Showing 252001 words to 255000 words out of 265571 words

Chapter 85 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28931

Soyayyarsa na kara shiganta Tunda ta auresa alheransa ke Lullube rayuwarta Allah ya barsu tare.
Su ya Aisha suna so suzo suna suka kira mallan suka mai mgana yace ai ya Danmallam baya taron suna Hajiya ta saka Baki tace na Dangi ne sannan kuma ai na Farko ne, gaba ba lalle su zo ba To sai ya amince kuma Daman yana son ganin yaran saboda akwai Tunasarwa Dayake Bukatar yi musu kan wani abu da suka manta.
Jin Dadi da sukaji Labarin mallam ya bada Izinin su taho ana Gobe suna ya Zulaihat da ya Ikram suka Diro sai Hamida da ya Zulfa Suka kamkame Amina suna Murna sai da Yakaka ta mata mgana akwai Dinki ajikinta Don na ta samu Jego mai kyau k'ashinta ya fara karfi shiyasa ta sami kwarin jiki Sannan Yakaka Jego take mata na Mutanen da sannan suna kauri abinci da Namoni da kifaye kawai takeci kafin me wannan Kibar na Amina kadan Tatafi ta riga tabi jikinta sai tafi kyau ma ahaka yar Duma Duma da ita..hamida ta Dauki yaran sai hawaye tana Tuna irin rayuwarsu ta baya Allah mai kyauta da kari Amina ce ta zama uwa haka..?
Kaunar yaran ya mamayeta ta kamkamesu sai da ya Zulaihat ta mata Tsiyan ba ita kadai bace uwarsu sannan ta amince suka Dauka da yammah sai ga ya Aisha ta Diro ita da ya Abida duk sai sukayi ma gidan mallam Tawaye gidan Amina suke yada Zango.
Sai Hira kawai ke tashi Cikin Farinciki Girkin suna agidan Baba mallam za"ayi su Anty Fadila da su Shamsiya sai matar ya Nazir itama tazo ita da Ya Jalela tare suka zo sune yan gayu zasu yi girki ya Zahra ma ita da Ya Abida sukazo Tunda garinsu Daya,Har ya Nazifa tazo ita da ya Fatima ya Akila ce bata samu zuwa ba sai ya Jadwa.
Hanne kuma sunyi waya sai da Safe zata zo.
Gida ya cika da Dangi an manta komai ana ta Hira da annushuwa Anty Hadiza tayi ma Amina kitso da kunshi Yan gusai da sukazo sai tsiya suke mata suna Fadin da wayau tana gyara yarta Harda Zafira akazo wacce za"ayi Bikinta nan da wata Uku.
Adaran Sai ga Akilu da zubairu sun zo ma Amina barka aranar suka dawo Daga Zaria sun je Rigistration sun samu Admmision,Sai da suka Dauki yaran suka kallesu suka juya suna kallon Amina Dake zaune tana shan Tea Akilu ya kara kallonta kafin yace"Tab..Su Aminene an zama uwa..Sai arage Rashin kunya..
Sai kunga hararan da Amina ta Sakar musu sai kun Dara su kansu sai da sukayi Dariya Fari tayi musu kafin ta Hura Hanci tana fadin"Banson Wulakanci..Kun dai san yanzu ni ba Sa"arku bace ko..?
Ya"yana Biyu..!
Dariya suka saka mata itama sai da ta Dara su kallonta suke yi suna mamakinta wai Amina ce ta Haihuwa lalle Haihuwa ta Allah ce.
Sun Dade kafin su tafi harda kudi suka bama yaran nasu Amina ta karba Tana fadin"Eyye..Kawu Akilu da Kawu Zubairu..!
Yanayin yadda tayi mganar ne yasa sukayi Dariya har Hamida Dake wajen tace"Mai hali dai baya fasawa. !
Akilu yace"Wlh kuwa hamida..!
Daganan suka musu sallama da Fatan Allah ya raya suka fita Daga Dakin sun dan bata Lokaci afalo tare da su ya Aisha kafin su tafi su suka zo da Umaima Hajiya tace su kawota ta zauna cikin Yan"uwanta zatafi sakewa..!
Kusan kwana sukayi basu barci ba sai da Yakaka ta kora Amina taje ta kwanta yaran kuma sun fara kuka iyayansu suka Daukesu duk da Amina ruwan nononta ya kawo Dr Ghali ya Rubuta madaran da aka siya ana kara musu dashi suna da tsotson tsiya in ji Amina don ma Yakaka na mata jan Ido da sai ta horar dasu da yunwa Amina ce fa ai sai Allah kadai ne zai iya mata..!
