Showing 3001 words to 6000 words out of 191031 words

Chapter 2 - BAIWATA COMP HAUSA NOVEL

30 Aug 2024

67960

Ardayi dake d'an gyara matsatsan rigarta mai k'ananan hannaye ce ta d'an tab'e baki tace" To ita kanta karatun ya sha mata kai ne bare kuma ta koya ma 'yarta?"

Sai lokacin kad'ai Safiya ta kalleta tace" Kinga, idan muna magana tsakaninmu ki daina saka min bakinki, bana so."

Kallonshi tayi fuskarta a d'aure tace" Me ya sa ka hanata kyautar ita ma?"

K' ank'ance ido yayi da mamakin tambayarta yana d'an gyara rigarshi ta shadda da aka ma k'aramin d'inki kasancewarshi d'an zamani bai cika son manyan kaya ba yace" Ban gane ba? Ke baki ji abinda na ce ba ce?"

D'auke kanta tayi daga gareshi sannan tace" Gaskiya ba ka adalci ko kad'an, ita ma fa haihuwarta kayi kamar sauran, me yasa za ka dinga fifitasu a kan ta?"

" Saboda sun fita. " Ya fad'a cikin d'aga murya, ido cikin ido ta kalleshi kafin ta kalli Saleema tace" Zo nan."

Da sauri Saleema ta k'arasa gareta tana matso k'walar da suka taru a idonta, kama hannunta tayi suka juya a wurin suka barsu nan, tab'e baki yayi irin ko a jikinshi kafin ya shiga wata sabgar.


*Kwana uku* kenan da faruwar wannan abu ya ga sauyi sosai daga Safiyar, dan ta daina walwala haka ma Saleema ba ya ganinta a falon tana wasarta, wanda dama ko can ita kad'ai takr wasar suma su Hadeeya suna ta su, k'arara duk mai ido ya ke gane da bambaci a tsakanin matan, wanda ba komai ya jawo haka ba sai fifikon da amarya ta samu fiye da uwar gida, ita ma kumata same shi ne dalilin dogon karatun da tayi wanda a yanzun take cin gajiyarshi ta hanyar aiki a banki.

Tsakanin mata da miji dama aka ce sai Allah, damuwa da hakanyasa shi dawowa gidan bayan ya tabbatar yaran na makaranta kuma Ardayi na wajen aikinta, a d'aki ya sameta kwance da alamar bata jin dad'in jikinta, k'arasawa yayi ya zauna kusa da ita yana kallon kyakyawar fuskarta wacce tana d'aya daga cikin abinda yasa har yau yake tare da ita da kyautatawa.

Hannu ya kai ya tab'a wuyanta yace "Me yake damunki ne?"

A hankali ta yunk'ura ta gyara zamanta kafin tace "Ba komai."

Da sauri ya fuskanceta sosai ya rik'o hannunta yace "Safiya hushi kike da ni akan abinda ya faru? Kiyi hak'uri kinji, b'acin rai ne ya sa da kula son da nake ma Saleema, ina so na ga ita ma ta zama kamar 'yan uwanta, shiyasa kika ga ina haka."

A tausashe ya d'an fara lumshe ido ya kwanto da ita jikinshi cikin muryar da ta fahimci kan zancen yace" Kiyi hak'uri kinji *Sofee*."

D'an murmushi tayi ta d'ago daga jikinshi za ta yi magana, sai kuma ta yi saurin rufe bakinta saboda aman da ya tuk'ota, da sauri ta sake toshe bakin tana had'eshi gudun kwafsawa, cike da kulawa ya kalleta yace" Oh! Baki da lafiya ne? Me yake damunki ne?"

Sunkuyar da kai tayi cike da kunya ta girgiza kai, d'an kawar da kai yayi a ranshi yana mamakin kunya irin ta Safiya, shekara goma sha d'aya da aure amma har yau kunyarshi take, shi ba zai iya tuna ranar da ta nuna mishi buk'atarta ba sai dai ya karanta a tsakiyar idonta ko daga jin sautin muryarta, hakan na birgeshi matuk'a a game da ita, sai dai kuma a matsayinsu na ma'aurata yana so ya ga tana komai b'aro b'aro, duk da dai hakan ba wata matsala ba ce dan kunyar tana taimakonshi sosai. Sake kallonta ya sake yi yace "Safiyyyyya."

