Showing 180001 words to 183000 words out of 265571 words

Chapter 61 - TA FITA ZAKKA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Dec 2024

28921

karisa gabanta ta mata sannu Dr Isa ya taso ya kara Dubata ya tambayeta me take ji tace ba komai jikinta ya rage Zafi Zazzabin ya Sauka mganganuna ya Rubuta mata ya Sallamesu sai ga Amina na takawa da Kafarta har wajen mota sai alokacin hajya ta kare mata kallo Taga Cikin da Likita yace yabi Jikin Amina Allah mai iko Annabi mai Dumbin Daraja.
Basu tafi ba sai da ta Kira Nasir yazo haraban asibitin ya same su koda ya Tambayi Hajiya me likita yace sai taki Fadamai ta dai basa Takardan mganin daya bata shi kuma yace ta Jira yaje ya siyo ba Dadewa sai gashi ya Dawo da Ledan mai Tambarin General Hospital Gumel.
Shi Nasir bai wani tsaya duba takardan mganin ba shiyasa bai Fahimci ko na menene ba.
Daganan sukayi sallama bayan ya leka Motar yayi ma Amina Sannu ta amsa tana Dagamai kai.
Har suka kai gida Hajiya ta kasa gasgasta abunda taji Aranta kawai sai ta shiga wani Tunani Tsakanin miji da mata sai Allah bata Zargin Amina har ga Allah sai dai kuma likita yace Cikin Jikinta wata Hudu da kwana goma sannan in ta Lissafa dai dai Danmallan shima nada wajen wata hudu da sati Biyu in bai fi ba da komawa Madina,kenan kafin ya tafi ne in ma wani abun ne ya shiga Tsakaninsa da Amina Allah mai iko sai abun ya bata mamaki matuka.
Sanda suka Dawo Mallam bai fita ba ammh yana Sauri zai je Fadar Sarki ana nemansa shiyasa bai Tsaya ma sun yi mgana da Hajiya ba ganin Amina Taji Sauki har gata ma tana Tafiya da kanta kuma cikin ikon Allah har suka kai Shashen Hajiya basu hadu da kowa ba.
Suna shiga Hajiya bata Zauna ba ta Hado ma Amina tea mai kauri ta matsa mata tasha ta bata mgungunanta duk yawancin na karin Jini ne sai na Vitamin C da polic acid na masu Ciki sai kuma panadol sai da ta sha ta natsu Fatan ta kada tayi Amai sai kuma Allah yasa batayin ba.
Hajiya ta rakata Dakin su Hanne ta kwantar da ita kan gado sannan ta Zauna gefenta tana kiran sunanta Aminaa na kokarim mikewa Zaune Hajiya tace ta koma ta kwanta.
Hajiya ta kalleta Cikin ido kafin tace"Mama kinsan me Likita yace yana Damunki..?
Amina ta girgixa kai kanta a kasa Hajiya ta gyara Zama kafin tace"Yace Kina CIKI har na Tsawon wata Hudu da kwana goma..!
Dam!!!
Gaban Amina ya fadi ta kalli Hajiya da Kumburarrun Idanuwanta ta maimaita Cikin mamaki "Ciki ...?
Hajiya ta gyada mata ai sai acikin Ran Amina tayi wata Hamdala ta yi kabbara ta sake yin wata kabbara domin mganar mamanmu take Tunawa da tace bazata Haihu da Ya Danmallam ba sai Sakina sannan kuma auran haka zai kare ba Fa'ida Ashe ashe basu sani ba Allah ya Riga yayi ikonsa..!
Ganin kamar bata wani Razana Sosai bane yasa Hajiya tace"ko kin san da shi ne Amina baki Fadamin ba..?
Amina na sharan Hawayen data rasa ko na Dadi ne ko na Murnan Karshen mamanmu da Anty Amarya yazo ne. Bata sani ba cikin kukan tace"Wlh bansani ba Hajiya bansani ba..!
Hajiya ta Dafa hannun Amina Kafin tace"Basai kin Rantse ba nima da naga Jiya naga yau ban gane ba sai ke yarinya karama Mamah..?
Yi shurunki..!
Hajiya ta fada tana Faman share ma Amina Hawaye Tsausayinta na kamata.
Hajiya ta Dakata tana Fadin"Tambayarki zan yi Tsakaninki ga Allah Mamah..kada kiji nauyi na ina so na gasgata wani abu ne..
Shin Kafin tafiyar Danmallam wani abu ya shiga Tsakaninku ne..?
Ai sai Amina taji kamar kasa ta Bude ta Shige sai ta juya baya ta Dunkule kanta tana mai jin kunyar Hajiya abunda ya faru Tskaninta da Danmallam yana Dawo mata kamar a jikin magiji.
Hajiya ta Daga hannu tayi kabbara Tare da Hamdala ta mike tsaye ta Fice Tana Mai Farinciki wanda ya kasa Boyuwa a saman Fuskarta.
Tana fita Direct Dakinta ta shiga waya ta Dauka ta Kira Danmallam bakinta kamar Gonar auduga saboda Murna

