Showing 12001 words to 15000 words out of 191031 words

Chapter 5 - BAIWATA COMP HAUSA NOVEL

30 Aug 2024

67959

had'e fuska?"

K'ara turo baki ta yi gaba ta na k'ok'arin saka rigarta duk da sanye take da hijab saboda kunyar Maman da ta ke ji ba za ta iya tub'ewa a gabanta ba tace "Ni wallahi Mama ba na son zuwa gidan nan, dan kar Abba ya ce na rainashi zan tafi kawai."

Murmushi Safiya ta yi da mamakin wai Saleema ba za ta iya saka riga a gabanta ba dan kar ta lafiyayyen k'irjin da ya cika mata gaba tace "To wai me ya sa ba kya so? Can ma gidan hutu ne fiye ma da na mahaifinku."

Juyowa Saleema ta yi ta kalleta tace "Mama, ba wannan ne matsalar ba, kin san ko k'auye zan iya rayuwa, kawai dai yaran nan na sa ne ni wallahi ba su kwanta min a rai ba."

Da mamaki Maman tace "Su wa kenan?"

Cike da yatsina fuska tace "Yan mazan mana, duk ba su da tarbiya wallahi."

Rik'e hab'a Maman ta yi da mad'aukakin mamaki tace "Ikon Allah! Saleema yaushe ma ki ka musu sanin da ki ka gane haka? Shin *Mu'az* d'in da ko shekara bai yi da dawowa daga karatu ba? Ko kuma *Mu'awwaz* d'in da ke da tsantseni da share mutane?"

Ta na gama saka rigar ta cire hijabin ta na saka zip tace "Dukansu Mama, wallahi kura ce da fatar akuya, dukansu rainawa mutane hankali suke, ba ma kamar tuzurun nan."

Dariya Maman ta sake har da k'yalk'yalawa tace "Wa ye tuzuru kuma?"

Ba alamar wasa tare da ita tace "Shi Mu'az d'in mana, shekara talatin ba aure amma ya na nuna bai damu da komai da kowa ba, hmmm ! D'an rainin hankali kawai."

Maman ta dai abun dariya da mamakin yanda ta hak'ik'ance ta na ta sababi take, to ita ba ta ma san yaushe ta musu wannan sanin ba haka? Tabbas sun tab'a zuwa gidan amma fa tun ba ta kai shekara goma ba a duniya, duk da ta san ta bata da mantuwa kan abin da ya shafi rayuwar duniya da karatunta na islamiyya, amma dai ba ta tunanin har yanzu ta na tune da abinda ya faru shekara *tara* da ta wuce.

Haka ta gama shiryawa amma sam ba ta so haka ba saboda ita ta gama fahimtar duk wani da Abbansu ke alak'a da shi ta kusa sosai to d'an boko ne da ke da wayewa, sai dai na wani ya fi na wani kawai. Ta na gama shiryawa ta fito farfajiyar, a nan ta samu su Hadeeya har da mahaifin na su a tsaye da alama so ya ke ya ga tafiyarsu da kuma Mamansu gefe ta na amsa waya.

Sanye take da doguwar riga wacce gaba d'aya gabanta yake a bud'e, ma'ana aka masa doguwar tsaga har zuwa cibiyarta, sai siket d'in atamfar da ya rufe mata cibayar inda a baya kuma yake yage da tsaga shima har idan tana tafiya kamar za ka hango gwiwoyinta, k'aramar jakarta ta rataya ta tsakiyar wuyanta da hannu, sai takalmin kalar jakar masu d'amara da rufaffiyar sama, kwalliya ce ta ban mamaki ta d'auka sai dai ko d'an kwali babu a kan ta, hasalima d'an kwalin rik'e yake a hannunta, a hakan wai shi ma wani kalan tsarin ne.

Kayan sun matseta sosai yanda suka fito da kyakyawar surarta da kuma kyawun fuskarta, masha Allah kuma abun ka ga farar fata sannan mai kaurin jiki, hakan yasa Hadeeyar ta zama basu da maraba ita da Saleema da ta bata shekara uku da haihuwa saboda su na da kumari.

