Showing 138001 words to 141000 words out of 265571 words

Chapter 47 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28934

Shuru kawai tayi,Ganin kamar yanayinta ya Sauya ne yasa Mallam yace"Kiyi hakuri marliya..kema kada ki saka baki wannan ba Hurumin mu bane..!
Da Toh ta amsa mai tana kokarin nuna komai ba komai bane kada mallam ya Fahimci yanayinta..
Washegari ta kira sakina ta lallasheta akan tayi Hakuri da mganar Binsa ta bari in ya koma mallam ya tabbatar mata zai dawo domin ya koma da ita Tunda Sarood bata da wani amfani kamar Hoto take.
Sakina ta yarda ta Hakura ammh tace yana tafiya itama Dutse zata je tayi Sati Daya ta huce daga Bakincikin yadda zata fara zama da Amina agida Daya Matsayin Mijin su daya.

**********

Ana gobe tafiyar Danmallam Da Daddare Sakina ta Fadamai Tana so gobe in ya tafi zata je Dutse ta gaishesu,bai ce mata komai ba alokacin sai da safe domin jirginsu 12pm zai tashi zuwa Jidda,lokacin yayi wanka ya shirya Cikin Shigar jallabiya Fara da bakin wando sai Hula yana Fesa jikinsa da Turaransa na Arab Sakina ta shigo Dakin Cikin Shigarta na kwalliya kamar ko yaushe sai da ta isa kusa dashi ta karbi Turaran Hannunsa ta karishe Fesamai bayan ta gama ta maida Turaran kan Madubun Dake Dakin ta Rumgumesa tana Fadin"Zan yi kewarka Habibi..!
Shima riketa yayi na wani Lokaci kafin ya dago kanta ganin Hawaye ya Cika idanuwanta yasa ya Girgizamata kai yana fadin"Kada kiyi kuka..Ki batamin kwalliya..!
Jin haka yasa ta kara Narkewa tana mai yar shagwaban zai tafi ya barta nan ya lalace wajen ya lallashinta sai da karar wayarsa ta katsesu sannan ya Saketa Wayarsa Dake kan gado ya Dauka ganin Aliyu ne yasa ya Daga yana Fadin"Badai har ka iso ba..?
Dagachan bangaran Aliyu yace"To akace maka ni irinka ne..Gani Falon mallam muna jiranka..!
Umar yace"Ina Jafar ya iso..?
Aliyu yace"To mu da bamu da sabuwar Amarya Swt sixteen ai duk mun Hallara..!tsaki yaja kawai ya Katse kiran yana girgiza kai yana Tunanin Aliyu bai da girma sai na Jikinsa.
Sakina ta kuramai ido tana kallonsa Hannunta ya rike yana fadin"Muje su Aliyu nachan gidan mallam suna jira na..!
Marairaicewa tayi kafin tace"To haka zaka tafi baka karya ba..?
Yana kokaron Daukan jakan kayansa yace"Kinsan bana iya sakama cikina wani abu in zan hau jirgi..Kada ki Damu zan ci wani abu ko achan ne..!
Saman kafadansa ta Dora kanta tana fadin"Zaka tafi bakace min komai ba..!
Kai Tsaye yace"Name fa..?
Ta karkace kai tace"Na tafiyana Dutse mana..su Daada nake son naje na gaishesu tun fa Bikin Sadiya ban koma ba..!
Kai Tsaye yace"Kije ammh ba yau zaki Tafi ba ki bari gobe..!
Da sauri tace"Saboda mene Habibi..?
Har na kirasu nace fa ina tafe yau..!.
Hancinta yaja kafin yace"Saboda Haka nace..Kuma ba Sati zaki yi ba..kwana Uku na baki..!
Baki ta Bude tana kallonsa sai ya Rufe mata bakin da nasa ya bata sumba mai tsawo kafin ya saketa Jakarsa ta amsa ya Riko hannunta suka fito Har Falon,har ga Allah ya manta da Amina sai da ya kalli Dakin sannan ya Tuna da ita Hannun Sakina ya saki kafin yace"Jirani ina zuwa..!
Tana hararansa ya shige dakin Sarood wanda ya zama na Amina yanzu..!
Barcinta take sha sosai domin barcin da batayi bane kwana Biyu take ramasu ga Filet da mug nan har da Sauran Buredi a kasa dataci ta Rage sannan Dakin duk ya Hargitse ga Hijabai nan da kaya saman gadon bata Kwashe ba,Amina sai jiya ta Sake wanka shima kayan jikinta ne suka isheta tayi wanka ta sauya tayi Daidai kan gado tana barci Daga ita sai Zani Tayi Daurin gaba ko Riga bata saka ba.!