Washegari da Hidimar suna aka tashi su Mamata gidan Aba suka koma suka kwana da Safe suka shiga gidan mallam suna taimakawa da aiki,an yanka Raguna Hudu kowannen Biyu sannan an yanka kaji da Zabbin na Gidan gonar Baba mallan chan gidan su ya Zulaihat suke ta gyaransu da kuma aikin abinci duk ba su yi Taro ba isu isu ne kawai sai mutanen Gusai.
Da Safen sai ga Aliya matar Aliyu tazo ita da yaranta zuwa karfe goma sai Mutanen yola Hanne da mijinta Aminu har cikin gida ya shigo ya zauna afalo suka gaisa da su ya Abida bayanan Amina ta sakayo Lullubi ta fito suka gaisa Hanne ta Dauko mai yaran ya Dauke su yayi musu addu"an aransa yana ganin mganar Nenne wato Aurensa da Hanne ne Sanadiyar Haduwarsa da Amina ita kuma auranta da Danmallam shine silar Haduwarsu da Amina Allah kenan ya Musu addu"a ya ijiye musu kudi yayi musu sallama kano zai wuce sai in zai koma zai Biyo ya Dauki Hanne su koma gida.
Hanne ta rumgume Amina tana murnan ganinta ta Rumgume yaran ta kalli Amina kafin tace"Amina wai da gaske yaran nan naki ne..?.
Amina ta Harareta kafin tace"Ba nawa bane..na mami Hanne ne da Mami Hamida..!
Tafada tana Dariya ita Hanne gani take kamar wasa ta Yafito Hamida tana Fadin"Hamida kinga ikon Allah ko..?
Amina an shiga kwaryan manya..!
An zama uwa..!
Amina na dariya batace musu komai ba Hamida tace"Sai a rage jidali Tunda an zama uwa ko Aminene..?
Amina tace"To Allah yasa ya ragun kunsan ba yin kaina bane..!
Suka Hada Baki wajen fadin"To yin waye..?
Sai da tayi Fari sannan tace"Na Allah ne..!
Dariya Hanne tayi ta Daka mata Duka abaya Amina ta sosa wajen tana Fadin"Lala sai na fadama Hubby na..!
Dariya suka kwashe mata suna Fadin su Hubby an jiki..!
Tun Safe Amina tayi wanka ita da yaran suka fara shiga suna fita suna fita gadonta kuma cike da kayan suna yan"uwanta sun mata kara ba wacce tazo Hannun Rabbana Aba ma da Turamansa da kayan yara Mallam ma kaya sai wanda ya gani Amina ba abunda zatace ma yan"uwanta da iyayanta sai godiya domin sun mata komai aduniya wajen ganin sun ingata rayuwarta.
Ya Danmallam bai zo gidan ba Ranar suna Saboda mutane sun dai yi waya da Safe da wayar Sarood daman ai nan ta kwana tare dasu ya Abida,wajen azahar sai ga su ya Aisha da kololin abinci kala kala lemuka daman da ruwa tun jiya aka Sauke su nan da nan aka fara Cin abinci Daman tuni kowa yayi wanka ya Shirya kansa Yakaka da Safe gidan Baba mallam ta koma tace bazata iya ba ta bar ma su Abida gidan su shakata..
Abun da ya bama Amina mamaki Sai ga Sa"adatu da ya Sadiya har da ya Jidda sun zo mata suna abun Sai da ya bata mamaki ammh bata nuna ba ta Saki Fuska suma sauran yan"uwa suka karbesu hannu Biyu da suna Dari Dari Daga baya suka shige Cikin yan"uwana ana ta Hiran masu Ciki su ya Abida da su ya Zeenatu har ya Zulaihat duk ciki garesu su ya Ikram kam yama tsufa tana ta fama dashi Chan da yammah sai ga su mariya da Samira yan makarantar Haddarsu Amina baki ta rike tana kallonsu tace"Su Mariya ne da su Samira. !
Suna dariya Mariya tace"Wlh mune su Amina..!
