Showing 99001 words to 102000 words out of 191031 words

Chapter 34 - BAIWATA COMP HAUSA NOVEL

30 Aug 2024

67993

ji kunya ma dan ta san Mu'awwaz dai ba bacci yake a wannan lokacin ba, takaicin duniya haka ya isheta ita da Ummee har Ummee ta tafiyar, saida aka kwashe awa uku cir kafin ta fito a mugun jikkace, Gaishata ba tace musu komai ba musamman da ta ga Mu'awwaz na kallon Nafissa yana dariyar mugunta, har ta蓳ata yake yi gabanta sai kawai ta ga ya fi alkairi ta ja baki tayi shiru, fita sukayi tare da kanshi ya jasu zuwa gidan. A mota ma sai ya kalleta ya 茩yal茩yale da dariya yace "Ya dai?"

Harara kawai take banka masa dan ita gaba蓷aya jikinta ne bata jin da蓷inshi, wata hikima ce ta ubangiji da ya sa har cikin jikinta ma ke tsaye a mahaifarta har yanzu, amma a jijjigar bala'in da ya gani da ya zube yanzun, dan kuwa zuwa na 茩eta ya mata ba sassauci. Har suka isa gidan bai daina mata dariya ba, Gaishata data yi saurin fita tana tsaki ne ya ba Nafissa damar wulla masa harara tace "A ganinka bajinta ka yi? 茦arfin maganin?"

Murmushi ya sake yi ya jinjina kai yace "Idan kin dwo anjima sai mu jaraba babu maganin mu gani."

Turo baki tayi ta jingina kanta a jikin kujera ta lumshe idanu, ta 蓷an jima haka kafin ta kai hannunta kan mararta tace "Ba lallai ya rayu, ciwo nake ji nan sosai, na san ma ka lalata min shi."

Da sauri tamkar wanda dama 蓷abi'arsa ce nuna mata damuwa ya 蓷ora hannunshi dake kan mararta cike da kulawa yace "Ke! Ba bakinki ba, zai rayu in s..."

Sai kuma yayi saurin 蓷auke hannunshi yana kawar da kai da nuna bai damu ba yace "Sai me? Sai ki samu wani ai."

Kallonshi tayi ta girgiza kai sannan ta zura hannu ta bu蓷e motar, kamar daga sama ta ji muryarshi a tausashe yace "Daga nan zan wuce siyo miki maganinki, zan kawo miki nan sai ki sha."

Juyowa tayi ta kalleshi sai kuma ta ta蓳e baki tace "Uhum!"

Har za ta fita ya sake fa蓷in "Ku蓷in bikin fa?"

Komawa tayi ta zauna tace "Na manta ai, kawo to."

Murmushi yayi ya sa hannu aljihu ya ciro ku蓷in ya 茩idaya sannan ya mi茩a mata, da mamakin yawan ku蓷in ta kalleshi tace "Duka?"

Da idanu ya mata alamar e, ta蓳a baki tayi ta fita tare da rufo masa 茩ofar, zagayawa tayi ta kama hanyar shiga gidan, jin bai tashi motar ba yasa ta tsayawa ta juyo, idanunshi na kanta kamar mai son ganin ta shiga sannan ya bar wurin, irin yadda ya tausasa kallonshi gareta yasa bata san sadda ta masa alama da idanu ba tace "Tafi mana."

Girgiza mata kai yayi sannan yace "Ki shiga."

Sa alamar tambaya tace "Ba ka yarda dani ba?"

Girgiza mata kai ya sake yi alamar a'a, murmushi ta saki wanda a tsawon zamansu ba ta ta蓳a kwatanta yi masa ba sannan ta 蓷aga masa hannu tace "Sai ka dawo."

Murmushi ya kuma sakar mata da ya masa kyau a fuska, juyawa tayi ta shige ciki tana sakin 拼ar dariya ta ayyana "Me ke damunmu yau?"

