Showing 237001 words to 240000 words out of 265571 words

Chapter 80 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28938

izinin Lahi bazasu taba ganin gazawarka ba..Allah ya Dauke Hadiza ni kuma nayi alkawarin Zan aura maka wacce ta fi Hadiza komai da komai kamar yadda na aura maka ita da farko..!
Aba ya mike da taimakon Jafar yana kokarin Daidaita yanayin sa yace"Nagode mallam..Allah ya kara Nisan kwana..!
Kawai sai yaji kamar yasaka kuka Baba mallam ya kariso ya rumgumesa yana Buga bayansa Kafin ya Dagosa yana faman share masa hawaye yakuma ja Hannunsa suka fice Daga Falom aka Bisu da kallon Tsausayi da kauna.
Su ya jafar ma suka mimmike da su Aliyu jiki duk a sanyaye Ya Danmallan ne ya isa wajen su Hanne yana Fadin"Noor ki bar wannan kukan kinga fa bake kadai bane..Sake su..Ku saki juna hakanan..!
Jin muryansa y???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?asa suka saki juna suna kuka Sai suka basa Tsausayi sai ya fara rike hannun Amina sannan ya rike na Hanne da Hamida ya jasu har gaban Hajiya yana fadin"Hajiya ki yi abunda kika saba..!
Don Allah kice subar kuka in suka bari Noor zata bari itama..!
Hajiya tayi mirmishi ta Karbi Hannun Amina kafin ta karbi nasu hanne Hajiya Nasara tataso ta karbesu tana Fadin"kada ka damu Danmallam bazasu kara kuka ba Insha Allahu..!
Ya kalleta kansa na kasa kafin ya juya yabi bayan su Nasir da suka fice tun dazu.
Aka bisa da kallo sha"awa irin su Anty Amarya kuma sai kunci da Nadama mara amfani.
Hajiya ta tasa su Amina Cikin Dakinta ta Kira Yakaka dasu Aisha tace su lallashe ita kuma ta koma Falo tace a kwashe kayan Amina akai Dakinsu Hanne..
Yan gusai kuma suka koma gidan Aba suma da su ya zulahait domin Hamida ce kadai tare da su Amina Su ya jadwa ma suna Shashen Hajiya suna faman kuka su kuma sai suka koma gida suka Hada kai suna ta kuka ya Zulfa da ya Zeenatu da ya Zulaihat sai yaya Zahra bamai lallashinsu su kansu yan gusai sai Tofin Allah tsine suke yi ma Mamanmu.
Kamar wasu marasa galisu haka akayi banza dasu Haj.Uwani ta fara rarrafawa ta Fice cikin kunya da kuka sai Anty Amarya da ta fita tana kuka sai Mamanmu kallo arziki ba wanda ya kara yi musu har suka shige shashensu Daga Anty Amarya har Haj.Uwani Datse shashensu sukayi suna ta kuka ita Anty Amarya ba yan"uwanta duk suna asibiti wajen Sakina da tayi bari ita kuma Hajiya uwani Daga ita sai Umaima dake kwance batasan meke faruwa ba su Nazifa bata san ina sukayi ba,Bata Tunanin ma zasu nemeta nan kusa.
Mamanmu kuma fakaitan idon mutane tayi ta shige Dakinta chan kurya tana kuka saboda yawanci bakin suna Dakin yaya ne yaran kuma suna Dakin su Amina kowacce tana Ciki tana Dirzan kukan nadama da nasani da kuma rashin madafa Daga mallam har Aba basu ce musu komai ba ballatana su san ina matsayinsu.!
Su Amina kuwa Dakyar suka Daina kuka suka koma ajiyar zuciya.Yakaka tayi ta kokarin Lallashinsu.
Sannan su kansu ya Jadwa sai da Hajiya tayi ta musu nasiha suka Saurara sannan Hidiya matar Nazir da Aliya matar Aliyu na tare dasu ita duk ta tsorata tasan tana da Zafin kishi ammh bata san Bin malamai ba..su matan su ya Jafar ma suna nan tare dasu Sarood Hajiya Nasara ta kaita Shashenta Hayaniya ya saka mata Ciwon kai,su fatima na Tare da ita suma duk jikinsu yayi sanyi sun kara Godema Allah Daya tsare imanin Mahaifiyarsu domin ba wayau bane kuma ba Dubaransu bane.
Su ya Danmallam kuma suna Shashen mallam,shi da Jafar da Nasir sai Nazir,Aliya su shamsu dai suna Dakim su Nazeem sun kulle kansu Nazifa dai Ta koma Shashen Hajiya Nasara bayan sun gama kukan nasu.
