min hannu Ke ji chan ki karata Wlh Amarya da Sakina bazasu barki ki zauna Lafiya ba.!

Amina tace"Tab..Sai dai ni ce bazan bar su zauna Lafiya ba Mamanmu..!
Ta razana gabanta na Fadi tace"Bangane ba..?
Amina tayi dariya kafin tace"To ai ba Tsoronsu nake ji ba..mamanmu ai Amina nake kirarina badai ta Mutum ba sai ta Allah su din banza!
Basu isa suyimin Abunda Allah bai min ba..!
Ta dade tana kallon Amina sai taga kamar Shagube tayi mata shiyasa cikin son tabbatarwa tace"ko kin fara son Danmllan din ne..?
Ta fada cikin Hararanta Amina ta Zaro Ido kafin tace"Ni..?Allah ya kyauta..ni Aminu kadai nake so..!
Ta Karishe Fada cikin wani yanayi Mamanmu ta sauke Numfashi kafin tace"Na Dauka kin fara son shi ne nace Ke kika sani..Domin Danmallam dai ya fara Tsufa auran wuri ne bai yi da kuma Haihuwar da bai samu ba..Kadan ne Aba din ku fa ya Girmesa..

Amina ta zaro idanuwanta suna shekk tace"Kai Mamanmu ko Aba fa bai Tsufa ba ballatana ya Danmllam..!
Mamanmu tace"Eyee..Kina son shi kenan Tunda ke baki ga tsufansa ba..?
Tafada tana Dungure mata kai Amina ta Dafe wajen tana fadin"Allah ya Tsari Amina..wannan ne zan so..Ya taba fa cemin banda natsuwa kuma ni wai kazama ce..!
Ta fada kamar alokacin yake fada mata Takaicin abun na Dawo mata Mamanmu ta kwace hannunta tana Fadin"ni sakeni..Kekika sani..Ba ina neman hanyar kwatan miki yanci ba kina bani kunya ba..Na barki dashi..Kin dai ji kazama yake ce miki Allah kadai yasan kuma wata kalma zai kara Jifanki dashi in ya ganki agidansa an riga an Tusamai ke..!
Amina ta Tura baki kafin tace"Sai na rama wlh..!
Mamanmu ta kalleta cikin Tunanin mafita ko mgana batayi ba ta Tura Kofar Tiolet din Dakinta tana Fadin"An kira sallah..!

Amina fita tayi ranta yadan yi sanyi ganin kamar mamanmu ta Dauki Zafi da Farko ammh Taji Dadi taga Daga baya ta saki ranta ajiyar rai ta sauke Tana jin kaso mafi yawa daga cikin Damuwarta suna yayewa Samun uwa irin Mamannu is a Bleessing..!
Mamanmu kuwa har Aba ya Dawo ta kasa samun wata mafita tana ganin ta bangaran Amina ba nasara Dole zata Jaraba ta bangaran Sa"idu ta Latsa ta gani ko zata ga Jini..!
Shiyasa koda ya dawo tayi wanka ta Shirya cikin riga da zani na Atamfa Hamida ta saka ta gyara Shashen nasa Dazu dataji Saukin jikinta Kayan abincinsa kuma tun kafin ya Dawo akai kai komai ciki.
Sanda ta fito duk suna Tsakar gida kan Tabarma suna Hira an kunna Gen akwai haske shiyasa basu shiga sun kwanta ba..!
Ganin bata ga Jawad b????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
a yasa ta kalli Zeenatu Dake fama da karatu tace"Ina Jawaad..?
Hamida ce tace"Aba na shigowa ya makale masa..!
Mamanmu kamar ta saki Tsaki yaron nan zai zame mata ciwon ido sai ta rabashi da Uban taga ya zai yi shege kawai..!
Mirmishi ta saki kafin tace"Ni ina Dakin Abban ku. Ku kwanta da wuri ke Zeenatu saboda makaranta Gobe..!
Da toh suka amsa mata har ta wuce suka cigaba da Hiransu Amina da Hamida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login