Showing 129001 words to 132000 words out of 265571 words

Chapter 44 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28957

bai cika son tana mai mgana in suna cin abincin ba yasa tayi shuru tana kurban tea tana kallonsa shima kuma in ya Dago suka hada ido sai yayi mata Yake kawai.
Sai da ya kusa gama cin abinsa sannan Amina ta fadomai arai kamar ya Tuna da wani abu ya Dakata da komai yana kallon Sakina Cikin wani yanayi yace"yarinyar nan ta fito kuwa..?
Wani irin Kallo tayi mai kafin tace"Wata yarinya kenan..?
Yadda ya kalleta ne yasa tayi Saurin gyara mganarta da cewa"Bansani ba..Nidai ban ganta ba..!
Tsam yayi yana wani Tunani bata ci abinci ba,Ba domin yadda Hajiya da maallam suka saka shi a Tsakiya ba da sai yace ta Dauwama adakin ai yunwa ba"a mata iskanci sai dai in ya kyaleta Allah zai kamasa kuma Hakkin mallam da Hajiya na wuyasa..!
Tuna haka yasa ya kalli Sakina kafin yace"je ki kiramin ita..!
Ido ta Zaro kafin tace"Ni kuma..?
Kai Tsaye yace"Eh ko bazaki ba..?
Jin haka yasa tace"ban ce ba..!
Tashi tayi tana Tura baki ta wuce ya Bita da kallo daman yasan lambo Tayi Sakina ai bazata Daina Halinta ba.

Afusace ta Buga kofar ta shigo Tana bin Dakin da kallo lokaci daya tana wani yamutsa Fuska nan kasan Cafet ta Hango Amina ta Dunkule waje daya acikin Hijabinta,Ga ghanas dinta nan inda ya ijiyemata ko kauda su batayi ba Ranta ya kara baci Cikin kufuluwa tace"Kee...!
Cikin Tsswa Amina bata jita ba Domin barci ne na wahala ya kwasheta bata sani ba Jiya yadda taga rana haka taga Dare bazata kwatanta kwana awajen da ba Hanne ba Hamida ba bata taba tsamanin wannan ranar ba ballatana ta Shiryama zuwanta Tunda ta shigo Dakin ta zube anan kasan Cafet ko motsi bata karayi ba tayi kukan har ta gaji ga Tsoro Daki ita kadai abunda bata saba ba,Bata iya barci ba Tsoro da Fargaba da kewa basu barta ba Dakyar ta Rarrafa da Asuba ta shiga Toilet din Dakin tayi alwala tazo ta Rama Sallar Isha"in da ake Binta jiya da kuma Sallar asuba shine fa tana nan zaune bata ma san barci ya kwasheta ba.
Sakina jin tayi banza da ita kuma taki Motsi yasa ranta ya baci a Tunaninta da gangan tayi mata yasa ta isa kusa da ita ta saka kafa ta Shureta daya sa Firgigit Amina ta farka Daman a Tsorace take cikin muryanta da Bata Fita sosai saboda kuka tace"Wayyo..!
Sakina ta saki Tsaki kafin tace"Baki ce wayyo ba sai nan gaba..Badai kin ce dani Zaki kishi ba yarinya..Ai wayyo Salamu Alaikum..!
Amina ta bita da kallo da kumburarrun Idanuwanta Hancinta ya Toshe da majina sai ja take ga kuka ga sanyin Dakin Domin A.C a kunne kuma fanka ma haka ita kuma bata yi Hausan tashi ta kashe su ba.
Sakina ta koma da baya tana mata wani kaskantattacen kallo kafin tace"Kazama kawai..Sai ki taso yana kiranki..!
Amina ta kalleta da mamaki kafin tace"Shi wa..?
Cikkn Shakewar murya Sakina ta ga tama raina mata wayau yasa ta juya tana fadin"Uban ki ba..!