Cike da rashin jin dad'in yanda ta ga yan uwanta sun shiryo ta kalli Hadeeya a tausashe tace "Haba Hadeeya, wannan wace irin shiga ce? Kina 'yar musulmai amma ki fita haka kanki babu rufi? Idan ma ba zaki saka hijab ba ko gyale ne ki saka mana."

Cikin tsiwa da raini da kaud'i Hadeeya ta kalleta tace "Ke kuma malama ina ruwanki da shigata? Kina da matsala da hakane? Ka ji min mata kai, so kike na yi irin shigarki kamar wata matar aure?"

Kafin kowa ya yi magana Ardayi da aka mata kiran gaggawa a wajen aiki ta k'araso da sauri kai tsaye mahaifinsu ta tunkara cikin shagwab'a tace" B茅b茅, kira ne da wajen aiki ana buk'atata yanzu, zan tafi sai na dawo..."

Ta yi maganar ta na fad'awa jikinshi ta sumbaci labb'anshi tare da d'agowa tace" Ba zan jima ba Bebe, sai na dawo."

Saleema da tun da ta ga ta nufeshi ta d'auke kanta saboda kunya, shi kan shi yanzu da shekaru su ka k'ara ja ya kan ji nauyi idan irin haka ta faru, sai dai Ardayi ta saba kuma ba ta ganin hakan a matsayin wata matsala.

Hannu kawai ya d'aga mata bai iya furta komai ba har ta k'arasa kusan su Hadeeya da ba ta san akan me suke magana ba ta rumgume su su ma musamman Hamdeeya har tana fad'a mata "Shoyerta (autata) ki kula da kan ki."

"To Momma." Ta fad'a cike da farin cikin za ta tafi unguwa na wasu kwanaki, suna kallo ta shiga motarta ta bar gidan.

Sai lokacin Hameeda da ita ma dai wata arniyar shigar riga da siket na shadda ne jikinta tace" Kama da matar auren ma wacce ta haihu, dan wannan hijabi da ta saka sai matan aure masu 'ya'ya, dubi fa daga nan baya har k'asa yake ja mata."

Kallon hijabin na ta sukayi kam mai hannaye wanda ya mata kyau sai kawai suka bushe da dariya suka tafa hannu Hadeeya na fad'in" Wa ya ga ta Allah."

Murgud'a baki Hameeda tayi ta harari Saleema tace" Wai a haka za ta bi mu, ki ga fuskarta ko hoda ba ta murza ba sai k'yallin mai take, mtssss! Ni wallahi da Abba da ma ka hanata zuwa."

Wani kallo Saleema ta ma Hameeda sai kuma ta kalli mahaifin na su da duk da yana jin me ke faruwa amma hankalinshi na ga waya yana latsawa tace" Abba ka a yaran nan magana mana, dubi fa shigarsu?"

Wayar da ya d'ora a kunne ya sa shi nuna mata su wuce su tafi kawai dreba na jiransu, cike da takaicin halin ko in kula ta fara yin gaba ta shige motar.

Tsaki Hameeda ta sake ja har suka k'arasa kusa da mota inda dreba ke jiransu suka shiga ya jasu zuwa gidan.



*______________*




*Alhamdulillah.*
09/06/2022 脿 22:37 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�


_Bismillahir rahamanir rahim_


_7_




Tabbas sun yarda Alhaji Auwal ya fi mahaifinsu kud'i nesa ba kusa ba, dan daga irin ginin da ya tarwatsa za ka fahimci haka, da kuma irin kayan alatun da suka k'awata gidan, ba su daina kalle kalle ba har mai aikin da ta musu jagora zuwa cikin gidan suka shigo k'aton falon.

Saleema da ke baya cikin sharb'eb'en hijabinta kallo d'aya ta ma uwar gidan ta saki murmushi saboda tuna shekarun baya da su ka sameta tana cikin ganiyar k'uruciyarta mace yar gayu da wayewa, amma yanzu shekaru sun lak'ume duk wannan ji da kan da k'uruciyar, ba abinda ya rage mata face dattijuwar fuskarta mai d'auke da gilashi.

