Showing 243001 words to 246000 words out of 265571 words

Chapter 82 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28907

Jadwa sun koma Shashen Hajiya Babba.
Hajiya uwani kuwa abakin Umaima sukaji bata agidan itama taje shashen taga ba kowa Ya Nazifa ke ta kula da kanwar nata ya uzairu ya koma inda yake Service ana gama Daurin aure Ko Tsayawa bai yi ba,Nazeem kuma nan da Sati Daya zai tafi Lagos ya Fara aiki sun yi mgana da Nazifa zata roki Mallan ya bata Umaima tatafi da ita Domin suna da Tabbacin zamam Mahaifiyarsu agidan mallam yazo karshe Duk da sai Dare ne mallam yazo da Labarin rasuwar Batula shima wani Cikin yayyin su Batula ya kirasa yake fadamai sai Lokacin ma kowa yasan bata agidan.
Ba wanda ma ya Damu ana ta Hada Hadar raka Amina Sabon gidanta Hajiya ta kasa zama su ya Abida sun tafi tun Mangariba suna gyara gidan suna Share kura da saka labulanya sannan Hajiya tasa Hadiza Amarya Aba ta dan ma Amina gyaran jiki Dayake Sana"arta ce sannan tazo da kayayyanki Tunda tayi ma su Hanne yan"uwanta sai tsiya suke mata suna cewa zata gyara yarta ita kuma tana jin kunya ba Zato ba Tsammani taji auran nan Daga sama har ta fara kuka Hajiya tace kul dinta ta Godema Allah Sa"idu mutun ne har da Rabi,Tun bayan Rasuwar mijinta bata kara marmarin aure ba, ta koma makaranta Tayi NCE sannan ta ke kuma Hadawa da Sana"ar gyaran jiki.
Sannan ita bazata ce ga Aba ba, Saboda ganinsa da tayi ba wani mai yawa bane ammh ai suna nan jiya abubuwan nan suka Faru marasa Dadi Hajiya ta mata fada tare da Rokonta ta rike auranta Hannu Bibbiyu.
To me zatace..? Sai Fatan Allah ya Zaunar dasu Lafiya sannan bata da matsala macece mai wayewa da sanin Duniya.,Yanzu kawun su Hajiya yace bazata koma ba nan da Sati daya zata Tare wajen Hajiya zata zauna abunda kuma ba"a rasa ba Hajiya da Mallam sun Dauke komai akan abunda ya shafi Sa"idu jikinsu har rawa yake yi Tabbacin kaunace daga Allah.
Shiyasa ko kafin ta gama yima Amina Dilkar da tayi mata sun Fara Sabawa Daman ita tana da Sakewa a manganunta Amina ta Fahimci Aba yayi Dacen mata suma kuma sun yi Dacen wata uwar
Har su ya jadwa sun shaida haka yadda ta gyare Amina ta sakata tayi wankan Turare Kora su ya Abida tayi waje suna ta mata Shakiyanci Hajiya tace ta korasu waje tayi aikinta Tana yi tana hada ma Amina da yan Shawarwarin rike miji ta bata wata Zuma ta sha saboda cikin jikinta tace bazata sha wani mgani ba sai ta Haihu Tun Amina najin kunya har ta fahimci ita Anty Hadiza ba ruwanta sai itama ta saki jiki tana Sauraranta.
Koda karfe takwas na Dare tayi Amina ta shirya Cikin Wata atamfa riga da Zani an Nadeta cikin Lafayan da Ya Aisha ta siya mata har kwalliya sai da Anty Hadiza mata aka fesheta da Turaren Humra masu kamshi Domin Hajiya tace da wuri za"a tafi kai Amina bata son Dare yayi.
Sai alokacin Sarood tasan Amina ce Amaryan Umar ya Aisha ta gayamata Cikin Larabci sai kallon Amina take yi da mamaki sannan ga Ciki ajikinta Ahalin Umar bai taba mata Zencen ba sannan ta Fahimci Sakina wani abu ya faru da ita duk da batajin Hausa ammh koken koken da akayi tayi jiya bana Lafiya bane..
Kamar wanchan karon an kai Amina Falon mallam ya saka mata albarka Daganan Idi ya Dauki Hajiya da Amina sai Yakaka da Haj Nasara..Sauran su ya Aisha kuma suka Bi sauran motocin su ya Nasir har da ya Nazeem ya Kai mutane a Motar makarantar su Amina.
Su ya zulahait suna baya baya Hajiya tace bai kamata ba su wuce su raka kanwarsu dole suka shige suma anayi dasu.