Su kansu zaman jugun jugum duk Dauriyan mallam Lamarin ya tabasa shi da Aba sai dai yayi kokarin nuna komai ba komai ba sabida Aba da su ya Danmallam.
Mganar Daurin auran gobe suka Tattauna Daganan ya Sallamesu dukkansu ba wanda yayi kokarin komawa gidansa duka nan suka kwana Har Aba da su ya Danmallam shi da Aliyu da Nazir a falon mallam kamar kwanan zaune ma sukayi su ya Nasir ne da Jafar suka kwana Dakin samarin gidan su Akilu da suma Jikinsu duk yayi sanyi har garin Allah ya waye ba wanda ya saka wani abu acikinsa ko su kansu matan sai da Hajuya tayi ta Fada ne suka sha Tea har su Amina.
Mazan kuma da Safe kowanne ya koma gidansa Ya Danmallam shi da Aliyu da Nazir gidansa suka tafi suka natsa kafin Lokacin Daurin aure kowa kagani ba walwala.
Ammh Danmalam bai tafi ba sai da ya leka Amina ya tabbatar da ta daina kuka sannan tana Lafiya.
Chan gidan Aba ma haka aka tashi Goggo Husai ne tazo ta zauna dasu Zeenatu tana nuna musu suyi hakuri Laifin Balaraba bazai shafesu ba su yi Hakuri Bikin kanwarsu ake yi to da hakane suka samu suka karya da Safe har suka Dan saki jiki Mamanmu kuma bana wanda ya san tana gidan ballatana abi ta kanta ta kwana kuka ta kasa fitowa ta zama mujiya yau gashi Bikin data cima burina ne ake yinsa ta zama kamar mujiya Cikin mutane.
Haka ma bangaran Anty Amarya ita Kadai kamar mayya ta gaji da kiran wayoyin su Jidda sun ki Daga kiranta Har ta A"i taki Daukan wayanta ballatana taji wani Hali sakina ke ciki ta rasa ina zata saka kanta taji Dadi har Sabeeha bata nan sun tafi da ita.
Hajiya Uwani kuma kafin Safe har ta Rame saboda tashin Hankali sannan tayi ta kiran Batula bata samu ba tana so ta Sanar da ita komai fa ya Tsaya.
Alokacin Datake kiranta ita ta kama Hanyar Minna domin taje ta aiwatar da gudurin Uwani bata sani ba,Ajalinta ne yake kiranta.
Domin sun fita Tsafe ba Dadewa suka samu Mummunan Hatsari da yayi Sanadiyar rasa rayuwakan mutum Hudu Dake motar har da Batula aciki..!

Sai da Hajiya ta saka baki sannan su Ya Aisha suka Tafi da su Amina gidan su ya Jafar saboda su Shirya Sa"adatu kuma Mallan ya kira Jidda yace Sa"adatu ta Dawo gida ko batasan yau za"a Daura mata aure bane..?
Ba Dadewa suka Dawo ita da Sadiya fuska duk ta Kode saboda kuka gidan su ya Jafar suka wuce tunda chan zasu shirya kafin Daurin auran.
Anan ne su ya Aisha ke jin Labarin Sakina cikinta ya zube sannan tana chan ana mata karin jini bata san inda kanta yake ba.
Sadiya ke maida musu zencen tana kuka su ya Abida na Faman bata baki Amina kuma na tare da su Hanne ita yanzu tama Daina kukan Hamida ce sai Ahankali ita da Hanne suna ta faman bata Baki ammh Taki sakin jikinta gashi ana Daura aure za'a tafi Dasu mallam yace bamai Daga wannan auran.
Baba Mallam da Aba tun safe suka fita ba wanda yasan inda suka je sun dai yi mgana da Hajiya kafin su fita Sannan har yan bazanga da bakin gusai suka iso maza basu dawo ba sai wajen 12,da rabi na rana suka Dawo Shima Baki akayi daga maiduguri wani kawun su Hajiya sai D'ansa guda Daya wanda ko Hajiya bata san da zuwansu ba.
Ashe Labarin abunda mamanmu ta aika yaje kunnen su kawu Salisu matan sun kirasu sun Fada musu komai,Kawu Salisu sai Fada yake yi yanaCema Aba ya saki Balaraba taje duniyace Mallam ne ma ke basa bakin kan mganar Aba dai bai ce koma ba ai ko bai ce balaraba ta bar mai gida ba in Tana da kunya basai ma ta jira yace ba zata san inda Dare yayi mata.
