Showing 174001 words to 177000 words out of 265571 words

Chapter 59 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28905

tazo ta sama tamin zagin kare Dangi da Zargina wai ni nake asiri ina Zubar ma Sakina da cikinta..Fitar nan da kika ga tayi ni tazo ta kare ma Tanadi Hajiya..!
Hajiya ta Zaro ido kafin ta saka Salati ganin haka yasa Haj.Uwani ta karkace baki ta Cigaba da fadin"wai malaminta ya mata Duba yace ci kin matan mallam ne..kawai hajiya sai tace ni ce..Nan tazo ina ta mata Rantsuwa taki yarda dani ina Fadamata kada tayi saurin yarda da irin mallaman nan na karya masu Hada Fada bata Saurareni ba Hajiya haka ta fita tana kukan da Ikirarin sai ta ga Baya na..!
Hajiya nan da kika gani daman wajenki Zani Na fada miki abunda ke Faruwa naji Ciwon wannan abun sannan na Fadamiki bazan kyale Amarya ba sai ta san tayi min kazafi..!
Ta karishe Fada tana kuka Wurjajan..hajiya kuwa sai Faman Salati take yi kafin tace"Kinga Uwani bar kuka..wannan mganar ba tawa bace..Bari naje na kira mallam na Sanar dashi abunda ke faruwa wannan mganar tayi muni da yawa Uwani..!
Haj.Uwani na jan majina tace"Ko kin gayamai Hajiya ni bazan yafe ba..Sai an Bimin Hakkina akan kazafin da Amarya tamin..!
Hajiya bata Saurareta ba ta Fice tana Jimamin wannnan abun aranta tana Jin Haushin Anty Amarya bata taba Zarginta da shiga malamai ba ammh jin abunda ta aikata sai taji duk ta Zube mata ina amfanin wannan aikin..?ta Biyema mallaman karya suna neman hada fada acikin gida.
Hajiya na fita Haj Uwani ta mike ta Share Hawayenta ta yi Dariya kafin tace"Marliya tun a yau zaki san kin Hada Hanya da Uwani Diyar Hamza Tsafe..!
Ta fada tana Dariya har ta Hango yadda Marliya zata gane bata da wayau a falon mallam Dakin da Umaima take ta leka barci take yi Domin yanzu ko Makarantar Haddar ta Daina zuwa saboda Ciwon nata ya tashi gadangadan ana ta dai fama da mgunguna ne.
Hajiya ko na fita Bedroom dinta ta shige nan ta bar Hanne da Hamida afalo suna rike da Littafansu bata ma Bi ta kansu ba ta Shige Daki wayarta ta Dauko ta Kira mallam bai yi nisa ba yana gidan mai anguwa ya Kirasa kan Cases din Filin wasu marayu da aka kawo mai mganar to daman mai anguwa in wani abu irin haka ya Faru na bangaran addini yana kiran mallam Domin su Tattauna.
Yana jin Hajiya tace yazo gida ba Lafiya yace mata suna ma kan Hanya.
Lokacin ana gabda kiran Sallar La"asar ne yasa suna Dawowa yace bari ya Tsaya yayi sallah kafin ya shiga Cikin gidan
Hajiya ta fito ranta a jagule sai yanzu ma ta lura bata ga Amina ba Tunda dazu da suka Dawo daga makaranta,yasa ta kalli Hanne da Hamida dake ta yin aikin da malamin Lissafinsu ya basu a makaranta tace"Ina Mamah yau. ?
