Showing 54001 words to 57000 words out of 191031 words

Chapter 19 - BAIWATA COMP HAUSA NOVEL

30 Aug 2024

67971

tsaye da alama ita yake jira, yana ganinta ya juya zai fita a falon, 蓷agawa mahaifiyarta hannu tayi dake tattare kwanukan dake kan tebur, ita ma hannu ta 蓷aga mata tace "A dawo lafiya Hajiar Babanta."

Ardiya da yau ba aiki take zuwa ba saboda lahadi ce ta kallesu sannan ta ta蓳e baki, Saleema ta bi da kallo tana ayyana ina ma Hadeeya ce haka ta faru da ita? Ai da mahaukaciyar kwalliya za ta mata, sai kuma wata zuciyar ke raya mata "Me ma yasa duk 茩o茩arinsu a makarantar boko ba su ta蓳a samun irin wannan karramawa ba? Me gwamnan zai mata?"

Da sauri ta mi茩e daga falon ta shiga 蓷akinta tana kiran lambar amaryar gwamnan wacce ko shekara ba ta yi ba a gidan, saboda 茩awancensu kawai za ta nemi alfarma ta saka mata idanu a kan zuwansu ne dan kar a samo wani abu a hanata dan ba ita ta haifeta ba.


*Suna* fitowa farfajiyar gidan mai gadi na tahowa a guje, yana zuwa ya zube 茩asa da alamar rikicewa a tare da shi ya 蓷aga hannu yana jinjinawa tamkar yadda ake gaishe da sarakai yake fa蓷in "Yalla蓳ai ba茩i ne, ba茩i ne a waje suna son ganinka, sa茩o ne daga *fada*."

Da alamar rashin fahimta Alhaji Yusuf ya kalleshi yace "Kai nutsu dallah, fa蓷a min su waye a wajen?"

Mi茩ewa yayi jikinshi na rawa dan abin da ke wajen nan ya fi 茩arfin wasa, lamarin ya jijjigashi ba ka蓷an ba, takardar dake 蓷aya hannunshi ya mi茩o mishi yana fadin "Duba ka gani."

Fizgar takardar yayi ranshi 蓳ace da tunanin shirme kawai yake mishi ya fara warware tsadaddar envelope 蓷in mai ban sha'awa fara tas tare da tambarin da aka yi zagayayyen rubutu aka rubuta *mai mara蓷awa*, yana warwarewa ya fara karanta doguwar takardar mai 蓷auke da nutsatsen rubutu da manyan ba茩i kamar haka.

_"Aminci, salama, albarka ta tabbata ga iyayen wannan yarinya *HALEEMATU YUSUF JIJI*, bisa 茩o茩ari da jajircewa na wannan yarinya fadar mara蓷awa na gayyatar wannan yarinya da iyayenta dan kwatanta karramasu tun a nan duniya kamar yadda Allah ya yi al茩awarin mayar da iyayen mahaddata Al茩ur'ani mai girma sarakai 茩ar茩ashin inuwar al'arshinshi mai girma, fatan za su amsa mana wannan gayyata da gaggawa?"_

_Sa茩o daga mai girma sarauniyar mara蓷awa *Hajia Ramlat Ali Haidar Kiari*._

Zazzaro idanu yayi ya zubawa mai gadin yace" Kai shashashan banza, wa ye ya baka? A ina ka 蓷auko wannan takardar?"

Nuna masa 茩ofa yayi yace" Ai Alhaji suna nan waje, suna nan wallahi suna jiranka."

Da mugun sauri ya tunkari hanyar fita, har kusa rabin tafiya sai kuma ya juyo da gudu gudu ya nufo Saleema dake tsaye ta rasa me ke faruwa, dan ita maganar mai gadina shirme ta 蓷aukeshi ita ma, ra蓳ata yayi ya shiga falon ta bishi da kallo, matsawa tayi daga jikin 茩ofar ta 茩arasa kusa da motar mahaifin na ta wacce mai gadin ya gama wankewa hancinta ya kalli 茩ofar fita, tsaye take tana jiran fitowarshi dan ta tabbatar zai fito.

