Showing 3001 words to 6000 words out of 265571 words

Chapter 2 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28917

zatayi Duka ba,Duk da Rashin jin Amina yarinyace mai Shiga rai sannan Kaunar junansu ajininsu yake koyaya wni abu ya samu Daya Dukkansu sai sun ji wani iri.
Amina na musu rashin kunya kunkuni da Sauransu suna zugawa in za"a Daketa ammh akazo ana Dukanta sun Rika bada Hakuri kenan Hamida mai Saurin kuka Harda kuka take sai an gama Dukan tazo tana Daga Aminan sai ta Kalleta tayi Dariyan dauriya da yaki da Abunda take ji tace"Wai Kuka kike Hamida..?kuka fa..Kima Daina kuka Amina ce Aminene ce badai mutum ba sai ta Allah..!
Hamida na sharan kwallah takan Dungure mata kai tana Fadin"To kidaina wasu abubuwan don Allah Amina..Ba domin kowa ba domin Aba da kuma yadda muka zama Zuru"ar gidan bazanga..!
Amina alokacin sai dai ta kalleta tana Fadin"A"ah fa..Ni bansan laifin da ake yawan Fadin Amina nayi ba. abunda dai nasani shine Amina..AMINA SA"IDU Haka Allah yayita..Ko ta Sauya shi Hali ai zanen Dutse komai zai Sauya da Mutum banda Halinsa..!
Yaya ce ta katse ma Hamida Tunaninta Cikin Fitan Bacin rai da wani bakinciki Yaya ta Rufe Amina da Duka kota ko"ina tana Fadin
AMINA Yanzu abunda kika Zabama rayuwarki kenan..?So kike kamar yadda kika saka ma ABA dinku Hawan jini nima ki sakamin ko..?Gidan Uban wa kika je bayan an tashi makaranta..?Duka Sauran yan"uwanki sun gaji da nemanki sun dawo..Saboda ke kin FITA ZAKKA agidan nan sai abunda kika dama kike yi ko Amina..?Bin Maza kika fara..?Nace bin Maza kika fara..?Wlh ina Tsausayinki Ranar da Bakinciki zai kai Alhaji kasa Nima kin Sakani kuka ba sau daya ba sau Biyu ba, Amina ki kashemu ki Huta nace ki kashe mu ki huta..!
Amina bakinta bai yi Shuru ba Fadi take"Ni bana bin maza..Wlh Allah Amina bata bin maza ki yarda dani Yaya..!
Take fada tana Tsiyayan Hawaye,Hawayen da Dukan Yaya ne kadai da kalamanta kan saka aga Fitarsu daga Idanuwan Amina.
Bakinta ta Bike sai da ya fashe cikin Takaoci tace"Kina Kara batamin rai in ina mgana kina mgana..Amina Bakin ki na Daya Daga Cikin Nakasunki bakin ki baya iya mutuwa koda girman Laifinki yafi girman Duniya ne..!
Amina ta sharce jinin bakinta tana Fadin"Yi hakuri Yaya..!
Haka kawai take fada tana kuka sosai abu Daya yafi Tsaya mata arai Cewar da yaya tayi tana bin maza tasan Tana da kafar yawo da Bin Gidajen kawaye gayyar ko ba"a gayyaceta ba Amina sai taje tasan tana da rashin kunya da Kafiya da Taurin kai da Tsokana tasan bata da Kirki wani Lokaci ammh Wlh maza basa gabanta Tsakaninta dasu sai goge reni Domin har ayanzu Amina bata jin kunyar zagewa ta Chasa wanda yayi mata shiyasa kaf ajinsu na Boko da islamiya suke shakkarta bata Duba Jinsu ita wanda yace mata kole ne zatace mai cas ammh bata bin maza ita ba yar iska bace!
Gabadaya jikinsu Hamida yayi sanyi Amina na kuka tana Fadin"Kiyi hakuri yaya..!