Sai dukkansu sukayi Dariya Hamida ta Fadama mariya Dayake suna Chart ai sukace sai sunzo sun ga Amina da abunda ta haifa aiko sun sha kallo Amina ta zama zara aciikin wata Duk inda tabi ita ake kallo ta zama abun Sha"awa kuma duka taron Saboda itane nan suka Hade dasu Hamida suna ta Hiran baya da irin abubuwan da suka faru Lokacin suna makaranta Har Sa"adatu ta shige Cikinsu
Dayake abun na malamai ne ba Kida ba wani Hayaniya ko Hotuna ta wayoyinsu suka taru yan"uwa suna ta Daukan kansu ya Danmallam kuma yayi walima achan masallacin Baba mallan anyi wa"azi sannan an ci an sha an raka yara da addu"a da Fatan Allah ya rayasu.
Aliyu na Tare dashi a matsayinsa na Amini sai su ya jafar da suka Dawo Daga wajen aiki da yammancin ranar tunda matan suna chan gidan Amina sai suka Sauke gajiyarsu Shashen Mallam nan sukaci abinci suka cigaba da Hira.
Aliya kuwa sai haba haba take da Amina abu kadan tace Amina kaza amina na yankwanata sai da Hanne ta mata mgana Amina ta mata wani kallo kafin tace"Ke ni fa na tsani Cusa kai..Ni ba kawartace ta kama kanta..!
Hanne tace"Kodai yaya ne ki mata uzuru ai don ke tazo.!
Amina ta bangaje Hanne tana Fadin"Naji..!
Hanne ta Bita da kallo Baki Bude akwai Hallayan Amina da Har Abada bazata iya sauyasu ba ance Hali ai Zanen Dutse ne.
Su mamaki ma ta basu da suka ga suna mgana da Sarood Cikin Harshen Labarci wayar Sarood din DanMallam ya Kira yace ta kaima Amina saboda ya yi ta Kiran wayanta bata Dauka ba Shiyasa ta kawo ma Amina ta karba sukayi mganar yace ina ta Jefar da wayarta tace bata sani ba suna cikin kaya mganar komawarsu asibiti yayi bayan yace mata sun yi mgana da Hajiya in sukaje kawai za"ayi ma yaran kaciya ne su Huta Amina tace ba Matsala Duk yadda suka yanke har ya bata Aliyu ya kara mata barka Sannan sukayi sallama ta fita Falo ta Nemo Sarood ta bata wayarta..
Hamida ce sai da tayi mgana ta kalli Amina sanda ta shigo Tana Fadin"Lalle Matar ya Danmallan kece kika kware da Labarci haka sai yarata kuke ke da yar Balarabiyar kishiyarki..!
Amina ta harareta Saboda su Sa"adatu na wajen yasa batayi mgana ba ammh ina ita ina wani Sakin jiki da Sarood ai kishiya sunanta Kishiya duk da tana da Kirki ammh dai kowa yayi ta kansa abunda ya faru agidansu ai Ishara ne ga masu sakarma Kishiya Ragamar gidansa da ya"yansu duk da ba Duka aka taru aka zama Daya ba akwai nagari acikin na banzan ammh Dai na banzan su sukafi yawa.
Sai dare ya Danmallam suka zo da Aliyu da su ya Jafar suka Dauki yaran su ya Aisha na fadin ayi ma yaran alkunya Danmallam yace kul..Da Mallam da Aba za"a dinga kiran su sune alkunyansu Daganan sai suka ja bakinsu sukayi Shuru ranar dai gidan Amina ya Cika da Baki duk nan suka kwana Ya Danmallan kuma da Abokinsa Dakin su Nazeem suka kwana..
Washegari wasu har sun yi shirin komawa irin su ya Zulaihat Sai ga Sakon mallam zai yi mgana dasu Dukkansu anjuma sai tafiya ta fasu kowacce ta Share waje ta zauna aka cigaba Da Hira Saboda an Haadu ba"a son Rabuwa da juna...gidan Amina aka kawo kan ragunan da aka gyara suka Dafa suka ci sannan Naman kuma achan su Mamata suka soya sai da aka musu nasu tunda dagachan aka Rabasa yadda kowa zai shaida harta Aba da Baba mallam an yi musu kullin su na Nama Anty Hadiza kuma ita tayi Yajin jego,zuwa yammah duk sun gama gyara ma Amina gidanta Yakaka ta Dawo ita tayi ma ma Amina wankan yammah ko kafin mangariba duk sun watse sun koma gidan Baba Mallam har su Hanne Amina da Farko Har da sa Rigiman ita ma sai taje Yakaka tace da Danyen Jegon ne zata fara yawo Dole ta Hakura ta koma tana ta Faman gunguni.