Haka ta shige gidan inda hankalinta bai kwanta ba saida ta ga Saleema, 蓷akinsu Saleemar ta yada zango har ta samu ta 蓷an kwanta dan sosai bata jin da蓷in jikinta, Saleema kuma har tsokanarta take ko dai za ta sama musu baby ne? Murmushi kawai take ba ta ce mata e ko a'a ba, kamar yadda ya fa蓷a kam bai fi minti talatin ba ya dawo ya kawo mata maganin, kuma har 蓷akin su Saleema ya shiga ya kai mata, abunda ya tsayawa Nafissa a rai shine ruwa sa ya sa Saleema ta kawo masa ya bata da kanshi kafin ya tafi, ita kanta Saleema saida tayi mamaki dan tunda ta ha蓷a aurensu baya kulata, maganarshi da ita marar da蓷i ko kuma gatse, amma yau sai ta ga hada tausasa mata yake har suka gaisa irin gaisuwa sosai.




*Alhamdulillah.*
09/06/2022 脿 22:50 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�


_Bismillahir rahamanir rahim_


_34_




Biki ya yi biki in ji mawa茩i sarkin wa茩a, an yi hidima sosai mata ma su aji kowace ta nuna ta ta bajintar da wayewa, daga 茩arshe dai dare na yi masu niyya suka shirya dan raka amarya 蓷akinta, Saleema ma ba'a barta a baya ba ta rufa musu baya dan rakiyar 茩anwarta 蓷akin mijinta tana mai mata faran farin ciki da zaman lafiya, duk da dai wannan biki da aka yi ta ga abubuwan al'ajabi, a ciki kuwa har da yanzun da suke kan raka Hadeeya gidanta, kwalliyar da aka mata ta ban mamaki yasa aka hanata yin ko da 茩walla na ba茩in cikin rabuwa da iyayenta, tana ji tana gani 茩anwarta ta fita a gidan ba alamar jimami ko ba茩in ciki bare damuwa na za ta tafi ta riski wata sabuwar rayuwar.

_(Kwalliyar da ake ma amarenmu yanzu har da kunya take gushe mana, dan wannan kwalliyar take hana amarya zubar da hawaye dan kar ta 蓳ace, wanda a al'adance mun saba ganin amarya na kuka, muna yara har hakan ya kan zama abun alfaharinmu mu ga amarya na kuka za'a kaita 蓷akin miji, amma ban da amaren yanzu, 茩o茩ari ma suke fuskarsu ta fito da kyau wajen 蓷aukar su hoto dan kar a ga muninsu, a cikin hotunan amarya guda goma bakwai idanunta na kallon camera ne, Allah ka shirya mana zuri'armu)_


Tunda Mu'az ya samu labari a wurin wani abokinsu cewa ai har da Saleema a gidan amarya ya tarkato duk abinda yake ya zo nan, duk inda ta gilma a 茩ofar gidan Hadeeya yana biye da ita sai dai bai yarda ta ganshi ba yana la蓳e, ba komai ya sa shi zuwa ba sai sanin akwai abokansu dayawa ire-irenshi, dan haka ba ya fatan a sapu wanda zai tunkareta da ko da maganar banza a wurin, dan haka yake tsaye kan duka wani motsinta har saida ya ga an fara mayar da mutane gida, saida ya ga motar wanda ta shiga tare da wa蓷anda suka shiga motar ya samu nutsuwa ka蓷ai ya bar 茩ofar gidan shi ma.


*A can* kuma sanda gidan yayi shiru sai ma'aikata dake ta gyaran gidan da wanke wanke, lokacin Ardiya da Gaishata suka shige 蓷aki tare da Hajia Iklima da ita fa duk ku蓷in nan na su take ganin ta fi su, ji take kamar a 茩auye take a gidan nan, ta matsu ta tafi gida ta huta, amma Ardiya ta ri茩eta wai za su yi magana mai mahimmanci, yanzu haka fuskarta a yatsine take tana ta ma 蓷akin na Ardiya da ko a 茩asar waje sai haka kallon wani kurkuku, ba dan nata 蓷akin ya di na Ardiya ba sai dan son nuna matsayinta ya fi na su.

Ardiya da ta maida hankalinta garesu gaba蓷aya ne tace "Hajia, kin san me na gani kuwa yau a gidan nan?"

Fuska a gatsine ta girgiza kai kawai alamar a'a, 蓷orawa tayi da "Hajia, wallahi da idanuna da kuannuwana na ji yalla蓳ai yana fa蓷awa wannan banzar ba茩auyar yarinyar wai yana sonta kula zai aureta, yau na ga abun mamaki."

Da rashin fahimta Hajia Iklima tace "Ban gane, wane yalla蓳an?"

Gaishata da ta samu labarin tun zuwanta ne tace "Mijinki mana, Alhaji Nasir, ni ai abun hauka ya so sa ni."

