Showing 90001 words to 93000 words out of 191031 words
a baya bai yi ba yanzu sai a sake ha蓷awa ta nan."
Tsaf ya gama fahimtar zantukanta kafin ya nisa yace "Gaskiya kin kawo shawara, kuma abinda nake so ki sani shine, ke ma fa uwa ce ga Mu'az, za ki iya zartar da kowane irin hukunci a kanshi, saidai abinda nake so ki fahimta, kinga Yayarta fa aka fasa aurenta da shi, kuma matsalar daga garemu ne, yau da a ce Saleema ce ta ce bata sonshi, ko kuma mutuwa mai raba tsakani ta 蓷auketa, ina ga zamu fi kowa murna da hakan, amma yanzu daya zama Mu'az ne ya ce ya fasa, ina ga kamar akwai nauyi mu kuma nema masa auren 茩anwarta."
Numfasawa ya sake yi yace" Amma ki bar min komai a hannuna, zanyi bincike akan lamarin, idan na fahimci zasu iya fahimtar junansu sai a bashi, amma ina ganin da kamar wuya, dan shi uzurinshi akan duk wacce za ta zamo iyalinshi ne, duk da dai na san soyayyar da yake ma Saleema ce ta kawo rugujewar auren."
Da sauri ta tari numfashinshi tace" Ai Alhaji ni na lura kamar Hadeeya tana sonshi, dan na ga hakan a tare da ita, da nayi 茩o茩arin tambayarta kuma saboda kunya sai ba ta yarda na san komai ba, shiyasa ma ka ji nayi maganar nan."
Jinjina kai yayi yace "Duk da haka, ki bar komai a hannuna zan bincika, idan dukansu sun amince sai a 蓷aura musu aure, amma ko da hakan ta kasance da gaggawa za'ayi saboda gudun matsala."
A sanyaye ta jinjina kai ba dan haka ranta ya so ba tace "Shikenan, Allah ya tabbatar da alkairi."
"Ameen." Ya fa蓷a yana gyara zamanshi, shiru 蓷akin yayi na wasu shu蓷a蓷蓷in mintuna, Alhaji Auwal yana tunanin ta ya ma haka zata faru? A gaskiya ya so Saleema ta zama surukarshi, duk da ba wai yana 茩in Hadeeya bane, sai dai ya fi ganin nagartar Saleema fiye da Hadeeya, dan a bayyane yake tarbiyarsu da nutsuwarsu ba 蓷aya ba ce, ko 蓷an zaman da sukayi nan bai ga wani abu a tare da Hadeeyar ba da zai zamar masa shaidar ta isa ta zama surukarshi kuma yayi farin ciki.
Kwana biyu kenan da yin maganar amma Alhaji Auwal ba wani yun茩uri da yayi, dama ya fa蓷a mata ne kawai dan ta shafa masa lafiya. Mu'az kuma har yanzu Hadeeya ba ta daina addabar rayuwarsa ba, ya shiryu ya koma ga Allah, babu abinda yake sai istigfari da sadaka tare da kusanta kanshi ga Allah ta hanyar yawaita sallolin nafila, amma Hadeeya tana yawan shiga rayuwarsa ta hanyar kira da turo masa hotunanta na shirme da hauka, sam yanzu kallon fuskar mata ma ya daina burgeshi, a yanzun da ya kusanci mahaliccinsa ya kuma 蓷aurin niyyar gyara halayensa, sai yake jin kamar ba bashi da sha'awa, tabbas ya yarda sallah maganin duk wata alfasha ce.
Yanzu ma yana tsaka da duba wani majinyaci ta kira wayarsa, yana gani amma ya share saida ya gama duba rahaton lafiyar 茩ashin mutumin kafin ya mishi abinda ya dace ya fita, mutumin na fita ya 蓷aga wayar a matu茩ar sanyaye yace "Ina ji?"
Cike da sangarta da shagwa蓳a tace "Dear tun yaushe nake kiranka baka 蓷agawa? Wai me na maka ne? Me yasa kake wula茩antani dan ka ga ina sonka?"
Dafe goshinshi yayi ba tare da ya hassala ba yaxe "Me kike so?"
Cikin turo baki tace "Magana nake so muyi da kai."