Kusanta suka fara zuwa inda take zaune, Hadeeya da Hameeda daga tsaye suka gaisheta da "Ina yini?"

Hamdeeya kuma kusanta ta zauna dan ta san matar ita ma tana wangale mata baki sai dai ba ta ce mata komai ba, yayin da Saleema dake gefe ta durk'usa kamar za ta yi zaune tace "Ina wuninku Mama."

Da fara'a da kuma jin dad'in gaisuwar ta Saleema ta kalleta cike da kulawa tace "Lafiya lauSaleema, kina lafiya?"

"Lafiya lau." Ta fad'a cike da kunya, maida hankalinsu sukayi kan wata dattijuwar da ke shigowa falon hannunta rik'e da waya, kallo d'aya suka mata ita ma suka gaisheta kasancewarta amaryar gidan. Cike da yauk'i da jan aji ta wani yatsina fuska tace "Lafiya lau, har kun iso ?"

Kafin kowa ya ce wni abu Hameeda ta kalleta tace "Aunty ina *Ummeeta*?"

Cike da yatsina fuska tace "Ta na ciki." Ta fad'a tana nuna mata k'ofar da ta fito, mik'ewa Hameeda ta yi ta nufi d'akin suka bi bayanta da kallo, wani d'an murmushi amaryar ta saki saboda sak ta hango Hameeda da d'anta Mu'awwaz a matsayin ma'aurata, a ganinta ba k'aramin kyau za su yi ba. Dan haka ma ta wuce inda za ta je ta na ayyana abubuwa da dama a game da ganin Hameeda, dan sam shigarta ba ta d'auketa bakin komai ba sai kawai wayewa da zamananci, sannan ta na da labarin ilimin yaran daga wajen mahaifiyarsu.

Hajia *Rabi* ce ta kalli su Hadeeya tace "Ku wuce ciki kuma, kun san ana rana duka yaran su na bacci."

Tab'e baki Saleema ta yi a ranta ta ayyana "Tunda an saba musu ba."

Mik'ewa sukayi Hajia Rabi ta kalli mai aikin tana fad'in "Ki nuna musu inda aka gyara musu, idan su ka yi wanka sai ki kai musu abinci."

Kallonta Saleema ta yi sanda suka kama hanyar d'akin tana mamakin to wankan me za su yi? Ba fa daga wani garin suke ba, tafiya ce da ba ta wuce minti ashirin ba, amma dai ba ta ce k'ala ba suka wuce cikin.



*_____________*



K'aramin littafin dake d'auke da kala-kalan abincin da aka mik'o masa ya girgiza kai tare d'an murmushi yace "Um-um! Nagode da wannan ma."

Kyab'e fuska *Sharhasila* ta yi kamar za ta yi kuka tce "Haba dai Yallab'ai, ka zab'a mana, ni fa zan biya."

D'an sunkuyar da kai ya yi kamar mai tunani sai kuma ya d'ago ya sake girgiza kai yace "Ya isa haka Baby, kin san bana son zuwa irin wuraren nan cin abinci, hasalima ni na fi jin dad'in cin abincin gida."

Had'e fuska tayi tare da kawar da kai sam abinda ya fad'a bai mata ba, to ita ina za ta iya wani girki? Tabb'! Kallonshi tayi tace "Yallab'ai, amma dai ka san ba ni zan dinga girki ba idan mun yi aure ko?"

Da mamaki Huzeifa ya kalleta yace "Ban gane ba? To wa zai yi? Ni?"

D'an murmushi ta yi cike da shashanci tace "A'a haba, ina nufin sai mu samu yar aiki."

Iska ya feso a bakinshi yana jin wani b'acin rai na hauhawa masa, to shi bai san wane irin aure ne za su yi da Sharhasila ba, dan tana tak'amar ita yar mai kud'i ce, kuma ita ta nunashi ta ce tana so, sai ya zama zai zaunata mulkeshi ne? Abubuwa na hauka da kidahumanci ta ke kawo masa fa, wannan wane irin abu ne?