Sune har Babura inda gidan Amina yake Kowa yaje yaga gida sai santi da son barka su ya Abida sun gyare ko"ina sai tashin kamshi Sannan ga wutar nepa haske ya gauraye gidan akwatinta Daya Ya Aisha ta Daukomata Sauran kayan sai gobe Hajiya tace zata za"a kawo mata..
Hajiya da kanta ta shiga da Amina gidanta bayan tace tayi addu"a har kan gadon auranta sannan ta Dafa kanta ta Saka mata albarka
Matan kuma suna ta Zagayen gidan suna Santi Su jidda har da Sadiya duk sun zo ganin gida harta Sarood tazo aranta kawai ta Sadakar Umar na son Amaryan nan tasa tundaga abubuwan ma da suka Faru.
Su ya Zulaihat suna sharan kwallah suna saka albarka Da wuri Hajiya tace suyi Haraman tafiya haka Amina ta rumgume yan"uwanta tana kuka bata bambamce su ba Har ta su ya Zulaihat Saboda su Daya suka Dauki juna aka suka Taru suna faman lallashinta sai da tayi shuru sannan suka fara Shirin Tafiya Tun dazu su hanne suka kira amare dukkansu sun isa gidajensu Lafiya sai fatan Allah ya bada Zaman Lafiya.
Kafin karfe Tara na Dare duk sun watse an maida su gida sai Amina kadai aka bari tsoro ta fara ji gashi ba megadi bai riga ya Daukesa ba Sai misalin karfe goma na Saura na Dare Taji shigowar mota Daman ta kasa Zaman ciki tana Falon ta kasa Zama waje Daya duk Haduwar gidan tsoro bai barta ta wani Dubasa Dakyau ba
Danmallam na shigowa falon da Amina ya fara cin karo Daman yasan Za"a rina Amina ce fa sarkin Tsoro rike da ledan kaza da madara ta fadamai ta rumgumesa tana mai kukan shagwaba ya barta ita kadai tana jij tsoro.
Yana shafa bayanta da Hannu Daya Lokaci Daya yana shakan kamshin Turarenta yace"Shii..Ba shikenan ba gani na shigo ba..Ni dai yau ataimaka kada kukan nan naki ya hanani Shagali..!
Tana jinsa sai ta kara kamkamesa Shima yana rike da ita har suka zauna Saman Kujera ya Dora ta ita da Cikin Saman jikinsa bayan ya Sauke Lodojin Kasan Cafet harshensa ya sa yana Lashe mata hawayenta Lokaci Daya yana Fadin"Noor nidai kimin kudin wannan kukan naki na siyesa na kwana Biyar..Lokacin na gama Shagalina sai ki dawo da kukanki..!
Yafada cikin Shagwaba yana kwaikwayon muryanta Dariya ta saka ta Fara Dukansa da Hannunta a kirji Tana fadin"Hubby..La..la..!
Dariya shima yake ya rumgumeta yana Shafa Cikin jikinta Lokaci Daya yana Fadin"Eh Noor..Kinsan ai nayi kokari ko..?
Kiyi hakuri yau kam bazan iya Hakuri ba..!
Yana fada yana Shafa wuyanta Lokaci Daya yana shakan kamshin Turarenta dake jikinta Sama sama taji yana Fadin"Noor..!
Chan kasan makoshi tace"Uhmm!
Cikin wata kasalalliyar murya yace"Ya sunan wannan Turaran..?
Itama cikin wani yanayi yace"Bansani ba..Anyy Hadiza ta sakamin..!
Kai Tsaye yace"Wacece haka..?
Kanta na nutsewa saman kirjinsa tace"Amaryan Aba..!
Yar dariya yayi ya kamkameta yana Fadin"Ina yinta sosai..kamar tasan ina bala"in son kamshi..Barin ma irin wannan..!
Daganan bai Tsaya ba ya shiga wata Duniya Har Lafayan shi ya warware yana Shagalinta itama saita Dafe shi Tana taimaka mai domin bata juya ma wannan al"amarin baya ba.
Ganin zai shiga wani duniyar yasa ya Sarara mata duk tayi laushi yasa bai Takura mata ba,ya je kitchen da kansa ya Samo Filet da kofi yazo ya juye Zabbin Daya Siyo yana Fadin"Na Biya bashi kazan amarci..!
Tana daga kwance tace"Biyan bashi kazan amarci Amarya da Tsohon Ciki..!
Dariya ya Fashe da Shi yana Fadin"Ke bana son jidali..Kinsan dai Cikin maza sai an tona za"a samu mai kokarina ko..?
