Showing 120001 words to 123000 words out of 191031 words

Chapter 41 - BAIWATA COMP HAUSA NOVEL

30 Aug 2024

68019

albarkaci abu 蓷aya, amma kada ki sake aibata min 拼a."

Juyawa yayi yana kallon Ahmad dake wasarshi da waya yace" Ku tashi ku bani wuri."

Mi茩ewa duk sukayi suna hararar juna, suna fita falonsu Safiya ta kalleta tace" Aure nufi ne na Allah, sannan lokaci ne da shi tamkar rayuwa, ke baki isa ki hanata aure ba idan lokacinta yayi..."

茦yasta yatsunta tayi tace" Kuma ina mai tabbatar miki za ki sha mamakin wannan jinkirin na ta, dan ina ji a jikina alkairi zai zama in sha Allah."

Cike da izgilanci da rashin sanin gaibu ta bushe da dariya tana tafa hannaye tace" To madadin mamakin da zan sha ki ce min zata *auri sarkin garin nan mana*, kinga sai na kasance cikin wanda zasu dur茩usa gaishe da gimbiya... Hahahahahaha, wayyo Allah cikina."

Ta 茩arashe da wata dariyar tare da barin Safiya a tsaye, saida ta shige wasu hawaye masu zafi suka kwaranyo mata, sosai taji zafin maganar ta Ardiya, gashi kuma Saleema ko saurayin ba ta da bare ta sa ran sanin wanda zai iya kasancewa mijinta, ita fa rashin aurenta yanzu bai dameta ba, to nawa ne ma shekara ashirin da biyu? A al'adar hausa ne sai a ga yarinya ta jima, amma ko anan larabawa wannan ba wani abu bane, hasalima idan baki kai talatin ko ka蓷an ga 茩asa da haka ba kamar ma baki isa auren bane, sai wacce Allah ya so da rahama ne za ta yi shi da ashirin da sama... Addu'a ce ba zata daina yi mata ba, sannan ga tauyeta da akayi wajen hanata fita, idan fitar ta zma dole kuma sai ya ce su tafi tare ko kuma ya ce ta tafi da Ahmad, sam kamar dai bai yarda da Saleemar ba, ita kuma ta so yin magana amma magabatanta sun nuna mata rashin yin shi ya fi alkairi, ta zuba masa idanu ta ga iya gudun ruwansa.

A farfajiyar gidan ta zauna kusa da fanfon da wasu lokuta ma茩ota ke shigowa 蓷iban ruwa, a nutse sosai take sauraren ro茩on da Gimbiya ke sake yi mata karo na uku kenan tun ha蓷uwarsu, da za茩uwa da son jin me ye matsalar matar tace "Ranki shi da蓷e, ba wai zan shiga hurumin da ba nawa ba, amma zan so sanin matsalarku dan ta zama a ddu'ata ta musamman, tabbas Allah ya fimu sanin abinda ke 蓳oye a zu茩atanmu, sannan yana amsa addu'a idan muka ro茩e da ya biya mana bu茩atunmu na alkairi. Ranki shi da蓷e, wata茩ila abinda kuka nema a wajen ubangiji ba alkairi bane, shiyasa bai baku ba har yanzu ko kuma ya musanya muku shi da wani abun da yake alkairi a gareku, wata茩ika kun san abinda ya baku 蓷in ko kuma baku fahimta ba, misali lafiya, ita ka蓷ai da Allah baku ma alkairi ce kuma ya cancanci ku gode masa, duba da wasu suna kwance suna kashe zunzurutun ku蓷i dan a sama musu wannan lafiyar da Allah ya bamu a kyauta."

Cikin tausashiyar muryar kuka tace" 瞥ata, ai lafiyar ce take neman yi mana wasa, yarima Abdus-samad a sukurkurce bana gane kansa, kinga dai ana son na蓷ashi a matsayin sarkin mara蓷awa, amma abun ya gagara, sau uku ana daf da na蓷i sai ya gigice, 蓷ayan tunda ya bar garin bai kuma dawowa ba saida ya shekara biyu..."