Kallon kyakyawar fuskarta ya yi wacce ta fad'a masa wuni ta yi wajen gyaran jiki da kwalliya wai dan za su had'u wurin cin abincin nan kawai wanda shi a wajenshi bai da wani anfani, cikin tausasa murya yace "To me yasa ke ba za ki dafa ba?"

Turo baki ta yi irin shagwab'ar nan cikin harshen faransanci tace "Amma Bebe ai kasan ni aiki nake zuwa ko? Yaushe zan maka girki sannan na yi aikina? Ba zan iya ba gaskiya."

Shi ma a harshen faransancin yace "To ai macece ke, kuma ba'a yi auren ba, zaunawa za ki yi kafin lokacin ki tsarawa kan ki rayuwarki, kar ki maida hankali kan abinda ba zai anfani lahirarki ba, Sharhasila wannan aiki da kike moriyarki da shi iya duniya ne kawai, idan ki ka fi k'arfin shed'an ne za ki nemi lahirarki da aikin, dan haka a ganina tun ba'a d'aura aurenmu ba ki tsarawa kanki komai ta yanda za ki ba wa komai lokacinshi yanda ya kamata."

K'ank'ance ido yayi sosai ya na ci gaba da kallonta yace" Kin san wani abu? Mutum ne ni mai matuk'ar son kulawa, hakan yasa mahaifiyata ke fad'a min wai wasu lokuta kishi nake da k'annaina..."

Yar dariya ya yi ya d'ora da" Gaskiya ne, sai na ji idan ina magana da ita bana so kowa ya mana kutse bare a tilasta mata raba hankalinta gida biyu, sannan ina da matuk'ar son abincin gida, ma'ana ina son abinci irin su tuwo, d'an wake, faten doya, biski, dambu...da sauransu."

Tsareta ya yi da ido yace" Da fatan dai duk kin iya wannan? Idan ma ba ki iya ba ina fata za ki koya saboda ni."

Tunda ya fara magana ta zuba masa ido ta na kallo, dogon bayanin nan da ya zauna ya na mata sai ta ji kanta ma ya fara ciwo, to ita kam ta rasa hadisi na nawa ya karanta mata, a gaskiya ba ta ma gama fahimtar zancen shi ba, dan haka ta na buk'atar k'arin bayani.

D'an gyara zama ta yi tana kallonshi tace "Bebe ban gane ba, ka min dalla-dalla mana, ka na nufin ni ma sai na koyi iya tuk'a tuwo kenan?"

Murmushi ya mata yace "B za ki iya ba kenan?"

Kawar da kai ta yi tana nazari na wasu dakik'u, a gaskiya duk yanda take so da k'aunarshi ba za ta iya wannan wahalar ba, amma kuma sanin waye Huzeifa ya sa ta d'an yi wata shawarar, tunda dama ba shi ya fara cewa ya na son ta ba, ita ce ta ji ta na k'aunarshi saboda kyawawan halayenshi har ta masa tayin soyayyarta, da fari kam ya nuna baya ra'ayi saboda kasancewarta 'yar mai kud'in unguwarsu, amma da ta dage ya kuma shawarci mahaifiyarshi sai ya amince har yanzu suke shirin zama mata da miji nan da kwanakin da ba zasu gaza goma sha biyar ba. Dan haka ta kalleshi da murmushi a fuskarta tace "Bebe, ai kasan soyayya ta sa na ce ina sonka, dan haka ba abinda ba zan iya yi maka ba."

Fad'ad'a Murmushin shi ya yi yace "Nagode sosai, ai na d'auka ba za ki yi ba."

Da irin zolaya tace "Ni na isa? Idan fa ka fasa aurena?"

Dariya ya yi cikin tattausar muryarshi yace "Ba zan fasa aurenki ba, sai dai na miki kishiya bayan auren."

Zaro ido ta yi ta dafe k'irjinta cike da tashin hankalin da ya ziyarceta lokaci d'aya tace "Bebe, dan Allah ka daina min irin wasar nan bana so..."

Tsal! Ta taso daga kan kujerarta ta dawo kusa da shi sai dai dake babu wata kujerar sai ta durk'usa k'asa ta rik'o hannunshi, da sauri ya d'an jaye hannunshi saboda gudun matsala, dan baya son ya sake shiga halin da ya shiga d'azu daga kallon wata.