Yana gida bai fita ba yaga Kiran Hajiya sai da gabansa ya fadi suna Falo Tare da Sarood ne ya barta ya shiga Cikin Bedroom dinsu,kafin ya Katse kiran yabi bayan kiran Hajiya Tana Dauka ko amsa sallamarsa batayi ba tace"Danmallam kana jina..?
Cikin Wani yanayi yace"Ina jin ki Hajiya..!
Ta cigaba da Fadin"Tambayarka zan yi kuma ina so ka fadamin gaskiya..!
Zama yayi gefen gado yana fadin ina jinki Hajiya..!
Hajiya tace"Wani abu na auratayya ya Shiga Tsakaninka da Amina ne kafin tafiyarka.?
Ina kasa ta Tsage Danmallan ya shige ya kasa mgana gabadaya sai jikinsa ya Fara rawa kamar yana gaban Hajiya,Ya kasa mgana ma kamar ya kashe wayar haka yake ji meya kawo wannan mganar..?
Badai wani abu ne kuma ya faru ba..?
Jin yayi shuru yasa Hajiya tace"Amsar ka tana da muhimmanci Danmallam..!
Muryansa a shake yace"Ehhh..!
Hajiya tace"Allahu akbar Sarkin gagara Misali..UMAR? ka godema Allah..Amina nada ciki har na Tsawon wata Hudu da kwana goma cikin ka Umaru..!
Haka yaji Hajiya tace kafin ta katse kiran sai ya fara Tunanin kodai bai ji Daidai bane..?
Wata Aminar ke da Ciki..?
Kwakwalwarsa ta Fara Hasko masa Amina ita ce ke Dauke da Cikinsa kuma ya Tabbata Hajiya bazata Kirasa tamai wasa ba..!
Allahu akbar ya furta sau uku ashe Ashe Daman wannan kwan Hallitar yasa tafiyarsa bata yuyu ba aranar? Allah ya Kaddara mahaifan Amina Zata Dauki wannan hallitar shiyasa tafiyarsa bata samu ba sai da ya Dawo gida sannan cikin abunda bai Tsammani ba ya tara da Amina ashe ashe ya saka mata kwan haihuwa ashe ashe ya zama Daya da ita baisani ba..!
Wannan shine ake kira Zanen kaddaran..?
zakaran da Allah ya Nufa da Cara ki ana muzuru ana shaho sai yayi.
Yau Cikin Farinciki suka tashi shi da Sarood na warkensa gabadaya jiya ya tabbata namiji ga Sarood ya maida ita mace shiyasa bai fita ba ya Zauna yana kula da ita Allah yayi gaskiya Qur"ani waraka ne bai san Sadda ya Durkushe a saman cafet din Dake Bedroom din ba ya Daidai ci gabas yayi Sujudul shukur Muryansa cikin Zaki da gardi yake fadin.

"Alhamdulillah..Alhamdulillah..Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban Halittun duniya Annabi muhammadu Sallalahu alaihi wasallam.."