Ita uwa Dabam take acikin Ranta tanajin kamar Amina ta koma Ruwan sanyi da Yaya zata Daina damuwa akanta Mamanmu zata Daina kuka akamta ammh ko ta Dauki alwashin abanza da ta gama Damuwarta za taji kamar kara mata wasu abubuwan akeyi wani Lokacin ita kanta Har mamakin irin Taurin zuciyarta take ko na wani kato albarka.
Dukkansu Hakuri suke bama Yaya batace komai sai kwallah Data ke sharewa Zeenatu ne ta Ruga Dakin Mamanmu ta taso ta wacce take kurya tadan kwanta Sama Sama taji Zeenatu na Fadin"Mamanmu..Mamanmu..!
Bude ido tayi tana Fadin"Zennatu meyasa kika tasheni..?nasan barcin yammah bai da dakyau..Kaina ke Saramin..!
Da sauri Zeenatu tace"Daman nasan baki ji ba.Yaya yau ranta ya baci gashi chan tana kuka tana Dukan Amina..!
Ai bata gama ba ta ingize Zeenatu ta Diro Daga kan gado Dankwali a Hannunta Zaninta na neman Faduwa ta Fice da gudu Zeenatu ta Bita da kallo ta Girgiza kai.
Tana fitowa ta isa ga Amina ta Rumgumeta tana ganinta ta riketa tana kuka take fadin"Mamanmu don Allah ki fadama Yaya bana bin maza Wlh ban bi maza gidan su yar Ajinmu naje Zainab isa kudina naje amsowa na iske sun yi tafiya ba kudi a hannunsa saina tako akafa mamanmu ammh kiji fa abunda yaya ke..!
Bata karisa ba ta Rufe mata baki Cikin Rauni tace"Basai kin fada ba..Nasanki Amineene..bazaki fara Halin da bana ki ba..
Share Hawayen Daina kuka matukar mamanki na Raye baki ba hawaye har Abada..!
Tafada tana share mata kwallah Cikin kauna Yaya kada kai tayi ta bi hanyar Dakinta tana Fadin"ki Rika samun waje acikin ranki kina fadama Amina gaskiya..Ko tana so ko bata so Ta fita zakka acikin gidan nan..!
Daga haka ta bankade labule ta shige Dakinta Mamanmu bata Damu ba mikewa tayi tana Dago Aminan Lokaci Daya tana Fadin"Hamida Dauki Jakar Amina ki kaimata Wajen Dirowarta..Ke Zeena zubo mata abincinta a filet ki hado mata da Ruwa da Zobo yanzu adakina..!
Zulaihat dake gabanta ta kallah kafin tace"Matsa ki bani waje..!
Zulaihat ta kalleta kafin tace"Mamanmu..!
Rai bace ta balla mata Harara tana Fadin"Ki yi wanke wanke..Gobe Aminan tayi..ku kuma kuyi abunda na sakaku..!
Daga haka ta shige Dakinta Dauke da Amina Dake kuka kamar ta maidata Ciki Hamida ta ja Jakar makarantar Amina zuwa Dakinsu Dirowansu kusa da juna ne Domin gadon su ma ahade yake ita tana Sama ne Amina na kasa saman gadonta ta ijiye mata ta Fice ta koma bakin Famfom ta Cigaba da wankinta ita kuma Zeenatu ta shiga Kitchen ta Bude Cooler ta Dibo Taliyar da Kifin Dake ciki ta Bude Fridge ta Dauko Ruwa da Zobo ta Fito zuwa Dakin Mamanmu.
Ita kuma Zulaihat ranta bace ta Fara Fito da kwanukan da aka bata akichen Zuwa bakin Famfo.
Hamida Dake Dauraye kayanta Tace"ki barshi Anty Zulaihat in na gama shanya zan wanke!
Kai tsaye tace"Yauwa.Daman duk Ranar da Amina ta kwaso jidalinta yafi Shafarki..!
Daga haka ta wuce Bata bi takan Hamidan Dake Dariya ba tana Fadin"Amina ce Anty Zulai..Wlh ko Aba baya iyawa da jidalinta ko Ya Jafar gajiya yake..!