Sake rik'o hannun na shi tayi ta rik'e gam tana kallon idonshi da na ta idon da sukayi jajir suka tara ruwa alamar kuka, cikin rikitacciyar murya ta dinga mitsika hannunshi ta na fad'in "Ka na ji ko B茅b茅 ? Dan Allah ka daina irin haka bana so, ka ga ba zan iya kishi da wata a kan ka ba, dan Allah ka min alk'awarin ba za ka tab'a min kishiya ba?"

Da mad'aukakin mamaki ya kalleta sosai ya na nazartarta, daga bisani numfashi ya sauke yana ci gaba da kallonta yace" Tashi ki zauna, kina ga fa kallonmu a ke."

"Ni ban damu ba su kallemu, ka min alk'awari ka ji mijina." Ta fad'a da alamar fashewa da kuka, jinjina kai ya yi yasake nuna mata wurin zaman da d'aya hannunshi yace "Dan Allah ki zauna sai mu yi magana."

Da sauri ta mik'e ta zauna ka kujerar ta zuba mi shi ido ta na kallo kamar wanda take son gano ta inda yake fitar da numfashi. A hankali Huzeifa ya d'an girgiza mata kai cikin sanyayyar muryar da hakan d'abi'arsa ce yace mata" Ba zan iya miki wannan alk'awarin ba *Sharha*, saboda ni d'an adam ne ban san me Allah ya tsara min a gaba ba."

Jin hakan daga bakinshi ya sa ta fashewa da kuka da iya gaskiyarta kawai ta kifa kanta a kan teburin, cike da damuwa da jin tana muzantashi cikin mutane ya k'ara tausasa murya yace" Dan Allah Sharha ki daina kukan nan, kin ga tashi mu bar nan in dai kuka za ki min."

Kamar ba ta san ya na yi ba haka ta dakeshi, mik'ewa ya yi ya sake maimaita" Tashi mu je na ce."

Nan ma shirun ta masa, ranshi ne ya d'an fara b'aci dan haka ya zagaya kusanta ya d'auki jakarta da wayarta da makullai dake aje, bai tsaya jiran komai ba ya finciki hannunta suka fita a wajen dan shi fa duk taushinshi mutum ne kuma da baya son iskanci, sam ba zai lamunci ta mayar da shi wani lusari ba dan baya da kud'i sannan *mad'inki ne* shi, haka kawai ba za'a raina masa wayo ba, ta ya ma zai mata wannan alk'awarin? Ta san me alk'awari yake nufi a shari'ance? Ta san me zai faru da shi idan Allah bai nufeshi da cikawa ba? Ba ma duk wannan ba shi fa gaskiya *mace mai addini* ya ke da burin samu, hakan yasa ya ke tunanin ko ya aureta idan bai sameta yanda ya ke buk'ata ba to indai ya samu halin k'ara aure to zai k'ara, sai kuma ta nemi katse masa hanzarinsa da wani tunaninta irin na hayudawa haka kawai.

Tuk'i kawai yake a motar ta ya na kallonta jefi-jefi, yanda ta d'aga hankalinta akan tashin d'aukar mata alk'awarin nan da irin kukan da ta yi, a ganinshi ko iyayenta aka ce sun rasu iya hakan ne kawai za ta yi, idonta sun yi jajir sosai sun kumbura abu ga jar fatar da ba ta saba da hayaniya ba. Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon gabanshi yace "Ki yi shiru Bebe, kukanki fa ya na tab'a min zuciyata sosai."

"To idan ka hakane ka min alk'awarin mana." Ta fad'a kamar za ta matso daf da shi ta sumbace shi, d'an tab'e baki kawai ya ui ya girgiza kai bai ce mata komai ba, cikin tausa murya tace "Bebe me ye a ciki ne wai? Alk'awari fa kawai za ka d'auka da fatar baki."

Wata nauyayyar ajiyar zuciyar ya sake saukewa yace "Sharhasila hadisin Anas d'an Malik fa ya ji daga bakin Manzon Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login