Achan gidan ya Danmallam kuwa Ana Idar da Sallar Isha"i mallam ya Hada Taron daya ce za"ayi Sannan har da su ya Nazeem da Uzairu sun iso aranar dukkansu mallam ya kira su yace yana som ganinsu gabadayansu suna Falon mallam illah banda Amina da ya Akila da bata samu zuwa ba sai ya Jadwa.
Ammh harda su ya Danmallan suna wajen,Aliyu dai sun tafi dazu da yammh shi da Aliya,Sai su ya Jafar da ya Nasir ya Nazir shima bashi wajen Tunda bai samu zuwa ba sai Aba sai Jawaad har Anty Hadiza da su mamata mallam yace su shigo Tunda Tunatarwa ne ya kamata suna wajen..
Nasir ne ya Bude taron da addu"an sannan Mallam ya fara jawabinsa da Farko Yayi musu wa"azin riko da Zumuncu da yadda zasu Hada kansu waje Daya su zama Dangi Daya kamar yadda yake fata sannan ya gangaro kan wa"azi kan shirka da azaban da Allah yayi tanadinsa domin masu Hadashi da wasu,Tunda ya fara mgana suka Fahimci inda ya Dosa sai jikin kowa yayi sanyi bai fito ya Fada musu Sakin daya shiga Tsakaninsa da Uwani da Marliya ba ballatana ta Bangaran Aba yadai gyara Zama ne ya Fara karanta musu muhimmancin Uwa ga ya"yanta sannan da irin yadda Annabi ya Fadi Darajan uwa.
Mallam ya kallesu Daya bayan Daya kafin ya Cigaba da Fadin"Ita uwa tana Daraja da kima..Annabi ya ambaci abi uwa sau uku kafin yace abi uba kunga ko ta haka kadai ya isa kusan Tasirin uwa..Sannan duk lalacewar Uwa uwace..Domin ta Dauki Ciki na Tsawon Wata Tara ta sha wahala kafin ta Haifi abunda ke Cikinta ga azaban Radadin Naguda wanda aka Fadama cewa acikin Azaban mutuwa ne aka Dibosa kadan..Kuma dukkanku kusan mutuwa tana zafi da azaba Saboda Alokacin da Annabi Sallallahu Alaihi wasallam zai bar Duniya Sai da ya ce Lalle mutuwa tana da zafi tana azaba da magagi Annabi ma kenan wanda ya kasance Shugaba ne na Hallitun Duniya ya Dandana azaban mutuwa ballata mu bayi da kowa kowan ba..?
To acikin wannan azabar ne aka Dandana ma uwa wajen Haihuwa bayan ta haihu kuma ta fara Wahalan shayarwa da Reno walwalun duniya akanta suka kare taki ci taki sha Duk domin ta inganta rayuwarka Sannan ta Jajirce wajen tarbiya bata barci Saboda ganin ta inganta Rayuwarka komai lalace uwa komai nata kan ya"yanta ne,kuma komai zata aikata mai kyau ko mara kyau ne to bazata Fara Duba kanta ba sai ta Duba ya"yanta ku Saki ranku ku Bude zuciyarku..Ku sani Cewa Uwa ta wuce wasa komai ta Zama awannan Duniyan bai kamata ta Fuskanci Tsagwamma da Kyama awajen ya"yan data Haifa bq ..Ko kuwa kowa zai gujesu bai kamata ku ya"yansu ku juya musu baya. !

Mallam ya Karishe Fada yana nazarinsu ganin yadda Gabadaya Jikinsu yayi sanyi ne yasa ya Cigaba da Fadin"Komai kuka samu anan Duniya baku isa ku biya kwayan Zarra na wahalan da iyayanku sukayi akan ku ba..Sannan kada ku manta Kisaar da wani cikin Sahabai yace ya Dauki mahaifiyarsa a saman kafadansa yayi dawafi da ita shin ko ya Biyata wahalansa da tayi akansa..?.
Annabi ya shaida masa cewa ko Kwayan Zarra bai biyata ba kun ga kenan Allah ne kadai yasan Alherin Uwa ga abunta ta Haifa..Da wannan Tunasar da nayi muku nake Fatan zaku Hankalrta..Uwani da Marliya da Balaraba sun aikata Laifi mai muni ammh kuma ga wajen Ubangiji abu ne mai Sauki in suka Rokesa zai iya yafe musu sannan muma mu sani afuwa da yafiya abu ne mai kyau tunda muma muna kuskure sannan Allah Gafurin Rahimun ne yana yi mana Gafara a duk sanda muka aikata Laifi yana mana afuwa koda Laifin mu yakai Cikin Duniyar nan ne to meyasa mu bazamu yi musu afuwa ba .?