茦a茩茩arfar ajiyar zuciya ya sauke yace "Shikenan, ba zan iya zuwa gidanku ba gaskiya, saboda ina kunyar mahaifinku, mu ha蓷u wani wurin sai muyi magana."
Cike da zumu蓷i tace "Yawwa, mu ha蓷u gidansu 茦awata, anjima zan je can."
A ta茩aice yace "Shikenan, ki turo min kwatancen gidan."
Bai jira amsa daga gareta ba ya yanke kiran ya aje wayar yana jan tsaki da mamakin fitina ta wannan yarinya, 茩arama da ita amma sai iya shege cike da kai. Wayar ya sake 蓷auka ya daddana, lambar ya 茩urawa idanu da tunanin ko ya kirata ya ji ya take? Shin tana hushi da shi ko kuwa? Ta raunata kamar yadda shima yake fama da jinya har yanzu?
Ajiyar zuciya ya sauke ya jingina a kujerar yana jujjuyawa, babbar yatsarshi ya kai daidai lambar yana son dannawa amma kamar ana hanashi, kamar bazata sai kuwa yatsarshi ta danna kira wa lambar, kamar wanda ya tsorata sai ya zabura ya mi茩e tsaye yana 茩urawa lambar idanu yana jin yadda take kururuwa da *蓷innn*! Ta 蓷auki sakanni tana ruri sai kuma 茩it! Aka yanke kiran.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil!" Ya ambata tare da lumshe idanu ya koma ya zauna, sake aika kiran yayi amma aka kuma yankewa, daya aika na uku ma sai aka ce wayar a kashe take, matse bakinshi yayi guri 蓷aya yana ayyana "Na san haka za ta faru dama, Saleema mai aji ce da kuma kunya."
Rufe ya rufe idanu ya jingina sosai yana juya kujerar yace "Ya Allah ka bani kamar Saleema, ita kuma ka bata wanda ya fini da komai, Ya Allah ka bata wanda farin cikinta zai fi dukiya mahimmanci a gareshi."
Da kanshi kuma ya amsa da "Ameen ya Allah."
*Saleema* kuma kiran farko wayar na hannun yara suna wasa, mi茩o mata sukayi tana ganin kiran ta yanke tare da jan tsaki ta ayyana "Me kuma zan maka? Da蓷in baki zaka min Mu'az, na sanka fa."
Har za ta mi茩awa yaran wayar ya sake kira, sake katsewa ta yi ta tashi ta shiga 蓷akin Aunty Lubna, na uku ma haka ta yanke tare da kashe wayar gaba蓷aya, kan gado ta zauna ta 茩urawa wayar idanu tana kallo, 拼ar rayuwar da sukayi da shi take tunawa, irin so da 茩aunar da yake nuna mata a zahiri, yanda baya hushi duk abinda za ta masa, wasu lokuta ba gaira ba dalili za ta hassala amma sai ya nuna shi fa ba komai bane, karshe ma ya 蓳ige da bata ha茩uri, tabbas ya koya mata sonshi, a lokacin da bata tunanin komai sai rayuwa da shi, sai kawai ya nuna mata ita ba ajinsa ba ce ba zai iya rayuwa da jahila irinta ba (wato ita abinda ta 蓷auka kenan), dan cuta kam ta yarda ya cuceta, amma kuma ba ta ri茩eshi ba ta yadda zata gagara yafe masa, can ya je shi da halinsa.
*Alhamdulillah.*
09/06/2022 脿 22:50 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
_Bismillahir rahamanir rahim_
_32_
Tunda ta shiga dosowa inda yake tsaye shi da Zeid yake 茩are mata kallo, wani murmushi ya samu kansa da yi shi ka蓷ai, ko dan Allah ya fara ganar da shi gaskiya ne? Gaba蓷aya sai yake ganin bayyana tsiraici yanzu a matsayin 茩auyenci da rashin kunya, sam babu wani abu da yarinyar ke yi dan ta birgeshi da yake birgeshin, yanzu haka kwalluya ce ta ban mamaki tayi, amma sai ta zama abar dariya ba da kuma mamakinta da yake, a ganinta za ta birgeshi har ya amince da wautarta, to shi wace lalacewar ce za ta sakashi auren 茩anwar Saleema? Ai ba Hadeeya ba da ya tsaneta wacce duk ita ta zama silar komai, ko Hameeda da yake ganinta bata shiga abinda bai shafeta ba ba zai iya ba.
