Showing 174001 words to 177000 words out of 191031 words
ta matso nonon har yayi tsartuwa a fuskar Abdus-samad dake shirin zama kusa da ita yana son 蓷aukar yaron, da sauri ya kalleta yana kallon nonon data mayar a riga yace "茦walele ne kike min?"
Girgiza kai tayi a sanyaye ita dai dan su rabu lafiya tace "A'a wallahi, ba dagangan bane."
Zaune yayi kusanta daf da daf ya kai hannu yana 茩o茩arin ciro nonon, ri茩e hannunshi tayi tace "Baban 蓷ana, ka ga dai wallahi Ummi fa蓷a take min idan ta ga ka ta蓳ani sai ta ce banna da hankali, wai ko araba'in 蓷in Abba ban yi ba amma na yarda kake ta蓳ani."
Ha蓷e fuska yayi irin sosai din nan yace "Na ce miki wani abu zan miki? Ruwan da na ga suna ta zuba ne fa zan gani ya suke."
Da sauri ta 茩ara matse rigarta tace "Farare ne, fari tas wallahi."
Harara ya galla mata yace "In gani to, idan ba haka ba wallahi a kai zan 蓷auke ki na kaiki 蓷akina, kuma dai kinsan me zai faru."
Bu蓷a tayi da alamar mamaki sai kuma ta sassautawa hannunshi ri茩on da ta mishi, ciro nonon yayi yadda yayi 蓳ul-蓳ul da shi ya dinga kallo yana ha蓷a yawu, satar kallonta yayi yace" Da za茩i sosai ko?"
Makale kafa蓷a tayi tace" Ni ma ban sani ba."Tana rufe baki ya kai bakinshi kan nonon yana fa蓷in" Bari muji ya 蓷an蓷anon yake, ai kinga mun manta sanda mu muka sha...umumumumum"
Lumshe idanu dukansu sukayi inda Saleema ta matse 茩afafunta gam, dan fa ba laifi gyara na 茩asa da 茩asa ta sha a hannun Mamanta da kuma jakadiyar nan dattijuwa, madadin ya saketa sai ya tallabo bayanta yana kwantar da ita a kan gadon shi kuma yana 蓷agowa daga zaman da yayi har ya mata runfa. Jin yadda nononta ya saki alhalin 蓷azun a tumbatse yake da ruwa yasa ta saurin tureshi ta tashi zaune tana ta蓳a nono, kallonshi tayi shi kuma yana kallon 蓷aya nonon tace "Inna lillahi! Haba Abban Abba wannan wane irin abu ne? Dubi fa ka shanye mishi madara, ya zanyi kenan idan ya tashi anjima?"
Lumshe mata idanu kawai yayi yana lashe la蓳蓳anshi, matsawa yayi kusanta idanunshi sunyi jajir alamar da magana a 茩asa cikin rarrabe kalamai yace" Matan...mu, kinga...dai arba'in 蓷in nan..ba kyau in ji malamai, tunda kina sallarki...me zai hana ki ba mijinki ha茩茩inshi? Hakan fa...zai sa ki zama 拼ar aljanna...lamba 蓷aya."
Turo baki ta ma茩ale kafa蓷a tace" Ni fa gaskiya tsoro naje ji."
Da sauri ya kalleta ya dakata daga shafar cinyarta yace" Tsoron me, ba gani nan ba?"
Girgiza kai tayi tace" Ummi ba za ta bari ba, kuma idan na sake 蓷aukar wani cikin fa? Abba ko wayo baiyi ba."
Da sauri yace" ba za ki 蓷auka ba, Ummi fa ta baki magani kinsha ko?"
Girgiza kai ta sake yi alamar dai ba ta yarda ba, Mi茩ewa yayi yana cije fuska yace" Shikenan, abun farin cikin shine da Allah ya yo ni sarki, gida cike da hadimai kala-kala, sai fa wacce na za蓳a ma za'a wanketa yanzun nan a kawo min 蓷akina ta tayani bacci."
Sunkuyawa yayi ya sumbaci yaron sannan ya nufi hanyar fita yana fa蓷in" Ke tunda ba ladar kike bu茩ata ba ai shikenan, gasu nan hadiman kullum cikin kwarkwasa suke da kwalliya dan dai na waiwayesu..."
Da gudu ta tare gabanshi tana kallonshi a marairaice tace" Tsakani da Allah za ka uya neman hadimarka?"
Kawar da kai yayi yace" Me zai hana? *Mallakina ce* fa."