Sai mu barsu su ji da Laifinsu Tsakaninsu da Ubangijinsu,Sannan ku sani aibata su ko gayamusu mummunar kalma bai Dace ba..Ku Sausauuta kalamanku kan iyayanku Domin Fadin mummuna mgana akansu Tamkar ja da hukuncin Allah ne Tunda shi ya Kaddari komai Daya Faru..Daga karshe ina Umartanku Gobe kuje ku Duba iyayanku mata sannan ku Musu kalamai mai Dadi Daga karshe ku yi afuwa ga laifikansu ko Wani Nauyin Zai ragu daga garesu..!

Gabadaya Falon baka jin komai sai Shesshekan kukan su ya Zulaihat Hamida ma sai kuka take jikinta Duk yayi sanyi,Saboda tasan ta aikata kuskure ta yi ta yabama mamanmu manganganu Allah ta Tuba dukkansu haka Suke fada aransu sannan Jikinsu Duk yayi sanyi da Nasihan mallam bayan nan ma Hajiya ta Dora da nata kafin su tashi sai da suka Tabbatar ma da mallan cewa komai ya wuce sannan zasu bi Umarninsa..
Haka taron nan ya tash??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????i kowa jiki ba Dadi alamu nasihan mallam ta Shigi Kowa sannan Hatta Aba yaji Nauyin Zuciyarsa ta Ragu yana Tunanin zai iya yafe ma Mamammu har ya Jafar ma yaji aransa ya yafe mata shi da su ya Jawahir aransu sukaji sun yafe ma Mamanmu tun balle ma da su mamata ke Labarin Halin da mamanmu ke Ciki nan da suka ji Tsausayinta bayan sun Furta sun yafe mata.
Washegari Mota guda sukayi su ya Zulaihat zuwa Gusai har da Ya Jawahir da ya Jalela sukace zasu ce sai ya Sadiya da Jidda da Sa"adatu suka Dauki Hanyar Dutse sai Ya Nazeem da Nazifa da ya Uzairu sai Umaima suka Dauki Hanyar Tsafe sun yi waya da Shamsu zai samesu achan..!
Dukkansu Halin da suka iske iyayan nasu ya Raunana ta su sun kara Tsorata da Duniya Mamanmu nata yafi muni Tana kwance Cikin kashi da Ftsari bata iya mgana abinci ma ko ambata rabi ke shiga Cikinta ba baki ba Ido haka su ya Zeenatu ke kuka kamar ransu zai fita har ta su ya Jawahir sun koka Mamanmu sai dai taji muryansu bata gani sai kuka tana Faman mika hannunta mai Lafiya.
Allah Sarki ya Zeenatu da ya Zulfa da ya Jawahir suka Zage suka gyara mamanmu suka Sauya mata kaya ya Jaleela ta bada shawaran su kaita asibitin Basu ji Haushin kowa ba Ganin yadda aka banzarta da mamanmu ka shuka alheri ma ya ka kare ballatana ka shuka Sharrin
General Hospital Gusai suka kaita Liktoci nata Fadan an bari Jikinta ya Saki agida Dayake akwai kudi nan da nan aka karbeta aka shiga da ita aka Fara bata Taimakon gaggawa su kuma suna gefe suna ta Faman sharan kwallah
Zuwa yammah ta Dan fara Dawowa Hayyacinta sai dai anan asibitin zasu riketa zasu rika yi mata gashin kashi sannan sun saka mata abun Fitsari ta kasanta sannan da Drip wanda zai taimaka ya Dawo mata da Ruwan jikinta Daya zaganye a kwance aranar dai basu samu daman Dawowa ba Sai washegari da Mamammu ta dan Fara mgana kadan kadan tana kuka tana Rokonsu gafara suka Rumgumeta suna kuka suna Fadin sun yafe mata Jaleela ce da Jawahir suka Dawo Gumel aranar saboda washegari zasu tafi? zulfa da Zahra suna chan sai Hamida sai washegari zata koma Zulaihat ma Dagachan ta koma Jigawa sun bar ya Zahra data tambayi Mijinta zatayi sati wajen mamanmu Alla barshi ya Zulaihat zata Dawo ta karbeta sai ita ta koma gida.
Achan Tsafe ma abun ba Dadi Haj.Uwani ciwo ya kusa cinyeta ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login