茦u茩茩ura musu idanu tayi tace "Ban gane ba? Wace yarinya ya ke so?"

Ardiya ce tace " 瞥ar kishiyata mana, wannan marar ajin Saleema."

Wani mugun kallo ta aiki musu tace "Mijin na wa?"

Sai kuma ta feso iska a bakinta ta tashi tsaye ta 蓷auki jakarta tace "Sai anjima."

Da sauri duk suka tashi tsaye Ardiya na fa蓷in "Wallahi ranki shi da蓷e ba 茩arya muke fa蓷a miki ba, ni da idanuna na gansu, da safe sanda ya shigo nan ina masa godiya na abun arzi茩i da ya turo mana, sai mahaifinta ya ce ita ma wai ana son ganinta, na yi mamaki sosai shine na la蓳e dan na ji me ke faruwa, qhine na ji yana cewa yana sonta da aure har ma ya bata katinshi ta kirashi."

Gyara tsayuwa tayi cike da jin kai tace" Kun gane, bana ha蓷a komai da mijina a rayuwata, kada ku jazawa yarinya bala'in da kafatanin danginta zasu shaida ta ja rigima da ni, idan kun san da wasa kuke tun wuri ki daina, dan ku kanku zan iya aje mutumcinku da nake gani gefe na shuka muku ta'asar da bakuyi tsammani ba, kun gane?"

Cike da jin da蓷in zantukanta Gaishata tace" Ba wasa ba ce Hajia, wallahi gaskiya muke fa蓷a miki."

Ha蓷e fuska tayi sosai tana huci tace" Kenan shiyasa ranar ya gayyaceta har gidanmu? Na yi mamakin yadda ya kar蓳i ba茩i a wannan lokacin kuma a gidanshi, abu ne da baya faruwa."

Sai kuma ta kallesu tace" Me yasa kuka gaya min? Ba ku san zan iya 蓷aukan kowane irin mataki ba?"

Murmushi Ardiya tayi tace" Mun sani, kuma dan ba ma so haka ta faru shiyasa muka sanar da ke, ki 蓷auki matakin da ya dace kawai."

Wani malalacin murmushi tayi tace" Kinsan da zan iya komai a kan mijina?"

Kallon juna sukayi Ardiya da Gaishata sai kuma Ardiya tace" Saleema yarinya ce mai tsoro da taka tsantsan, ina ga ma kashedi ya isheta ta fita harkar mijinki, musamman idan kika mata barazana da Mahaifiyarta."

A 茩ufule, da sigar dabamci tace" Shikenan, zan ha蓷u da ita gobe, zan fara ganin me ye take da shi da bana da, kafin na kora mata kashedin."

Juyawa tayi rai 蓳ace ta fice a gidan Gaishata da Ardiya kuma suka fashe da dariya, Gaishata ce tace" Yar banzar yarinya, ba uta ta ha蓷ani da al茩a茩ai ba gashi nan har ta samu ciki tana shirin haifa min ba茩in jika, da yardar Allah ita ma ba za ta yi farin ciki a gidan aurenta b"

Dariya Ardiua tayi ta koma ta zauna tace "Ta ma fara samun wanda ya dace tukuna, ta ya Hadeeya ta auri wanda ko Mu'az bai kai da komai ba, sannan na yarda Saleema ta auri gwamnan garin nan? Ba na fa蓷awa Iklima bne dan ina sonta, dan ta 蓷aga hankalin kowa a fasa auren ya sa na yi haka, idan har ba ta samu mijin da bai kai Zeid ba to ba zan ta蓳a hutawa ba."



*Washe Gari*




茦arfe *05:14* Saleema ta fito da sauri za su tafi wajen damu tare da Nafissa, sosai doguwar rigar ankon atamfar ta mata kyau duk da hijabi ta 蓷ora wanda musamman 蓷inkashi tayi saboda ranar, har ta kai farfajiyar inda Nafissa ke jiranta Ardiya dake tsaye suna magana ita da 拼ar uwarta tace "Saleema."

"Na'am." Ta fa蓷a tana juyowa, nuna mata falon tayi tace "Je 蓷akina ki 蓷auki turarukan Hadeeya na nan a kan gado ki tafi da su."