Sautin kukanta ne yasa Saleema tashi tsaye tana jin ba da蓷i sosai sannan ta 蓷ora da" Ba mulkin nan ya fi damuna da ake son lalata min rayuwar yaro akan shi ba, sai yadda aka hanasa sakewa yayi aure kamar kowa, yana son yin auren kuma Allah ya hore mana abun yin auren ko da guda hu蓷u ce a lokaci 蓷aya, amma da za'a mishi maganar aure 茩aramin mahaukaci yake dawo ya nemi illata kanshi ko yayi ikrarin ruguza wacce za'a aura masa 蓷in, wasu matan ma da kansu suke cewa basa son shi... Na rasa wannan wace irin jarabawa ce, mun yi addu'a, munyi sadaka mun yi aikin Hajd da azumi da tawasuli a gurin Allah akan lamarin nan, amma har yanzu shiru kike ji tamkar... Astagfirullah! Saleema yanzu haka Abdus-samad shekararshi talatin da biyar, amma ko auren fari baiyi ba 茩anenshi har ya haifi yara biyu, 茩annensa mata kuma ba'a ma magana."

Kukan matar shi yafi tsuma zuciyarta har ta fashe da kuka ita ma, sai gashi suna kokawa ba mai rarrashi wani, dan Saleema har ta fara hango kanta idan fa ita da ke mace t kwashe shekarun nan ba aure? Ya za ta yi? Sun fi minti uku suna kuka kafin Saleema ta fara sassautawa tana shan majina cikin dakusashiyar murya tace "Ranki shi da蓷e, kuyi ha茩uri, ku sani duk abun daya faru da bawa 茩addararsa ce, ita kuma 茩addarar nan an rubuta tun kafin halittar kowa, *al茩alamin* daya rubuta 茩addarar tamu, da *allon kiyayewa* da aka rubuta 茩addarar tamu, malamai kansu sun yi sa蓳ani kan wanene aka fara halitta, wannan ya nuna girman da 茩addara take da shi da kuma anfaninta ga 蓷an adam, 茩addara jarabawa ce, ita kuma jarabawa sai mai imani ka蓷ai Allah yake jarabta dan a gwada 茩arfin imaninmu, a Al茩ur'ani ma Allah ya fa蓷a cewa dan kun ce kunyi imani sai mu barku hakanan ba jarabawa? Kenan rayuwar mumini cike da jarabawa masu da蓷i da akasin haka."

Numfasawa tayi tace" Ranki shi da蓷e, Allah maji ro茩on bayinsa ne, ku ro茩eshi da magiya da kuka a lokacin da kowa ke bacci, akwai tabbaci addu'arku ta kar蓳u a wannan lokacin, sannan kuyi ta da ya茩inin lallai yana jin ku kuma zai amsa muku, shi da kansa ne ya fa蓷a a Al茩ur'ani, _Idan bayina suka tambayeka game dani to ni ina kusa dasu, ina amsa ro茩on mai ro茩o yayin da ya ro茩eni, ya ce ku ro茩eni sannan kuyi imani dani domin su shiryu._, ranki shi da蓷e ku saka ya茩ininku akan ubangijinku, ya fi ku sanin me ke damunku, wata茩ila kuma jinkirin da zai zama alkairi a gareku ya muku, ina fatan Allah ya warware muku wannan matsalolin na ku, sannan zan sake magana da malaminmu su ci gaba da sakaku a addu'a, in sha Allah komai zai yi daidai, sannan nima..."

Shirun da tayi yasa Hajia Ramlat data kasa kunne tana sauraren yarinyar jikinta har tsuma yake tsigar jikinta na tashi tace" Ina jinki Saleema, ci gaba, hakan na sama min nutsuwa da jin addu'ata ta kar蓳u a wajen ubangijina, kamar yadda kika fa蓷a tayiwu an jinkirta mana ne saboda za'a bamu babban rabo ko ba'a nan ba, wata茩ila a gobe kiyama."

Da murmushi a fuskarta ta sadda kanta, kunya take ji ta fa蓷a mata wasu addu'o'i ta ce a dinga karanta masa a zam-zam, yadda ta nuna ana ta addu'a ta san an yi mishi, sai dai ita fa ya茩inta akan addu'o'in dabam yake, dan hadisi ne ingantacce daga bakin fiyayyen halitta, ta tabbata idan aka yi da gasgatawa za'a samu biyan bu茩ata, dan haka kar ta fa蓷a a ce an yi, sai kawai cikin ladabi tace "Ranki shi da蓷e, dama ruwan addu'a ne ban so ko kuna da bu茩ata ba?"

Da hanzari Hajia Ramlat tace "Saleema me zai hana? Kin kuwa san irin tashin hankalin da nake ciki game da wannan matsalar? Saleema ina so, ko da kina so a tura a kar蓳a ne saina tura, tunda kin ce ke ba kya fita."