Take fada tana Dariya shanyan kayanta tayi tazo ta fara Jika kwanukan sai ga Amina ta fito Daga dakin mamanmu kallonta tayi itama ta kalleta kai tsaye tace"Gobe da Safe har zuwa rana zan yi wanke wanke..Zan rama miki kada kice kin Dauki Jidalin Amina..!
Tafada tana Share bakinta Daya kumbura Hamida kai kawai ta kada Amina ce sai tayi mgana.
Ta fara wanke wanke sai gata tafito jikinta Riga ce doguwa na Atamfa sai Hular Dake kanta Kayan makarantarta ne ke Hannun ta Zata wanke saboda gobe Asabar suna Hadda Tun Safe sai yammah,haddar tasu daya take da islamiyan shiyasa ana tashi Uku da Rabi ayi sallah aci abinci a shiga islamiya itama Madaratul Umar Bin kallab din mallakin Baba mallam ce snnan gabadaya malaman makarantar ya"yansa ne da Dalibansa har ya jafar yana koyawar ajin manya Wato Jss1 da ajin matan aure ya Nasir da ya Uzairu da ya Nazim Duka suna koyarwa anan,Sai dai yanzu Ya Nazim da ya Uzairu suna Makarantar jami"a sai sun dawo Hutu suke zuwa Yaya shamsu ne shima Dukka da kananun shekarunsu Kansa na ja yayi Sauka da Hadda ga Sauran Littafai kai duk ya"yan mallam haka suke akwai kwanya kuma ance duk Kwanyarsu basu kai Babban DA'N MALAM ba dake jami"ar madina yana koyawar chan yake zaune da iyalansa sai karshen shekara suke zuwa gida sai dai Sakonsa akai akai yana zuwa ga mahaifansa.
Har ta fara wankinta ta gama bata cema Hamida komai ba itama batace mata ba Tana idar wa kenan tana Shanya Sallamarsu Ya Jafar da da Ya Nasir ta karade gidan da Sauri Amina ta juya tana kallonsu Fes suka Hada ido hudu da Ya Jafar wata uwar Harara ya Zuba mata yana fadin"Gama Shanya..Ki Tsaya a inda kike ki kama kunninki..!
Nasir Dake gefensa yace"in kin gama kama kunnin ki hada da Tsallon Kwado..Yau zaki gane iskancinki kadan ne Amina..!
Daga haka suka wuce lokacin suna amsa gaisuwan Hamida Jawaad dake bayansu ta kallah yana mata Gwalo yaro dan shekaru goma.!
Amina Rai ta bata a fili ta Furta.."Azzalumai Biyu kenan..Allah ya Hadasu abota kamar yadda Muguntarsu tazo Daya..!
Hamida ta kallah wacce ta zuba mata ido Hararanta tayi da karfi Tana Fadin"Bana son gulma Hamida..!
Kanta ta kauda tana Dariya gama Shanyar tayi ta koma bakin kofar gida ta Coge taki yin abunda akace sai taji motsi sai ta yi kamar ta Duka ta kama kunni sai taga basu bane sai ta Mike Dakin yaya suka fara shiga.
Tana chan tana Hararan Hamida suka Fito Da sauri ta Duka ta Daga hannunta Sama Jafar ya kalleta Cikin wani yanayi kafin yace"Kada kiyi..Kiga yadda zan yi dake agidan nan..!
Nasir kuwa wayarsa yake latsawa hannanunsa Daya Dauke da Littafan Karatu na addini Dakin mamanmu sukayi sallama suka shige Amina ta bisu da Harara afili ta Furta"Duka ai baya kisa..!












*Janafty*
*15/07/2022*

*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janaftyd'?*

*SADAUKARWA:ga Halima yusuf gwarzo (Besty) Alherin Allah ya kai miki a dukkan inda kike*

_Wannan Labarin Jinjina ce gareki *SUMAIYYA ABDULKADIR TAKORI*(Takorinmu) Allah ya raya miki zuru"a ya tabbatar da aminci da zaman Lafiya agidan auranki_

*
Hamida na wanke wankenta Ammh Rabin Hankalinta na kan Amina ganin yadda ta koma ta zauna Dirshan a kasa Tana wani cin mgani kamar babu abunda ma ya Dameta yadda take zaune kamar tana zaune acikin Daki ne cikin Natsuwarta.