Girgiza masa kai tayi ta tallabo kumatunshi tace" Dan Allah ka min al茩awarin ba zaka sake sa茩a hakan a zuciyarka ba, ni kuma wallahi zanyi dubara na zo 蓷akin naka yanzu."
Kallonta yayi yace" kin tabbata?"
Da sauri tace" Allah kuwa." Jinjina kai yayi ya tallabo ha蓳arta ya sumbaci bakinta yace" Sai kin zo."
Yatsa ya nunata da shi yace" Amma ki sani idan baki zo ba zuwa sade za ki ji shelar sarkinki ya bu蓷e wata sabuwar a leda."
茦ura masa idanu tayi tace" Wallahi dan kana sarki ne da sai in wanke fuskarka da mari, Abdul ya kake wula茩antani haka?"
Shafa kuncinshi yayi yana murmushi ya ra蓳ata ya wuce bai ce mata 茩ala ba, da kallo ta bishi har tana jin yana ma Ummi saida safe ita ma ta amsa, zaune tayi tana tunanin yadda za ta yi ta je dakin shi Ummi idanu take saka musu sosai, shi kanshi da ya jima yanzu da ta shigo ta ce tana son ganinshi, ta kusa awa 蓷aya tana tunanin yadda za ta yi sai kawai ta mi茩e tana murmushi, hijabinta ta 蓷auka ta saka ta fito ta samu Ummi ta mi茩e ita ma tana shirin shiga ta gansu sannan ta kwanta.
Da mamaki ta kalleta tace "Lafiya na ganki da hijabi haka?"
Ba alamar wani 蓷ar 蓷ar tace "Ummi, wani littafina ne nake ta nema ina son karantawa, shine nake so na duba a 蓷akina ko 蓷akinshi, ina tunanin a can na barshi."
Kallonta tayi sosai kamar mai son gano gaskiya, sai dai dake bata ga alamar inda inda a tare da ita ba ko rashin gaskiya sai ta jinjina kai tace" To amma kiyi sauri, kinga da 茩ofar ce zan rufe."
"To Ummi." Ta fa蓷a tana kama hanyar fita dake sadata da na ta falon, har tayi nisa Ummi tace "Ina nan fa ina jiranki." Ta fa蓷a tana zama akan kujera, jinjina kai tayi ta fice a 蓷akin, murmushi Ummi tayi tana ayyana in dai har sai ta je 蓷akinshi, to fa ba yanzu za ta dawo ba.
*Alhamdulillah.*
29/06/2022 脿 20:57 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
_Bismillahir rahamanir rahim_
_56_
*Bayan wata biyu*
Kallonta Saleema ke yi tana murmushi, ita ma da murmushin a fuskarta tace "Wallahi gimbiya ba zan 蓳oye miki, ni da na ga dinkin ya birgeni sosai, shiyasa na kai wa mai 蓷inkinmu na nuna mata hotonki na ce irin shi muke so, wallahi da aka mana 蓷inkin sai bai ma Yayata ba yadda ta ganshi a jikinki, shiyasa ta kuma siyan wata shaddar ta ce na kawo miki ki mata idan ba damuwa."
Wayar dake hannunta ta 蓷an daddana ta nuna mata tace" Kinga wanda aka mana 蓷in."
Kar蓳a tayi ta duba da kyau sannan tace" 茒inkin yayi, sai dai a irin shaddar da akayi shi ne bai dace ba, sai kuma kwalliyar wannan da iya rabin wuyan aka saka da ya fi."
Mi茩a mata wayar tayi tace" Ba damuwa aunty, in sha Allah za'a mata kamar waccen 蓷in."
Kayan ta kar蓳a ta 蓷auki abun rubutu ta warware rigar da aka ba do a matsayin awo ta dinga aunawa sannan ta maida mata rigar tace" Jibi za'a iya zuwa a kar蓳i kayan."
Waro idanu tayi tace" Jibi ka蓷ai?" Dariua Saleema tayi tace" Gobe ma dan akwai wasu ayyukan da ke gabanmu."
Jinjina kai tayi tace" To shikenan Allah kaimu, nawa ne za'a bayar?"
Girgiza kai tayi tace" Idan aka zo amsa sai a biya."
"Tooo." Ta sake fada tana tsareta da idanu sanda ta mi茩e tana ri茩o gyalenta ta baya tare da 蓷aukar Abdallah dake neman 茩iyawa.