Jinjina kai tayi tace "Shinkenan ranki shi da蓷e, a turo 蓷in."

Da farin ciki suka rabu inda Saleema ta koma 蓷aki da sauri, robobin zam-zam guda shida ta 蓷auko dan dama ita ma tana aiki dasu ta juyesu a kofi sannan ta 蓷auro alwala ta yi sallah raka'a biyu, daga amanar-rasul zuwa ayatul kursiy, suratul jin da fala茩 da nas, duka saida ta karanta kafin ta shiga karanta addu'o'in da duk ta san an ce daga bakin fiyayuen halitta suke kuma suna magani, tana gamawa ta mi茩e ta 蓷auko wani kofin kwalba mai murfi ta juye ruwan a ciki ta ri茩e da hannaye biyu tana kallon kanta a madubi, lumshe idanu tayi fuskarta 蓷auke da murmushi tace "Na yi ne da sanin cewa ka ji ni, Allah kaine Allah, dan girman mulkinka, dan tsarkin zatinka, dan 茩udura da buwayarka, Allah ka 蓷aukewa wannan bawa naka duka larurarshi, kai ne Allah, kuma kai kace mu ro茩eka zaka amsa mana, Ya Rahman, ya Jabbar, ya Mutakabbir, Ya Razza茩, ya 茦ahhar, ya Hayyu, ya 茦ayyum, ya Wahhab, Allah dan tsarkin sunayen nan naka na 蓷aukaka da isa, Allah ka biya mana bu茩atunmu na alkairi."

_"Ameeeen ya Hayyu ya Qayyum."_

Shigowar Hamdeeya 蓷akin ne yasa ta juyowa tace" Wai ki zo kin yi ba茩o."

"Uhum!" Ta fa蓷a tana kama hanyar fita dan dama da hijabinta a jikinta, tana zuwa farfajiyar gidan ta samu dattijon da shigarshi ta sassau茩an yadi marar nauyi, gaisawa sukayi a mutumce da ladabi kafin ta mi茩a masa ledar 蓷auke mai kofunan tace "Gashi Baba, a bashi yasha da bismillah tare da mafi girman ya茩ini, sannan a shafa masa a jikinsa in sha Allah komai zai yaye, gobe ma a sake bashi yasha tare da shafa masa, haka har a masa na kwana ukun, idan an ga sauyi sai a ci gaba in sha Allah."

Shi dai tunda gimbiya ta turo shi nan yake ganin yarinyar mai mahimmanci ce a garesu, dan haka ya kar蓳a da alamun rusunawa yace" An gama ranki shi da蓷e, Allah ya amince."

Murmushi ta masa tace" Ameen, a gaida ranki shi da蓷e." Juyawa tayi ta koma ciki shima ya fice, Ardiya na ganin ta taho ta fito daga bayan 茩ofar da take le茩asu tana dariya, saida Saleema ta zo zata shige ta kalleta sama da 茩asa tace" Yanzu kuma Saleema da tsofaffi kika koma soyayya? Lallai ta 茩are miki."

茦ala ba ta ce mata ba ta wuce ciki kallo 蓷aya kawai ta mata, ita kuma ta蓳e baki tayi tana sake murmushi tace" Shi ma sai na tabbatar ba kowa bane, ko da yake ma daga ganin kayanshi ka san ba zai rasa zama wani tsohon 蓷an kasuwa ba."

*Ko da* ya kai dattijon nan Sheikh *Mukhtar* ya kar蓳a ya shiga har 蓷akin da yariman ke kwance yana bacci, dan tun jiya da suka yi maganar na蓷i ya dafe kai ya fa蓷i shi ba somamme ba kuma ba mai motsi ba. Yana kawowa a hankali ya zauna yana mi茩a mata yace "Mi茩o 蓷aya."

Bu蓷e ledar tayi ta fito da kofi 蓷aya ta bu蓷e murfin ta mi茩o masa, kifa masa yayi a baki yace "Yi bismillah."

Lumshe idanu yayi sannan ya furta bismillah a 茩asan ma茩oshi, bashi ruwan yayi yana sha kamar wanda suka masa da蓷i, tas ya shanye sai ka蓷an da aka rage gimbiya ta shafe masa jikinshi da su har saman kanshi.

Ganin ya kwanta kamar zai yi bacci yasa Sheikh Mukhtar fa蓷in "Mu barshi ya kwanta, sau茩i na samu a cikin bacci."