Hanne tace"Tana gidan baba Sa"idu dazu da muka shiga gaida mamanmu ta kwanta sai ta fara barci mu kuma da Zamu tahilo bamu tashe ta ba..!
Hajiya bata ce komai ba ta kada kai kafin tace"ku tashi kuyi sallah Lokaci yayi..!
Daga haka ta koma Cikin Bedroom dinta Ammh aranta sai da tayi Tunanin barcin Amina yayi yawa kamar kasa yanzu ko da asuba fa Dakyar ake tashinta wani Lokacin da Daddare kafin takwas Amina ta kwanta sannan in suka Dawo makaranta sai tayi barci ammh sai bata kawo wani Tunani ba tafi Barinsa a Saboda Basa Zama a zirga Zirgan makaranta da Sauransu.
Hajiya ta idar da Sallah kenan Kiran mallam ya shigo mata yace gashi ya shigo Gidan Hajiya batayi kasa agwiwa ba ta saka lullubinta ta Biya Shashem Hajiya Uwani Dake zaman jiran Kiran mallam suka tafi Falon mallam suna zuwa Hajiya tace ta fara gayama Mallam yadda taga Anty Amarya sannan tace Uwani ta maimata abunda ta Fadaamata Haj.Uwani ta gyara Zama ta Fara Rattafama mallam yadda ta Fadama Hajiya ta karishe cikin kuka tana Fadin"Mallam abu dayane in na Tuna yake min ciwo..Da Amarya ta Zargeni da laifin kisa Mallam..?
Ashe haka ta Tsaneni bansani ba..Ta rasa kazafin da Zatamin sai kazafin kashe gudun jini Tun kafin ya Fito Duniya..? Wannan in gaban yan Sanda za"a kai ai babban cases ne mallam..!
Mallam da ransa ya gama baci ko mgana bai yi ba ya Daga wayarsa ya kira Anty Amarya wacce ke cikin Bedroom dinta tunda ta Dawo Daga Shashen Uwani ta shige ta rufe kanta tana kuka kukan rashin mafita da madafa kukan takaici da gazawa a karo na farko ko sallah bata tashi tayi ba sai ga Kiran Mallam sai da gabanta ya Fadi balle Dayace tazo ta same sa afalonsa a kausashe.
Ai bata gama Sarewa ba sai da Sawo Hijabinta Fuskarta duk ta kode ta iso Falon mallam ganin Hajiya da Haj Uwani sai da yasa gabanta ya Fadi Jikinta ya fara rawa ta Tsaya Cak ta kasa gaba ballatana baya.
Mallam cikin kaushinsa yace ta kariso ita ake jira,Jiki a sanyaye ta kariso ta Zauna gefen kafar Hajiya a kasa tana kallon Uwani dake mata Dariya a kasa kasa Daganan tasan wani makircin ta kulla mata..
Kanta ya Daure sanda Mallam yake karanta mata abunda Uwani tace ya Kalletaa Cikin bacin rai yana Fadin"Marliya ashe ban Dade ina muku nasihan yarda da malaman tsubbu ba..?
Shine kika kai kanki bayan kin yarda dashi shine ya karanto miki karya kika zo kika Hadamin Fada acikin Ahalina alhalin na Dade ina gargadinku..?
Anty Amarya ta Tsure hankalinta ya tashi ta kalli Haj.Uwani dake matsan kwallar karya ta maida kallonta kan mallam taga yana mata wani kallo Sai kuka ya taso mata ta Fashe da kuka Tana fadin"Wlh ma..!