Yanda ya ja sunan na ta ya sa ta d'agowa ta kalleshi, da murmushi a fuskarshi yace "Ko dai ciki gareki?"

Da sauri ta rufe fuskarta ta sake duk'ar da kanta tana ji kamar ta nutse k'asa, cike da farin ciki ya jawota jikinshi yana fad'in "Masha Allah Sofee na, dama kullum addu'ata Allah yasa ke ce za ki haifa min auta a gidan nan, kin san na fad'a muku yara shida na ke da buk'ata a rayuwata, idan ma zan samu k'ari to kar su wuce bakwai."

Ita dai rufe fuskarta tayi da da rigarshi tana mamakin tsari irin na shi, in banda abun shi ko wa ya fad'a masaana wa Ubangiji iyaka? Wato shi ne ma zai k'ayyade yaran da yake so ya haifa a duniya.

D'agota yayi yana lek'a fuskarta yace" Amma dai ki shirya mu je asibiti dan a duba lafiyarku, bana so na rasa wannan Safiya kamar yanda na rasa sauran."

Narai narai tayi da manyan idonta tace" Bana tunanin wannan ma zai tsaya, kamar sauran shima na san zai tafi ne."

Girgiza kai yayi yace" A'a ki daina fad'in haka, in sha Allah za ki haifeshi. "

Kamar za ta fashe da kuka ta kalleshi tace" Abban Hajia shida fa, shida na samu duka suna zubewa, har hutu aka bani ko hakan zai sa a dace amma har yanzu shiru."

Cike da jimami da tausaya mata ya k'ara rumgumeta a jikinshi yana rarrashinta, kasancewar d'akin a bud'e take yasa Saleema da ta taso daga islamiyya shigowa kan ta tsaye ba tare da tunanin za ta samu mahaifinta a d'akin ba duba da kwana uku kenan ma ko magana ba ta ga sunayi da mahaifin na ta ba, sai dai tana ganinshi ta zabura ta juya za ta koma waje, inda Safiya ma ta firgita da sauri ta mik'e daga jikinshi tana son matsawa nesa da shi, da mamaki ya kalli uwar ya kuma kalli 'yar, sai ya rasa duk me ye haka d'in? Kamar wani wanda aka kamada wata matar? Da fa Ardayi ce ba ruwanta, hasalima ita har kayan baccin take sakawa kuma a gaban yaran, idan ta kama ma har rumgumeshi za ta fara yi a hakan kuma a gabansu, a ganinsu dai ai iyalinsu ne ba komai.





*Alhamdulillah.*
09/06/2022 脿 22:37 - MOM LATEEF馃槝: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*BAIWATA*
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 馃馃
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
鈽� *[G. M. N. A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�


_Bismillahir rahamanir rahim_


_3_




Cikin ladabi Safiya ta kalleshi tace "Abban Hajia."

"Na'am." Ya amsa yana kallonta, ci gaba ta yi da cewa "Dama Saleema ce take fad'a min wai tana son shiga koyon d'inki, ka san nan kusa da mu akwai wata dake koyawa mata d'inki."

Murmushi ta saki a fuskarta ta ci gaba da fad'in "Na fad'a mata ta yi yarinta dayawa, amma kuma na ga tana da k'ok'ari wajen yin d'inki, dan kullum da abubuwan take fama a gidan nan."

Aje cokalin da yake cin abinci ya yi ya kalleta sosai yace "Safiya, gaba d'aya alamu nuna min suke ke kike hana yarinyar nan maida hankali kan karatunta, 'yata ta cikina ta yi d'inki? D'inki fa ?"

Girgiza kai yayi dake nuna abun ya ma bashi dariya yace "A tarihin gidanmu ko mai siyar da sutura babu, ta ya zan bar yata ta fara koyon d'inki?"

Kallonta yayi da kyau yace "Kina ji na? Saleema idan har ba ta fito min a matsayin babbar likitar mata ba to ta zo min a matsayin wata engineer ko babbar 'yar jarida, idan fa hakan ya gagara ne zan so ta zama hazik'ar mace a cikin siyasa."