Tana Dariya tace"Sosai ma Hubby..!
Mirmishi yake mata yana jinsa cikin wani yanayi.
Shi ya taimaka mata ta tashi zaune haka ya tasata yana bata abaki itama tana bashi Sun kusa cinyewa ta kalli Kazan tana Fadin"Kazan amarci ai kanka ka siyo mawa ko..?
Yana Dariya yace"Naki ne..Na zata kin sam min ne fa..!
Cinya ta Dauko ta Turamai abaki Tana Fadin"Ai tunda kaci kazar amarcin Amarya sai ka famshe mata..!
Cikin Farinciki yace"Da gaske Noor..!?
Yafada yana rike hannunta kunya ya kamata ta Dukar da kanta kawai sai ya Saketa ya Cika mata Kofi da madara ya bata tasha shima ya Cika ya sha bai Tsaya ma wasa ba ya Dauketa ita da Cikin sai Bedroom din su acikin Tiolet ya Sauketa yace su yi alwala shi ya taimaka mata tayi alwalan sannan shima yayi nashi suka Fito shi ya jasu Sallah raka"a Hudu sannan sukayi ma auransu da Zuru"arsu Addu"a.
Jikin ya Danmallam har rawa yake yi shi ya Raba Amina da kayan jikinta duka bayan shima ya raba nasa da Jikinsa ya kamkameta suna Sharing din Body Cantact sannan suna jin Bugun zuciyar juna
Cikin hankali ya fara Sarrafata Amina bata bari kunya ya Cutar da ita ba ta tallafesa tana taimakamai sai da Tafiya ta mika ne ta fara mai kukan shagwaba shi kuma ya mika bazai iya komawa baya ba sai kawai ya Tallafeta Sosai yadda Cikin jikinta bazai basa matsala ba
Cikin karyewan Sauti yace"Noor..Ahankali fa zan yi..Kadan kadan..!
Yake fada mata yana tusa kansa a wuyanta Amina tace"Hubby..Shi..Da Zafiiii...!
Fadi kawai yake"Noor a hankali zan yi na rantse miki da Allah..!
Daga gani baya cikin Hayyacinsa ba wani Zafi Amina take ji ba,kawai Kukan Shagwaba take jin Dadin mai Duk sai ya karamai karfin gwiwa.
Ya Dauki Lokaci mai Tsawo tare da Amina lokacin da bai taba Samu ba Shudewar Mintina Talatin da biyar sannan dukkansu suka samu natsuwa da juna haka ya kamkameta yana Fadin"Allah yayi miki albarka Noor..!
Yadda kika farantamin Allah ya farantamiki..!
Tana kwance saman kirjinsa yace"Ameen Ameem Hubby..Ana Behabbak..
Yana kamkame da ita yace"Ana bihabbeki Khatheran..!
Haka suka kwana cikin Farinciki da Asuba bayan sunyi sallah suka koma Amina tayi Dauriya sosai wajen mijinta shima yasani yana ta saka mata albarka.
Sai wajen goma sukayi wanka suka Sauya kaya Hajiya ta aiko Idi Direba da abinci da akwatun Amina Duka suka kwasa zuwa Cikin gida.
Wuni sukayi suna cin amarcinsu Amina tabara kala kala take masa yana Biye mata Da rana ma Daga gidan mallam aka aiko musu da abinci da Daddare ma haka.
Har sai da akayi kwana Biyu sannan ya Fita ya yi musu Cafane shi ke taya Amina Girki abunda bai taba yima Sakina ko Sarood ba..Bai taba Zaton Amina ta iya abubuwa haka ba bangaran Girki da bangaran kwanciya da miji ta kwancemai kai har mamaki ma take bashi wlh ga Ciki ammh bata taba nuna mai Raki ba.
Saka albarka kuwa ta shashi har ta gode Allah Shiyasa take nuna juriyanta akan komai ganin yadda yake Lalacewa akanta.
Su Hanne sun kirata da wayoyinsu da Hamida suka fara waya sai daga Baya Aminun ya siya ma Hanne waya tana Yola ita da Nenne suna zamansu Lafiya sai Hankalin Amina ya kwanta.
Bangaran gidan mallam kuwa Baki na nesa da na kusa sun koma gidajensu Dakin Hajiya Daga Anty Hadiza sai Yakaka da tace sai Amina ta Haihu zata koma.
Bangaran Aba kuwa baya kwana agidansa gidan gona yake kwana Jawaad kuma yana wajen Hajiya Mamanmu kuma ita kadai agida kamar mayya tayi kukan har ta gaji Ta rame ta lalace sannan ga Fama da Mutuwar jiki da kasala tunda akace Aba yayi aure zuciyarta ke zafi.