Abu daya ke bama Hamida mamaki bama ita ba kowa da kowa Dake gidan nan yana mamakin yadda Amina bata jin tsoron Ya Jafar da Ya Nasir wadanda kaf gidajen sune manya kuma su ke hukunci da kuma Daidatuwar Tarbiyansu bama su ba na Sama dasu su ya Zeena suna Tsoronsu da basu girmansu banda Amina Har yau har gobe bata taba ganin Wannan Tsoron da Shakkarta acikin Idanuwanta ba.
Tagama wanke wanken kenan taji an fara kiran sallah Daga masallacin gidan Mallam Daidai da fitowar Zeena Daga Dakinsu kanta ba Dankwali sai akayi rashin Sa"a Lokacin Ya Jafar da Ya Nasir suka fito Daga Dakin Mamanmu tana Biye dasu abaya.
Bata da yadda zatayi sun riga sun ganta Ya Jafar ya Duka yana Saka Takalminsa mai igiya Hamida Ta kalli Amina Dake zaunenta tace cikin Rada..'Ke Amina ga su nan fa sun fito..!
Daga ido tayi ta kallesu kafin ta mike Tsugunne ta daga hannunta sama kamar gaske.
Ya Nasir ne ya kalli Zeena Dake kokarin komawa Daki Cikin Muryansa mai Cike da Iko yace"Wacece nan take yawo ba Dankwali..?
Ba yadda Zeena zatayi Dole ta juyo tana Fadin"Nice ina yini Ya Nasir..!
Harara yayi mata kafin yace"Dillah wuce ki saka Dankwalin ki..Kuna manya kuda su Hamida zasu yi ku musu Fada..!
Bata ko kara mgana ba ta shigo Dakinsu Daman Dakin Mamanmu zata shiga ta Dauko littafinta jiya ta manta Dashi,bata zata har alokacin basu tafi ba Shiyasa ta fito haka.
Tana Shiga Dakin Zulaihat data mike Tana Tatattara Littafanta tace"Kema kin samu Rabonki kenan..!
Zeena bata iya mgana ba Umh kawai tace ta Dauki Damkwalin Abaya ta saka lokaci Daya tana Tura kofar Bandakin Dake Daknsu ta shige Tare da Rufowa Zulaihat ta Bita da kallo Lokaci Daya.
Achan waje kuma Nasir ne ya kalli Hamida yana Fadin"wai sau nawa zan ce kudaina zama bakin Famfo nan da mangariba..?baku gujema Lafiyarku ko .?
Kanta na kasa tace"Ai nama gama yanzu zan tashi ina wanke wajen ne..!
Mamanmu ta kalleta tana Fadin"Wato Zulaihat ke ta bar ma aikin kenan..?gobe kuwa sai tayi shi..!
Tafada Daidai Lokacin Data hango Amina da Sauri tace"Amina wa ya sakaki kama kunni da mangariban nan...?
Jafar kai tsaye yace"Nine mamanmu..Zata fadamin inda ta Biya bayan an tashe su daga makaranta..!
Mamanmu ta Bude baki zatayi mgana ya Rigata da Fadin"Don Allah Mamanmu kada ki saka baki..Bazan Daketa ba in har ta bani amsar Tambayana..!
Mamanmu tace"Kada ku maida Amina Jaka mana..Jikinta fa ya Saba Da dukanku..!
Bai Saurareta ba ya Nufi Aminar Nasir ne ya tsaya yana Fadin"Wake ja Mamanmu..?yarinya Daya Tal zata zame ma kowa ciwon kai..!
Mamanmu tace"Sai addu"a..nidai kada ku tabamin D'iya..Nasan ku da Duka kamar kun Hada kauna..!