Kallon Hadeeya yayi dake cin abinci yace "Me kike so ki zama a rayuwa?"

Cike da iyayi ta waina idonta kafin tace "Abba, ni dai gaskiya irin aikin Momy nake so, irin yanda take shigarta idan za ta tafi, da jajircewarta a kan aiki yana birgeni sosai."

Jinjina kai yayi cike da gamsuwa ya kalli Hameeda yace "Ke kuma fa yar Abba?"

Cike da yarinta tace "Abba, ni dai so nake na yi dogon karatu akan harkar tattalin arziki."

Cike da jin dad'i ya jinjina kai har da murmusawa yace "Da kyau 'yata, wannan shi ne abinda ya kamata."

Hamdeeya ya kalla da fara' a yace "Autata dai na san bata da matsala ko?"

Cike da k'uruciya Hamdeeya tace "Abba ni dai malama zan zama."

Dariya yayi yace "Hakan ma burine mai kyau."

Kallon Ardayi yayi wacce duk abun nan da ake hankalinta na kan wayarta yace "Masoyiyata kin ji fa, dan haka sai ki k'ara zage damtse."

D'an murmushin yak'e tayi dan hankalinta ba nan yake ba tace "Dole mana, kar ka damu masoyi."

Sai lokacin ya sake kallon Safiya dake ta kallonshi da mamaki yace "Kin dai ji, dan haka ke ma idan za ki d'ora ta a turbar da ta dace ki fara tun yanzu, amma bana son maganar shirmen banza da wofi."


*Bayan kwana biyu*


Hannunta ya kamo suna shigowa d'akin ya kalli Safiya dake gyara gadonta yace "Yanzu wannan shirin da shi za mu tafi da ita? Baki ga yanda yan uwanta suka shirya ba?"

Juyowa tayi tana kallonshi sai kuma ta kalli shirin jikin Saleema, doguwar riga ce ta shadda jikinta mai kwalliya sai hijab da ya dace da kayan tare da takalminta masu kyau da tsada, sake kallonshi tayi tace" Me ye aibun shirinta?"

D'an gajeran tsaki yayi yace" Kin wani saka mata manyan kaya, baki ga na yan uwanta bane?"

D'an kawar da kai tayi tace" Ka yi hak'uri, amma gaskiya bana sha'awar koyawa yarinyata fitar da tsiraici tun tana k'arama, gwara ta san hijab shine rufin sirrinta."

Cikin jin haushi yace" Ke da anyi magana sai ki nuna kin fi kowa tsoron Allah, to wannan 'yar abar wani ne zai yi sha'awarta ? Ina ma abun yake a nan?"

Wani tsaki ya sake yi yace" Kinga dan Allah d'auko min wasu kayan na canza mata idan ke ba zaki iya ba."

Jinjina kai tayi ba yanda za ta yi ta d'auko mishi riga ta kanti ta kawo, da kanshi ya fara k'ok'arin taimakawa Saleema, hakan yasa ta fara kakkare jikinta cike da kunya saboda rashin sabo, yana gama taimaka mata ta saka kayan ya kama hannunta za su fita, da sauri ta kalleshi tace "Abba hijabina?"

Harara ya wurga mata yace "Dallah muje malama."

Haka ya ja hannunta suka fice a gidan tana ta jin ta wata iri ba yanda ta saba fita ba. Wajen taron ma da suka isa kasa sakewa ta yi har matar abokin na shi wacce take murnar shagalin k'arin shekarar d'aya daga cikin yaranta ta masa magana ko me yake damunta, cike da takaicin halin k'auyenci da dabbanci a ganinshi na Saleema yace "Ba komai, iskanci ne kawai."

Dan a ganinshi k'auyenci ne duba da yan uwanta da sauran yaran yanda suka sake cikin yara yan uwansu suna ta tik'ar rawa dalilin k'aton redion da aka saka musu, sai ita da ba ta waye ba za ta wani had'e wuri d'aya kamar mai jin mugun sanyi.