"Tohhhh." Saleema ta ambata a zuciyarta ganin mahaifinta ya fito da wasu sababin kaya ba wanda ya saka yanzu ba, kuma wannan 蓷in kaya ne da ita dai za ta ce ta jima rabon da ta ganshi da irinsu, wato babbar riga da yar ciki ga kuma hula, duk da mahaifinta ya girma amma fa idan ya 蓷auki wani shirin ita kanta birgeta yake har tayi fatan samun mijin da ya iya 蓷aukar wanka kamar sa, abun mamaki duk da shirin da yayi madadin ta ga tafiyarta tamkar ta 蓷awisu data saba gani, amma sai ta ga yana tafe yana gyara kayanda kyau da hular kanshi sannan da sauri kamar zai tashi, kuma ko kallonta bai yi ba kai tsaye waje ya nufa sai hannu da ya mata alamar ta taho. Tunanin da ya zo mata ne yasa ta 蓷aga 茩afa ita ma da sauri ta bi bayanshi.

Ba ta 茩arasa kaiwa ba ta ji an 蓷auki wata irin busar sarewa a 茩ofar gidan tare da wani irin kirari da ya yi kama da mutanen gargajiya, ma'ana daga masarauta suke, jiki a sa蓳ule ta fito tana son ganin me ke faruwa a nan 蓷in, sai dai bai bata damar gane komai ba ya nuna mata wata irin Prado da aka bu蓷e alamar ta shiga, da mamaki a fuskarta ta nufi motar za ta shiga dan ba za ta iya musa mishi a wurin nan ba, za ta shiga motar wani galadima da ya fi sauran 茩warin murya ke fa蓷in "Takawarki lafiya ba茩uwar sarauniyarmu, gaba salama baya salama, *拼ar baiwa*, 拼ar albarka irin albarka, wacce ba ta gaji tsiya ba."

Baki bu蓷e take kallonshi da ma sauran galidiman da suke cikin kaya iri 蓷aya, duka manyan riguna ne da rawuna a kawunansu, inda rigunan nasu ke da wata irin kala ta yelow mai haske da ja. Ta na shiga motar aka rufe sanda mahaifinta ke daf da shiga da tunanin nan zai zauna shima, sai dai ina wata motar aka nuna mishi dake gaban motar da take wacce 茩arama ce 茩irar Mercedes kamar sauran motoci hu蓷un, ta biyar 蓷in dake tsakiya ita ce Saleema take ciki, suna gam shiga gaba蓷ayansu aka tashi motocin cikin nutsuwa suka 蓷auki hanya, mai gadi dake 茩ofa yana kallonsu cikin farin ciki da jin da蓷i yake fa蓷in "Allah ya tsare, Allah ya kiyaye, ai da ka ga wannan kiran ka san alkairi ne, in sha Allah da arzi茩in da ya fi na ku za ku dawo, kira daga fadar mara蓷awa? Ai ku gode Allah kawai."

Tsare tsaren lamarin gidan sarauta Saleema ta zubawa ido tana kallo, tunda suka samu wucewa babbar 茩ofar fadar da 茩yar da caje caje aka rabata da mahaifinta aka ce za'a kaishi wajen gagara badau ita kuma aka yo wannan falo da ita mai neman zautar da ita, wani gauron ajiyar zuciya ta sauke tana sake ha蓷e jikinta waje 蓷aya domin sanyin falon ratsata yake yi kamar a garin 茩an茩ara, sanyin kansa idanunta ba su nuna mata na'urar dake busa mata jikin da falon gaba蓷aya ba, uwa uba irin tarin abubuwan da aka jere mata cikin wasu irin kwanonin da ko wu茩a za'a 蓷ora mata a saman wuyanta ba zata ta蓳a iya bu蓷e su ba balle har ta anfana da abin da yake ciki, kai ta tabbata idan ta yi garajen cin abu 蓷aya a nan sai ta 蓳arke da zawo, domin ba kalar cimar da ta saba 蓷auka bace.

Shirun falon ya fi komai damunta, kanta a 茩asa duk a tsorace take, bata san cewa babu wanda zai iya yin 茩wa茩waran motsin 蓷aga hankali a irin wannan lokacin ba, *mai jiran Gado* bai shigo ya gaisar da mahaifiyar tasa ba, yau an sako shi a gaba da ba茩i kuma 茩a'ida ne baya tsallake rana 蓷aya bai le茩o inda mahaifiyarsa take ba.

A ka蓷an ta 蓷auki kusan awa 蓷aya da rabi a zaune, tun 茩afafunta basu gajiya ba har suka fara mata zogi kafin ta ringa jin murya na gabatar da isowar wacce aka kira da gimbiya uwar marayu, uwar talakawa, uwa a wajen jama'ar MARA茒I.