Yana jinta yar Dariya kawai yayi Hamida kam data gama kwashe komai ta maida Kitchen Dakin Yaya ta shige ta sameta Har ta Kabbarta Sallah Cikin kurya ta shige ta samu Jawaad na saka Jallabiya da Sauri yana Fadin"Ya Hamida Don Allah su Ya jafar na nan..?
Hararansa tayi kafin tace"Bansani ba..Sai ka fita kagani..!
Dariya yake yi kafin ya Fice ta bishi da kwafa tana Fadin"Zaka Dawo zakasan wanda kake ma Dariya..!
Daga haka ta shige Tiolet din Dake Cikin kuryan Dakin na Yaya.

Jafar gaban Amina ya Tsaya yana kallonta kamar yadda itama take kallonsa abun na bashi mamaki ba kowa ke iya Hada ido dashi ba Saboda kwarjininsa da yadda kannensa ke tsoronsa? ko Jadwa Datake Daga shi sai ita bai jin tana kallonso ido Cikin Ido.
Kai Tsaye Cikin Kakkausar Muryansa yace"Da aka tashe ku makaranta ina kika Tsaya..?ko nace ina kikaje..?
Amina kai tsaye tace"Gidan yar ajinmu Zainab isa..!
Da mamaki yace"Yaya ta aikeki ko mamanmu..?ko Aba..?
Itama Cikin dan mamakin ta Waro Idanuwanta kafin tace"Kudina naje amsowa..!
Tafada tana Dan Tura baki Hannu yasa ba tsammani ya bige bakin yana Fadin"Watarana sai na rabaki da Hakoranki na gaba..!
Nasir Dake bayansa yace"An fa Tada sallah Jafar..!
Jin haka yasa ya ja kunnenta Har sai da tayi kara Cikin Fada yace"Kije kiyi sallah ki jirani kafin na wuce zan dawo ban yarda da mganarki ba..!
Sannan ya saketa gefe ta koma tana Sosa kunnenta Nasir ma sai da ya bata Rankwashi mai Zafi sannan suka Fice Sai ga Jawaad ya Fito ya Bisu abaya da Gudu yana ma Amina gwalo,Tana Dafe da kanta Dataji zafin har Tsakar kanta tace"Yaro in na kama ka sai na Lahira yafi? ka jin Dadi..Na fika Jidali da Fitina..!
Tafada kafin ta mike tana Kakkabe Jikinta nan bakin famfon ta karisa ta Bude ta fara alwala sai da ta gama kana ta shige Dakin Mamanmu ta isketa kan Darduma tana Lazimi..!
Kai Tsaye Amina ta wuce uwar Dakinta tana Fadin"Mamanmu na Dauki Hijabinki Cikin Wardrope dinki..nawa suna Dakinmu kuma bana son shiga..!
Tafada Muryanta Cikin yar shagwaba Tana Daga zaunen kan Darduma ta Daga mata kai Ciki ta shige ta Bude makeken Wardrope din ta Bude barayin Gogaggun Hijaban Mamanmu ta Dauko guda Daya ta fito tana zuwa Mamanmu ta matsa gefen Darduman Datayi sallar duk da Shinfidadden Cafet din italiyan din Daya malalen Falon
Tana cikin Sallar mamanmu ta Fice kuma Tana da tabbacin Dakin Yaya zataje domin duk bayan mgariba da isha"i adakin take yinsa suna Hira da Tattauna wasu abubuwa Kamar ba Kishiyoyi ba..
Tana Idar da Sallar ko dan ad??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????du"a bata Tsaya yi ba ta mike Zaraf kamar an tsunguleta mganar Ya Jafar take Tunawa Dayace zai dawo duk da tasan da Wahala ya dawo yau sai gobe saboda akwai wa"azin da Baba mallam ke yi kowani bayan Sallar mangriba zuwa Isha"i sannan in an gama zasu Rufe da Sallar Isha"i kuma Tana da Tabbacin Aba ma ya dawo suna masallacin Tare in ma sun fito daga waje zasu gaisa ya wuce gidansa ina ma wannan mayyar matar tasa zata barsa ita Har mamakinta take yadda take mutuwar son Ya Jafar ko ina abun so a wajen wanda ya maida mugunta Dabi"arsa.