Amina ta bita da kallo har ta fita itafa bata gabanta ita yanzu kokuwa take da wannan Sabuwar rayuwar shiyasa Zagin Sakina bai ma Dameta ba kamar bazata je ba Domin jiri take gani in ta mike ammh Tuna Kalaman ya Danmallam yasa ta mike jiri na Dibanta ta fice Daga Dakin zuwa Falo Daidai sanda Sakina taja kujera ta Zauna Dammallam na zaune bai ce mata komai ba sai ga Amina ta fito tana Layi Cikin hijabinta kamar zata fadi Daga nesa ta Tsaya tana kallonsu kafin tace"Gani..!
Daga sama har kasa yake kallonta alamu sun nuna ko mai yarinyar nan batayi ba tunda ga jiya kenan ganin yadda Fuskarta ta Kumbura ne ya bashi mamaki Sakina kuwa Kamar ta yi Tsaki haka taji da taga yana kare ma Amina kallo bata ma lura da kallon kyama yake binta dashi ba..!
Saboda mugunta sai da tafi minti Goma a Tsaye tana neman faduwa sannan yace"kizo ki ga abun kari nan.!
Amina da Tagaji da Tsayuwa tace"Ni na koshi..!
Ko kallonta bai yi ba ya maida hankalinsa wajen cin Doyansa Sakina ta juya tana kallonta ta Harareta bata ma ganta ba ta juya tana Faman Kama Hijabinta ta koma inda ta Fito nan inda ta baro ta koma ta zauna ta Hada kai da gwiwa ta fara Rera sabon kuka Allah sarki sai yanzu ta kara Tabbatama da kanta da cewa tayi maraici tazo inda ba mamanmu ba Hamida ba Hanne,Wadanda sune ita in basu Rayuwar Amina bazata taba cika ba Aminu ne ya fado mata arai ko wani Hali yakeciki..?
Tasan da shi ta aura ta tabbata zai lallasheta zai mata komai Saboda yana sonta ammh kalli inda Kaddara ta kawota inda ba"a san Darajanta ba Daga megidan har matan gidan basu da Imani Allah ya isanta wlh bazata taba yafe musu ba mugaye kawai..!
Tun daga Lokacin Amina ko motsinsu bata sake ji ba tun tana Daurewa har ta kasa Cikinta ya kulle yunwa take ji ga jiri ga rashin barci sai mulmula take saman cafet dafe da Ciki tana faman kuka ita kadai Zata mutu acikin wannan gidan wayyo ita Amina..!

Umar kuwa agida ya wuni bai Fita ba sai da yammah da ya kira Jafar yazo suka hadu shima iyakarsa haraban gidan bai shiga b,Mganar Visa dinsa sukayi so yake cikin satin nan ya koma Madina bazai iya sake wasu kuma kwanaki ba,gabda mangariba Jafar ya tafi shi kuma Daganan masallaci ya wuce sai da akayi sallar Isha"i ya dawo ya iske Sakina tayi sabon wanka bayan ta gama girki ta gyara gidan yana tashin kamshi Sai ransa yayi fari,Yana son Sakina saboda Tsabtarta,sannan uwa uba kuma kwalliya,yau din ma ta tsuke cikin Riga da wando,ko Dankwali bata saka ba gayu take ji yau din,Ko bai yi mgana ba tasan ya yaba tunda yana ta kallonta yana mirmishi.
Abincin mara nauyi tayi musu Faten Dankwalin Turawa da hanta sai Coffea data hada musu tare suka zauna suka ci abincin su kafin su dawo Falo su zauna Sakina ta Dora kanta saman cinyar Umar shi kuma yana wasa da gashinta,Hankalinsa na wajen kallo a tashar Sunna Tv Qur"an,sakina kuma har ta fara barci bata damesa da mgana ba sanin Halinsa hira in ya sota suna yi bai so ba kuma baya son ana damunsa Duniya ta mata sabuwa yadda taga ya manta da Halittar Amina acikin gidan
Kamar wasa wayarsa ta Dauki Sautin kidan Larabawa Sakina ta Bude ido tana fadin"Habibi kamar ana kiran wayarka fa..!