"Karki ce tak a nan wajen marliya..Baki da abunda zaki fadamin bana Kiraki Domin kimin karin bayani bane..na kiraki ne naja miki kunne Wlh Tallahi in na karajin mgana makammancin wannan sai na Saba miki in ma ban yanke Igiyan auran dake tsakanina Dake ba. domin ina kyamatar Zama Dake Marliya tunda kin zama Mushuruka mai bin malamai da yan Tsubbu makiya Allah..!

Anty Amarya ta tsorata ta Duka gaban Hajiya ganin yadda mallam yake mgana tasan ransa ya baci Uwani tayi nasara akanta tace"Hajiya don Allah ki bama mallam Hakuri ba Laifina bane kuskure ne..da sharrin Shedan..!
Sai kuma ta rike kafan Hajiya tana gunjun kuka Hajiya taji Tsausayinta ta Duka ta riketa tana fadin"Tashi ki Zauna marliya..!
Komawa tayi ta zauna tana kallon Haj.uwani Dake matsar kwallah tana mata Dariya ba wanda ya Lura
Hajiya ta kalli mallam kafin tace"Mallan kayi hakuri don Allah..Tace Sharrin shedan ne ayi mata uzuri..!
Kema Amarya ki gyara wlh bazan Boye miki ba kimarki ta Zube awajena tunda naji kina daga Cikin masu Bin malaman karyan nan ammh Tunda kin bata Hakuri ya wuce..Mallam kai ma kamata Hakuri..!mallan cikin bacin rai yace"Bani zata bama Hakuri ba Uwani gatanan baiwar Allah da ta zargeta tana zaman zamanta zata bama Hakuri in kuma wlh bata yafe mata ba sai Allah ya kamata !
Yafada cikin nuna bacin ransa lokaci Daya yana Kauda kai baya son kallon Anty Amarya
Hajiya ta juya tana kallon Anty Amarya tun kafin ma tayi mgana ta Zube gaban Uwani tana Fadin"Kiyi..hakuri sharrin shedan ne ki yafemin..!
Haj.Uwani ta share Hawayenta kafin tace"Shikensn tunda Hajiya da mallam sun saka baki..Ammh wlh da naso ne sai na kai mganar nan gaba..Ammh Tunda kin bada Hakuri ya wuce sai ki kiyaye ki daina yarda da mganar makaryatan malama nan makiya Allah da addininsa..!
Hajiya tace"Tabbas Allah ya Karemu gabadaya..!
Haj.Uwani ta amsa da Ameen da karfi mallam ya mike yana Fadin"Sannan mgana ta karshe bayan mu Hudun nan kada naji wannan mganar abakin wani..Na kasheta Daga yau..!
Daga haka ko mgana bai kara ba ya shige ciki bakincikinsa Daya yana tafe wa"azi akan mata masu Bin malamai ammh yau agidansa ma ake yi wannan aikin..?
Tayaya ransa bazai baci ba..?
Hajiya kuwa sai da ta kara yima Anty Amarya Nasiha sosai da nuna mata illah rashin yarda da Allah da kaddaran da Illah barin Shedan ya saka mutum wasi wasi da kuma illar Bin malaman karya na Tsubbu.
Sannan ta sallame su Anty Amarya ta Mike kamar tana kan kaya ta Fice Haj.Uwani sai daga baya ta fito Hajiya kuma ta bi mallam ciki ta Rarrasosa..!
Haj Uwani har takai shashenta tana Dariya Allah Allah take yi ta Kira Batula ta labatar mata abunda ya faru yau sai ta Kira ta bata Dauka ba Shiyasa ta bari sai an juma ta Sake nemanta kan kujera ta kame a falonta ta Dora kafa Daya kan Daya tana Mirmishin jin Dadi da Nishadi ko banza yau ta bama Marliya Daya daga Cikin Tsoronta..!
Anty Amarya kuwa haka ta shiga Shashenta bata gani tana jin Sakina da Sa"adatu na kiran sunanta da suke
Falo bata bi ta kansu ba ta shiga Daki ta Bame kofa da key jikinta na Rawa da Hannunta ta Dauki wayarta Dake kan madubi ta Dokama Balaraba kira.

Mamanmu na cikin bedroom dinta bata Dade da tashi daga barci ba tayi sallah tana Zaune tana Tunanin irin girkin da zata Tsarama Aba da Daddaran nan Tunaninta ba kowa agidan Jawaad na Haraban gida yana Kwallo Su Hamida basa nan suna gidan mallam Domin bata Dauka Amina bata bisu ba dataji Fitansu ta Dauka gabadaya suka fita..shiyasa bata Damu data leka Dakin su Aminar ba da ba kowa acikinsa yanzu sannan Dazu da ta fita alwala taga kofar Dakin a Sakaye abunda bata sani ba Iska ne ta Dan Tura kofar Dakin Amina na ciki tana barci.
Wayarta Dake gefenta ne ya katse mata tunani ita azaton ta Aba ne Domin yanzu ko yana wajen aiki haka suke cikin waya yana tambayanta ko ba wata matsala sai taga Madina ne ke kiran Wani katon Tsaki ta saki kafin tace"Kai madina bazata barni na Huta ba..ya kamata ta Hakura tunda ita dai kamar bata da sa"a ne..matsaww...!