Komai dama aka ce da sannu sannu ake farawa, 茩alubalen da suka fuskanta a baya sai gashi yanzu nema yake ya zama tarihi, a da sai su kwana biyu babu 蓷inkin, amma dalilin 蓷inkin da ta zanawa kanta na sunan yaronta yanzu za ta iya kar蓳an 蓷inkin uku na manyan mata ko fiye ma da haka, yanzu haka su kansu yaran shagon basa zama babu aikin, kullum cikin aiki suke da kuma kar蓳an ba茩uncin mata. Mata kuma dama da zamani suke tafiya, 蓷inkin ko babu kwalliya indai zasu sa ya bi jikinsu a ce sun yi kyau to an gama, sannu sannu wannan ya ga 蓷inkin ya ce ina aka miki? Waccen ta ce kai ma wacce, sai komai ya fara tafiya musu daidai yadda suke da bu茩ata, yayin da wasu kuma su kan zo ne kawai dan gani da idansu da aka ce gimbiya Haleematu ce, hakan yasa yanzu kullum cikin kar蓳an ba茩i take iri daban daban, dan ma wasu idan ta ga irin wayayyu ne an zo mata gida da matsatsun kaya kai babu 蓷ankwali sai ta ce a jirata a shagon sai ta saka hijabinta da ni茩ab ita ta samesu a can, wasu kuma ta kan basu damar samunta a falonta gudun kai da kawonta kar yayi yawa tsakanin gidan da shagon. A haka har suka saba sosai da Hajia Mardiya da kuma matar shugaban 茩asa Hajia Balaraba wacce aka fi kira da Hindu.
Kallon envelope 蓷in ta sake yi sannan ta 茩ara ri茩e wayar a kunnenta tace "Saleema, envelope na gani, da gaske Yaya Huzeifa zan kai wa?"
Murmusawa Saleema tayi tace "Da gaske mana, zan miki wasa ne Fareeda?"
Jinjina kai Fareeda tayi tace "To shikenan, zan tafi yanzu na kai mishi, Allah yasa alkairi ne."
Dariya Saleema tayi tace "Alkairi ne ma in sha Allah."
Da haka suka yi sallama Fareeda ta 蓷auki adaidaita zuwa gidansu bayan ta sanar da mijinta ya ce ba damuwa, a shago ta sameshi daidai Sudeis ya kawo mishi ruwa daga cikin gidan ya fita, da kallo ta bi yaron da tausayi kafin ta 茩araso ta zauna suna gaisawa yace "Daga ina kike?"
"Yaya daga gida." Ta fa蓷a tana ciro envelope 蓷in nan a jakarta ta mi茩a mishi, kallonta ya fara yi yace "Me ye kuma wannan?"
Murmushi tayi tace "Karb'i mana Yaya, sa茩o ne aka ce na kawo maka."
"In ji wa?" Ya fa蓷a yana kallonta sosai, saida ta sauke ajiyar zuciya tace "In ji gimbiya Saleema uwa ga mutan mara蓷awa."
Gabanshi ne ya fadi sosai har saida ya 蓷an dafe 茩irjinshi ya furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Sai kuma ya kara kallonta yace "Wasa kike min Fareeda?"
Sani dake zaune gefensu ne yace "Ta ya zata maka wasa da sunan gimbiya kuma? Kar蓳a ka gani malam."
Fareeda kuma sake mi茩a mishi tayi ya kar蓳a jiki a sa蓳ule ya shiga bu蓷ewa dan hada tambarin dake nuna lallai daga masarautar mara蓷awa sa茩on ya fito, fito da abun ciki take suka waro idanu dukansu, kallon Fareeda yayi yace" Ku蓷i ne fa."
Jinjina masa kai tayi tace" Ta tambayeni ko har yanzu kana 蓷inki ne na ce me kuwa zai sa ka daina, ta tambayeni maganar karatunka fa? Na ce rayuwa ce ta sa ka ajiye neman aikin ka ci gaba da sana'arka, shine ta turo wannan ta ce na kawo maka kayi anfani da shi."
Kallon ku蓷in yake irin yadda suke mi茩e zatt sai 茩yalli suke, a hankali ya fara maidasu a envelope 蓷in yana fa蓷in" Kenan bata manta dani ba? Kullum gulmata kuke ko?"
Dariya Fareeda tayi tace" A'a wallahi Yaya, ni ina ga ma sau biyu ka蓷ai muka ta蓳a... " Da sauri ta nuna mishi wata 拼ar takarda da ta fa蓷o daga ku蓷in tace" Yaya takarda."