Kamar zai tasheta domin zarni da wari ya ishesa yasa kawai yayi Tsaki ya fice Daga Dakin yana Fitowa yaci karo da Sakina inda ya barta tana kallonsa shima ita yake kallo kafin yace"Sakina..!
Ta amsa da Na"am cikin Kaushinsa yace"Zan tafi kada ki shiga shirgin yarinyar nan ki kama girmanki..in kin yi Girki ki bata..Sannan gobe in zaki Tafi ki Fadamata domin ta Rika fitowa tana sama ma kanta wani abu..Ban son Rigima Allah in naji wani abu ke zan bata ma rai saboda ke na bar ma Amanar gidana..!
Sakina ta Tura baki kafin tace"Ni fa bazan dinga mata girki tana kwance ba..Itama ai matarkace sai ta fito ta girka nama na kaima kayi Adalci..!
Kai tsaye yace"Wannan me ta iya banda kazanta..?
Sakina ta Hura hanci kafin tace"Sai tayi kazantarta taci kayanta Daman bani zata mawa ba..!
Kai ya kada kafin yace"Allah ya kyauta sannan Hajiya tace zata koma makaranta nan Idi zai rika zuwa Daukanta..!
Aran sakina tace to ni ina Ruwana batayi mgana ba shima bai ce komai ba ganin zai tafin yasa ta rikesa ta sakamai kuka ganin haka yace ta sako mayafi su tafi gidan mallam tare jiki na rawa ta je ta Dauko hijabi suka Fice shi ya tuka Motar da kansa bayan ya sallami megadi itama Sakinar ya bata katin bankinsa guda daya suna Mota yace mata"Na amfanin yau da kullum in ya taso ke da yarinyar nan kuyi amfani dashi..kayan abinci kuma in ya yi kasa Jafar ko nasir zasu kawo..!
Karba tayi kafin tace'Ni dai ka daina Hadani????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
da kazamar matarka meyasa baka bata nata ba..?
Kai Tsaye yace"Saboda kice babba sannan kuma kin Fita Hankali..kuma Amanar komai da komai a Hannunki na bari..!
Bata kara mgana ba har suka iso ita Cikin gida ta shige shi kuma Falon mallam suka gaisa Aliyu nata kallonsa yana Dariya cikin gida ya shiga yayi ma Duka matan sallama Shashen Hajiya ne na karshe yana Duke gabanta tana fadin"Allah ya sauke ku lafiya..Allah ya Tsare..!
Yana ta ansa mata da Ameen Yana shirin tashi tace"Ina wayar da nace ka siya ma Amina ka ko siya ne..?
Sai alokacin ya tuna kansa na kasa yace"Na manta Hajiya..ammh yanzu zan barma Jafar kudin zai siya mata..tunda su zasu rakani Airport shi da Aliyu..!
Hajiya tace"Ai ya shigo mun gaisa..Sannan ka shiga gidan Sa"idu kuyi sallama da shi da balaraba..!
Da toh ya amsa mata ya tashi ya fice ta Bisa da Fatan nasara.
Bai koma falom mallam ba sai ya wuce gidan Aba ya iskesa ma yana shirin Fitowa haka ya tarbesa ko zama bai yi ba sukayo sallama ya kira Mamanmu suka yi sallama Fadi take Allah ya Tsareka Umar..Allah ya bada sa"a ina Diyata Amina..?
Ina fatan tana lafiya..!
Kansa na kasa yace mata tana lafiya har Haraba ta rakosa tana ta addu"a sai da suka fice da Aba ta saki shewa kafin tace afili"Komai na tafiya daidai..yadda muka Tsara..!
Wajen goma da wani abu suka mika Hanya Jafar da Aliyu zasu rakasa Filin Jirgi,Sakina kuma har suka tafi bai kara ganinta ba.
Ita kuwa tana Shashen Anty Amarya sai da ta tabbatar da sun tafi sannan ta fito ta mata Anty Amarya sallama Domin ta fadamata ne ya barta tatafi Dutse,bata fada mata yace sai gobe zata tafi ba sanin bazata barta tatafi ba in ta fadamata gaskiya.
Gida ta koma ko ta kan Amina bata bi ba,Ta hada kayanta akwati Cike da kaya ta kulle Ko"ina harda Kitchen sai da ta kulle ta saka key din a jaka Dakin da Amina ke ciki ne kadai ta bari sai falo tayi Ficewarta Ta sanar ma da megadi zatayi tafiya ammh akwai wata yarinyar agidan ya bita da Allah ya kiyaye Su Danmallam ko Kano basu kai ba Sakina ta kama Hanyar Dutse ko ajikinta.