Sai da ta Daidaita kanta sannan ta Daga Kiran tana fadin lafiya"Madina Allah yasa lafiya kira da bayan la"asar haka..?
Anty Amarya cikin kuka tace"Dayyaba mun kade mun gama yawo..Ashe duk abunda muke ciki siirinmu yana Bankadane bamu sani ba..Tabbas muna Shuka a idon makwarwa Dayyaba. !
Mamanmu ta ce cikin mamaki"Bangane ba madina..?
Waye yasan sirrinmu..?
Anty Amarya tace"Hajiya UWANI 'ce Dayyaba..A tsirara take kallonmu Duka Sirrukanmu dani Dake yana Tafin Hannunta ne. !
Mamanmu ta mike Dafe da Kirji Tana Fadin"Mun shiga uku Madina wani irin labari kike son ki Fadamin..?
Anty Amarya ta share hawayenta tana Fadin"Ai bama uku muka shiga ba goma ne Dayyaba..!
Nan ta fara gayamata komai da komai Tunda daga farko da zuwar da tayi ta Samu Haj Uwami da yadda suka kare da Sharrin data kulla mata ta karishe da Fadin" Kinga yadda take kuka afalon mallam kyce ta Allah ce Dayyaba..Wlh Uwani ta shirya yin Fito na fito damu kuma in muka yi wasa..Tana gabda Kware mana Zani a Tsakiyar kasuwa..!
Mamanmu ta Mike Cikin wata irin Murya tace"Karya take yi madina..Uwani bata isa ba..In juranta Sammako mu mun Dade atafe..Bata isa ta zo ta lalatamana Aikin da mukayi wahala mukayi shekaru muna Wahala ba Haba Madina Hajiya Uwani muguwar matace bata da mutunci kuma bata da imani Tsakani ga Allah yadda Hajiya ta yarda da ita sai da ta Cutar da ita..?
Sannan ina laifin in ta Hana Amina Haihuwa ko zama da Umar daman haka muke so auran yadda yake gantale ya kare a gantale itama wannan Balarabiyar ai in ta Hanata Haihuwa mu taimakon mu tayi ammh Sai ta Hado da Sakina..?
Tasan shekara nawa kika kwashe kina Wahala kan Sakina ta Samu Ciki ta Haihuwa ta zama Mowar mata agidan Umar..?
Ko kuwa tasan Shekara nawa ni na bata ina Zaune da Fuskar balaraba Domun cikar Burina..?
Shekaru fin Talatin ina Kun san bakin Cikin Sa"idu da Matarsa YAYA shekaru talatin na kwaahe ina Bautama ya"yanta shekaru masu yawa na kwashe ina nuna ina son yarinyar nan Amina har saki sai da Tsinnanniyar tajamin sai acikin wannan shekarar ne na samu yadda nake so shima bayan kasa ta Shafe idon yaya..To bata isa ba ki Fadamata bata isa ba..Bazamu bari ta Rusa mana Shekarun da muka kwaashe muna Wahala na Samu Sa"idu Dakyar Madina saboda haka fa na Hada kai Dake domin cikar Burina ke kina komai Saboda Sakina ni kuma inayin komai saboda Sa"idu ne ko JAFAR daya so ya nuna taurin kansa nayi mganinsa yanzu..Duk da abaya ba AMINA NASO ta kangare ba..Ba ita naso ta zama mara kunya ba..Ba ita naso ta koma haka ba Jafar naso ya koma haka ammh duk da Haka ban Sare ba Madina lamarina ba ja da baya kuma ba Faduwa ballatana Na karaya kema bai kamata ki karaya ba Madina..!
Ta karishe Cikin Hargagin ta na Daukan ita kadai ce agidan idonta ya Rufe bataji bata gani.

Amina dake Tsaye Tsakiyar Falon Mamanmu sai da ta rike bango Sakamakon wani wawan jiri Daya kwasheta jin kalaman dake fitowa daga bakin mamammu wanda suke mata amsa kuwa acikin kunnuwanta tana Fatan yasa abunda taji ba gaskiya bane ba Mamanmu bace ke wannan mganar ba.
Tasowarta Daga barci kenan ta fito tayi alwala ta Duba Bayinsu na Daki ba Ruwa sai taji kanar mgana Daga Dakin mamamu sama sama yasa ta fasa yin wajen famfo ta shigo Dakin da niyar kiran sunan mamanmu sai dai mganar data ji ne yasa ta tsaya sanda Taji kalaman mamanmu da suka kusa saka Zuciyarta ta Buga.
Bata gama Dawowa daidai ba ta Sake jin muryan mamamu Cikin Fusata tana Fadin.

"Ita din banza Madina da zata Tsorataki. me akayi akayi HAJIYA UWA..? Muka kauda YAYA har Lahira ballatana ita..? Karki manta Saboda Cikar Burina kika taimakamin muka saka Malam ya Kara mata gudu zuwa Lahira.kamar yadda nake kokarin taimaka miki auran AMINA DA UMAR ya kare ahakan sannan bazata taba Zama wata mai Daraja awajensa ba Sakina ce kadai zata haifasama D'a jikan mallam da Hajiya..Saboda haka ki kwantar da Hankalinki Rai fa ba abakin komai yake ba wajen Biyan Bukata AMARYA..!

kai Amina ta Dafe saboda ya Fara juyamata Hannunta Duka Biyu ta saka ta Toshe kunnuuwanta Lokaci Daya tana girgiza kanta Hawayen da suka fito mata suka fara ambaliya saman Fuskarta kamar an Bude famfo..!