Zuwa Lokacin Yan Daurin aure sun fara Zuwa Mutanen Yola ne suka fara zuwa da Mata guda biyu suka zo aka kai su Shashen Hajiya sai yan Zaria suma sun Iso da mace Daya.
Na gombe ne karshen isowa su kan maza ne kadai suka iso banda mace ko Daya.
Amaran nachan gidan ya Jafar an samu sun yi wanka sun saka wani Less din da Mallam ya Dinka musu mai Fari da Golden sai Hijabansu mai ruwan kasa Itama Amina ta shirya Cikin leshinta mai Tsada da ya Aisha ta Dinka mata iri daya da ita har da Yakaka sai dai ita Bubu tayi saboda Cikin jikinta kowa ka gani ba walwala ido Duk ya kumbura.
Su ya Zulaihat sun zo da Safe suka Hade dasu Hamida da Amina suna ta kuka dasu ya Jadwa suna ta basu Hakuri su kuma suna cema musu ba Laifinsu bane sai da ya Aisha tace zata Kira Hajiya sannan suka sarara.
Misalin karfe Daya da wani abu na Rana Kofar gidan mallam ya Cika ba matsaka Tsinke su ya Danmallam sai Lokacin suka iso Cikin shigarsu ta alfarma haka ma su Ya Jafar mallam ma da Sabuwar shadda da rawani haka ma Aba kowa dai yayi kokarin Boye abunda ke ransa har da su Nazeem kuwa.
Alokacin kuma Hajiya Uwani ta san da abunda ya faru da yar"uwarta Batula sai ta rude kuka kamar zata Haukace bata tsaya neman kowa ba ta Hada kayanta Ko Umaima bata Tsaya bi ta kanta ba,ta ma bar Shashen nata tana Shashen Hajiya ta shiga Cikin yan Biki ita kadai ce batasan me ya faru ba mutane sun yi yawa yasa har ta fito ta tari abun hawa ta hau zuwa Tasha ba wanda ya lura da ita ammh Nazeem ya ganta sai dai bai nuna ya ganta ba yana Tunanin abunda ya Dace da ita kenan ya Dauka ta neman ma kanta mafita ne kafin mallam ya koreta.
Anty Amarya kuma tana Shashenta ko kare bata kara gani ba,kaf Danginta suna asibiti wajen sakina su jidda kuma suna Tare da Sa"adatu domin cire mata Damuwar dake damunta duk da suma karfin Hali ne Mamanmu kuwa Sai da ta raina kanta Har Daki yan Gusai suka Bita suka mata tsofin Allah Tsine shiyasa ta kasa Fitowa Tayi kuka har ta bama uku Lada yan"uwanta sun Tsine mata kamar me sun ce ana Gama Biki yau gobe zasu koma sannan sun ga karfin Halinta Data iya Takowa gidan Sa"idu..
Ita kuma tana Tunanin ina Zata..?
Bata da inda zataje a karbeta Ta riga tayi ma rayuwarta mummunan Tabon da har Abada bazai goge ba.
Karfe Biyu aka Dauran auran su Hanne,Na Aba aka fara Daurawa da Hadiza Babbar Diyar kanwar Hajiya Yagana Datayi aure mijinta ya rasu bata kuma taba Haihuwa ba..!
Hadizan ma da ita aka zo Biki Suma kansu basu sani ba sai da aka Daura shi ya kawo kawun Hajiya Tun Daran Jiya mallam ya kirasa yamai bayani Tun Safe kuma suka Biyo Jirgi Daman a Bauchi yake da zama shi da iyalansa. !
Daurin auran daya bama kowa mamaki Hajiya kam Bakinta yaki rufuwa Mallam a koda yaushe Tunaninsa mai kyau ne

Daga nasa sai na Hamida sai na Sa"adatu na hanne ne na karshe Bayan an Daura auran aka shiga taya juna Murna ya jafar yayi mamaki Lokacin Daya ga wanda Hanne ta aura har ya bashi Hannu sukayi musabaha bai daina mamaki ba.
Har sai da shi yace mai""Ya jafar Allah ya Rubuta Amina ba matata bace..Hannatu ce matata..,!
Ya jafar ya jinjina kai aransa yana kara yima Allah kirari.