Mi茩ewa ta yi tsaye a lokacin da matar ta 茩arasa saukowa, domin cikar zatin halittarta da lallausan murmushin da take fitarwa dole ya saka ka girmama girman darajar sallolin nafila dake 茩ara haskaka goshin makusancin ubangijinsa.

茦asa Saleema ta so zubewa dan gaishe da matar, sai dai kafin ta karasa ta ji wani hannu mai laushi ya tarota an mi茩ar da ita tsaye, saida matar ta 茩arewa fuskarta kallo kafin ta saki lallausan murmushi a hankali ta janyota jikinta tana furta "Masha Allah, Masha Allah, Assalama alaiki hasken matasa."

Ita 蓷in da kanta sakin lalausan murmushin da ya sake haska tata fuskar tayi, madadin ta zaunar da ita a 茩asa sai ta zaunar da ita kan kujera sannan ta zauna gefenta ta ri茩o hannunta tana kallonta da murmushi tace " Saleema 拼ata ya gida, ina Umminki da Abinki? Ya ya karatu?"

Cike da kunya da girmamawa Saleema ke bata amsa, ita kuma tana sake jin da蓷in hirar da ita sosai, ba wani sha mata 茩amshi ko ja mata aji kamar yadda wasu gimbiyoyin ke yi take ta hirarta Saleema wace farin ciki ke cike a cikinta, yau ita ma gata ga sarauniyar garinsu wacce ko kallon a hoto ba ta ta蓳a tunanin ganinta ba, dama dama ma sanda Allah ya wa mai martaba rasuwa sun zo tare da iyayensu wajen gaisuwa, amma fa basu samu damar ko da shigowa babban falo da ta ji ana magana ba bare su ga wani daga cikin iyalen mamacin.

Shigowar jakadiya da du茩awarta nesa kadan ya sa su maida hankali gareta, muryarta a tausashe kanta a sadde sosai take fa蓷in "In sha Allah Mai jiran gado zai 茩araso nan da 拼an mintuna."

Jin haka ya saka Saleema bin gimbiya da kallo ganin duk 茩amshin 蓷akin da sanyin 蓷akin ta saka an 茩ara wani, du irin tsaftar dakin ita da kanta ta mi茩e tana kallon wajen da zai zauna 蓷in sannan ta dawo ta zauna tana murmushi ta fara sanar mata ko wanene aka kuma sheda 茩arasowarsa dan haka ta yi shiru.

Idannunta ita kam a 茩asa suke, kwata kwata bata ji takun tafiyarsa ba, sai lallausan 茩afafun da idanuwa ka蓷ai sun isa su shaida ma ka laushinsu masu 蓷auke da gashin saman 拼an yatsu ba茩a茩e si蓷ik, lallausa masu she茩i da girman 茩afar suka shaida mata mai 蓷auke da su 蓷in namiji ne, dan haka ta 蓷ago da dubanta hankali kwance ta sauke a kansa a lokacin da ya 蓷an ja ya tsaya da mamakin ganin wata ba茩uwa na zaune daf da daf da mahaifiyarsa zama irin wanda rabonsa da ganin mutum ya mata haka har ya manta.

Ido cikin ido suka kalli juna, 茩ara kallonsa ta yi harda 蓷an wara idanunta sai kuma ta 蓷an ta蓳e bakinta ka蓷an ta janye dubanta a kan fuskarsa a ranta ta ayyana "Allah mai girma da iko, mai tsara tsarin halita, ga fatarshi dai mai duhu, amma yana 蓷auke da kyakyawa kuma salihar fuska."

Wani mamakin ya nemi kasheshi ganin ya 茩ara second kusan goma bai ga zubewarta 茩asa da di蓳an gaisuwarta ba, bai san cewa bata ta蓳a sanin hakan ake yi ba da ta yi, domin ita 蓷in bata cikin masu raina wasu ma balle wannan da take tunanin ko wanene babba ne a gidan sarautar, dan ita kam wallahi bata sanshi ba.