*Janafty*
*TFZB2005*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*


Sun isa Filin jirgin mallam Aminu dake kano shabiyu saura na rana sai dai sun iske jirgin su Danmallam da zai tashi zuwa Jidda da misalin 12pm na rana an fasa ya koma sai 3pm na rana sakamakon Weather babu kyau an dan samu Tsaiko kadan jin haka yasa Umar yace Aliyu da Jafar su koma kawai basai sun jira ba Tunda an sauya Lokaci.
Basu wani jima ba suka mai sallama suka tafi daman da motar Aliyun suka zo kafin su tafi sai da Umar ya bama Jafar akan ya siyama Amina waya domin in ya sake yatafi bai siya ba Kashin shi ya bushe wajen Hajiya shi kanshi Jafar yayi mamakin jin yace har da layi zai siya mata ya mata Rigister.
Sun koma gida da Labarin Tsaikon da aka samu su maallam suka bisa da Fatan Alheri Aliyu bai tsaya ba Daganan yayi sallama dasu mallam ya Dauki hanyar Dutse..

Amina bata san wainar da ake toyawa ba,sai da ta gaji da barci sannan ta tatashi shima kiran sallar azahar ya tasheta da ake ta kwalawa a wani masallaci dake kusa dasu sannan ta iya tashi gabbanta duk sun gaji Tsami ma kafafunta ke mata sosai,Dakyar ta iya mikewa taja jiki ta shiga Tiolet ta Sha ruwa a famfo sannan tayi alwala tazo tayi sallah sai dai kuma yunwa take ji,Ammh duk da haka bata fita ba ta koma ta kara nadewa a Tunaninta Sakina zata kawo mata kamar yadda ta saba sai har wajen uku saura na Rana bataji motsin kowa ba cikinta har ya fara Curewa waje daya yana mata Rugugi.
Tunawa da tayi sakina ba Imani gareta ba Daga ita har megidan sai su barta ta mutu basu da asara shiyasa ta mike ta taimaki kanta kayan datayi amfani dasu da safe ta Dauka ta fita zuwa Falo tana leken sakina sai dai bata ganta ba ko motsi ma babu agidan.
Bata gama mamaki ba sai da taga Kitchen a rufe sannan Hankalinta ya tashi,Sai alokacin ta Lura duka Dakunan suna kulle ne mamaki ya kara kamata to ina yan gidan suka shiga ne..?
Tabe baki tayi daga baya aranta tace ina Ruwanta dasu sun dade basu tafi ba suma shekara waya damu..!
Nan saman Dining ta watsar da kofin da Filet din,kamar zata koma daki sai wata zuciyar tace mata bafa kowa agidan ki sha iska tuna haka yasa ta koma falo ta samu kujera ta zauna tana kara bin Falon da kallo tana nazarinsa baki ta tabe ko ajikinta.
Sauran buredin data rage da Safe ya Taimaketa shi ta Samuka ya cikamata Ciki,Har barci ya Dauketa nan saman kujera bata sani ba sai bayan La"sar ta tashi tayi mamakin irin barcin Datake yi kwana biyun nan,Tashi tayi ta koma Daki tayi sallah sannan ta kara fitowa Ciki dai ba abinci shiyasa duk ta kasa sukuni Allah ya taimaketa a saman Dinning Sakina ta manta da kayan Tea su Amina ta samu ta sha da Ruwan Sanyi tunda ba na zafi ta kuma Samu katon Buredi a wajen ta hada dashi taci ta koshi tayi Dam ta koma Daki aranta tana fadin kafin su dawo nayi barci Domin ni bana Tare da yunwa..!
Sai dai kuma har akayi mangariba bata ji Duriyar kowa ba sai Hankalin Amina ya fara tashi Har sake fitowa tayi ta Duba ba wanda ya Dawo ta koma ta zauna tayi Tagumi sai kuka tana Tunanin yadda Sakina da Mijinta suka zama marasa imani suka tafi suka barta ita kadai agida wannan Rashin Imani ne Allah ya isanta Bata yafe ba in wani abu ya sameta su da Allah..!
Bata kara Tsorata ba sai Dare yayi Amina tsoro ya cikata gashi nepa sun Dauke wuta Duhu ya cika gidan ita kuma batasan inda ake kunna Solar ba batama san da ita agidan ba,Ga shi Daga waje Hadari ya Hadu Farkon Damuna,sai ta kasa zama itace Dakin ta ko falo ta kasa zama sai ta zauna motsi kadan dataji sai ta mike tana waige waige ta fara Firgita sai kuka Amina Bilhakki da gaskiya take kuka saboda Tana tsoron saukan ruwa barin ma in ana iska ko tsawa,tana wannan kukan aka fara iska mai karfi winduna na kadawa da Labulai sai Amina taji kamar ta yi iska ta ganta agida Bayan mamanmu ko Hamida saboda tsoro Daki ta koma ta Dunkule kan gado tana Kuka Lokaci daya da makyarkyata Idanuwanta a kulle gam bata so ma ta bude ga ko"ina duk Duhu Hankalinta gabadaya ya tashi banda Salati da wayyo wayyo babu abunda take yi.
Adaidai Lokacin aka tsuke da ruwa mai karfi kamar da bakin kwarya,Ga iska ga Rugugin Tsawa Amina ta rasa ina zata sa kanta taji dadi gabadaya ta Tsorace,ta kamkame jikinta waje daya,ta tusa kanta cikin Filo tana rufe kunnuwanta ga iska sai kada winduna yake yi da Labulai kamar zasu balle Fitsari kamar Amina zatayi a wando Saboda Tsoro hawaye kuwa ya wanke mata fuska da majina bata sanin ma sanda yake fitowa wani na Fitowa wani na Kara fitowa.