Chan saman dinning ya barta da sukaci abinci,Yasa ya Daga kansa yana Fadin"itace..!
Mikewa tayi tana fadin"Bari na Dauko maka..!
Sanda ta karisa ta Dauko wayar sai da gabanta ya fadi ganin sunan mallam,sai da Annurinta ya Dauke tsayawa tayi har wayar ta katse jin ta Shuru yasa ya dago yana kallonta kafin yace"Waye ke kirana..?
Sakina ta kariso ta mikamai tana Fadin"Mallam ne..!
Gabansa sai da ya fadi ya karba da Sauri Lokaci daya yana fadin"Dauke min karar nan..!
Ba musu ta Dauki Remot tayi kasa da Volume din shi kuma yabi bayan kiran Mallam
Da sallama mallam ya daga Kiran Umar ya zamo daga kan kujera kamar yana gabansa yace"ina yini mallam..?
Mallam na zaune afalonsa Gefensa Hajiya ce yaa amsa yana fadin"lafiya lau Umaru ya wajen iyalan naka..?
Ya amsa da lafiya kalau kansa na kasa kamar yana gabansu Sakina na kallonsa ta gefen ido a duniyar nan Umar na bala"in ji da mutanen nan guda Biyu mallam da Hajiya na ukun su kuma wannan Mayen Baba Sa"idun inyana mgana dasu kamar ya kwanta musu saboda Biyayyah..!
Mallam yace"Masha Allah..lafiya yau baka shigo anguwan namu ba..?
Nace to bari na kiraka naji Allah yasa ba Rigiman me sunan mamana bane har yanzu bata bari ba..Domin yanzu nan yan"uwanta suka tashi daga nan tun jiya suke kuka ko makaranta ba su je ba suna ta koke koke sai da na kira su yanzu nayi musu nasiha na lallashesu da cewa su bari tayi ko sati Daya ne sai suje su mata yini..!
Danmallam yayi shuru bai yi mgana ba Mallam ya gyara zama yana fadin"Ina ita maman tawa..?ina fatan ta Daina kukan ko..?
Danmallam kansa na kasa yace"Eh ta bari Baba..!
Runtse ido yayi yayi karya Domin bai san ko ta bari ba..
Mallam yace"Madallah Sai kayi hakuri Umaru kaji ko..?Mamana yarinya ce karama yanzu bata da kowa sai kai..Kai zaka zama mai mata Tarbiya Tunda ta bar karkashinmu..In tayi ba Daidai ba kamata nasiha cikin jan hankali,Duka ko Tsawa basa gyara Tarbiya jan mutum ajiki da nuna mai so shi ke sa ya rage wasu abubuwan..Don Allah Umaru ka kula da Mamana..itace karama acikin matan ka ba lalle ta kai su wasu abubuwan ba..ku rika mata uzuri in ta aikata wani abun Umaru..!
Kansa na kasa ya gyada kai kamar Mallam na ganinsa kafin yace"Insha Allahu..!
Mallam ya cigaba da fadin"Ina ita abokiyar zaman nata..?fata dai ba wata matsala..??
Cikin Ladabi yace"Babu mallam..!
Mallam ya jinjina kai kafin yace"Dakyau itama Saratun nayi waya da Mahaifinta namai bayanin komai har ita nace abani nayi mata Nasiha sosai..ina rokin Allah ya hada kanku..Sannan kai kuma Allah ya baka ikon yin Adalci..!
Umar ya amsa da Ameen Ameen daganan yayi shuru kafin yaji mallan yace"Ina ita maman tawa..!
Ko tayi barci ne..?
Umar ya runtse ido murya kasa kasa yace"Eh..!