Ganin kamar a tsayen nan ya 茩i motsawa, ita kuma tana so ta basu waje sai kawai a 茩asan ma茩oshi cikin sriryar muryar ta a nutse ta furta " *Barka dai.*"

Mi茩ewa ta yi ta 蓷an zagaya ta nufi hanyar da aka biyo da ita da nufin basu waje dan ta lura kamar hakan ya ke so, gimbiya da ta 蓷an zaro idanu ta kalli yaronta ganin har yanzu yana tsaye sai ta bi Saleema da kallo ta sakar masa murmushin da ta tabbata zai sanyaya abin da take hange a yanayinsa tana kallon jakadiya na nunawa Saleema wajen da zata zauna, ta yaba hankalin yarinyar na basu wajen da ta yi domin dama ba'a zama idan zai gana da mahaifiyarsa.

Sai da ya daina jin motsin kowa sannan ya 蓷aga 茩afarsa ya 茩arasa gabanta ya du茩ar da kansa 茩asa sosai ya 蓷ora hannunsa saman 茩afarta da ya ga ta 蓷an kumbura alamar ta yi tafiya sosai bayan tana fama da hawan jinin da ya zame mata ciwon 茩afa kuma an hannata yawan taka kafar a sanyaye sosai ya gaisheta irin gaisuwar da yake yi mata ita daya jal a kaf duniya.

Da murmushi ta janye 茩afar tata dan bata so ya fara magana a kan 茩afar da dan zumu蓷i ta shiga labarta masa ko wacece Saleema da kuma dalilin ganinta a nan 蓷in da ya yi ta 蓷ora da fa蓷in "Kar kalar gaisuwar da ta maka ta 蓳ata maka rai Abbana, ka san bata san ya ya ake yi ba na tabbata shi yasa, yarinyar akwai hankali da nutsuwa, dama iyayenta zasu bani ita da mun bu蓷e islamiya a nan falona muna karatu."

Duk irin wannan doguwar maganar da ta yi amsar da ya bata 蓷aya ce 茩wal, dan shi a ganinsa wannan 蓷in ai bai shafe shi ba, ita ma amsar a 茩asan ma茩oshi ya amsa da" *Uhum!*" Kawai kuma mata shiru bai yi alamar zai sake cewa komai ba.

Baki ta ta蓳e da 蓷an jin haushin amsarsa, ita kam miskilancin 蓷an nata wani sa'in haushi yake bata! A tausashe ya dubeta yace "Ummi, likita ya ce ki rage taka 茩afar nan, dan Allah ki rufa min asiri ki rage taka ta."

Dakatawa ya yi ka蓷an da maganar yana sake hango 茩afar da take 蓳oyewa yace "Bani 茩afar na murza Ummi."

Ajiyar zuciya ta sauke ka蓷an ta mi茩o masa 茩afar, kamawa ya yi ya 蓷ora saman tufafinsa a hankali ya shiga murzawa yana 蓷an jan yatsun ya sake 蓷agowa yace "Ummi kin ci abinci kuwa?"

Nan ma amsar ta bashi wace ta saka shi yin murmushi domin sai da ta fa蓷a masa komai da ta ci ya ji cewa bata ci magi ba balle yaji, saida ya gamsu da murza 茩afar sannan ya sake sadda kansa yana jin adu'o'inta a gareshi, har ta gama sannan ya mi茩e ya mata sallama cike da 茩aunarta a zuciyarsa ya kama hanyar ficewa.

A lokacin da ya fito sake tsayawa ya yi ya kuma zuba idannunsa a kan yarinyar, ba komai ya sa haka ba sai dan yana so ya tantance abinda mahaifiyarsa ta fa蓷a da kuma shi wanda yake gani, abinda yake gani kawai tsagerar 拼a ce marar kunya da zata dube shi ta ce masa wai Barka dai, Barka dai? Barka dai kamar ka fa蓷a ma irin 茩anin an naka, barka dai gaisuwar da ko mahaifiyarsa ba haka suke yi ba, barka dai amsar da shi yake badawa ne ba wai wacce ake bashi ba. Yanzun haka mahaifinta ya baro mutum mai kamala, wanda saida ya du茩a ya gaisheshi duk da ya tareshi, sai dai ita 蓷in bata da kunya.

Gashi yanzu ma dan kuturun wula茩anci ya na tsaye yana kallonta amma gaba蓷aya ta maida dubanta kan tv da ba kunne take ba, Saleema kuma tsarguwa ce ta sakata 茩urawa waje 蓷aya ido tana Allah Allah ta bar gidan nan mai cike da shiru da takura ta ko ina.