茒an zungurarshi Zeid yayi yace "Abokina, idan kai baka sonta ka min hanyar aurenta mana, ni ta min a yadda ta zo 蓷in nan."
Da mamaki ya kalkeshi yace "Ba ka ce 拼ar islamiya kake so ba?"
Cike da basarwa yace "Kai dai a fara da wannan 蓷in."
Ta蓳e baki yayi ya girgiza kai ya maida dubanshi gareta sanda ta 茩araso da fadin "Sannu."
Kallo mai kama da harara ya bita da shi jin ta kallesu duk sun haifeta amma ta ce musu wai sannu, da fa Saleemarsa ce sallama za ta yi kanta a sadde, sannan ta ce "Ina wuninku." Amma dake halayen ba 蓷aya ba, numfashi kawai ya sauke ya tsura mata idanu suna gaisawa da Zeid sai wani wasae baki yake shi ya ga 茩aramar yarinya. Kallon da ya ma Zeid yasa shi ha蓷e fuska ya kalli Hadeeya yace "Bari na baku wuri."
Gefe ya koma yana hangensu wayarshi a hannunshi, Mu'az kuma kallonta yayi yace "Ina jinki, me za ki fa蓷amin?"
Farrr! Tayi da idanunta ta dan matso daf da shi tace "Dear, dama ina so na sake fa蓷a maka ne cewa ina sonka, dan Allah ka ce zaka aureni, tunda ba ka auri Saleema ba."
Sadda kanshi yayi 茩asa yana murmushi na wasu sakanni sannan ya 蓷ago ya kalleta, gyara tsayuwa yayi sosai ya lafe a jikin motarshi ya kalleta yace" Hadeeya, aure da ni da ke ba zai yiwu ba, ban san me yasa kike sona ba, amma ni ina son mace ne kamar 拼ar uwarki Saleema, Hadeeya ina yawan fa蓷a miki ke yarinya ce, idan na amince na aureki zuciyata ba ta sonki, zaki fuskanci matsi a gidana, sannan abunda ya faru tsakaninmu tun farko, ba lallai mu mutunta junanmu ba, sannan bana tunanin zamu iya zama lafiya, sannan kinga abinda ya faru tsakanina da 拼ar uwarki, idan har kika ga iyayenmu sun amince da auren nan, to tabbas kawaici suka mana, amma ba dan rayukansu na so ba, dan dalilin da na bayar na fasa auren wacce na ke so, ba lallai ya gamsar dasu ba da har zai sa su sake daukarki su bani, amma kinga wannan...?"
Ya fa蓷a yana nuna mata Zeid dake gefe sannan yace" Aminina ne, ban da wani sama da shi, na sanshi sos1i fiye da yadda na san kaina, yanzu haka maganarki yake min wai yana sonki kuma zai aureki, ki amince masa Hadeeya zai ri茩eki da kyautatawa, saidai akwai abinda ba zan 蓳oye miki a game da shi ba, idan kin amince zan miki bayani dan abu ne da ya shafi rayuwarsa ta sirri."
Kallon Zeid tayi, ta sake kallonshi sosai kamar mai son gane ya mata ko a'a, sai kuma ta kalleshi duk da bata ga makusa a Zeid 蓷in ba tace" Amma fa ni kai nake so."
Wani murmushi yayi yace" So? So Hadeeya? Kin san shi ne? Me ye so?"
Yatsina fuska tayi cike da shirme tave" Kawai ka ji abu na birgeka, kuma kana bu茩atarsa."
Girgiza mata kai yayi yace _" Hadeeya, ba komai bane so face gizo, abune na 蓷an lokaci da akan ji shi farat-蓷aya, 茩auna ita ke haifar da so, amma so baya kawo 茩auna, hakan yasa ma茩aunata sukan rayu har abada duk tsanani, amma masoya su kan rabu da dalili mara ma'ana saboda babu 茩auna."_
Kallonta yayi yace" Ba zan ta蓳a yarda da soyayyarki ba Hadeeya, dan na san babu 茩auna a cikinta..."
茒agowa yayi daga jinginar da yayi ya kalleta yace" Ki fara sanin yadda zaki 茩aunaci 拼ar uwarki kafin ki so wani, kada ki kuma kirana a waya bare ki je inda na ke, idan ba haka ba zan ajiye sanayya a gefe 蓷aya na miki abinda ban ta蓳a kwatanta yi wa wata mace ba."