Mallam yace"To shikenan Allah ya zaunar daku lafiya..ga Hajiya nason mgana Dakai..!
Bai gama zufan karyan daya yi ma maallam ba Hajiya ta karbi wayar suka gaisa kafin tace"In fatan Amina taci abinci kafin ta kwanta..?
Dakyar yace"Eh Hajiya taci..!
Kai ta kada kafin tace"Shikenan ka kula da ita kaga dai yarinya ce..Wlh ban yarda ka hada kai da matanka ku cutar da ita ba..Domim ba sa"ar su bace..!
Yana jin Hajiya bai iya mgana ba ta cigaba da fadin"Ina mganar mu ta kwana..?
Sannan yaushe zaka koma..?
Kai Tsaye yace"Ina so cikin satin nan Hajiya Visa na nake jira..!
Hajiya tace"Kake jira..?Ita Sakinar fa..?
Kai Tsaye yace"Nan zan barta..Sai na Sake dawowa..!
Hajiya ta bude baki tana kallon mallam shima yana kallonta kafin tace"to ka dai samar ma Amina wajen zama domin na fada maka da ita zaka tafi in har ka sake dawowa..!
Insha Allahu yace mata,Sannan ta cigaba da fadin"Mganar karatunta da islamiya da Boko zata cigaba da zuwa..ammh nace ta huta na sati Daya..Idi Direba in ya Dauko su hanne Daganan zai biya ya Dauketa in suka Dawo ya sauketa agida sai sun dawo islamiya sai ya maidata gidanta..!
Shi dai nashi dan bi ne yasa yace"Duk yadda kika ce haka za"ayi hajiya..!
Hajiya tace"Shikenan..Allah yayi muku albarka gabadayanku..!
Ya amsa da Ameen Ameen yana fadin Allah ya kara girma.
Daganan sukayi sallama ta katse wayar,Sauke wayar yayi ya koma ya Jingina da kujera yana Neman yafiyar Allah yayi ma iyayensa karya karo na Farko arayuwarsa..!
Sakina kuwa kallonsa take yi Ta gama Sarewa tunda taji yama Furtama Hajiya bada ita zai koma ba Tabdijam akwai Daru in dai ita da kazamar yarinyar nan zasu zauna awaje daya..!
Mamaki ya kamata Da taga ya mike Tsam cikin Mamakinsa tace"Habibi badai barci ba ko..?
Kai Tsaye yace mata"A"a..!
Bata gama mamaki ba taga ya nufi Dakin da Amina ke ciki har Lekasa sai da tayi gabanta na faduwa ita dai bataji me mallam da Hajiya sukace mai ba ammh tabbas suna da alaqa da Shigarsa wajen Amina komawa tayi ta Zauna tana girgiza kafa tasan halinsa da sai tabisa Dakin taga abunda zai mata..

Shikuwa kai Tsaye ya Tura kofar Dakin ya shiga da sallama,Sai dai sallamansa ta makalene daya ci kusa cin karo da Amina Da azaban yunwa da ciwon ciki yasa ta gangaro har kofar Dakin,Baya yaja da Sauri yana kallonta Lokaci daya yana karema Dakin kallo hatta jakunkunarta yadda ya shigo dasu haka suke kofar Bayi a Bude ta barsa tana nan cikin Hijabin nan ko wanka yana da Tabbacin batayi ba ga ruwan hawaye nan da majina duk ya bushe mata abaki batama san ya shigo ba kwance take hannunta Dafe da Cikinta kamar mai barci
Ransa ya baci da wannan kazantar,wlh ba domin mallam da Hajiya sannan kada Allah ya kamasa da Laifin Saba musu ba bazai leko Dakin nan ba kamar ma Zarnin Fitsari nan da nan yaji zuziyansa ta fara tashi toshe Hanci yayi da hannunsa kafin yace"Ke...!
Kamar a mafarki taji muryansa da Sauri ta Bude ido suka hada ido harara ya sakarmata kafin yace"Miye haka..?Tashi zaune..!