"To." Ta fa蓷a da sauri ta dawo 蓷akin tana rataya jakarta 茩arama akan kafa蓷a, tana shiga 蓷akin mace biyar ta samu suna ta hira, a jumlace ta gaishesu da "Ina wuninku." Duk da wasu daga ciki sun gaisa tun sanda suka zo, amsawa sukayi 茩asa 茩asa har ta ra蓳a ta nufi kan gadon. Wata kakkauran mata mai 茩iba ce ta mi茩e tsaye tana fa蓷in "Ku fito mu jira waje ko, Hajia Iklima amaryar gwamna Alhaji Nasir za ta yi magana da mai shirin aye gurbinta."

Dammm! Gaban Saleema ya fadi tayi saurin kallon matar dake hakimce kan gado tana latsa wayarta, saida ta ji jikinta ya 蓷auki rawa dan ba ta san ita ce matarsa ba, 蓷aukar ledar da ta ga kwalaben turaruka tayi ta shiga jerin matan dake fita har da Gaishata dake dariya tana fa蓷in "Amarya kuma uwar gida ba, ta gidan ma ya ta iya da ita?"

Bushewa sukayi da dariya har da tafa hannu suka fice, matar nan mai 茩iba ce ta juyo za ta rufe 茩ofar ta ga Saleema bayansu tana shirin fita, da hannu 蓷aya ta hanka蓷ota ta dawo 蓷akin tana fa蓷in "Ba ki ji an ce za ta yi magana da ke ba ne?"

Tangal-tangal tayi kamar za ta fa蓷i kafin ta tsaya kan 茩afafunta, a hankali ta juyo ta kalli Hajia Iklima da har yanzu kamar ba ta san me ke faruwa ba, gyara tsayuwarta tayi tana ta kallon matar tana jira ta ji me za ta ce mata. Saida ta yi niyya da kanta ta sa 茩afarta da babu takalme ta turo kujerar robar dake gefenta sannan ta mata alama da hannunta mai waya alamar ta zauna, jiki a sanyaye ta ja kujerar ta zauna tare da 蓷ora ledar turarukan a cinyoyinta tana ci gaba da kallonta. Numfashi ta sauke tare da 蓷aukar jakarta mai kyau da tsadar gaske ta saka wayarta a ciki sannan ta maida hankalinta kan Saleema, a nutse cike da aji da yatsina fuska tace "Saleema ko? Gundarin ba茩i ba kame-kame ba, ina so ki sani ni ba tsararki ba ce da zaki dinga kula min mijina, ban sani ba ko uwargina kika sani shiyasa kike tunanin kin isa ha蓷a shinfi蓷a da mijina, to ki sani ni ba lusarar mace ba ce, ki fita a harkar mijina, a hakan ma dan ina ganin darajar Ardiya ne yasa na miki kashedin nan, ba dan haka ba zan iya aikata komai a kanki kuma ba za'a san ni nayi ba bare wani ya 蓷aga maganar, kin fahimta?"

Gyara zamanta tayi ta nuna mata 茩ofa tce" Za ki iya tafiya."

Jakarta ta sake 蓷auka ta ciro wayarta za ta ci gaba da dannawa, tashi Saleema tayi jikinta duk a mace ta kama hanyar fita, tana daf da fita ta 蓷aga kai ta kalleta tace" Da na ce zan iya aikata miki komai, ina nufin komai, daga ciki har da salwantar da rayuka, ki kiyaye."

Duk da a tsorace Saleema ta girgiza kai saida tace" Wa'iyazubillah! Da fari ina tunanin dalilin da gwamna zai sa ya ce yana sona, amma yanzu na fahimci dalilin, dole yana bu茩atar tsaftattaciyar soyayyar da ta nin茩aya a cikin tafarkin addinin islama. "

Sai kuma ta saki murmushi tace" Idan Allah yayi shine mijina bana jin akwai mahalukin da ya isa ya dakatar da hakan, amma ki sa ranki a inuwa, matashi ma mai jini a jika ya nemi aurena yanzu zai yi wuya na amince masa bare babban mutum irin wannan, na barki lafiya."

Tana fa蓷a ta juya ta fice bata jira ta jie za ta ce ba dan ta ga fuskrta da yanayin mamaki, dan batayi tsammani za ta fa蓷a mata haka ba, amma dai ta ji sanyi sanyi da ta ji alamu na nuna mata cewa ba lallai ta yarda da bu茩atar da mijin na su ya zo mata da ita ba.