Anty Amarya ma kamar mujiya bata ko Fitowa,Chan duste labari duk ya bazasu kowa yasan abunda ta aikata shi dai mallam ya zura mata ido bai ce mata komai ba ballatana tasan mafitanta
Sannan duka ya"yanta ba wanda ya kara bi ta kanta har Sabeeha na wajen Hajiya sai jefi jefi take ganinta Turakan mallam kuma Daga Hajiya sai Haj.Nasara
Bangaran Hajiya uwa tana chan gidansu Cikin wani irin Hali Duk da ba wanda yasan abunda ya faru sun fara Zargin akwai wani abu saboda mallam bai zo ba ballatana ya"yanta ko Hajiya ma batazo ba ahalin in Lafiya lau Tare da Hajiya zata zo haka aka watse bakwai din Batula da tata ta kare Aka bar Uwani ita kadai Tana Faman da Bugun zuciya mutuwar Batula ya kara Raunanata Gata nan kawai ammh ita kadai Tasan Halin Data ke Ciki kuka tayi shi kamar Idonta zai Tsiyaye Kiran wayan su Nazeem kam har tagaji basa Dauka Shamsu ne ma ya taba Dauka yace kada ta kara kiransa Nazifa kuma Blooking dinta ma tayi,bata da karfin gwiwan komawa Gumel domin tasan zamanta achan ya Kare.
Rayuwa ta juya musu baya alokacin da basu zata ba,.
Sati Daya na Cika Anty Hadiza ta tare adakin Yaya,sai abunda ba"a rasa ba Hajiya ta kara mata sannan Aba yayi mata akwati Biyu na lefe su Yakaka ne gaba gaba yan raka Amarya ita da Haj.Nasara.
Aranar da Daddare Danmallan suka zo shi da Amina data matsa sai ya kawota taga Hajiya da Aba da Mallam,sai da suka zo sannan Hankalinta ya kwanta Shashen Hajiya ya barta yaje shashen Hajiya nasara ya ga Sarood Tunda tana wajenta yace ta koma gidansu na kofar arewa tace ya barta anan tasan ba wani Damuwa da ita zai yi ba yana da amarya Shi ko ba haka bane gani yayi ba yanzu zasu koma ba Sai nan da wata Biyu gwara ta koma gidanta zai fi in ya gama kwanakin sa wajen Amina sai ya koma mata ammh sai ta nuna bata so..!
Sai kawai ya kyleta ganin kishi take shi ko aransa ma tunani yake sarood bata iya kishi ba ai kishi na wajen Aminaa Jidali.
Shi tunda abun nan ya faru bai kara neman sakina ba,shi abakin ma Hajiya yaji Yan"uwanta sun maida ta Dutse daganan bai kara bi ta kan mganarta ba sai da komai ya bayyana sannan ya Fahimci bai taba Son Sakina ba komai ya kare acikin Ransa kwata kwata shi dai bai ma tsaya ya yanke wani hukunci akanta ba sai dai bata acikin Ransa kwata kwata.
Basu koma ba sai Sha Dayan Dare Har gidan Aba suka je,Mamammu ta window take lekonsu tana Kuka kukan Nadama da Bakinciki.
Amina Bakinta yaki rufuwa ganin Anty Hadiza Dakin Aba ta rumgumeta tana murna sosai itama ta riketa cikin Farimciki jawaad tana murna ya samu mama.
Haka kowa ke shigowa yana fita bawanda ya Damu da wata mamanmu mamakin karfin Halinta ma Aba ke gani data ke cikin gidan bata kara gaba ba.
Agaban idonta ya shigo gidan da Ledoji a hannunsa ga shi yaci Farar Shadda yayi kyau rabonta data gansa tun Ranar da komai ya bayyana..!
Agaban idonta Sa"idu ya Shige Dakin Yaya da wata mace suka Sakayo kofa sai taji jiri na Dibanta ta Daga kafa kenan Jirin ya yarfar da ita faduwar da zai yi Sanadiyar shanyewar? barin jikinta Guda Daya..!






*Janafty*

*TFZB2029*


*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*


Wajen kwana Biyar Aba yana cin Amarcinsa hankalinsa kwance ya samu natsuwa da Anty Hadiza fiye da yadda ya Tsammanin samunta.