Dawowarsu ke da wuya ya samu kiran waya daga malamin Saleema, dan ba ya kirashi da malaminsu duka ba saboda su Hadeeya sai sun ga dama suke zuwa makarantar islamiyya, Saleema ce dai babu abinda ke hanata zuwa dan ba ciwo ba, bayan sun gaisa a tsanake da mutumtawa malamin ke fad'a masa "Alhaji dama akan Saleema ne, shiyasa na ce bari na kira muyi magana."

Gabanshi ne ya fad'i dan abu d'aya tunaninshi ya bashi, wato a islamiyar ma bata gane komai? A nutse malamin ya d'ora da "Dama Saleema na d'aya daga cikin hazik'an yara a islamiyar nan, kuma abun birgewa yanda take da matuk'ar fahimta akan ilimin hadith, to dama akwai lokacin da aka ware ga maye da suke d'aukar karatun hadith, shine nake neman alfarma ko za'a lamunce mata sai ta dinga zuwa lokacin da za'a yi darasin? Zai zama idan an tashi k'arfe sha biyu na rana ita ba za ta koma gida ba za su wuce ajin d'aukar hadith, k'arfe d'aya da rabi sai a sallamesu."

Shiru Alhaji Yusuf ya yi yana tunanin abinda malamin ya fad'a, sai shed'an ke raya masa to dama tana gane karatun islamiya na boko ne ba ta ganewa? Sai kawai zuciyarshi ta raya mishi ai da gangan ne ta ke k'in aje hankalin a boko, tunda gashi tana gane hadith. Jinjina kai kawai ya yi yace "Shikenan."

Ya kashe wayar da tunanin matakin da zai d'auka, har ya yanke hukunci bai sanar da kowa abinda zuciyarsa ta yanke masa ba, yana jiran lokaci yayi ya zartar kawai kowa ya gani ya kuma sani.



*Washe gari*


Ganin ta dawo da kuka yasa ta tarbeta cike da kulawa tana tambayarta "Saleema, me ya faru ? Wa ya dakeki?"

D'aga kanta tayi tace "Abba ne a waje yace wai na dawo, kuma wai daga yau ba zan sake zuwa makarantar ba."

Da mamaki sosai a fuskarta tace "Ban gane ba za ki sake zuwa ba? Me kika masa?"

Cikin kuka tace "Nima ban sani ba, kawai koroni yayi."

Numfashi ta sauke tana ji akwai dai wani abun, amma haka kawai ba zai hanata zuwa makaranta ba, nuna mata gado tayi tace "Zauna nan, bari na je na ji me ki ka yi."

Za ta fice a d'akin Saleema tace "Mama idan ya ce wani abu na masa ki bashi hak'uri dan Allah."

Murmushi ta sakar mata sannan ta fice a d'akin, a farfajiyar ta sameshi zaune da na'urarsa yana dannawa, kujerar gefenshi ta ja ta zauna a nutse tace "Abban Hajia, ta sameni yanzu take fad'a min wai ka hanata zuwa islamiya, shine na ce na san dai wani laifin ta yi ko?"

Ba tare da ya kalleta ba fuska a d'aure yace "Ba ta yi laifi ba, kawai dai na soke zuwa makarantar ne, ba kuma ita kad'ai ba har da yan uwanta."

Hankali tashe zuciyarta a kid'ime ta furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!"

Da sauri ya juyo yana kallon da tunanin me ye na salatin? A razane tace "Alhaji, islamiyar fa ka ce ka dakatar da zuwa?"

A k'ufule yace "Haka na fad'a Safiya, ko kina da ja ne?"

Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke tace "Me ya yi zafi haka? Islamiya?"

Mik'ewa yayi a hassale ya d'auki wayarshi da na'urar sannan ya kalleta yace "Na riga da na gama yanke hukunci, na kula wannan karatun ne ya ke d'auke mata hankali tana kasa fahimtar wanda nake so ta fahimta, shiyasa na ciresu gaba d'ayansu dan hankalinsu ya tsaya wuri d'aya."

Mik'ewa tayi tsaye tace "U'uzubillah! Alhaji ka san me kake shirin aikatawa kuwa? Kai tsaye fa kamar kana k'ok'arin ingiza yaranka ne ga mummunar hanyar da ba zata b'illar da su ko ina ba sai halaka."