Da Sauri tatashi Ta koma ta Jingina da gado sai hawaye kamar an Bude Famfo.
Cikin Bin Dakin da kallo yace"Fitsarin kwance kikayi..!?
Bata kallesa ba ammh aranta sai da tace ita bata Fitsarin kwance ammh a sarari sai ta girgizamai kai Cikin Takaici yace"Baki da baki ne..?
Muryanta a shake tace"A"a..!
Kallonta yake yi yana kauda kai kafin yace"To zarnin nan da nake ji daga ina ne..?
Kanta na kasa ta kasa mgana Tsawa ya Daka mata kafin yace"Ina mgan kina jina ke kurma ce..?
Da Sauri tace"A bayi ai nake yin Fitsarin ..!
Sai kuma ta sakamai kuka karamin Tsaki yaja kafin yace"Banda kina kazama a ina aka taba yin Fitsari ba"a kora ruwa ba..Sannan a kasan tiolet din kike tsuggunawa kina yi bakya hawa Sit din..?
Kai ta gyada mai alaman hakane ransa ya kara baci kafin yace"Kin ma yi wanka..!.?
Nan ma tace "A"a..!
Ya kara kallonta kafin yace"Lalle kazantarki ta shahara..!
Ya sake bin kayan ta da kallo kafin yace"Wadanan kayan fa..?waye zai kauda miki..?Ke banda kazanta baki iya komai bane..?
Nan ma kai ta gyada mai cikin mamaki yace"Eh fa kikace..?
Sai ta kara Saka kuka cikim kukan take fadin"Ni ban iya ba..agidama Hamida take min ko mamanmu..!
Galala yayi yana kallonta aransa yana Auna yadda aka gurgurta rayuwarsa da aka auramaaa wannan yarinyar.
Kofar Tiolet ya nuna mata yana fadin"Maza tashi ki shiga ki sa ruwa ki wanke zarnin fitsarinki..Sannan ki Tabbatar da kin yi wanka sannan kizoki Sauya kayanan dake jikinki..!
Kasa tashi tayi sai da ya Daka mata Tsawa sannan ta mike jikinta na rawa cikin Haushi yace"Dilla cire wannan Hijabin sai wari yake..Tun jiya abu na Jikin ki baki cire ba saboda kazanta..!
Bazata iyamai musu ba na farko tana Tsron Rashin Imaninsa na Biyu kuma mganar Aba Dayace in tayi mai gaddama bai yafe mata ba.
Hijabin ta cire ta Tsaya Tsumi tsumi tana kallon kasa tiolet din ya nuna mata yana fadin"Oya shiga..!
Tafiya ta farayi sai jiri ya kwasheta zata Fadi da hanzari ya saka hannu ya Rike hannunta kafin ya saketa ta Fada,kan gado Cikin mamaki yake kallonta tana kuka tana Dafe da Cikinta tana fadin"Wayyo Cikina..!
Kai Tsaye yace"Yunwa ko.?
Kamar tana jira ta dagamai kai yar Dariya yayi kafin yace"Ai ita yunwa ba"a mata iskanci..Duk Taurin kanki ai gashi nan ta koya miki hankali..!
Tsaki yaja ya fice Daga Dakin ta bisa da kallo aranta tana addu"a da Fatan Allah yasa abinci zai kawo mata domin ta kusa rasuwa..!








*Janafty*












*Janafty*
*20/09/2022*



*TFZB2003*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*

Sakina na zaune inda Umar ya barta taga ya sake fitowa cikin mamakinta sai taga ya nufi Dinning ya Dauki katon mug ya tsiyaya ruwan tea ya saka madara da Milo sai siga bata iya shuru ba sai da tace"Habiba yau kuma Tea zaka sha da madara..?