Su Danmallam suna cikin jama"a suna ta Faman gaisawa da mutane Bakinsa har Kunne shi da Aliyu,da Nazir nan kasan ransa Halin da Amina take Ciki yake so ya sani Sakina kuma bata gabansa bai san Halin Datake Ciki ba Sannan basu kirasa ba shima bai nemi kowa ba.
Suna cikin gaisawa da Mutanan ne ya Hango Amina suna tafe ita da Zafira Amina ta saka Hijabi mai Ruwan Sararin Samaniya kalan leshinta da Takalminta mai Saukakan Tudu tana Tafiya cikinta yana gaba da ita Saboda Girmansa har suka shige gidan mallam
Ayadda Danmallam yaga Fuskarta ta Kumbura ne yasa Hankalinsa ya tashi yaja Hannun Aliyu suka bi bayansu Baya son yaga Amina na cikin Damuwa,suna shiga kuma haraban gidan yan bazanga suka taresa ana ta gaisawa yasa basu samu karisa cikin gidan da wuri ba.
Amina kuma daman Ya Aisha ne tace Hajiya na kiranta, taso ta jira su taho dasu Hanne suna Sauya kaya yasa tace Zafira ta rakota su suna chan ko Mganar auran Aba din ma basu sani ba sai bayan tahowarta sannan Anty Fadila take fadamusu itama Mijinta ne ya kirata ya Fadamata.
Amina har ta shiga Shashen Hajiya ta zama abar kallo da Sha"awa suna shiga Falon cike da jama"a.
Da Hajiya suka ci karo da ta fito Daga Dakinta Taci gayunta itama bakinta Har kunne Amina suna gaisawa da yan Falon yawancin yan"uwan Hajiya ne taga dai ana nuna tw ita bata san me ya faru ba.
Yakaka ce Amina ta Hango zaune itama ta sha gayunta ta karisa suka gaisa Yakaka na fadin"wasu baki ne suka zo suna son ganinki..Hajiya ta saka aka kiraki..!
Hajiya ta kariso wajensu zatayi mgana kenan sai ga wata Farar mata gajera ta fito Daga Dakin Hajiya bayan ta wata mata ce itama suna yanayi sai da tana dan tsawo ita.
Hajiya na ganinsu ta juya tana Fadin"Yauwa Nenne ga ma Aminar nan ta kariso..!
Ta fada tana riko Hannun Amina har gaban matar da Amina ta kasa Dauke Ido a kanta.
Wacce aka kira da Nenne ta Rike Hannun Amina cikin Fara"arta take Fadin"Allahu akbar Rahina..Kinga Aminar Aminullahi..Allah ya rubuta Ba matar sa bace..Rabo ne rabo ne ya Haddasa abubuwan da sukayi ta Faruwa..!
Wacce aka kira da Rahina tabi Amina da kallo Kafin tace"Ba Shakka yau naga Amina..Aminar da kaf Danginmu ba wanda bai santa ba..Sannu Amina Allah ya raba Lafiya..!
Tafada tana kallonta sai Amina ta kasa mgana ta koma tana Binsu da kallo Hajiya tace"Bafa ta gane ku ba inaga sai kun mata bayani..!
Tafada tana Dariya.
Nenne ta kara rike Hannun Amina Tana Fadin"Amina baki gane ni ba ko..?
Ai nasan baki sanni a Fuska ba sai Muryata..Nice fa NENNE..Nennen Aminu fa..!
Sai alokacin Amina ta Gane ina ta san muryan Ido ta waro kafin tace"Nenne..!
Nenne na Dariya tace"Alkwarin Allah ya Cika Amina..Aminu da bai Sameki ba..Sai Allah ya kaddara yar"uwarki Hannatu ce RABONSA..!
sai amina ta kara zaro ido Cikin mamaki bata samun Damar mgana ba Ya Danmallam da ya Aliyu suka shigo Falon bayan su kuma ya Nazir ne yana Cema yan Falon Tawagan Angon Hannatu zasu shigo su gaida su.
Sai Amina ta juya suka Hada ido da ya Danmallam ya sakar mata ido ita bashi ma take kallo ba Wanda ya shigo ne cikin Farar shadda da babbar Riga shi da wasu maza su uku.
Su ya Danmallam suka basu waje su ka kariso tsakiyar Falon suka Duka suna gaida wadanda ke falon.
Kan Aminu na kasa ne Yaji Nenne na Fadin"Aminu yau dai naga AMINA..yau naga Amina..!
Take fada Hakoranta duka suna Waje..Atare Aminu da Danmallam suka Dago kansu.