Bai taba zaton balaraba tana cikin gidan nan ba, bata kara gaba ba,saboda Dakinta yana rufe ne sannan bata fitowa yayi zaton tayi ma kanta Hisabi ne ta kara gaba Acikin ransa kuma wannan kuncin da bakinciki da Tsanar Balaraba baya jin zasu sake shi nan kusa yana jin har duniya ta Nade bazai iya Yafe mata ba.
To shi kanshi baisan tana cikin gidan ba,ballatana Anty Hadiza da bata Dade agidan ba,Sai ranar kwana na shida ne Wari ya rika fitowa Daga Dakin da Kakarin mutum kamar zai yi Amai Lokacin Aba ya fita gidan Gona Anty Hadiza ke tsakar gida tana Shara taji wannan abun sai hankalinta ya tashi ta tsorata sai dai bata bar kiran sunan Allah ba Mayafinta ta Dauka ta je gidan mallam Shashen Hajiya ta gayamata abunda ke faruwa ita kuma Hajiya ta Sako Hijabi ta Biyo bayanta.
Koda suka zo Dakin yana rufe ne ta Ciki ba yadda zasu yi su shiga sai an balle kofar sannan Hajiya tana da Tabbacin Balaraba na ciki Saboda ai ita tayi waya da yan gusai a manganganunsu bai nuna balaraba ta koma chan ba sannan tana da yakinin kunya da Nadama ne suka sakata ta kasa fitowa kamar yadda ya Kanannaye Marliya itama ko Kamshinta bamai ji itace ma Sarkin Tsausayi take umartan su Lami da in sun gama girki su shigar mata dashi Cikin Shashenta kada yunwa ta mata Illah.
Hajiya mallam ta kira awaya bai yi nisa ba yana makarantar Haddar su Amina suna taro yace ga shi nan zuwa Daganan sai ta kira Aba tace ya Dawo gida shi har ya rude ya zata ko wani abu ne ya faru da Hadizar shiyasa yazo Hankalinsa tashe ko kafin ya kariso Mallam har ya dawo sannan ga Jafar ga Nasir su suka kira mai Balla kofa kafinta yazo ya Balle kofar Gabadayansu sai da suka toshe Hanci suka samu shiga Dakin Halin da suka Iske Mamanmu aciki Dole bawa ya kara Tsoron duniya..
Tana kwance a kasa inda ta Fadi Jiki ya jirkice Baki ya karkace Anan tayi kashi da Fitsari bazata iya tsshi ba Idanuwanta sun kafe saboda kuka sannan ta galabaita da yunwa da kishi Tana ganin Hasken rana ya shigo ta Fara laluban inda zata Hango mutane sai idonta ya koma yana ganin Duru Duru bakinta ya bushe ba"a kajin me take fada sai mgana take yi ba wanda ya Fahimta ashe ruwa take fadin a bata Anty Hadiza ce ta karkata kunnenta har taji abunda take fadi ta Ruga Kitchen ta Dauko ruwa Tsausayinta har ya kamata Idanuwanta ya ciko da Hawaye ta kasa ma Daga kanta ita kadai kuma ba wanda ya taimaka mata hakanan ta Zuba mata ruwan wani ya shiga Bakinta wani kuma ya Zube a kasa.
Hajiya ta kalli mamanmu ta kara kallanta kawai sai ta gyada kai ta Girgiza kafin tace"In bawa bai ji Tsoron wannan rayuwar ba yayi asara..Allah ka Tsare mana Imaninmu..!
Aba ko na tsaye yana kallonta aransa yana jin Dadi samnan yana mata Fatan abunda zata gani sai ya fi haka Ya Jafar ko nadaga bakin kofa bai ma kariso ba domin in akwai Hallitar Daya Tsana to ya ga mamanmu ne yanzu nan komai zai Dawo mai acikin kansa Nasir ne ke gefen Aba Mallam kuma Duke yake gaban Mamanmu ya kasa mgana Acikin ransa kuma Kabbara da Kirari yake ma Allah yana Tunanin yaushe bawa zai gane cewa Duniya ba matattaba ne. ?
Yaushe zamu san cewa rayuwar nan tana cike da tashin Hankali ne..?
Kai ya girgiza kafin yace"Innalillahi Wa"inna ilaihirraju"un..!
Haka kawai yake fada Aba kuma kawai sai ya juya baya zai fice Daga Dakin Mallam ya Daga kai ya kallesa kafin ya kira sunansa shiyasa ya Tsaya kafin ya Juyo yana kallon Mallam din.
Mallam ya mike yana Fadin"Ina zakaje..?
Baka ga Matarka cikin wani mawuyacin Hali bane..?
Kallon Baba mallam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login