Saninsa tun abaya madara bata wani Damesa ba,Bai mata mgana ba taga ya Dauki mug din ya nufi Dakin da Amina take wajen kallonsa kadan ya Rage bata fado daga kan kujera ba sai da taga shigansa sannan ta maida kallonta acikin ranta tana fadin kan uba..!
Shi kuwa yana shiga ya iske Amina inda ya barta kwance tana numfashi Sama sama,Kai tsaye yace"Tashi zaune..!
Ba musu ta mike tana wani karya wuya saboda yunwa mikamata Kofin yayi ta karba tana wani lankwashewa Cikin bada Umarni yace"Shanyesa yanzu..!
Ba musu ta kafa kai ta fara sha Jikinta da Hannunta na rawa Lokaci Daya yana tsaye ya jingina da wardrope din Dakin yana Binta da kallo ganin yadda jikinta ke rawa yasan taci Ubanta da yunwa yaji dadin haka shifa Tana cin Darajan masu Daraja ne ammh ba domin haka ba ko zata mutu ne bata isheshi kallo ba wlh.
Duk da kyamkyamin Dakin dayake yi bai fita ba yana Tsaye yana Nazarinta Abun dariya ya basa Daya ga karamar kafarta Dauke da Jan lalle tare da Hannayenta wai nan shi akayi mawa ko. ?
Shi allah kada ya nuna mai sanda zai kula wannan yarinyar wacce bakomai acikinta sai iskanci da rashin kunya.
Yana wannan Tunanin baisan tashinta ba sai kakarin amai da ya jiyo a Tiolet lekata yayi yana fadin"Ke miye haka..?
Amina na Duke daga cikin Tiolet tana maida numfashin wahala tace"Cikina ne ke juyamin..!
Tafada tana kara Dafe Cikinta Saboda yadda yake Hautsina mata Ta Dade bataci komai ba shiyasa Dan mallam karamin Tsaki yaja bai yi mgana ba Sai ga Amina ta fito tana layi ta sake fadawa saman gadon Cikin mamaki yake kallonta ganin harta gaban Riganta ya fara baci da amai haka gefen bakinta zuciyarsa yaji ta Fara tashi yayi saurin matsawa baya yana Fadin"Ke meyasa kin cika kazanta ne..?
Aman da kikayi wa zai wanke miki..?Sannan ji bakin ki da gaban rigarki duk amai baki da Hankali ne..?
Ya karishe fada yana kauda kansa Sabida bayason kallonta kyama take basa ita kuma ga ciwo ga fadansa kawai sai ta fashemai da kuka tana Fadin"Nifa banda lafiya in na mike jiri nake gani..!
Daure Fuska yayi yana fadin"To ba anan ba maza mike ki wuce Tiolet ki Tabbatar da kin wanke kazantar ki sannan ki tube kayan jikin ki,kin yi wanka..Wlh kada ki bari na Dawo na iskeki a haka ranki zai baci..!
Kukanta ta karama Volume tana fadin"Wlh bazan iya ba..!
Tsawa ya Dakata mata Lokaci Daya yana Fadin"Zaki tashi ki wuce ko sai na saka miki hannu..?Tunda kika zo gidan nan kike sakani mgana ki yi abunda nace tun kafin na yarda da Shawaran zuciyata na kaiki inda ake gyaraama irin ku zama..!
Ai bai gama mgana ba Amina ta mike tana Kuka ta shige Tiolet din Kamar ta Fadi Jikinta ba karfi Tsaki yaja ya Fice aransa yana Jinjina kazanta irin na Amina bai taba Zaton haka take ba.

Sakina ta na nan inda ya barta Tana jiran fitowarsa,kusa da ita yaje ya zauna yana sauke numfashi sai yanzu yaji ya shaki iska ammh Dakin chan wlh ba yanayi mai Dadi ganin yadda ya Zauna yayi ne yasa ta gyara zama tana Fadin"Meya faru Habibi..!?
Bai kalleta ba ya mike yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login