Juyawa ya yi cikin takun 茩asaitarsa da ya sakata saurin juyowa tana satar kallonshi har ta0 sage wuya dan kallonsa, har ga Allah sai ta ji tausayinsa har take ji kamar ta mi茩e ta je ta taya shi 蓷aga kafar ya taka da kyau, wannan tafiya haka shi yake yi ama ita ce ta gaji daga zaunen nan, dan ya kai minti 蓷aya kafin ya fice a falon da ita a ganinta idan ta tashi ai kamar wal茩iya za ta wuce.


*Ga mai bu茩atar humra ta musamman ta yi magana kafin ta 茩are, humra ce da sai kin gwada kawai za ki ga alfanunta ta hanyar ganin murmushin mai gidanki fiye da baya, humra ce da wasu sinadaren da ba'a saba ha蓷a humra da su ba馃 wacce ta shirya siya kawai za ta min magana. Ga anfani ga sau茩i, 茩aramin awo bakin farashin 1000f ga 拼an niger, ga 拼an Nigeria kuma 1000k.*




*Ru茩ayya* (Mrs Abdul) wannan page ta ki ce kyauta.




*Alhamdulillah.*
09/06/2022 脿 22:49 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�


_Bismillahir rahamanir rahim_


_22_




Fitowar nutsatsiyar gimbiyar tare da wasu hadimai a bayanta yasa Saleema mi茩ewa tsaye tana mamakin ta ina suka shiga 蓷akin, idan ta canka daidai 茩ofofi ne bila adadi a gidan na sarauta, al'amarin ya so zautar da tunaninta sanda gimbiya Ramlat da kanta ke feshe jikinta da wani ha蓷a蓷蓷en turare mai sunan *Maryam*, sannan ta umarci jakadiyarta d ta saka mata alkyabbar nan, ba 蓳ata lokaci aka shiga sakawa Saleema wata rantsatsar alkyabba fara tass mai kwaliyya sosai da birgewa, ta 蓷auka an gama yanzu kam gida za ta tafi, sai jakadiyar ta sunkuya ta aje mata wasu takalmi na fara farare sak irin alkyabbar jikinta, wasu irin 茩ananan jakunkuna guda biyu gimbiya Ramlat ta kar蓳a a hannun wata hadima ta ba wa jakadiyar dake kusa da Saleema sannan tace "Ki kai mata sa茩on nan motar da za ta mayar da ita gida cikin aminci."

Kallon fuskar Saleema tayi tare da yin takwaf takwaf d fuskarta, dan gaskiya ba dan ba ya daga cikin al'adarsu auren dole ba, da ta nemawa *yarimanta* auren kamilar yarinyar nan, ita dai kyawunta take gani fiye da kima, sannan nutsuwarta take gani fiye da tunanin mai hasashe, ba dan yau ne ha蓷uwarsu ta farko ba kar yarinyar ta ga wautarta, da ta fashe mata da kukan shagwa蓳a sannan ta ce mata "Dan Allah ki auri 蓷ana, ko shi ma zai shiga sahun masu cikar kamala wacce aure ka蓷ai ke samawa bawa ita."

Amma sai ta shafo fuskar Saleema tace "Allah ya miki albarka, Allah ya baki miji na gari kamar *蓷ana*, wanda zai kula da ke ya mutumtaki."

Cike da kunya Saleema ta sadda kanta 茩asa sannan ta amsa 茩asan makoshi da "Ameen."

Alamu ta mata da cewa "Ki je, na san yanzu Abbanki na jiranki."

Rusunawa tayi kamar za ta sunkuya tace "Nagode ranki shi da蓷e, Allah ya 茩ara lafiya da nisan kwana mai albarka."

Murmushi kawai tayi tana jin kewar yarinyar na lullu蓳eta tun bata mata nisa ba, tana kallo jakadiyar da hadiman nan suka tisa Saleema a gaba har suka fice a falon na ta na musamman, tsintar kanta tayi da yi wa yaronta addu'a ya samu mata kamar yarinyar nan.

Abbanta na tsaye yana jiranta jikin mota, da idanu kawai ya rakata ganin wata shiga da aka mata tamkar wata gimbiya ko sarauniya, shi dai bai gushe yana kallon 拼ar tashi ba har saida suka shiga mota aka 蓷auki hanyar mayar da su gidansu, a lokacin ne kiran sakataran gwamna ya kirashi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login