Baki ta Tabe bata tsaya Cire Hijabin Jikinta ba ta Fice Takalmin mamanmu na Yawom Tsakar gida ta Zura ya ma mata yawa sosai karamar kafarta ta Zurma aciki batason shiga Dakin su ne Saboda hamida tasan su Ya zeenatu ba lalle su bi ta kanta ba ammu Hamida gani taake tafi kowa Shigar mata Hanci da Dunkunkune in ta koma Dakin Hamida tayi mgana sai ta tankata kuma Hakan kamar wani Lasisi ne ta siyo ma kanta Fada Wajen Aba Shiyasa ta zabi Tafiya gidansu Hanna tayi zamanta sai Dare yayi Lokacin Hamidan ta kwanta sai ta Dawo.
Batare data Fadama kowa ba,kamar yadda ta Saba yin komai gaban kanta ta saka kai ta fice Daga gidan kuma Har ta fice bata Hadu da kowa ba,Awajen ma ba kowa Saboda an shiga masallaci Wajen yayi Haske Saboda an kunna Generator massllaci ba wuta suma ana Dawowa sallah su Ya shamsu zasu tada na cikin gidan Mallam babba ne mai bama Duka gidan da gidansu wuta taji dai ana ta Fada D'an malam Dake madina ya aiko da kudi aka siya har ma gyaran gidajen da aka sabunta musu wattanin baya duk shi yake turo ma dasu Ya Jafar kudi su kuma suna aiwatar da umarninsa.
Tasamu nasaran shiga gidan kanta Tsaye saboda Buba megadi shima yana masallaci wannan Dokar Baba Malam ne,ba hujja kana jin ana Kiran Sallah ka fake da wani aiki ya zama Dole kowa ya bar komai ya tafi kiran Allah
Gidan Baba Malam ya wuce yadda zan kwakwatanta muku Babban gida ne mai Dauke da Haraba mai girma Dauke da Motoci guda biyar hudu suna Bayyane Daya kuma an Lullubeta da Tamfol Tadade ahaka in ba mai mallakin Motan ya Diro garin ba bamai da ikon hawanta Duk da bai Saka Dokar haka ba,Sai Dayar bakar prado din ta mallam ce in fita ta kamasa Dayar 306 iri daya guda Biyu Daya ta Ya Jafar ce Daya ta Nasir,Sai wata benz baka ta Aba ce,Sai babbar Macapolo ta Jigilan makaranta ne.
Haraban gidan na Zagaye da Fulawowi masu kyau da yarari.
Daga Cikin gidan kuma Flat Biyar ne ajere na Farkon na Baba Malam ne grefensa akwai Dakuna kamar guda Biyar saboda mazan gidan Falt din Dake bayansa kuma Shashen Hajiya Babba ce Uwargidan Mallam sai shashen mai bi mata Hajiya uwa Daga nata sai na Anty Nasara na Anty Amarya shine na karshen wanda Daga gefensa kuma wani katon Kitchen ne da Store mai Dauke da Kimai na Bukatar mace na girki Kowacce tana da nata ashashenta ammh Gudun Fitina yasa aka Fitar da na waje inda duk wacce keda girki Zata Fita ita da yara da masu aiki suyi komai Tare Dokar gidan ce da Tsarin komai Bisa Tarbiya da Sunna Baba mallam Sharahararran malami ne Daba iya Nigeria ko Gumel ba Har Kasheshen Larabawa an san dashi.
A Babban Falon Dake shashensa ake Taruwa Matan da yaran maza da mata aci abinci sannan Ashashen sa ne kadai akwai Talabijin shima kuma In suna wajen sai Tashar Karatu sai wa"azi in ba kaga an Sauya sai in Dare ya Tsala yana so ya kalli Labarai Sun saba ya Zame musu jiki Duk wanda ya kwana da tashi agidan Mallam ina ka Fito karatu ina zaka ne..Me kace Aya ce mai na maida maka Hadisine ba iya Iyalan gidan ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login