Murfin motar ya jawo zai bu蓷e yace" Kada kiyi biyu babu, 茩ofar abokina a bu蓷e take, idan aure kike so dan biyan bu茩atarki bismillah, namiji ne shi har da 茩ari."
Shigewa yayi motar ya barta nan tsaye, Zeid na ganin haka ya tako da sassarfa ya zagaya ya shige motar bayan ya kalli Hadeeya da mamakin yadda take tsaye kiskirim kamar wacce bata motsi, yana shiga Mu'az ya ja motar suka bar unguwar ba tare da sake waiwayarta ba.
______________
Kowa rayuwarsa yaci gaba da yi da taimakon mai hura musu numfashi, sam Mu'az bai san da labarin fara soyayyar Hadeeya da Zeid ba sai da ya ji wai za'a kai ku蓷i gidansu Hadeeya, yayi mamaki sosai kuma daya tuntu蓳i Zeid da maganar ya nuna masa kawai ya share wasa ne fa, amma a ranar da aka tabbatar masa an kai har ya ga hotunansu a status 蓷in abokansu sai ya sake mamaki sosai, amma tunda ya fahimci ba'a son sa da maganar ne sai ya yi kamar bai sake ji ba. Zeid kuma a ganinshi Mu'az baya sonshi da Hadeeya ne tun farko, shiyasa yake ganin zai iya yi masa bu茩ulun tona masa asiri a rabashi da ita, shiyasa yasa aka gaggauta komai kafin ya farga har ya tura ku蓷inshi, a yanzu kuma ya san ya gama sace zuciyar Hadeeya da kalamai da nunamata 茩ololuwar soyayyar da ba zata iya rayuwa babu shi ba. Ita kanta Hadeeya sai yanzu take jin tana so, inda Ardiya ba dan ta so ba akayi hakan, dan ita ta so ta samu Mu'az, amla da Hadeeyar ta ce uta fa ga wanda take so yanzu kula ubanta ya goya mata baya sai t zuba musu idanu kawai, a yanzu harinta na gaba Hameeda ce, gaba蓷aya za ta saita makamanta ta tsaya tsayin daka har sai ta ga ta samu wanda ya fi mijin da Hadeeyar ta kawo mata a matsayin suruki.
Kwanan Saleema biyar a gidan Lubna ta dawo gida, tana so ta ma mahaifinta maganar ta koma makaranta, saidai tsoron abinda zai faru ya hanata fa蓷a, dan bata manta dukan da ta sha ba har saida ta yi jinya a 蓷akin Mamanta. Dan haka kullum take zaune 蓷aki da litattafanta tana karatu wani lokaci kuma da Al茩ur'aninta.
*Bayan wata biyu*
Ba tare da mamaki ya bar fuskarta ba ta 蓷auki katin da ta gani a 拼ar jakar kyauta da aka bata tun masarauta, wacce tunda ta zo ita dai bata bu蓷a ba mahaifiyarta ce ta ga abinda ke ciki kula ta mayar, yanzun ma tana canzawa kayanta wurin zama ne ta ga katin, zaro idanu tayi tace "Lahhh! Wallahi lambar Maman nan ce sarauniya."
Jujjuyawa ta fara yi da niyyar 蓷aukar waya ta kira, sai kuma ta tuna ranbonta da waya tun ranar da Mu'az ya dinga kiranta tana kashewa har ta kashe wayar gaba蓷aya, dama ba damunta tayi ba shiyasa bata kuma damuwa da ita ba tunda ta kai ta aje, da sauri ta nufi kayan Mamanta ta shiga binciken neman wayar, tana ganinta ta 蓷auka da sauri ta fito falon tana 茩walawa Hamdeeya kira. A tsakiyarsu Ardiya ta sameta da 茩awayenta sun cika falon da kaya saboda za su je gyaran 蓷aki, tsaye tayi ta mata alama da hannu tace "Zo."
Ma茩ale kafa蓷a tayi alamar ba zata zo ba, harara ta dalla mata tace "Za ki zo ko saina takaki?"