Adaidai Lokacin Adaidaitan da Danmallam ya hau daga Tasha zuwa gidansa koda ya fito rike da Jakarsa sharkaf yake da ruwa,har diga yake yi sai rawan sanyi yake kudi ya bama mai adaidaitan baisan ko nawa bane Saboda yayi mai Hallaci tunda suka sauka atashar Gumel aka fara Ruwa shi yana da Allagis din Ruwa ya tabasa komai kankantarsa sai yayi mura da Zazzabi in ma bai kwantar dashi ba yayi ta taran masu adaidaita suna cewa baza su shigo Cikin gari ba Dakyar wannan ya Daukosa ganin yana rawan sanyi Ganin irin kudin Daya basa ne yasa ya Leko yana fadin"Nagode yallabai Allah ya kara Budi..!
Da kai ya amsamai lokaci daya ya wuce zuwa Bakin get din gidansa ya kwankwansa har sau Biyu shuru Wayarsa ya ciro a aljihun wandonsa yaga ta Mutu daman ba chaji tun suna Filin jirgi Take buga Battery low,sannan kuma ga ruwa ma ya tabata domin sosai ta jike,Kara buga Get din yayi Allah yasa Buzun megadin yaji ya fito da sauri ya leko lokaci Daya yana haskasa da Fitilansa mai Haske ganin Danmallam da kansa yasa Cikin mamaki yake kallonsa bai Damu ba yace ya Budemai get da Sauri ya Budemai karamar kofa ya shiga gidan megadin ya bisa yana tambayansa bai samu tafiya bane..?
Eh kawai yace mai lokaci Daya ya Nufi Kofar da zata sada sa da Falon gidansa so yake ya samu yayi wanka da Ruwan zafi ya kwanta,jikinsa kamar ba Nasa ba.
Sai da yana shiga Duhu ba Haske abun ya bashi mamaki yana Tunanin ko Sakina ta kwanta ne kafin a Dauke Wuta ba"a kunna Solar ba,Isa Cikin Falon yayi ya isa inda makunnin Solar yake ya kunna Haske ya gauraye duka gidan falon yake bi da kallo ganin sa Tsab ba kuma Hayaniyar kowa Bai Damu ba ya kama Hanyar Dakinsa sai dai kuma me..?Sai yaji sa a rufe Mamaki ya kara kamasa sai ya Nufi Dakin Sakina yana kiran sunanta nan ma yaji kofa a Rufe bai kawo bata nan ba ya fara mata knooking yana Kiran sunanta ammh Shuru..!