*Janafty*

*TFZB2015*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*



Hajiya na fita Daga Dakin Amina ta Dago kanta sai da ta tabbatar da Hajya ta shige Dakinta sannan ta Mike Zaune kan gadon ta yaye rigar kikinta Cikinta Daya fara tasowa kadan take kallo sai da ta kuramai ido sannan ta Fahimci ba"a sama yake ba yana kasan maranta ne dan tasawar da yayi ashe ashe ba Timbi bane kamar yadda suke Tunani ita dasu Hanne Ciki ne na Haihuwa..?
Ita yau Amina ke da Ciki zata Haihu..? Yau ina yaya take..? Bata raye saboda haka bazata ga wannan ranar ba..?
Mamanmu ta rabata da yaya Har gaban Abada mamanmu bazata ga Daidai a Rayuwarta ba Tana hawaye tana shafa Cikinta Daga jiya zuwa yau wanu Tsanar mamanmu ne ke yawo acikin ranta Tsanar da ko Anty Amarya bata yi ma irnsa ba Domin ta Cutar da Rayuwarta tundaga matakin Haihuwa har zuwa jiya da asirinta ya Tonu Shafan Cikinta take yi ta ke taji wani kaunarsa na mamaye aranta Dariya tayi acikin Ranta tana Hango Amina da y'a tab lalle za"a ga uwa anan wajen Sun so su hana ta Tarewa auran ma ba da son ransu bane sai dai In dan Rana ta fito tafin Hannu bai isa ya kareta ba Allah yace kuma ya isar da Cewarsa Hawayenta ta share wani kunci na Shiga aranta Tana Dafe da Cikinta tace"Allah ya kare min duk abunda ke Cikina..Allah ba ikona bane ko Dubarata ba ne da ka bani wannan kyautar ajikina kuma ka karesa batare da kowa yasan dashi ba Ya Allah ina Rokinka da kariyarka ka cigaba karesa har ya fito Duniya domin Fitowarsa Duniya ko bayyansa Shine Zai Taimakamin wajen Tona ma mugaye azzalumai asiri mara sa Tsoron Allah Kamar yadda suka ce na Ratso aikin su batare da sun sani ba nayi alkwarin Dawowa Amina Sa"idu gusai dina mai Biyayya da ladabi Mai Tsayawa ga Kafafunta nayi alkwarim Daga yau bazan kara kuka Domin na gaza ba sai domin imanin ka ya Allah ka Tsareni da Tsarewarka kabani Kwarin gwiwan da zan bankada Azzalumai dani suke zencen mu zuba mu gani shege kafasa Aminene nike kirarina badai ta mutum ba sai ta Allah..!
Ta karishe fada Lokaci Daya wani karfin gwiwa na shiganta Tsoro yana barin ranta son Cikinta da son ta Rainesa ya fito Duniya ya Zauna aranta Abu Daya take son gani Tozartan Mamanmu da Sauran masu mugayen zuciya irin su Anty Amarya da Haj.Uwani yau gata da ciki in sun isa su hana Allah ya ikonsa ashe karyan Boka da mallam suke tunda suka kasa bankado musu wannan sirin Shashashan banza azzalumai Da Yardan Allah karshen ku yazo ku Fara Kirga Lokacin da zaku wulakanta.


Hajiya ta rasa ina zata saka kanta Saboda Farinciki,Ta kasa zama ta kasa Tsayuwa waje daya ta Daga Hannunwanta duka biyu sama tanayima Allah kirari domin wannan shi ake kira tsammanin Abunda baka yi Tsammani ba.
Hajiya ta rasa da wa zata ra ba wannan Farinciki na ganin Amina Dauke da cikin Danmallam ta Dade batayi farimciki irin na yau ba gashi mallam baya nan balle ta ruga ta Fadamai suyi wannan murnan tare yaya kuma bata Raye balle ta Ruga ta Fadamata Amina zata zama uwa nan bada Dadewa ba Amina zata koma yadda take so sai Bata a duniya lokacin da hakan ta faru sai dai tana Fatan Ta cikin samu salama acikin kabarinta har Abada.
Haj.Uwani ta Fado mata arai itace tafi Kusa da ita in wani abu ya sameta bayan mallam da Sa"idu itace ta ukun Datake sani yasa ta kwashi Sauri zuwa Shashen nata bakinta kamar zai tsage Saboda murna.
Koda ta shiga Falon ba kowa tsit tana Tunanin kila tana ciki ne yasa ta yi sallama sai dai ba"a amsa mata ba ta Bude baki zata sake wata sallama ne Taji Muryan Haj Uwani cikin shewa da Dariya tana Fadin"Batula naso kina wajen nan kiga idanuwan marliya gaban mallam da Hajiya..?
Kinga yadda ta muzanta ba halin ta Fadi wata mgana na riga na gama Daureta da Jijuyoyin jikinta..sai uban kuka take yi mallam kuwa yayi mata Fata Fata Hajiya har da yar Nasihan kan Marliya ta Daina bin malamai wlh Batula naso kiga yadda marliya ta koma abun Tsausayi..!