Tana turo baki ta taso ta nufota Ardiya kuma ta harari Saleema, hannunta ta kama zasu fita farfajiya, daf da zasu fita wata gogaggiya kuma wayayyar] ar 茩walisar mata ta shigo 蓷akin, 茩amshin turarenta daya daki hancin Saleema, daga sama har 茩asa ta kalli yanayin shigarta da suturarta mai tsadar gaske, irin ajin matar da shan 茩amshi, dole ta tabbatar babbar mace ce, kauce mata tayi ta fara wucewa tana gaisheta a ladabce, a yatsine ta amsa mata wanda hakan ya ma Saleema zafi, duba da ba wasu shekaru ne a kanta, ba zata fi ashirin da bakwai zuwa da takwas ba, girma ko dukiya a ganinta ba su zaisa ta wula茩antata ba, sharewa kawai tayi ta fita a 蓷akin dan ba ita ce gabanta ba.
Ardiya na ganin amaryar gwamna Alhaji Nasir ta mi茩e tana wasar baki da mata sannu da zuwa, 蓷an murmushi kawai ta mata amma ba ta amsa ba, duk matan nan dake 蓷akin suna ta hayaniyarsu suna kuma gaisheta ba wanda ta amsa ba, kallon Ardiya kawai tayi a sanyaye a kuma sha茩e tace "An kawo kayan?"
Da sauri Ardiya ta juya kan kujerar data tashi ta 蓷auko ledojin guda biyu tace "An kawo, gasu ma, duba ki gani Madame."
A yatsine tace mata "Karki damu, ina sauri ne, dreba na jirana."
Take mata baya Ardiya ta yi har suka fita a farfajiyar tamkar wacce ke maula a wajenta sam ta manta da na ta ajin da kuma wayewarta.
Saleema na tsaye tana jiran Hamdeeya da ta aika siyo mata kati matar ta fita, da kallo kawai ta bita kafin ta 蓷auke kai sanda jami'i biyu suka take mata baya sai mace 蓷aya ita ma jami'a ga kuma 拼ar abi yarima a sha ki蓷a. Tana nan tsaye Hamdeeya ta kawo mata sa茩on ta kar蓳a ta koma ciki, zaune tayi a tsanake ta shiga saka katin har ta gama sannan ta shiga saka lambaobin tana jin gabanta na faduwa sakamakon kiran da za ta aikawa wannan babbar lalba ta babbar mace.
Sosai ta 茩ame tana jiran a 蓷aga kamar wacce za ta 蓷auke numfashi, saida wayar ta yi kamar za ta yanke aka 蓷aga, a hakan ma dan an kira 茩aramar wayar sarauniya Ramlat ce, alamu ne na wanda ya kira makusancinta ne sosai, dan ahalinta kadai take ba wannan lamba, da ta ga ba茩uwar lamba sai ta 蓷aga dan tasan duk yadda aka yi ita ce ta bayar da lambar ko kuma wani ahalinta ne ya kira da wata lambar. A matu茩ar nutse ta fara da "Assalama alaikum."
A tausashe, a rarraba ta amsa mata da "Wa...alaiki..salam."
Numfashi Saleema ta sauke tana sakin murmushi ta ma rasa me za ta ce da jin wannan murya, abun mamaki da bata taba tsammani ba sai ta ji matar tace "Saleema, ke ce?"
Fada蓷a fara'arta tayi tace "E, ni ce, barka ranki shi da蓷e."
A yanzun sai ta ji yanyin maganarta ya canza, ma'ana daga da茩ilen nan zuwa sauri sauri ka蓷an tace "Saleema, me yasa ba ki kirani tun tuni ba? Na yi ta dakon kiranki amma shiru, kina lafiya?"
A tusashe da ladabi tace "Lafiya lau, a gafarceni, waya ne bana Abbana baya so na ri茩e sai yanzu ya yarda."
Tana 茩arashe fa蓷a ta rintse idanu sakamakon 茩aryar da tayi, a ganinta ta ce bata ga lambar ba sai yanzu kamar bata daraja kyautar da ta mata bane, sai dai abunda Saleema bata sani ba hakan ma da ta yi 茩arawa kanta girma da kima tayi da kuma kankaro mutumcin mahaifinta har take ganin jajircewarsa akan tarbiyar yaranshi. Cike da jin dadi tace "Hakan ya yi kyau, kuma ina goyon