Aje ku蓷in yayi ya 蓷auki takardar ya warware, da manyan ba茩i da kuma harshen hausa ne aka rubuta sa茩o kamar haka _" Ka 蓷auki hakan a matsayin kyauta daga 茩anwarka, ban ji da蓷in yadda komai ya faru ba, hakan yasa ko godiya ban maka ba, ina ma za ka ga shagon 蓷inkina? Na san da ka fini farin ciki."_
Daga 茩asa ka蓷an aka rubuta _*" Nagode Yaya Huzeifi, daga Saleema.*"_
Tun yana sakin murmushi har ya fashe da sanyayyar dariya yana 茩ara kallon takardar kamar wani zararre yake fa蓷in" Allah sarki, Allah sarki, ka ji ita ma shago ta bu蓷e na 蓷inki, tabbas na ji da蓷i kula ina miki fatan alkairi, kuma dama na jima da hango hakan, da yardar Allah sai kin fini shahara da cin anfanin 蓷inki."
Sai kuma ya kalli Fareeda dake ta doka murmushi yace "Ashe bata manta sunan nan ba Huzeifi, ina ma zan ganta da idona ta kirani da Huzeifi ko alhudahuda?"
Mi茩ewa Fareeda tayi tana sa蓳a jakarta tace "Ba ko za ka ganta ba wallahi, dan ko mijinta ba lallai ka gani ba idan ba a tv ba."
Hannu ta tara mishi tace "A bani ku蓷in adaidaita to."
Dariya yayi ya ciro jaka goma a cikin ku蓷in yace "Fareeda ai kin fi k'arfin na adaidaita, kar蓳i ke ma kisha shagalinki."
Godiya ta masa sosai dan ta san dama zai iya yi mata hakan dan har yanzu tsaye yake a kansu da bu茩atunsu, har za ta fita yace "Idan kunyi waya ki gaidamin ita, kuma ki ce nagode sosai."
Jinjina kai tayi ta fita a shagon, Sani dake kallonshi da mmaki ne yace "Ban ta蓳a ganin an maka kyauta ka kar蓳a lokaci guda ba bare kuma har kayi ta wannan farin cikin."
Girgiza kai yayi yana murmushi yace "Wannan kyautar ta musamman ce, ku蓷in nan da takardar tamkar kayan tarihi haka zan adanasu."
Murmushi Sani yayi yace "To a bani ladar ganin idanuna dai kafin a kaisu gidan tarihin?"
Ba musu shi ma ya bashi kamar yadda ya ba Fareeda sauran kuma ya maida a envelope 蓷in tare da takardar sannan ya jawo 蓷an gidan da ake ajiye zae da allura ya saka ciki kafin ya tashi tafiya gida. Tsananin farin cikin da ya shiga ne ma ya mantar da shi yawan 茩uncin da yake shiga idan Sudeis na kukan Mamanshi wacce yanzu ta kusa kile shekara 蓷aya a gidan yari tana kar蓳an hukunci, shi ba dan yaron nan ba da ko tunanin Sharhasila ba zai sake yi ba a rayuwarshi, shiuasa ma haka na faruwa ya tattaro kayan yaron dake gidansu Sharha ya mi茩awa matarshi amana, yanzu haka ta ha蓷a Sudeis 蓷in da 茩aninshi da ta haifa mishi ko wata 蓷aya ba'a yi ba.
_______________
Abdallah na kwance kan 茩irjinshi yana bacci ita kuma kanta na kan cikinshi tana zanenta a takarda kamar yadda ta saba, kallon yadda take zanen yake yi yace "Matanmu, wato ni ne aka 蓷auka shashasha ko?"
Kallonshi tayi tace "Lahh! Da aka yi me gwanina?"
Hararanta yayi yace "Sai kawai kika koyi 蓷inkin mata, ko sau 蓷aya ba ki yi tunani a kaina ba."
Dariya tayi ta mi茩e 茩afarta 蓷aya tace "Kwantar da hankali shalele, ina nan ina zanen yadda babbar rigarka za ta kasance."
"Da gaske?" Ya fa蓷a yana kallonta, 蓷aga masa gira tayi tace "Da gaske mana."
Lumshe idanu yayi yace "Kin san me, ya kamata ki maida hankali kiyi zane na musamman da zaki shigar da kayan gasar fitattun 蓷inkuna na wannan shekarar wacce ake yi tsakanin 茩asa da 茩asa."
Bu蓷e baki tayi ta zaro idanu tace "Wace ni yalla蓳ai? Ka san da ko shiga nayi sai nayi nasarar lashe gasar a iya nan garin fa kafin na wakilci Mara蓷i mu isa ga matakin 茩arshe a babban birni, haba daina maganar nan ma."