*A gurguje*: a gajiye suka dawo gida sukayi wanka tarz da saka kayan bacci suka kwanta, kallonta Safiya tayi tace "Yau dai ki je 蓷akinku mana, mahaifinki mita yake wai ina rabaki da 拼an uwanki."

Kallonta tayi daga kwance tace "Mama yau kuma? Yaushe rabona da kwana 蓷akin? Kayana fa duk suna nan."

Tashi tayi zaune ta kalli mahaifiyarta da kyau ganin yadda take gurgurar goro saboda zuciyarta dake tashi, a tsanake ta shiga fa蓷a mata abinda ya faru jiya tsakaninta da gwamna da kula haukan da matarsa ta mata. Da mamakin wannan lamari Safiya tace" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Iklimar? Da wayonta?"

Ta蓳e baki Saleema tayi tace" Mama ba wannan ba, ni fa ba son mijinta na ke ba, ta ma daina wahalar da kanta a kaina, dan bai min ba."

Kallonta tayi da mamaki tace" Kina nufin ba kya sonshi?"

茒aga kai tayi alamar e, numfashi ta sauke tace" Kin fa蓷awa Abbanki?"

A 蓷an tsorace tace" Mama, shine nake tunanin kar Abba ya zo bai ji da蓷i, ki masa bayani da kanki."

Jinjina kai tayi tace" Shikenan, zan fa蓷amasa."

Murmushi tayi tace" Yawwa Mama."

Komawa tayi ta kwanta tana fa蓷in" Mama yau dai kar ki tasheni fitsari, dan ban sha ruwa ba."

Harara ta dalla mata tace" Ai tashin da kike min ne na tsana a rayuwa, a ce idan kina son zuwa 蓳an蓷akin sai kin tasheni na rakaki? Shiyasa idan na farka kafin ki tasheni ni nake tashinki."

Dariya kawai Saleema ke 茩yal茩yalawa tana fa蓷in" To Mama cikin daren sai na je ni ka蓷ai? Gwara ina ganin mutum a kusana ya fi."

Ta蓳e baki tayi tace" Na ga mijin da zai juri wannan shiriritar, namijin ne yana bacci zai tashi dan rakaki fitsari?"

Murmushin gefen la蓳蓳a tayi ta kalleta tace" Zai yi mama, zan sameshi, mai ha茩uri tamkar Yaya Mu'az."

Kallonta tayi tace" Da alama dai Mu'az 蓷in nan ba zaki manta da shi ba duk da abinda ya miki."

A sanyaye tace" Mama ta ya zan manta lokaci 蓷aya? Da sannu zan manta da shi da suk wani abu da ya koyar da ni shi."

Da sauri ta gyara kwanciyarta tace" Yawwa Mama, kuma kin gani, jiya hirarmu da gwamna saida na 茩aru da wani abu dangane da shekarun Nana Aisha (R. A), yana da ilimi, ga dattako, ga kirki kuma kyakyawa kamar ba tsoho ba."

Ta 茩arashe tana fashewa da dariya, duka Safiya ta kai mata tana fa蓷in" Ke rufe min baki, marar kunya kawai."

Dariya ta dinga yi har ta ji bacci na son 蓷aukarta, zaune tayi tsakiyar gadon ta 蓷aga hannayenta ta shiga karanta addu'o'inta na tsarin jiki kafin ta shafe jikinta ta kalli mamanta tace" Mama cin goron ya isa, ki kurkure bakinki sannan ki ui addu'a mu kwanta."

"To." Ta fa蓷a tana mi茩ewa ta shiga ban蓷aki, dan da wuya darzn da zai zo ya shu蓷e Saleema ba ta tunatar da ita addu' a kafin ta kwanta ba, ko da kuwa a 蓷akin mahaifinta za ta kwana ranar, dan haka 拼ar ta zamar mata tamkar 茩awa sannan abokiyar hira da shawara, kuma tana jin da蓷in yadda ita kanta ta 蓷auketa 茩awa.

Wannan karan dai ya goyi da bayan ra'ayin nata 蓷ari bisa 蓷ari, tunda Safiya ta shaida masa yadda sukayi da matar gwamnar ya ji gaskiya shi ma hankalinshi bai kwanta ba, dan gaskiya abinda zai ta蓳a masa lafiyar 拼a baya son shi ko kusa, da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login