Amina na dunkule akan gado tana rawan jiki taga lokaci Daya Haske ya kawo leko da kanta tayi sai taji dan sanyi a zatonta nepa sun kawo wuta ne,Sai rabin hankalinta ya kwanta ganin haske sai dai kuma me sai taji kamar tana jin motsi saurarawa tayi sai kuma bata karaji ba sai da ruwan yadan Dauke sama sama taji ana kiran sunan Sakina sai ta kara Tsoracewa kara Dunkulewa tayi saman gado jikinta na rawa kamar a mafarki taji an shigo Dakin data ke sai Amina ta kara shigar da kanta Cikin Filon ba inda jikinta ba ya rawa addu"a kadai take yi duk abunda yazo Bakinta sai ta fada Hawaye kuwa kamar an Bude famfo.
Kamar a mafarki taji muryansa yana Fadin"Ke...ina Sakina..?
Haka ya fada yana Tsaye daga kofar Dakin yana binta da kallo Cak ta Tsaya da rawan jikin sai da ta Leko ta filon ta hangesa Tsaye sannan ta sauke Numfashi Cikin Dan salama ta Dauke Filon Fuskarta ta mike zaune tana kara Dunkule Hijabin jikinta.
Kallonta yake yi ganin hawaye Chaba Chaba a fuskarta yasa yace"Me yasa same ki kike kuka..?
Ina sakina taje ne..?
Kanta na kasa tace"Ni bansani ba..Ni kadai ce agidan..kuma tsoro nake ji ina ta jin motsi..!
Sai ta kara fashemai da kuka bai Damu da kukanta ba Fadi yake yi"Sakina bata nan..?
Cikin alamun Tambaya Amina ta Dagamai kai kafin tace"tun dazu ba kowa agidan sai ni kadai agida..Tsoro nake ji don Allah ka maidani gida..!
Bai ma Saurareta ba gabadaya ransa ne ya baci kenan Sakina bataji mganarsa ba sai da tatafin yau kyafci yayi kawai yana Sakin Hucin Zafin zuciya,Allah ya kaddara bazasu tashi ba Koda ukun tayi matsalan bata kau ba nan aka sanar dasu sai jibi zasu tashi da Daddare yaso ya kama Hotel anan kano har zuwa jibin sai kuma yaji ya kasa gwara ya dawo gida bayason ya Wahalar da su Jafar yasa bai kira kowa ba ya tafi tasha ya hau motar Gumel sun fara tafiya Motar ta samu matsala wajen awa biyu kafin agama gyaran koda suka shigo gumel an yi issha"i sannan sun zo ana ruwa kamar da bakin kwarya,Shi ba ya iya Fakewa ako"ina shiyasa ruwan ya Tabasa sallar kadai ya tsaya yayi a wani gidan mai,kamar zai wuce gidan Mallam sai kuma ya fasa saboda bayama son sun san Tafiyarsa bata Yuyuba.
Sai gashi ya dawo ya iske wannan Rainin da Sakina tayimai gashi bai da key din kowani Daki acikin gidan Suna wajen Hajiya,Sannan akwai wani hannun Jafar yanzu kuma Dare yayi bazai yuyu ya kira yace a kawomai ba sai ya Tada musu hankali a yanayin Dayake ciki ko Ta kan Amina bai bi ba dake sharan hawaye Jakar hanmunsa ya Sabule nan saman Cafet ya taka ya nufi Cikin Tiolet din Dakin ya Rufe.
Ransa sai da ya kara baci ganin yadda kazantar Amina ya maidashi ga kayanta nan data cire saman kwandon wanki bazata iya Budewa ta saka ba sannan ga pant din ta nan da ta wanke basu fita ba ta shanya ajikin Famfo ransa ya kara baci bayin Daga gani an Dade ba"a wankesa ba Bashi da wani Zabi sai nan Tiolet din Shiyasa bai fito ba sai da yayi wanka ammh kuma sai da ya wanke Bayin tas sannan ya iya yin wanka da ruwa mai Zafi ya gasa jikinsa yana jin yunwa ga Mura ta kamasa ga kuma Sanyi Dayake ji Towel ya Dauro a kugunsa ya fito kayansa kuma Cikin kwandon wankin ya Bude ya saka yana Fitowa suka hada ido da Amina yadda ta Zabura sai da ta bashi tsoro Ido ta Runtse ta sheka da gudu ta Fice Daga Dakin tana fadin ta shiga uku da Harara ya Bita kafin yaja Tsaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login