Shuru na wani Lokaci ya biyo baya Hajiya bata Fahimci kan zencen ba ganin kamar tana waya da Yar"uwanta Batula yasa Ta juya da niyyar Barin Falon AllaH barshi ta Dawo an juma ko in ita Uwanin ta shigo sai ta Sanar da ita sai dai tana Daga kafarta da niyar Fita taji Uwani na Fadin"Haba ni ce fa Batula kar kin manta ni..Ai marliya bazata kara kiran mai alewa bata da kudi ba..Alokacin da nake fadama Marliya Irin Tuggu na sai ta ga nata ai bakomai bane Batula na Fadamata zan yi shekaru aruru ina bin bayan Hajiya ne kamar wata Sakarya..?
Na Fada mata na riga fara aiki akan biyan Bukata saboda haka sai da ta hakura da nata Cikar Burin ta barni na cika nawa in burina ya gama cika zan sallameta sai ta nuna Taurin kai cewa ita bazata yarda ba sai na Fadamata me nayi ma Sakina da yasa ta ke Barin duk cikin data samu. ?
Nace mata ta kwantar da Hankalinta ba Sakina kadai ba, har ita Balarabiyat da ita kanta Aminar ko sau D'ari zasu samu Ciki sai yabi Rariya alkawari ne na Daukan ma kaina Nazir ya fara Haihuwan ma mallam Jikiko guda Biyu hakan ya Zama kuskure ammh yanzu bazan kara maimata kuskure na ba..Duk da Haka sai da nasa aka maida su mara sa amfani a wajen mallam kamar yadda aka maida Nasir yanzu abubuwa nawa akeyi agidan nan kafin kiji mallam ya kama sunansa an Dade..? Kamar yadda na saka Mama ta sa Nazir yayi nisa da Gumel din da har Abada bazai iya zama na Sati Daya acikinta ba na saka ta Lula kurciyar Danmallan madina yadda bazasu zauna ma agarin bama ballatana Mallam ya gansu ya ce zai Dorasu kan dukiyarsa Batula kin san yadda na sha Wahala shekaru aru aru kan ganin ya"yana akan gaba akomai agidan nan to Wahalata ta kusa zuwa karshe Nazeem sauran kadan ya karisa ya Dawo uzairu kuma yana Bautar kasa kafin ya gama Nazeem ya Dawo daganan zan Dora harshashen Burina ya fara cika ga Shamsu shima ya fara nasa karatun kina ganin zan bari marliya tazo ta rusamin Shirina na ne..?
Shine na Tauna Tsakuwa domin aya taji Tsoro Batula na tabbata na Saka tsorona azuciyar Madina,bama ta da wayau ne ni da ya kamata ta godemin Batula..? Nan ta maida balarabiyar nan kamar Hoto wajen Umar kan Tariyan Amina kuwa babu abunda basu yi ba ita da mai tayata din saboda kar ta tare ammh sai da ta taren sai ni kuma na karisa musu aikin na Dorata kan Tsarin dana Dora Sauran..Domin na Riga na fadamata indai ina Numfashi Cikin matan Umar ba wacce ta isa ta Haihu ya"yana basu fara Haifama mallanm jikoki ba Domin Tunda Mama ta Fadamim mallam ya son ganin Ya"yan Umar tunda yafi soyuwa wajen ya'yansa ni kuma na mike Tsaye na hana Faruwar hakan sai dai ya Mutu bai taba Haihuwa ba batula. !