A hankali ya tallabo Abdallah ya kwantar da shi gefenshi sannan ya 蓷aga kanta sukayi zaune suna kallon juna, hannayenta ya ri茩e yace" Kinsan wani abu?"
Girgiza kai tayi alamar a'a, a nutse yana wasa da yatsunta yace _" Ni ba ma蓷inkiya nake gani a nan zaune tare dani ba, *瞥AR BAIWA* nake gani, Saleema ba wai burinki na son 蓷inki ya kasa cika da wuri bane saboda an hanaki cimmasa, ni abinda nayi tunani shine, burinki bai cika da wuri bane saboda babban buri kike 蓷auke dashi, ba kowane mai 蓷inki bane ke iya zanawa sannan ya fitar, amma kowane mai zane ma蓷inki ne, *Ummu Abdallah*, ki kalli kanki a madubi sannan ki tambayi kanki wa蓷annan amsoshin, na farko wacece ke? Na biyu, me kike so a rayuwarki? Na uku, ya matsayin da kike kai yanzu? Na hu蓷u kuma ki tambayi kanki *Mecece Baiwarki*?"_
Mi茩e 茩afafunshi yayi tare da jawo kanta ya 蓷ora a cinyarshi yana shafawa yace" Idan kika samo wannan amsoshin to za ki san manufar da ta sa kika ala茩antu da 蓷inki, baiwarki ba za ta tsaya wajen yi ma mata 蓷inkin biki ko na anko bane, idan kika yi tunanin ciyar da harkokinki gaba, ina mai tabbatar miki za'a kai matsayin da duk wata celebrity idan ba ke kika zana mata kayanta ba to za ta ji kamar ba ta cika mace ba."
Tunda ya fara magana zuciyarta ke kakkarwa jikinta na tsuma tamkar an fara mata ki蓷an gangi, yanzun da kanta ke saman cinyarshi sai ta shiga sakin murmushi tana shafa cinyarshi, tabbas gaskiya ya yi, kuma ya kamata ta yi wannan tunanin tun tuni, amma hankalinta bai zo nan ba sai yanzu da adalin mijinta ya hasko mata shi. Ha茩i茩a ba abinda za ta ce ma bawan nan sai godiya, da fari ya cika mata burinta wanda ko iyayenta basu iya taimaka mata da komai ba, yanzu kuma gashi yana son sake 蓷orata a hanyar da za ta nemo *BAIWARTA* a duk inda take.
*Washe gari* da safe tsaye take gaban madubi tana 茩arewa kanta kallo tamkar yadda yace, irin yadda ta mulmuje tun bayan haihuwarta da kyawun da fatarta tayi, sannan wani leshe ne a jikinta da ta ma sassau茩an 蓷inki amma ya yi kyau sosai, 茩an茩ance idanu tayi ta furta "Wacece ni?"
Ta jima tana kallon kanta kafin tace _"Wacce aka haifa da buri, sannan za ta mutu da buri, haka Allahn daya haliccemu ya fa蓷a."_
Sai kuma ya karkace kanta tana tuno tambaya ta biyu cewa me take so a rayuwarta? Tsayar da kanta tayi wuri 蓷aya tace _"Ina son mijina, iyayena, 蓷ana da wa蓷anda zai haifa anan gaba, surukata mai 茩aunata, sai kuma jama'ar da mijina ke mulka... Ummmm! Sai kuma...*sana'ata*."_
Murmushi tayi sannan tace" Sai na uku."
Alamar tunani tayi kafin tace _"Matsayi ne na shahara da ban ta蓳a tunanin zan samu kaina a ciki ba."_
Rumgume hannaye tayi tace _*" BAIWATA?* TANA INA? TA YA ZAN SAN TA?"_
茦urawa kanta idanu tayi ka 蓷auka baiwar ce z ata fito a idanunta ta ganta, ta jima haka da sauri ta 茩yasta hannu tace _*" Ilimina na addina, Zanena, 蓷inkina, mijina shine *BAIWATA.*"_
Da sauri ta juya ta fita a 蓷akin ta nufi 蓷akinshi dan sanar dashi ta gano *BAIWARTA* itama yanzu, abu ne da bata ta蓳a tunanin kawoshi a ranta ba bare ta tambayi kanta mecece baiwar ta ta, amma sanadiyar mijinta gashi yau ta gano baiwarta, a hakan ma wai wanda suka bayyana a gareta ne,