Fita sukayi tana ta waiwayenshi, a falo suka samu 茩aninshi zaune, gimbiya ce tace "Ka je 蓷akinshi ka zauna, idan yana bu茩atar wani abun sai ka masa."

Jinjina kai yayi ya mi茩e yana tattare alkyabbarsa ya shige 蓷akin. Wuri ya samu ya zauna shima ya buga tagumi yana kallon 茩a茩茩arfan namijin da ciwo ke neman halakashi, ya 蓷auki awa 蓷aya zaune shi bai yi bacci ba sai sauraren tattausar 茩ira'ar Sheikh Abdur-rahaman As-sudais dake tashi a 蓷aki, yana ta lumshe idanu kamar bacci na son 蓷aukarshi kawai ya ji kakkarin amai daga kan gadon.




*BAIWAR SALEEMA KENAN*



*Alhamdulillah.*
15/06/2022 脿 11:51 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�


_Bismillahir rahamanir rahim_


_40_



Hankali tashe suka shigo 蓷akin sanda 蓷aya daga cikin hadiman ta sanar da su, kallo 蓷aya Sheikh Mukhtar ya ma aman da yake ya san cutar da ta jima a jikinshi ce yake amayewa, amai ba茩i茩irin tamkar turirin wuta na tashin haya茩i, saida ya gama amai suka gyara mishi kwanciya aka tsaftace wurin. Da izinin Allah ko da dare ke yi Abdus-samad ya mi茩e kan 茩afafunshi kamar ba shi ba.

Har zuwa lokacin Sheikh na gidan, a wannan lokacin da ya ga abun al'ajabi kallon Gimbiya yayi yace " *Wacece ita*?"

Tsaf ta fa蓷a masa dalilin da yasa ta san Saleema har zuwa yau 蓷in nan, jinjina kai yayi yace "Ya茩ini take da akan ubangijinta, kuma ya barrantar da ya茩ininta, wata茩ila ma ita 蓷in tana da *BAIRWATA* amma ita kanta bata sani ba, ki yi wani abu akan yarinyar nan Ramlat, ki yi wani abu a kai."

Da fara'a ta kalleshi cike da jin da蓷in har yau akwai wanda ke iya kiranta da sunanta kai tsaye ba Hajia ko ranki shi da蓷e da sauransu, jinjina kai tayi tace" Zuwa safe zan kirata na mata godiya."

Kallonta yayi ba alamar wasa yace" Ta fi 茩arfin godiya ta fatar baki, ki darajta *Baiwar* da Allah ya mata, shekara nawa muka 蓷auka muna 茩ulunboton duk abinda muka sani, ina ce har gaban 蓷akin Alla na je musamman na yi wa yaron nan addu'a? Amma me ya sauya? Lokaci 蓷aya ta bado ruwan addu'a yasha ya fara amayo cutar dake jikinshi."

Jinjina kai tayi cike da farin cikin abinda ke shirin faruwa da su tace "Za'a yi yadda ka ce Yaya, zuwa gobe da safen zan fara kiranta, daga bisani sai muje gidansu tare da kai idan komai ya lafa."

Da mamakin rashin fahimtar kalamanta yace "Zuwa gidansu kuma bai yi girma sosai ba?"

Girgiza kai tayi tace "Bai yi ba Yaya."

Jinjina kai yayi yace "Shikenan, zan biki sau da 茩afa muje, duk abinda kika yi zan kalleki ne na kuma yi miki *ladabi*."

Dariya tayi da ta fito da kyawunta har da tsagarta ta barebare dake kan kumatunta da kuma gefen fuskarta sama da kunnuwa ka蓷an.



_______________



Suna zaune a 茩ofar shiga falonsu it da Ahmad da Mamanta Ardiya ta fito daga falon ta nufi 茩ofa hannunta ri茩e da waya, jim ka蓷an ta dawo tare da ba茩o yan biye da ita a baya suna ta hira da dariya, saida ta zo daf da su ta kalli Safiya, suma kamar dai sauran kishiyoyi ne, yau fa蓷a gobe a shirya, yanzu haka dake suna magana cike da raha ta nuna mata saurayin tace "Kinga 蓷an Yayata da nake baki labari, wanda yake zaune a Japan."

Da fara'a Safiya ta waro idanu tace "A'a masha Allah, mutan waje yaushe aka zo?"

Da harshenshi da baya fita sosai ya amsa da 茩yar da cewa sati 蓷aya kenan, sama sama suka gaisa sai lokacin Saleema ta kalleshi tace "Ina wuni."