Shi Danmallam Wanda aka kira da Aminu yake kallo shi kuma Aminu Nenne ya kallo sai kuma karaf suka Hada ido Hudu da Amina..
Mennarsa da rashinta yasa kadan ya Rage bai Haukaace ba itace agabansa ta Sauya har da Tsohon Ciki ma ajikinta..!









*Janafty*

*TFZB2028*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*


Aminu kallon Amina yake yi da wani mamaki a saman fuskarsa yana mamakin ganin sauyawarta da komai ma acikin shekaru biyu da wani abu daya shafe bai ganta ba abunda yasa ya kasa daina kallonta Katon Cikin Dake jikinta wannan ya kara tabbatar mai da gaske ya rasa Amina rashi na har Abada..!
Shi kuma Danmallan kallon Aminu yake da wani abu acikin ransa kamar almara sai yaji ransa na kuna da wani kishin Aminu acikin ransa in ya tuna abubuwan da suka faru sannan Abaya Amina taso Aminu shiyasa yaji wani Duhu ya mamayesa na ganin Aminu da irin kallon dayake bin Amina Dashi ko shi mallam bai tattauna dashi kan wanda Hannatu zata aura ba abunda a bazata yajisa.
Aliyu dake gefensa shima Aminun yake kallo saboda ai shima yasan Labarinsa sai da Dariya ta kusa kamashi yadda yaga Shehi yake kallon Aminu kamar zai shakeshi yana Faman sakin Huci Sama sama.
Aliyu ya raba ta gefen kunnensa yana Fadin"Cool Down mana Shehi..!
Hararansa yayi kafin yace"Ta ina naga Wani Cool down baka ga yarda yake ta kallemin mata bane..?.
Ko ba auran Hannatu a kansa bai san Noor ta Haramta garesa bane yake binta da kallon Daya wuce ka'ida..?
Aliya na Danne dariyan sa Lokaci Daya yana Fadin"Yi hakuri zai bari..Kallo Daya ne fa na Musulunci..!
Wani Kallo da yayi ma Aliyu sai da ya matsa yana Dariya lokaci Daya yana Fadin"Ana Asif..Shehin Amina..!
Kwafa Umar yayi bai kara mgana ba Amina yake satan kallo ransa yayi fari Daya ga bata kallon barayin Aminu yanzu sai ya karkata yana kallon Aminu sai yaga kansa na kasa suna mgana da wanda ke gefensa ajiyar rai yayi har yana Hararan Aminu ta gefen ido Aliyu na ankare dashi yana Dariya aransa yana Ayyana wani irin so Shehi ke yi ma Amina..?
Bai taba ganinsa ya nuna kishi kan abu ba sai ayau din nan.
Nenne kuma na rike da Hannuwan Amina Fara"arta taki gushewa sai Faman washe baki take yi har gaban su Aminu dake Durkushe shi da Nura da Abokin aikinsa Oscar duk da yanzu ya Daina waka ammh ana tare ba"a rabu ba.
Har gabansu takai Amina tana Fadin"Aminu kaga abunda nake fada maka ko..?
Na sha Fada maka Allah ya Boye wani abu Tsakaninka da Amina saboda irin son da kayi mata..Rabo ne..Wannan Rabon ne ya raba Tsakaninku sannan da kuma Kaddaran auran yar"uwanta Hannatu Allah mai iko Amina..Rahinatu kin ga Ikon Allah ko..?
Rahina ta jinjina kai kafin tace"Nagani Allah ya rabasu lafiya. !
Ta amsa da Ameen Aminu dai kansa na kasa ko Dagowa bai yi ba Amina na haka ta kasa sakewa sannan mamakin yadda al"amura suka juye basu barta ba.
Nenne tace"Ina mijin naki Amina..?
Ance Babban yaron Hajiya kike aure wanda ke zaune a madina ko..?
Kai kawai Amina ta iya Daga mata Cikin Fara"a Nenne tace"Yana ina..?
Ina so na gansa ne mu gaisa..?
Amina ta Dago kanta tana kallon Dannallam da yayi saurin Dauke kansa Dukkansu suka bi wajen da kallo har shi kanshi Amunun Daidai da karisowar Hajiya wajen Dazu ta bar Falon ne sai yanzu ta shigo Nenne na ganinta tace"Hajiya wancan ne Mijin Amina..?
Ta fada tana nuna barayin da su Danmallam suke Hajiya ta murmusa kafin Tace"Eh Shine..Danmallan ka kariso ku gaisa da Mahaifiyar Aminu wanda ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login