Hajiya tsabar mamaki da Rudewa sai da ta Bude baki kamar sau goma tana Rufewa Jikinta yayi wani irin sanyin mamaki da al"ajabin jin kalaman Dake Fitowa Daga Bakin Uwani Duniya Haka ta lalace bata sani ba..?
Kana Zaune da Mutum Tsakani ga Allah shi kuma yana nan yana Cutarka ta karkashin kasa duk da bata Fahimci wasu mganganun ba ammh ta Fahimci Daga marliyan har Uwanin basu da zuciya mai kyau sannan Duk Jirgi Daya ya kwasosu sannan abunda ya Faru jiya wannan Tsakaninsu ne sannan Daga baya Uwani ta maida abun kan Marliya..?
Ashe Uwani ke zubar da Cikin Sakina..?
Ita tayi ma su Nazir kurciya kin zama a kusa da mallam..?
Gabadaya sai taji kanta ya kulle ta kasa wani Tunani har zata tafi ta koma Shashenta sai ta fasa so take taga Idanuwan uwani taga ko zata iya Hada ido da ita Hajiya mace ce mai Juriya da Takwalli shiyasa koda taji haka Razanan Dake zuciyarta bai nuna a saman Fuskarta ba Murya ta Bude kadan ta kara yin wata sallaman tana Fadin"Uwani ko bakya Ciki ne..?
Haj.Uwani Dake waya taji kamar mganar Hajiya afalo gabanta ya fadi ko sallama bata yima Batula ba ta Datse kiran ta fito falo da Sauri har Zaninta na neman Faduwa har ga Allah sai da gabanta ya fadi data ga Hajiya Cikin Daburcewa da kinganta kinsan bata da gaskiya ta washe baki Tana fadin"Hajiya ke ce daman..?
Yaushe kika shigo. ?
Hajiya ta kalleta na wani Lokaci ganin yadda take zufa yasa tayi wani Mirmishi aranta tace ruwa ai ya kare ma Dan kada kuma Uwani a Fili kuma cewa tayi"Eh shigowata kenan ina ta Sallama shuru..!
Ajiyar zuciyar data saki sai da Hajiya ta jita ta sauke Numfashi tana Fadin"Eh wlh ina cikin Tiolet ne Fitowa ta kenan naji sallamanki..Sannu da zuwa hajiya..
Ki zauna mana kina Tsaye..?
Hajiya ta kada kai kafin tace"A"a ba zama nazo yi ba..Naga duk yau baki Fito bane shine na leko naga ko lafiya.?
Haj.uwani na sosa kanta tace"Lafiya lau barci ne a idona Hajiya jiya ban samu barci ba Umaima tatashi tana ta Kuka cikin Dare..!
Hajiya ta kada kai kafin tace"Allah ya Sauwake ya bata lafiya..!.
Uwani ta amsa da ameen Cikin Fuskar Tsausayi taso taja hajiyar da Hira sai hajiyar tace mata tana wani abun ne bari ta koma Shashenta sai ta shigo Suka Rabu da Uwanin akan zata shigo har da raka Hajiya tana fita ta kulle kofar Shashenta lokaci Daya tana Sauke Nunfashi Fatanta Daya Hajiya bataji wayar ta da batula ba ai da aikinta na Shekaru ya rushe alokaci Daya bata ma san meyasa ta bar Falon nata abude ba..!
Hajiya har ta kai Shashenta mamakin Abunda taji Uwani na Fadi bai bar ranta ba ko iya karisawa Dakinta batayi ba ta samu saman kujera afalonta ta Zauna tayi Tagumi tunani take ko Tun Zamanta da uwani tun suna Gusai tataba Cutar da ita ne..?
Balle itama ta rama ta Hanyar abunda take Fadin ta aikata..?
Sai taga bata samu komai ba sai Mutuntawa da girmama juna da Tarin Alherinta ga Uwani ashe daman alheri na komawa sharri..?
Allah Sarki Danmallam Uwani ta Curar dashi wajen salwantar mai da Cikinsa bama ita kadai ba tace har Amina in ta samu Ciki sai yabi Rariya..To ita Allah ne..?
Ta isa da taja da abunda yace ne..?
Sai jikinta ya fara rawa kada Uwani ta Farga da Cikin Amina shima ta ga bayansa Domin bata da Imani Allah Sarki Nasir bawan Allah har da shima bata barsa ba..?
Ba ruwansa mai Sanyi da Hakuri Duniya ma bata Damesa ba duk Cikin ya"yanta shi kadai ne tabbas maallam bai wani Damu da lamuransa ba ashe da Dalili .?
Ga Nazir da ya"yansa suma din badai kaji mallam na mganarsu ba duk da yake son ganin jikikinsa a gabansa shima ashe da Dalili..?
Sai dai Uwani tayi kuskure tana Takama da Boka da mallam ne su kuma Allah suka Rike ko Daya abunda tama ya"yanta bai Dameta ba don sun yi nesa da ita bashi ke nuna sun manta da iyayensu ba Bata bakinciki da Haka Tunda suna chan suna neman na kansu ne kuma tana da yakinin addu"arta garesu shi ke Tsare dasu Duk kwanan duniya sai sun kirata sun gaisheta sannan haka mallam sannan Duk wata Daga Nazir har Danmallam suna aiko ma ta da kudi hakama mallam koda basu Cikin wahala ammh Basu manta cewa iyayensu dana Hakki akansu ba ko Nasir sai dai tace Allah ya biyasa da gidan Aljannah Shi da Jafaru ga Sa"idu wh Tallahi yau ko mutuwa Umaru da Naziru sukayi bazata ce tayi kukan maraici ba Domin sa"idu da ne kamar da goma sannan ga Nasir da Jafaru da bai Taba sakawa ta Ji zafin Rashin Zaman ya"yanta Biyu kusa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login