茦afafunta dake mi茩e masu duhu amma kuma tafin 茩afar mai hasken nan ba sosai ba shima, saidai a wanke suke a gyare sai cikon naman dake nuna zasuyi laushi, ga zara zaran yatsunta da wannan ya fi wannan wannan ya fi waccen. Le蓳蓳enshi na 茩asa ya lashe dan abinda ya hango a 茩afafun yasa jin jikinshi amsawa gaba蓷aya har ya ji yana mata sha'awar saka sar茩ar 茩afa a 茩afafun, bai iya amsawa ba dan lokacin daya 蓷aga kai ya kalli fuskarta da sigar amsawa, a kan 茩irjinta dake bu蓷e ma'ana babu hijabi ya sauke dubanshi, sai kawai ya bi bayan Ardiya dake masa izinin ya shigo ciki.

Har 蓷akin baccinta ta saukeshi ta kawo masa abun sha kafin ta zauna suna ta蓳a hira a harshensu na buzanci da kuma sirkin faransanci da suke sakawa, shiru ya 蓷an ratsa na wasu da茩i茩u kafin yace "Aunty, wacece wannan a waje na gani?"

Yatsina fuska tayi tace "瞥ar mai gidan ce, ga Mamanta nan ka gani har kun gaisa."

Bu蓷a idanu yayi yace "Wow! Amma dai akwai halitta a wurin nan, me yasa baku mata aure ba kamar su Hadeeya?"

Ta蓳e baki tayi tace "To ai mijin ne babu, idan ta samu za'a mata, yarinyar ce ta cika nauyin 茩afa akan komai, hatta cikinta saida mahaifiyarta ta yi wata goma da shi kafin ta haife, haka ma a karatu ita ce baya, sannan ga ba茩in jini har yanzu babu saurayi."

Wani sakaran murmushi yayi yana ayyana" Ni kam na ga gurin hutuna, ba dai ba茩in jini ba sai dai rabona." A zahiri kuma cewa yayi" Ta samu mijin ai auntyna."

Da sauri ta kalleshi tace" Ban gane ba?"

茒aga mata gira yayi irin na 拼an duniya ya kashe mata idanu 蓷aya yace" Ina sonta, zan aureta."

Rarako idanu tayi tana kallonshi da mamaki da jin haushin abinda ya fa蓷a mata, ta ya zata yarda Saleema ta auri *Kabil* bayan ta san waye shi kuma 蓷an waye? Daga Hadeeya dake auren marar mutuncin nan Zeid, har Hameeda dake auren 蓷an mataimakin gwamna, babu wanda ya kamo mahaifin Kabil a ku蓷i, kuma abun haushin ma su 蓷in jinin buzaye ne da suke kashe ku蓷i tamkar babu gobe, su in dai bu茩ata za ta biya to ku蓷i ba komai bane a wajensu. *Sai dai* kuma! Kabil 蓷an iska ne na 茩arshe, dalilin da ya sa ma kenan ba ta so ha蓷ashi da 蓷aya daga cikin 拼a拼anta ba, yadda labari ke ya蓷uwa a ahalinsu shine, a 茩asar Japan giya yake sha uwa ruwa, mata kuma tamkar 蓷an taure haka yake, a jita-jitan da ta ji shine har cocaine yake ta蓳awa yanzu. Wannan dalilin yasa ta sakin fuskarta ta shiga doka murmushi tana fa蓷in "Abu mai sau茩i, ba dai kana sonta ba?"

茒aga mata kai yayi alamar e, jinjina kai tayi tace "Idan ka aurenta can za ka tafi da ita?"

Murmushi yayi yace "Ba ta yadda zan yarda na bar dan茩waleliyar yarinyar nan a nan, da ita zan tafi can luna holewa."

Murmushi tayi cike da mugunta tace "Shikenan, ka jira yanzu lokacin dawowar Abbanta yayi sai na gabatar da kai, na san ba zai 茩i ba."

Murmushi yayi yana lumshe idanu ya mata alamar to, mi茩ewa tayi tace "Muje na bu蓷e maka falonshi sai ka zauna acan ka jirashi."

Mi茩ewa yayi ya bi bayanta yana 茩arewa 茩ugunta kallo, sai kuma ya yi murmushi ya 蓷auke kanshi har suka shiga 蓷akin ya zauna inda ta nuna mishi, har ta juya za ta fita yace "Aunty, ki turo yarinyar ta kawo min ruwa."

Murmushi ta mishi sai kuma ta jinjina kai alamar to

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login