*Janafty*

*TFZB2014*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*

To mu kawar da ita nace madina tunda zata kawo mana matsala mana..Nafa fada miki tun abaya wajen biyan bukata rai ba abakin komai yake ba ke kika kara tunatar dani hakan madina Lokacin da kikace mu Kawar da YAYA naki baki Dama ina ganin kamar a lokacin bai kamata ta mutu ba naso ne sai na kunsa mata kwatan kwacin bakincikin da ta kunsamin amamh da kika nuna min mutuwarta itace masalaha bagashi tatafi ta barmin Sa"idun ba kuma sai da ta kauce na samu abunda nake so to kamar hakane in dai Hajiya uwani zata zame miki matsala wajen cikar naki Burin Madina mu kawar da ita kawai..!

Amina Tsabar Rudin data ke ciki yasa kafafunta suka kasa Daukanta bata san sanda ta sulale ta zube saman Cafet din dakin mamanmu Lokaci daya tana Saka Hannuwanta duka biyu ta toshe Bakinta saboda kuka ne ke son kwace mata ba taredata sani ba.

Mamammu fa..?mamanmu Innalillahi wa"inna ilaihirraju"un ita ke fadi da bakinta ta kashe Yaya ta kashe yaya wannan mganar amsa kuwwa take mata sannan mganganun sun Haifar mata da juyawar kan data kasa gane wani yanayi take ciki abu daya ta sani Taji abunda Tunda take bata taba jin makancin sa ba taji abunda Hasashe ko zato ko Tsammani bata ba Zato zata jisa Daga Bakin data aminta dashi ba.

Rarrafawa tayi kamar mai koyon Zama saboda ta kasa tashi ta Dage labulen Dakin mamammu na ciki ta gefe kadan so take ta Tabbatar da abunda taji domin gani take yi kamar ba Mamanmu din bace mai irin Muryanta ne sai gashi taga Fuskar mamanmu cikin yanayin da bata taba ganinta ba Tana Tsaye tana waya ta cigaba da mgana cikin Zaro ido tana Fadin"to maza ki kira mallam..Ayi mana mganinta mu koma gefe muna Cin Duniyarmu da tsinke a Matsayin Dayyaba da Madina chan gefe kuma muna Cigaba da yaudaran mutane da Salihan Fuskokin mu na Balaraba da Marliya..!
Bata tsaya ma ta gama ji ba ta juya Cikin Rarrafen har ta fice Daga Falon batare da tayi wani motsi ba Hawaye kuwa kamar an bude Famfo haka wasu ke fita wasu na kara Bulbulowa Idanuwan mamanmu ya rufe shiyasa kwata kwata bata ji wata alaman akwai wani acikin gidan ba.
Amina na fitowa Tsakar gida tayi tayi tatashi sai ta kasa Domin gabadaya jikinta ya Saki Lokaci Daya ta kasa gasgasta abunda taji kuma ta gani Mamanmu kadai kanta ke iya fadi da sunan yaya Anty Amarya bata wani bata mamaki ba jin sunanta Daman ita Tuni Tasan Halinta ammh acikin wannan yanayin ace Mamanmu ce ke da Alhakin Duka abubuwan da suke Faruwa ta yaya zuciya zata iya Daukan wannan Gaskiyan..?
Dakyar ta iya mikewa sai da ta rike Karfen barandan su sannan gabadaya kanta juyamata yake Bata gani Dakyau wani irin Biji Biji take gani Allah ya taimaketa taga Hijabin Haddar Hamida kan igiya data wanke ta Taka Sannu sannu tana Nunfashi Sama sama ta Daukosa ta sakasa ko Takalmi babu a kafarta haka ta Fice Daga gidan Cikin wani yanayi duk Takun da Zatayi sai kalaman mamanmu sun mata amsa kuwwa acikin kunnuwanta Daki Daki Dayasa Cikinta ya Cure waje Daya Dakyar take iya taka kafarta a Haraban gidan taga Jawaad yana kwallo yana ganinta ya nufeta yana Kiran sunanta sai kawai Amina ta kallesa ta kara kallonsa Tabbas sai Allah ya Tsine ma balaraba ko da Hakkin Jawaad aka barta sai Rayuwarta ta D'aida'ice Rumgumesa kawai tana so ta Fashe da kuka ammh ta kasa acikin Kirjinta take jin wani zafi kamar zata mutu batare da tamai mgana ba taja Hannunsa suka fice domin gabadaya gidan ne yayi mata wani zafin Datake jinsa har acikin jikinta suna tafe yana Fadin"Ya Amina ina Takalmin ki. ?
A islamiya an ce mana ba kyau tafiya ba Takalmi..!
Bata ma Sauraransa ita dai kawai Jefa kafa take yi Allah ne ya kaita Falon Hajiya ba Domin tana ganin Hanya Dakyau ba suna shigowa Hamida da Hanne suka Dago suna kallonta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login