Cike da shashantar da zancen ya kalleta sama da k'asa yace "Allah ko?"

Sai kuma ya ja tsaki ya wuce ya barta tsaye yana fad'in "A ganinki kenan."

Da kallo ta bishi tana jin yanda hankalinta ke sake tashi dan gaskiya wannan babban bala'i neke tunkarosu, islamiya ? Inda za'a koya wa yaran sanin ubangijinsu? Shi ne zai tsigesu saboda karatun da anfaninsa iya duniya ne kawai, shi ma a haka ba kowa da yayi shi ke morarshi ba.

Kamar wasa sai kuwa maganar nan ta zama babba, Safiya da abun ya dameta ta yi iya k'ok'arinta wajen sake tuntub'arshi, amma a k'arshe mummunan kashedi ya kirta mata cewa zai d'auki tsatsauran matakin da ya dace a kan ta idan ta sake mishi maganar nan, hakn yasa ta tuntub'i wanda take ganin sun isa su fad'a masa su ji.

Duk shekarun da suka d'auka haka ba ta tab'a faruwa ba, amma sai dayawa suke ganin laifinta dan su ma bokon suka sha suka k'oshi, dan haka suke ganin me ye a ciki to? Abinda yake ganin ya fi mishi ne ya yi sai su zuba mishi ido, wannan tashin hankalin da zulumin da ta shiga na tsawon sati biyu ya haddasa mata rashin cin abinci da muguwar damuwar da ta kwantar da ita rashin lafiya, wanda daga k'arshe cikin jikinta ya zube a wata asuba ta idar da sallah.

Kamar kowane lokaci idan haka ta faru asibiti ya kaita aka mata wankin ciki, daga bisani lokitocin suka basu shawarar ko dai za'a juyar da mahaifarta ne saboda tana daf da kaiwa matakin da hakan zai iya cutar da ita, amma sam Alhaji Yusuf ya ce bai yarda dan gaskiya har yanzu ya na so ya ga wani sabon jaririn daga wajen Safiya, saboda mata ce da ba ya shakka ko k'yamar sake had'a zuri'a da ita, haka kuma ya yi bak'in cikin rasa wannan cikin da yake ganin har ya wuce wata uku amma gashi shi ma ya tafi, karo na bakwai kenan.


*SHEKARA D'AYA*



Hankali tashe ta k'araso wajen mai gadin tana fad'in "Sani dan Allah ba ka ga in da Saleema ta yi ba?"

A ladabce ya girgiza kai yace "Tun d'azu data fita dai nan ta yi..." Ya nuna mata hannunshi na dama ya d'ora da "To kuma ban ga dawowarta ba har yanzu."

Cike da d'imuwa tace "To ka ga dan Allah ka daure ka duba min ita a shagon nan na bayanmu, nan na aiketa ta siyo min madara ga shi har yanzu ba ta dawowa ba, ina tsoron kar wani abun ne ya sameta."

Cike da son kwantar mata da hankali yace "A'a in sha Allah ma ba abin da ya faru, bari na dubo na gani."

Cikin damuwa ta amsa da "Yawwa nago..."

Mak'alewa sauran maganar ta yi sakamakon tsayawar motar Alhaji Yusuf a k'ofar gidan, da sauri ta dawo cikin gida ta tunkari komawa falo, ba wai dan babu hijabi a jikinta ba ko tana tunanin ranshi ya b'ace kan tana magana da mai gadin shi, sam wannan ba ya a tsarinshi dama, hasalima da kan shi yake fita tare da su ya zab'ar musu kalar mayafan da yake so su saka. Tashin hankalin shine aikin da ya saka ta yi masa ba ta kammala ba gashi har ya dawo, shi kuma mutum ne da baya son wasa da cikinshi, duk yanda yake girmamaka indai za kai masa wasa da cikinshi to za ku samu matsala, dalilin da yasa kenan ko Ardayi na wajen aikinta ya kan umarceta ta sarrafa mi shi wani abun, dan baya son cin komai a waje.

Tun ba ta gama shigewa falon ba muryarshi ta dakatar da ita sanda yake fad'in "Me kike nema a waje?"

Cak

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login